*ASM Bk2030*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……….Tun da suka hau hanya ba wanda ya tanka ma wani Fatuu ta juyar da kanta tana kallon gefe yayin da Khalid ke driving sai dae a akai akai yake d’an juyowa ya kalli Fatun, hannu ya kai ya kunna music ya rage volume sosae kidan na tashi kad’an kad’an, har lokacin kuma bata kalleshi ba can ya juya ya kai hannu ya kamo hannunta da ta d’aura akan lap d’inta a firgice ta juyo ta kalleshi duk da dare ne tana d’an ganin fuskar shi sakamakon hasken fitilun wasu Motocin dake wucewa, ganin murmushin da yake saki yasa ta tamke fuska ta fizge hannun nata ta k’ara juyar da fuskarta, bai tanka mata ba ya kai hannu yana kokarin bud’e glove box jin k’arar bud’ewa yasa ta d’an juyo tana kallon abunda yake wani abu ya fiddo ya maida wurin ya rufe saidae bata gane mi ya d’aukko ba hakan yasa ta sake juyawa, wani d’an babban kwali ya fiddo sam nima na kasa gane na miye har saida ya bud’e yasa baki ya ciro cigarette guda, ashe kwalin sigari ne saidae ina tunanin ba irin tamu bace ta nan daga yanayin kwalin da kuma yanayin shi kan shi karan sigarin, amfani yay da lighter dake a cikin kwalin ya kunna kafin ya mayar da kwalin ya fara sha idon shi a kan hanya, a hankali warin ta ya fara kaima hancin Fatuu ziyara can ta juyo kaman an zabure ta lokacin da ta tabbatar daga cikin Motar warin yake, a razane take kallon Khalid dake smoking hankalin shi kwance idon shi akan hanya, wani irin bugu kirjin Fatuu ke yi gaba d’aya hankalin ta ya tashi nan take ta fara gasgata zancen su Zakiyya na yana shaye shaye, duk kallon da take mashi yana gani ta wutsiyar idon shi can ya d’an juya yana murmushi yace “kin k’i man hira as if am alone in d car dat’s why na fiddo abunda zai taya ni hiran” sam ta kasa ce mashi komai bin shi da ido kawae take, cigaba da driving yay yana shan abun shi cike da k’warewa wasu kwalla masu zafi ne suka ciko a idanunta a rayuwarta ta tsani ta ga mutum na shan sigari ko warin ta ma bata so don ma wannan bata k’auri sosae amman duk da haka har zuciyarta ta fara tashi hakan yasa ta juya da sauri tasa gefen gyalenta ta toshe hancinta da bakinta lokacin kuma ta samu damar fara zubda kwallan da suka taran mata, Har suka k’araso bata sani ba jin ya tsaya yasa ta d’ago da sauri tana kallon wurin da k’yar ta gane inda ya parker wato a farkon gidan bai je kopar gidan ba daga inda suke tana hango inda teburin Kamalu na rake yake da sauran Mutane dake zaune a kofar gidan harda yara dake wasa, da sauri ta kai hannu zata bud’e ta fita hakanan taji bata yarda da inda yay parking d’in ba aikuwa kafin ta bud’en taji carabb ya kamo hannun ta a fusace ta juya ta kalleshi tace ya sakar mata hannu ta tafi, shiru kaman bazai tanka mata ba tana ta kiciniyar kwacewa ta kasa don ba k’aramin ruko yay ma hannun nata ba ganin bata iya fizge hannun yasa ta fara mashi magiya kan ya kyaleta cikin kararrar murya, d’an murmushi mai sauti yay kafin yace “Wife why ain’t u romantic at all? ko ni driver d’in ki ne ya kamata ki fita kawae ba tare da kin man godiya ba…” Tun kafin ya k’arasa da sauri tace “To Nagode” yar dariya yay ganin duk ta rud’e yace “ni ai ba driver en bane I just give u an example ba wai godiyar nike so ba at least a single kiss da zai nuna u’r grateful” waro ido tay ya wani lumshe mata ido yana pointing lips d’in shi da sam basu yi kalan na masu shaye shaye ba da yake yana kula da hakan sosae, da sauri ta girgiza mashi kai alamar bazata yi ba sai kace ba yanzu a gabanta ya gama shan sigari ba ai koma bai sha ba bazata yi ba tunda tasan ba kyau, kokarin janyo ta ya fara yi ta toge hakan yasa ya d’an matso gab da ita kiciniyar kwace hannunta taci gaba da yi tana cikin hakan ba zato ba tsammani sai jin d’ayan hannunshi tay Saman boobs d’inta wata kalan gigicewa tay don abu ne da ba wanda ya ta6a mata hakan koda kuwa yar uwarta mace to mima zai kai hannun wata ko wani kan chest d’inta ita da ba yar iska ba, ganin gaba d’aya hankalin ta ya koma kan cire hannun na shi yasa ya shammace ta ya saki hannunta d’aya ruk’e ya kai hannun nashi ya tallabo kan ta ya had’e fuskokin su tana bud’e baki da niyyar yin Magana kuma ya had’e lips d’in su, iya k’ok’ari Fatuu tayi na ta janye bakinta abun ya gagara sai gunji take tana gurnani had’i da bugun shi saida yay sucking up duk wani saliva na bakinta sannan ya saki kan nata ya maida nashi jikin headrest breathing rapidly, a gigice ta bud’e Motar ta fice ta duk’e anan kan kace mi ta fara Kwara amai kaman yan cikinta zasu fito tana ji ya ja Motar ya tafi bayan ya tillo mata ledar turarurrukan ta, saida ta amayar da komae na cikinta a wurin kafin tasa wani irin kuka mai cin rai wannan wane irin bala’e ne a yanzu kam ta gasgata zancen su zakiyya gaba d’aya in ba d’an iska bane mi zai sa yayi mata hakan, da kanta ta rarrashi kanta ta mik’e kaman bazata d’auki ledan ba sai kuma ta d’auka kallabinta a kwance tana tafiya tana goge kwallan da suka k’i daina zubowa had’i da tofar da yawu sai sheshsheka take wani iri take jinta duk ba k’arfi a jikinta, har ta shige ba wanda ya lura da ita lokacin da ta shiga falo su Yadikko duk suna zaune dasu Mino da k’yar ta k’ak’alo d’an murmushin dole tayi masu sannu su Mino na mata sannu da zuwa cikin wasa Yadikko tace ai tayi zaton a can zata kwana bata ce komae ba ta wuce cikin d’akin tana shiga ta cire gyalen ta don duk kyankyamin shi take don sai take jin k’aurin sigarin da ya sha a jikin shi, aje ledar hannunta tay ta wuce band’aki don yin wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar bacci da ta wuce gwuiwar ta ta haye gado zuciyarta nata tariyo mata abunda ya faru duk sai take ji ta tsangwami kanta ba kamar bakin ta ji take kaman ta cuzge shi duk kuwa da irin dirzar da ta yi mashi a bathroom, tana kwancen Yadikko ta shigo dama ta shigo d’azun ta taras tana wanka a bakin gadon ta zauna da d’an murmushi tace “an dawo lafiya?” a hankali tace mata lafiya lou, shiru ta d’an yi sai kuma ta k’ara cewa “Ya yan gidan nasu sun yi maraba da ke kuwa?” Kai ta d’aga mata kafin tace Momynsu na gaidata da fara’a tace tana amsawa Fatun ta lumshe idanunta jin kwalla na niyyar zubo mata yadikko ta bita da kallo can tace “Ya akai ne na gan ki duk wani iri ga idon ki kaman kin yi kuka ko dae kin 6oye man wani abu” bud’e idon tay ta d’an yamutsa fuska tace mata har ta fara bacci ne sannan aka maido ta cike da gamsuwa yadikkon ta jinjina kai tace to ta tashi ta ci Abinci kafin taci gaba da baccin, tana son ci don cikinta ba komae amman da ta tuna abunda Khalid yay mata sai taji bata iya ci tace mata a k’oshe take kawai, tana kwance bayan fitar Yadikko sai ga sak’o ya shigo wayarta ta d’auka tana dubawa bata gane wanda ya turo ba saida ta shiga ta fara karantawa ta gane Khalid ne Don bata yi saving number d’in tashi ba, sak’on ban hak’uri ne ya turo mata ya nuna son da yake mata ne yasa ya kasa resisting har hakan ta faru kuma kar ta damu hakan ba wani abu bane tunda ya biya sadakin ta ba yaudarar ta yake ba amman tun da bata so bazai k’ara mata ba har sai an d’aura masu aure yana fatan zata yafe mashi sosae yay mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali, ta dad’e tana kallon sak’on kafin ta kife wayar, ba laifi ta d’an ji sanyi a ranta ba kamar da yace bazai sake mata hakan ba sai dae kuma abunda ya fi damunta da yace sai an d’aura masu aure don ita yanzu k’yamar shi ma take can sai gashi ya kira K’in picking tay sai bayan da ta yanke wani kiran ya sake shigowa sannan tay picking ta kara wayar a kunnanta ba tare da ta ce komae ba sanin tana sauraran shi yasa yaci gaba da bata hakuri yana kwantar mata da hankali har dae ta saukko ta fara tunanin k’ilan da gaske ne ya canza hali kamar yadda Mahaifin shi ya sanar da Baffanta dama kuma yadikko tace duk zargi ne abun da su zakiyya suka fad’a ba wanda ya tabbatar, da wannan tunanin ta d’an sake mashi suka d’an yi hira kafin daga baya yace ta kwanta saida Safe, Washe gari Juma’a sai gashi yazo da daddare bayan sallar Isha koda ta fita yana zaune a Mota yace ta shigo tace a’a ba sai ta shiga ba yana yar dariya yace to shi bai iya fitowa ya tsaya kaman wani d’an k’auyen su, k’arshe da yaga ta toge duk da yace ba abunda zai mata sai yace ta shigo sai tabar kopar bud’e sannan ta amince, Ranar Lahadi wurin sallar Azahar aka kawo lefen Fatuu dankara dankaran akwatuna guda takwas set biyu masu hud’u hudu shak’e da kaya na gani na fad’a masu kyau da tsada abun ka da aikin Naira gaba d’aya wad’anda za’a d’inka har an gama, a d’akin Yaya aka kai su nan kowa ke zuwa gani sai yabawa ake ana zuba k’auyanci, sam Fatuu bata yi farin cikin kayan ba da su Mino suka zo suna fad’a mata bin su da ido kawae take yanzu dae ta idasa tabbatarwa da gaske Aure za’ayi mata, wurin k’arfe ukku na rana Khalid ya kirata bayan ta d’aga ya sanar da ita zai zo bayan sallar la’asar zasu d’an je wani wuri, shiru ta d’an yi mashi a ranta ta shiga tunanin ina kuma zasu har saida yace bata ji bane sannan tana tura baki tace ina zasu yace bata ji yace wani wuri zasu bane, sam ran ta bai kwanta da fitar ba don ita yanzu tsoron shi take hakan yasa tace mashi ita bazata je ko ina ba, shu’umin murmushin shi yay yace Ok tunda shi bai isa da ita ba bari ya kira wanda ya isa dashi ya sata ta bi shi nan take ta gane Ard’o zai fad’a mawa k’arshen ta kuma ya sanar da Baffanta ta san kuma bazai ji dad’in hakan ba, ba yadda ta iya tace mashi zata shirya tamkar ta fasa ihu, bayan la’asar ta gama shiryawa tasa jallabiya bak’a tay rolling veil d’in tana gamawa bada dad’ewa ba sai gashi ya kirata ya sanar da ita yana a kopar gida, a Falo ta samu yadikko tace mata sai ta dawo da yake ta sanar da ita game da fitar tace a dawo lpy, Yana zaune a Mota ta fito ya k’ura mata ido har ta k’arasa ta bud’e gaban ta shiga fuskarta a d’aure ta gaishe dashi yana murmushi ya amsa yace ta rufe su tafi bin shi da kallo tay tace “Wai ina zamu ne?” d’age gira yay yace “zan saido ki ne” tura baki tay ba tare da ta ce komae ba ganin bata da niyyar rufe kopar yace mata zai kai ta ta gaisa da wasu ne sannan ta rufe yaja suka tafi, Yar tafiya sukae suka k’araso bakin garin daidai k’aton gidan Gonar su ya karya kan Motar ya shige gate d’in farko dake a bud’e mai gadi na d’aga mashi hannu yay mashi horn ba tare da ya tsaya ba, wata tafiyar suka k’ara yi kafin suka sake isowa wani gate d’in na fence ya tsaida Motar ya fita ya bud’e Fatuu nata bin wurin da ido bayan ya dawo yaja suka kutsa ciki, wurin parking ya nufa ya parker Motar ya kalleta da Murmushi yace ta fito, a hankali ta kai hannu ta bud’e Motar bayan ta fita tay tsaye tana k’are ma wurin kallo shi kuma ya koma yaje ya rufe gate d’in tana cikin kallon wurin zuciyarta ta ayyana mata nan ai kaman gidan Gonar su ne dammm kirjinta ya buga sam ita da farko bata gane ba sai yanzu bayan ya dawo in da take tsaye yace mata su shiga yay Maganar yana nuna mata k’aton Flat d’in dake gaban su togewa tay tana bin shi da ido yace “Let go in wife” tana tura baki tace “Amman ai gidan kaman ba kowa” yana murmushi yace waya gaya mata ba kowa bata ga gida bane lafiya lou, shiru tay tana nazari lokacin Maganar yadikko da ta ce har Chairman d’in da Matan shi suna zuwa Hutu nan ta fad’o mata hakan yasa tay tunanin k’ilan da gasken akwae Mutane ganin ta d’aga k’afa yasa yay gaba yace su je tabi bayan shi suka nufi entry d’in, Babban falo ne mai d’auke da duk wani abu da zaka samu a falon yan gayu akwae corridors a 6angaren dama da hagu bin falon da kallo Fatuu tay Khalid d’in ya nuna mata ciki wajen da Sofas suke yace suje, zaunawa yay kan 3 seater ya nuna mata gefen shi yace ta zauna tay tsaye tana kallon shi kafin tace mashi ina wad’anda zasu gaisa d’in yace ta zauna mana ko zai cinye ta ne kaman bazata zaunan ba sai kuma ta d’an d’osana ta zauna a d’arare tana ta kallon shi, yana ganin ta zauna ya fad’ad’a murmushin shi had’i da d’an kwantar da kan shi yace ko ita fa, shiru tay ganin kallon da yake mata yasa fuska a d’aure tace “Wai ina Mutanen?” Hannu ya kai ya shafi sumar shi still da murmushi akan fuskar shi ya fara Magana “Wife ba fa wasu da zaku gaisa I just want us to spend time together yadda zamu k’ara fahimtar juna don naga kin k’i sakin jiki da ni gashi nan da few days zamu zama Couples” wani kallo ta bi shi da shi baki bud’e shi kuma sai faman lumshe mata ido yake can ya fara matsawa wurinta tay zumbur ta mik’e ta kumbura baki a fad’ace tace “shine duk gidan mu bai isa ba sai ka kawo ni nan harda yi man k’arya to ni dae ka tashi ka maida ni ko in tafiya ta tunda nasan hanya!” d’an ta6e baki yay kawae bai ce mata komae ba aikuwa a fusace ta juya ta nufi hanyar fita daga falon saidae tana kaiwa kopar taji ta a rufe gam wani bugu kirjinta yay kenan kulle kopar yay bayan sun shigo, juyawa tay ta kalle shi ko kallon ta bai yi ba hakan yasa jikinta mutuwa ta nufi cikin Falon gefen kujerar da yake ta tsaya idon ta a kan shi kamar zatayi kuka tace “Don girman Allah kai hak’uri ka maida ni gida” bai kalleta ba sai ma cigaba da latsa wayar shi da yake yay kwalla ne suka fara zubo mata taci gaba da yi mashi magiya saida ya mula yasha iska sannan ya d’aga ido ya kalleta cikin kashe murya yace “Don kin ga na damu da ke shiyasa kike taking advantage d’in hakan kina neman wahalar dani ko? Kuma ni kike ce ma makaryaci don kawae na buk’aci mu kasance tare dama ashe har yanzu baki daina rashin kunya ba?” d’an girgiza kai tay tace “a’a kai kace zamu gaisa da wasu ne ai da ka fad’i man gaskiya” kya6e baki yay ya d’age gira yace “in na fad’i maki gaskiya zaki zo ne?” shiru tay tana ci gaba da yamutsa fuska yaci gaba da cewa “Zuwa yanzu yakamata ki d’auke ni kaman yadda na d’auke ki just 6 days ya rage a d’aura mana aure what’s there don na bukaci mu kasance tare, da wasu ne ma yanzu tuni sun d’auki kan su matsayin ma’aurata, kodae ban yi maki bane?” Wani wahalallan yawu ta had’iya a halin yanzu dole ta bi shi gudun kada yay mata wani abun ganin daga ita sai shi gashi ya kulle kopa, sake tambayarta yay bai yi mata bane a dabarbarce tace a’a yayi mata yace to ta kwantar da hankalin ta ba wani abu zai mata ba kuma nan gidan da take gani nan za’a kawo ta don haka gidan tane ya nuna mata gefe inda ta tashi yace ta zauna suyi hira tace to sai yaushe zasu tafi yace bada jimawa ba, bata da yadda zatayi dole ta koma ta zauna ya kai hannu kan c-table ya d’auki remote ya kunna masu kallo, bayan ya koma ya zauna yana murmushi yace mata miye labari a hankali tace mashi babu ya tambayi taga kaya akwae abunda babu tace mashi kawae akwae komae duk kuwa da bata ma ga kayan ba, tambayarta yay abubuwan da take so da wanda bata so ta kasa bashi amsa yace shi bari ya fad’i mata ya shiga lissafo mata tana dae ta kallon shi can ya tambayeta wai tana da saurayi farko shiru tay mashi don tsoron bashi amsa take ganin hakan yasa shi cewa in fa tana son ya maida ta gida ta bud’e baki ta rink’a mashi Magana ta girgiza mashi kai a hankali tace bata da shi yana dariya yace ta dai fad’a ne ya za’ai mace kaman ta ace bata da saurayi yace “Ni kin ga inada yan mata saidae ba wadda ta yi man matsayin Matar aure na don duk basu da qualities irin naki” sototo tay tana kallon shi haka ya ci gaba da bata mamaki ta hanyar yi mata kalamai masu d’aure kai har dae ta d’an fara sakewa sai gashi har tana yin d’an murmushi in ya kama can ya mik’e yace bari ya d’aukko masu lemu kishi yake ji itama tana bak’uwa ya barta ba ko ruwa duk da nan d’in gidanta ne, bada jimawa ba ya dawo ruk’e da babbar robar Fanta da glass cups guda biyu ya d’aura su akan c-table ya bud’e ya fara tsiyayawa cike da tsokana yake fad’in “nasan Fulani da son jan lemu” kallon shi kawae take sai kace shi ba bafullatanin bane, bayan ya zuba ko ina ya mik’a mata cup d’aya ta amsa ta ruk’e shima ya d’auki d’ayan ya koma ya zauna ya kai baki ya fara sha, ganin ta ruk’e wanda ya batan yasa shi ce mata ta sha mana ko tsoron sha take bata ga shima ya sha ba jin hakan yasa ta kai cup d’in ta fara sha……
***** *****
Bayan Wani Lokaci, A hankali ta fara motsa idanunta da sukae mata nauyi kafin da k’yar ta idasa waresu kan Pop ceiling d’in da take facing, k’ura ido tay tana kallo kaman mai nazarin wani abu can ta mik’e zaune zumbur da mamaki ta kai idonta saman gadon da take zaune kafin ta bi cikin d’akin da kallo with extreme surprise tunanin abunda ya kawo ta d’akin ta shiga yi da yadda akai har ta kwanta kan gadon, lokaci guda kwakwalwarta ta fara tariyo mata abubuwan da suka faru kafin yanzu, to miya faru da ita ne bayan ta sha lemun da ya bata? ta jefa ma kanta tambaya, wani irin bugu k’irjinta yay da sauri ta kai idonta jikinta ta fara bin kanta da kallo abun mamakin lafiya lou rigarta na a jikinta haka dogon skin tight d’in da ta sa a ciki shima yana nan hannu ta kai ta shafi kanta dake bud’e amman gashinta na a fake shima, kan ta ya gama d’aurewa tana cikin hakan taji an turo kopar da sauri ta kai idonta wurin Khalid ne ya shigo jikinshi sanye da singlet sai wandon jeans d’in da yazo da shi suna had’a ido ya sakar mata k’ayataccen murmushi ya tsaya a jikin kopar ya goya hannuwan shi a kirji yace mata ta tashi kenan, tabdijancan! ido waje take kallon shi murya na rawa tace “Ya akai nazo nan waya kawo ni??” d’an yamutsa baki yay yana lumshe ido yace “kin yi bacci ne and u’w not comfortable there har kina niyyar fad’owa shine na maido ki nan” k’ara zaro ido tay ta furta Kalmar ya maido tan nan da ya fad’i, a kidi’me tace “to ya akai nayi baccin ni bansani ba?” d’an watsa hannuwa yay alamar bai sani ba ta k’ura mashi ido alamar bata yadda ba can murya kaman zata yi kuka tace “Daga shan lemu sai bacci…” dakatawa tay tana tunani can ta tuno da maganin bacci da Kawu Amadu ya ta6a amso mata a rud’e tace “k…ko dae maganin bacci kasa man kai man wani abun???” d’an ta6e baki yay yace “u can check ur body” daga haka ya juya ya fita, da sauri ta saukko daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror tana kallon kanta ko zata ga wani canji amman bata ga komae ba da sauri ta d’aga rigarta sama ta k’ura ma k’irjinta ido boobs d’inta na acikin bra lafiya lau sakin rigar tay ta gwada yin tafiya don tasan in dae yayi mata wani abun a gurin zata gane amman bata ji komae ba lafiya lou take tafiya kasa yadda tay ta nufi wata k’opa da take tunanin toilet ne ta tura sai gashi toilet d’in ne ta shige, sosae ta duba under d’inta lafiya lau bata ga wani canji ba tsaye tay sam ta kasa yarda da bai mata wani abu ba don zuciyarta na raya mata wani abu yasa a cikin lemun nan, hakanan bazata yi nauyin baccin da har zai maido ta d’aki ba ba tare da ta farka ba tana haka taji wani abu na yawo cikin rigarta da sauri ta zura hannu ta jawo sai ganin hannun bra d’inta tay wani irin bugu kirjin ta ya fara yi ta zazzaro ido waje da sauri ta k’arasa gaban mirror d’in dake cikin wurin ta k’ara d’age rigar sama sai lokacin ta lura da bra d’in bata kamata sosae ba kamar yadda ta sata, hannu na rawa ta fiddo breast d’inta guda tana dubawa koda ta kalli nipple d’in da sauri tasa hannu ta rufe bakinta ganin yadda yay jajir da shi gashi ya fito sosae, wani irin kuka Fatuu ta saka tana fad’in ta shiga ukku ta bani ta lalace sakin rigar tay a fusace ta juya ta fita ta nufi falo, lokacin da ta shiga yana zaune ya kishingid’a jikin kujera ta tsaya gaban shi kaman an jefota cike da Masifa tace “Ashe abunda zaka aikata man kenan yasa ka kawo ni nan, dama an ce kai d’in manemin mata ne d’an shaye shaye kuma dama ban yarda da duk abubuwan da kake fad’a man ba, ba wani so na da kake yaudarata kawae kake kana son ka cutar dani don in kana sona da gaske bazaka man haka ba nima kuma ban son ka ban kaunar ka na tsaneka kuma bazan Aure ka ba wllh!!!” d’age gira yay yana kallonta da d’an murmushi hakan yasa ta k’ara k’ulewa taci gaba da zazzaga mashi Masifa har tana kiran shi da Mazinaci aikuwa tana fad’in hakan ya daka mata tsawa ya mik’e har saida ta d’an ja baya fuska tamke ya fara Magana “Kar ki k’ara kirana da wannan sunan! Ke in ni Mazinaci ne kina tunanin yadda na samu dama akan ki zan kyaleki ne iya hakan??” Duk da ta tsorata tay k’arfin halin cewa “ai duk d’aya ne miyasa zaka bud’e man jiki har ka ta6a man jikina!” tay Maganar kwalla na zubo mata, sassauta murya yay cikin sigar rarrashi yace “it’s just a romance wife and ba don na biya sadaki ba ba abunda zai sa in ta6a ki kuma duk laifin ki ne kin k’i ki saki jiki da ni, I truly love u shiyasa nike maki hakan kuma bai kamata ki tada hankalin ki ba komi nai maki ai ni zaki aura ko…….” A fusace tace “Allah ya kyauta! wllh bazan Aure ka ba na tsane ka kuma sai Allah ya saka man abunda kai man tunda dai ba d’aura mana aure akai ba” yar dariya yay ya girgiza kai yace “Do u think is as simple as u said?” banza tay mashi tana huci kwalla naci gaba da zubo mata yace “Look Wife ki bar wannan a tsakanin mu ba wani abu bane muje in maida ki” wani kallo take bin shi da shi cike da takaici ranta na mata wani irin suya ya wuce Bedroom d’in bada jimawa ba ya dawo ya maida rigar shi ya mik’a mata veil d’inta kaman bazata amsa ba yace ta amsa su tafi Magrib ta kusa in kuma zata kwana ne anan to, amsa tay ta yafa yay mata alamar suje tayi gaba yana bin ta a baya suka fita ba yadda ta iya ba don ta so ba ta shiga Motar don kuwa akwae tafiya ga Magrib tayi, tunda suka hau hanya take sheshsheka yana bata hak’uri had’i da nuna mata ba fa wani abu bane shi yanzu ma ji yay ya k’ara sonta don gaba d’aya yadda yake son Matar shi ta kasance haka take, suna isowa ta bud’e Motar ko rufewa ba tayi ba tay gaba, Lokacin da ta shiga falon iske Yadikko tay tana salla ta wuce uwar d’akan ta fad’a kan gado tasa kuka mai cin rae yadikko na sallame sallar ta shigo d’akin da sauri don tun tana sallar take jiyo sauti kukanta, hayewa tay Saman gadon ta d’ago Fatun tana tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta kwashe komae ta fad’a mata tace “ban son shi yadikko don Allah ki fad’a ma Baffana kada a Aura man shi mutuwa zanyi in na aure shi, wllh da gaske d’an iska ne kuma yana shaye shaye” Ajiyar zuciya kawae yadikko ke saukewa tasan hakan ba mai yuwuwa bane ba kamar yanzu da ya rage saura yan kwanaki bikin, sosae ta shiga rarrashinta tana nuna mata lokaci ya k’ure kuma ita a tunaninta da gaske don ya biya sadakin yasa yay mata hakan tunda yana ganin saura yan kwanaki ta zama Matar shi ta daina damuwa tunda ma shi d’in da yay mata hakan zata Aura kuma da bai son ta abunda yafi hakan zai aikata mata ya dawo yace kuma bazai Aure ta ba, ita kanta yadikkon hankalinta ya tashi sosae da jin abunda ya faru hakanan ta danne don kar ta k’ara tada ma Fatun hankali da k’yar ta shawo kanta ta d’an saukko har taje tayo wanka ta dauro Alwala bayan ta gama sallar ta d’aga hannu tana kuka tana rokon Allah kan ya kawo mata Mafita, kasa cin Abinci tay duk da tana jin yunwa ta sha yar fura kawae, koda ta kwanta sak’e sak’e taci gaba da yi a ranta da ta tuna wani ya gane mata jiki har ya ta6ata sai wani kunci ya k’ara lullu6e ranta lokaci guda ta fara tunanin yadda zata guje ma Auran Khalid abunda bata ta6a tunanin yi ba tunda aka fara Maganar Auran sai yanzu……….
…
.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.