Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 72 Complete Novel

WECE CE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SEVENTY-TWO📍


“Wai kece mahaifiyar khaleel dama?”…
Cewar mami tana dubanta da mamaki itama….
A sanyaye momma tace;
“Eh nice”….
“Ikon Allah, bantaba ganin kamannin ba kuwa, sai yau dana ganku tare”….
Momma ta san mami ne tin a lokacin wani case da mami ta taba tsaya musu lokacin tana matsayin barrister, sun yi winning case din suka rabu cikin mutunc, abinda yasa tasan ta zama chief Justice kuma a news ta gani…..
Suna cikin haka sai ga bappa ya fito, har kasa momma ta duka ta gaidashi, har lokacin bata dena mamakin ganin mami ba, uwa uba kuma shi kansa bappa daya kasance public figure, in dai wayennan ne familyn fatima zainab toh lallai deen yayi gaskiya dayace bazata iya messing up dasu ba.. Cikin girmamawa khaleel ya gaida bappa da mami shima…
“Mahaifiyar khaleel ce bappa”…
Mami ta sanar da bappa bayan ya zauna….
“Oh masha Allah, sannu ko ”….
A sanyaye momma tace;
“Nasan zakuyi mamakin ganina, ba komai bane ya kawoni illa neman yafiyarku”….

Gyada kai bappa yayi ya cewa mami;
“Fatima kirawo jamila da ita zara’u”..
Mami bata dade da shiga ba sai gashi sun fito tare da baby tee da umm, baby tee na ganin momma ta juya zata koma ciki mami tayi saurin riko hannunta suka karasa suka zauna……
“Jam mahaifiyar khaleel ce, mom khaleel ga mahaifiyar fatima”….
Mami ta fara da introduction….
Kallon juna sukayi momma tayi saurin sadda kanta kasa, kallon umm kawai datayi sai da gabanta ya fadi saboda kana ganinta kaga wayayyiyar mace me ji da ilimi da gayu, in banda tsananin kamar da sukeyi da baby tee ma babu wanda zece ta haifi kamarta, wani ma sai ya dauka kanwartace ballantana mami da har tsayi deen ya fita, tabbas ta yarda da maganar deen dayace baby tee me nasaba da asali ce gaba da baya dan gabadaya mutanen dake zaune a gabanta sanannun mutane ne da suka shahara a duniya baki daya…..
Sai taji inama ta dawo da hannun agogo baya tayi treating baby tee right, hawaye ne suka silalo a saman fuskarta tayi saurin sharewa….
A hankali ta fuskanci baby tee tace;
“Bansani ba ko zaki iya yafe min fatima, bansani ba ko zan iya cin darajar khaleel, tabbas na cutarta dake fatima amma dake ubangiji ya nufeni da rahama tun a duniya na fara ganin sakayya, ko iya yanda khaleel yake bijirewa umarnina akanki ya isheni ishara, baya ga haka kuma wallahi nayi nadama, nayi nadamar duk wani mugun abu dana aikata a rayuwarki, nayi nadamar kin amincewar tarayyarku da khaleel danayi, amma ina rokonki ki yafemin badan halina ba dan Allah”…..
Ta karashe da fashewa da kuka….

“Karya kikeyi munafuka! Ko kin manta abinda kikace ne? Bappa wallahi karku yarda da muguwar matarnan”….
Cewar deen da shigowarsa parlourn kenan yaji maganganun momma na ban hakuri kamar ba ita bace ta gama zagin baby tee jiya ba, dama fita zeyi yace bari ya fara lekosu, kwata kwata besan bappa yazo ba sai yanzu yake ganinsa…..
“Kai saifu! Kai! Yi mana shiru! Jeka abunka, jeka”….
Bappa ya dakatar dashi yana nuna masa hanyar ya fita, dogon tsaki yaja sannan ya bar parlourn….
Tashi umm tayi tabar parlourn itama saboda gabadaya maganganun momma haushi suke bata, gani take kawai ta tuba ne saboda bata da option sannan irin muguntar da sukayiwa baby tee bata tinanin zata iya yafewa, ko zata yafe toh ba yanzu ba maybe nan gaba idan abun ya rage damunta…..
Gyaran murya bappa yayi yace;
“Shi dan adam dama ajizine sannan kuma kowa yana lefi saidai na wani yafi na wani tsauri, shi kanshi Allah muna masa lefi ya yafe bare mutum, saboda haka mu dai mun yafe nasan kuma zara’u na bame ruko bace, me yafiya ce kuma me tausayi ce, nasan Insha allahu ta yafe itama amma bari muji daga bakinta, ke zara’u dago ki fadi abinda ke ranki kinji ko?”….
Ya fadi hakanne saboda kar baby tee tayi tinanin ana mata dole tace ta yafe ne….
Lumshe ido tayi a hankali tace;
“Na yafe”….
Tabbas momma tayi gaskiya da tace batasani ba ko zata iya cin darajar khaleel, maganar gaskiya darajarsa taci sannan kuma bata taba riketa a ranta ba saboda ta rama itama, babu irin iskancin da bata mata sannan babu yanda batasa danta ya bijire mata ba..
“Haka kawai kin yafe babu abinda zakice?”….
Cewar bappa yana dubanta….
“Eh”….
“Toh Alhamdulillah, haka mukeso dama, ubangiji Allah ya kara kauda shedan a zukatanmu”…
“Ameen ameen”…
Nan bappa ya dora da nasiha me ratsa jiki da zuciya, sun kara kusan minti talatin kafin sukayi sallama suka tafi, kunyar idonsu bappa ne ya hana Khaleel personal magana da baby tee, ya dai tafi da niyar dawowa anjima….
A hanya momma take kara nunawa khaleel irin danasanin datayi, ta kuma masa alkawarin bazata kara kawo wata matsala tsakaninsa da baby tee ba….

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Be sha wahalar gane address din data bashi ba kasancewar ko wani gida a street din an rubuta house number din baro baro, sai da yayi parking sannan ya kirawota a waya, da murna tace masa gatanan zuwa tashigo dashi..
Zama a clkin mota yayi yana jiranta, haka kawai yake jinsa wani iri kamar yana aikata ba daidai ba, kamar yayi tafiyarsa kafin ta fito, amma kuma hakan be dace ba kuma ba girmansa bane, toh shi yanzu ya zaiyi mami ta bashi deadline, ko dazu saida ta kirasa a waya ta sake warning dinsa akan hakan, duk yanda yaso fahimtar da ita kuma taki fahimta, tace masa ta riga ta rantse sai yayi aure rana daya da baby tee and umm is not going back on her words akan maganar auren so gwara ya fara shiri, a dazun ne yayi finalizing decision dinsa, ze kawo musu wata ayi auren, bayan sati daya da auren ya samu reason me kyau ya saketa, inya so sai a kyaleshi yayi rayuwarsa, atleast an san ya taba auren so za’a shafa masa lafiya, amma kuma yanzu sai yake jin kamar ba daidai bane hakan, babu dadi yayi playing da feelings din yar mutane for his own selfish interest, babban solution din kawai rashin yin auren gabadaya, toh amma ya zeyi a fahimcesa a kyalesa?…..
A haka ta fito ta samesa, tana ganin motar taji aranta shine dukda tinted glass ne..
Ji kawai yayi an bude kofar motar ta daidai inda yake zaune a driver seat, a take yaji ta bashi wani katon red flag, ba kuma ze iya shiru ba….
“Why would you open door like that? Idan bani bane a ciki ba fa?”…
“Ai nasan kaine a cikin”….
Ta bashi amsa tana fadada murmushin dake kan fuskarta…..
“Karki sake hakan, it might not be me one day”….
“Okay, sannu da zuwa, mu shiga daga ciki”….
A wani katafaren parlor aka saukesa sai kamshin turaren huta yake me dadi, ga abinci nau’ika iri iri an jereshi a tsakiyan parlourn, guri ya samu ya zauna akan wani two sitter, yana zama suhaima tazo ta zauna dab dashi ta fara zuba;
“Welcome once again handsome, tinda kace in turo address din gidanmu na kasa samun nitsuwa saboda na dauka bazaka zo ba, sai yanzu naji zuciyata tayi sanyi, you have no idea how I have been longing to see you, bana tinanin ka ganeni amma zan fada maka ni wace yanzu, nice wadda muka hadu a Iranian International Airport, na maka magana ka mareni”…

Numfasawa tayi ta cigaba da cewa;
“Marin da naji kamar an ninkamin soyayyarka data kamani lokaci guda, tin daga wannan ranar ko baccin arziki banayi saboda tinaninka, kullum cikin bibiyarka nake amma nakasa samun kwakkwaren information akanka, har deferring semester sai da nayi akanka, cikin ikon Allah na dawo Nigeria bayan na samu information kana chan dama ni haifaffiyar yar kaduna ce amma anan abuja muke zaune da iyayena, it was almost surreal dana ganka a supermarket dinchan, a ranar inada tabbacin nafi kowa farinciki a duniya, zanso ace zaka iya bude zuciyata kaga irin son da nake maka, ina kuma fatan zaka karbi soyayyata hannu bibbiyu handsome”……

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Binta yayi da kallo feeling very awkward, haka kawai zuciyarsa take masa comparing dinta da baby tee dukda yasan hakan bashi da amfani, yasan baby tee itama sai a hankali amma babu yanda za’ayi tazo ta budewa mutum mota haka sannan yanda wannan yarinyar ta sake tana zubo zance sai yake ganin kamar hakan ba daidai bane, atleast tinda ya kawo kansa sai ta bari taji dame yazo amma sai ta saki baki tana zubo zance haka, gashi yanda tazo ta wani zauna dab dashi, baby tee kuwa duk da rashin jinta yasan she’s very classy, karyane ka ganta taba magana anyhow da mutum, uwa uba kuma miskilace mutane dayawa da sukazo welcome party dinta sai da sukayi complain bata kulasu, sai red flags dinsa akan suhaima ya kara yawa…
“Tashi ki koma chan ki zauna”….
Ya fada yana daure fuska, Allah ya sani shi baya ganin ayi ba daidai ba yayi shiru….
Ba musu ta tashi ta koma chan din saidai yanayin fuskarta ya chanza…

Suna tafiya bappa ya dubi mami yace;
“Fatima kirawo Jamila ku sameni a masaukina”….
“Toh bappa”….
Zaune suke a gaban bappa ko wacce zuciyarta rawa yake, sunsan dole kiran daya musu yanada nasaba da maganganun da sukayi dazu, basu dai sani ba ko yayi magana da mahaifiyarsu……
“Jamila meyasa kika fita dazu ana magana?”…..
Sunkuyar da kai kawai umm tayi batace komai ba….
“Inaso ki zama me yafiya a duniyarnan saboda babu wanda ya wuce aikata hakan in hakan na cikin kaddararsa, kowa yasan basu kyauta ba amma abinda hakuri be bamu ba tashin hankali baze bamu ba, bayaga haka mu musulmai ne kuma munyi imani da kaddara me kyau ko akasinta, kiyi hakuri ki sassauta zuciyarki ki maida komai ba komai ba, ita kanta zara’un tace ta yafe, idan kika cigaba da haka zata bijire itama, dan Allah ki gyara”….
“Insha Allahu bappa”…..
“Sannan mahaifiyarku tazo min da wani zancen, ko ince abinda kuka fadamata, kun nemi a kara muku lokaci kuma na amince saboda wani dalili da ba sai na fade shi ba amma fa ba baku lokaci zanyi sai sanda kuka ga dama ba, a’a yanke muku lokaci zanyi wanda na tabbata duk abinda kukeyi kun kammala kafin nan”…..
“Toh bappa,mungode”…
Suka hada baki wajan fada….
“Sai kuma daya maganar akan zara’u, dama shi yaran ya nemi a saka bikin tintini kuka ce a’a, saboda haka wannan ba matsala bane, zan tuntubi wakilinsa muji yanda za’ayi, ko haryanzu kina kan bakanki na sati biyun ne?”….
Ya karashe yana duban umm…..
“A’a bappa, wata daya dai ko biyu, duk yanda kukasa kawai”…..
“Shikenan”….
Nan suka cigaba da hirarsu na uba da yayansa…..

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

Kamar yanda eesha tayi alkawari sai gata tazo gidan da yamma, sai da ta fara gaisawa da mami da umm kafin ta tafi dakin baby tee, samunsu tayi suna zaune dasu twins suna hira abunsu, gaisawa sukayi sannan su twins suka fita suka barsu…..

Sai da suka fita eesha ta dubeta tace;
“Teema ya jikin?”….
“Da sauki”….
“Sai naga har kin dan fada”…
“Allah ko?”….
“Wallahi kuwa, gobe fa za’a fara bikin”……
Da mamaki baby tee;
“Kai haba, bikin har yazo”….
“Eh wallahi, ni fa so nayi ki bini mu tafi tare, sai bayan bikin sai ki dawo”….
“No kinsan bani da lafiya yanzu, saidai inzo gobe”…..
“Toh shikenan Allah ya kaimu”…..
sai bayan magrib baby tee ta rako eesha waje, basusan drivern eesha be karaso ba sai da suka tsaya a bakin gate, hira suka cigaba dayi akan bikin while suna jiran karasowansa…..

Parking deen yayi a daidai inda suke, yayi whining glass yana dubansu…..
Dawowarsa kenan daga inda yayi branching bayan ya bar gidansu suhaima, a dan maganar da sukayi da ita yake ganin wasu halaye a tattare da ita, amma kuma zato zububi koda gaskiya ne, so tari kuma mutanen da kake zargi sai ka samu ba ruwansu sai wanda baka yiwa kallon haka kuma ya baka kunya, ya dai yanke shawarar gwadata dukda kota chinye jarabawar ba lallai ya iya aurenta ba…
“Meye zaku tsaya akan titi kowa yazo wucewa yana kallonku?”…..
Yayi maganar yana kallon baby tee.. Amsa ta bashi da;
“Eesha ke jiran driver dinsu ya karaso, rakota nayi”…..
A bazata sukaji yace;
“Ta shigo in kaita”……
Kallon juna sukayi ko wacce da abinda ke ranta, eesha dai ta kasa boye murnarta, baby tee kuma bakace ga yanayin da take ciki ba….
Sallama eesha tayiwa baby tee ta tafi ta zagaya tashiga gefen me zaman banza ta zauna, baby tee ko tsabar yanda ta shiga tinani ko sallamar da eesha take mata bataji ba, kamar wacce aka zungura tace;
“Yaya nima zanje”…..
“A’a koma ciki baki da lafiya”…..
“Ni dai na samu sauki”….
“I don’t want to repeat myself, kawai ki koma”…..
Babu yanda ta iya haka ta juya zuciyarta a cunkushe da tinanini kala kala, meyasa yace ze kai eesha? Me zece mata da sauransu….
Sai da yaga tashige gida sannan yaja motar suka tafi….
Tuki yakeyi a nitse babu wanda yace wani abu har suka karasa gidansu eesha, godiya ta masa tana shirin fita taji motar a kulle, jiyowa tayi ta kallesa yana danna wayarsa yace;
“Do you still love me?”….
Kamar ta zuba ruwa a kasa tasha haka taji, tasan tambaya ce kawai amma babu yanda za’ayi mutum ya maka wannan tambayar haka kawai….
Baki na rawa tace;
“Yess..ss bazan taba dena sonka ba”….
Lock din motar ya bude motar yace;
“You can go”…..

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Fita tayi farinciki mamaye a zuciyarta da fuskarta, ko parlour bata karasa ba ta fara kiran baby a waya dan ta bata wannan daddadan labarin, saidai baby tee na ganin kiran amma ta share, sai da wata zuciyar tace mata gwara ki dauka kiji meyafaru sannan ta dauka, wani irin ihu eesha ta fasa a kunnenta bayan ta daga wayar sannan tace;
“Teemaaaaaa guess whaaaaaaat?”…
Toshe kunnenta tayi gabanta na faduwa jin murnar da eesha take tace;
“Karki kashemin dodan kunne mana, what happened?”….
“Yayanki ya tambayeni if I still love him, what does that mean?”…..
“Oho ya za’ayi in sani, ai da kin tambayesa abinda yake nufi”…..
Cewar baby tee da wani irin tone mara dadi, ita kanta eeshan dan tana cikin murna ne amma data gane gatse baby tee ta mata….
“Kinsan shi da kwarjini, I couldn’t even utter a word wallahi”…..
“Toh me kika ce masa daya ce haka?”…
“Kema kinsan abinda zance, ce masa nayi wallahi ina sonsa har abada”…
Wani iri baby tee taji aranta ta maze tace;
“Allah ya bar kwana, kaina na ciwo zan kwanta”….
“Subhanallah ciwon kan ne ya dawo, Allah ya baki lafiya, wallahi har na kagu gobe tayi kizo muyi maganar nan face to face”……
Yatsine fuska baby tee tayi aranta tace zakiga wanda zezo kuyi magana gobe, a zahiri kuma tace;
“Allah ya kaimu”….

Washe gari mami ta fara koyawa baby tee abubuwa, da shara suka fara, da kyar baby tee ta koyi rike tsintsiyar, karshe ma kuka ta saka wai hannunta na ciwo, dole mami ta kyaleta tace zasu cigaba gobe…
Khaleel be iya yazo ba saboda attitude din da baby tee take bashi, ya kirata a waya yace zezo tace bata da lafiya kar yazo…..
Eesha tinda safe take kiran baby tee akan ta tawo amma taki daga wayar, sai da yamma sannan ta daga ta fadawa eeshan bata da lafiya, tazo dinner din gobe kawai..
Washe gari ma haka ta sake cewa bata da lafiya, umm tace bata isa ba sai taje, ai wannan ya zama wulakanci yarinya na binta tazo tana cewa bata da lafiya bayan garau take, dole bata da yanda zatayi ta kira eesha tace mata gatanan zuwa, ga mamakinta sai eeshan tace mata gata a gidan nasu ai, haka suka tattara suka tafi gidan make up badan taso ba…..
A ranar da safe deen sukayi magana da suhaima yace mata yanaso su hadu, a kuma ranar yake son aiwatar da plan dinsa, da farko ce mata yayi zezo gidansu, daga baya kuma ya mata text yace ta samesa a Fraser Suites Hotel, ba a fi minti biyar ba sai gashi ta maida masa da ‘okay, I’m on my way’….
Hmmm kawai yace sannan yayi saurin tafiya chan din shima, dama yana gida ya mata wannan text din saboda yaji me zatace…..
Be dade da yin lodging ba sai gashi ta kirasa wai a wani room yake, fadamata number room din yayi ba’a jima ba yaji ana knocking…
Tashi yayi ya bude sannan ya bata hanya tashiga ya maida kofar ya rufe….
Zama yayi a bakin gado yana kallonta, for the first daya taba karewa fuskarta kallo, fara ce sosai har wani jajajaja fuskarta yayi, kana gani kaga farin bleaching, daga wannan be tsaya ya suffanta wani abun na fuskarta ba, ya zaro wayarsa a aljihunsa yace;
“Kin san meyasa nace kizo ki sameni anan?”…..
Kai ta gyada masa alamar eh…..
Smirking yayi yace;
“Wow! To meyasa?”…..
“Saboda kana son kasancewa dani, you want intimacy”….
Murmushi me ma’ana yayi yace;
“Intimacy? Well kusan hakane, toh kin amince ne?”……
“In dai akanka ne babu abinda bazan iya ba handsome, ko kullum kakeso muna haduwa a hotel dinnan wallahi zanzo, inma so kake inzo in zauna tare dakai na wani lokaci a shirye nake”…..
Sai da ya bari ta dire sannan ya nuna mata kofa yace;
“Toh tashi kije, Allah ya hadaki da dan iska irinki”…..
“What do you mean?”….
Ta tambaya hankali tashe…..
“I mean you’re not my type, an gayamiki in iskancin zanyi da ragowar titi zanyi? Ki fice daga dakin nan tin kafin in chanza miki kamanni, I hate nonsense!”…..
Fashewa da kuka tayi tace;
“Dan Allah karka min haka handsome, wallahi ni ba yar iska bace saboda kai na shirya zama yar iskar, dan Allah karka min haka”…..
Wani irin ball yayi da ita sai gata a bakin kofa sannan ya tako ya bude kofar ya karasa cillata waje……
Wani kuka me ciwo ta saki sannan ta tashi ta tafi da kudirin kulla masa sharrin da dole sai ya aureta…

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 Complete Document

Zama yayi rike da kansa cike da takaici, mamaki yake meyake damun matan duniyarnan? How can you be willing to do anything for a man? Kuma wannan daga ganinta yar hannu ce dan babu novice din da zata amince kai tsaye batareda an mata dadin baki ba, infact wannan da kanta ta nunamasa tasan abinda yake nufi, which means a shirye tazo ma, wai shi take gayawa yanason kasancewa da ita? Toh yaji uban me a jikinta?…..
Tsaki yaja ya kunna data dan yayi danne danne ko zeji sanyi aransa, kamar ance ya shiga instagram yaci karo da abinda ya sake dage masa hankali, murza idonsa yayi dan ya tabbatar da ita din yake gani ko kuwa, rawa wayar ta farayi a hannunsa bayan ya tabbatar da ita dince, arewafamilyweddings ne sukayi posting baby tee sanye da wani fitted gown da wani lace me kyau irin dinki zamani yayi mugun zama a jikinta babu and wani tudu na jikinta da ba’a gani, an mata wani make up me shegen kyau, aka mata video tindaga sama har kasa sannan ta juya aka dauki bayan kamar dai yanda masu kwalliya keyi idan zasuyiwa mutum video, wani abu me daci ne yaji ya tokare masa a makoshi ya daure yayi swiping dayan hoton, nan kuma tana tsaye a cikin hall din bikin aka mata hoton, cike gurin yake makil da maza da mata, ko a hoton da aka mata maza kusan biyar ne a kusa da ita dake a gaban stage aka mata, scrolling kasa yayi ko zega event center din saboda yawanci ana sawa, yana dubawa kuwa yagani, wurgar da wayar yayi ya fita a birkice….
Tuki yake na rashin hankali sai kauce masa akeyi, ko gani gabansa bayayi da kyau, ikon Allah ne kawai ya kawosa gurin, yana zuwa ya shige ciki ko bi takan bouncers din dake tambayar gate pass dinsa beyi ba ya bangajesu ya shige wuce, yana zuwa yaga abinda ya karasa tarwatsa zuciyarsa, baby tee ce a tsaye akan stage sai hyping dinta ake maza zagaye da ita sai liki suke mata!!..

Back to top button