Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 43 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                          FORTY-THREE📍

      Dagowa Abby yayi ya kalli deen da yabi hanyar da ba nan bane rest room din ba…..Nuna dayan side din yayi yace;

     “That’s the rest room over there”…..

    “Okay”….

Deen ya fada yana fasa yaye labulen……

Shiga yayi ya gama harkokin gabansa sannan ya dawo ya zauna inda ya tashi……

Sai a lokacin fatima zainab ta zame jikinta daga na khaleel jin abinda takeji ya ragu saidai har lokacin tanajin kirjinta na bugawa kadan kadan…….

      “Relax love, Nothing’s gonna happen, relax okay?”……

Khaleel ya rada mata a kunne cikin tausasawa……

Gyada mishi kai kawai tayi sannan ta lumshe ido kamar me jin bacci, khaleel be kara cewa komai ba duk a tinaninsa bacci take nan ko wani tashin hankalin takeji a ranta…….

Tinda Deen ya dawo ya zauna ya nemi nitsuwarsa ya rasa, ko dazu daya shiga toilet yaje ya danyi clearing mind dinsa ne saboda false abu da take gayamasa, ya ma zaayi ace yanajin irin abinda yake ji idan tana kusa dashi bayan yasan daga shi sai Abby a cikin jirgin, abun mamaki koda ya dawo be samu nitsuwar da yake so ba sai ma bunkasa da abinda yakeji yayi, daurewa yayi ya cigaba da kame kansa dan in zebi ta zuciyarsa tashi zeyi ya duba lungu da sako na jirgin saidai hakan babu tsari sam tinda Abby na nan, abin ne yaci karfinsa ya fara juye juye be sani ba, rikicewa yayi ya fara kalle kalle daga zaunen da yake kamar wanda yake neman wani abu…….

Abby da yaga sai kalle kalle Deen yake ya tabasa yace;

      “Wani abun kakeso ne?”……

Girgiza kai yayi da sauri cikin san waskewa yace;

     “No, not at all, I was just surveying the plane dake akwai wani project da nake akan aircraft cabin so I was using the opportunity”…..

     “Okay nagane, that’s very good, I’m proud of you son”……

     “Thank you Abby”…….

Murmushi Abby yayi cikin sanyin murya yace;

      “tell me about her”…..

Kallonsa Deen yayi cikin rashin fahimta yace;

     “Who?”……

     “Boddi na!”….

Abby ya fada yana blushing…..

Yake Deen yayi yace;

     “She’s fine! Ai zamu je kaganta”…….

Murmushi Abby yayi sannan cikin wani irin yanayi daya tsinci kansa yace;

      “Is she still gentle?”….

Gyada masa kai kawai Deen yayi alamun yes…..

       “I’m glad she still is”….

Deen be basa amsa ba ya jewo masa tambayar datake ransa tin farkon ganin daya masa saidai abinda yake kansa yasa ya sha’afa…..

      “Ina baby tee?”……

Dan shiru abby yayi sai chan kuma kamar wanda ake bawa umarnin magana yace;

     “She’s fine”…..

     “Good, zan bika in ganta kafin na dawo dubai”….

Cikin sanyin murya abby yace;

     “Okay”……

Daganan kuma sai shiru ya biyo baya, ba wanda ya sake cewa komai amma kowa da abinda ke damunsa a rai, haka suka cigaba da tafiya in silence duk bayan after 30 mins air hostress ke kawo musu menu su zabi abinda sukeso dan long journey ne, likewise su khaleel da fatima zainab saidai akwai direct entrance ta chan da ba sai anbi ta gurin su deen ba……..

       “Wifey?”…..

Khaleel da yaji tanata motsi ya kirata…..

     “Yes honey”….

Ta amsa masa cike da so da kauna……

Murmushin jindadi yayi yace;

     “I am the luckiest person in the world to have you, my love. Every day I realize how lucky I am to have your love, your kindness and your devotion. You make my life better by existing. I hope you know how every little thing you do makes my life better and brighter; I value you so much that sometimes I just stop and look at you thinking about how very lucky I am to have found you. My heart just swells up with love for you, with every day in my heart, I cherish your love!”………

Wani irin kallo ta masa with much adoration tac;

       “I looked around the world and I’ve not seen any man as great and caring as you are, having you has made me the Luckiest woman darling”…….

Ai ji yayi kamar ya tashi sama dan dadi, besan sanda ya zage ya cigaba da zubo mata dadadan kalamai ba;

     “Kin wadata zuciyata da farin ciki, kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki a gare ni ta musamman ce, hakan ya sa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da ƙarfin iko. Ina Son Ki Sosai My Wife To Be!”……

Kasa magana tayi tsabar yanda kalaman dayake mata yake tsumata yake sata farin ciki da nishadi…. 

     “Koda a ce za ki sa wuta a jikina na babbake na zama toka, ba zan damu ba, matuƙar zaki ɗauke ni, ki kasance tare da ni a duk inda kike. Fatana mu kasance tare da juna a cikin wuya ko daɗi. Ina Son Ki Wifey”……

 Khaleel ya sake fada yana kallon kwayar idonta cike da shauki da kauna…… 

 Ware idanunta tayi yanda zasuji dadin saka ido cikin na juna tace;

     “Na maka alkawari darling khal, na maka alkawari zan kasance da kai duk rintsi duk wuya, Ina Sonka nima!”……..

      “Har in mutu bazan taba mantawa da wannan ranar ba, kin gama min komai wifey! I love you is an understatement”……

Tini ta manta da wani bugun zuciya da tsoro da takeji suka cigaba da soyayyewarsu while jirgi nata tafiya…….

Karfe biyun rana private jet din Abby ya sauka a private port dinsa dake cikin garin abuja……..

Abby ne ya fara sauka bayan jirgin ya tsaya, Deen be motsa daga inda yake ba saima kokarin saita tracker da yayi ya duba yaga ko ansake kunna wayar be sani ba tinda yasa wayarsa a flight mode da sukayi taking off, saida ya gama saitawa tsap sannan yayi relaxing yana kallon yanda abun ke processing…….

Kamar a mafarki yaji takun takalma daga gefensa, mamaki abun ya basa dan duk a tinaninsa daga shi sai Abby a cikin jirgin bayan pilot da air hostress, juyowa yayi da sauri dan yaga su waye, yana juyowa idonsa ya sauka akansu, murza idansa ya hau yi dan ya tabbatar su din yake gani dagaske……. 

Tinda sukayi ido hudu dashi suka sandare a gurin kadama fatima zainab taji labari dan lokaci daya ta nemi ta fita hayyacinta, ganin ya mike ya sata yin hanyar toilet a guje tana fadin;

      “Runaway honey khal, ka guduuuuuu”…….

Dan a yan kwanakinnan ta saba dace masa honey khal ko darling khal bata iya kiransa kai tsaye…..

A guje shima Deen ya bita ganin ta fita a guje tana kiran wani gardi kuma honey a gabansa saidai ko kafin ya karasa ta shige toilet ta rufe kanta, kwafa yayi juyo yayi kan khaleel a zuciye….. 

Chakumoshi yayi ya bugashi da kujerar da Abby ya tashi sannan ya shiga zabga masa maruka a fuska, saida ya zuba masa kyawawan maruka goma a hagu da dama sannan yayi ball dashi ya cilla shi inda suka fito, binsa ciki yayi yayi wani kukan kura ya shako wuyarsa cikin wata iriyar murya irin na wanda ya dade yana kwasar bakin ciki da takaici yace; 

      “Dan uwarka da ubanka an daura muku auren?”…

Shiru khaleel daya jigata ya kasa magana yayi…..

Sake ball Deen yayi dashi ya kuma binshi ya kamo shi cikin muryar datafi wanchan tashin hankali yace;

      “Zaka bani amsa ko sai na kashe ka?”…….

Cikin tsoro da fitar hayyaci khaleel ya bashi amsa batareda yasan abinda yake cewa ba…..

       “An daura”……

Wani irin kukan zaki Deen yayi ya shiga jibgarsa kamar an aikosa, tsabar yanda yake dukansa har kara jirgin yakeyi, ji kake kichi kichi kichi kamar ana yaki……

A lokacin abby ya kai matattakalar karshe kasancewarsa me koyon tafiya shiyasa yake tafiya a hankali, ai ji kawai yayi jirgi na girgidi kamar wanda ya kwace a hannun pilot bayan jirgi a kasa yake, luuu ya tafi ze fadi Allah ya taimakesa securities dinsa da suka karaso a lokacin sukayi saurin taresa da sabon jinya ya kamasa shida yake tatata…… 

Saida Deen yayi wa khaleel ligis a lokacin ko hannunsa khaleel baya iya dagawa sannan ya janyo wani biro da takarda daya hango a cikin gurin ya mikawa khaleel dake kusan a sume ya daka masa tsawa yace;

     “Saketa yanzu, saki uku zaka mata!!”……

Cikin rawar jiki khaleel ya karba ya mata saki akan auren da baa riga an daura ba tsabar rudewar dayayi…….

Har deen ze juya ya koma kanta wani abu ya fadomasa a rai, cije lebe yayi ya sake yayimo khaleel ya sauke masa wani sabon lafiyayyen marin sannan yace;

      “Did you touch her?”….

Daga masa kai kawai khaleel yayi dan wallahi baya gane abinda yake cewa…..

Cikin kunan rai Deen ya sake sauke masa naushi a baki yace;

      “Did you sleep with her? Did you make love to her?”…..

Gyada masa kai khaleel ya sakeyi dan shi kadai ne amsar da ze iya basa dan bakinsa baze iya furta komai ba, gyada masa kan da yakeyi shima jinsa yake kamar ana zare masa rai, saidai baze iya kin kulashi ba dan ya tsorata dashi sosai………..

Wani mugun ihu Deen da yaji maganar khaleel tamakar saukar mashi yayi sannan ya kinkimi khaleel ya zuge window ya cilla shi wai ya mutu kawai daya barshi da ransa yana tina ya taba kusantarta……

Ajiyar zuciya ya sauke me karfi yanajin wani sanyi a ransa bayan ya cilla khaleel ta window sai kuma ya koma toilet din data rufe kanta a guje……..

Bubbugawa ya hau yi kamar ze balla kofar, fadi yake;

      “Ki bude kona balla kofarnan! Ki bude, I must kill you today, why did you marry him? Why will you allow him to sleep with you? Why? Why?”……..

Tana tsaye tana jinshi amma ko motsi ta kasa, sosai ta shiga tashin hankalin da bata taba shiga irinsa ba a rayuwarta, hankalinta in yayi dubu ya tashi sai gumi take dukda akwai ac a toilet din……..

Cigaba da buga kofar yayi yanata zuba sambatun dabe sani ba, yana kara maimaita mata saiya kasheta kamar yanda ya kashe khaleel…….

Kalmar data daga mata hankali kenan taji tsuuuuu period dinta ya zubo abinda taketa fama dashi yazo, sai ga wani zawo shima ya tawo mata, fashewa tayi da kuka ta zauna a toilet seat tana kashi…….. 

Be saurara ba ya cigaba da buga kofar yana kara fadin mugayen kalamai, a haka kofar ta dan fara losing alamun ze iya ballewa anytime soon……..

Saddakarwa kawai tayi wani sabon zawon na zubo mata, hawaye ne suka shiga zubo mata kamar famfo, haka zawon shima yake tawo mata kamar ruwan famfo, giving up kawai tayi tayi relaxing a toilet seat dan ko tsarki bazata iyayi ba, toh ina taga ta tsarki bayan zawo be tsaya ba?…….. 

Abby daya tsaya a gefe yana wuce gajiyar faduwar daya kusayi da niyar ya dan samun kwarin jiki sannan yaje ya duba meke faruwa a cikin jirgin kawai sukaga an jewo khaleel ta window, inda Allah ya taimakesa anan su abby suke tsaye da securities dinsa da basu shiga cikin jirgin ba saboda Abby be basu umarni ba, shi kuma fadin daya kusayi ne ya sasa rikicewa, saura kadan khaleel ya dira akan Abby securities din Abby sukayi saurin tareshi kamar dan jariri lokacin ya riga ya sume, a mota aka sashi da niyar kaishi asibiti……… 

Sai a lokacin Abby ya basu umarnin zuwa su duba abinda yake faruwa saidai suna zuwa sukaga Deen yayi jaming entrance door din, hankalin Abby ne ya tashi ganin suna jin hargowa har lokacin ga khaleel an cillo shi it means fatima zainab ce kawai a ciki da deen gata mace kuma, the only option daya rage musu shine a shiga ta pilot route amma akayi rashin saa pilot din daya tuka jirgin harya tafi, haka Abby yasa a ka kirashi a waya akace ya dawo yanzu yanzu, ko kafin ya dawo su samu su shiga Deen ya kusa balla kofar toilet din da take ciki………

Hakuri securities din Abby suka hau bashi akan karya balla kofar sai kawai ya nemi ya koma kansu daga ya mari wannan sai ya naushi wanchan, ganin kamar baya cikin hayyacinsa yasa sukayi maza sukaje suka fadawa Abby……

Mutane biyar ne suka taimakawa Abby ya hau jirgin dan tsakani da Allah gani yake kamar fadi zeyi……

Sosai Abby ya rude ganin yanda Deen ya fita hayyacinsa sai cewa yake idan ya balla kofar da kansa saiya kashe ta ita kuma taki budewa….. 

Tsawa Abby ya daka masa yace;

     “Bakada hankali ne Saifuddeen, me kakeyi haka?”…….

     “ I must deal with her wallahi Abby, I must teach her a lesson”…..

Deen ya fada kamar ze tashi sama…….

Wani lafiyayyen tsawa abby ya sake daka masa cikin bacin rai yace;

     “Ashe baka da tinani bakada lissafi? Ina maka kallon me hankali ashe shashasha ne kai? Kasan kuwa me kake cewa? Kisa! Kisa! Ko tsoron furta kalmar bakayi?”…..

Zeyi magana kenan abby ya daga masa hannu, nuna masa hanyar kofa yayi yace;

     “Sauka kasa ka jirani!”……

Kamar zeyi kuka haka ya sauka yanajin kamar yayi hauka yanda Abby ya katsesa akan abinda yake……

Knocking Abby ya mata a nitse yace;

      “My dear open the door Abby ne”…….

Cikin sheshsheka kamar jira take wani yayi magana tace;

     “Kasheni zeyi Abby, yace sai ya kasheni”…….

Cikin tausayawa Abby ya sake fadin;

     “Karki damu babu abinda ze miki ai ina nan, just open the door, I promise you babu abinda ze same ki, kinga bayanan yanzu ma”…….

Sai a lokacin taji zata iya daurewa tayi tsarki, tsarkin tayi ta bude kofa a hankali tana dan leke taga ko yana nan har lokacin, kallonta abby yayi cike da tausayi ganin yanda tayi tsilli tsilli da ido kamar an jijjiga saurayin bera a buta, abin dariya kamar ace fitt ta fita a guje…… 

Girgiza kai Abby yayi yace mata;

     “Muje babu abinda ze miki kinji ko?”….

Daga masa kai tayi tana makale dashi har suka sauka……

Suna sauka idonta ya sauka cikin na deen dake tsaye yana mazurai idanunannan nasa sunyi wani iri, kanta yayi a haukace tayi maza ta bar kusa da Abby da sauri tayi hanyar fita daga landing area din sai dai kash a rufe yake tin bayan an budema pilot din ya dawo aka sake rufewa, zagaye suka hau yi kamar wasu yara su abby na tsaye suna kallon ikon Allah…….

Saida Abby yaga abin nasu na neman wuce gona da iri sannan ya daka musu tsawa yana yafito Deen da hannunsa, yi yayi kamar be gani ba ya cigaba da binta, itako taki yarda ta tsaya dan bataki ko kwana zasuyi suna zagayen suyi ba da akan ta bari ya kamata, da taga hanya ma da tuni ta fita daga filin jirgin…… 

      “Saifuddeen! Saifuddeen!”…..

Abby ya sake fada a kausashe……

Dan dakatawa Deen yayi ya kalli abby, babu alamun wasa abby yace masa yazo, zuwa yayi yana wani hura hanci, mamaki sai kama Abby yake ganin yanda Deen ya koma kamar ba wanda ya sani ba……

Mota kawai ya nuna masa yace;

     “Shiga!”…..

Nunata Deen yayi yace;

     “Ita fah?”…..

Harararsa Abby yayi yace;

     “Kana nufin mota daya zaku shiga kuna abu haka? Allah ya kiyaye”……

     “Toh wani mota zata shiga?”….

     “Chan! Inda akasa khaleel!”…..

Kai tsaye Deen yace;

     “Wallahi bazata shiga mota daya da wancen dan iskan ba!”…..

     “Shikenan zata shiga wanda zan shiga”….

Abby ya fada dan bayasan ayita jan magana…..

      “Better!”…

Ya fada yana mata wani kallon banza daga nesa…..

Shiga mota kowa yayi suka bar harabar gurin…….

Asibiti motocin Abby suka nufa kamar yanda yace a fara zuwa chan dan a duba khaleel, neman birkice musu Deen yayi wai shi baze je asibiti, saida abby ya tsawatar masa ya kuma masa tatas akan rashin tausayinsa, ya zaayi ace ka jiwa mutum ciwo amma ko a jikinka, sai ce masa yayi khaleel deserves it, Abby kuma yace dole sai anje dashi, haka bashida yanda ya iya suka nufi asibiti, emergency akayi rushing khaleel suka zauna zaman jiran feedback……….

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

     Shirye dad da mom suke tsap kowannensu ransa a hade, kadama dad yaji labari dan shi yafi jin ciwon abinda ya faru tinda dansa ne wai a haka ma mom tanata kwantar masa da hankali………

Tun bayan ya kira mami ya mata kashedi akan rashin zama a gurinsa da Deen bayayi ta masa tass dan dama itama tana cike dashi kuma duk a tinaninta Deen yana kano, maganganu ta gayamasa san ranta, harda cewa  Deen din da rabon da taganshi harta manta shine dan renin hankali ze kirata yau ya mata borin kunya ya nuna mata Deen baya kano bayan tasan yana kano, ransa ne yayi balakin baci yaga abun bazeyiwu ta waya ba, gwara yaje ya sameta face to face ya mata nasa cin mutuncin, mom dake zaune tanajin duk wayar da sukayi tashiga kwantarwa da dad hankali sannan tace zata rakasa, nan ko itama so take taje ta saukewa mami nata rashin mutuncin dan gani take mami ce ta hana deen ya so hameeda, gashi tayi duk wani abu daya dace amma yaki son yar lelenta……. 

Shine suka shirya suka tawo abuja, a halin yanzu ma suna garin abuja sun gama shiri  zasu tafi  gidan mami……..

      Sun fi two hours suna jiran zuwansu amma shiru basu zo ba, alhaji habibu ne yake ta basu karfin gwiwa akan su kara hakuri yasan yanzu zasu gansu, daddy ko dama bece uffan ba tinda suka zauna…….

Dafa kafadar daddy Alhaji habibu yayi yace;

      “Ka kwantar da hankalinka babu abinda ze faru”…..

Kamar jira daddy yake yace;

     “Ya zaayi in kwantar da hankalina? Kana ganin komai ya kusa kwabe mana kace in kwantar da hankalina? Bazan iya ba”……

      “Ni nasan abinda zamuyi shiyasa nace ka kwantar da hankalinka”…… 

Daddy ze sake magana kenan suka ji knocking, fasa maganar yayi ya tashi da sauri yaje ya bude, kamar yanda yayi sammani su yagani, hanya ya basu suka shiga yana biye dasu……

Gaishesu suka farayi daddy ya katsesu da fadin;

      “Just go straight to the point! Baku ganshi ba haryanzu?”………

Dariya wanda ya kasance ogansu yayi ya dora kafa daya kan kujera yace;

      “Bamu ganshi ba amma muna da tabbacin inda yake!”…….

Zabura daddy yayi ya mike yace;

     “Ina yake? Ina yake?”…….

    “Kwantar da hankalinka alhaji! Zan fadamaka amma sai an bamu cikon kudin mu!”……

Alhaji habibu ne ya karba da fadin;

     “Bangane sai an baku cikon kudin ku ba? Ai ba haka mukayi daku ba, cewa mukayi idan kunyi kidnapping dinshi zamu cika muku!”…….

       “Eh toh bamu daukeshi ba amma mun samo inda yake, guri ne kuma da bazamu iya shiga ba sai dai kuje da kanku ku daukoshi, idan kun shirya sanin inda yake ku bamu sauran kudinmu, idan baku shirya ba kunga tafiyarmu”…….

Ya fada yana yiwa yaransa signal din su tafi, daddy ne ya dakatar dasu da sauri dan yasan idan suka wuce bazasu dawo ba, wa kuma zasusa su nemo musu khaleel idan wannan manyan yan ta’addan sun  kasa……..

     “Munji zaa cika muku kudin ku dawo”….

Cewar daddy yana lalubo wayarsa dan ya musu transfer…….

Dawowa sukayi aka tura musu cikon million goma a take sannan ogansu ya fara bada bayani…….

      “Fada sukayi da dan gidan Justice Fatima shine ya garkameshi  a chan gidan babarsa!”…….

      “What?!!!!”……. 

Su daddy suka hada baki wajan fada……. 

      “Eh yana chan, munyi kokarin shiga mu dauko shi muka kasa saboda akwai tsaro sosai a gidan”……

A zuciye daddy ya kalli Alhaji habibu yace;

      “Tashi muje gidan, wallahi saina mata rashin mutunci yau kuma dole a fito min da dana”…….

     “Muje! Nima ta dade tana shigar min hanci, yau zamuyi maganinta”…….

Fita sukayi suka shiga mota suka dau hanyar gidan mami…….

    

         Har mom da dad suka karaso unguwar su mami  dad be dena fada ba, har wani ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya gansa a cikin gidan, tsabar yanda ransa ke a bace shi yake driving da kansa ko driver be tawo dashi ba bare securities, yana shirin horn bayan sun karaso gidan suka ga gate din gidan a bude, lokacin an budewa mami data dawo daga office gate, danna kai dad yayi ya shiga shima, securities basu hanashi ba dan sunyi tinanin tare suke da mami………

Lokacin da dad yayi parking mami harta shige ciki, da sauri yabi bayanta saboda hangota dayayi tashiga main parlor dinta………

       “Fatima! Fatima!”…..

Mami da har ta fara hawa sama ta juyo muryar dad a cikin parlornta……

Juyowa tayi da sauri cikin mamaki tace;

      “Ya zaka shigomin parlor kai tsaye haka? Who even permitted you to come in?!”……

Cikin hargowa yace;

     “Har sai anbani wani permission a wannan tsinannan gidan zan shigo? Toh open your senseless brain and listen to me; zan daurawa Deen aure da Hamida in few weeks time saboda haka ki janye maganar koma wacece kikeyi, sannan ki fita daga sabgar yaro na dan ban gane kanekanen da kikayi a rayuwarsa ba ko wayata ya dane dauka saboda makircinki”………

Katseshi mami tayi tana nunashi da yatsa tace;

      “Dakata mallam!! Kai har ka isa ka tako har gidana kana gayamin maganar banza? Toh bari kaje sai yadda nayi da Saifuddeen yanzu kuma babu yanda ka iya, zancen daga wayarka kuma ban basa dama bane shiyasa, da’na kuma baze auri yar munafukar matarka samira ba!”…..

Karab mom ta saka baki da fadin;

     “Karya kike wallahi fatima! Nace karya kike! Babu abinda ze hana danki auren ya’ta wallahi, kuma”…..

        “Yi mana shiru karamar yar iska kawai! Ke har kin isa yaya tana fada kina fada dan baki da mutunci bakida kunya butulu! Kai kuma Abubakar ka bani mamaki! Yanzu har zaka iya kwaso jahilar matarka kuzo kuciwa yaya mutunci har gida? Toh wallahi bazamu yarda ba this is against the law! Ku saurari sammaci mahaukata guda biyu kawai!!”……

Umm da fitowarta kenan ta katseta cikin bacin rai, bacci take taji hayaniya na tashi tana kuma jin maganganun da suke fada sama sama, sakkowa tayi ba shiri shine taci karo da maganar da samira take gayawa mami, ba karamin baci ranta yayi ba abinka da wanda be iya fushi……….

Sosai jikin dad yayi sanyi dan tinda suke samun sabani da mami Umm bata taba sa baki ba, har haduwa sun tabayi da ita suka gaisa cikin mutunci kamar babu komai tsakaninsa da yayarta, sannan ko lokacin da aurensu ya mutu tayi making effort sosai gurin sasantasu suka nuna mata bazasu sasantu shine ta hakura ta zuba musu ido, sai gashi yau Umm ta kalli tsabar idansa tana gayamasa maganganu, harda ce musa mahaukata shida matarsa……… Amma be karaya ba dan ya riga yayi nisa baya jin kira, yana shirin bawa Umm amsa daidai da ita kenan aka banko kofar parlourn…..

      “Ina Justice din take! Ina take! Wallahi sai an fito min da dana yau”……

Cewar daddy da ya shigo da balaki da masifa…… 

      “Kai kuma daga ina? Wai me ake nufi da mu ne a gidannan yau? Ko wani trash sai ya shigo anyhow? Wai babu securities a gidan ne!”……

Umm ta fada tana nufo su daddy…….

      “Ba wannan bane ya kawo mu! Kawai ku fadawa danku ya fito mana da danmu yanzu yanzu!!”…..

Cewar alhaji habibu daya biyo bayan daddy……..

      “Boddi na! Boddi na! Ina kike dan Allah”….

Umm zatayi magana kenan ta juyo muryar da ko a mafarki bata san karajinta a rayuwarta, muryar da bata san tina wani abu ya taba hadata da meshi, sai ta dauka kawai irin hallucination din data saba ne……

      “Boddi na! Boddi na! Boddiiiiiiii”……

Abby ya sake fada da karfi yana shigowa parlourn….

Fatima zainab na ganin Abby yayi gaba ta ruga a guje ta shige ciki, kan Umm dake tsaye a daskare tayi ta rungumeta tana boyewa a jikinta, ita tayi hakan ne saboda kar Deen ya mata wani abu tinda tasan be isa ya tabata a gaban mamansa ba……

Zubewa a kasa daddy da alhaji habibu sukayi ganin wacce suke nema ido rufe gata tazo har inda suke…..

Ido hudu Abby sukayi da Umm da already ta fita daga duniyar mutane, firgit kamar wadda aka tasa daga bacci ta shiga murza ido dan ta tabbatar da shi din take gani…….

      “Ni ne boddi na! Ba mafarki kike ba”…..

Abby ya fada fuska dauke da madaukakin farin ciki, irin wanda be karayi ba tin bayan barinta rayuwarsa……..

Sai a lokacin Umm ta tabbatar dagaske shi dinne, sam bataji farin cikin ganinsa ba saima hada rai da tayi ta jefo masa tambayar;

     “Ina ya’ta! Ina baby tee?!!!”….

Abby zeyi magana kenan sukaji mom ta kwallara ihu kamar wata mahaukaciya sabon kamu, cire mayafinta tayi cikin ihu tace; 

     “Zan fada! Wallahi zan fada!”……

Deen ne ya mata wani mugun kallo yace;

     “‘Me zaki fada?”…..

Wani ihun ta sakeyi tace;

      “Nina binne! Wallahi nina binne”……

~uniquebarakancy~

Back to top button