Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 60 Complete Novel

**ASM Bk2060*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

……… Lokacin da su Hajiya suka fito Abbas na tsaye bakin Jeep d’in da ya zo da ita har an shiga da Fatuu, Aunty Mareeya da Feenah da inna Zaliha da Matar Baba shehu duk suka shiga ya juya kan sauran k’awayen Fatuu da suka rage don wasu sun tafi ya nuna masu Jeep d’in Saleem yace su je su shiga harda Fauzy ita ta shiga gaba sai Haulat, sauran wad’anda suka rage Abokan aikin gwaggo Hajiya ta nuna masu Motar da Tk ya zo da ita suka shiga Amadu na a Front seat, kowa ya samu wuri sai wasu daga cikin Makwabta ne basu samu ba Hajiya tace su taka a k’asa itama a k’asan zata duk akai dariya ta kira Abbas yazo gaban su tace mashi su d’an zagayo da su Fateemar ita ma ta shaida an yi mata d’aukar Amare yana murmushi yace to ya juya, Motar Saleem ya nufa ya zagaya driver side ya bud’e yana zauna ya d’an d’age kan shi jikin headrest ya sanar dashi zasu d’an zagayo dasu roundabout ya jinjina mashi kai ya rufe mashi kopar, saida yaje ya sanar ma Tk shima sannan ya dawo Motar tashi, lokaci guda gaba d’aya suka kunna motacin sai lokacin gwaggo dake tsaye ta tuna da kayan Fatuu ta yi ma Hajiya Maganar ko a d’aukko kafin su tafi tace ta bari in suka dawo sai Tukur yazo ya d’auka tace to, Tk ne ya fara jan tashi dama shine a gaba lokacin da suka baro gidan Hajiya da zasu zo ya mik’i hanya Abbas ne a tsakiya sai ta Saleem k’arshe suka tafi,

 

Bayan tafiyar su Hajiya tace masu su tafi su jira su acan gidan, har zasu tafi ganin an bar gidan a bud’e yasa Hajiya cema gwaggo akwai sauran mutane ne a gidan za a bar shi a bud’e, sai lokacin ta ankare da sauri ta juya tana fad’in ta manta Hajiya na cewa ko duk tafiyar Fateemar ce tasa ta rikicewa, bayan ta shiga ta d’aukko wayar ta da makulli ta fito ta rufe gidan suka tafi, ta k’aramar kopa suka shiga suka nufi part d’in Haisam, lokacin da suka shiga a gyare harabar take tsaf an gyare shukokin flowers d’in wurin gwanin sha’awa suka nufi kopar shiga parlon, suna shiga makwabtan da aka je da su suka saki baki galala suna bin parlon da kallo ga wani ni’imtaccen sanyin Ac had’i da fitinannan k’amshi da ya karad’e cikin parlon, gwaggo dae sai d’an murmushi take itama tana k’are ma parlon kallo, parlon yana nan yadda yake amman an k’ara wasu abubuwa kaman daga bayan L-shape ansa dining table mai kujeru hud’u suma leather ne bak’ak’e sai daga gaba bangon dake kallon su an sa wani jigunannan console mai jan hankali golden haka saman kujera L-shape an canza throw pillows an sake wasu masu design mai kyau da d’aukar hankali, Carpet d’in k’asa ma an canza wani sabo wanda ke akwae da an maida shi wurin dining table, haka flowers d’in dake a angles d’in parlon an k’ara wasu, d’an madaidaicin Fridge d’in dake parlon an maida shi cikin kitchen sai sabon freezer da aka siya mata a cikin kayan kitchen aka aje shi a parlon daga can wurin dining table, a jikin bangon parlon an manna manyan Frames harda mai Ayatul kursiyyu, blinds d’in jikin Windows ma an canza su zuwa manyan labulaye wanda daka kalla ba sai an fad’a maka ba zaka shaida masu kud’i ne Saboda had’uwar da sukai kuma sun hau da parlon sosae, komae ya hau daidai nan aka shiga yabawa ana sa Albarka tare da Addu’oi, Hajiya tace masu su shiga suga sauran d’akunan suka ce to suka nufi hanyar corridor, Bedroom d’in ma tsab dashi sai k’amshi ke tashi nan ma an canza labulayen ciki haka gadon ma yasha babban bedsheet mai pillows da yawa ko a ido ka kalle shi kasan zai yi mugun taushi, nan ma sosae suka yaba daga baya Hajiya tace suje su ga Kitchen ta juya gaba suka bi bayanta, d’ayan d’akin da yake matsayin Lab d’in shi a da shine aka maida mata kitchen d’in, bayan sun shiga ciki sosae shima suka yaba komae an tsara shi har a sama anyi cabinet haka k’asan ma cikin kankanin lokaci an maida d’akin Kitchen na yan gayu, bayan sun gama gani suka nufi Parlor sai faman yabo da san barka ake, duk suka zazzauna suna dakon isowar su Fatuu farinciki Fal cikin zuciyar gwaggo har fuskar ta ta kasa 6oyewa sai d’an murmushi take ganin wai autar ta ce zata rayu a cikin wurin, sai godiya take ga Allah acikin ran ta,

 

Tun da suka tafi Fatuu ke ta faman kuka har Abbas saida yay mata Magana yace gidan fa Ya Handsome d’inta za’a kaita ba wani wurin ba ai farinciki yakamata tayi ba tay ta yin kuka ba sai kace za’a kaita inda za’a cuta mata, Aunty Mareeya itama tace abun ya bata mamaki wannan kuka haka sai kace za’a kaita gidan makiyinta Feenah ce tace “ai dole duk da hakan sai taji ba dad’i barin gidan da ka saba rayuwa a ciki ka koma wani wuri ba abu bane da ba za’a ji komai ba”, inna Zaliha tace gaskiya ne ba kamar yadda suka shak’u da gwaggon ta,

Aunty Mareeya tace “hakane, amman dae kukan yayi yawa bai kamata ta sama kanta damuwa ba tunda dai ga baki ga hanci ba nisa tayi da gida ba, muda aka d’aukko daga wani gari sai an dad’e kafin muje gida ita kuwa data fito fa zata ga gidan koda bata shiga ba zata ji dad’i, gani ma zatayi tamkar ba ta bar gidan ba tunda duk unguwa d’aya ne kuma in taso ma kullum taje nasan ba zai hana ba” inna Zaliha dake d’an murmushi tace “hakane amman dai kar ace kullum sai anje d’in hakan bai kamata ba, ita mace ta zauna a d’akinta shi yafi mutunci ba kullum ai ta ganinta tana sunturi a waje ba hakan bai dace ba” gaba d’aya suka ce gaskiya ne harda Abbas, saida suka shawo roundabout na Barhim sannan suka koma. A cikin kwanar gate suka parker Motocin bayan sun iso duk aka firfito Aunty Mareeya na ruk’e da Fatun gefenta Abdul ne ruk’e da hannunta guda suka shiga ta k’aramar k’opa da sauran Mutane, lokacin da suka k’araso bakin kopar shiga parlon Aunty Mareeya ta tsaya da ita tace tayi Addu’a sannan ta shiga da k’afar dama wad’anda ke a bayan su duk suka tsaya saida ta gama sannan suka shige sauran suka bi bayan su, suna shiga d’aya daga cikin makwabtan dake zaune suna jiran isowar su ta mik’e ta rangad’a gud’a mai sautin gaske su Hajiya suka shiga sakin murmushi itama ta mik’e ta nuna masu inda zasu shiga da ita kowa ya baza ido yana k’are ma parlon kallo, hardae Aunty Mareeya da Feenah bin parlon suke da kallo don ba k’aramin had’uwa yay ba ya matuk’ar burge kowa ga wani irin k’amshi mai had’e da sanyin Ac da ya baza ko ina na parlon, Fauzy ma ta jinjina had’uwar wurin har d’an jinjina kai take haka sauran k’awayen su Zainab Muhammadu ma baki bud’e take k’are mashi kallo, ba wanda ma yay tunanin kayan ciki wai ba sababbi bane don kana kallon su zaka ga sabunta a tattare dasu tunda dama iya Haisam d’in kadae ne ke amfani dasu kuma masu matuk’ar inganci ne hakan yasa sam basu canza daga yanayin da aka siyo su ba, Saude ce tay masu jagora zuwa Bedroom d’in nan ma saida aka sa Fatun tayi Addu’a a bakin kopar shiga sannan ta shiga da k’afar dama aka wuce ciki da ita wurin gado, nan ma dae sosae Mutane suka yaba anata Addu’oi, a can tsakiyar gadon aka sa ta haye ta zauna ta jingina da headboard kanta na sadde cikin gyale Fauzy ma ta hau ta zauna gefen ta haka Abdul ma har lokacin yana ruk’e da hannunta duk ya damu tun da yaga tana kuka shima a Mota har kukan yayi yana fad’in ta daina kuka, bayan an gama ganin Bedroom d’in har Laundary room da toilet saida mutane suka shiga suka gani harda su Aunty Mareeya, bayan sun gama dubawa suka fita zuwa Kitchen ya rage daga Fauzy sai sauran k’awayen su, su Zainab dake zaune a bakin gadon sai faman santi suke suna Allah ya maida su damshin Fatuu Fauzy na dariya take amsa masu Zainab tace suje suga sauran wuraren suma duk suka mik’e suka nufi laundry Fauzy ta juya ta kalli Fatuu da har lokacin bata d’ago ba ta kai hannu ta d’an d’aga gyalen ta lek’a fuskar ta suka had’a ido idanun nata sun yi jawur Fauzy ta jawota jikinta tana Fad’in “Haba Amaryar Ya Haisam kukan ya isa hakanan, keda zaki murna ki farinciki Allah ya cika maki burin ki yau gaki a gidan shi a d’akin ki mallakin ku keda shi, don Allah kiyi hakuri kar kija ma kan ki wani ciwon a wannan daren mai daraja da zaku idasa dunk’ulewa ku zama abu d’aya” d’aga idanunta da suka sauya kala tay ta d’an kalli Fauzyn dake ta sakin murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, yar harara Fatuu ta jefa mata ta maida kan ta k’asa Abdul dake a jikinta shima yace “Aunty Fatuu kar ki k’ara yin kuka don Allah, Baba Zakee ba zai cuce ki ba kuma zai rink’a siya maki kayan dad’i da yawa harda Computer ki rink’a yin game” d’an murmushi tay ta d’aga mashi kai kafin ta kai hannunta da ya sha k’unshi da had’add’un awarwaro yan manya guda hud’u sai zobba guda biyu ta shafi fuskar Abdul d’in yaron yana k’aunar ta sosae, d’aga ido Fauzy tay tana k’ara kallon d’akin tace yakamata a k’ara sa turaren wuta cikin wanda Aunty Mareeya ta kawo tace bari tay mata magana ta sauka daga saman gadon ta nufi kopar fita, tana fita parlon taga ba kowa a ciki tun bayan da suka gama dudduba ko’ina Hajiya tace atafi part d’in ta a ci Abinci kar a 6ata ma Amarya nata shine aka d’unguma aka tafi can, wayar ta ta fiddo daga cikin side bag d’inta ta fara k’ok’arin kiran Auntyn bayan tayi picking ta tambaye ta suna ina ta fad’i mata tace gata nan zuwa, fita tay daga cikin parlon bayan ta fito part d’in duk da bata san in da part d’in Hajiyar yake ba bata sha wuyar gane hanyar da zata bi ba saboda ko ina fayau yake da haske tamkar da rana, tana shigowa harabar ta hango part d’in ta nufe shi, bayan fitar Fauzy a hankali Fatuu tasa hannu ta yaye gyalen kanta yadda fuskar ta ta fito sosae, d’aga kai tay ta fara bin bedroom d’in da kallo har yanzu ganin abun take tamkar ba gaske ba kaman mafarki ne, wai yau itace a cikin bedroom d’in Ya Haisam a saman gadon shi kuma ma a matsayin matar shi Allah kenan buwayi gagara misali acikin ikon sa komai mai yuwuwa ne cikin sauki, cigaba da k’are ma d’akin kallo tay iya fentin shi abun burgewa ne balle kuma rantsattsun tsadaddun furniture d’in ciki, sam d’akin baida hayaniya ga wasu jigunannan labulaye, bedsheet d’in saman gadon cikin wanda Hajiya ta siya mata ne lokacin da za’ai mata aure da kayan kitchen har saida ta kai hannunta ta d’an ta6a jikin shi gwanin taushi, tana haka ta shiga tunano can baya tun daga kan farkon ganin shi lokacin da ya raba su fad’a da Jameela mai awara, a nutse taci gaba da tunanin baya sai faman sakin murmushi take lokacin ta tuno da ran da tazo kawo mashi takardar list d’in littattafan da yace taje ta d’aukko bata gan shi a parlon ba ta zo bakin corridor ta tsaya tana yin sallama tace ga takardan, jin shiru bai amsa ba yasa tace ko ta shigo ne ta kawo mashi ya bata amsa da tunda d’akin ta ne ai sai ta shiga daga bayanta ashe bai a cikin d’akin, wani irin murmushi ta saki har fararen hak’oran ta suka d’an bayyana a ranta ta ayyana yanzu gashi ya zama nawa d’in gani ma zaune a saman gadon ka, k’ara tunano lokacin da zai kaita makaranta tay da tace don dai ita k’arama ce da sun yi soyayya kuma in ta gama Secondary School cigaba zatai da karatu yace to ko ya jirata ne tace ai lokacin ita ta zama babbar budurwa shi ya kuma ya tsufa, tace in yana so zata had’a shi da yar ajin su sofiya moussa yace bai sata ba daga baya kuma ta hau yi ma safiyar sharri har tana ba ma lalle ya so ta ba don k’aton baki gare ta hak’oranta kuma sun d’an turo kuma bata da jiki kamar sandar suluka take, tunano hakan har saida tay dariya mai d’an sauti, ita kanta tasan tayi ma Haisam hauka iri iri kafin ta girma amman bai ta6a yin fushi da ita ba ko ya canza mata, in ma tayi abunda ya nuna ta 6ata mashi rai da ta bashi hak’uri yake hak’ura, tabbas dole ne ka ra6i Haisam sai ya burge ka don komai nashi na musamman ne samun irin shi wanda ya had’a abubuwan da ya had’a zai matuk’ar wahala, ga tsantsar kyau, ga kud’i, ga kirki, ga hali mai kyau, ga ilimi, ita kam ko iya haka ta gode ma Allah don ya gama mata komai samun Haisam a matsayin miji ba k’aramar baiwa bace wllh, wata zuciyar ce ta raya mata in kuma bai son ta fa kuma dangin shi suka k’i amincewa da ita, sosae jikinta yay sanyi lakwas yin wannan tunanin, tasan koda bai son ta bazai cutar da ita ba tana da tabbacin hakan inda za’a samu matsala wurin dangin nashi ne in basu amince da ita ba ga kuma matar shi Fanan, sosae Fatuu ke jin zullumin abunda zai je ya dawo in ta samu labarin auren nasu don ita shaida ta kan irin son da take ma Ya Haisam ga hirar da ta ta6a ji yana yi da Abbas da ta tabbatar da cewa Fanan d’in ce ta fara son shi da ya nuna baiso shine har ta kwanta gadon Asibiti, tsayawa tay da yin tunane tunanen Saboda gaba d’aya jikinta ya mutu ta zuba ma bangon da take facing ido a ranta ta shiga ayyana ita bazata so Ya Haisam ya shiga matsala Saboda ita ba, in dae bai son ta da bai cigaba da zama da ita ba, wata zuciyar tace ki ka sani ko yana son ki kaman yadda ake hasashe tunda har abu ya shiga tsakani kuma ya nuna rashin jin dad’i da kika zubar da cikin, shiru tay don a wannan ga6ar baza ta iya yanke hukunci ba duk da a yanzu tasan gaba d’aya abunda ya farun bada niyya bane kuma da ya nuna yayi fushi kan abunda tay k’ilan don aikata hakan laifi ne kaman yadda ya fad’a mata da taje bashi hak’uri da kuma gudun kar wani abu ya faru da ita ba wai don yana son cikin ba ko ita, haka tay ta sak’e sak’e, jin Abdul yay tsit yasa ta kai idonta kan shi taga ashe yayi bacci ta fara k’ok’arin gyara mashi kwanciya a gefen ta tana cikin haka taji an turo kopar Bedroom d’in ta kai idonta da sauri, Kawu Amadu ne ya shigo yana sanye da sabuwar shadda light blue da ya d’inka musamman Saboda ranar, suna had’a ido suka sakar ma juna murmushi ya iso bakin gadon ya zauna sai faman murmushi take mashi ta kasa yi mashi magana,

 

“Amarya, Allah dai ya amince Romeo ya zama naki” ya fad’a yanata murmushi still itama murmushin take ta k’i cewa komae,

 

“Ko duk Farin ciki ne ya hana ki magana?” Ya fad’a yana murmushi da sauri tasa tafukan hannuwanta da suka sha k’unshi ta rufe fuskar ta, bayan ta cire tana kallon shi yace “kinga ikon Allah ko?” Kai ta d’aga mashi alamar eh, “zaki iya tuna abunda na fad’a maki a can baya lokacin dana iske ki a d’aki cikin mawuyacin hali har kika fad’a man Saboda Ya Haisam ne?” Shiru bata ce mashi komae ba ta maida idanun ta k’asa, yaci gaba “lokacin na fad’i maki in Ya Haisam rabon ki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba za ki ga yazo ya Aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kin tuna?” d’agowa tay ta kalle shi tare da d’aga mashi kai, yaci gaba “kin ga maganata ta tabbata, Wannan kad’an ne daga cikin ikon Allah, in dae zaka dogara gare shi to tabbas zaka samu biyan buk’ata ba kamar in ka had’a da hakuri da kuma Addu’a, in kika ga duk kin yi wannan amman bukatan ki bata biya ba to abun ba Alkhairi bane gare ki sai ya musanya maki da wanda yake Alkhairin, shi yasa ake son bawa ya kasance mai yawan godiya ga Allah, in ka samu ka gode mashi haka in ka rasa, a koda yaushe in zaka yi Addu’a to ka rok’i abunda yafi zama Alkhairi a gare ka, duk abunda kaga kasamu to shine yafi Alkhairi, Allah ubangiji da kan shi acikin suratul baqara yace zaku so wani Al’amari alhali ba Alkhairi bane a gare ku, haka zaku K’i wani Al’amari alhali Alkhairi ne a gare ku, Allah ne mafi sani ko baku sani ba, to kinga ba buk’atan ka matsa ma kan ka akan dole sai ka samu wani abu tunda ga mai badawa wanda ya san abun Alkhairi ne a tare da kai ko sharri sai ka mik’a komai a Wurin shi ka dage da Addu’a, a k’arshe ina taya ki murnar samun abunda ran ki ke so ina fatan kuma ku zame ma juna Alkhairi, Allah ubangiji ya bashi ikon ruk’e ki da Amana ya kauda dukkan wata fitina, kema Allah ya baki ikon yi mashi biyayya ya albarkace ku da zuria d’ayyiba Amin” idon shi a Kanta ya k’arasa fuskar ta da d’an murmushi take kallon shi ba tare da ta ce komae ba, d’an tsuke fuska yay yace “ba zaki ce Amin ba” d’an yamutsa fuska tay ta d’an sa hannu ta rufe wurin idanun ta alamar kunya, yace “ke ni zaki wani nuna ma ke mai kunya ce, miye abun kunya an roka maka abun Alkhairi ba sai ka amsa ba” jin haka yasa ta ce Amin a hankali tare da d’an kallon k’asa, kafin ya kara cewa wani abu aka turo k’opar bedroom d’in gaba d’aya suka kai idanun su wurin Tk ne ya shigo shima yana sanye da irin shaddar Amadun da alama anko su kai suna had’a ido da Fatuu ya washe baki ya tunkaro su yana fad’in “Amaryar mu, amaryar mu” yadda ya furta sautin kaman Wak’a Fatun tana ta murmushi ya k’araso bakin gadon shima ya zauna kusa da Amadu ya k’ara ce ma Fatuu dake kallon shi Amaryar su ta gaida shi, da sauri yace “ah ai yanzu ni ne yakamata in rink’a gaishe dake tunda kin koma Aunty na” bata ce komae ba tana dae ta murmushi ya juya kan Amadu yace “kaga ikon Allah ko, yanzu fa dole in rink’a girmama ta tunda ta zama Matar Yayana kuma uban gidana” yar dariya Amadu yayi Tk d’in ya juya kan Fatuu yace “Aunty Amarya Allah yasa dae a rink’a rangwanta man, a da daba k’ark’ashin ikon ki nike ba ma baki d’aga man k’afa ba balle kuma yanzu da kike da cikakken iko dani….” Maida kallon shi yay kan Amadu yace “AA (Ahmad Abdullahi) ka tuna can baya lokacin da aka sa in kaita yawon salla ta maida ni kaman yaron ta tay ta wahalar dani?”

 

“na tuna mana har saida kay ciwon k’arya” ya k’arasa yana dariya shima Tk tuntsirewa yay da dariya tunowa da lokacin, Fatuu ma dariyar take dama lokacin daga baya ta gane ciwon k’arya ne har ta fad’i ma Haisam bayan ya dawo tace bata gama yawon ba har ta rok’e shi ya idasa kai ta hakan ne silar farkon zuwan ta gidan Abbas, Amadu dake kallon shi yace “har ka kai Yayar Fauziyyar ta d’aukko sauran kayan?” d’an girgiza kai Tk yay “No tace in bata makullin Motar ta iya sai

su d’aukko ni in huta shine na bata” kai Amadu ya d’aga Tk ya juya kan Fatuu dake kallon su, da murmushi yace “na taya ki murna yar k’anwar mu yanzu kuma Auntyn mu, Allah ubangiji yasa Alkhairi ya baku zaman lpy, wllh baki ji dad’in dana ji maki ba lokacin dana samu labarin auren, Ya Haisam cikakken mutum ne harda ma rabi, samun shi matsayin abokin rayuwa abun a taya mutum murna ne sam bani da shakku a kan shi don yayi 100% kuma kun bala’en dacewa wllh, zaku ji dad’in yin rayuwa tare don kun riga da kun gama fahimtar juna, shine zai iya maki don ma yanzu naga kin natsu….au tuba nike Hajiya tah su6ul da baka ne” gaba d’aya suka sa dariya ya k’ara cewa “dama ni ne mai kula da part d’in nan wurin gyara shi, to yanzu Aunty zan ci gaba da aiki na ne ko yaya?” Yay tambayar idon shi akan Fatuu dake ta faman sakin murmushi ta kasa ce mashi komae,

 

Amadu ne yace “ah dama ai don ba mata ne, yanzu kuma tunda gata na me kaci gaba ita zata rink’a gyarawa” da sauri Tk yace “No ka bar Hajiyata ta yanke hukunci don itama tana da iko dani yanzu” ya juya kan Fatuu yana fad’in ta yanke yadda za’ai sai Faman dariya take, da k’yar tace mashi ai ba ita zata yanke hukunci ba Ya Haisam ne yace shikenan, ya juya kan Amadu yace “gaskiya AA yakamata muma fa mu fara haramar shigewa daga ciki, ko da yake k’ilan ma sai na riga ka kai da ko budurwa nasan baka da ita, ko kayi ta Yanzu?” Amadu dake murmushi ya girgiza mashi kai alamar a’a,

 

“Gaskiya yakamata ace by now kana da budurwa ko kuma ka tsaida wadda zaka aura tunda nasan ba’a rasa masu son ka kaine kawae baka basu dama” Amadu dake yar dariya yace “No k’yale budurwar nan bari dae in nemi kud’i su taru tukunna in lokacin auren yayi zaka ga bazan sha wahalan samu ba tunda na gama had’uwa” dariya sosae Tk yasa bayan ya tsagaita yace “kuma wllh in dae kana da kud’i bazaka sha wata wahalan samun irin Matar da kake so ba, wai ni yanzu yan mata na soyayya tsakani da Allah kuwa? Ni kaina nan wai d’an ganin da ake ina fantamawa da motoci aka kuma ji gidan da nike kar kaso kaga yadda yan mata suke lik’e man, nan basu san Almajiri bane” gaba d’aya sukai dariya Amadu yace ai yanzu yafi k’arfin a ce mashi Almajiri shima ya zama dangin Senator d’in, suna haka aka turo k’opar duk suka kai idanun su kan masu shigowar, Abbas ne da Saleem da k’yar Abbas ya matsa mashi suka shigo don ya k’iya yace mi zai shigo ya yi, su Amadu na ganin su suka mik’e suna gaishe dasu kafin suka nufi kopar fita su kuma suka k’arasa shigowa ciki idanun su akan Fatuu da itama kallon su take da d’an murmushi haka Abbas ma murmushin yake mata, a gaban gadon suka tsaya yana kallon ta yace “Mom Zarah Amaryar mu, an daina kukan ko?” Kai ta d’an d’aga mashi alamar eh kafin a Sanyaye ta gaishe dasu suka amsa,

 

“haka yakamata ai kar ya haddasa maki wani ciwon muda muke so a biya mu abunda muka rasa a yau……”, bai rufe baki ba daga bayan shi yaji an ce “mi kake ci na baka na zuba ai kunsan dai ita d’in bata wasa bace da kun bata zata biya ku” Aunty Mareeya ce da ta shigo ruk’e da kwalin kwalaben kayan k’amshi tay Maganar duk suka juya har da Saleem suka kalleta Fatuu kuwa wata irin kunya ce ta rufe ta da sauri ta sadda kan ta k’asa, shigowa tay cikin d’akin ta nufi wurin dressing mirror Abbas ya bita da murmushi don sai ya d’an ji kunya duk da tun a Mota wurin kawo Fatuu ya fahimci bakin ta a sake yake itama, Saleem ne ya kalli Fatuu cikin cool voice d’in shi yace mata Allah yasa Alkhairi bata amsa ba sai d’an murmushi kawae tay mashi Aunty Mareeya ce ta amsa tare da juyowa ta kalle shi kafin ta maida idon kan Abbas dake ta murmushi itama ta yi had’i da d’an girgiza kai tana a gaban dressing mirror, ta fiddo wasu had’add’un kwalaben humra da turaren wuta tana jerawa a wurin a parlor ma ta jera wasu a cikin gidajen da su tv suke sosae suka k’ara k’awata wurin, Saleem ne ya juya zai tafi Abbas dake kallon Fatuu yace mata bari su je sai ya kawo mata Angonta Aunty Mareeya tay carab tace suna jiran shi yazo ya siya bakin Amarya a wurin su tay Maganar tana dariya shima Abbas d’in dariyar yake ya juya suka fita,

 

bayan fitar su Fauzy ta shigo ruk’e da burner data gama turara parlor ta jona ta anan aka zuba turare Bedroom d’in ya fara turaruwa shima Aunty Mareeya da ta gama ta shiga yi ma Fatuu bayanin yadda zatay amfani da wasu daga cikin kayan kamshin ita dae kai kawai take d’aga mata, bayan an gama turara d’akin Fauzy ta hau gyara bedroom d’in duk da ba wani 6aci yay ba tana cikin gyaran Aunty Mareeya ta sake shigowa hannunta ruk’e da cup ta nufi side d’in da Fatuu take ta zauna a bakin gadon ta bata tace ta shanye abun ciki, ba musu ta amsa ta kafa baki saida ta shanyen ta mik’a mata Cup d’in tace ta taso zata nuna mata abu a kitchen tace mata to ta zuro da k’afafun ta ta mik’e suka nufi hanyar fita Fauzy nata sakin wani kalan murmushi wanda da gani da biyu take yin shi, bayan sun je kitchen d’in bin d’akin Fatuu tay da kallo an tsara shi ya koma babban Kitchen a ranta ta shiga tuna lokacin da ta fara shigowa cikin shi yin fitsari da ta zo ba Haisam hak’uri da kuma lokacin da yay mata Assignment d’in maths tuna lokacin har saida ta saki murmushi, waya ta6a tunanin wai d’akin zai zama kitchen d’inta gaba d’aya part d’in ma, wata drawer Aunty Mareeya ta jawo ta ce ta matso, nuna mata abubuwan dake ciki tay wanda sauran magungunan ta ne da aka siya mata a wurin Aunty Bee ta shiga yi mata bayanin yadda zata rinka amfani da kowanne Fatun na d’aga mata kai har ta gama, tambayarta tay ko a cikin kitchen d’in akwae abunda bata iya amfani da shi ba ta gwada mata, a sanyaye tace duk ta iya tana ganin yadda Aunty Saude mai aikin nan gidan ke amfani da su Aunty Mareeyar tace da kyau daga haka suka fito suka koma Bedroom d’in, suna komawa Feenah ta shigo tace ma Aunty Mareeya ance su fito za’a maida kowa gida tace to dama sun gama mata komae ai, ta kalli Fatuu da tay zuru jin zancen zasu tafin ta tambaye ta akwai wani abu ta girgiza mata kai sukuku da ita ta juya ta nufi wurin k’atuwar wardrobe d’in d’akin, a gefenta ta d’aukko jakar ta ta dawo bakin gadon Feenah na tsaye, zuge zip d’in jakar tay ta kai hannu ta ciro wata farar shopping bag mai d’auke da tambari ta d’aura ta akan cinyoyin Fatuu tace “Yar k’anwata Amarya ga tawa gudunmawar nan saura kuma kice zaki k’i yin amfani dasu Saboda wai kunya, ke da shi yanzu ba sauran wata kunya don kun riga kun zama abu d’aya, an san kunya abu ce mai kyau amman yanzu a wani wurin in kika ce zaki saka kunya to zaki k’wari kan ki ne da kuma shi Mijin naki don haka ba a komai zaki rink’a nuna kunya ba…..” Katse ta Feenah tay da fad’in “ba kamar yadda take da kishiya kuma ma baturiya, gaskiya dole sai kin zage wllh don su ba wata kunya gare su ba don ma ita tana ruwa biyu…..” Aunty Mareeya ta kar6e “kin ji dai ko, wannan nasan har yawo daga ita sai d’an pant in ma tasa kenan tana iya yi a gaban shi, don haka ki zage wllh balle ke da ma kike da surar jan hankali Tubarkallah, ki kuma dage da gyara jikin ki ciki da waje, duk magungunan da nayi maki bayani kada ki wasa da shan su sannan kuma kada ki k’asa a guiwa wurin faranta mashi irin su ta nan wajan aka fi kama su, ki sashi ya susuce ta yadda duk in zaiyi Magana sai ya ambaci sunan ki alamar kece a ran shi koda yaushe” gaba d’aya suka sa dariya harda Fauzy dake can d’ayan side d’in gadon raku6e,

 

Feenah ta d’aura da fad’in “Bayan wad’annan kuma sai a had’a da biyayya don itace zata k’ara taimakawa wurin siye zuciyar shi duk da nasan ke mai biyayya ce a gare shi tun ba yanzu ba, to ki k’ara akan wadda kike mashi don yanzu ne zata fi yin aiki kuma zaki fi cin ribar yin ta, a k’arshe ina Addu’ar Allah yasa Alkhairi a zaman ku ya had’a kawunan ku gaba d’aya da abokiyar zaman taki ya kauda fitina ya bashi ikon yin Adalci a tsakanin ku, ya albarkace ku da zuria d’ayyiba” su Aunty Mareeya ne suka amsa ita kuma Fatun kan ta na a k’asa, lokacin Abbas ya lek’o cikin d’akin yace su suke jira fa duk suka mik’e ya d’aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d’aukar shi zatay ba ya k’arasa shigowa cikin d’akin ta kinkimo mashi Abdul d’in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad’in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k’aramar rigima za’ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d’in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k’ok’arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d’an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k’walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d’an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace “ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had’u School” da k’yar ta k’arasa Maganar, jin kuka na niyyar k’wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d’age k’afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali……………..

 

 

 

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button