Karfe A Wuta Chapter 40 By Ayshercool
Muryarta na rawa ta ce “Meyafaru? Wani abun ne ya same shi, ko ya yi wa wani?”Ya ce “Ni ma ban sani ba, oga walid ne ya ce “In zo mu tafi tare “Jikinta a sanyaye, ta kulle gidan, ta bi Nura guduma suka tafi, suna tafe tana ta addu’a a ranta.Wani private clinic suka je, emergency suka nufa, ana ta kai komo da matasa, da aka ji wa raunuka daga wurare daban-daban na harkar zaɓe, kasancewar an yi tarzoma sosai da sosai a wasu wuraren, kuma nan asibitin ne mafi kusa.Da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wani irin yammmm haka jikinta yake yi mata, saboda tsoro da tashin hankali.A ƙofar wani ɗaki, ta tarar da Walid hankalinsa a tashe, yana kaiwa yana komowa.”Yaya walid, meyasame shi? Ko mutuwa yayi?”Walid ya ce “Ki nutsu ba mutuwa yayi ba, yana ta kiran sunanki ne kafin mu zo nan”.”To meya same shi, yana ina?”Ganin likita ya fito daga ɗakin da yake facing ɗin su, ya sanya ta saka kai ta shiga ita ma.Gigicewa ta yi, ganin Wuƙa a kwiɓin Al’amin a tsaye tsororo, jini baya zuba, amma tana jikinsa, ga gefen kansa, an naɗe shi da bandeji. An saka masa oxygen, gefe ga oxymetre na reading vitals ɗin sa.Cikin kuka ta ce” Innalillahi wa Innalillahi raji’un, meya same shi haka? Waye yayi masa haka, Master dan Allah ka tashi, kar ku ce mini mutuwa yayi” tayi maganar tana rirriƙe hannunsa cikin tsananin tashin hankali.Kukan jauhar ya janyo hankalin likitoci, da m’aikatan jinya, suka ce meyasa aka bari ta shiga?Da ƙyar aka fito da jauhar ana rarrashinta, aka tabattar mata da yana da rai, tiyata za a shiga da shi a cire masa wuƙar, sai a duba kansa.Cikin tashin hankali ta ce “Dan Allah likita zai rayu?””In sha Allah, da kun biya kuɗin za a shiga da shi”Ta kalli Walid ta ce “Yaya Walid, nawa ne kuɗin?”Walid ya ce “Kuɗin da yawa, P.A ɗin Indabo muke kira, su biya kuɗin, hannunmu kuɗin ba za su kai ba ayi masa aikin””Ka gani ko? Sun ma ƙi ɗaga wayar, su suna can hankalinsu a kwance, suna jiran sakamakon zaɓe, ni kuma an kassara shi, wannan tashinsa ai sai Allah”Liti ya ce “Ki yi haƙuri, in sha Allah zai tashi””Nawa ne kuɗin?””Da ɗan yawa, ki bari kawai”Ta girgiza kai ta ce “Ni ku gaya mini dan Allah, a nema tun da wuri, wuƙa ce fa a cikinsa” tayi maganar tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.Suka din ga rarrashinta, amma taƙi saurarsu, Liti ya ce “Bari na yi gaggawa na je na samu wannan banzan mutumin P.A, ko dai a san yadda za ayi a biya, wallahi ko mu jiƙa musu aiki”Jauhar kamar za ta yi hauka, ƙarfin Addu’a ne kawai ya saka mata nutsuwa, ta din ga kaiwa tana komowa, gashi an ce ba zata sake shiga ta ganshi ba.Jauhar ba ta san yadda aka yi ba, liti da Nura guduma suka dawo da kuɗi, suka biya.Ake ce ana buƙatar jini, dan da yiwuwar ana cire wuƙar, jini ya ɓalle. Haka suka din ga zirga-zirga, jauhar itakaɗai a cikin su, babu wani daga danginsa, babu daga nata.Nura guduma ne ya bayar da jininsa, dan shi ne yayi dai-dai da na Al’amin, aka shiga da shi tiyata.Hawaye suka kasa barin idanunta, zuciyarta ta din ga wani irin zafi, ba ta taɓa tsanar wani abu ba, tsana mai muni sai yau duk da ba ta taɓa ganin indabo ba, tsananin haushinsa take ji, dan shi ne musababbin wannan tashin hankalin.Ta kai ta kawo, ta tsuguna tayi kuka, aka shafe sama da awa guda, ba a fito da shi ba, tayi alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta, ta tayar da salla, sai dai tana cikin sallar sai ta hau wasi-wasi, da tunanin me zai faru ta kasa nutsuwa.Babu tsammani likitocin suka fara fitowa, dan team ɗin tiyatar sun kai su biyar, gaba ɗaya suka nufe su, suna tambayar yaya?.Jagoran tiyatar ya ce “Alhamdilillah, an cire wuƙar, kamar yadda muka yi tsammani ya zubar da jini sosai, amma an saka masa jini, zamu kai shi ɗakin hutu, amma ba ma son a din ga shiga ana fita da sunan dubiya, kafin a kai shi ɗakin hutun, za a yi masa hoton kai, duk da saran da aka yi masa a ka bai yi zurfi ba, amma akwai buƙatar a duba”.”Alhamdilillah ala kulli halin, Doctor mun gode Allah ya saka muku da alkhairi, ya jiƙan magabatanku, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya ku bar aiki lafiya, ka da Allah ya wulakanta rayuwarku bayan ajiye aiki”.Cikin farinciki suka din ga amsar addu’a jauhar, da Amin, tare da ba ta ƙwarin gwiwa a kan zai tashi ya warware gaba ɗaya.Bayan an yo hoton, suka tabattar da babu internal injury, jauhar ta zauna ta zuba masa ido, ga jini yana shiga jikinsa a hankali.Walid ya ce “Ina ganin ki koma gida, ko ni sai na kwana da shi a nan, kin ga idan ya tashi ba abun da zaki iya yi masa””A’a idan na koma ba zan iya zama bama, hankalina ba zai kwanta ba, ni kawai ku bar ni”.”To ai dole sai da namiji, ko zaki iya ɗaga shi, idan yana buƙatar hakan?”Cikin ƙwarin gwiwa ta jinjina kai alamar eh.Duk da alhini da suke ciki, sai da suka yi murmushi.Walid ya ce “Bakomai, ki kwana da shi, sai na kwanta a waje ni, idan ana buƙatar wani abun sai ki kira ni, yanzu bari na sayo wani abun, ki ci”.”Bana jin yunwa”Haka suka kwana da Al’amin, amma bai farfaɗo ba.Ta din ga kallon wayarta, tana tunanin wa za ta kira, kamata yayi ace tana da wanda za ta kira, a kawo mata abun da zata buƙata saboda zaman asibiti, amma ta san ko za ayi mata sai an yanƙwanata ko gaya mata maganar da zata ɓata mata rai.Kwana suka yi likitoci na kaiwa da komowa a kansa, ƙarfe shida ta kira Abbu a waya, ya dawo daga masallaci kenan, ya ga kiran jauhar. Ya ɗaga a nitse suka gaisa.Ta gaya masa abun da ya faru, dumm ƙirjinsa ya buga, duk da ba wannan ne karon farko da Al’amin yake kai kansa in da ake cutar da shi ba.Abbu ya ce “Shikenan, ki yi haƙuri ki daina kuka, in sha Allah zan zo asibitin, daina kukan haka yarinyar kirki”.Rahila da bacci take yi, sama-sama take jin sa ta ce “Lafiya, kai da waye?””Matar Al’amin ce, wai suna asibiti an caka masa wuƙa a ciki jiya a wurin zaɓe””Kai amma ka tsorata ni, shi ne ka ke ta rafka wannan salatin haka? Yau ya fara zuwa ayi masa illa a yawonsa? Dan Allah ka kwantar da hankalinka”Ya kalleta ya ce “Wuƙa a cikin sa fa aka ce mini, waya sani ma ko mutuwa yayi, Rahila Al’amin fa ɗa na ne, ba shi nake ƙi ba miyagun ɗabi’unsa ne ba na so””Lallai kam na ga Alama, Allah ya bar soyayya” ta juya ta cigaba da bacci.Ƙarfe shidan, Nura guduma ya zo Asibitin, Walid ya saka ya raka jauhar gida, ta ɗebo kaya.Suka tafi, jikinta duk a sanyaye.”Dan Allah Nura kana ganin zai tashi?”Ya ce “Eh mana, in sha Allah, shi fa master ɗan baiwa ne, bar ganin abun da yake yi, yana da sa’a sosai da sosai in sha Allah zai tashi “”Amma ya aka yi aka yi masa haka?””Wallahi ban sani ba, wai dai husuma ce ta tashi a wurin tattar sakamakon ƙananan hukumomi, amma ban san shi ya aka yi hakan ta faru ba”Jauhar ta ce “Allah ya sa ya tashi ya warke”Ya amsa mata da “Amin”Ko da taje gida, ta ɗebo kaya suka koma, Alluran da aka yi masa sun fara sakinsa, ya na ‘yan maganganu a hankali.Ban da ‘yar madara babu abun da yake kira, ta je ta zauna a kusa da shi, ta riƙe hannunsa, ta kifa kai tana kuka mai ban tausayi.”Gaskiya ƙanwa idan baki daina kukan nan ba sai kin tafi gida, duk muna jin abun da ki ke ji, daurewa muke yi, ba gashi yana magana ba ya kusa dawowa duka”Ta girgiza kai “Yaya walid ba ka san me nake ji bane””Mun sani, amma ki yi haƙuri”Abbu ne yayi sallama, wanda jauhar ba ta taɓa tsammani ba, ta dai gaya masa ne kawai, kar ace ba ta faɗa ba.Da sauri ta tashi ta durƙusa ƙasa tana gaishe shi ya ce “Jauhar sannu ya mai jikin?””Jiki da sauƙi Alhamdilillah”Su Walid ma duk suka gaishe shi.Ya ƙarasa gaban gadon, ya ƙura masa ido, ya ce “Ya aka yi abun ya faru”Tayi sauri ta ce “Zai dawo gida ne wasu suka yi masa haka da daddare”Kallon da su liti suka yi mata, ya sanya Abbu gane ƙarya take yi.”Yanzu ya ake ciki to?”Walid ya ce “An yi aiki an cire wuƙar”Ya jinjina kai ya ce “Alhamdilillah, Allah ya tashi kafaɗunsa”Suka amsa da “Amin”‘yar madara da yake ta maimaitawa ya sanya Abbu cewa “Wace ‘yar madara kuma?”.Gaba ɗaya suka kalli Jauhar, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya.Abbu ya yi murmushi ya ce “Ikon Allah”Nurse ta shigo, ta ba su takarda a sayo magani.Abbu ya bayar da kuɗi aka sayo, ya din ga yi wa jauhar nasiha a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta, dan har a lokacin tana kuka.Sai dai wata nustuwa ta saukar masa, ganin Al’amin yayu ƙalau da shi.Har azahar suna tare da Abbu, daga bisani, ya ajiyewa jauhar kuɗi, ya ce “Duk yadda ake ciki su kira shi.Liti ne ya fita waje, ya kira P.A da wayar Al’amin, aikuwa ya ɗaga.Wata muguwar ashar ya narka wa P.A sannan ya ce “Saboda kai ɗan haramun ne, nake kiran wayarka tun jiya, ka ƙi ɗagawa. Saboda baku da mutunci daga kai har ubangidan naka, saboda kare ƙuri’arku, da ƙoƙarin hana ƙona sakateriya, yara sun fi sha biyar suka rufar masa da sara, ban da Mu ma akwai yaranmu a wurin da sai sun kashe shi, ka san ba maganin tauri yake sha ba, bakomai ba. Ka tsaya ka saurareni ma jiyan ka ƙi, da ƙyar aka samo kuɗin yi masa aiki, to wallahi ku saurari abun da zamu yi mu ma, wallahi hukumar zaɓen zamu cinnawa wuta, uban kowa ma ya rasa. Zaka gane ba ka da wayo daga kai har shi””Ka ga tsaya, duk na san a cikin yaransa ne, ku yi haƙuri kun san yanayin halin da muke ciki ba a nutse muke….”Halin da ku ke ciki ya fi rayuwarsa kenan? Ku sauraremu nan da wani lokaci” ya kashe wayar.Ya koma ɗakin da Al’amin yake, ya tarar da ya farfaɗo, har an ɗaga shi zaune ma, jauhar ta haɗa tea tana bashi, sai dai idanunta sun gaza daina zubar da hawaye.Al’amin ya zuba mata ido ya ce “Abbu ya zo nan?” Ta ɗaga masa kai alamar eh.”Dan ke ya zo ko bani ba? Ke ki ka yi masa magiyar ya zo?””A’a”Walid ya ce “Liti mu ba su wuri, abun na baru ne””Master”Ya kalleta, idanunsa sun yi ja, alamar yana jin jiki.”Ba na ce ka daina yi wa kanka illa ba, ko dan saboda ni? Sai zuciyata ta fashe hankalinka zai kwanta ko? In sha Allah kujerar nan ko ya sameta sai ta zame masa masifa. Ban taɓa yi wa wani muguwar addu’a ba amma na yi masa. Nayi nayi ka rabu da mutumin nan, ba mutumin arziki bane ba, amma ka ƙi aishikenan gashi nan yanzu ka janyo mana wahala”.Ya lumshe idanunsa, dan ba ya son ya ga tana zubar da hawaye.Jauhar ba irin addu’a da ba ta ja wa indabo ba, dan shi ne kanwa uwar gamin ƙara ta’azzara rashin jin Al’amin.A washegari hukumar zaɓe, ta sanar da soke zaɓen ƙaramar hukuma uku, ciki har da ta su Al’amin wadda kuma take ta indabo, sakamakon tashe-tashen hankali da aka samu, da kuma ƙona wasu daga takardun da aka kaɗa ƙuri’a.Tuni P.A ya sanar da Indabo saƙon su Walid, kuma kansile ƙanan hukumomin, babbar barazana ce ga nasarar indabon.Babu shiri, washegari da daddare suka shirya suka tafi wurin malamin su, da shi da P.A, malamin ya tabbatar musu da cewa, an samu tangarɗa a aikin da aka yi ne, yarinyar da yayi amfani da ita, ta haura shekarun da ake buƙatar, kuma a yanzu ba abun da zai iya yi musu, sai dai a bi wasu sabbin dabarun, a samu a haye.Suna tafe a hanya P.A ya ce “Honorable, wallahi yakamata ka duba mai zamani, da ƙyar idan ba yaransa ne, suka tayar da tarzoma ba, ka san dole zamu sake buƙatar su, mussaman yanzu da zaɓen ya zama inconclusive”.Indabo ya ce “Matsalar yaron nan na ta ƙarewa wallahi””To ya zamu yi, haƙuri zamu yi tun da muna amfanarsa”. Indabo ya amince da hakan, P.A ya kira liti ya tambaye shi in da suke kwanceAl’amin so yake Jauhar ta zauna a kusa da shi, ya ji ɗuminta su yi hira, amma alamu suka tabattar masa da fushi take yi, dan da tayi masa abun da za ta yi masa sai ta koma gefe, ta ɗauki wayarta tana karanta Alqur’ani.Ga kawo-kawo ɗin da ake yi, kuɗin hannunta duk sun ƙare, dan ma su liti suna tsaye suna tallafawa, kuma idan Abbu ya zo ya kan ba ta kuɗi, duk da zuwan nasa biyu ne kawai.Wajen ƙarfe ɗaya na dare ne, Ranar Walid da liti duk suna nan, duk da da facemask, a fuskar Indabo sai da suka gane shi, suka tashi suka ni bayansu.Jauhar ta ɗaga kai ta kallesu, Al’amin ya buɗe idonsa da yake a rufe a da.Jami’an tsaron suka bashi kujera ya zauna, yana kallon Al’amin da satar kallon jauhar.Ta tashi ta ce “Lafiya?”P.A ya ce “Baki gane ni bane, wanda ku ka zo wurina lokacin yana prison, honorable ne wannan, ya zo da kansa ba saƙo duba shi” ta haɗe rai sosai, kamar ya make shi ta huta haka take ji.Ya sauke facemask ya ce “Sannu kin ji, ya mai jikin?”Shiru tayi tana cigaba da haɗe rai.Ya kalli Al’amin ya ce “Wannan ce ‘yar madarar kenan?” Al’amin ya ƙura masa ido, bai yi magana ba.Ya kalli Walid ya ce “Ba ya iya magana ne?””Yana yi””Dama cewa na yi bari na zo na ga yanayin jikin naka, Allah ya ƙara sauƙi. Ban sani ba ko ka samu labarin an soke mana wasu ƙuri’un abun bai yi daɗi ba, muna nan dai muna ta addu’a “Ya karkace ya ciro kuɗi kaya guda, ya miƙawa jauhar ya ce “Ga wannan a sai magani”Ta girgiza kai cikin takaici ta ce “Ba ma so, ka riƙe kuɗinka ni babban burina da fatana, ka fita daga rayuwar mijina, nima ina burin na ga ya shiryu ya zama mutumin kirki, kai ne ka ke saka shi aikata duk wani abu na rashin kyautawa. Idan ya shiga matsala kuma ka zame ka bar shi. Yanzu an riga an cuce ni, an tsugunar da shi. ‘ya’yanka su suka fi cancanta su yi maka irin aikin da yake yi maka, tun da sun fi morarka, idan abun na Allah ne ka karɓi takardunsa ka sama masa abun yi mana, amma babban burnku yaran wasu su sha su bugu su sayar da rayuwarsu a banza gare ku”.Ɗaya daga cikin jami’an tsaron ya daka mata tsawa, ta ce “Wallahi ko zaku kashe ni sai na faɗi gaskiya, nima ‘ya ce, kuma na cancanci zama da nagartaccen miji, na san akwai iyaye da yawa da suke da burin ganin yaransu a hanya madaidaiciya amma duk hana hakan, ni dai dan Allah ka rabu da mijina, ka ƙyalemu”Maimakon ya ji haushi, sai yayi murmushin ya ce “P.A wato duk isa da kwarjinin namiji ya je gaban mace, sai abun da Allah ya yi, kalli Mai zamani a gaban matarsa. Aishikenan yarinya haryanzu baki san rayuwa ba, wannan yanayin mafita kawai ake nema, ki daina yi wa manya rashin kunya. Kuma mijinki zaki gaya wa ya daina abun da yake yi ba ni ba. Tun da a haka na ganshi, ki karɓi kuɗin nan”.”Ba ma so, ba zamu karɓa ba” tayi maganar tana kuka.Ya miƙawa P.A kuɗin, ya karɓa ya miƙawa Viper, shi kuma ya karɓa.Indabo yayi murmushi ya fice da tawagarsa.”Master ni ka dizga ka kunyata a gaban mutane, gara ka cigaba da karɓar kuɗinsu kana shaye-shaye ana yi maka lahani, ni ko? Kai am tired na gaji, ba zan iya ba na sare. Na ɗauka abun mai sauƙi ne, amma ya wuce yadda nake tunani, you are not willing to change. Kana samun sauƙi gida zan koma, na gaji da auren”Liti ya ce “Subhanallah, dan Allah kar ki yi mana haka anty ƴar madara, muna murna Allah ya saya mana shi, kuma ki tafi ki barmu, ba fa shikaɗai ba har mu zamanki tare da shi muna amfana””Eh, kuma har da ku ai, kullum ku kuke ƙara haɗuwa da shi, ku ke ƙara abun da bai kamata ba, Allah ya sa na mutu na huta”.Duk wannan abun, yayi burus yaƙi magana.”In sha Allah, ba zaki mutu ba, ana mugun tare ai””Ba wani tare, ku daina shaye-shaye mana, kuma kullum a kansa tsautsayi yake faɗawa, ni na gaji, yana warkewa tafiya zan yi na haƙura da zaman da shi” tayi maganar tana kuka, har ta fara tari mai haɗe da haki.”Mai laya””Allah ya ƙara maka lafiya””Ayi walƙiya, sai da safe”Walid ya ce “Iya wuya, yadda ka ke so haka za ayi” suka tashi suka fice, ya juya ya saukko daga kan gadon.Kamar ba ciwo ne a cikin sa ba, ya tunkaro in da take ya zauna, ya ƙura mata ido tayi shiru ta sunkuyar da kai, tana haki sama-sama.”Ki ka ce tafiya zaki yi?””Eh” ta bashi amsa kai tsaye.”Yaushe?” “Kana warkewa gida zan koma, tun da ba ka so na, kullum cikin sakani ka ke a tashin hankali, na ce maka ba na son ka din ga zuwa in da za a ji maka ciwo, amma ka ƙi, ka dizgani a gaban wannan mutumin. Wallahi ba zan taɓa yafe masa ba, duk shi yake ƙara ɓata ka”.”Yanzu abun da ki ka yi dai-dai ne? Ubangidana ne fa, ki ka tsaya kina yi masa rashin kunya”.A ƙule ta ce “Shi dai-dai ɗin yayi mini, ba dan Allah ya yi da sauran kwananka a gaba ba, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, ni na rasa in da zan saka raina, abun da nake ta tunanin zan iya ashe ya fi ƙarfina, shikenan”.Gyara zamansa yayi, ya janyota jikinsa, yana kissing ɗin ta a hankali.She’s not in mood, ta so ta ƙwace, sai dai kuma raunin jikinsa ya hanata yin hakan, kar ta fama masa.A hankali ya cire bakinsa daga nata yana kallon ta, amma ta haɗe rai tayi kicin-kicin.”Ki gaya wa likitocin nan su sallameni gobe, ko kuma na yi tafiyata”Da sauri ta kalleshi ta ce “A hakan ba ka warke ba?””Eh na gaji da yadda ake zuwa ana magana da ke, haushi nake ji, shi kansa indabo shirun da nayi masa, shi ne mafi alkhairi da mummunan naushi zan yi masa””Dan Allah ni ka daina taɓa ni, asibiti ne fa, idan wani ya shigo fa?””To je ki rufe ƙofa ki dawo, zafi nake ji, ina buƙatar fankata, lamba uku kawai, ba sai an ƙure mata gudu ba””Ko mafici ba zaka samu ba, ni rabu da ni” tayi maganar tana sake ture shi.Ya ƙi tashi ya din ga takura mata, duk dan ta sake ta ɗan samu nutsuwa daga fushin da take yi.”P.A wane mahaukaciya ne ya aura wa yarinyar nan mai zamani?””Allah masani honorable””Ikon Allah, kalarta kalar muryarta, ai rannan na kira ta ɗaga, kai ka ga yarinya zuƙeƙiya kamar ita tayi kanta. Amma kamar ta dace da aikin da malamin nan fa ya bayar, ya aka yi ba ka yi mini zancenta ba, gashi wannan an samu matsala”P.A ya ce “Honorable, kai ka san ba kowane kaya ne yake taɓuwa ba, idan aka taɓa wannan za a iya samun matsala, kuma na manta da ita ne gaba ɗaya wallahi”Indabo ya ce “Wace irin matsala? Ai tsaf za ta taɓu, ba tare da ya sani ba, idan ma ya sani na san yadda zan yi da shi. Lallai ‘yar madara tayi kalar madarar sosai. Wannan yarinyar ita ce rauninsa kenan?””Sosai kam, dan alamu sun nuna yana mugun sonta”Indabo yayi wani irin murmushi yana shafa tumbinsa.Maƙwabtan su Jauhar sun yi mata kara, na zuwa duba Al’amin, suka kakkai mata abinci, daga gidan su Baba ya je Saifu sai mama, sun je sun duba shi, duk da maman ta gaggaya mata baƙar magana a kansa.Satinsa ɗaya da ƙyar, ya uzzura akan lallai, sai an sallame shi, haka aka sallame su suka koma gida.Cikin ikon Allah, Indabo yayi nasara, bayan faɗi tashi, da shige-shige yayi nasarar samun kujerar ɗan majalisa.Har gida Abbu ya sake zuwa duba Al’amin, sai dai kamar wurin jauhar ya zo, da ita suka ɗan yi hira, ya tashi ya tafi.Hafsa kuwa abun duniya ya hanata sukuni, da ƙyar ta samu Alhaji mu’azzam ya fara saurararta, sai dai yadda yake bin matarsa sau da ƙafa, yake ƙona mata rai, sai abun da ta tsara yake yi a gidan, idan ba ta ga dama ba, sai ya shafe kwana goma bai taka wurin Hafsa ba, amma kuɗi akwai su, komai take buƙata akwai shi, sai dai fa tsakaninta da miji sai an ga dama a bata aro, wataran yana wurin nata ma, za ta kira shi, kuma haka zai tsallaketa ya tafi wurin matarsa, ga yaransa marasa kirki, sun rainata rashin kunya kala-kala.Da ta matsa ma da ƙorafi, ya ce idan ta gaji ta tafi, shi fa duk lokacin da ya zo wurinta, baya gane komai, haƙuri kawai yake yi shi ma, ta ƙyale shi.Ta gaji tayi yaji, Anty ta din ga yi mata masifa, a kan dan me zata dawo gida, sai asirinsu ya tonu, dole ta cigaba da zama har zuwa lokacin da za a samu mafita.Al’amin ya warke sarai, ya cigbaa da harkokin sa, sai dai jauhar kusan kullum tana gargaɗinsa a kan indabo.Gashi ta riƙe masa wuta a kan yin salla a kan lokaci, da yin azkar, har zama tayi ta ciro masa addu’oi na musamman ta rubuta masa su.Ita kanta ta san ikon Allah ne, da ƙarfin addu’a da take yi, da kuma yadda take bin sa da kyautatawa da biyayya, ya sanya take iya sarrfaa Al’amin, har yake jin nauyin aikata wasu abubuwan saboda ita.Da asuba idan ya je salla ya dawo, da kanta take ajiye masa sigari, kara biyu ko uku, ta ce masa ya sha banda shan ƙwaya kuma.Ta jira ya gama sha, yana ƙaurin yana komai, ta naniƙe masa a jikinsa, dan mantar da shi damuwa, kewar kayan shaye-shayen sa.Da daddare suna kwance, ta ce “Master, ka san abun da matar nan tela tayi mini?”Ya ce “A’a””Wai na cewa matar nan dan Allah, ta koya mini ɗinki, idan ta yarda zan tambaye ka, na din ga zuwa, ta ce mini za ta yi shawara, wai daga baya ta ce mini mijinta ya ce a’a bai yadda na din ga zuwar masa gida ba, ko kara ba ta yi mini ba, duk wahalar da nake yi mata, wani abun ta biyani wani sai dai na yafe kuɗin, na ji haushi dama kuma ba ta zo tayi mini jajen abun da ya same ka ba””Saboda ni me mijin ya ce bai yadda ki je gidansa ba?””Wallahi ban sani ba, na dai ji babu daɗi gaskiya, amma ban san dalilinta ba”Al’amin ya ce “Manta da ita, Allah ya baki wani abun da ya fishi, uwar son kuɗi””To wa ya ƙi kuɗi master” yayi murmushi yana shafa bayanta.Da asuba, mutane sun fito daga masallaci, faruku tela ya ga Al’amin a ƙofar gidan sa.Gabansa ya faɗi ya ce “Lafiya kuwa?”Al’amin ya ce “Saƙonka na ji, ‘yar madara ta ce a koya mata ɗinki ka ce a’a, fine idan na kuma ganin ‘ya’yanka sun tako mini gida, sai na daddatsa su, na zuba a leda na kawo maka.Na kuma yi suspending ɗin shagonka, na wata guda, wallahi ka buɗe sai an sassara mini kai” yayi tafiyar sa ya bar faruku a wurin, cikin tashin hankali.Ƙarshe sai da aka haɗa da zuwa har gida, magidanta suka zo ban haƙuri, jauhar tayi mamakin abun da yayi, ita kawai hira tayi masa abun miji da mata, amma ya je yana yi wa mutumin barazana. Ta ce zata yi masa magana ba wani abu, malam faruku ya cigaba da buɗe shagonsa.Ya dawo da daddare, ta sha kwalliya, kamar yadda ta kan caccanza tare da ƙirƙiro da sabbin abubuwa, domin sabunta abubuwa da yawa a rayuwar auren na su, saboda rage barazanar gundurar juna.Ya nemi wuri ya zauna a falo, yana ta sauke numfashi, ta fito ta na murmushi ta haye kan cinyarsa, ta zuba masa ido ya lumshe idonsa yana ta huci kamar kumurci.”Nawan” tayi maganar tana shafa sajensa.”Yau kuma me aka sha haka? aka ƙi kulani” yayi shiru bai ce mata komai ba.”Master””Mmm””Me ka sha yau?””Wiwi”Jauhar ta ce “Da me?”Ya girgiza mata kai alamar babu.”Ba ka saba ƙarya ba” ta saka yatsanta a bakinsa, ta ciro guntuwar ƙwayar da take ƙasan harshensa, laɓɓansa sun yi fari.”Ƙwaya ko? Meyasa. Na ce fa idan an ɓata maka rai ne, ko kana cikin damuwa ka yi ta ambaton Allah, kana azkar, meyasa za aje a sha ƙwaya, ka ɓata mini shirina na yau gaba ɗaya”Babu tsammani, ya miƙe da ita a jikinsa, ya tafi da ita ɗakinsa, rabi a buge yake, rabi a cikin hayyacinsa, yayi ƙoƙarin kissing ɗin ta, ta ce “Ba zaka sumbace ni, da sauran ƙwaya a bakinka ba master, me aka yi maka?””Mhmmm bakomai, i need you”Ta ce “A hakan, a buge fa ka ke””Ina hayyacina, kin yi mini kyau ne sosai” kasa hana shi tayi, ya gama ya cigaba da yi mata surutai.Ta rungume kansa a ƙirjinta tana shafawa ta ce “Na san wataran zaka daina master, Allah ya shirya mini kai mijina””Madarata”Ta ce “Idonka biyu””Mmm””Me zaka gaya mini?””In sha Allah zan daina, ki cigaba da yi mini addu’a” yayi maganar cikin muryar maye sama-sama.”Addu’a kullum ina yi maka master, Allah ya nuna mini ka daina””Madarata””Master na”Ya ja jikinsa, ya kai bakinsa saitin kunnenta, ta yi shiru, tana jiran ya yi mata magana.Kawai ya fara murmushi, yana yi mata numfashi a kunne.”Zaki koma makaranta””Allah ya ja zamaninka, godiya nake”Cikin mayen ya sake cewa “Ki daina yawan kuka ba na so””To ka daina sakani””Allah ya bani kuɗi na kai ki makka” “Amin Mijina, da alama ƙwayar nan nishaɗi take sawa””Ke ce nishaɗin nawa” yayi maganar yana dariya.Ita ma murmushin ta yi masa, ya kwanta a gefenta, bacci ya ɗauke shi.Da Asuba ya rigata tashi, ya tasheta shi kuma yayi wanka yayi alwala ya fita.Da wani irin tashin zuciya ta tashi, kamar za ta yi amai, ta danganta hakan da awarar da ta yi wa cin ƙoshi jiya da daddare ulcer ta tayar mata.A ɗakinsa ta yi sallar ta idar, idonta ya sauka a kan robar cocala da ke gefen katifarsa.A take ta ji idan ba ta sha coke ɗin nan ba, akwai matsala.Ta ɗaukko, ta buɗe ta kafa kai ta fara sha, sai da ta shanye tas, sannan ta ajiye jarkar, still ta din ga jin kamar za ta yi amai. Ta yinƙura ta tashi, ta tafi banɗaki, ta yanke jiki ta faɗi, jini ya fara gangarowa daga hancinta.
Ayshercool 08081012143
