Hausa novels

Kanwar Maza Page 83 Complete Novel By Ayshercool

Page 83

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

 

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”

 

Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi.  Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….

 

(*Ina ma’abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma’ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

 

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

 

 

 

Miƙewa Ammi ta yi cikin sauri ta ce “A ina ki ka ji?”

 

Nusaiba ta ce “Yanzu su musa suke faɗa, wai a asibiti ya kwana ma, tun cikin dare aka kai shi”

 

Rikicewa ammi tayi, ta nufi ɗakinta, Nusaiba ta bita ta na cewa “Ammi me zaki yi?”

 

“Nusaiba asibitin zan tafi, ni babu wanda ya gaya mini ai”

 

Nusaiba ta ce “A’a Ammi, kar ki je su yi miki wani rashin mutuncin, ki fara kiran takawa ki gaya masa”

 

“Yaron ya kwana a asibiti, ki ce sai na kira takawa na gaya masa?”

 

“Dan Allah ammi ki bari ya zo tukuna, sai ku tafi tare ma, kar su cutar da ke” da ƙyar Nusaiba ta shawo kanta, ta amince a kira takawan tukuna”.

 

Juma’a ce, dan haka rumaisa ta ce ba zata makaranta ba, dan jikinta babu daɗi ko ina ciwo yake yi mata.

 

Takawa sai lallaɓata yake yi, yana son ya fita aiki, sai sangarta take yi masa, da shagwaɓa kala-kala.

 

Wayar Ammi ya gani, dan haka ya ɗaga tare da yin sallama.

 

Cikin ruɗewa ba tare da ta iya amsa sallamar ba ta ce “Takawa, kana ina ne? Mahmud aka kwantar a asibiti, wai ya kwana yana ciwon ciki jiya, so nake na je”

 

Takawa ya ce “Dan Allah ammi ki kwantar da hankalinki, ki bari na je wurin aiki, idan aka saukko daga masallacin juma’a zan zo na kai ki ki duba shi”.

 

“Baka da hankali ne? Ka san ciwon ciki kuwa? Yaron ya kwana a asibiti amma ka ce sai an idar sa sallar juma’a awa nawa? Idan zaka kaini ka zo yanzu, idan ba zaka zo ba zan yi tafiyata ko me za su yi zan jure tun da ni na kai kaina”

 

“Kiyi haƙuri gani nan” rumaisa ta zuba masa ido, bayan ya kashe wayar ya ce “Duk ta rikice a kan ɗan da bai san darajarta ba, nan zai yi ciwo ta je duba shi, ta hanata ganinsa ta ce bacci yake, ko baya son hayaniya amma za  taje duba shi, ammi ba ta gudun abun da zai ɓata mata rai sam”

 

Ruma ta ce “Dan Allah zuciyar mutum ce a jikinka? Ka san me ake nufi da uwa da ɗa kuwa? Kai banda dalilin sihiri da nake da tabbacin shi ya raba ammi da daddy, kai kana zaton akwai dalilin da zai sanya ta zuba ido ta barwa wata mata ɗan ta.

To ai ko ni da abun da ke cikina bai zo duniya ba, da shi da Sabir, ban ga wanda ya isa rabani da su ba, kai idan aka ce za ayi asirin ma, sai na haɗa asirin da bokan na ci ubansu wallahi.

Dan Allah papa kaima ka sassauta wannan ƙiyayyar, yanzu bari in saka kaya in bika”.

 

Ya ce “No, ki zauna a gida, zan je kawai”

 

Ruma ta ce “Hankalina ba zai kwanta ba, ka tafi da ni dan Allah, idan ba haka ba zan biyoka idan ka fita”.

 

“Mimi kina da matsala, cikin nan ne bana son a gani”.

 

Ta kalleshi ta ce “Saboda me?”

 

“Kin fi kowa sani ai, ba na son wani abu ya samu cikin nan naki, kullum cikin Addu’a nake yi Allah ya sa ki haihu lafiya, kin san komai ai”

 

“Babu abun da zai faru sai ikon Allah, ka tafi da ni saboda zatin Allah, hijjabi zan saka, ba wanda zai gan shi ai” kasancewar rumaisa ta ƙware a iya magiya, tamkar ƴar maroƙa, haka ya sanyata a gaba suka tafi.

 

Da shi da Nusaiba, da Ammi, haka suka rankaya asibitin da aka ce Mahmud yana can.

 

Gaba ɗaya Ammi ba ta cikin nutsuwarta, takawa ya ce “Ammi dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin San ki na da high bp”.

 

A rikicen dai Ammi ta ce “Kai ka san sani high bp, ka tambayar mini ɗakin da yake dan Allah ”

 

Ruma ta din ga kallon ammi cikin tausayawa, haka ta shafe shekaru da soyayyar nan da tausayi suna nuƙurƙusa zuciyarta, ruma ta jinjinawa mugunta irin ta mummy.

 

Ba ƙaramin razana ammi tayi ba, ganin Mahmud a kwance ba ya motsi, ga ruwa an saka masa, ga kuma oxygen da take taimaka masa yana numfashi, gefensa kuma mummy ce a zaune.

 

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Mahmud meya sameka haka?” Ammi ta yi maganar cikin rawar baki.

 

Jin muryarta ya sanya shi ya motsa, ya fara yi wa ammi nuni da hannunsa ta zo.

 

Cikin hanzari ammi ta ƙarasa, idonta na ta zubar da hawaye.

 

Ya miƙa hannunsa ya riƙe nata, sai dai ba baki, sai hawaye da yake zuba ta gefen idonsa.

 

Ammi ta riƙe hannunsa tana jejjera masa sannu.

 

Ya ɗora hannun a kan cikinsa.

 

Ruma ma ta ƙarasa gaban sa cikin kuka ta ce “Daddy meyafaru? Meya sameka?”

 

Wata irin miƙa yayi bakin sa yana zubar da kumfa, cikin sarƙewar numfashi ya ce “Daughter mutuwa zan yi. Ammi. Amm….Ammi na faɗa yau rumaisa, Ammi ki yi mini Addu’a cikina” yayi maganar tamkar numfashin sa zai bar gangar jikinsa.

 

Daga rumaisa har Ammi kuka kawai suke, Nusaiba ma kuka take.

 

Cikin kiɗimewa Mummy ta tashi cikin azama, ta ce “Mahmud ciwo ba mutuwa bane ba, kar ka sake cewa zaka mutu, haba Mahmud kar ka yi mini haka dan Allah ” tayi maganar tana fashewa da kuka.

 

Ya buɗe ido a galabaice ya kalli Mummy, ya zare hannunsa daga na ammi, ya riƙo nata “Mummy na gode, na gode Mummy”

 

Ya sake zare hannunsa daga na Mummy, ya miƙawa adam, sannan ya cewa ruma “Ki ce masa ko sau ɗaya ya riƙe hannuna Daughter” ya yi maganar yana sake mimmiƙe wa.

 

Cikin matsanancin kuka da tashin hankali rumaisa ta kalli Adam ta ce “Papa dan Allah”

 

Adam da tuni ya karaya, kuma ya tsorata da lamarin, A  hankali  ya tako, ya zauna a kusa da rumaisa, ya saka hannunsa a na Mahmud ya rungume shi.

 

“Ina son ka ɗan uwana, Ƙaddara ce”

 

Mummy ta rasa in da zata sanya kanta, dan lafiya ƙalau Mahmud ya kwanta, idan har ta ce ba ta ƙaunar Mahmud ƙarya take yi. Saboda yayi mata biyayya fiye da yaran da ta haifa, kuma ta saka an ƙwace shi an bata shi, dan mugunta, amma kuma sai ta fara son sa daga baya.

 

Likita ne ya shigo, ya din ga yi wa Mahmud wasu allurai.

 

Bayan fitar likita, duk sun yi shiru sun zuba masa ido, Adam yana rungume da shi, rumaisa ta miƙe zumbur, dan tamkar ana mata raɗa ta ji komai.

 

“Me ya haɗa shi da jabir ne?”

 

Takawa ya ce “A ina?” Duk suka tsaya suna kallonta.

 

“Meyasa ya daki Jabir ya kulle shi?”

 

Duk suka zubo mata ido.

 

ganin da Mahmud yayi Mummy, tana cikin damuwa, ya sanya ya sakata a gaba, a kan ta gaya masa meke damunta, ta kasa ɓoye masa ta gaya masa komai. Ba ƙaramin girgiza yayi ba da jin abun da Jabir ɗin ya yi ba shi da ruƙayya, tun da ya fita a fusace, sai wayar Hajiya Lubabatu ta gani, ta tabattar mata da zata ga abun da za ta yi wa Mahmud muddin bai saka an sakar mata ɗa ba domin kuwa ta san muddin asirin jabir ya tonu ba zai yi sarauta ba, kuma ta fuskanci kamar yanzu Mummy ƙoƙari take taga Mahmud ne ya samu sarauta.

 

Sai a yanzu Mummy ta tuna da furucin hajiya Lubabatu.

 

Tashi rumaisa ta yi ta fara tashin Mahmud.

 

Takawa ya ce “Ya samu bacci fa”

 

“Tashe shi kawai, daddy”

 

Ya buɗe ido a matuƙar wahale ya kalleta.

 

“Meya haɗaka da jabir?”

 

“Bakomai” ya furta yana numfarfashi.

 

Ta ce “To koma me ka yi masa, babarsa ta ce zaka gani”

 

Takawa ya ce “Mimi bana son rigima fa, ke a ina ki ka ganta?”

 

Ruma ta ce “Ɗazu da asuba ina bacci, na gansu su na faɗa, ban san a kan menene ba, amma ita ta ce zai gani, jabir yana police station ko?”

 

Ammi ta tashi ta kamo ruma ta zaunar da ita, ta ce “yi shiru da bakinki” shi dai takawa a iya sanin sa, suna tare da ruma, kuma ba wani wurin suka je ba, balle ace ta ji.

 

Mummy ta hau bala’in cewar mahmud sun yi faɗa da Jabir, amma ba wani abu da Hajiya Lubabatu ta yi masa.

Tayi maganar tana karewa saboda kar a gane sun samu saɓani da Hajiya Lubabatu, kuma muddin asirin lubabatu ya tonu, na ta ne ya tonu.

 

Takawa ya ce “Mimi ba ta ƙarya a cases irin wannan, zan yi bincike a kai, duk wanda na gano da saka hannunsa wani abu ya same shi, wallahi sai ya fuskanci hukunci ko waye shi”.

 

“Matarka ba ta ƙarya ni nake yi kenan?”

 

Ammi da sauri ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri, ku yi haƙuri Takawa kar in sake jin bakin ka, rumaisa ku yi shiru mu yi masa addu’a”.

 

Ruma ta ce “To ammi, amma wallahi ba ƙarya nake yi ba”

 

Mai sunan baba ne yayi sallama ya shigo, hankalinsa a tashe, “Subhanallah” yake ta maimaitawa saboda halin da ya ga Mahmud a ciki, dan kuwa sun yi waya jiya da safe, yake ce masa zasu haɗu yau.

 

Bai iya yi wa kowa magana ba, ya ƙarasa gaban gadon yana ambaton sunansa.

 

Gashi da an kira sunansa yake amsawa, ya buɗe idonsa ya kalli mai sunan baba.

 

“Mahmud, meyafaru haka ne? Wayarka na kira wata yarinya ta ɗauka ta ce mini wai kana Asibiti” ya cewa mai sunan baba “Ɗago ni”

 

Mai sunan baba ya sanya hannu biyu, ya ɗago shi, ya jingina da jikinsa.

 

Ammi ta din ga ajiyar zuciya ganin Mahmud a zaune.

 

“Ku yi haƙuri duk na tayar muku da hankali”

 

Mai sunan baba ya ce “Kar ka damu sannu ya jikin naka?”

 

“Da sauƙi, zan sha ruwa”

 

Mai sunan baba ya kalli Adam, Adam ya ɗaukko roba ya tsiyaya ruwa ya bawa umar, ya karɓa ya bawa Mahmud, ya karɓa ya sha sosai.

 

Ya ce “Alhamdilillah, ina ƙanwata tana lafiya?”

 

“Lafiya ƙalau, bata san me ke faruwa ba, na riga na fito sannan na kira wayarka, sannu Mahmud”

 

“Yauwwa yaya” kasancewar haka yake kiran umar.

 

Ammi ce ta ce “Mai sunan baba ya gida?”

 

Ya ce “Afuwan ammi, hankalina ne a tashe wallahi, ya gida ya mai jiki kuma?”

 

Ammi ta ce “Jiki da sauƙi Alhamdilillah”

 

Mummy kuwa sai cika take tana batsewa, Fauziyya ba ta taɓa ƙarewa mai sunan baba kallo ba sai yau, lallai Iman ta auri mai kyau, da cikar zati.

 

“Me zaka gaya mini ne ka ke nema na?”

 

Mai sunan baba ya ce “Ka ji da jikinka ka samu lafiya, kana tambayata me zan gaya maka” yayi maganar yana murmushi.

 

“Am curious about it” yayi maganar yana lumshe idanunsa, saboda allurar baccin ba ta sake shi ba.

 

“Zan gaya wa yayanka ya gaya maka”

 

“Wai Takawa? Ba zai gaya mini ba”

 

Mai sunan baba ya ce “Zai gaya maka mana, zaka ci abinci ne?”

 

Ya girgiza kai ya ce “Bari sai na gama farfaɗowa, idan kuma na mutu….

 

“Shhhh, zaka farfaɗo in sha Allah, har aurar da kai sai na yi”

 

Ammi bakinta ya ƙi rufuwa dan murna, ita ba ta san ya aka yi ma ta sa ta zo ɗaya da Mahmud ba, saboda Mahmud akwai taurin kai da rashin mutunci, mai sunan baba kuma akwai izza da son girma, amma yadda yake yi masa zaka gane akwai mutuntawa da girmama juna a tsakaninsu.

 

Ya kwantar da Mahmud, ya ce “Ka yi bacci, zan je gida ƙanwarka ta yi maka girki, mu zo ta duba ka”

 

“Kar ka wahalar da ita, ga Mummy ga Ammi ga daughter duk na wanda na samu zan ci”.

 

“Ba wata Mummy, na ammi zai ci” Rumaisa ta faɗa tana harare-harare.

 

Fauziyya ta buɗe baki za ta yi magana, amma kwarjinin mai sunan baba ya cika mata ido, dan ta san ƙarya take, ta zagi rumaisa a gabansa ya ƙyale ta.

 

Ya kalli Adam ya ce “Ina son yin magana da kai”

 

Mamaki ne ya kama Adam, amma ya tashi ya bi bayan mai sunan baba suka fita.

 

Fauziyya ce ta ɗora da rashin mutunci.

 

“An yi magana wani ammi ce za ta bashi abinci, sai ka ce ammin wahalar sa ta sani, uwarmu ce dai ta yi masa duk wata wahala ta rayuwa”.

 

“Da tayi mata fashin ɗan? Kallon biri ku ke masa yake yi muku na ayaba fa. Uwar me ta tsinana wa rayuwar ta sa ban da masifa, uwar riƙon arziki ce za ta raba uwa da ɗan ta, ta raba jini da jininsa, ta raba shi da ɗan uwan sa, yanzu dai shi ma ya san gaskiya, gurbin ido ba ido ba ne, kuma wallahi ko bayan shekara dubu, tuwo sunan sa tuwo”

 

Ammi sai ƙoƙarin hana magana take yi, amma rumaisa tayi mursisi ta din ga gasawa Mummy da Fauziyya magana, ita kaɗai su biyu ba tare da kunya ko tsoro ba.

 

Duk abun nan da ake yi Mahmud yana jin su, amma yayi shiru kamsr mai bacci.

 

Mai sunan baba ya kwashe komai ya gaya wa takawa, game da Alhaji Aminu, jikin takawa har tsuma yake yi ya ce “To yanzu Lagos ɗin zamu je, ko yaya za a yi? Mu ga shi Alhaji Aminun, idan ta kama tambayarsa zamu yi, ko ma a tafi da ammi sai ayi ”

 

Mai sunan baba ya ce “A’a ina ga gara mu mu je mu tabbatar, tun da yanzu tana cikin damuwar rashin lafiyar Mahmud, dama da shi na so mu je, to gashi ba shi da lafiya”

 

“Bakomai, bari mu ga zuwa gobe in Allah ya kaimu, in dai ya ƙara warwarewa, sai mu je kawai, ina fatan Allah ya tabbatar ya sanya ƴan uwan iman ne ”

 

Mai sunan baba ya amsa da Amin, har takawa ya juya zai tafi mai sunan baba ya ce “Na ce ba” ya juyo ya tsaya yana sauraren sa.

 

“Akwai buƙatar duk abun da ya faru a baya ya wuce, a fuskanci gaba.

 

A zamana da Mahmud babu abun da yake marari da so da ya wuce ka, you have to play your role as his senior brother, babu abun da yafi ɗan uwa daɗi. Ba zaka gane hakan ba sai ranar da babu shi a duniya”

 

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce “Haka ne, na gode sosai” mai sunan baba ya jinjina masa kai ya tafi.

 

Samha sun je duba Mahmud a asibiti, dan tuni labari ya zaga masarautar, Mahmud ba shi da lafiya, ƴan dubiya sun fara kaiwa suna komowa.

 

Sai dai fa cacar baki taƙi tsayawa a tsakanin Fauziyya Mummy da rumaisa.

 

Muraran yau ruma take nuna musu asalin tantirancinta.

 

Samha za ta saka baki ruma ta ce “Yi mini shiru, ba dake nake ja gayyar mushirikai maƙiya Allah, ai wallahi a doron duniya ban ga bokan da zai yi asirin da zai kamani ba, sai dai ku yi wa wasu”.

 

“Su waye mushirikan?”

 

“Gaku nan gaba ɗayanku, ban da yawon asiri da ƙoƙarin rusa rayuwar mutane me ku ka saka a gaba, azzalumai maƙiya Allah”

 

A rikice ammi ta fita neman Adam, suka yi kiciɓis a hanya, ta ce masa maza ya je ya ɗau rumaisa ya mayar da ita gida.

 

Sai dai suna shiga ɗakin, suka tarar Samha da Fauziyya tamkar za su rufe ruma da duka, ita ma ta tsaya ta riƙe ƙugu tana bala’i, Nusaiba sai ba su haƙuri take.

 

Babu abun da ya gigita Samha sama da ganin tirtsetsen ciki a jikin rumaisa bayan ta miƙe, ta riƙe ƙugunta.

 

Ruma ta ce “Mamaki ki ke yi ko Samha, kin ga ciki a jikina? Baba uwani ba ta gaya miki na cire layar da aka saka a cikin katifar ɗakunan mu ba?.

Ai tunda Allah ya sa na ritsuta, duk wani lungu da saƙo, sai da ta tone komai, na zauna na warware abun da ki ka ƙulla mini na tsiya, masifarku sai dai ta ƙare muku”.

 

Cikin matsanancin tashin hankali Samha ta ce “Me ki ka nufi? Nima sharrin zaki yi mini?”.

 

“Wallahi na fi ƙarfin in yi miki ƙarya, rufa miki asiri kawai na yi, amma tarkacen layoyi da kayan tsubbun duk da ku ka binne mana a cikin gida an tone su, na kuma tara su wuri ɗaya saboda sheda, duk bala’inki ke da Adam sai dai ido Samha”

 

Ba tare da sanin Adam ya shigo ba, ta yi ƙoƙarin hankaɗa Rumaisa.

 

Amma cikin zafin nama, ya hana faruwar hakan, ya ɗauketa da mari.

 

Tsit suka yi suna kallon Adam.

 

“Wallahi ko da makamancin wasa, ki ka sake ki ka yi wa rumaisa wani abu, sai na taka ki, sai dai zumuncin ya watse uban kowa ya kama gabansa wallahi. Kuma na gode da abun da ki ka yi mini, na mayar da ni mara amfani a gidana, sai dai Allah ba a azzalumin sarki bane ba, kanki ki ka yi wa samha”

 

Mahaifiyar Samha ta fara bala’i “Wane irin mutum ne kai? Duk abun da yarinya ta faɗa sai ka yarda da shi, kai ba ta laifi kenan. Saboda rashin ta ido, a gabana ka mari ƴa ta”

 

“Saura Jamil ma, wallahi sai na warware kowane munafuki, babban algungumi mara tsoron Allah”

 

Nurses ne suka shigo, suka ce su fa asibitinsu ba wurin hayaniya ba ne ba, dan haka a tafi a bawa mara lafiya damar hutawa.

 

Adam ya maze ya ce kowa ya tafi Shi da Ammi za su zauna, ruma kuma anjima zai mayar da ita gida. Mummy ta ce bai isa ba.

 

Likita ya zo da kansa, ya ce wace mahaifiyar Mahmuda ta zauna da shi, ita da mutum ɗaya, ruma ta nuna Ammi ta ce “Ga mahaifiyar sa nan” Mummy na ji tana gani aka sallame su, ya rage sai ruma Ammi Nusaiba da takawa.

 

Mahmud ya kalli ruma ya ce “Daughter kina ganin bai yi wuri ba?”

 

“Bai yi ba daddy, yakamata komai ya zo ƙarshe, enough is enough”

 

Adam ya ce “Ban gane me ku ke nufi ba”

 

“Zaka gane very soon, amma kar ka matsa Please”

 

Ammi ta ce “Mahmud, a kawo abincin? Ya ka ke ji yanzu?”

 

“Alhamdilillah da sauƙi, Yaya zai kawo abincin”

 

Da azahar takawa ya tafi sallar juma’a, bayan ya dawo ne Iman suka zo tare da mai sunan baba.

 

A lokacin Mahmud yana zaune, har yayi salla jikin da sauƙi.

 

Iman ta din ga jera masa sannu, mai sunan baba ya ce “Deeja zuba mana abincin tare da shi, ko zai samu ya ci da yawa”.

 

“Cikina dai babu daɗi, kar a ɗura mini abinci da yawa”.

 

Mai sunan baba ya yi murmushi, ya ajiye abincin a kan gadon, ya ce “Ko a baki zan din ga baka ne? Na iya ɗura ka tambayi deeja ka ji”

Iman ta sunkuyar kai, saboda ammi na wurin a zaune da nusaiba.

 

Takawa kuwa ya cewa ruma ta tashi ya mayar da ita idan sun gama cin abincin.

 

Iman sai tsokanar ruma take yi, wai yau abun ɓoye ya fito fili, sabir zai yi ƙani.

 

Ta din ga tura baki, tana harar su.

 

Ko da suka je gida gaba ɗaya takawa ya hau yi wa rumaisa faɗa.

 

“Why are you making things complicated rumaisa?”

 

Cikin rashin fahimta ta ce “As how?”

 

“Ni da ke idan kin gaya mini abu ina yarda da ke, sauran mutanen fa? maganganu sun fara yawo, mahmud ya daki Jabir ya rufe shi ba wanda ya san dalili, mahaifiyarsa ta je an ƙi sakin sa an ce sai mahmud ya je. Kin ce Samha na asiri, a dalilinki na daketa, komai ya hargitse na ma rasa ya zan yi, wambai ya ce lallai in zo da ni da ke, kun hargitsa al’amura, babu wanda ya san me ku ke ciki, kina ɓoye mini wasu abubuwan”

 

“Wait” tayi maganar tana ɗaga masa hannu.

 

“Duk cikin wannan maganganun naka, marin Samhan da ka yi ne ya fi baka haushi kenan? To sai ka koma ka bata haƙuri ai. Ka san dai ba zan yi mata ƙarya ba, tun da lokacin da na zo gidanka ba uwar abun da na sani, balle in san an yi maka wani asiri baka da lafiya, ko in yi wa Samha ƙarya. Kuma ba wambai ba ko gaban waye idan na je ina da gaskiya kuma zan faɗeta.

 

Ta ƙarasa ta saka mukulli, ta buɗe wata wardrobe, ta ɗaukko wata Viva bag, cike da takaici ta watsa masa.

 

Ta ce “Ga kaɗan daga binne-binnen da aka yi a hanani zama, daga ni har kai, da yake Allah ba azzalumin sarki bane, duk in da nake rayuwa in dai da sihiri, sai na sani. Ka duba a ciki har da abun da Samha ta yi, ta saka aka sanya a cikin katifarka da tawa, banda abun da aka binne”

 

Jikin takwa yayi sanyi, tsigar jikinsa ta tashi, saboda uban tarkacen da suka zubo daga cikin ledar, sai uban wari suke, ƙoƙarin rumaisa ya gani, da ta iya ajiye wannan tarkacen a ɗakinta.

 

“Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ƴan bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking ɗin ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haɗa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faɗa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana”

 

A gigice cikin tsawa ya ce “Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faɗa ne? Jamil fa ki ka ce”

 

“Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ƙi, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka ɗauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi”

 

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Innalillahi wa Innalillahi raji’un ” ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa.

 

Banza ruma tayi masa, ta fice daga ɗakin ta bar shi.

 

Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faɗa ba gaskiya bane ba.

 

Jikinsa yana rawa, ya ɗaukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya ɗaga amma ya kasa magana.

 

“Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaɗai ba ne ba, manyan ƙusoshin ƙasar nan SMOKE! Sai dai magana mara daɗi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare”

 

Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske.

 

Ruma ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya haɗa gumi, sai tsuma yake yi.

 

“Ka tashi ka bar mini ɗakina, ɗakin maƙaryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so haƙuri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai”.

 

Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar ɗakin.

 

Ta kwashe kayan ta ɓoye, ta ɗauki wayar sa, ta buɗe pin ɗin, ta kira Iman.

 

Iman na ɗagawa ta ce “Kun tafi ne?”

 

“Eh, amma yanzu su mama suka shiga”

 

Ta ce “Ok”.

 

Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga “Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?”.

 

“Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sauƙi sosai”.

 

“Mama dan Allah ba shi wayar”

 

Mama ta miƙawa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi.

 

“Hello daughter”

 

“Jikin ka da sauƙi daddy?”

 

Ya ce “Sosai Alhamdilillah”

 

“Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ƙarshen wannan lamarin, zamu haɗu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ƴan sanda”

 

Ya ce “Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week”

 

“Shikenan daddy, na gode sosai”.

 

Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ƙarfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana roƙon Allah ya basu sa’a.

 

Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta.

 

Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ƙarya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.

 

Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ƙarfe biyu suna hira.

Ta yi iya ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haɗawa da abubuwan alkhairin Mummy.

 

Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya ɗuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faɗa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala’i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse.

Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ƙarar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station ɗin aka kai shi ba.

 

Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.

 

Suna tsaka da wannan bala’in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinsu.

 

Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi.

 

***

Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara ɗaki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ƙanana.

 

“Rumaisa” ta ji ya kira sunanta.

 

“Ba zamu Asibiti ba?”

 

“Sai ka dawo, kar na je na kuma ɓata muku zumunci”

 

“Kiyi haƙuri, na rasa yadda zan yi ne”

 

Ta ce “Ni ba zani ba”

 

“Dan Allah ”

 

Ruma ta ce “Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da ƴan sanda a wurin”.

 

Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je.

 

Ya ƙyaleta ya fita tafi.

 

Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki.

 

Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba.

 

Ammi ta ce “Takawa, ya dai?”

 

“Bakomai” zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce “Mummy sai yanzu ko?”

 

“Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni”.

 

Ya ce “Allah ya baki haƙuri, a cewa likita ya zo ya sallame ni, saboda ayi ta ƙare a yau”

 

Mummy ba wanda ta kula sai mahmud, suma ba su kulata ba.

 

“Mahmud ina ka kai Jamil ne? Kana a wannan yanayin zaka je wani wuri? Ka sa matar nan ta tayar wa da mutane hankali, sai bala’i take yi. Ta shafa mini kashin kaji, wai ni na saka ka dake shi ka kulle shi. Ga wani zancen ma wai ko an kama Jamil gaske ne ko ƙarya oho”

 

Ammi ta ce “Kenan maganar ruma gaskiya ce”

 

“Ba da ke nake ba, da ɗana nake malama” Mummy ta yi maganar gatse-gatse ga giwa.

 

Ammi ta ce “Allah ya baki haƙuri”

 

***

Katafaren falon ya cika ga Wambai, ga turaki da wasu manya daga masarautar kano.

Ammi ta hallara, ga Mahmud dan ko gama warwarewa bai yi ba. Aka jima sai ga rumaisa da takawa, Bashir jami’an tsaro da wasu daga cikin yayyen rumaisa, ga Samha a wurin da mahaifiyar ta, ga Hajiya Lubabatu da duk wanda yakamata su halarci zaman.

 

Gaban Samha sai dukan uku-uku yake yi, dan bata san mai rumaisan za ta kwatsa ba.

 

Wambai ya ce “Su kuma waɗan nan lafiya?” Yayi maganar yana nuna jami’an tsaro, da suka shigo da jabir, a wahale.

 

Bashir ya ce “Ranka ya daɗe, zuwanmu wannan zaman yana da matuƙar muhimmanci, zaka ji dalilin zuwanmu in sha Allah. Zuwanmu nan ayi tattaunawar da mu, sai ya fi sirri, saboda wasu abubuwan da za a bayyana, akwai kunya ace wasu laifukan daga gidan girma da daraja suka fito”

 

Adam ya ce “Allah ya taimake ka, wannan ita ce rumaisa matata kamar yadda ka sani, waɗan nan kuma ƴan uwanta ne, wannan kuma abokan aikina ne”

 

Wambai ya kalli rumaisa ya ce “Ke! Ke ce mai haddasa mana husuma da tashin hankali a cikin family ko? Kafin ki zo lafiya lau mu ke zaune, amma daga zuwanki kin hargitsa komai, ki ce wancan yana asiri, ki ce wannan baya son wannan saboda me?” Ya fara yi wa ruma faɗa, tayi shiru ta sunkuyar da kai.

 

Turaki ya ce “Ina ganin, a fara bari mu ji ta bakinta tukuna ranka ya daɗe, kar a yanke mata hukunci kai tsaye”

 

Wambai ya kalleta ya ce muna saurarenki.

 

Ruma ta ƙulu, basarwa kawai ta yi, ta haɗiye wani abu mai ɗaci sannan ta ce “Kafin na ce komai, zan fara da bawa babana haƙuri a kan abubuwan da zasu fito daga bakina, duk da ya san wasu, na san bai san wasu ba. Ina neman afuwarka babana mai girma turakin kano”

 

Turaki yayi murmushi mai ciwo, sannan ya ce “Kar ki damu yarinyar kirki, kamar yadda na riƙe miki alƙawari a baya, ina umartar ki da ki faɗi komai, dan fita daga zargi.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 84 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button