Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 33 Hausa Novel

Ta jijjiga kai alamar a’a ba tare da ta dago ba, ta cigaba da kukanta. Kawai sai Mommy ta hakura da tambayar ta zuba mata ido, a hankali ta daga hannunta tana shafa kanta; ta dai san da maganar saura kwana uku a daurawa Mustapha aure don haka watakila wani abun yayi mata wanda ya sosa mata rai shine ta taho nan tazo tana wannan kukan. Saida ta dauki loakci tana wannan kukan sannan ta dan numfasa ta dago ta kalli Mommy, suna hada ido kuma sai ta sake fashewa da kuka.Cikin sheshekar kuka tace ‘Mommy ba zan iya ba, ba zan iya ba Mommy.’Ta dago fuskarta tana share mata hawayen tace ‘Menene ba zaki iya ba Khadeeja?’Ta tsagaita da kukan sai dai hawayenta ya kasa daina fita; ta sa bayan hannunta ta goge hawayen ta kalli Mommy suka hada ido na dan lokaci. Ta kawar da kanta tace ‘Mommy ban san me Mustapha yake so da ni ba. Bayan ya gama raina min hankali lokacin da yana neman aure yanzu kuma duk da ban bashi matsala ba amma ba zai barni na zauna lafiya ba.’Ta share mata hawaye tana cewa ‘Me yayi miki kuma.’‘Mommy nace masa ina so ranar da za akawo amarya na taho nan idan sun gama kaita sai na koma ya hana ni, na hakura nace zan zauna amma ba zan yi taro ba; su kawo amaryarsu kawai su tafi. Da farko har ya yarda amma yau yake gaya min wai babarsa tace zata zo a nan gidan namu zata yi biki, kuma yace ba zan tafi na barsu ba. Mommy so suke bakin ciki ya kasheni? Dansu zai yi min kishiya kuma suzo suna celabrating a gaba na?’Da mamaki Mommy tace ‘Ikon Allah, ita mahaifiyar tasa ce zata yi biki saboda zai kara aure?’Ta sa hannu ta goge ragowar hawayen da yake kan fuskarta sannan tace ‘Eh Mommy, wai zasu zo suyi biki. Kin ga kenan nace ba zan karbi amarya ba amma zasu yi min dole.’Mommy ta kama hannunta ta kalleta sannan tace ‘Kiyi hakuri kin ji, zaki iya. Kishiya bata kashe kowa ba in sha Allahu kema ba zata kashe ki ba. Ki bi su a hankali, dare daya ne ayi ya wuce. Da an kwana biyu itama zata zama kamar ke kuma yanda yayi miki haka zai yi mata.Ta jijjiga kai tana murmushi mai dauke da ma’anoni tana cewa ‘Hmm! Mommy ba zai taba yi mana adalci ba. Kina ganin yanda tum kafin ta shigo shi da yaransa da ‘yanuwansa suka karkata wajenta. Gaskiya ban saka rai Mustapha zai iya yi min adalci ni da matarsa, sai dai kawai nace Allah ya bani hakuri ko kuma ya kawo min mafita mafi alkhairi.’‘kada ki damu, ai ba shi yayi kansa ba, in sha Allahu Allah ba zai bari ya cutar dake ba daga shi har ‘yanuwan nasa gaba daya.’‘Hmmm!’ ta sunkuyar da kai tana kallon yatsinta da take wasa da su.Jimawa kadan tace ‘Mommy bana son ayi min biki a gida, bana son a akwo min maryarsa ace za a bani amanarta ko ayi mana fada tare. Amma kinga duk sun shirya hakan zasu yi.’Mommy ta sake kamo hannuwanta duka biyun ta kalleta suka hada ido sannan tace ‘Kada ki damu, kamar yanda na gaya miki na ranar ne kawai. Kuma kema ‘yan uwanki zasu zo, duk da kince kada azo da yawa toh yayayrki zasu zo da kamar mutum hudu haka. Nabila kuma tace gobe zata taho ta tayaki kwana zuwa lokacin da zasu gama bikin. Kada ki damu in sha Allahu omai zai wuce.’Haka suka zauna Mommy tayi ta bata baki har zuwa yamma. Ta samu zuciyarta tayi sanyi amma dai bata da tabbacin ko zata iya dauka, ta dai hakura taga yanda zata kaya kamar yanda Mommy tace.Sai da yamma sanna ta shirya ta koma gidan zuciyarta cike da wasi-wasi.Washegari ‘yan uwan amarya suka zo suka yi kafi. Basu ja fitna ba don haka lafiya aka rabu, ta sa Hafsa ta mika musu kuloloin abincin da ta bayar aka dafa musu; don ita tunda suka shigo gidan ta haye sama kuma har suka gama bata sauko sun hadu ba. Sun tura Hafsa taje ta kirawota sau ba iyaka amma haka hafsan take dawowa tace musu saman a rufe yake. Haka suka gama kafinsu suna ta rangada guda, ga turare da suka bade gidan dashi. Sai da suka kusan gamaw sannan yara suka dawo daga makaranta, nan da nan suka shige cikinsu da yake sun saba da kannenta saboda yawan zuwa gidansu da suke yi.……….Dawowarsu daga gidan kafi yayi daidai da dawowarta daga wajen lalle, a zaune ta samesu a farfajiyar gidan ana ta hirarraki. Ta dubi yayarta Ummi tace ‘Yaya har kun dawo daga kafin?’Ta tabe baki tace ‘Hmmm! Mun dawo’Ta dan kalleta da alamar tambaya tace ‘Ya naga kina yatsina fuska? Komai dai ya tafi dai-dai ko?’Salma wadda cousin dinta ce tace ‘Um babu laifi. Amma fa mu a kasa Mustaphan ya nuna mana daki guda daya da parlor yace nan ne naki kuma a nan mukayi kafi. Saman gidan nan ma dai ‘yar mulkin uwargidan taki bata ko bari mun hau ba ta ja kofa ta rufe don bamu ko isa ta sauko mu gaisa ba ta aiko mana da kulolin abinci kamar wasu mayunwata.’Ta zmburi baki ‘Ban gane a kasa ya baku daki ba? Ai ni sama mukayi da shi kuma ya amsa min a kan haka.’‘To ai kuwa dai bai isa ba don Hajia Babba ta haye sama, bata ko saukowa idan bata bawa bako mahimmanci ba.Nan da nan idonta ya kawo kwalla, ta mike ta daga waya ta nufi cikin gidan. Ba tare da bata lokaci ba Yaya Ummi ta mike ta bi bayanta. A daki ta sameta har ta lalubo lambar Mustapha zata buga. Ta dafe wayar tace ‘Ba sai kin kirawoshi ba domin karya kawai zai yi miki ya sake bata miki rai, alamu dai sun nuna itace mai gidan. Kada ma ki daga hankalinki a kan wannan maganar balle ki hanaku morar satin amarcinku, don in kika hana muku wannan kwankin to kin yi mata alfarmane don ita zata so haka. Ko da ma kunyi magana da shi din ki nuna masa babu komai.’Ta kalleta tana zumbura baki tace ‘Yaya babu komai fa kika ce? Ai ba haka muka yi da shi ba. Tun lokacin da ya sayi gidan fa muka je dashi nace sama nake so kuma ya amince, shine zai je kuma ya canja magana.’Tayi murmushi tace ‘Kika san me aka yi masa ya canza? Wannan mata duk da ban ganta ba amma na san a shirye take, idan bamu dage ba zuwa zaki yi ki zama ‘yar kallo don da alama tana shimfida mulki yanda ranta yake so.’‘To yanzu ya za a yi?’Tayi murmushi ‘Kada ki samu zan yi magana da Inna, dama kin ga tunda aka fara maganar bikin nan take faman nemar miki taimako. Kin ga yanzu sai a mayar da hankali ayi aikin da zaki hada kan gidan ki mallake a sauke miki ita daga benen kuma a cireta daga zuciyarsa gaba daya.’‘Anti dama fa bata zuciyarsa gaskiya, don gaskiya hakuri kawai yake yi da ita ba tun yau ba. Da bakinsa ya gaya min babu ragowar kaunarta a zuciyarsa…..’‘Ke rabu da shi, namiji ai munafiki ne. za dai muyi maganinsa tunda mun ga kamun ludayinta.’ Ta katseta tana yarfe hannuwa.Ranar daurin aure tun da sassafe baki suka fara zuwa gidan, zuwan nasu ma sai ya fi mata sauki tunda ya bata dama ta baro Mustapha a sama ta taho wajen bakin. Ba zata iya tsayawa a inda yake ba yana ta faman walwala yana kaiwa da kawowa yana kwalliya, sai ta ga kamar yana yi ne don ya bata haushi. Don haka taji dadi sosai da aka ce mata Yaya Jidda ta zo da mutane. Nan ta sauko suka gaisa, ta bude musu dakin baki tunda dama a daya parlor din suka sauka wanda ba na amarya ba. Sosai Yaya Jiddan ta so su hau sama amma sam Khadeeja taki bada fuska, don haka suka hakura suka baje zugarsu a nan kasan. Duk wani abu da suke bukata na cefanensu sun taho da shi da mayan tukwanensu, shi kansa Mustaphan bai san a nan zasu yi girkin ba da ya biya an girka musu don baya son a bata gidan nan. Amma haka yana ji yana gani kafin ma ya sauko an sauke kayan aiki an hau kokarin hura wuta; a cewar Yaya Jidda sun bayar a yi musu tuwon shinkafa da masa da shinkafa amma masu yi miyarsu bata dadai don haka su zasu girka tasu miyar. Nan da nan ya ja motarsa ya fice daga gidan suka tafi daurin aure. Tunda Mustapha ya fita ta dauki Hammad ta haye sama, suka zauna da Nabila wadda dama bata sauko ba ma balle ta ga kalarsu. Hafsa mai aikinta dai ita dole ta zauna ana komai da ita, sannan ga su Afaf wadanda tuni suka shiga cikin dangi ana ta rawar kai. Can kusan la’asar su Yaya Mama suka zo ita da cousins dinsu mutum biyu da kuma kannen Mommy su biyu. Bayan sun gaisa da Yaya Jidda a parlor din kasa kai tsaye suka haye sama. Basu dade da hayewa ba kuma Hajia mahaifiyar Mustaphan ta iso da tata zugar, nan da nan gida ya cika ana ta kaiwa da kawowa. Bayan an gaggaisa Hajia ta dubi Yaya Jidda tace ‘Ina Khadeejan ne? Ban ganta ba.’Inna Ramla tayi sauri ta amsa kafih Yaya Jidan tace wani abu ‘A’a suna sama benen nan fa ita da ‘yanuwanta, benen da ‘yan gidan ma ban ga suna hawansa ba tunda duk gasu nan tare da mu.’ Ta sake duban Yaya Jidda tace ‘Ban gane tana sama ba.’ Ta tabe baki ‘Toh haka muka gani, tana saman ita da ‘yan uwanta.’Kafin tace wani abu Khadeejan ta sauko sauko parlor din da sallama; Shukra ce ta hau ta gaya mata zuwan Hajia shine tayi sauri ta sauko saboda kada tayi laifi.Ta ratsa mutanen har gaban Hajia ta tsuguna ta gaisheta cikin girmamawa sanna tayi mata Allah ya sanya alkhairi. Ta dubi mutanen duk suka gaggaisa tana kama sunan wadanda ta sani. Har ta mike Hajia tace ‘Ina Mommyn naki, bata zo ba?’Tace ‘Eh, bata zo ba, su Yaya Mama ne kawai suka zo.’‘To madalla.’

Back to top button