Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Was She) Chapter 79 Complete Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

                  Unique Barakancy🌹

SEVENTY NINE

“Na ce maka khaleel be mutu ba, ba gashi ina jin muryarsa ba”…
Shine abinda baby tee ta fada tana kokarin tashi daga jikinsa….
Tashi umm da mami sukayi suka fita daga parlourn suma suna mamakin abinda ya kawo likitan…..
Kara rungumeta yayi a kunne ya rada mata;
“You’re just hallucinating baby girl, bawani khaleel anan”…..
“Toh ka sakeni inje gurinsa mana”…
Ta fada da karfi da sai da attention din mutane ya sake dawowa kansu….
Haka kawai yaji zuciyarsa na zargin wani abu saidai yasan ba hakan bane bama, amma dole ne ya saka ido sosai akanta, ganin zata fara masa fizge fizge yayi bismillah ya fara mata karatun qur’ani a kunne yanda babu wanda zeji…..
Sun dade a haka kafin ya fara jin saukar numfashinta a fuskarsa, dagota yayi yaga tayi bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli inda ya bar likitan chan a tsaye dazu sai yaga bayanan, kwafa yayi sannan ya dauketa chak ya musu sallama ya fita, binsu sukayi da kallo babu wanda ya iya amsawa, yana fita sudais dake zaune daga gefe yabi bayansa….

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document
A hankali yake takawa dauke da ita ta sakar masa jiki hankali kwance tana bacci kamar a gado, ko ina sukayi binsu kawai ake a da ido anata yan gulmace gulmace kamar ba gidan mutuwa ba, yana barin main entrance din yaji muryar sudais a bayansa….
“Kaga yanda mutane keta kallonka kuwa, kai ko kunya bakaji”….
Tsaki yayi yace;
“Kunyan uban me zanji, basuga halin da take ciki bane, besides she’s my wife”….
“Ai su basusan she’s your wife ba, yanzu wani sai yayi maka wata fassarar daban”….
“To hell with their thoughts, su sani ko karsu sani nidai na san halalina na taba”….
Dariya sudais yayi yace;
“Iyeeee su halal manya, koda yake kunyi abinda yafi haka a gida ma bare nan”….
Wani irin kallo ya masa kamar ze dakesa yace;
“sudais ka rabu dani karka bari na sauke abinda yake damuna akanka wallahi”….
Sassauta dariyarsa sudais yayi yace;
“Me yake damunka”….
“Ba sai kaji ba”….
“Allah ya wuci zuciyarka boss”…..
Daidai nan suka karaso inda sukayi parking motarsu a parking space, Deen na shirin bude mota ya ajyeta sudais yace;
“Saif kamar likitan dake kula da yarinyar nan nagani dazu fa”…..
Fasa bude motar yayi yana rike da ita yace;
“Dan iskan ne mana, sai ya gayamin ubanme yazo yi anan”….
“Calm down please, zatayiwu gaisuwa yazo musu shima, maybe he knows the lost”…..
“Kaga yayiwa wani magana dayazo? I was distracted bansani ba ko kaga fitarsa ma?”…..
“Gaskiya ban gani ba, I was on my phone too”….
“Zeci ubansa! Budemin kofar baya”…..
Budemasa sudais yayi ya kwantar da ita cikin kulawa, yana gyara mata hijab dinta yaji sudais na amsa sallamar da aka musu, rufe motar yayi zeyi magana wanda ya musu sallama ya rigasa tare da miko masa hannu yana fadin;
“Yallabai ina wuni”…
Bige hannunsa deen yayi kamar be taba dariya ba yace;
“Kutumar ubanka kake mikowa hannu? Uban me ya kawo ka gurinnan”…
Ba iya shi kadai bane yayi shock har sudais da yake tsaye sai da mamakin tsaurin idon Deen ya kamasa, a kalla mutumin ze iya girmansa da kadan ko kuma suyi sa’anni amma yake masa magana kamar da yaro karami yake…
Sudais zeyi magana yayi saurin daga masa hannu ya kalli Doctor din ya sake cewa;
“Tambayarka nake!!”…..
Murmusawa Doctor din yayi yace;
“Kayi hakuri yallabai, dama na fita na dawo ne aka cemin batanan, shine nace bari na biyo bayanku gudun kar a samu matsala sannan kun fita batareda sa hannu ba”…..
“Mun fita batareda sa hannu ba? Sa hannun wani mahaukacin, kai? Allah ya kiyaye!
Sannan kai dakikin ina ne kake tinani za’a samu matsala dan bakanan, in banda kara mata ciwo ma me shirmammen asibitinku sukeyi”….
“Ba lefina bane, dokar ce tazo a haka yallabai”….
“Toh ba za’a bi ba, kuma daga yau mun bar muku unprofessional hospital dinku, get lost”….
Sosai rashin jindadi ya bayyana akan fuskar likitan, duk maganganun da deen ya gayamasa basu dameshi ba sai cewa da yayi sun bar asibitin, kwantar da kai yayi cikin nuna alhinin halin da take ciki yace;
“Kayi hakuri yallabai, dan Allah karku bar asibitinmu, in kuka bari waze kula da ita”….
Kallonsa deen yayi na yan sakwanni zuciyarsa na tafasa yace;
“Mijinta! A professional Doctor”…..
Kasa boye mamakinsa yayi ya zaro ido yace;
“Ba ance wanda zata aura ya mutu ba”….
“Oh har bincike kayi kenan? A binciken naka kuma ka kasa samo complete gist din kuma?”….
“Wallahi ce min akayi bata da aure yanzu”….
Ya fada cikin subutar baki……
“Shiyasa kake makale mata kenan? Ta samu sauki sai kace kana sonta shikenan kuyi aure ko?”….
Deen ya fada yana tura hannunsa cikin dashboard din motar da niyar zaro abu…
“Eh kuma fa…”…

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

Be karasa ba yaji saukar belt ta ko ina a jikinsa, kamar wanda aka rike yanajin zafin duka amma ya kasa guduwa, deen ko sai masifa yake yana zuba masa belt din babu kakkautawa…
“Dan ubanka idan jikinka ya gayamaka zaka gane matar wace basai kayi wani binciken ba”…
Sudais na gefe sai dariya yake dan shima likitan ya bashi haushi yanda ya zage yana magana….
Sai da Doctor din yaga dauriyarsa ta kare sannan ya fita a guje yana ihu sai sosa jikinsa yake, deen har ze bisa sudais ya hadashi da Allah da annabi ya barsa haka, shiga mota sukayi sudais yaja yanata sheka dariya abunshi…….
Suna hawa titi sudais ya buga tafi yace;
“Mutumina ban tabajin masifarka ta burgeni ba irin yau, ashe da gaskiyarka da kake cewa baka yarda dashi ba”…..
“Ni dai kayi a hankali karka tasarmin mata tana bacci, ba in ina fadan abu ana ganin kamar I’m too strict bane, ai gashi kagani”….
“Gaskiya dai, wallahi ka burgeni yau, shege wai ai bata da aure”….
“God knows I’m tired of all this shits! Once our relationship is approved aka bani matata we will run far away from everyone, no one is ever gonna see her again”….
Fashewa da dariya sudais yayi ya kallesa yace;
“Earth din zaku bari gabadaya kenan, egg din Abby da umm zaka tafi da ita wata duniyar, you’re joking man”….
Dafe kansa yayi yace;
“Shit kuma fa hakane, but still zaku dade baku ganmu ba”….
“Allah ya bada sa’a, mu dai yan kallo ne tinda ka samu abinda kakeso dole ka ya da kowa”….
“But you know I’m always there for you koda daga nisa ne ko?”….
Deen ya jewo masa tambayar yana tsaresa da ido….
“Yes boss, wasa nake”….
Shiru ne ya biyo baya na yan mintuna kafin sudais yayi breaking silence din da fadin;
“Tell me how it started?”…..
Dagowa deen yayi daga gyarama baby tee kwanciya a jikinsa da yake yace;
“What?”…..
“How did you fall in love with her”…..
Dan jimm deen yayi kamar kar yace komai sai kuma yace;
“I honestly don’t know when I fall in love with zahrah but I know it all started with her eyes, her pretty eyes….”…
Sai kuma yayi shiru, curiously sudais yace;
“Cigaba please”…..

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Shiru ne ya biyo baya na kusan minti uku har sudais ya cire rai yaji yace;
“Ka tuna seminar dinnan da mukayi da aka bani award har nile university suka kawomin invitation?”….
Gyada kai sudais yayi yace;
“Na tuna, lokacin ina Cyprus ko”…..
“Exactly, sudais inaga kaddarar haduwa da zahrah ne yasa nayi accepting invitation dinnan even though sai da dad yasa baki but I didn’t really argue”….
Curiously sudais yace;
“Nile? Who is sponsoring her?”….
“Alhaji Ibrahim, but I paid her last school fees”….
“That’s good, ina jinka”….
“It was on a faithful and grateful Monday, haka kawai ranar naji I need to go to the school after two weeks of accepting the invitation, first thing I heard ina shigowa class din was a loud hiss, tsaki sosai irin na rashin kunya sudais ni kuma kasan na tsani tsaki, na juyo in ciwa meshi mutunci naga niqab a fuskarta sai nayi tinanin matar aurece, but I still want to punish her sai nace ta cire niqab din, do you know what this gorgeous did?”…..
Deen ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta da take bacci a nitse…..
Dariya sudais that is already engulfed in the story yayi yace;
“What did she do?”….
Girgiza kai deen yayi yana ganin abun kamar yanzu yake faruwa yace;
“Takowa tayi har gaban podium har kan stage inda nake ta cire niqab dinta slightly that I can only see these captivating eyes”….
Ya karashe yana shafa idanunta dake a rufe….
“Ina jinka”…..
Cewar sudais cikin zakuwa…..
“Her eyes were beautifully scary that I almost lose my balance, infact I couldn’t hold it kawai na koreta daga class din”…..
“Ka koreta kuma?”….
“Yes but it was the biggest mistake I made because it was the beginning of my struggle, sudais through out ranar banyi bacci ba all I’m seeing is her eyes, tin ina ganin abun kamar wasa naga ya fara damuna sosai, my heart is just curious to see that scary eyes again and to see the face behind those eyes, amma na kasa ganinta, na sake lecturing class din because of her but she didn’t attend nayita roaming up and down still couldn’t find her, alas kasan ina naganta?”….
“Ina?”….

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

A hankali kamar bayaso yace;
“In a hotel”…..
Dan bude ido sudais yayi yace;
“Hotel?”…..
“Yes sudais, transcorp hilton for that matter”…..
Ya fada a sanyaye….
“Not to judge a book by it’s cover but meya kaita gurin?”…..
“How would I know? Nifa in fadamaka haryanzu ina da serious cases da zahrah, I have a lot to query her about”….
Kasa kasa sudais yace;
“Don’t ask her, figure it out yourself”…
“How?”….
Kasa da murya yayi kamar wani ze jisu yace;
“I and you know why you want to ask her those questions and what you want to know, so save everything after consummation, in baka gamsu ba sai ka tambayeta”….
Dariya deen yayi ya rankwashesa yace;
“Fitsararren yaro kawai amma fa ka kawo shawara me kyau”….
Kashe masa ido daya sudais yace;
“Kana wasa dani gayannan, wata hudu fa kawai ka bani kake kirana yaro”….
“Eh mana wanda bashi da aure yaro ne ai, kayi zuciya ka samo mata”….
Fashewa da dariya sudais yayi harda rike ciki kamar ba driving yake ba yace;
“Inji wanda ko matar ba’a kai masa ba, well ni dai cigaba da bani labari dan Allah, daka ganta a hotel sai me ya faru?”…..
“Da farko I was so disappointed saboda niqab din dana ganta dashi even in the hotel amma kafin in samu damar magana da ita tayi disappearing”….
Zaro ido sudais yayi yace;
“Ta bace fa kace?”….
Gyada kai yayi yace;
“Eh nidai haka idona yagani dan lokaci daya na nemeta na rasa”….
“Ikon Allah, sai kayi yaya”….
“Ya kuwa zanyi, haka na cigaba da nemanta without thinking of giving up, coincidentally I keep on seeing her in the same hotel amma kafin in mata magana ta bace har wata rana na kusa ganin fuskarta amma yarinyarnan ta min karyar aljanu, na sakankance ina mata karatu naji ta farayi itama, I don’t know how but I can remember listening to her melodious voice reciting qur’an, a haka ta gudu ta barni bansani ba”….
Sake shekewa da dariya sudais yayi yace;
“Gaskiya kanwata ta burgeni, kace tayi playing smartness akan smart”….
Memakon yaji haushin zancen sai ma dariya da yayi yace;
“Tinda na hadu da zahrah na goge wannan sunan daga jerin sunayena because this sleeping beauty has over played me”…..
“Ai itace daidai da kai, wallahi ko kadan banga lefinta ba, toh yaushe ka samu kaga fuskarta?”…..
“Lokacin da akayi kidnapping dina, tinaninta ne ya hanani zama a cikin gurinnan kawai na gudo, mutanannen suka biyoni kawai naga mota tazo wucewa nasa hannu looking for help, ashe itace a ciki bansani ba, she helped which is something I can never forget even though munyi accident at the end, I saw her bayan na farfado and that’s where the battle begun”…..
Gyada kai sudais yayi yace;
“Allah sarki, ina jinka”….
“Sudais bansan inada matukar hakuri ba sai akan yarinyarnan, nida na balakin tsanan rashin kunya sai gashi ina fancying nata, sannan babban abinda yake damuna shine bata da gurin zuwa sai transcorp gashi na kasa gane me takeyi achan worse of it she’s very unserious dan sai tayi one month bata shiga class ba and she has a very good academical record that got me doubting whether she’s giving her body to the lecturers? Ga taurin kai baka isa ka mata magana taji ba, frankly duk abinda banaso shi takeyi gashi taki ta fadamin wacece ita, gabadaya zarginta nake but I still don’t want to leave her, wani abu dayayi breaking heart dina kuma shine sameer daya keta bani labarin budurwar khal daya keso yayi snatching ashe itace, can you believe har dubai take zuwa gurin khal ta zauna lokacin? Banyi bacci ba the day I found out sameer ita yakeso shima wallahi, another blessed thing datamin batasani ba shine guduwa daga prison danayi akanta, da ban gudu ba da sai dai wani bani ba because the prison was burnt entirely that same night I left, and na gudu ne saboda mun hada plan da sameer mukayi kidnapping dinta da niyar a daura musu aure, kawai naga itace”..

Also Download Hira Da Matattu Page 1 By Jamila Umar Tanko

Katseshi sudais yayi da tambayarsa;
“Da wata ce haka zaku mata dagaske?”…..
Lumshe ido deen yayi yana jin wani iri a ransa yace;
“Nayi nadama sudais, nayi nadama sosai, na kuma godewa Allah she’s the girl that I have been haunting, da bansan da wani ido zan kalli umm in tasan I’m part of that shitty marriage da akama yar’ta ba”…..
“Alhamdulillah hakan be faru ba, so what did you do after that?”…..
“Gidana na kaita but unfortunately mami da umm sunzo sun ganta”…..
Zaro ido sudais yayi kamar a lokacin abun yake faruwa yace;
“Toh me sukace? I can imagine myself in your shoes waiii”….
“They thought I raped her because her legs were bleeding and in reality bigewa tayi alas umm treated her and they found out the truth”….
“Alhamdulillah amma fa abubuwa sun faru, kasha wahala gaskiya amma shine bazaka iya kirana ka fadamin ba? Atleast I could help”…..
Murmushi kawai deen ya cigaba da basa labarin duka challenges din da yayi facing akanta, har suka karaso gida suka kayi parking suka cigaba da zama a mota labari yake basa, sudais ko ji yake kamar labarin karya kare, sun dau lokaci me tsawo kafin ya karashe da fadin;
“If stubbornness was a person, it would definitely be my zahrah”….
Tare da juyowa ya shafa fuskarta kawai yaga idonta a bude tana kallonsa, mazewa yayi yaja mata hanci yace;
“Ke yaushe kika tashi?”….
Janye hannunsa tayi tana bata rai tace;
“Yanzu and why are you calling me stubborn?”…..
Dagota yayi yace;
“Ke kadai ce zahrah?”….
“Toh wacece?”…..
Murmushi me fadi yayi yana shafa kumatunta yace;
“My wife”….
Bige hannunsa tayi ta bude motar ta fice….
Tana tafiya sukasa dariya shi da sudais, sai da suka gama dariyarsu sannan sudais yace;
“Wallahi yarinyar nan tana sonka, you just have to make her understand”..
“Hmmm nifa bana gane kanta ne sudais, sometimes sai naga kamar tana kishina sometimes kuma sai naga kamar she doesn’t care, but I really can’t wait to see zahrah head over heels in love with me, I really want to see her care so much that she would cry if I’m not around her and lastly I can’t wait to see her in my comfort zone irin a gidana a dakina kagane yaro?”….
Ya karashe cikin tsokana….
“Bangane ba, mallam ka sauke girman kai kaje ka fadamata yanda kakeji bani zakazo kana cikawa da surutu ba”….
Be jira sudais ya dire maganar ba ya fice shima, sudais yayita kiransa ya masa banza ya shige ciki, girgiza kai yayi yayi parking motar sannan ya fito yabi bayansa, a bedroom dinsa ya samesa yana gyara kan mirror, be damu da yanda yayi kamar beji shigowarsa ba cikin son kara kular dashi yace;
“Tsakani da Allah an hada baby tee da aiki, gaskiya ka chanza hali”….
Turaren da yake hannunsa ya cilla masa yana fadin;
“Allah ya isa for calling my wife baby”….
Chafke turaren sudais yayi yana dariya…
Sake cillo masa wani yayi yace;
“Tinda ubanka ne ze zauna min da ita sai ka hana auren”…..
Kaucewa sudais yayi saura kadan turaren ya samesa ya fice a guje yana dariya, haka kawai yakeson kunna deen tinda ya gano abinda ke saurin tabasa shi kuma deen baya iya jurewa ana tabasa yake kunnuwa…..
Baby tee na shiga taga mami zaune a parlour tana amfani da wayarta, hannu mami ta buda mata tace;
“Come here daughter”….
Da sauri ta tafi taje ta shige jikinta, bubbuga bayanta mami ta hau yi tana tambayarta basu koma asibiti ba tace mata eh gida sukazo ta dora da fadin;
“He called me stubborn kuma banyi komai ba”….
Mami na dialing number umm saboda ta barsu asibiti su a tinaninsu nan zasu koma tace;
“Rabu dashi ze zo ya sameni, zan rama miki”….
Umm bata daga wayar ba sai sallamarta da sukaji, amsa sallamar mami tayi tace;
“Ke nake kira yanzu ince miki nan suka tawo”….
“Hospital din sun kawo discharge letter, bansan dai meya faru ba but from the look of things saif yama Doctor dinnan wani abu”….
“Kingani ko, nifa shiyasa banso mun tafi ba kikace mu tafi”….
“Toh zama zamuyi tayi? And the doctor has no right da ze bi patient dinsa”….
Umm ta fada tana zama kusa da mami..
“Toh Allah ya kyauta, ina hajiya ruwaidan take?”….

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

“Dropped her in her friend’s house”…
“Okay”…
Tashi baby tee tayi daga jikin mami ta koma na umm, rungumeta umm tayi tana pecking kumatunta, a kullum kara jin sonta take har cikin zuciyarta kuma kullum cikin addu’a take Allah ya bata lafiya ya kuma daidaita tsakaninta da saif…
“My baby how’re you feeling now?”….
Memakon ta bata amsar abinda ta tambayeta sai cewa tayi;
“Umm kinga saif ya zageni ko”….
“Waye saif din?”…
Umm ta fada tana tsareta da ido”…..
Shiru tayi ta rasa abinda zatace….
“Toh karna sakejin kin kirasa kai tsaye koda wasa, in rashin kunya kikasa a gaba ko kusa dani karki kara zuwa, dagani”….
Ta fada tana janyeta daga jikinta, bata kara ko minti daya ba ta bar parlourn, baby tee na ganin ta tafi ta koma jikin mami cikin marairaicewa tace;
“Nifa ba haka zance ba”….
Murmushi mami tayi tace;
“I know sweetheart amma karki sake kinji ko?”….
“Yes mami”….
Cire mata hijab tayi tace;
“Muje kiyi wanka kice abinci sai kije kice mata tayi hakuri bazaki sake ba kinji ko”…
“Toh mami”…
Mami da kanta ta hada mata ruwan wanka tayi wanka ta tasa ta a gaba ta bata abinci taci sanann ta turata gurin umm…..
Umm na kwance taji an turo kofa a hankali sai kuma akayi siririyar sallama aka tsaya daga bakin kofar, sarai umm ta gane itace tindaga kamshin turarenta amma tayi kamar bataji ba, sai da taga tsayuwar yayi yawa sannan tace;
“In bazaki shigo ba ki fita”…
Sai a sannan tashigo kamar wata munafuka ta tsaya daga chan gefe tace;
“I’m sorry I won’t do that again”…
Kallonta umm tayi ba yabo ba fallasa ta nuna mata kusa da ita tace;
“Zo ki zauna”…
Karasowa tayi ta samu guri ta zauna a gefenta tana sunkuyar da kai….
Kamo hannunta umm tayi a nitse tace;
“Fatima a duniyarnan bayan mu iyayenki saboda ba a hada son kowa dana iyaye baki da babban masoyi kamar saif, sam be chanchanci abinda kike masa ba, infact saif in cewa yayi ki saka hannu a huta ya kamata kisa without hesitation because he has sacrificed a lot for you, including his life, amma naga babu wanda kika raina irinsa saboda kinga yana biye miki, idan kika sake saif ya kubcemiki he’s a treasure you’ll never get back, infact da badan shi ba I don’t think you’ll be sitting alright haka koda yake bakisan kidney dinsa ya baki bama ko?”…..
Umm ta karashe tana girgiza kai…..
A sanyaye baby tee that is feeling very guilty a lokacin tace;
“Kidney dinsa? Bansani ba umm”….
“There are more to that, we will talk about it tonight”….
“Okay mom”…..
Cikin kulawa ta sake ce mata;
“Kinci abinci?”….
“Naci, mami fed me”….
Umm zata sake magana wayarta dake kan mirror ya fara ringing, tashi baby tee tayi ta tafi dauko mata wayar, tana daukowa taga WhatsApp video call ne, da dp din caller din ta gane abby ne saboda hotonta ne akan profile picture dinsa, da murna ta daga kiran tana zama kusa da umm……
“My boddi and my mini boddi”….
Abby ya fada yana fadada fara’arsa, Allah kadai yasan irin farincikin da yayi ganinsu tare……
Umm na jin shine tayi maza ta kauce ta koma other end din gadon…
Kyalkyalewa da dariya baby tee tayi tace;
“Abby what’s the meaning of boddi”….
Murmushi yayi yace;
“Duk zaman da kikayi a gidan hajiya no one call you with that name?”….
“They did but I didn’t ask the meaning”…
Gyada kai yayi yace;
“Okay it means beautiful in fulfude language, by the way how is your health?”…..
Dariya baby tee tayi ta juya ta kalli umm sannan ta juyo tace;
“Naji sauki Abby, so this is the meaning of what you’re calling her all this while?”…..
“Yes baby or isn’t she beautiful?”….
“She is she is”…
Ta bashi amsa tana satar kallon umm data juya baya….
Cikin tsokana kawai saboda umm ta kulasu Abby yace;
“Do you want to know about your parent’s love story?”….
Fashewa da dariya baby tee tayi irin wanda basu taba ganin tanayi ba tace;
“Yes dad, please tell me”….
Dariya abby yayi yana jin wani sanyi aransa, seeing her happy alone makes him happy….
“We actually met at a conference”….
Da sauri umm ta fizge wayarta ta katse kiran sannan ta nunawa baby tee kofa tace;
“Fita”….
Tashi baby tee tayi ta fita sai dariya take, tana fita tashiga dakin mami dan ta karbi wayarta ta kira abby taji labarin because she was already interested….
Tana fita umm ta bita da murmushi, harga Allah dariyar baby tee is so contagious da duk wani yaga tana dariya sai yayi kodan basu taba ganin tayi dariya roughly bane haka? Ba karamin dadin ganin fara’a sosai akan fuskarta tayi ba sai dai bataso suyi wannan conversation din…..
Bata samu mami a dakin ba data shiga, sauka kasa tayi dan ta duba ko tana kasa, tana sauka taji an banko kofar parlorn an shigo, daga kai tayi taga eesha a tsaye tana mata wani irin kallo, karasawa inda take baby tee tayi murmushin fuskarta na daukewa dalili kuwa shine tasan matar deen ce yanzu, daurewa tayi tace;
“Welcome eesha, where have you been?”…..
Wani lafiyayyen mari eesha ta sauke mata a fuska tana wuci, dafe kuncinta baby tee tayi in shock, ko gama dawowa hayyacinta batayi ba eesha ta sake sauke mata wani lafiyayyen marin a dayan kuncinta sannan ta shake wuyarta tace;
“Allah ya isa tsakanina dake munafuka algunguma azzaluma mayya, dama na dade da sanin sonsa kike kawai munafurtata kike amma ki sani saif nawane ni kadai, babu wanda bazan iya kaudashi ba akansa”….
Karap wannan zantuka a kunnen deen da hankalinsa ya kasa kwanciya da yanayin da suka rabu da baby tee yashigo dubata…..

Kuyi hakuri kun jini shiru for a while, I’ve been terribly sick that’s why, but I’m fine now alhamdulillah, Insha Allah zamuyi mugama soon..

Karanta>>> Ingantaccen Matsi  Da Bashi Da Illah

Back to top button