Hausa novels

Ruwan Zuma Page 24 Hausa Novel

(24) Bayan Haydar ya hau gadon Laila ta lura da halin da yake ciki amma tayi kamar bata gane ba. Lokaci-lokaci yana tura kanshi jikinta numfashinsa na fita cikin sauri-sauri, ta taga abun ya fara canja mata yanayi ta matsa daga jikinshi ta koma can gefe tana cewa, “Munyi magana akan hakan, I need space.�? “I’m sorry.�? Ya juya mata baya amma minti kad’an da haka taji ya fara juye-juye ya kasa bacci. Ita kanta babu baccin a idanunta amma why not yayi hak’uri har zuwa lokacin da taga hakan ya dace? Tun k’arfe sha biyu yake juye-juyensa har biyun dare bai daina ba, ita kuma gyangyad’i take yi tana farkawa saboda motsinshi na hanata bacci. “Laila.�? Ya kira sunanta cikin wata murya abun tausayi. “Umm.�? Ta amsa ba tare data juyo ba amma zuciyarta ta tsinke da halin da yake ciki. Ta gane ba haka banza yake wahala ba, me yasha? “Please ko irin dabarunku na mata ne.�? Ya rok’eta yana kai hannunsa jikinta. “Haydar me ka sha?�? Ta tambayeshi tana juyowa. “I don’t know, Mas’ud ne ya bani.�? Shiru tayi amma a ranta zagin Mas’ud take yi domin kamar da gangan yake mata haka. Don meyasa zai bawa Haydar wani magani? “Kayi bacci.�? Kawai tace dashi kana ta koma kan shimfid’in data masa a k’asa ta kwanta. Bata shirya fara mu’amala dashi ba. Yana ganin ta koma k’asa idanunsa suka cika da hawaye har suna zuba a gefen fuskarshi. Juyawa yayi ya duk’unk’une a guri d’aya yana rocking jikinsa tamkar mai jin sanyi. A daren yayi wankan ruwan sanyi sau uku amma babu abunda ya ragu a halin da yake ciki, k’arshe da kyar bacci ya d’aukeshi wajen k’arfe hud’u. Ana kiran sallah asuba ya farka ya shiga band’aki yayi alwala ya fito ya wuce masallaci bayan ya zurma garen da Mas’ud ya bashi jiya. Bai dawo ba sai da gari ya fara haske, ya shigo d’akin a daddafe domin baya iya ko minti biyu a tsaye dalilin hajijiya da yake ji tamkar zai fad’i k’asa. Laila tana lura da hakan amma ta kasa masa magana sai ma ta bar masa d’akin ta koma falo tana tuna abunda ya faru jiya da dare. Shin ta kyauta masa? Sai da ta tabbatar yayi bacci ta koma d’akin tayi wanka ta shirya cikin atamfa d’inkin bubu, kwalliya tayi mai sauk’i kana tabi jikinta ta turare ta fito falo wajen k’arfe taran safe, tuni masu aikinta sun mata shara sun d’aura mata breakfast. Kitchen d’in ta shiga ta samesu su biyu suna aiki suka gaisheta ta amsa tana bud’e tukwanen da suka d’aura. “Hajiya mun gwada bud’e shashen Oga Mas’ud zamu yi shara amma mun samu a rufe yake.�? Fad’in Samira cikin girmamawa. “Key d’inne ya 6ace, amma idan na samu za’a bud’e ku gyara. Idan kun gama aikin ku tafi na sallameku sai kuma gobe. Zan dinga yin girkin.�? “To Hajiya.�? Suka fad’a a tare. Bayan sun gama sun tafi Laila ta shirya komai a dinning table amma zuciyarta na ga tunanin Abul, ko ina ya shiga? A wani hali yake shine bata sani ba. Tana zaune a falo k’arfe goma taji ana kwankwasa k’ofar falon tace a shigo, “Zan iya shigowa babu komai?�? Ta jiyo muryar Mas’ud cike da gatse yana dariya. Ko meya fito dashi da sassafen nan sai Allah, bata kulashi ba ta cigaba da danne-danne a wayarta domin haushinsa take ji ba kad’an ba. Sai da ya gaji don kansa ya shigo falon yana rufe idanunsa ta tafukan hannayensa amma yana gani ta 6ulin yatsunsa. A hakan ya k’arewa falon kallo sannan ya mayar da dubansa kan Laila wacce ta had’e fuska tamau bata ko kallonshi. “Amarsu ta Ango mai zakin miya. Kai Ina shigowa gidan nan k’amshi girki da turare yaso ya d’agani ya mayar dani d’akin matata. To ina Angon yake?�? Ya fad’i hakan yana zama kusa da ita yana bugan kafad’arta yana mata signa bakinshi a washe. Juyowa tayi ta dalla masa harara yayi gum da bakinsa yana kawar da kanshi gefe yana kunshe dariyarsa. “Kalti ina kwana? Kin tashi lafiya?�? Yace da ita yana had’a hannayensa guri d’aya alamar ban hak’uri. “Lafiya, ya Naana?�? “Tana can tana kwance wai baza ta iya tashi ba.�? “Ban tambayeka hakan ba Mas’ud. Wai ni yaushe ka fara rainani ne?�? Ta fad’i hakan tana ajiye wayarta a gefe tana aika mishi harara. “Kinsan komai nawa nake fad’a miki, kece dai kike 6oye mini naki.�? “Bana buk’atar kayi sharing wannan dani.�? “Shikenan, kin yiwa kanki. Amm kunyi karyawa ne? Wallahi yunwa nake ji kuma bazan iya shiga kitchen na dafa mana ba.�? Ya fad’i hakan yana zuwa bakin dinning d’in yana bud’e kulolin. “Munyi amma bamu yi daku ba.�? Tabi bayanshi tana buge hannunsa ta rufe kulolinta. “Kina nufin wannan duk na Haydar ne? Ai ya amsa yawa, ki sam mana kad’an don Allah.�? “A’a.�? Tace dashi tana zama a kan kujeran dinning d’in fuskarta a kwaye. Sai a lokacin Mas’ud ya gane halin da take ciki shima ya zauna fuskarsa na mirrowing nata. “Abul ko?�? Ya tambayeta yana mai jin zuciyarsa na k’una. “Bana samunshi a waya Mas’ud, ban san a wani hali yake ciki ba. Wallahi ina cikin damuwa, Sabrin ma ta kashe wayarta bana samunta.�? Shiru yayi na sakanni kana ya dubeta da kyau yace, “Kalti in fad’a miki inda kika yi 6ata a wajen bawa yaran nan tarbiyya, ranki ba zai 6aci ba?�? Gyad’a kai tayi hawaye na taruwa a idanunta. “Tun farko kinyi sakacin nuna musu cewa zaki iya yin komai don farincikinsu, kin nuna musu sune zasu tankwaraki kiyi abunda suke so ba wai ke ki tankwarasu suyi abunda kike so ba. Kin nuna musu kina tsoron rabuwa dasu shiyasa suke amfani da hakan wajen wahalar dake Kalti, karki manta ke kika haifesu ba su suka haifeki ba. Idan kin kasa basu umurni wa kike tunanin zasu ji maganarsa? Kina d’aurawa kanki nauyin cewa wai ba zaki bari su wahala ko suyi rashin uba ba, ai wani lokacin wahala ke saita mutum ya gane cewa duniya ba gurin aji dad’i a watse bane. Ban ce karki nuna musu so ba, amma karki nunawa yaro zaki iya salwantar da farincikin ki domin shi, ki nuna mishi kema mutum ce yayi respecting d’inki for that. Ki daina damun kanki da batun Abul domin tun jiya na samu labarin halin da ake ciki na kuma baza cigiyarsa. Ita kanta Sabrin Abul ne yake juyata, domin Idan ya shiga damuwa itama sai ta damu kamar ke. I’m sorry to say that amma Abul yana juyaki Kalti.�? Shiru tayi tana tunani mai zurfi domin in wani ne ya fad’a mata hakan kai tsaye zata ce baya son ‘yayanta ne, amma tunda Mas’ud ya iya furta mata tasan gaskiya ya fad’a ba don baya sonsu ba. Saboda bata manta raino da son da yayiwa yaranta ba tun kafin su san kansu. “Ya zanyi to? Ba’a san inda yake ba fa.�? “Na sha fad’a miki Abul ba yaro bane, zai kula da kanshi a duk inda yake. Ke dai kiyi ta mishi addu’a kuma ki daina damun kanki har in gane inda yake in dawo dashi gida.�? Gyad’a kanta tayi tana yarda da maganganunsa duka, amma har lokacin bata ji damuwar Abul ya fita a ranta ba. A yau kuma ta gane laifinta ta gane inda ta gaza wajen basu tarbiyya. “Sabrin fa?�? Ta tambayeshi tana kallonshi. Murmushi yayi ya kamo hannunta cikin nashi yace, “Ki bata kwana biyu ita ma zata nemeki, ai ba’a canjawa tuwo suna, kuma in bake ba, wa suke dashi a duniya wanda ya fiki? They must learn to respect your decisions tunda ba aikata haramun kike yi ba. Ki daina damuwa kinji?�? Gyad’a kai tayi tana jin k’arfi a zuciyarta domin Mas’ud yasan lagonta kuma yasan maganar da zai fad’a ya ganar da ita gaskiya kuma ta gane laifinta. Haydar ne ya bud’e k’ofar d’akinta ya fito cikin shirin fita, yayi wanka ya saka k’ananan kaya wanda yayi masa matuk’ar kyau tamkar bashi yayi kwanan wahala ba. Sajenshin da gashin kanshin nan sun kwanta luf sai shek’i suke yi ya fito a angonshi sak. Yana ganin Mas’ud kusa da Laila sannan ga hannunsu a had’e yaji zuciyarsa babu dad’i, Mas’ud da ya lura da kallon da yake yiwa hannunsa sai yayi saurin sake mata hannu yana matsawa gefe yana murmushi. “Ai na d’auka har yanzu a market take, ashe ta amarce jiya.�? Yayi magana mai harshe biyu wanda yasa Laila tayi rolling idanunta cikin gajiya da halin Mas’ud. Shi kuma Haydar isa gurinsu yayi hankalinshi na kan Laila wacce take kawar ta kanta tana gyara zamanta. “Ina kwana.�? Tace dashi cikin girmamawa. “Lafiya kalau, kin tashi lafiya?�? Haydar ya mayar mata da gaisuwan fuskarsa d’auke da murmushi domin ya gane she’s feeling guilty akan abunda ta mishi jiya. Wani irin ihu Mas’ud yayi yana dariya yana tafawa wanda hakan ya tsorita Laila ba kad’an ba, domin ta d’auka wani abun ne ya sameshi. “Wai me ya kawoshi ne da sassafen nan?�? Haydar ya tambayi Laila. “Neman abinci.�? Mas’ud ya bashi amsa cikin raha tamkar sun dad’e tare. Dariya suka yi kana Haydar yace, “Ka tashi lafiya, ya Amaryar taka?�? “Ba kamar taka ba.�? Yayi maganar yana tashi tsaye ya shiga kitchen. “Kin ji har an fara mini gori ko?�? Haydar ya fad’i hakan yana mata kallon k’auna. “Ban san yau me yake damun Mas’ud ba, ko giyar angoncin ne take kad’ashi oho.�? Laila ta share zancenshi ta fara zuba mishi abinci a plate. “Ya isa haka.�? Ya dakatar da ita bayan ta saka serving spoon d’aya na gwaten dankali wanda yaji kayan lambu. “Kana nufin dama haka kake baka cin abincin sosai, ban san abubuwa da yawa naka ba Haydar haka kaima baka san nawa ba.�? Ta zauna tana kallonshi ya d’auki spoon ya d’ebi abincin ya kai bakinsa. “Yau d’inne bana jin d’and’anon a bakina. Bana sha’awar komai.�? Ya k’ara kai loma ta biyu ya kur6i tea d’in data had’a mishi ya tashi tsaye. “Zan fita.�? Jikinta a mace itama ta tashi tabi bayanshi zuwa bakin k’ofa, “Ina zaka je?�? Ta tambayeshi tana jingina da k’ofar. “Neman aiki, I have to provide for you Laila. Nauyinki ya dawo kaina.�? Wannan maganan da yayi yasa taji wani sanyi a ranta ta gane cewa bata yi za6en tumun dare ba, da wani ne zama zai yi tayita ciyar dashi kuma yana ra6anta. “Allah ya baka sa’a ya kuma kawo aiki mai kyau.�? Murmushi yayi cikin jindad’i ya matso kusa da ita yana cewa, “You have no idea yanda nake buri da fatan Allah ya kawoni ranar da matata zata mini wannan addu’an. Ameen and thank you.�? Ita kuma Laila ganinshi kusa da ita da tayi har tana shak’ar k’amshin turarensa da asalin scent na d’a namiji sai taji zuciyarta na hauhawa tamkar zata faso k’irjinta. Bai ta6ata ba, illa rankwafo da kanshi da yayi dalilin ya fita tsayi kana yayi kissing d’in goshinta ya koma da baya yana murmusawa. “Me zan kawo miki?�? Yace da ita yana sakala hannunsa cikin aljihunshi ba tare da yasan hakan na matuk’ar burgeta ba. Gyara muryarta tayi domin tasan Idan tayi magana zai iya fitowa a shak’e, tace, “Agwaluma.�? Dariya yayi sosai har Laila na jin kunya ko dai ya gane yana affecting d’inta ne? “Kin samu Insha Allah. Take care.�? Da haka ya fita daga gidan ya kama hanyar da zai sadashi da titi. Mas’ud kuma kwai ya soya a kitchen ya fito ya samu har Haydar ya tafi, Laila kuma na zaune a kan kujera tana aikin tunani. “Ya fita ne?�? Ya tambayeta yana rufe cooler daya sako kwan a ciki. “Ni dai da sunan kayi aure ne amma baka barni na huta ba Mas’ud.�? Ta fad’i hakan tana kallon kulan hannunshi. “Ki godewa Allah zaki ci ladan ma’aurata, daa naso ke zaki soya ma, amma na lura yaronki na hararata sai na fasa.�? “He has a name yunno.�? Tace dashi tana masa kallon banza. “Ohh yanzu an daina kiranshi yaro kenan?�? Yayi ‘yar dariya ya fita daga gidan babu ko sallama. Hakan yasa Laila ta tabbatarwa kanta cewa Mas’ud zai dawo anjima, sau nawa? Shine bata sani ba. Yana fita da motarshi ya hango Haydar na tafiya ya isa gurinshi, “Ka shigo in rage maka hanya mana.�? Yace dashi yana sauk’e glass d’in motarsa. Haydar tsayawa yayi fuskarsa d’auke da murmushi yace, “A’a ka koma gurin Amaryarka. And nagode Mas’ud, ka zama tamkar brothern da ban ta6a samu ba. Thou jiya ka mini mugunta kuma zan rama.�? Dariya Mas’ud yayi kana ya mik’o mishi hannu suka tafa yace, “Anything for Kalti. Ina son duk abunda take so matuk’ar abun ba zai cutar da ita ba. Amma zo ka shiga domin ina son fad’a maka wasu abubuwa game da Kalti wanda baka sani ba. Ina ka nufa?�? “Gidanmu.�? “Ok hop in.�? A hanya Mas’ud ke fad’awa Haydar duk wasu halaye daya sani na Laila shi kuma yana jinshi yana ajiye komai a kwakwalwarsa. A k’ofar gidansu ya ajiyeshi yana cewa, “Ban yi wanka ba da na shigo na gaisa da maman Ango mai blue balls.�? Haydar dariya yayi yace, “Banyi tsammanin dama haka kake ba.�? “I can be scary if I like, ko kin gwada?�? “No man. Ka ta6a naushina ko ka manta?�? Cikin d’an kunya Mas’ud sosa k’eyarsa yana murmushi yace, “Ohh, about that I’m not sorry bro, kayi d’anyen kai ne. We are cool now.�? Ya mik’a mishi hannu suka k’ara yin musabaha kana yaja motarshi ya tafi. Haydar kuma wayarshi ce ta fara ruri ya d’auka yayi sallama aka amsa mishi. A take ya gane muryar Alhaji Abdul ce, shiru yayi bai ce komai ba Alhaji Abdul yace, “Haydar ka tashi lafiya?�? “Lafiya kalau Alhamdulillah.�? Ya bashi amsa muryarsa babu yabo babu fallasa domin bai san dalilin da yasa ya kirashi ba bayan ya kwace masa mata a ranar aurensu. “Naji ance sati kenan rabonka da zuwa aiki, kar kayi tunanin don wani abu ya faru tsakaninmu kace baza kayi aiki a company na ba. You are still an employee, babu wanda ya koreka sai dai idan kai zaka bar aikin. Sannan albashinka da zamu baka a watan gaba wato na wata biyu kenan zamu baka a yau, consider it as your marriage gift. Congratulations Allah ya baku zaman lafiya.�? Yana gama fad’in hakan ya kashe wayarsa ya bar Haydar da tsananin mamakin wannan abu. Yana shiga gidan Ammi yaji k’aran shigowan sak’o a wayarsa. Bai duba ba yayi sallama Ammi ta amsa daga cikin d’akinta tana tashi zaune fuskarta cike da annuri. “Wa’alaikas salam Ango, Muryarka nake ji?�? “Nine Ammi.�? Ya shiga d’akin shima fuskarsa d’auke da fara’a domin yayi kewarta. Tana kwance akan gadonta ta tashi zaune shima ya hau saman gadon ya kwantar da kanshi kan cinyarta. “Nikam tashi mini a kan cinya, mutum da girmanshi da iyalinshi amma ya dinga abu kamar na goye.�? Murmushi yayi ba tare da ya matsa ba yace, “Ke dai kice kinyi missing d’ina Ammi.�? Shafa kanshi ta fara yi ya lumshe idanunsa yana jin tsantsar sonta a zuciyarsa. “Har yanzu na k’asa yadda wai Alina ya zama babban mutum.�? “Hmm.�? Kawai yace, a ransa kuma yana cewa ‘ban zama ba tukun�?. Gaisheta yayi ta amsa tana tambayarsa kwanan Laila. “Tana nan lafiya tace a gaisheki.�? “Ina amsawa. To Ali ya batun aiki kuma tunda ka daina zuwa inda kake?�? Sai a lokacin ya tuna maganarshi da Alhaji Abdul yake fad’a mata yanda suka yi, ya k’arishe da cewa, “Amma bazan koma ba Ammi, zan nemi wani aikin.�? “Kaji mini shashanci, samun mutum irinshi sai an tona Ali. Duk da abunda ka mishi bai gani ba yace ka dawo kan aikinka ai ya maka halacci.�? “Ammi bazaki gane yanda nake ji bane, idan na tuna wai ya nemi matata har ya kusa aurenta sai naji bak’in ciki. Ikon Allah ne kad’ai yasa Laila ta zama tawa.�? Ya tashi ya zauna yana dubanta. “Sai ka godewa Allah daya canja hakan Ali ya baka ita ba dabararka ta baka ba. Ka koma aikinka domin a yanzu da kake da iyali zaman haka d’in bazai yiwu ba.�? “Ammi jiya na yiwa Nasir magana kan zai rok’i maigidansa ya mayar dani aikin kantin, idan har ya yarda kinga babu batun komawata Lu’a Ventures.�? “Suna mai dad’i irin sunana.�? Ta fad’i haka tamkar mai daydreaming tana kallon sama. Can kuma ta dubeshi cikin bashi umurni tace, “Ka koma kan aikinka Ali tunda shi da kanshi ya kiraka yace ka koma.�? Bai ce komai ba ya d’auki wayarsa da take ruri yaga wata sabuwar number ce. D’auka yayi fuskarsa babu fara’a yace, “Yes.�? “Nine Accountant na Lu’a Ventures. An tura maka dubu saba’in daga account d’in company. Muna jiran ka dawo aiki ranar monday.�? “Zan yi tunani akai.�? Ya kashe wayarsa kana ya duba sak’on daya shigo wayarsa. Alert d’in kud’in ne kamar yanda suka fad’a wato dubu saba’in ciff. “Ammi bana jin zan iya komawa aikin nan, hankalina ba zai ta6a kwanciya dashi ba.�? “Kana da wani aikin ne bayan shi Ali? Kayi tunani dai.�? Ta fad’i hakan tana dafa kad’arshi. Gyad’a mata kai yayi ya koma kan cinyarta yana tambayarta me take buk’ata zai mata cefene an turo mishi kud’in aikinshi. Bai bar gidan ba sai bayan azahar bayan ya yiwa Ammi sayayya na kayan abinci ya bata dubu goma a hannunta yace ta rik’e. “Sai gobe zan dawo Ammi. Idan kina buk’atar wani abu ki kirani a waya.�? Ya fad’i hakan yana fita daga gidan. Addu’a ta bishi dashi kamar kullum ta koma tana bubbud’e ledojin sayayyan daya mata taga har da d’anyen kaza wai tayi ferfesu. “Allah ya k’ara maka bud’i kafi haka Alina.�? Gurin Nasir ya wuce kai tsaye ya sameshi suka gaisa yana tambayarshi ya ake ciki. “Wallahi Haydar yanda kwanaki ka bar aikinka lokaci d’aya bai mishi dad’i ba, yanzu maganar da nake maka cewa yayi sai dai in zaka yi gadin kantin, sai ka dinga shift da Dalhatu. Kaji yanda aka yi.�? Shiru Haydar yayi yana tunani, ya koma aikinsa ne ko dai ya k’ar6i gadin? “Shikenan zan yi shawara.�? Yana fad’in hakan ya koma kasuwa ya sayawa Laila Agwaluman da tace tana so tare da wasu kayan abinci da yake tunanin babu a gidan nata. Ko da tana dashi shima zaiyi iya bakin k’ok’arinsa ya ciyar da ita. Bai koma gidansa ba sai bayan la’asar ya samu Laila tare da k’awayenta biyu wato Hajiya Maryam da Hajiya Shatu. Suna ganinsa kowacce ta fara gyara gyalenta suna murmusawa. Gaisheshi suka yi cikin girma da arziki shima ya amsa fuska a sake Laila na k’arban ledojin hannunsa. “Sannu da dawowa.�? Tace dashi ya bita da kallo ganin har ta canja shiga. Yana son mace mai kwalliya kuma Allah ya bashi. Kitchen ta kai kayan shi kuma ya shiga d’aki ya bar k’awayen nata a falo. Tana dawowa suka sake ‘yar k’aramar gud’a, Hajiya Maryam har ta rasa inda zata saka kanta. “Kai matan nan ashe kin san abunda kika gani, ni wallahi tunda nake ganinshi ban ta6a kare masa kallo ba sai yau. Ashe duk wannan russunawan da yake miki yasan me ya hango. Wallahi ji nake yi kamar In zama ke.�? Laila ta watsa mata harara cikin wasa amma a zuciyarta bata ji dad’in k’arewa mijinta kallo da tayi ba, tace, “Allah ya shiryeki ke kam, Bari baban Ilham ya jiki zamu ga yanda zaku kwashe.�? “Ke nima fa ina ga yaro zan nema d’anye shataf inyi wuff dashi.�? Fad’in Hajiya Shatu tana d’aukan jakarta, dama ita bazawara ce dalilin sakinta da uban ‘yayanta yayi. “Ina kuma zaku je naga kuna shirin fita?�? “Mijinki ya dawo kuma me zamu zauna muyi. Kinga Hajiya mu tafi gwanda ita a gidan mijinta take.�? Hajiya Maryam ce ta fad’i hakan kana ta rankwafo ta yiwa Laila magana a kunne wanda yasa taji kunya ba kad’an ba. “Kai matan nan ban san yaushe zaki san kin tsufa ba. Ni kam ban sani ba.�? “Ai ba’a tsufa a harkan nan.�? Ta kare kanta tana dariya suka fita dukansu. Bayan Laila ta musu rakiya ne ta dawo ta shiga d’akinta gurin Haydar. Ganin baya cikin d’akin ta gane cewa ya shiga wanka ne domin ga kayanshi nan ya tu6e ya ajiye a kan gado. A yanda ta lura dashi yana son jefar da kayanshi a ko’ina sai dai a bi a tsinta a adana mishi. Tattare kayan tayi ta kaisu kwandon kayan dotti ta ajiye kana ta bud’e wardrobe d’inta inda ta jera masa tsiraran kayan da yazo dasu ta fara ciro masa wanda zai saka. Duk wannan abunda take yi murmushi ne a fuskarta tana jinta tamkar sabuwar halitta, wai itace da aure kuma take yiwa mijinta hidima take samun ladanshi? “Murmushin me kike yi?�? Ta jiyo muryarshi a bayanta alamar ya fito daga wankan. Juyowa tayi ba tare da murmushin ya bar bakinta ba tace, “Babu.�? “Fad’a mini dai.�? Ya d’auki deodorants d’inshi data ajiye a gaban mirrow ya fara sakawa tana bin jikinshi da kallo. “Kawai, haka kawai. Ummm su Hajiya Maryam ne suka bani dariya.�? “Kuma? To me suka ce?�? Ya fad’i hakan yana cire towel d’in jikinshi ya tako zuwa gurinta babu komai a jikinshi. “Haydar.�? Ta kira sunanshi tana daskarewa a gurin idanunta a zare tana kallonshi, sai dai har ya iso gurinta bai ta6ata ba illa ma ra6ewa da yayi ta gefenta ya fara bincika gurin data ajiye mishi kayan nashi. Wata three quarter ya d’auka ya saka a gabanta kana ya fita zuwa falo yana cewa, “Na tambayeki abu amma kinyi shiru baki bani amsa ba. Come and feed me Mummy, yunwa nake ji.

Mum Fateey 👌

Back to top button