Uncategorized

Tubali Book 2 Page 1 Hausa Novel Complete

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Da al’hinin ganisa ya tsananta harbawa da ƙirjinta yakeyi.

Shikuwa Rayyern a nitse ya kawar da kansa gefe, hade kuma da juyawa, kan Fridge.

 A hankali ya dan sunkuyo kan, fridge din dake cikin kitchine din ya bud’e, cikin sa’a kuwa ya samu chocolate aciki.

Ba tare da ya kuma kallon inda takeba ya.

 D’aukan chocolate din nasa yayi mai, batare kuma dako juyowa  ba, ya nufi hanyar fita Kitchen din cikin nitsuwa.

Jannart kuwa zuciyarta ne ke harbawa da wani irin k’arfi, gaba daya ta kasa d’ago kanta kasan cewar kanta a sunkuye ne yasa idonta sauka kan tatrausan fararen sawunshi da in ya taka sai gefe da gefen yayi ja, kana in ya daga yayi fari,  wani irin bugawa chest da kuma Heart dinta keyi.

Cikin mgnar zuci tace.

“Wannan mutumin kuma? To Meya kawosa cikin gidannan? Me yakeyi anan?”.

Numfashi ta dan fesar a hankali kana taci gaba da nazari da zancen zuci. “Toh kenan shima d’an gidanne.

 Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.”

Ta fad’i hakan acikin zuciyarta, lokaci daya kuma sunan wanda ake kira amatsayin Mijinta ya fad’o mata a rai. “Rayyern!”

Ta maimaita sunan cikin zuciyarta domin har yau har yanzu bata taɓa iya furta sunanta kan harshen ta ba.

Lokaci d’aya kuma tayi saurin girgiza kanta.

Dan bataji ajikinta cewar shine Rayyern din da ake ta fadi ba, fact ma har yanzu batasan wayene mijinnata ba.

cikin sauri kuma ta d’an d’ago Kai ta sake kalloshi. 

Dai-dai lokacinne kuma ya kusa kaiwa gab fita daga cikin kitchine din.

Sunkuyar da kanta k’asa tayi, kana cikin sanyin muryar ta dake d’an rawa tace.

“i…in Ina kwana.” ta fuzgo maganar a hankali.

Idonshi ya ɗan lumshe jiyo sautin muryarta.

Ido ta zuba mishi ganin yana tafe kamar bai ji taba.

Ƙasa tayi da kanta, sai kuma ta ɗan ɗago idonta jin kamar yayi mgn amman bataji kamar

“Lafiya.”

Daya amsa mata atak’aice batare kuma dako ƙara ko second biyu ya fice daga cikin kitchine din. 

Fitar tasace kuma yasa Jannart sauke Ajiyar zuciya, tare dasa hannu ta dafe kirjinta da takejin yana Azabar bugu, bayansa tabi da kallo, har acikin zuciyarta tana me mamakin ganinsa da tayi a cikin gidan. 

Numfashi ta dan fesar tana mai yin rau-rau da idonta.

Sabida bataji amsawar da yayiba dan larurar kunnuwanta.

Yayinda a zuciyarta kuwa take fargabar baro Yah Junaid ta kuma samo irinsa a nan.

A hankali tace.

“Abba munyi gudun gara mun tadda zago!”.

Shikuwa Rayyern yana fita falon, Wayarsa ya zaro tare da dannawa numbern Mamy kira.

Bugu biyu kuwa Mamy ta d’aga wayar.

Kasancewar daman jiran d’aga wayar nata yakeyi ne, yasa tana d’agawa ya kwaɓe fuska, tare da cewa.

“Mamy ina kikajene gidan babu kowa.”

Mamy kuwa da ke tsaka da sayan kayayyaki daka tawa tayi.

Jin abunda ya fada dinne kuma yasa ta cewa.

“Kamar ya gidan babu kowa Rayyern? baga Jannart ba.”

Fuskarsa ya kwab’e batare daya nuna damuwarsa da zancen ba kuma yace.

“Mamy yunwa nakeji.”

“Yunwa kuma Rayyern? to kaje ka tambayi Jannart zata baka abinci.”

Mamyn ta fad’a in a serious.

Jin hakanne kuma yasashi Katse kiran, tare da turo bakinsa gaba, tamkar karamin yaro, cikin guna guni yace.

“Ni meye hadina da wata Jannart, ce ko Jalila ce ma babu abunda ya shafeni da ita, I told you ai, I don’t love her, but kuka shareni kuka wani medani kamar karamin yaron da baisan abinda yake yiba.” 

Ya k’are maganan yana me karasa haurawa saman.

Anan cikin falonnasu na sama ya zauna, bayan ya zuba.

Wasu daga cikin Chocolate din cikin Fridge.

Kana ya debi na cinsa a plate,

sannan ya zo ya zauna yana latsa wayarsa tare da b’are chocolate dinsa yaci, bayan ya gama cine kuma ya d’aura da ruwa.

Acan Shoprite kuwa, su Mamyn sayayya sukayi sosai, Yayinda kuma Rabin sayayyar tasu, kayan sawa ne, kama daga kan dogin riguna abayas, sai kuma yan kanti wandunan pallazo, da kuma skirts, sai atamfofi da lesuka, kama daga kan takalmi shoes, Hijabs, vails, bags, dama duk wasu abubuwan buk’atan Mace babu wanda basu saya ba.

Haka dai suka dawo gida da kaya niki niki.

Wanda zuwa lokacin kuma tuni Jannart ta kammala, had’a musu komai na lunch akan dining harma ta koma falon ta, bayan tayi sallan azahar ne kuma ta kwanta.

Su Mamy kuwa Sai da karfe 1 ta gota,  kafun suke dawowa.

Ramadan nayin parking cikin gidan, Hadi ya matso da sauri ya budewa Mamy marfin motar.

Bayan sun fito daga cikin motar ne kuma, Ramadan, Riyyam da kuma Hadi suka shiga jidon kayan da suka sayo din, suna shigarwa zuwa babban falon k’asa.

 Bayan sun gama shigo da kayanne kuma, Hadi ya koma waje.

 A tsakiyar falon suka ajiye kayyakin tare da kimtsasu wuri daya kayan masu yawane, domin duk wani abu na amfanin Mace babu wanda basu sayo ba hatta audugar mata Mamy ta saya mata, ga kuma wasu had’add’un akwatuna set masu kyau da suka sayo.

Mamy kuwa wanda shigowarta cikin falon kenan, jakan dake hannunta ta ajiye, tare da wuce wa kaitsaye ta nufi bedroom dinta, saboda Ganin da tayi lokacin sallan azahar na kokarin gotawa.

Ramadan da Riyyam kuwa, anan cikin bathroom din dake cikin falon, suka d’auro alwala, tare da jerawa atare suka wuce masallacin, dake jikin gidan nasu.

Bayan sun idar da sallan azahar dinne kuma, suka sake dawowa cikin gidan, gaba ɗaya a sokane suke tafiya, wanda da dukkan alama kuma yunwa sukeji da tarin gajiya, saboda zagayen da suka sha a cikin Shoprite din, wai danma sun dan saya biscuit, sunci acikin Shoprite din.

Dawowarsu cikin falonne kuma suka samu, Mamy zaune, wanda itama idar da sallanta kenan, ta dawo falon ta zauna.

Akusa da Mamyn suka zauna.

Yayinda Riyyam kuwa ya langwab’ar da kai, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin yanayin shagwab’an wanda in yanayi, tsananin kamanninsu da Rayyern ke k’ara bayyana yace.

“Wash Allah Mamy yunwa nakeji, har inaji kaman babu hanji acikina.”

“To Riyyam, yanda naji gidannan gaba daya, ya gauraye da kamshi, ai nasan abinci na musamman Auntynku ta girka mana.”

Mamyn ta fad’i haka tana murmushi, saboda sosai maganan Riyyam din ya bata dariya.

Jannart dake kwance anan cikin falonta kuwa, cikin dan bacci Marar nauyin daya d’auketa ne, ta soma jin tashin hayaniyarsu,  bud’e idanunta tayi, tare kuma da tashi ta zauna.

Shiru tayi na y’an wasu mintuna, Jin da gaske maganan su Mamyn ne ke tashi acikin falon, yasa ta d’aukan mayafinta ta rufa, ahankali ta mike tsaye, kana cikin takunta na nutsuwa, ta nufi falon nasu kaitsaye.

Ahankali ta murd’a handle din kofar falon nata ta fito, tozali dasu Mamyn da tayi ne kuma yasa ta sakin dan murmushi, tare da karasowa ta durkusa a gaban Mamyn.. 

“sannunku da dawowa Mamy.” 

Jannart din ta fad’a tana me duk’ar da kanta k’asa.

“Yauwa sannunki dai Jannart, ya fama da kad’aici.”

Mamy ta tambaya cike da nunawa Jannart din kulawa.

Jannart kuwa Murmushi tayi tare da cewa.

“Alhamdulillah amma da bakwa nan gidan ba daɗi Mamy”. Tayi mgnar cikin fito da gskyr zuciyarta.

Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa.

“Meyasa baki taso Rayyern yazo ya tayaki zamaba”.

Tayi mgnar cikin son nuna kusancinsu.

Ita kuwa Jannart da sauri tayi ƙasa da kanta.

Kana cikin nutsuwa ta mike tsaye,  direct gaban fridge ta nufa, inda ta bud’e ta dauko ruwa, da kuma tamarine juice maisanyi,  bayan ta shiga kitchine ta dauko cups ne kuma, ta sake dawowa cikin falon, tare da ajiye juice da ruwan agaban Mamyn, cikin nuna tsantsar kulawa tace.

“Mamy ga ruwa kusha, nasan kunsha hanya, sannan ga abinci ma, tun d’azu na gama.”

Murmushin Jin dadi Mamyn tayi, tare da karb’an ruwan, da Jannart din ta tsiyaya a kofi Tasha, 

Zuciyarta kuma  cike da annushuwa tace.

“Masha Allah Jannart Allah ya miki albarka.”

“Ameen.”

Jannart din ta amsa cikin jin daɗi.

Yayinda shikuwa Ramadan dake zaune, ya tankwashe k’afafu Kallon Jannart din yayi, cikin dan sigar gajiya yace.

“Aunty Jannart wallahi yunwa nakeji, tun breakfast din safe, sai wani dan biscuit da naci, abamu abinci please.”

Murmushi Jannart din tayi, kana cikin sakin fuska tace.

“Sorry  akwai abinci zakuje dining ko kuma akawo muku abincin nan.”

“Kai Anya kuwa, gaskiya dai Jannart kawo mana shi nan muci, saboda dukanmu agajiye muke.”

Mamy ta cab’i zancen domin itama kanta yunwa takeji.

Jannart kuwa kaita jinjina tare da cewa.

“To bari nakawo muku abincin nan.”

Tana gama fad’an hakan kuwa, ta mik’e tsaye, tare da nufan dining table din, food flasks din da ta zuba abincin aciki ta d’auko, atsanake kuma ta shiga jere musu shi agabansu.

Bayan ta kammala haka dinne kuma, ta d’auki plates tare da fara saving ko wannensu, had’add’iyar jollop rice and coleslaw din, ta zubawa Mamy, sai kuma pepper chicken onion soup din da ta zubashi acikin wani plate da ban.

Kamar yanda ta zubawa Mamyn kuwa, haka ta sakawa su Ramadan da Riyyam ma, way’anda sukayi zaman  dirshan.

Saboda ma tunkafun su saka abincin abakinsu, kamshi duk ya cika musu hanci.

Turawa kowannensu abincin agabansu tayi, yayinda na Mamy kuwa ta kai mata har gabanta.

Tare da d’aukan cup ta zubawa kowannensu Shaka’n da ta had’a. 

Ramadan da Riyyam kuwa, tun a Loman farko da sukayi, duk suka lumshe idanunsu, saboda wani irin dadin abincin da sukaji, tun kafun su gama tauna abincin kuwa suka soma jijjiga kansu, cike da gamsuwa, Ramadan yace.

“Masha Allah, nice taste gaskiya Aunty Jannart kin iya girki, ko daga aroma dinma kin biya.”

“Sosai kuwa Aunty Jannart, gaskiya abincinki akwai dadi, wayyo Allah kaman kunnena zai tafi.”

Cewar Riyyam-nsra daya cab’e zancen.

Ba’iya Mamy dake dariya ba kuwa har Jannart saida tayi murmushi.

Ahankali kuma ta mik’e tsaye, tare da sunkuyar da kanta k’asa cikin sanyi tace.

“Mamy bari na koma d’aki.”

Saurin Riko hannunta Mamy tayi, kana cikin kulawa tace.

“A’a Jannart Ina kuma zaki, ki zauna mana muci abincin tare, ko wani abu zakiyi a dakin?”

“A’a.” Jannart din ta fad’a ahankali, tare da soma wasa da y’an yatsun hannunta. 

“to zauna kinji, kada kice zakiji kunyan mu, duka munzama daya.”

Mamyn ta fada mata cikin kulawa.

Jin hakanne  kuma yasa ta zama, tare da bud’e food flask din Fan cake din, ta soma kokarin saka Musu acikin plate. 

Ramadan da Riyyam kuwa tuni suke ta zuba santi akan abincin.

Wanda hakan yasa, Mamy daukan pillow ta saka musu, amatsayin waiji, sabida yanda suka cikasu da surutu. 

Acan compound din gidan kuwa, Abba da Rayyern dinne suka shigo, atare kasancewar su sai yanzu ne suke dawowa daga masallaci, saboda Koda aka Idar da sallah basu bar masallacin da wuri ba.

Dab da zasu k’arasa jikin kofar falonne kuma, Rayyern yaga Abba na kokarin wucewa gaba.

“Abba Ina kuma zaka?”

Rayyern ya tambaya, da dan mamaki.

Hakan ne kuwa yasaka Abban sakin murmushi, kana cikin kulawa yace.

“K’ofar baya zanbi Rayyern”.

Da sauri yace.

“Meyasa?”.

Yana mai ci gaba da tafiya yace.

 “Sabida surkata daga yau ma tacan zanna shiga da fita.”

Fuska Rayyern din ya kwab’e, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, Yayinda Abba kuwa kaitsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da kofar falonsa na baya.

Rayyern kuwa fuskarsa ad’an tsuke yake mgnar zuci.

“Ba ga irin ta nanba kuma kanku takura zata zame muku”.

Ya ƙare mgnar yana tura kofar falon ya shiga, bakinsa d’auke da sallama. 

Jin sautin muryarsa ne kuma, yasa Mamy dasu Ramadan d’agowa suka kalleshi, tare kuma da amsa masa sallaman nasa.

Idanunsa ya d’an zuba musu, musamman Ramadan da Riyyam, wanda yaga sun maida gaba daya hankalinsu wajen cin abinci, musamman ma Ramadan wanda ya ritsa pepper chicken, babu abunda kakeji atsakaninsu sai kat-kat  k’aran spoons.

Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma dasa hannunsa ya dafe cikinsa, dan ƴar yunwar da yake ji.

 buɗe idanun  nasa da zaiyine kuma ya sauk’e ganinsa akan Mamy,  wacce ta d’an zuba masa ido.

 Idonshi ya kauda tare kuma da karyar da wuyansa gefe.

yanayin yanda Mamyn taga yasa hannayensa akan lafaffen cikinsa ne, kuma yasa ta gyara zamanta, kana cikin tausasa murya tace.

“Kwata kwata bakason cin abinci Rayyern, kana son barin kanka da yunwa bana son hakan

Kai kullum rayuwarka ta ƙare a cimar zaki, duda kasan matsalar da ke damunta, da anyi mgn sai kace.

Ba zaƙine matsalar ciwon kaba.

 Zo kaci abinci kaji, gashi nan da d’uminsa kaci tun kafun ya huce, saboda nasan bakason cin abinci mai sanyi.” 

D’an kwab’e fuskarsa yayi, had’e da kawar da kansa gefe.

Yayinda Ramadan dake ta cin nama kuwa ya d’ago da kansa ya kalli Hamman nasa, kana cikin santin abincin yace.

“Hamma Rayyern abinci yayi dadi, ka gwada ci  kaji pepper chicken dinnan kuwa, badai dadi ba.”

Ya k’are maganar yana me yagan cinyar Kazan  yasa abakinsa. 

Riyyam-nsra kuwa, juyawa da kallonsa yayi ga Jannart, wanda take zubawa Mamy juice na pineapple and Orange din da tayi, kanta ak’asa yake, domin tun shigowar Rayyern din bata ma d’ago kanta ba.

“Nasara miki Aunty Jannart, wallahi kin iya dafa abinci sosai, tunda na shigo Nigeria banci fancake mai dadin naki ba, please kullum kina yi manashi kinji..” 

ya k’are maganar yana me rausayar da kansa gefe, alaman rok’o.

Jannart kuwa da har yanzu kanta ke k’asa murmushi tayi, batare kuma da tace komai ba, ta zuba musu shaka a cup shida Ramadan. 

Mamy kuwa Rayyern dake tsaye yana Kallon wani waje daban ta kalla, still kuma cikin kulawa tace.

“Babana zokaci abinci kaji, ka daina zama da yunwa.”

  Kansa ya d’an girgiza alaman “A’a.”

Batare kuma daya ce komai ba, ya zagaya ta gefensu, kaitsaye ya nufi hanyar steps din da zai kaishi zuwa sama, ko kusa kuwa bai kalli inda Jannart take ba, impact baisan da cewar tana acikin falon ba.

Mamy kuwa da kallo ta bisa, harya soma haurawa saman stairs dinne kuma ya Dan tsaya, tare kuma da juyowa ya kalli Mamyn nasa yace.

“Mamy Abba fa ya shigo, yana side d’insa.”

Kai Mamyn ta jinjina, Yayinda shikuwa Rayyern din kaitsaye ya haura sama. 

Jannart kuwa har dai zuwa yanzu ta kasa d’ago kanta, saidai jin alaman tafiyarsa yasa ta sauk’e b’oyayyar Ajiyar zuciya. 

Mamy kuwa food flask din abincin ta d’auka, bayan ta mik’e tsaye ne kuma tace.

“Barin kaiwa Abbanku nasa abincin.”

Bayan ta wuce sashin Abban ne kuma, Jannart din ta d’an gyara zamanta, tare da d’ago kanta, ta kalli babban tv’n dake cikin falon,  inda taga tv channel dinsu, wato Arewa24 suna haska film din, Nisan Kwana.

D’an maida hankalinta ga tv’n tayi, Yayinda su Ramadan kuwa har yanzu cin abincin nasu yaki k’arewa, santi kawai sukeyi,  shakan da ta had’a kuwa tas suka shanye shi. 

Acan b’angaren Rayyern kuwa yana shiga cikin falon nasu, jacket din dake saman rigarsa ya cire, tare kuma da karasawa gaban fridge dinsa, bud’e murfin fridge din yayi.

Hade da d’auko babban kwalban  chocolate d’insa, wanda saboda tsabar sanyi harya fara daskarewa.

Murfin kwalban ya b’alle, tun kafun ya zauna kuwa ya saka spoon acikin kwalban, tare da d’ebo chocolate din ya soma sha.

Idanunsa ya lumshe, alokacin da yaji zakin chocolate din na mamaye bakinsa. 

Cikin nutsuwa kuma ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon,  bayan ya daura kafafunsa akan rug ne kuma ya ci gaba da Shan chocolate d’insa. 

Yana girgiza k’afa alaman yana enjoying mood dinnasa. 

Mamy kuwa Koda ta isa part din Abban, zaune ta sameshi a falon, ganinta ne kuma yasa Abban sakin murmushi. 

Kana cikin sakin fuska yace.

“Banyi tunanin zuwanki yanzu ba ai, naga kaman yaran naki sun rik’eki da zance saboda daga nanma inajin tashin maganganunku.”

Murmushin Mamyn tayi, adaidai lokacin da take k’arasowa gabansa ta durk’usa,  kana muryarta atausashe tace.

“Barka da dawowa.” 

“Yauwa, kuma sannunku da dawowa, fatan kunyi sayyaya lafiya?”

“Lafiya lau Alhamdulillah, munsayo duk wasu abu da suka dace gacan kayan ma acikin falo, ko kuncesu ba mu yi ba.”

Mamy ta amsa tana me kokarin zuba masa fried rice acikin plate.

Abban kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, kuma yace.

“To Allah ya Amfana.” 

“Ameen.” Mamyn ta amsa tana me ajiye masa plate din abincin agabansa, hade kuma da zuba masa juice, and fancake. 

Juice din Abban ya d’auka ya d’an kurb’a, cikin rashin son tauyeta kuma yace.

“Kije ki gama da yarannaki ko, ni Idan yaso kyaji dani anjima.” 

“To.” Mamy tace tana murmushi, kana kuma ta mik’e ta fice daga Cikin falon. 

Koda ta dawo falon,harsu Ramadan sun kammala cin abincin.

Inda Riyyam da kansa ya tartare wajen,. Tare dakai plates din da suka b’ata kitchine.

Mamy kuwa zama tayi tare da jawo kayyyakin da suka sayo.

“Jannart  zokiga kayayyakin da muka sayo.”

Mamyn ta fad’a tana me bubbud’e kayan.

Inda ta fara ciro wasu tsala tsalan laces, da kuma atamfofi masu kyau, Hadi da materials da shadda laces.

Jannart kuwa ganin yanda kayan suke da kyau sosai ne yasakata sakin murmushi, tare da cigaba da Kallon kayayyakin da Mamyn ke fitowa dasu.

Bayan Mamyn ta faka su laces din agefe ne kuma, ta soma ciro had’add’un Turkish, and Dubai abayas and kimonos, masu kyau da tsadar gaske,  kasancewar kuma abayas din irin new design dinnan ne yasa suka dauki hankalin Jannart. 

Mamy kuwa sauran shoes bag and vails, da kuma sauran abubuwan da suka sayo duk ta nunawa Jannart,  kana cikin kulawa kuma tace.

“Jannart ga kayayyakin naki, Allah yasa sunyi miki.”

Murmushi Jannart din tayi, tare da d’an sunkuyar da Kanta, tana kallon datsassun abayas masu masifar kyau da laces din cikin sanyin murya kuma tace.

“Komai yayi, nagode sosai Mamy Allah Ya saka da al’khairi.”

“Ameen Summa Ameen Jannart, ba komai ai yiwa kaine.”

Mamy ta amsa, tana me zaro wayarta, inda ta dannawa number’n, tailor din da ta amince da k’warewar sa kira.

Bugu biyu kuwa tailorn ya d’auka, bayan sun gaisane kuma Mamy ta shaida masa cewar tanason ganinsa.

Kasancewar yasan inda Naira take ne kuma, yasa take yace.

“Toh Hajjajo. Ganinan zuwa.”

Kashe wayan Mamy tayi, tare da Kallon Jannart cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart wani irin dinkuna kikeson ayi miki, kinsan ku y’an matan zamanin nan yanzu baku cika son riga da zani ba.”

Sadd’a kai k’asa Jannart din tayi,  ladabce  tace.

“Ni Mamy komai akayi ma inasawa.” 

Murmushin Mamyn tayi tare da cewa.

“Shikenan To bari tailan yazo.”

Nan dai suka shiga d’an tab’a hira, Yayinda Riyyam-nsra da Ramadan keta jan Jannart din da hira.

Suna nan azaune kuwa, cikin abunda bai wuce 15mn ba saiga tailorn yazo.

Bayan sun gaisane kuma Mamy ta basa, k’atuwar ledan da ta Ware kayayyakin dinkin aciki, kana cikin sakin fuska tace.

“Fahad ga y’atanan dan Allah kayi mata dinkuna masu kyau, way’anda zasu sake fito da ita sosai, sannan kuma akan kari muke buk’atar kayan.”

Murmushi Tailan da Mamyn ta kira da Fahad yayi, kana Cikin  bata girma yace.

“Insha Allahu Hajiya za’ayi mata dinki dai-dai da zamani, kafun nan da sati biyu kuma zaku samu dinkin Insha Allah.”

“Yauwa to Allah yasa, yanzu za’a baka size dinta ne, ko  zaka gwada ta?”

Mamyn ta fad’a tana me Kallon Jannart da kanta ke sunkuye.

Kanshi ya ɗago ya ɗan kalli Jannart kana yace.

“A’a basai na gwada taba, ai naganta kuma Insha Allah zanyi mata komai yanda ya dace.”

Fahad din ya kare mgnar yana sake harhad’a kayan waje daya.

Mamy kuwa kaita jinjina cike da gamsuwa tace.

“To nawa ne kudin dinkin naka.” 

D’anjim Fahad din yayi, saboda shi kansa baisan nawa zaice ba, kasancewar kayan suna da yawa, dole sai ya nutsu ayi total tukunna.

Fahimtar hakanne kuma yasa Mamy mik’ewa tsaye, tare da cewa.

“Kad’an jirani inazuwa.” 

Kaitsaye sama ta haura, tana shiga cikin falon saman kuwa ta hango Rayyern zaune, ya daura kafarsa daya kan d’aya, Yayinda idanunsa kuwa ke lumshe, sai kuma goran swan dake rike a hannunsa.

“Rayyern.”

 Mamy ta kira sunansa.

Jin sautin muryar Mamynnasa ne kuma yasashi bude idanunsa.

Tare da gyara xamansa yace “Mamy.”

“Na’am tunanin mekakeyi?” Mamyn ta tambaya cike da kulawa.

Kansa ya dan juya,  kana cikin sanyi yace.

“Babu komai Mamy, kawai dai nagaji ne.”

“Da kyau.

dama kudin dinki nazo karb’a awajenka, yanzu na kira taila kuma yazo, zai tafi da kayayyakin da muka sayo zaije ya dinkosu.” 

Mamyn ta fad’a tana me tsaresa da idanu.

Wanda hakanne kuma yasashi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, kana akasalance yace.

“Eyyah Mamy ai duk kun kwashemin y’an kud’ad’ena, kuma fa bana da wani kudi sosai, sannan ba atm dina yana hannunku ba naga shima yadda kuka yasheni kamar ba gobe.” 

Murmushi Mamy tayi, saboda tasan maganar cewa ma bashi da kudi ba gaskiya bane.

Sai dai al’adarsa ce bai cika son almobazaranci ba, yana fadin hakanne kawai saboda kaucewa mgnar da suke ta lika mishi

“Cash mukeso yanzu ba wai transfer ko wani abuba, tailor ne yazo, ko atm card din kakeso mu bashi yaje ya cire?” 

Cewar Mamyn.

Rayyern kuwa da sauri ya kalleta tare da cewa.

“Atm card na din zaku bawa wani, uhumm lallai Mamy abun ya magaga”.  shi bawai kudin bane bayason bayarwa, a’a kawai dai shi ayanda aka lika masa auren ne baiso ba, saboda dama yasan dolene sai antakurasa akan hakan.

Ita kuwa Mamy ido kawai ta zuba mishi.

Mik’ewa tsaye yayi, tare da nufan d’akinsa, kaitsaye  gefen bedside drawernsa ya nufa, Koda ya ya karasa bud’e drawern yayi ya d’auko, bandir din kudi, Rafa daya inda kuma kowani Rafa daya 50k ne.

Juyowa yayi ya dawo falon, tare da damk’awa Mamyn kudin.

Cikin shagwab’a da kuma turo baki yace.

“Mamy gashi yanzu a barni in huta ko. Kuma a kamo min ATM na kin san Ramadan ba mutuncine dashi ba, in ya samu kudi.”

Karb’an kudin Mamy tayi, batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin.

Koda ta sauko kasa, duka 50k din ta bawa Fahad.

Da ya tashi tafiya ne kuma ta had’ashi da Hadi  ya kaisa har zuwa babban shagonsa. 

Sauran kayan da suka rage din kuwa, Mamyn da kanta ta Taya Jannart suka shigar dashi, can cikin bedroom din Jannart din. 

Cikin kulawa kuma haka Mamyn ta Taya ta suka shirya duka sauran kayan acikin wardrobe,  kayan shafa kuwa anan kan dressing mirror Jannart din ta jere su.

Bayan sun kammala komai ne kuma,  suka sake dawowa nan cikin  main falon.

Zama sukayi inda Riyyam da Ramadan kuwa suka shiga sana’arsu ta buga game, ganin yanda Game din ke dadi ne kuma yasa, Jannart maida gaba daya hankalinta garesu.

Mamy kuwa kallonsu take fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi, saidai kuma ganin yanda hankalinsu duk ya tafi akan game dinne yasa, ta mik’ewa.

Anutse ta nufi sashin Abba. 

Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, bakinta dauke da sallama. 

Abba dake rike da wani littafi na Tafsir, ne ya amsa mata sallaman tare da d’ago kansa ya kalleta.

Itakuwa Mamy fuskarta dauke da murmushi ta k’arasa shigowa cikin falon, cikin muryar dake nuna tautasawa tace.

“Allah yasa bankatseka daga abunda kakeyi ba.”

Murmushi Abban yayi, cikin fadada fara’ar dake kan fuskarsa kuwa yace.

“Sam baki katseni ba, kamar kinsan cewar kuma dama ina nemanki.”

Abban ya fad’a yana me jawo wata leda dake gefensa. 

Mamy kuwa k’arasowa inda yake zaunen tayi, tare da durkusawa ta zauna agabansa.

Abba kuwa Ledan dake hannunsa ya mik’a mata, atausashe yace.  

“Waya ce wannan d’azu na sayowa Jannart ita, ki kai mata, duk na sha’afa shiyasa d’azu da kika shigo ban baki ba.”

Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mamy, cikin farinciki kuma tace.

“Kai Masha Allah, amma gaskiya Jannart zataji dadin hakan, Allah ya kara bud’i.” 

Mamy ta fad’a tana amsar ledan.

“Ameen.” Abban ya amsa, Yayinda ita kuwa Mamy ta mik’e, tana fad’in.

“Bari nakai mata wayar na dawo.” 

 Abban kuwa Kai ya jinjina alaman “To.”

Haka Mamy ta fito daga sashin Abban fuskarta d’auke da murmushi, ta karaso nasu sashin. 

Har yanzun kuwa su Jannart na zaune.

Akusa da Jannart din Mamyn ta zauna, kana cikin tausasawa tace.

“Jannart ga sak’o inji Abbanku.”

Jin hakanne kuma yasa Jannart, d’ago Kai ta kalleta, tare kuma dasa hannayen ta bibbbiyu ta karb’i ledan, da Mamyn ke mik’o mata.

Ahankali ta warware ledan, tare dasa hannunta ta zaro kwalin dake cikin ledan.

Idanunta ta d’an zaro waje, saboda Ganin kwalin waya da tayi, kirar Samsung Galaxy S21 ultra.

“Wow Samsung galaxy S21 ultra, gaskiya Abba yanaji dake Aunty Jannart.”

Riyyam-nsra ya fad’a, Cikin nuna jin d’adinsa.

Jannart din kuwa, itama tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskarta, wanda saboda jin dadin kyautan da tayi ne kuma yasa, har hakwaranta suka bayyana alokacin da take murmushi.

Cikin tsananin jin dadi, da kuma nuna yaba kyautar da Abban yayi mata tace.

“Nagode sosai Mamy Allah ya kara arziki, ya kuma kara rufa asiri, Allah ya jik’an magabata.”

“Ameen Ameen Jannart, ba komai ai duk yiwa kaine, yanzu ke tamuce komai mukayi miki basai kinyi mana godiya ba.” 

Mamy ta fad’a ciki kulawa. 

Jannart kuwa rungume wayartata tayi, cikin jin dadi da kuma duk’ar dakai tace.

“Mamy nagode sosai, kuma inason yiwa Abba godiya.”

“Bakomai Jannart, taso muje to sainayi miki iso zuwa wajennasa ko.”

Cewar Mamy tana me mik’ewa tsaye.

Ganin hakanne kuma yasa Jannart itama mik’ewa tsaye, tabi bayan Mamyn, Yayinda tabar wayar nata awajen Ramadan, wanda tuni harya cirota ya kunna, domin shikansa wayar tayi masa kyau. 

Mamy kuwa ahankali ta murd’a handle din kofar falon Abban, tare dasa kanta ciki, hakanne kuma yasa Jannart dake biye da ita, itama ta shiga bakinta dauke da sallama. 

Abba dake zaune kuwa, ganinsu ne yasashi fad’ad’a fari’arsa, cikin sakin fuska yace.

“A’a Jannart.”

Murmushi Jannart din tayi, tare da k’arasowa dan nesa da Abban, ta durk’usa tare da zube guiwowinta ak’asa, kanta ta duk’ar k’asa, cikin muryar dake nuna girmamawarta agaresa tace.

“Abba naga waya,  nagode sosai, Allah ya kara budi da arziki, ya jikan magabata.”

“Ameen summa Ameen Jannart, idan kina buk’atar wani abu ki sanarwa Mamynku, kinji kada kiji nauyi ko kunyarmu, muba iya surukanki bane kawai mu matsayin iyaye muke a gareku.”

Abban ya amsa, yana murmushi.

Itama Jannart din murmushi tayi, tare da mik’ewa cikin sakin fuska, ta fice daga cikin dakin.

Direct falo ta dawo, zama tayi akan sofa, tare da karb’an wayan nata ta soma dud dubawa.

Sosai wayar tayi mata kyau, musamman da colourn wayan ya kasance bak’i. 

Hira suka dan tab’a dasu Ramadan, din kafun daga bisani ta tashi ta shiga ciki.

 Kasancewar tana danjin gajiya ajikinta ne kuma yasa, kaitsaye toilet ta wuce tayi wanka.  

Bayan ta fito ne kuma ta shafa, daya daga cikin mayukan da Mamy ta seyo mata, tare da binjikinta da Body spray mai dadin kamshi. 

Direct wardrobe dinta ta bud’e, daya daga cikin dogin rigunan da Mamyn suka sayo mata ta saka ajikinta, kamar kuwa tun can dominta akayi rigar, saboda yanda rigar ta zauna mata d’as ajiki.

Dai-dai lokacin kuwa aka soma kiraye kirayen sallan la’asar, kasancewar kuma tayi alwala tun acikin toilet shiyasa kawai hijab dinta ta zura tare

da tada sallan, bayan ta idar ne kuma ta kwanta.

Acan cikin gidan kuwa Rayyern tunda ya shiga daki baifito ba, sai yanzu da yaje yayi sallan la’asar, still kuma sake dawowa gidan yayi, tare da komawa daki yayi kwanciyarsa, kasancewar yau din weekend ne shiyasa yakeson morewa hutunsa. 

Su Ramadan kuwa Koda sukayi sallan la’asar, cikin gari suka kutsa shida Riyyam. 

Haka dai sukayi wunin wannan ranar.

Mamy na mai jan Jannart a jiki sosai, ba laifi kuma ta ɗan sake.

             Washegari

Acan gidan Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, tashin hankali kam sun shigesa k’arara sun wuni sun kwana cikinsa, musamman awajen Alhaji Idi Sale Dakata, dako zaman kirki ya kasa yi, hankalinsa amatukar tashe yake, badon komai ba kuwa, face sanin da yayi cewar, b’acewar Jannart babban tashin hankalinsu ne, haka kuma kaman wani kalubale ne dake fuskantarsu, wanda ba zasu tab’a iya tsaidashi ba kwana yayi baiyi bacciba a wannan daren.

Mom kuwa tayi hawaye har saida idanunta suka bushe, gaba daya ta shiga damuwar rashin Ganin Jannart din, Yayinda duk wani zarginta ta d’aurashi akan Junaid, saboda sanin da tayi cewa, ba k’aramin aikinsa bane sace Jannart din.

Abdull ma gaba daya haka yayi wuni jiya ya kwana  yau kuwa tun da safe ya gayawa Yah Azeez abin da ake ciki.

Abinda yayi masifar tada hankalin Azeez kenan.  saboda b’atan ƙanaartasa ya daki zuciyarsa sosai.  

Haka kuma yau ɗin ma gari na wayewa Alhaji Idi Sale Dakata ya fita, da kansa ya dinga zaga gari waiko zai  samu wani labari amma Ina.

Daga karshe dai haka ya dawo gida zuciyarsa duk ba dadi. 

Har dare kuwa babu wani labari akan Jannart din.

Yayinda Barrister Kabir kuwa ya buwayesu da zurya da tashin hankali.

Acan gidansu Rayyern kuwa ana idar da sallan isha’i   Ramadan da Riyyam suke dawowa gida.

Mamy kuwa bayan ta kammala dinner, har d’aki ta kaiwa Jannart nata zaune ta sameta bisa sallaya tasa hannunta duka biyu ta tallabe h…!

Habarta tana lallatsa wayarta.

Cikin sauri ta ɗago kanta jin motsin Mamy.

Ita kuwa Mamy ajiye mata tray’n tayi gefenta tare da cewa.

“Ki ajeyi wayarnan haka, kizo kici abinci.

Ga tea kisha da zafinsa mgnin wannan sanyin da akeyi mana”.

Cikin girmamawa tace.

“Toh Mamy sannu ngd”.

Kai ta jinjina kana juya ta fita.

Kasancewar kuma yanayin garin ana  busa sanyi mai masifar ratsa jikine, yasa su Mamyn ma basu wani jima afalon ba, suna kammala diner din, kowannensu ya wuce dakinsa.

Rayyern kuwa dama ko saukowa k’asan baiyi ba, abincinsa ma sai Mamy ne tasa Riyyam ya Kai masa daga nan ya zauna gefenshi yanata zuba mishi surutu. 

Nan ma baiwani ci sosai ba sabida ya rigada yaci Chocolate ɗinsa shi yasa Riyyam din ya fita dashi. 

Duk da cewar yanajin bacci kuwa, bai kwanta ba harsaida ya motsa jikinsa, na kusan tsaeon 1 hour kafun ya kwanta.

Cikin yan mintuna kadan kuwa bacci ya daukesa, saboda duk garin ya dauki sanyi sosai.

Acan b’angaren Jannart ma, da wuri ta kwanta, tare da shigewa cikin lallausan blanket dinta, tana rik’e da wayarta kuwa bacci ya dauke ta.

Washegari.

Kamar kullum kuma Koda yaushe, dukansu atare suka dawo daga sallan Asuba.

Inda suna shigowa kuwa Mamy ta tarbesu da hadin Coffee dinta, mai dadi.

Bayan sunsha ne kuma duk suka miƙe  suka wuce sama dan sake kwanciya, Mamy kuwa kaitsaye kitchine ta wuce. 

Tare da soma shirye shiryen had’a musu breakfast. 

Tana cikin aikin nata ne kuma, Jannart ta fito zuwa main falon.

Sanye take da Hijab ajikinta, Jin motsi acikin kitchine dinne kuma yasa ta, nufar kitchine din kaitsaye saboda tana da tabbacin cewa Mamy ne.

Mamy kuwa dake tsaye, Jin alaman tafiyan mutum ne yasa ta Juyowa da sauri,  dai-dai lokacin ne kuma Jannart din ta k’araso bakin kofar kitchine din riƙe da mug din coffee da Mamy ta kai mata.

Murmushi Mamy tayi, tare da fadada fara’ar dake kan fuskarta, atausashe tace.

“A’a Jannart da sanyin safiyar nan me kika fito yi?.”

Kai Jannart din ta jinjina, cikin girmamawa kuwa tace.

“Mamy aikin zamuyi.”

“Da wannan sanyin, a jeki kwanta?”

Mamyn ta fada tana murmushi.

“A’a Mamy aiki da yawa ai bari na tayaki.”

Jannart din ta fad’a tana me k’arasa shigowa cikin kitchine din.

“A’a Jannart ki bar aikin nan ba damuwa, jekiyi kwanciyarki kinga ana sanyi, kuma yau dinma bawani aiki mai wahala zanyi ba, abinci mai sauki zan dafa.”

Mamyn ta fada mata haka cikin kulawa.

Hakanne kuma yasa Jannart din ta d’an langwabar da kai, murya asanyaye tace.

“Dan Allah Mamy ki bari na tayaki, banajin bacci shiyasa.”

Murmushi Mamyn tayi, Ganin kuma Jannart din ta dage ne yasa ta, matsawa gefe tare da cewa.

“To ga Irish patatoes nan ki fere, ni bari na k’arasa had’a wannan farfesun, Idan kika gama saiki soya mana chips ko.”

Kai Jannart din ta jinjina, alaman to, Cikin nutsuwa kuma ta d’auki abun fere dankalin ta somayi.

Cikin abunda bai wuce mintuna kad’an ba kuwa ta kammala, da kanta ta kunna gas, tare da soma soya chips din, suna dan hira da Mamy harta gama.

Wanda zuwa lokacin tuni Mamy ta gama had’a ferfesun, harta fara soya kidney sauce din da za’aci chips din dashi.

Ganin hakane kuma yasa Jannart, had’a musu had’adden sandwich, sai kuma green apple juice wanda acikin mintuna 15 kwata kwata ta kammala had’a shi. 

Sosai Mamy taji wani irin farinciki ya cika mata zuciya, musamman saboda yanda taga Jannart din na taimaka mata da ayyuka batare da ganda ba, aikin da zatayi acikin 2hour sai gashi, da taimakon Jannart sunyi shi, acikin awa daya da yan mintuna.

Bayan sun kammala had’a breakfast dinne kuma, Jannart da kanta ta kwashe abincin ta jeresu akan dining table, Yayinda Mamy kuwa ta kwashi food flask din da aka sawa Abba abincin aciki Ta kai masa zuwa sashinsa,  sai kuma nasu Baba Maud’o, wanda sai gari yayi haske za’a Kai musu. 

Duk wani abu da suka b’ata kuwa saida Jannart din ta wanke, bayan ta gama kimtsa komai ne kuma Mamy ta kalleta, murya atausashe tace.

“Allah Ya miki albarka Jannart, yanzu kije kiyi wanka saiki zo muyi breakfast ko.” 

“To Mamy.”

Jannart din ta amsa, kana anutse ta juya ta nufi part dinta. 

Koda ta shiga cikin bedroom dinta, kayan dake jikinta ta cire, wani sabon towel ta daura, kaitsaye kuma ta shige Bathroom tayi wanka da ruwa mai ɗan karen ɗumi sabida yanayin ciwonta yafi tashi a irin lokutan sanyin haka. 

Koda ta fito feshe jikinta tayi da turare mai sanyin kamshi, bayan ta murzawa jikinta mai ne kuma, ta shafawa fuskarta powder, sai kuma wani brown  lipstick da ta gogashi sama sama akan labb’anta, dama kuma ba al’adarta bane yawan kwalliya.

Wani dogon riga mai kaman Kimono ta zaro, tare da sakawa ajikinta, d’as rigan ya mata ajiki, kasancewarsa Maroon color kuma shiya kara bayyana kyau da hasken fatarta.

Dogon gashinta ta tubke atsakiyar kanta, tare kuma da d’aukan mayafin rigar ta yafa akanta, wanda ya sauko harzuwa kan kirjinta. 

Alokacin da ta kalli madubi kuwa, murmushi tayi saboda ita kanta tasan tayi kyau.

Agogo ta kalla, wanda yake nuna mata karfe Takwas harda wasu mintuna. 

Wasu lallausan takalma flat ta saka ak’afafunta,  cikin yanayinta na nutsuwa kuma ta bud’e kofar dakin ta fice wayarta na rik’e a hannunta. 

Kaitsaye Falon Mamyn ta fito, fitowar nata kuwa yayi dai-dai da fitowar su Ramadan da Riyyam.

Riyyam ne ya kalleta tare da k’arasowa, inda take Cikin sakin fuska yace.

“Barka da safiya my kyakkyawar Aunty na, gaskiya Hamma Rayyern yayi dace, Yah Allah Nima kabani kyakkyawa mata.”

 Lallausan murmushi ta sakar masa, tare da yin k’asa da kanta, cikin dakekkiyar murya tace.

“Barka da safiya Tiktoker Riyyam.”

Dariya Riyyam din yayi, Yayinda Ramadan da sai yanzu yake k’arasowa, shima fadada fara’ar dake kan fuskarsa yayi, cikin kulawa yace.

“Barka da safiya Aunty Jannart fatan kin tashi lafiya.”

D’agowa tayi fuskarta dauke da murmushi ta kalli Ramadan din, kamar yanda yayi mata magana a mutunce kuwa haka itama ta mayar masa.

Dai-dai lokacin kuwa Mamy ta fito daga sashin Abba.

Riyyam kuwa Wayarsa ya zaro, tare da Kallon Jannart din, cikin kulawa yace.

“Hamma Ramadan Aunty Jannart kuzo na d’aga mana selfie, Mamy kema ki shigo.”

Murmushi duk sukayi, Mamy kuwa Kanta ta girgiza, fuskarta dauke da dariya tace.

“A’a nikam kudai kuyi selfien ku.”

Tsayuwa sukayi inda suka saka, Jannart din atsakiyarsu,  Riyyam din kuwa shiya d’aga musu wayar yayi musu selfie, har kala uku. 

Bayan sun gama ne kuma Mamy tace.

“To saiku zo muyi breakfast ko.”

Kai suka jinjina dukansu, tare da karasawa dining table din suka zazzauna, Jannart da kanta tayi saving nasu.

Bayan sun fara cin abincinne kuma, Riyyam-nsra ya ciro Wayarsa tare, da turawa Mamynsa hotunansu da sukayi yanzun, Ganin Mammyn bata online ne kuma yasa shi danna voice,  batare kuma daya gama cinye abincin dake bakinsa ba yace 

“Good morning Mammyna, ga amaryar Hamma Rayyern dina kiganta, she’s so cute Mammy kisa mata al’barka, kiyi musu addu’a’n zaman lafiya da samun yan tagwayen yara.”

Yana gama fadin haka yayi sending voice din, tare da ajiye wayartasa ya cigaba da cin abinci.

Mamy da Ramadan kuwa murmushi kawai sukayi, saboda sun San yanda Riyyam yake matukar kaunar mahaifiyarsa sun fahimci duk motsinshi sai ya sanar mata.

Jannart kuwa jin abunda Riyyam din ya fad’ane yasa ta sunkuyar da Kanta k’asa, acikin zuciyarta kuwa ta maimaita abunda Riyyam din ya fad’a.

“Amaryar Hamma Rayyern kiyi musu addu’a’n samun yan tagwaye.”

Ya tabbata kenan cewa, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne mijinta. 

Saboda shine kad’ai Rayyern din da tasani acikin gidan, shi dinne kuma wanda suke cewa Hamma Rayyern shine kuma mutumin da baimin mgn in na gaidashi ma bai amsawa ko yaushe fuskarshi kamar ta Yah Junaid. 

 Share duk wani tunanin dake zuciyar nata tayi, tare da ci gaba da tsakalan abincinta tana ci.

Mamy kuwa ganin Rayyern baisauko ba, yasa tayin tunanin ko bacci yakeyi, shiyasa bata tura ankirasa ba.

Atsanake haka suka kammala breakfast din, dukansu kuma cikin falon suka dawo suka zauna.

Inda Riyyam-nsra keta basu labarai kala-kala, wanda duk mafi yawansu  akan TIKTOK ne.

Acan b’angaren Abba kuwa yana kammala yin breakfast d’insa, ya kimtsa tare da bud’e kofar falon nasa ta bangaren baya ya fice, hannunsa rike da key din mota, saboda akwai inda zasuje da Baba Maud’o.

Fitowarsa compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da shigowar motar Barrister Kabir. 

Ganin motar Barrister Kabir dinne kuma, yasa Abba sakin murmushi, tare da dan tsayawa.

Barrister Kabir kuwa yana gama dai-dai-ta parking din motar ya bud’e murfin ya fito, Fuskarsa dauke da murmushi.

Karasowa yayi tare da bawa Abban Hannu suka gaisa.

Cikin sakin fuska Abban yace.

“Barrister ashe kana tafe, sannu da zuwa, mu isa daga ciki.”

Kai Barrister Kabir ya jinjina, tare da cewa.

“To bari na gaisa da Baba Maud’o.”

Ya k’are maganan yana me mik’awa Baba Maud’o hannu sukayi musabaha.

Bayan sun gaisa da Baba Maud’on ne kuma Abba Yayi masa jagora zuwa cikin gidan.

Ta babban kofar falon kuwa suka shiga,  wanda dai-dai lokacin kuwa su Jannart duk suna zaune akan sofa, ita dasu Ramadan.

Da Sallama abakinsu suka kutsa Kai Cikin falon.

  Jin sautin muryar Barrister Kabir ne kuma yasa Jannart saurin d’ago kanta.

Ganinsa dinne kuma yasa  Murmushin jin dadi bayyana kan fuskarta.

Shima Barrister Kabir din murmushi yayi, tare da karasowa cikin falon ya zauna.

Mamy kuwa da murmushi akan Fuskarta tace.

“Barrister sannu da zuwa”.

Cikin jin daɗi ganin yadda Jannart ta dan sake a cikinsu yace.

“Barka dai Hajia ya bakuwarku?”.

Murmushi Mamy ta ɗanyi tare da cewa.

“A’a ai mu bamu da bakuwa, mu duk nan yan gidane”.

Murmushi sukayi baki ɗayansu.

Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli  Jannart daketa murmushi tace.

“Jannart kawo masa ruwa ko.”

Mik’ewa Jannart din tayi, Tana murmushi, taje ta kawo masa ruwa da kuma ragowan drinks din da ta had’a, harma da sandwich din.

“Abbana sannu da zuwa.”

Ta fad’a cikin tsananin farin cikin da ta samu kanta aciki, tare kuma da ajiye masa dan tray din da ta Hado ruwan agabansa.

“Yauwa Jannart sannu.”

Barrister Kabir din ya amsa yana murmushi, tare da juyawa suka gaisa da Mamy.

Ramadan da Riyyam ne kuma suka gaidashi, fuska asake ya amsa musu.

Jannart kuwa sabida tsananin jin dadin ganinsa, dan matsowa kusa dashi tayi, tare da manna kanta jinin hannun kujerar da yake zaune a kai, cikin yanayin  rauni tace.

“Abba Ina kwana.”

Murmushi Barrister Kabir din, yayi cikin jin dadin yanda ya ganta yace.

“Lafiya k’alau Jannatuwa, ya kwanan bak’unta.”

Kanta tad’an sunkuyar kasa, fuskarta dauke da dan murmushi tace.

“Alhamdulillah Abba, yasu Aunty Dijat Hafeez,da Hafeeza”.

“Alhamdulillah suna lfy”.

Ya bata amsa yana kallonta.

Cikin nitsuwa tace.

“Ayya Abba da kazo min da Hafeeza.” 

Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da dubanta yace.

“Uhummm Jannart kenan, waya gaya miki yanzu, bayanni akwai wanda zai na kawo miki ziyara.”

Fuskarta ta dan shagwabe, cikin sanyi tace.

“Ayya Abba yanzu har Aunty Dijat dasu Hafeez babu mai zuwa, ba wanda zaizo wajena kenan.” 

Kai Abbansu Rayyern ya jinjina tare da cewa.

“Shima ai zamu hanashi zuwa sai naga kin saki jikinki kin dena zama kina tagumi da zubda hawaye”.

Da sauri tace.

“Abba na dena”.

Yar dariya sukayi kana

Barrister Kabir yace.

“Ato kin dai ji kam ko”.

Turo dan karamin bakinta gaba tayi, wanda hakan yasa Mamy, Ramadan da kuma Riyyam duk sukayi murmushi.

Adai-dai lokacin kuwa Rayyern wanda fitowarsa  daga part d’insa kenan, ya soma saukowa daga kan steps din,  cikin shigar wani lallausan yadi mai kalan mobile blue mai masifar taushi da sheki  wanda akayi masa dinkin half jamfa da kuma, wando pencil, sosai kayan sukayi masa masifar kyau yanayin kalarsu ya kara hasko farar fatarshi ta fito ras, 

Hular damanga farace a amsa mai ratsin Nobel blue ɗin.

 Yayinda kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa ke zuba sheki har wani dauke ido yakeyi.

Sai takalmin toms Noble blue dake kamarsa.

Kamshi kawai yake zubawa, yanayin yanda yake takun nasa kuwa cikin dan sassarfa alamun sauri yakeyi. 

Yayi kyau matuk’a, Daddaɗan kamshi da kuma jin sautin takusa ne kuma yasa, duk suka kalli steps din.

Dai-dai lokacin kuwa ya gama sauk’owa.

 Ganin Barriter Kabir da yayi ne kuma, yasa shi ɗan yamutsa muskarshi.

“Kai wannan menne irin mutum ne mai masifar nacin tsiya mutun kamar maye!. 

Wannan jaraba har ina, toh yanzu kuma Meya kawoshi da sanyin safiyar nan, kamar mai binmu bashi.”

Yayi mgnar zuci tare da kwaɓe fuska yana mai k’arasowa cikin falon.

D’an rusunar da kanshi yayi, cikin naɗe murya can ƙasa yace.

“Barka da zuwa Barrister.”

“Yauwa Barka Dr. Rayyern.”

Barrister Kabir din ya amsa masa, cikin sakin fuska.

Rayyern din kuwa dan matsawa gefe yayi, tare da zama akan kujera dake gefen Ramadan.

Ganin hakanne kuma yasa Abba kallonsa, cikin kulawa yace.

“Rayyern fita zakayi ne.”

“Eh Abba”.

Ya bashi amsa a takaici.

Cikin tsaresa da ido Abba yace.

“Ina zakaje”.

Ya ƙare tambayar da alamun son cikekken bayani ina zaije me kuma zaiyi.

Hannunshi ya ɗan d’ago.

Tare da saidashi kan wuyanshi.

Ya ɗan shafa wuyanshi har zuwa kan ƙeyarsa kana a hankali yace.

“Inason zanje company ne, saboda P.A yamin waya, wai akwai wani inji da ba’a gane kansa ba,  like dai baya aikin daya dace kana Engineer bello yana can yana jirana shima.”

Kai Abban ya jinjina,  kana cikin gamsuwa yace.

“To Allah Ya bada sa’a.” 

Da “Ameen.” Ya Amsa.

Barrister Kabir kuwa, ledan dake hannunsa ya mik’awa Jannart dake zaune akasa, cikin kulawa yace.

“Jannart ga waya nan na sayo miki, akwai new sim acikinsa, bayan number na kuma bansa miki numbern kowa ba, sannan kada ki fara amfani da laptop dinki yanzu, kina dai charging nasa amma kada ki yi using dashi,domin  hakan  zai taimaka wajen gujewa duk wani shaida.”

Karb’an ledan da yake mik’o mata din tayi, cikin jin dadi tace.

“Nagode sosai Abba Kabir Allah ya kara budi.

 Amma fa jiya Abba ma ya sayamin sabuwar waya.”

Ta kare maganan tana meyi masa nuni, da Wayar dake hannunta.

Barrister Kabir din kuwa murmushi, yayi cikin jin dadi yace.

“Masha Allah waya tayi kyau sosai, Allah yasanya al’khairi ya kuma saka da alkhairin.”

Da “Ameen.” Duk suka amsa, saidai banda Rayyern wanda ya kawar da kansa gefe yana kallon Riyyam-nsra daketa lallatsa woya ya kifa kai har kamar zai hade goshinsa da wayar haka yasa ya tsareshi da ido yana nazartarsa.

 Dan ko kasa inda take dinma bai kalla ba sai dai yana jin amon muryarta.

Barrister Kabir kuwa Mikewa tsaye, yayi tare da Kallon Jannart din, cikin tausasa murya yace.

“To Jannart ni zan wuce, dama sakon da nazo kawo miki kenan.”

Murmushi Jannart din tayi, cikin sanyi tace.

“Abba ka gaida gida, ka gaishemin da Aunty Dijat dasu Hafeeza.”

“Zasuji Insha Allah.” Abban ya fad’a, tare da juyawa yayiwa Mamy sallama.

A gaida gida Mamyn tayi masa, sannan suka fice shida Abba.

Ganin hakanne kuma Yasa Rayyern ma mik’ewa tsaye.

“Rayyern katsaya kayi breakfast tukun kafun ka fita, gacan abinci akan dining.”

Cewar Mamy tana me kallonsa.

Fuskarsa ya d’an ya mutsa, tare da Kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa, adan kasalance yace.

“Mamy banajin yunwa sosai, kuma Idan na  tsaya break zan makara, saina dawo kawai ki ajiyemin lunch.”

Ya k’are maganan yana me nufar hanyar fita daga falon.

Wanda hakan yasa Mamy da Ramadan suka Bishi da kallo,  Mamy kuwa har cikin ranta tana mamakin, yanda Rayyern din yake tafiyar da rayuwarsa, gaba daya sam  cin abinci bai damesa ba sai dai wasu lokuta isasshen lokacin zaman cinnema yake rasawa, shiyasa idan ya tara yunwar tofa in ya samu ya ya zauna zaici da dama. 

Rayyern kuwa Koda ya fito compound din gidan, ya samu tuni harsu Abba da Baba Maud’o sun tafi, Yayinda shima Barrister Kabir Yayi nasa tafiyar.

Motarsa ya shiga, Yayinda Hadi ya jasa suka fice daga Cikin gidan.

Acan falo kuwa, har Rayyern din ya fice Jannart bata iya sake dago Kai ta kalleshi ba, saboda tun Kallon farko da tayi masa, taji zuciyarta na bugawa, wanda kuma batasan dalilin hakan ba.

Bayan fitan nasa ne kuma ta d’ago kanta tare da Kallon Mamy, ad’an ladabce tace.

“Mamy yau me zamu dafa da rana.”

Murmushi Mamyn tayi, kana atausashe tace.

“A’a Jannart yau kam kihuta, ina nan zanyi komai, basai kin wahalar da kanki ba wannan fa aiki nane!!!.”

“Mamy ba wahalar da kai bane zanyi, na saba ko agida ma duk ranar da babu aiki Ina taya Momy duk wasu aikace-aikace  gida, Dan Allah Mamy ki bari Ina tayaki ki dena cewa na bari.”

Jannart din ta fad’a cikin tausasawa.

Hakanne kuwa yasa Mamy jin sanyi acikin zuciyarta, saboda tasan Itakam tayi sa’ar suruka.

“Shikenan Jannart babu damuwa, na baki wuk’a da nama ki dafa mana duk abunda kikeso.”

Mamyn ta fad’a cikin sakin rai.

Riyyam nsra kuwa, cikin dokin cin abincin Auntyn tasa yace.

“Yauwa Aunty Jannart muje kitchine din, ni yau da kaina ma zantayaki aikin, amma mezaki dafa mana me dadi haka?”

Murmushi Jannart din tayi, tare da cewa.

“Muje zaka gani.” Yanayin yanda tayi maganan tana me mikewa tsaye ne, yasa Riyyam din rufa mata baya suka shiga kitchine.

Shida kansa yayi mata wanke wanke, Yayinda ita kuwa tayi greetting kwawa, saboda abunda ta tsara zata dafa musu shine.

Coconut rice, and onion sauce, sai kuma gas meat mai kayan kamshi, da salad cream,  ab’angaren drinks kuma, Banana Milk shake zatayi musu.

Anutse ta fara aikinta, Yayinda Riyyam keta yi mata hira, daga gefe guda kuwa yana tayata da y’an wasu ayyukan, kama daga kan yanke yanke zuwa yan kananun abubuwa masu sauk’i dai. 

Haka dai sukayi aikin cikin nutsuwa, almost 1hour kuwa ta kammala komai, tare da jeresu akan dining table.

Gaba d’aya gidan kuwa haka ya gauraye da kamshin girkinta.

Bayan sun kammala jere komai a dining table dinne kuma, ta kunna boner tare dasa turaren wuta mai dadin kamshi.

Mamy kanta ta yaba da aikin Jannart din, bayan sunyi sallan azahar ne kuma, suka zo kan dining table din sukaci abincin.

Saidai kuma Jannart din bata wani ci abincin sosai ba, ayanda Mamy ta fahimta kuwa shine, Jannart din irin Rayyern ce, kwata kwata basu dauki cin abinci serious ba sai dai tasan shi Rayyern in ya zaunawa abincin bai mishi da wasa ko dan yakan dade baici bane, ta lura ita kuma Jannart irin mutanen ne da zasuci kaɗan yanzu anjima su kuma cin kaɗan.

Bayan sun kammala cin abincinne kuma suka dawo falo,  hira suka Dan tab’a, lokacin da Ramadan da Riyyam suka fita yawo ne kuma, Jannart ta tashi ta koma side dinta, tana kwanciya afalonta kuwa bacci  ya dauke ta.

A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa.

A gajiye ya dawo gida, daga Tashar Arewa 24 TV da yaje, yanzu ya samu MD da kansa ya mishi bayanin ɓacewar Jannart da kuma hukuma da suka shiga lamarin kana yasa gidajen Rediyo su cekinta su kuma ya bawa gidan tv nasu cekiyar gaggawa.

Daga nan kuma asibitin Dr Lukman ya wuce inda anan sukayi tattaunawa mai yawa kana ya nufo gida.

Da sauri Mom tabi bayanshi.

Tana cewa.

“Alhaji anji lbrin Jannart kuwa?”.

Da sauri ta matsoshi ganin yadda ya dafe kanshi da hannaye bibbiyu yana mai jujjuya kanshi.

Kana ya tafi lu alamun zai fadi.

Cikin tsananin tashin hankali da kidima Mom ta saki ihu tare da isowa gareshi ta tallabeshi murya na rawa take kwarmawa Abdul kira.

da gudu Abdul ya shigo cikin tashin hankali tace.

“Abdul kira min Barrister Kabir Abbanku kace Daddynku ba lfy”.

Kafin ta ƙare mgnar kuma Alhaji idi Saleh Dakata ya sake gaba ɗaya naushin ya jata suka tafi kasa bisa carpet.

Ganin haka ne yasa Abdul gigicewa tare da zaro wayarsa ya kira Barrister Kabir.

Wanda shi kuma lokacin ya fito daga gida shi kenan.

Koda Abdul ya gaya masa abinda ke faruwa.

A firgici ya dauko ya wuce asibitin Dr Sajo ya dauko shi.

A gidan Alhaji Idi Saleh Dakata’n kuwa, suna cikin gigin suka jiyo muryar Dr Lukman yana sallama hakane yasa Mom sakin dogon numfashi tare da cewa.

“Dr ka shigo, kayi sauri shigo ka taimaka mana Alhaji zai fadi”.

Jin hakane yasa Dr Lukman kutsa kai cikin main falon nasu da hanzarin.

Daga nan shida Abdul suka tallabeshi suka a mota suka wuce asibitin Dr Lukman din.

Suna tafiya ba jimawa.

Barrister Kabir da Dr Sajo suka iso.

Bayan Ashiru ya musu bayanine suka nifi asibitin Dr Lukman ɗin.

A nan gidansu Rayyern kuwa.

Bacci Jannart tayi sosai dan Koda ta tashi tayi sallan la’asar sake komawa tayi ta kwanta.

Ahaka dai har magriba.

9:30 pm dai-dai ya shigo gidan, wanda kuma tun fitan da yayi da safe sai yanzu yake shigowa.

Da sallama abakinsa ya tura kofar main falon ya shigo.

 Jin da yayi ko ina shiru babu alaman motsin kowa ne, yasa kaitsaye ya wuce sama, saboda yasan zuwa yanzu su Mamyn nasa sunyi bacci.

Yana haurawa saman kuwa, anan cikin falonsu ya samu Ramadan da Riyyam,  ko wannensu rungume da waya ba abunda sukeyi sai chatting.

Kana ga TV a kunne tashar Arewa 24 TV.

Yayinda su basuma san me akeyi a TV’n ba.

A hankali ya ɗan juyo ya kalli TV’n sabida ganin program ɗin da Jannart tayi dashi ake haskawa.

Idanunshi ya zubawa rubutun dake tafiya kasan hotonsu mai motsin da yake fuskar TV’n.

*Daya daga cikin ma’aikatan wannan ma’aikata Mai gabatar da shirin Baƙon mako mai suna Jannart idi Saleh Dakata ta bata tun daren jumma’a,  kana har yau babu ita babu lbrin ta, a madadin tashar Arewa 24 TV muna cekinta Tata ga duk wanda Allah yasa ya ganta ko yaji lbrinta, ya taimaka ya nemi ɗaya daga cikin wadannan numbers din… akwai tukuici mai girma ga duk wanda ya kawo ta ko lbrinta kimanin Naira million 5. Muna addu’a Allah ya baiyana ta ya kuma bawa mahaifinta lfyar jikinsa wanda sanadin batanta ya tada masa ciwonsa*

Wani irin numfashin ya fesar a hankali tare da mai-maita karanta rubutun a karo na barkatai.

Can cikin zuciyarsa yake nazari.

“Tabbas akwai gadar zaren da ake sakawa, wanda ake neman mai ruftawa a ciki.

Dole suna da manufa a kaina.

Amman manufar Barrister Kabir tafi ta kowa girmama a kaina, tabbas ba haka kawai ya zaɓeni ya lika min wannan mayataccen aurenba, nasani haƙƙun nasan akwai wata boyeyyiyar manufa da niyarsa ta liƙamin auren ya kawo diyarsu ya ajiye mana a cikin gida.”

Idonshi ya lumshe tare da buɗe kana yaci gaba da nazari.

“Wani wasane suke son bugawa dani, yarsu ta zamo yar leken asirinsu kenan itace zata basu duk wata damar cimma nasarar turani kan gadar zaren da suke saƙamin ko meye.

Itace mai iya buɗe musu kofa ta su shigo rayuwata.

Meyasa Abba na bai gane hakabanba ya akayi Abba na yayi saurin yarda dasu?”.

Numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe tare da yin kwaffa.

Wanda sanadin hakane su Ramadan suka gane ya shigo.

Kallonsu kawai yayi tare da amsa sannu da dawowan da sukeyi masa.

Idonshi ya kuma maida kan TV inda ake haska fuskarsa data Jannart.

Batare daya ce musu komai ba, ya wuce zuwa dakinsa.

Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare ci gaba da nazari.

“Me Barrister Kabir yake nufi dani? Alhaji idi Saleh Dakata dai ɗan uwansa ne uwa ɗaya uba ɗaya.

Kana ita kuma wannan Jalila ne ko jalilu ne, yarsa ce ta cikinsa.

Haƙƙun Barrister Kabir medani tsanin hawa yake son yi!.”

A hankali ya tura ƙofar  shiga toilet.

A fili yace.

“Me yasa Abbana ya yarda dashi, ya akayi yayi saurin gamsuwa dashi.

Bayan kuma shine ya dauramu kan turbar kebanta kai da mutane da gudunsu da rashin yarda dasu.

Sanadin haka muka taso ba abokai ba kawaye bama sakin jiki da kowa, daga ni har Ramadan, sabida horaswar Abbanmu ta gudun mu’amala da mutane,

Yasha cemin.

Rayyern ɗan adam abin tsorone kada ka yarda da kowa, mutun duhun darene Allah kadai ke saninsa!

To ya akayi yayi saurin yarda da Barrister Kabir?

Tabbas shima Abba na akwai manufar yardar sa”.

A hankali ya ɗago ƙafarsa ta hagu ya sa cikin Bathroom din.

Hannunshi duka biyu yasa ya matse kanshi da ƙarfi.

Dan yadda yakejin kansa na jujjuyawa nazarurrukansu na hautsinewa suna haɗe zaren suna curkudeshi.

  Duk da azabebben sanyin da akeyi.

Ruwan sanyin ya sakarwa kansa.

Sabida jin kan nashi ya fara sarawar.

Bayan ya fito ne kuma, ya shirya kansa cikin wasu tattausun kayan bacci.

Wondon iya guiwa rigar irin mai hular nan.

Fridge d’insa dake cike da kayan ciye ciye ya bud’e, Apple goran swan water da kuma ledan diary milk ya d’auko.

Tare da komawa kan gadonsa ya zauna cikin sanyi yace.

“Ta yaya zan yarda da ita, a wani sashin ma zan ajiyeta bayan nasan ita ɗin makamin magautanane sun turora cikin rayuwata ne dan cin nasarar kansu a kaina.

Meyasa Abba na bai fahimci hakaba.

Itama da mugun nufinta a ranta fa, iyayenta zatayiwa aiki”.

Yayi mgnar yana mai ajiye Jannart a sashin da yake ajiye magautansa a cikin zuciyarsa da rayuwarsa da waɗanda yake zargi.

A hankali ya jujjuya kansa.

Kana ya ɗan gatsi apple din ya soma ci bayan ya gama ne kuma, ya  daura chocolate d’insa da ruwa akai.

Numfashi ya ɗan fesar 

Kana ya kwanta yana mai nazari.

 A nan asibitin Dr Lukman kuwa.

Barrister Kabir ne da Mom ke zaune gaban table ɗin Dr Lukman.

“BP’nsa ne ya hau sama sosai, sabida tashin hankali rashin yarsa.

Kana kuma rashin baccin da baya samun yi, sai nazari da damuwa yasa zuciyarsa ta kumbura.”

Dr Lukman ya ƙare mgnar yana mai yin ƙasa da idonshi sabida wani irin tsareshi da ido da Barrister Kabir yayi.

Cikin zubda hawaye Mom tace.

“Innallahi wa innailaihi rajiun, zuciyarsa kuma ta kumbura?”.

Cikin murje ido yace.

“Hakkun kuwa, sabida damuwa tayi mishi yawa, Jannart ta bata kana shima Junaid yana hannun hukuma, wanda kuma ƙaninsa uwa ɗaya uba ɗaya yasa aka kama ɗan nashi da wanne abu ɗaya zaiji?”.

Cikin haɗe fuska Barrister Kabir yace.

“Shine yace ma ni na kai Junaid hannun hukuma?”.

Da sauri ya girgiza kai alamun a’a

Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.

“Toh ka tsaya iya matsayinka, ka tabbatar da abu kafin kayi mgn”.

Yana faɗin haka ya mike ya fita.

Dakin da aka kwantar da Daddy ya nufa a bakin ƙofar shigowa yayi kiciɓis da Dr Sajo.

Hannunshi Dr Sajo yaja kana suka juya suka nufi parking lot.

Cikin motar Dr Sajo suka shiga.

Wani dogon numfashi Dr Sajo ya sauƙe kana a nitse yace.

“Dr Mina da Dr Lukman yayi aikin duba Alhaji tare da ita, ƙanwatace cousin sister na.

Na samu duk bayanin komai a wurinta”.

Da sauri Barrister Kabir yace.

“Dan Allah menene gskyan  abun dake damun Yayana?”.

Kai Dr Sajo ya jinjina tare da yiwa Barrister Kabir duk abinda Dr Mina ta sanar masa…

A nan Office din din Dr Lukman Kuma Barrister Kabir na fita, itama Mom ta fita.

Ta koma wurin mijin nata.

Ba ji mawa Barrister Kabir ya dawo akan dole a sallami yayanshi zasu sauya asibiti.

Kuma dole haka akayi.

Aka medashi asibitin Dr Sajo.

           Washegari.

Kamar dai jiya yaudinma Jannart ce ta-taya Mamy duk wasu aikace-aikacen gida, bayan sun kammala ne kuma suka zauna suna dan tab’a hira.

Kasan cewar yau Monday ne tushen aiki.

Yasa tuni Ramadan ya tafi.

Riyyam-nsra kuma Ahmad yazo sun tafi gidan Malam Mai-nasara.

Takwas  saura kwata. Ya sauko falon.

Cikin shigar Suit red color masu masifar kyau.

Hannunsa riƙe da wayarsa yana mgn.

Cikin sauri ya kalli Mamy tare da cewa.

“Mamy na tafi”.

Kafin ma tace wani abu tuni ya nufi hanyar fita.

Kawai sai ta bishi da ido.

Har ya fita kuma sai ya juyo ya leƙe fuska ya kwaɓe tare da cewa.

“Mamy na tafi”.

Murmushi tayi dan dama tasan tabbas zai juyo muddin batace mishi.

Allah ya bada sa’a yayi muku al’baka.

Cikin sauri ya kuma cewa.

“Mamy zan tafi”.

Fuska ta tsuke tare da cewa.

“Ka dawo kayi breakfast”.

Cikin kwaɓe fuska yace.

“Mamy sai na dawo, kinga Ramadan keta kirana, wai akwai matar da aka kawo haihuwa yaƙi kuma dole sai anyi mata CS, dan Allah Mamy ce Allah ya bani Sa’a yayi min al’barka Please Mamy say something”.

Ta sani in dai yace bazai ciba ko ta matsa mishi bazaici yadda take sonba.

Hakane yasa tace.

“Toh Babana Allah ya bada sa’a ayi aiki lfy rabbil yayi maka al’barka”.

Da sauri ya juya yana mai cewa.

“Yessss Mamy Amin Amin”.

Da ido ta bishi tana murmushi tana tuno wasu abubuwa masu tarin yawa.

Jannart kuwa dake cikin Kitchen tana wonke-wonke rumtse idanunta tayi tana mai jin yadda bugun zuciyarta ke harba a duk sanda sautin muryarshi ya sauka kan kunneta.

Duk da bata hangoshi ba, ita robonta da shima tun jiya da safe zuwan Barrister Kabir nanma bataga fuskarsa ba, kuma haka yanzuma.

Sai dai yanayin alaƙarsa da mahaifiyarsa yasata jin maraicin rashin tata mahaifiyar da jin bege.

Domin a gidansu babu irin wannan tarbiyar shaukin mahaifa da Kekkyawar shaƙuwar.

Haka dai taci gaba da aiki ita da Mammynsu.

Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai, domin Jannart ta samu nutsuwa acikin gidan.

Kasancewar yau tsawon kwananta biyar kenan da zuwan ta gidan.

Akullum kuma sabonsu k’ara-k’arfi yake, da Mamy, Ramadan da kuma Riyyam, harma kuma Abba da take samun kulawa awajensa sosai ta kuma take jin daɗin zama dasu.

Takan kalli Mamy matsayin Mom da Aunty Dijat dan duka biyu ta meye mata gurbinsu.

Abba a matsayin Daddy kana Riyyam-nsra ya meye mata gurbin Abdul Ramadan kuma gurbin Yah Azeez yayinda tasa a ranta cewa wato duk inda kake a duniya sai ka samu kalubalen makiyin dan gashi nanma Rayyern ya zame mata gurbin Yah Junaid a cewarta kenan.

Acikin kuma way’annan kwanki biyar din, sau biyu tak kawai Jannart da Rayyern din suka ga juna.

Tun gaisuwar da tayi masa ranan farko kuwa, wata magana bata sake hadata dashi ba tunda bazai amsa mataba a zatonta bazata kara gaidashi ba Dan matsalar kunneta yasa bataji amsawar da yayinba.

Rayyern kuwa kasancewar yau laraba, tun sassafe ya fita, saboda akwai wasu patients da suke da appointment din ganinsa. 

Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai 2:00 pm, inda ya tsaya yayi sallan azahar d’insa a Darul Hadith Masque. 

Yanzun kuwa Shigowarsa Cikin gidan kenan, hannunsa rike da suit dinsa, ya murda handle din kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama.

Mamy dake zaune ne ta amsa masa.

Ganin kuma yanda yake da’alaman gajiya atattare dashi ne yasa ta zuba masa ido.

Shikuwa k’arasowa cikin falon yayi, tare da zama akan kujera, idanunsa ya lumshe, kana cikin sigar shagwab’a da bayyanar tarin gajiya da yunwar dake cinsa yace.

“Mamy nagaji, kuma yunwa nakeji sosai.”

Ya ƙare mgnar yana juya kwayar idanunshi da sukayi jazir.

Ido Mamy ta dan zuba mishi cikin tausayawa tace.

“Badole kaji yunwa ba Babana, kwata-kwata bakason cin abinci,  saika wuni ka kwana batare da kasa abincin kirki acikin ka ba sai kayan zaki da Fruits.”

Mamyn ta fad’i haka tana me K’are masa kallo, saboda har wani dan rama taga yayi, saboda rashin cin abincin da bayayi akai akai dan abin nashi ya karune tun zuwan Jannart gidan.

“Kazo kaci abinci.”

Mamyn ta fad’a cikin kulawa.

Shikuwa Rayyern idanunsa ya d’an bud’e akasalance yace.

“Mamy me aka dafa.”

“Coconut rice, with onion sauce, gas meat, and salad cream, sai kuma milk shake, and plaintain da kuma fish.”

Mamyn ta bashi amsa atakaice.

Fuskarsa ya d’an kwab’e, tare da rausayar da kansa gefe, cikin sanyi yace.

“Shike nan Mamy ku kullum abu ɗaya.

Kwananfa naga shi kukayi kukayi taci ba sauki”.

Da sauri tace.

“Yoh ya mana daɗi Ramadan da Riyyam-nsra sukace a sake yinshi, nima kuma naji daɗinsa”.

Cikin tarin gajiya yace.

“Mutane ayi ta sasu tsatsagar shinkafa ba sauki kamar tsuntsaye.

Gsky ni bazan ciba, 

 abu mai dan ruwa ruwa nakeso, banason abinci mai nauyi.”

Jujjuya kai Mamy tayi tare da cewa.

“To Bari ayi maka.”

ta fad’a tana me mikewa tsaye.

Shikuwa mikewa yayi, tare da cewa.

“Mamy bari naje nayi wanka, Please a gama da wuri.”

“To.” Mamyn tace masa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya haura sama.

Mamy kuwa direct falon Jannart ta nufa.

Cikin sa’a kuwa anan cikin falon ta sameta tana game a wayarta.

Ganin Mamyn ne kuma yasa ta tsaida Game din, tare da sakin murmushi tace.

“Mamy sannu da shigowa.”

“Yauwa Jannart Sannu, game kikeyi ne.”

Mamyn ta tambaya cikin kulawa.

Jannart kuwa murmushi tayi, tare da ajiye wayan, cikin girmamwa tace.

“Eh Mamy, akwai abunda zanyi miki ne?”

“Kwarai kuwa Jannart, mijinki ne ya dawo wai, yunwa yakeji kuma abu mai dan romo-romo yakeso, Dan Allah ko zaki dan shiga kitchine kisama masa abu mai sauki.” 

Mamyn ta fad’i haka cikin tausasa murya.

Jannart kuwa jin ance mijinta ne yasa ta sunkuyar da kanta k’asa, cikin wasa da y’an yatsun hannunta tace.

“To Mamy bari na dafa masa.”

“Yauwa Jannart Allah dai ya miki albarka.”

Mamyn ta fad’i hakan, tare da juyawa ta fice daga cikin dakin.

Ita kuwa Jannart a hankali ta miƙe cikin nitsuwa

 ta rufa mata baya.

Koda suka fito falon kitchine Jannart din ta wuce, tare da soma kokarin had’a masa abunda xaici.

Hearty Chicken Gnocchi soup  ta had’a masa, wanda yaji kayan had’i da milk. 

Bayan ta kammala ne kuma ta juyesa, acikin wani  Dan madaidaicin glass bowl maikyau. 

Tare kuma da had’a masa spearmint tea ta juyesa acikin wani cup mai kyau.

Wani tray na glass ta dauka tare da jere masa abincin akansu.

Anutse ta fito daga cikin kitchine.

Din tare da ajiye tray din akan dining.

Dai-dai Ta juya zata sauka akan dining table din ne, shi kuma sai gashi ya na sauk’owa, Inda ya sanja shigarsa cikin wani riga da wando masu masifar taushi farare kala-kala.

Ganinsa ne kuma yasa Mamy dake zaune afalon tace.

“Babana harka fito.”

Kansa ya jinjina tare da shafa cikinsa, ashagwabe yace.

“Eh Mamy abinci.”

Murmushi Mamyn tayi, tare da cewa.

“Abincinka is ready Jannart sa masa abinci yaci.”

Dan tasan ba karamar yunwa ke azalzakarsaba tunda yaketa damunta da yunwa-yunwa.

Ita kuwa Jannart dake kokarin komawa dakinta

Jin abunda Mamyn ta fadane yasa ta tsaya.

Shikuwa Rayyern batare ma daya kalli Inda Jannart din take ba, yaja daya daga cikin kujerun dining din ya zauna.

Jannart kuwa Kanta ta sunkuyar, tare da juyowa a hankali ta fara ta kowa atsanake ta nufi dining table din.

Isowarta kan dining dinne kuma yasa, tayi kasa da kanta kana cikin sanyin murya tace.

“Sannu da dawowa.”

“Uhum.”

Ya amsa mata atakaice tare da kawar da kansa gefe, acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.

“Kowa yayimin sannu da dawowa, amma ita sai yanzu zata wani yimin iyayi munafuka yar leken asiri.”  

Jannart kuwa plate ta d’auka, atsanake ta zuba masa.

Hearty chicken Gnocchi soup din,  wanda tana bude bowl din kamshin nama da milk din ya daki hancinsa.

Zuba masa tayi tare da tura masa plate din gabansa, kana ta ajiye masa cup na Spearmint tea din agefensa.

Juyawa tayi atsanake ta bar wajen.

Shikuwa Rayyern numfashin ya ɗan shaƙar spoon ya dauka, ya ɗan jujjuya sabida yadda yake ta tururi alamun yanzu aka gamashi.

Yasan da zafi amman yunwar dake zakularshi barata barshi ya kira ya huceba.

Sa spoon din yayi tare dayin bismillah ya soma Kai gudan Tsokan Kazan bakinsa.

aloman farko kuwa dadin abincin ya ratsa sa, wanda hakan yasa shi sauƙe numfashi tare da  bude cikinsa ya fara ci duk loman da zaiyi kuwa saiya had’a da ruwan cikin hearty chicken din.

Kana kuma time to time

Yake zukan spearmint tea din, wanda yaji kayan kamshi, spearmint, and Lemongrass leaves, pinch of cloves and masoro, A piece of ginger, sai kuma sugar da ta saka mai dan dama aciki.

Sosai spearmint Tea din yayi masa dadi.

Hakan kuwa shiyasa yaci abincin sosai, irin cin daya jima baiyi ba, bayan ya kammala cin na plate din ne ya jawo yar kular da nufin ƙarawa sabida.

Bai gama jin ya kai dai-dai gejiba.

Wani ɗan guntun tsaki yaja tare da ture kular.

Baki ya ɗan tura tare da cewa.

“Mamy”.

Dariyar dake son tsubuce matane ta danne tare da cewa.

“Na’am”.

Cikin hararan hanyar kofar dakin Jannart ɗin yace.

“Mamy ni ban koshi ba”.

Cikin dariyar yadda yake hararar hanyar da Jannart ɗin tabi Mamy tace.

“To kaine ai Babana sai kayi ta tara yunwa in ka tashi ci in ba mutun yasan yadda kakeba sai yace kai ɗan boll ne ko pollo dan sune masu yawan cin abinci”.

 Fuska a kwaɓe ya mike ya tashi ya tafi wajen Abba.

Cikin danne dariyar dai Mamy tace.

“Yauwa to in kaje wurin Abbanku watakil ka samu wani abu dan na mishi gashi ɗazu”.

Shi dai baice komaiba ya tafi yana tura baki har ga Allah bai koshin ba 

Koda yaje a falo ya samu Abba. 

Yana cin gashin gargajiya na jan nama.

Zubawa a plate Abban yayi tare dasa mishi yajin.

Kana ya miƙo mishi.

Amsa yayi tare da gyara zamanshi.

Da kallon flaks haka yasa Abba ya gane abin da yakeso.

A cup din da yasha tea ya haɗa mishi.

Sokan naman ya kai bakinshi kana a hankali ya tauna tare da kiransa da ruwan tea din.

Shi kuwa Abba Qur’anin hannanshi yaci gaba da bita.

Sabida yasan idan yana cin abinci muddin ya tara yunwa to bai mgn kuma baya son kallo, dan cine zaiyi sauri-sauri sai ya kauda yunwarsa.

So haka yasa ya kauda kanshi daga gareshi.

Shi kuwa cikin 13mnt ya cinye naman da Abban ya saka mishi tare da shanye shayin.

A hankali yayi gyatsa tare da cewa.

“Alhamdulillah Abba na koshi”.

Kai Abban ya jinjina kana sai da yaje kan aya kana ya datse tare da shafa addu’a ya rufe Kur’ani.

Sai lokacin yace.

“Abba Barka da dare”.

Murmushi Abba yayi kana yace.

“Barka dai ka dawo lfy”.

Bayan sun gaisane kuma ya gyara zamansa, tare da fuskantar  Abban kana a nitse  yace.

“Abba daya daga cikin ingines dinmu fa yayi kadan, dole sai ansanja ankawo babba, To yanzu dai munyi magana, da wanda nasaya kayan awajensa, akwai wani babban ingine, amman  dole  zanje China na sayo”.

Cikin gamsuwa Abba ya jinjina kai.

Dan shima da yaje Engineer Bello ya mishi bayanin komai.

Shi kuwa Rayyern a nitse yaci gaba da cewa.

“Ina tunanin zuwana China kwanan nan in sha Allah, dan shine babban abinda zai hana a fara aikin.”

Kai Abba ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace.

“Masha Allah to yaushe ne zakaje china’n?”

Sake gyara zamansa yayi tare da tankwashe kafafunsa, cikin nutsuwa yace.

“Maybe next month Insha Allah, saboda  Idan na tashi booking flight, kawai Zanyi kasancewar dama akwai sauran visa na.” 

Kai Abban ya jinjina kana cikin gamsuwa yace.

“Masha Allah Allah Ya taimaka.”

“Ameen.” Rayyern din ya amsa nan dai sukaci gaba da hiransu, kafun daga bisani ya tashi ya tafi.

Alhamdulillah Alhaji idi Saleh Dakata kuwa jiki da dan sauki tuni ma an sallameshi ya dawo gida.

Sai dai yana cikin tashin hankali.

Junaid kuwa yana hannun hukuma.

Akwana atashi ba wuya, domin yau satin Jannart biyu, agidansu Rayyern din. 

Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata akan shirin kowa.

Zuwa yanzu Jannart ta dan saki jiki sosai dasu Mamy da Riyyam-nsra da Ramadan.

Yanzu ma zaune suke ita da Mamy acikin falon.

Yayinda Jannart ɗin ke zaune akan kujera 3seater.

Don lokacin ta gama sawa Mamy lallen gargajiya a ƙafarta.

Mamy kuwa tana Dan nesa da ita kan 2 seater.

Hira suke dan tab’awa kadan kadan.

“Yau kuma har yanzu  su Ramadan basu dawo ba.

Su dai sun suka samu ba aiki to sai yawo kamar ababen hawa”.

Kai ta dan dago ta kalli Mamy tare da yin ɗan murmushi kana tace.

“Uhum ai dama tun jiya suke cewa yau jumma’a, tun daga masallaci kai tsaye min jibir zasu wuce”.

Kwaffa Mamy tayi tare da buɗe baki zatayi mgn sai kuma tayi shiru tare da zubawa ƙofar shigowa falon ido.

Ahankali ya turo k’ofar falon, tare da jefo k’afafunsa, dake wani irin b’ari.

Ganin  alamun bude kofar falonne kuma yasa, Mamy saurin juyawa da kai saboda bataji anyi sallama ba.

Idanunta ta dan zazzaro waje, Cikin yanayin mamaki da kuma tsoron, yanayin da taga Rayyern din aciki wani irin yanayin dake nuna ba lfy ba.

Rayyern kuwa, da gaba daya yakejiin duniyar na juya masa,  Yayinda da hannunsa duka biyu ke dafe da mararsa.

A hankali cikin tsananin wahala yake daga ƙafarsa.

Gaba daya duk jikinsa rawa yake, ga kuma idanunsa da suka rufa, saboda tsabar azaban da yakesha duhu ya gama rufe ganin ko Kallon gabansa bayayi.

Cikin wani irin yanayin da ke nuna baisan inda Kai da hayyacinsa yake ba, ya tunkaro cikin falon da salon tafiyarsa, Wacce ke nuna galabaitansa.

Cikin tashin hankali Mamy ta miƙe tsaye.

Jannart kuwa ido ta zubawa Mamy ganin yadda take kallon hanyar shigowa ne yasa ta juyo kanta itama.

Shi kuwa Rayyern 

Isowarsa tsakiyan falonne kuma yasa,  shi fad’a kan 3seater inda Jannart ke zaune wanda shine kusa da mashigar falon.

Saboda yanda idanunsa suka daina ganine kuma yasa bai san cewa da Jannart din awajen baiyi ba sabida baya ganin komai sai duhu.

Yanayin yanda ya fad’a kan kujeranne kuma yasa, kansa ya sauk’a akan cinyarta.

Arazane ta shiga kallonsa, Yayinda Mamy ma cikin tashin hankali ta taso tayiyo

Kansa tana kiransa a firgice.

“Rayyern Rayyern!! Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un, Yau kuma ciwon cikin kane ya tashi, Rayyern bud’e idanunka.”

Mamy ta fad’a cikin tsananin tashin hankali da gigita gaba ɗaya jikinta tsuma yakeyi.

 Saidai Ganin da tayi kamar Rayyern din baya motsi ne yasa,  cikin yanayin kidima da tsananin tashin hankali ta juya bayanta tare da fara kiran.

“Ramadan!!!”.

Gaba ɗaya tama mance baya gidan.

Shi kuwa Rayyern wani irin azabebben numfashin yaja tare da cusa kanshi cikin j…!!!

Back to top button