Mijin Marigayiya Page 1 Hausa Novel
A hankali take tafiya domin ba sauri take yi ba, duk da dai magriba ta kusa amma ta san zata kai gidan nasu kafin a fara kiran sallar. Karar wayarta ce ta katseta, ta dan rage sauri a tafiyar tata sannan tayi kokari ta zaro wayar daga jakarta. Tayi murmushi bayan da ta ga wanda yake kiran nata. Ba tare da bata lokaci ba ta amsa wayar ta kara a kunnenta.’Hey Babe.’ Ta fada tana wani rangwada kai tare da juya kwayar idonta kamar dai ga Babe din a gabanta tana kallonsa.’Mai kyau, ya kike?’ Ya fada daga daya bangaren.’I’m fine. Yanzu nake dawowa daga school gashi nan na kusa shiga gida.’ ‘Oh, nima yanzu na mayar da su Afaf gida wajen Hajiya. Mun je shopping ne and I bought a few things for you nake so na kawo miki later. Is that ok?’’Yes Babe, kai ma ka san ina nan idan dai kaine kake son ganina. Ya yarana? Hope suna lafiya?’’Alhamdulillah ga su nan. I just can’t wait to have you so we can all live in one place na huta da visiting yarana.’’Aww! Kada ka damu, very soon in sha Allah. We will talk more about it idan ka zo in dha Allah don yanzu zan shiga gida ka san Mommy ta hanani waya a kan hanya.’Yayi ‘yar dariya yace ‘Kuma fa hakane, to sai mun hadu.’Suka yi sallama suka ajiye wayar. Da sallama ta shiga gidan tana ta fara’a kamar wadda aka yiwa wani babban albishir. Babu kowa a parlor din sai Mommy tana shirin tashi ta shiga sallar Magriba. Bayan ta amsa sallamarta tace ‘Yau kuma haka kike tafe kina tallan macleans?’’Kai Mommy! I’m just Happy.’ Ta fada tana dariya.Ta wuce dakinsu yayinda Mommy ta shige nata dakin. Tana sane da yanda take tafiya tana murmushi din kuma tana jin dadin hakan. Idan dai a kan Mistapha ne fiye da haka ma zata yi. Muryarsa kawai take bukatar ji ta shiga farin cikin da baya misaltuwa. Wata bakwai da suka wuce suka hadu, amma saboda yanda ya iya soyayya da tarairaya ya shiga zuciyarta kamar wanda suka yi shekaru a tare. Da ya sami yanda yake so ma da tuni an daura musu auri don shi a shirye yazo, itace take dan dakatar da shi don tana so ta gama level 1 kafin ayi mata auren.Sai dai a daren jiya Baffanta ya sanar da ita cewa ta gaya masa ya turo maganar aurensu.Ta jefa Jakarta a kan gadonsu wadda ta fada kan kanwarta Nabila. Nabila ta make jakar ta ja tsaki tace ‘A’a, must you be stubborn?’Tayi dariya tana cewa ‘A tashi dai a yi sallah.’ Ta matsa gaban wardrobe ta fara kokarin cire kayan jikinta.………Kamar yanda yayi mata alkawari ana idar da sallar isha’i ya iso gidan nasu. A tsakar gida suka zauna inda ta saka musu kujerun roba a rumfar mota, ta ajiye karamin tebur a tsakanin kujerun wanda ta dora ruwa da lemon roba masu sanyi a kai. Bayan sun gaisa suka dan taba hira, hirar da a mafi yawancin lokuta itace take yi shi binta kawai yake da kallo yana murmushi yana bata gajerun amsoshi. Mustapha kenan; haka yake kamar wani basarake, komai nasa a hankali sannan kuma bisa tsari. Wannan ya sa yake kara burgeta.Ta dauki ruwan robar da ta ajiye ta bude ta mika masa tana cewa ‘Ko ruwan baka sha ba Yallabai.’Yayi murmushi yayinda ya karbi ruwan yana cewa ‘Kuma kin san kishirwan nake ji ba, don tun daga gida muke waya da su Afaf har na zo nan suna ta surutu duk sun gajiyar dani.’ ‘Kai haba, surutun na su nawa yake?’ ta fada tana dariya.Suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da ya tashi tafiya wajen karfe tara. Sai da ta raka shi bakin motarsa kafin tayi masa sallama sannan tace ‘Baffana yace na gaya maka mutanen gidanku zasu iya zuwa maganar aurenmu ranar asabar mai zuwa.’Take fara’ar sa ta kara fadi, ya dubeta kamar ya rungumeta yana ta murmushin da itama yake saka ta murmushi. Yace ‘Allah Khadija! Kai amma na ji dadi wallahi, in sha Allah ranar asabar din kuwa zasu zo da kudin aure da sadaki gaba daya.’Tayi dariya ‘Kai garaje, saurin me kake?’’To ai na kula bakya tausayina, so kike kiyi ta ja min rai kina barina sauro yana cinyeni saboda zance.’ ya fada da murya kamar ta mai shagwaba. Tayi dariya ‘To kwanan nan zaka huta in sha Allah.’Sukayi sallama cike da farin ciki bayan ta sanar da shi gidan kakanta inda nan ne zasu je maganar auren nata.Cikin walwala yake tukin lokaci zuwa lokaci yana yiwa kansa murmushin ji dadi saboda wannan labarin da Khadija ta sanar da shi. Watansu bakwai kacal da haduwa amma ya nutsu da hankalin yarinyar kuma ya yaba da tarbiyyar gidansu, ya tabbatar zata kular masa da su Afaf kuma zata tsaya a kan tarbiyyarsu ba tare da wata mugunta ba. Wata takwas kenan da rasuwar matarsa Asma’u, wadda itace ta haifa masa yara hudu; Afaf mai shekaru goma sha daya, Habib mai shekaru tara, Nasreen mai shekaru shida sai Shukra mai shekaru uku. Ba wani rashin lafiya tayi ba, haka kawai da daddare tace kanta yana ciwo don haka a gaba ya sakata sai ta sha kwayar Panadol sannan ta kwanta; sai dai da yake kwananta sun kare haka aka wayi gari sai gawarta. Yayi matukar bakin cikin rasuwar Ma’u kuma ya ji tausayin kansa da yaransa, gaba daya rayuwarsa ta tsaya saboda rashin Ma’u. Tunda aka kwana uku da rasuwar Asma’u mahaifiyarta ta tattara yaran ta tafi da su gida aka cigaba da kula da su. Can yake zuwa kullum ya daukesu ya kaisu makaranta idan an tashi ya mayar da su. Ana kula da su sosai kuma suma suna jin dadin zaman gidan sai dai shi ya fi so ya rayu tare da yaransa. Da farko ya so ya kwashesu ya kaisu gidan yayarsa; tunda mahaifiyarsa ta tsufa da yawa ba zasu sami kulawa ba a wajenta. Amma sai mahaifiyar Ma’u tace ba zata bayar da yaran ba. Sun so su sami matsala domin da kwashesu yayi ba tare da izininta ba ya mayar da su gidan Yayar tasa, sai da manya suka shiga cikin maganar aka yi yarjejeniya a kan idan yayi aure zai je ya debi yaransa. Don haka ba karamin dadi yaji ba da Khadija tace an bashi izini ya turo.Ya riga ya sanarwa Khadija idan ta tare zai dawo da yaransa kuma tayi na’am da hakan. Shiyasa ma wasu lokutan yake kwasosu ya kai mata su har suka saba sosai. Yayi mata bayanin irin kaunar da yake musu da kuma yanda yake so ta dinga kula da su kamar ita ta haifesu; kuma ta yi na’am da hakan. Don ko a yanzun ma tana kokarin wajen hidimarsu da jansu a jiki ga kyaututtuka, gashi wata ran da kanta take masa waya ya kawo mata su.Duk da ya riga ya je gidan mahaifinsa da safe amma a daren ma haka ya koma cike da farin ciki ya sanar da mahaifinsa cewa iyayen Khadija sun bashi damar ya turo. Mahaifinsa yana zaune a kan kafet a dakinsa ya dubeshi bayan ya gama sanar da shi inda za a kai kudin yace ‘Shikenan rigimar yara ta kare ko, ga amarya ga yaranka sai ka sami natsuwa.’Yayi dariya ya sunkuyar da kai.Daga baya yayi musu sallama ya wuce gidansa cike da farin ciki. _____ Kamar yanda aka yi alkawari ranar Asabar 18th February, 2020 waliyyan Mustapha suka sami karba ta girmamawa a gidan kakan Khadija. Bayan sun gaisa an musu maraba suka gabatar da sadaki N100,000 da kuma kudin aure N50,000. Baba Sani kanin mahaifin Khadija ya sa hannu ya karbi kudin ya matsa ya ajiyesu a gaban mahaifinsu Alhaji Baba. Cike da fara’a da murmushi Alhaji yace ‘Ma sha Allah, Allah ya sa albarka Allah ya nuna mana.’Gaba daya mutanen dake wajen suka amsa da Amin. Baba Safiyanu wanda Yaya ne a wajen mahaifin Khadija yayi gyaran murya yace ‘Alhaji ni ina ga tunda ga sadaki an kawo kuma ga waliyyan ango ai sai kawai a daura auren nan yanzu. Yanda abubuwa suke tafiya rufe garin nan fa za ayi, tunda ka ga kasashen duniya suna ta rufewa fa. COVID 19 din nan ana maganar ta shigo kasar nan sosai, ko da wanne lokaci za a iya shiga lockdown.’Alhaji yace ‘Ikon Allah, kace abun ya zo mana kenan. To Allah ya tsare mu da zuri’ar mu.’ ya dubi waliyyan Mustapha yace ‘To idan a shirye kuke sai a daura auren ai, nan da sati mata sai suyi bikinsu su kai amarya kafin ace an kulle kasar.’
