.*ASM Bk2044*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..tun bayan daya dawo hayyacin shi ya k’ank’ame ta sosae jin yadda jikinta keta kerma gashi an kai wata ga6a da bata ma iya yin kukan mai sauti sai na zuciya k’walla nata gangaro mata ga zazza6i daya rufeta ruf lokaci guda, to shima dae kermar nashi jikin yake duk ya rud’e yanata bata hak’uri cikin wata irin murya mai nuna tsantsar tashin hankali gaba d’aya jin jikinshi yake tamkar ba nashi ba ga zazzabi dake neman rufe shi shima a haka bacci ya d’auke su su duka saidae Fatuu bana dad’i bane don sai sakin ajiyar zuciya take had’i da d’an firgita, suna haka aka maido da wuta sanyin Ac ya karad’e bedroom d’in kermar jikin Fatuu ta k’aro ba kamar da yake ba kaya a jikinta iya duvet ne da ya rufa masu, da k’yar ta bud’e idanunta da sukae mata wani irin nauyi jikinta na cigaba da yin kerma ga wasu kwalla masu zafi na gangaro mata a gefe da gefen idanunta sam ta kasa wani kwakkwaran motsi don duk ilahirin jikinta ciwo yake ga rad’ad’in azaba dake ratsa cikin jikinta ga kanta dake wani irin Sara mata ta k’ura ma ceiling ido idanuwanta a d’an lumshe she wishes what happened was a dream ba gaske ba saidae koda ga yanayin da take jin jikinta tasan gaske ne ya farun cikin ranta ta fara ayyana wannan wane irin bala’e ne miyasa Ya Haisam ya akaita mata hakan anya kuwa da gaske ne ba mafarkin ba, a hankali ta fara tariyo abunda ya faru tun daga farko ita dae tasan zata iya tuna lokacin daya kai hannu ya zuge mata zip dama rigar nada dogon zip har kusan k’ugu kuma bata sa bra ba sakamakon kamata da rigar tayi sosae sai tasa yar half vest kawae tunda kuma ya kai kan su ta fita hayyacin ta bazata iya tuna ga abubuwan da suka cigaba da faruwa ba sai lokacin da taji yana kokarin penetrating d’inta, hannu tasa ta rufe bakinta tana wani irin kuka mai cin rai miyasa hakan ta faru ya akai suka aikata hakan wata Zuciya ta raya mata sharrin shaid’an dama duk in mace da namiji suka ke6e ai na ukkun su shaidan ne ta k’ara ayyana to amman miyasa da tana rok’on shi kada ya aikata mata hakan yak’i sauraron ta mi zai sa ya cutar da ita har haka yanzu shikenan ya rabata da budurcin ta ya Haisam ya cuceta bai tunanin abunda zai je ya dawo ba Saboda son zuciya ya keta mata haddi wannan wace irin Masifa ce mutumin da ko a mafarki bata ta6a tunanin zai mata haka ba balle a zahiri mutumin da shine ya bata kariya hakan bai faru da ita ba a baya amman shi da kan shi ya aikata mata hakan mutumin da kowa nata ya yarda dashi ba kamar gwaggo har take iya barinta ta fita da shi da daddare sosae shine ya aikata mata wannan d’anyen aikin da tasan in gwaggo taji har zuciyarta na iya bugawa, innalillahi Wa’inna ilaihir raji’un! haka take ta maimaitawa tana juya kanta tafin hannunta guda dafe da goshinta tana haka taji fitsari ya matseta ta fara kokarin janye jikinta don ta tashi sai faman nishi take da k’arfi sai lokacin ta gane ba kaya jikinta ta k’ara sakin wani Sabon kukan da K’yar taja jiki ta matsa can gefe inda ta hango jallabiyar ta ta d’auka daga zaunen ta zurata don bata ma ga jar rigar ba da dubara ta isa k’arshen gadon a hankali ta zura kafafun ta k’asa saida ta daddafe gefen gadon da hannunta sannan cike da k’arfin hali ta yunk’ura ta mik’e har wani Jiri ke dibarta tasa hannu ta dafe kai tana d’aga k’afarta don ta fara tafiya ba shiri ta koma da6ar ta zauna har saida ta saki yar k’ara Saboda wani rad’ad’in azaba da ta ratsata, hannu tasa ta rufe baki ta fashe da wani sabon kukan jin fitsarin na niyyar zubowa yasa dubara ta fad’o mata ta duk’e k’asa ta fara yin rarrafe tana cigaba da yin kuka a haka ta nufi Toilet d’in baiwar Allah duk wannan abun Haisam bacci yake ta shara sai kace matacce, a wahalce ta isa toilet d’in da K’yar ta shiga cikin bathtub don ma tana da k’arfin hali lokacin da fitsarin ya fara zubowa wata zabura tay a gigice tace “Wayyo Allah na!!!” ta k’ara fashewa da kuka Saboda azaba da kyar ta gama tana ta gunji ta kai hannu ta kunna fanfon ruwan zafi ko da tai tsarkin sai taji wani dad’i ya ratsata aikuwa taci gaba da yi ta bar fanfon a kunne tana tayi har bayan wani lokaci sannan ta kashe sai gashi ta samu relieve sosae bata sha wahala ba wurin fitowa kamar da zata shiga, da k’afafunta ta fito sai dae da K’yar take tafiyar tana yi tana dafa bango ga k’afafun sun d’an bud’e bata iya had’e su a haka har ta fito cikin d’akin idanunta suka sauka akan Haisam dake ta bacci sumar shi duk ta yamutse wani irin haushin shi taji ya turnuk’e ta ya aikata mata wannan aika aikar amman baccin shi ma yake sha nan da nan ta ayyana dama da niyya yay mata hakan k’walla ne suka cigaba da zubo mata tana sharewa wata zuciyar ta raya mata kawai ta tafi gida tunda ko ta zauna in ya tashi bai wuce yace zai bata hak’uri tunda ba iya dawo mata da abunda ya rabata da shi zai yi ba da wannan tunanin ta lalla6a ta d’auki gyalen rigar kota kan jar rigar bata bi ba dama tashi ce ta bar mashi kayan shi a hankali take tafiyar ta nufi kofa akan hanya ta ga purse d’inta yashe a k’asa ta d’auka bayan ta fita a bakin k’opa dama ta aje takalmanta saidae tasan bata iya tafiya dasu hakan yasa ta ruk’e su a hannunta, ta d’auki lokaci kafin ta k’araso bakin gate d’in tsit kake ji da alama dare ya tsala sosai a bakin kopar security ta tsaya ta kai hannu tana kwankwasa wa sai gashi ya fito hannun shi ruk’e da bindiga ya bita da kallo ta d’an kauda fuskar ta ya ganeta hakan yasa shi cewa “Madam lafiya kuwa” kaman bazata yi Magana ba k’asa k’asa tace ya bud’e mata kopa zata tafi ne da alamun mamaki yace “tafiya kuma cikin daren nan ina shi yalla6an yake” nan ma shirun ta k’ara yi ta rasa mi zata ce mashi don kar ya zargi wani abu can dubara ta fad’o mata tace “wani aiki yake a computer shine yace in jira ya gama mu tafi to sai bacci ya d’auke ni yanzu bayan na farka kuma sai naga shima yayi baccin ban son in tashe shi ka bud’e man zan iya tafiya” daga jin yadda take Maganar zaka fahimci ba daidai take ba sai faman nishi take ga Maganar a wawware shiru Officer yay yanata kallonta ya lura da har jikinta ma kerma yake hakan yasa shi ce mata kamar ma bata lafiya ko tace mashi eh zazzabi ne ya rufeta shine ma yasa ta farka yace to bari shi yaje yay mashi magana sai yazo ya kaita don dare yayi sosae k’arfe d’aya saura da kyar ma in bata wuce ba da sauri tace ba sai ya kira shi ba zata iya yace “Madam bari dae in mashi magana don a irin wannan lokacin ba’a fita da k’afafu don karnuka keda akwae ta ko ina da sun ganta zasu yi mata tara tara su aikata mata d’anyen aiki yana gama fad’in hakan ya nufi cikin gidan Fatuu na k’walla ta ayyana d’anyen aiki ya wuce wanda aka aikata mata yanzu, kasa cigaba da tsayuwar tayi da K’yar ta zauna kan saman wurin k’afafunta na a k’asa ta takure jikinta dake ta rawar sanyi wani irin fayau take jin ta, yana shiga corridor d’in d’akin Haisam ya tunkari kopar ya tsaya yasa hannu yana kwankwasa wa tun yana yi a hankali har ya kai ya k’ara sautin bugun amman shiru kake ji ba alamun za’a tanka kuma dae ba zai yuwu ya kutsa kai ba, cigaba da kwankwasawa yay can cikin bacci bugun ya kai ma Haisam da K’yar ya fara bud’e idanun shi da sukai wani irin nauyi gashi har kala sun canza sun d’an yi ja d’ago kan shi yay da mamaki yake kallon kopar da ake bugawar can ya tambayi waye da kasalalliyar murya saida ya tambaya sau biyu sannan k’asa k’asa Officer ya jiyo shi da d’an k’arfi yace Officer ne cikin ranshi ya maimaita sunan Officer d’in kafin ya kai hannu ya yaye duvet d’in wani irin bugu gabanshi yay lokacin da idanun shi sukai tozali da jinin da ke a jiki kallon jinin yake with mouth agape can ya furta “ZARAAH!!!” aikuwa cikin zafin nama ya saukko da sauri ya nufi hanyar corridor ya nufi toilet don ganin ko tana ciki yaga wayam da sauri ya juyo lokacin idanun shi suka sauka kan milk d’in jallabiyar shi da itama ke d’auke da stains na jini ta cikin mirror d’in jikin press d’in shi k’ara rud’ewa yay ya nufi hanyar fita yazo bakin kopar ba tare da ya bud’e ba sosae ya d’an lek’a kanshi ya tambayi Officer ko lafiya anan ya fad’i mashi dama Madam ce da suka zo tare gata can bakin gate ta matsa sai ya bud’e mata ta tafi kuma ma bata lafiya don sai kerma take da sauri Haisam d’in yace mashi yaje gashi nan zuwa ya koma cikin Corridor d’in yana wani irin sauri da shi kanshi bazai iya tuna ga ranar da yayi irinshi ba wata jallabiyar ya zuro wuya a jirkice ya fito tun kafin ya k’arasa ya hangota raku6e a jikin pillar yana k’arasawa ya tsaya akanta ya kira sunanta shiru bata amsa ba bata kuma kalleshi ba sai ajiyar zuciya take yi da gani kukan zuci take Slowly ya duk’a a gabanta Officer na ganin haka ya juya ya koma cikin d’akin shi, k’ara kiran sunanta yay still bata amsa ba ya kai hannu ya kamo hannunta aikuwa ta fusge zafin da yaji a hannun ne ya k’ara tada mashi hankali cikin trembling voice yace “am so sorry Zaraah mu koma ciki sai muyi magana” banza tay mashi ganin bata da niyyar tashi yasa shi mik’ewa ya kai duka hannuwanshi zai d’auketa aikuwa ta fashe mashi da kuka mai sauti tana fad’in ita ya kyaleta yasa a bud’e mata gate ta tafi, fasa d’aukar tata yay ya mik’e tsaye don bai son Officer ya ji har ya zargi wani abu can ya sake duk’awa gabanta a hankali yace “kin ga yanzu dare yayi sosae kiyi hakuri mu koma ciki zan kira Uncle d’in ki sai in sanar mashi dare yayi mana sosae matar Abbas ta wuce dake gidanta in mun shiga ciki zamu yi magana kiyi hak’uri kinga ma baki lafiya sai kisha magani” da ga voice d’in shi zaka fahimce shima a rud’e yake har wani d’an nishi yake don shima zazzabi ne a jikinshi, duk yadda yay da ita su koma ciki tak’i sai ma ta kife kanta tana ta kuka har cikin ran shi yake jin kukan don yasan shine silar shigarta halin da take ciki yama rasa tunanin da zai yi cikin ranshi yanata ayyana miya faru dashi ne ya akai ya aikata wannan d’anyen aikin ina hankalin shi ya tafi ne, yasan tunda ta kafe to bazata koma ban hakan yasa shi ce mata to bari ya maida ita gidan cikin fushi tace ita bata so a bud’e mata gate kawae bai yi mamakin yadda tay mashi Maganar ba don yasan girman shi ya gama fad’uwa a wurin ta rarrashin ta ya shiga yi yana nuna mata illar fitar ta a wannan lokacin in dai bata bari ya kaita ba to saidae su kwana anan ala bashshi sai ya kira Amadun ya fad’a mashi abunda yace zai fad’i mashin, shiru tay saida aka d’an d’auki lokaci sannan tace suje ya kaita ya mik’e da sauri kai kace ba Haisam ba da alama bai ma san ina yake wurga k’afarshi ba dama Motar ba’a parking space take ba yana d’aukko makullin ya shiga ya tada bayan ya juyata ya iso gaban gate d’in ya bud’e ya fito ya koma wurinta yace ta taso suje ganin yadda take kokarin mik’ewa yasa shi kai hannu ya taimaka mata tana ta k’ok’arin kwacewa bai biye mata ba saida ta mik’e sannan ya saketa da k’yar taja k’afa ganin ta nufi kopar baya ya je ya bud’e mata saida dubara ta shiga ya rufe shima ya shige driver seat yay ma Officer horn sai gashi da sauri ya fito yaje ya zuge masu gate d’in Haisam yaja suka fice, bayan officer ya rufe gate d’in tsaye yay da alamun tunani yake saidai ya kasa hasashu komae k’arshe ya gyad’a kai ya koma cikin d’aki, tunda suka taho taci gaba da kukan da take k’asa k’asa tana sheshsheka shiru bai ce mata komai ba tunanin yadda zai maida ta gida acikin wannan halin yake can wata zuciyar ta raya mashi yakamata ma ya kaita Asibiti don da alama akwae matsala Saboda jinin da ya gani duk da first night dinsu da Fanan itama tay shedding blood d’in amman nata d’an kadan ne bai kai yawan na Fatuu ba da wannan tunanin ya yanke wucewa da ita Asibiti kawai, kanta na duk’e har suka iso jin an tsaya yasa ta d’ago lokaci guda ta gane Asibiti ne bayan ya kashe Motar ya bud’e ya fita saida ya rufe ta da Makulli sannan ya nufi ciki Fatun na mashi wani kallo ta cikin glass wa zai yi tunanin zai iya aikata mata haka ta raya a ranta, yana shiga reception sai ga wata Nurse zata wuce da sauri yay mata magana ta dakata baiwar Allah har saida ta saci kallon k’afafun shi don taga in ba kofato bayan yay mata ya aiki tace Alhamdulillah yace don Allah Doctor mace yake son gani tace mashi gaskiya ba mace duk maza ne shiru yay kawai yana tunanin bai kamata ace namiji ne zai duba ta ba ganin haka yasa tace mashi dole sai mace yace eh yafi son haka har zai juya tace “Yalla6ai akwae wata Mama tsohuwar nurse ce ba likita ba amman kusan ma kamar likitan ake d’aukarta don ta san abubuwa sosae in kana so tana nan sai ka ganta” da sauri ya kalle ta yace Ok tana ina tace suje ta juya hanyar da ta fito yana biye da ita har suka isa wata kwana a bakin wata k’opa ta tsaya ta juya tace mashi tana zuwa ya d’aga mata kai, lokacin data shiga mamar wadda dattijuwa ce tana kwance a saman gadon da ake duba mara lafiya ta d’age kai baki bud’e tana bacci ga gilashin fuskarta ya zame a gabanta nurse d’in ta tsaya ta kira sunanta har sau biyu bata farka ba hakan yasa ta d’an matsa ta kai hannu ta d’an bubbuga gefen kanta aikuwa sai gashi ta bud’e ido kaman an latsa mata remote ta k’ura ma nurse d’in ido ita kuma tana mata murmushi can ta yunk’ura ta tada kanta cikin fushi tace “Nurse Bilki ke wace irin muguwa ce ne?” D’an bud’a ido bilkin tay tace “Mama nice muguwa kuma” tsuke fuska tay tace “eh mana in ba mugunta da rashin tausayi ba duka fa ban dad’e dana samu na kwanta ba bayan gama kacaniyar Labour room shine kuma zaki zo ki katse man bacci?” Sanin halin ta na mita yasa bilkin cewa “to yi hakuri Mama dama bak’o kika yi ne shiyasa na tashe ki” d’an yamutsa baki tay tace bak’o kuma da tsakan daren nan waye shi bilkin ta fad’i mata yadda sukai da Haisam wata uwar harara ta zabga mata tace “to in banda iskanci baki ji likiciya yake son gani ba zaki tada ni ni likita ce?” d’an murmushi bilki tay tace “ai kema mama kaman likitan kike kuma don naga kaman yana cikin tashin hankali ne yasa nace bari in maki Magana k’ila wata matsalar ce yake son fad’i maki” cigaba da harararta tay kafin can ta yunk’ura ta saukko tana d’aure da zanin Atamfa saman farar doguwar rigar aikinta tambayarta tay yana ina tace yana nan bakin kopa ta nufi kopar tana mita bilkin na dariya a ranta tana ayyana dama ina ma’aikacin Asibiti yaga wata damar yin bacci mai yawa, Mama na bud’e kopar idonta suka sauka kan Haisam dake jingine da bangon dake opposite da Office d’in har saida tasa hannu ta gyara gilashin ta yadda zata gan shi da kyau ta bishi da kallo tun daga sama har k’asa ganin yana kallonta yasa tace shine mai neman ta yace eh yana kokarin matsowa gabanta tace tana d’an zuwa to yace Ok ta koma ciki suka had’a ido da bilki dake murmushi tace “Ke kin tabbatar wannan mutum ne kuwa ba Aljani ba nifa ban yarda da shi ba don kwanakin nan dama ina yan gane gane” Bilki mi zatayi ba dariya ba ganin yadda mama tayi zuru zuru da alama dae ta tsorata da Haisam d’in cikin dariya tace “Wllh mama nima dana gan shi har saida na kalli k’afafun shi dama banga lokacin da ya shigo ba sai dae naji anyi man Magana kawae ga abu na dare” turo baki Mama tay tace mata yanzu ya zasu yi bilkin tace ita tana ganin lafiya lou Mutum ne in ba haka ba mi zai sa yazo wurin su har yace yana son ganin likita Mama tace “Bilki raba kan ki da sharrin Mutanen 6oye” juyawa tay tace suje tare koma mi zai faru ya faru dasu duka bilkin ta bita tana fad’in kai Mama kefa dama kin tsufa ni kuma yanzu nike kuruciya ta a tare suka fita bawan Allah Haisam yana jingine da bango duk yayi zuru zuru bayan ta fito tace mashi tana ji miye matsalar yake son ganinta ba tare daya ji komae ba ya shiga yi mata bayani bayan ya d’an daidaita natsuwar shi tana ta jinjina kai ta d’an ta6e baki har ya gama saidae a yadda yay mata bayanin nuna mata yay matarshi ce, tambayar shi tay yanzu ina take yace tana Mota ta tambaye shi tana iya tafiya yace eh amman ba sosae ba ta kalli Bilki tace taje ta d’auki Wheelchair ta taho da ita su fara tsayawa Nurses room a turo ta tace to ta kalli Haisam tace suje, da taimakon Bilki Fatuu ta fito ta taimaka mata ta hau wheelchair d’in kafin ta tura ta tana biye da ita suka shiga saida ta tsaya aka tura sunanta ta computer sannan suka wuce wurin Mamar da zasu shiga tace ma Haisam ya jira ta nuna mashi waiting seats dake gefe alamar ya zauna yace ok, bayan an shiga da ita tare da Mamar aka taimaka mata ta hau gadon ta sanya hand gloves ta fara dubata tana yi tana yamutsa baki can ta fara mita tana fad’in “ni wllh irin wannan duk nafi ganin laifin iyayen ku su same ku suyi ta yi maku banke banken magungunan mata to su mazajen naku duwatsu ne da bazasu rikice har suyi maku aika aika ba, kamar ke yanzu ai baki wani bukatan magunguna iya lafiyayyen Abinci ma ya Wadatar kuma da gani ana ci sai abu ya faru kuzo kuyi ta ma Mutane jan ido” bilki dai na tsaye daga can gefe tana k’umshe dariya sosae ta duba ta bayan wani lokaci ta gama ta fara cire safar ta jefar a cikin dust bin kafin ta juyo ta kalli Fatuu tace “Allah ya taimaka baki buk’atar stitches kin samu rauni ne a farko wurin shiga da alamu ansa ma wurin k’arfi ne halan hana shi hakkin shi kika so yi ya nuna maki k’arfi haka?” sunnar da kai Fatuu tay idanunta suka ciko da k’walla da tasan halin da take ciki da batai mata wannan Maganar ba kallon bilki tay tace ta kamata su shiga toilet d’in cikin Office d’in ta taimaka mata da ruwan zafi ta zauna ta d’an samu relieve tace to ita kuma ta juya ta fita Haisam na ganin ta lek’o ya mik’e yaje gabanta tayi mashi bayanin komae tace yanzu dole ta dage da zauna ruwan zafi amman ba mai zafi ba sosae da d’an gishiri sai magungunan da za’a bata ta rink’a sha in tana haka zata samu sauki yace to d’an zare mashi ido tay tace “Amman fa ka k’yaleta ta huta sosae har ta warke garas kafin ka k’ara tunanin yin wani abu” jinjina mata kai kawae yay tace ya jira zata tura magani yaje Pharmacy yace to tana niyyar juyawa ya dakatar da ita ta hanyar rok’on ta ko ya samo mata wani abu a bata taci sai in ya amso magungunan a bata ta fara sha daga nan d’an kya6e baki Mama tayi tace halan fushi take dashi yasan in ya bata bazata ci ba d’an guntun murmushi kawae yay tace yaje ya kawo ya amsa da Ok ya wuce, bada jimawa ba ya dawo Cake da lemu ya samo a shop d’in cikin Asibitin su kadae ne yake tunanin zata d’an ci don ba Abinci a wurin bayan ya kwankwasa Nurse Bilki ce ta fito ta amsa kafin ya juya ya nufi Pharmacy d’in aka tura kud’in yaje ya biya kafin ya amsa magungunan suma ya kai masu ya koma ya zauna, saida Mama ta matsa mata ta cinye duka har lemun tana yamutsa fuska alamar bata so bayan ta gama suka rakota waje ba laifi tafiyarta ta d’an k’ara warwarewa yana ganin ta fito ya mik’e ta kauda kai gefe Mama tace to gatanan sai a kiyaye ya amsa da Ok yay mata godiya kafin ya rok’eta ta d’an bashi Account details nata farko kaman bazata bashi ba tace ai ba sai ya bata wani abu ba ai aikinta ne yace ya sani just kyauta ce sannan ta fad’i mashi nan take yay mata transfer d’in 70k yace taba Nurse Bilki 20k suka hau godiya har tana zolayar shi tana in Amarya ta haihu a sanar masu ya d’an dai yi murmushin yak’e kawae suka tafi yana ruk’e da ledan magungunan da bilki ta bashi, a hankali take tafiyar yana biye da ita a haka har suka fito shi ya bud’e mata back door d’in kaman bazata shiga ba yanata kallon ta ita kuma ta juyar da fuskarta gefe saida ta ga dama sannan ta shiga ya rufe kopar koda ya zagaya maimakon ya shiga driver seat d’in sai shima ya bud’e bayan ya shiga tana ganin ya shigo ta juya mashi k’eya shiru yay yana kallon bayan kan nata Magana yake so suyi saidae ya rasa ta inama zai fara can ya nisa yace “Zaraah” shiru bata amsa ba balle ta kalle shi cigaba yay “I know i ave wronged u dat sorry isn’t enough to make u forgive me but I will still use it to apologize for what I have done am very sorry Zaraah” banza ta mashi yaci gaba “nasan na cutar dake saidae billahi bada nufi hakan ya faru ba ni kaina I don’t know what came over me da har hakan ya faru amman koma miye laifi na ne cos am the one who took u there” nan ma dae tsit tay sai yar sheshsheka da take yi a hankali shiru yay yana ta kallonta a cikin ranshi kuwa bai mamakin duk abunda tay mashi ba don yasan dole ma girman shi ya fad’i a idonta sigh yay yace “in sha Allah zan gyara laifin da na aikata gobe zamu yi Magana da ke but before then pls don’t disclose what happened to anyone” cikin fushi ta juyo fuskarta jage jage da hawaye tace “ai in ban fad’a ma kowa ba Allah shi ya sani miyasa zaka man haka ka cutar dani bayan laifin da kasa muka aikata hakan bai isa ba har sai ka cutar da rayuwata…..” Fashewa tay da matsanancin kuka still yay yana kallon ta komae ya gama kwance mashi ya rasa ta ina zai taro matsalan ta gyaru gashi shi kanshi ba lafiya gareshi ba don zazza6i tuni ya gama rufe shi k’arfin hali kawae yake k’arshe dai hak’urin yaci gaba da bata yana zasu yi Magana gobe da k’yar ya samu ta d’an tsagaita da kukan ya bud’e Motar ya fita bayan ya rufe ya bud’e driver seat ya zauna kafin ya rufe yaja suka tafi………….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.