Hausa novels

Zakuna Biyar Page 7 By Princess Teema

A can gefe kuwa Leo sai da ya gama kwanciyansa ya miƙe ya yi wanka, shirinsa ya yi cikin ƙananan kaya masu kyau, yau ɗin ma dai ripped jeans ɗin ne, da alama ripped sun fi yawa a cikin kayansa, kyansa ya kara bayyana, amma kuma ya ɗan rame kaɗan alamar wahala a tattare da shi.Har zai fita daga room ɗin sai kuma ya dawo ya hau shin Noor daga barci, dan yana son koyawa yaron komai a tsari. A firgice Noor ya tashi yana ambatar sunan daddynsa, da alama mafarkinsa ya yi, wlh ba dan GIDAN SOJA ba ba’a tashin Noor daga barci, saboda ciwon nan nasa, yana firgita, amma yanzu har ya fara sabawa da tashin nasa da ake yi.In a cool way Leo ya ce. “It’s breakfast time, get up and let’s go eat”…….. Jin voice ɗin Leo yasa Noor sauke ajiyar zuciya, a natse ya ɗago jajayen idanunsa a kan Leo ɗin, tamkar zai yi kuka ya ce. “Please brother let me sleep, I really want to sleep”. Da kyar yake maganar. Sosai Leo ya ji tausayin yaron ya kama shi, sai ya ji yana buƙatar jin labarin Noor, kamar zai fita, sai kuma ya fasa, komawa saman bed ɗinsa ya yi, ya zauna tare da jawo jakarsa, buɗewa yai. Biscuits manya-manya masu daɗi ya ciro kwali biyu, da hannu ya yi wa Noor alamar da ya zo. Ba musu ya sauƙa ya je, gefensa ya nuna mashi, zama ya yi yana ta faman daka hamma. Miƙa mashi biscuits guda ɗaya Leo ya yi, ba musu ya karɓa yana cigaba da kallonsa. Ɗan nisawa ya yi kafin a natse ya ce. “I want to know your history, who are you? Why don’t you want to focus on the work that brought you here?”.Da sauri Noor ya waro idanunsa a kan Leo ɗin, lokaci guda ya ji murmushi ta kubce mashi, wani irin musulmin daɗi ya ji, wai yau Leo ne yake kula shi haka? Har yana neman jin tarihinsa? Bai san cewa dikkansu a ɗakin sarai Leo yana karantarsu ba, dik wani motsinsu yana sane da su, shi mutum ne da ya tsani haɗa hanya da dolaye marasa basira, sai da ya gama karantarsu tsab a ɗakin sannan ne kuka ga ya ɗan fara kula Noor, ya fahimci a ɗakin dikka babu dolo sai dai rashin mai da hankali a kan aiki, amma dikkansu akwai kaifin basira.Shi Noor na daban ne a cikinsu, kwakwalwansa tana da saurin gudun tinani, akwai wani baiwar da ALLAH ya ajiye a tattare, kawai tsabar sangarta ne da shiririta da ƴan uwansa mata da daddynsu suka yi mashi har tai mashi over yasa baya taɓa abin arziki, amma da zai taimaka mashi wlh za’ayi alfahari da shi a hukumar soja, zai kafa babban tarihin da zai yi wuya a sake samun wanda zai sake kafa irinsa.Shin kun yarda da zancen Leo dake cewa Noor zai kafa babban tarihi? Wace iriyar tarihi kenan? Wace iriyar baiwa ce a tattare da Noor? Mu je zuwa.Gyara zama ya yi, take ya ji barcinsa ta gudu, a natse ya ce. “My name is Nooriel Fayruz Zaheeran, ainahina European ne, mahaifina European ne, mahaifiyata ƴar kabilar scandinavian ce a kasar Mexico yankin Amurka kenan, amma mu mazauna CRYSTAL PALACE ne a cikin Us, mahaifiyata ta rasu a ranar da nike shirin zuwa duniya, na taso a tare da sisters ɗina mata su uku, sune komai nawa, sai daddyna”. Nan ya kwashi dikkan labarinsa, yadda daddynsa ya kwallafa rai kan neman ɗah namiji, dukiyar da ake jiran ya kula da shi, da komai da komai ya bashi labari.Kai jama’a ashe dole Noor ya haɗu ba karya, mahaifinsa European, mahaifiyarsa scandinavian a Mexico, kun san da cewa kabilun scandinavian suna daga cikin top ten kabilu mafiya kyau a duniya? Tushensu a Sweden suke, amma suna iya zama a ko’ina. A top ten ɗin ma su ne na 4 a kyau! Shiyasa ɗan yaron nan ya haɗu, ga kyawawan European eyes masu ɗaukar hankali. Mutane dayawa basa banbanta Europe da Ethiopia na Afirka, to bari in banbanta maku, idan kun ji Ethiopia to nan gida Africa ake nufi, amma idan kun ji Europe yana ɗauke da ƙasashe kamar haka, United Kingdom watau Uk kenan, ko ku ce England, ita ce uwa ga Europe gabaɗaya, sai Ireland, France, Spain, Portugal, Belgium, Netherlands, Luxembourg, Germany, Switzerland, Italy, Austria, Poland, Czech Republic, Slovakia, Hungary, Slovenia, Croatia, Bosnia and Herzegovina, Serbia, Montenegro, Kosovo, Albania, North Macedoni, Greece, Bulgaria, Romania, Moldova, Ukraine, Belarus, Lithuania, Latvia, Estonia, Finland, Sweden, Norway, Denmark, Iceland, Russia ta wani ɓangare sashen turai ne, wani ɓangaren nasu kuma yana sashen Asia, su dai suna tsakiya. Haka Turkey suna tsakiya, Andorra, Monaco, San Marino, Vatican City, waɗan nan su ne Europe, kuma sune ainahin turawa ba Amruka ba, America dik ƴan bariki ne a cikinta bakin haure! Na faɗa maku ne da dayawan lokuta idan na ce Europe sai in ji kuna fassara mun shi da Afrika! To ba ɗaya bane!. ————————Nisawa Leo ya yi jin labarin, a ransa yake mamakin jin sunan Fayruz Zaheeran, tabbas ya taɓa jin wannan suna, amma a ina? Ya mance, gefe guda kuma mamaki yake yi jin cewa Noor ya fi to ne daga CRYSTAL PALACE, like wow, waje ɗaya suke, dan shi ma Leo daga can yake, suna gini guda amma basu san juna ba. Da ya tuna suna gini guda sai ya ce kila a nan ya taɓa jin sunan Fayruz Zaheeran ɗin, lokaci guda kuma ya sake tunawa ashe fa suke da mallakin STARS BODY LUSH, zai iya yiwuwa ma a jikin mansu ya ga sunan. Jin labarinsa yasa ya ji tausayinsa matuƙa, sai ya guduri niyyar taimaka mashi da gaske, a farko ya fara bashi horo ne saboda kansa ya daina sanyasu ɗaukar last, yanzu kuma zai bashi horo ne a matsayinsa na maraya ya tsaya ya karfafa kansa. Tin daga wannan rana Leo ya fara horar da Noor horo ta musamman, ya ja shi a jiki sosai, su Zaynish sai mamaki suke yi yadda aka yi Leo yake jan Noor a jiki har suna magana, sun kuma yi mamakin yadda aka yi Noor yanzu baya faɗuwa a horo, yana kokari sosai.Sai ma da Leo ya zaunar da shi, ya nusasshesa cewa lallai ya tsaya tsayin daka ya zama namiji, kada ya biyewa shirme, kada ya manta mahaifinsa shi kaɗai ya mallaka namiji, shi kaɗai ya kwallafa rai a kansa, kada ya zubawa daddynsa ƙasa a ido, ya tsaya ya jajirce ko dan ƴan uwansa mata dake gida. Irin waɗan nan kalamai Leo ya dinga yi mashi, har ya sanya Noor ya ji wani irin karfi da kwarin gwiwa ya lulluɓesa, cikin ƙasa da wata guda gabaɗaya Noor ya canza, ba zaku taɓa cewa shi bane, ya zama jajirtacce, dik in da Leo ya sanya kafafunsa Noor ma zai sanya nasa, sun zama very close brothers!. ——————-🔥A yanzu sun kai watanni uku a GIDAN SOJA, sun tsaya tsayin daka suna karɓar horo babu wasa, manyan generals sun yi matuƙar sanya idanunsu a kan room 1 ɗin nan sosai, saboda jajircewa da baiwa irin nasu, yanzu ba iya Noor kawai ba, gabaɗaya ɗakin training ɗin dare suke yi, saboda su bada mamaki! Amma su Zaysh Leo yana basu horon dare ne dan kada su ja team na su ya rinƙa faɗuwa, Noor kuwa a yanzu yana bashi ne a matsayin Brother!. E akwai case.Yau takama Monday, 5:30 bayan sun yi sallar asuba, tsaye suke a hall da suka saba tsayawa, gabaɗaya matasan idan kuka gansu a yanzu sun canza, dikkansu jikinsu ya karɓi horo wuta-wuta, dik sun murɗe sun fara zama mazajen gaske, musamman team 1 dake satar hanya su yi horon dare, jikinsu ya fi na kowa murɗewa, shi kam Leo baa magana, dama jikinsa da horo ya zo AZURE, yana gym, yanzu ya zo ya kara wuta-wuta, ai idan kuka gansa sai ka sha jinin jikinka.Yanzu fa sun saba da Captain sosai, yana mugun son waɗan nan matasa, ya hora yara dayawa, bai taɓa jin wasu a ransa irin su ba!. Cike da takun jarumta ya iso wajen, kamewa suka yi suka sara mashi tamkar yadda suka saba. Saman stage ya haye, ba tare da ɓata lokaci ba ya ce. “1, 2, 3 start!” Cikin ɗaga murya.Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA…… “We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom’s call, for justice true, Our oath is strong, we’ll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!”.Bayan sun kammala rera taken nasu, ƙasa Captain ya sauƙa, jagoranci ya yi masu zuwa gym, dan yanzu kowacce safiyarsu tana farawa ne da gym kafin komai. Yana zuwa ba ɓata lokacin suka fara, a yanzu 500 push-ups suke yi in less than 15 mins, 500 sit-ups 300 burpees, kuma cikin zafin nama ba nuna kasala ko gajiya.Room 1 suna yi ma suna tafawa da juna, Captain ya ga sabon salo, dan kuwa idan suna yi sai su ce ɗaya ya hau bayan ɗaya, Leo ya ɗauki Noor a gadan bayansa, Zaysh ya ɗau Vash a gadan bayansa, watau yi haka ma ba wata wahala sai sun ɗauki abu mai nauyi. Dik Generals na sojojin nan sun shiga mamaki sosai gaskiya, musamman a kan canzawan Noor lokaci guda, hakan yasa suka tsananta sanya masu ido sosai. Bayan sun kammala push-up Captain ya sanyasu yin 200 squats da kaya a bayansu, wannan horo ana yi masu ne yadda zasu kware wajen iya ɗaukan ƴan uwansu a lokacin wahala, misali idan an harbi wani soja zasu iya ɗaukansa a bayan wuyan ko a kafaɗa ba tare da sun gaji ba, kun gane ai?Haka suka kwashi 1 hour ana koya masu yadda zasu gudu da koda gawar ƴan uwansu ne a filin yaki, aka dinga sanyasu ɗaukan kayayyaki masu nauyi, shiyasa zaku ga soja zai iya ɗaukar mutum dik girmansa a kafaɗa ba tare da gajiya ba, to sun saba, su yaku-yakunsu ma ɗaukan juna suke dik girmansu su ɗaura a bayan wuya kamar sun ɗauki kwali tsabar azaban horon ya bi jiki!.Bayan sun kammala wannan, wajen breakfast suka nufa, kamar kullum aka raba masu abinci, cikin natsuwa suka ci, yanzu an rage masu lokacin cin abinci, daga 30 mins zuwa 15 mins, dole ka kammala a 15 mins in ba haka ba ka ƙoshi, saboda horonsu yanzu ya ninku sosai shiyasa aka rage lokutan da basu da amfani sosai aka kara masu kan horo.Bayan kammala breakfast Captain ya ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi pain endurance test, ko kaɗan babu alamar gajiya a tattare da su, Leo da Noor sun haɗa kai, Vash and Zaysh sun haɗa kai.A wannan horo an sa su sun zauna a ƙasa ba tare da wani ya motsa ba na tsawon awa ɗaya, suna riƙe da bindigogi masu nauyi. Idan wani ya kuskura ya motsa, sai team nasu su fara daga farko. Ga ruwan da ake watsa masu daga sama dik dan kara masu azaba, ga nauyi bindiga, ba damar motsawa ko kaɗan, ko hannunka zai yanke saboda nauyi dole ka jure. A yau ne su Noor suka ga amfanin push-up da suke yi, dan shi ya karfafa masu hannayensu har suka iya ɗaukar bindigogin nan ba tare da sun motsa ba! Team nasu ita ce ta farko a fita wannan horo da nasara, sun yi murna, amma fa an ci kwakwa, ɗaukar bindiga mai cike da harsashe ba dik kai ba!. Waɗan da suka faɗi aka sanyasu suka fara daga farko, waɗan da suka yi nasara kuma aka ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi JUMPING FROM HEIGHT. Wahala kenan!Wajen wani katanga mai tsawon mita 20 aka kaisu, Captain ya ce suna da 10 mins dole su ko yi hawa katangar nan da gudu su tsallaka shi su dira ta baya!.Wai baku mamakin yadda sojoji suka iya dirowa daga wajaje masu tsawo? Shiga gida ta katanga baya basu wahala dik tsawonta, hakazalika zaku ga tun motocinsu bai gama tsayawa ba sun iya dirowa ƙasa da gudu, sun kuma iya hawa bene ta hanyar kakkama gini ba ta staircase ko kofa ba, to ga horon da ya koya masu irin wanna, dole su haye wannan katanga su dira. Dik wanda bai yi a kan lokaci ba kun san zai sake ne!.Ganin katangar da kyau Leo ya yi, a nan ya fahimci su Noor ba zasu iya ba, dan haka sai ya ce da Noor ya koma baya ya zo da gudu ya taka tafukan hannunsa da ya haɗa waje guda sai ya yi tsalle ya kama saman katangar ya haura sama. Captain dai yana tsaye yana kallonsu, dan a wannan waje basirarsu ta kwacesu ne, dole su koyi kowacce dabara su yi tsallaka kafin 10 mins.Ɗaure belt ɗin wandonsa da kyau Noor ya yi, baya-baya ya yi, da gudun gaske ya zo, cikin zafin nama Leo ya sanya gwiwansa ɗaya a ƙasa, sannan ya haɗe tafukan hannunsa cikin na juna. Noor yana zuwa ya taka tafukan nasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar tayasa ɗaga kafafun nasa, ya yi tsalle ya damki katangar. Cikin zafa ya haye tare da rike waist ɗinsa yana mai da nunfashi, saura sojojin sai faman gwadawa suke yi babu wanda ya iya, Noor shi ne na farko da ya fara hawa. Miƙewa Leo ya yi tare da komawa baya, cikin zafa ya zo da gudun gaske, ya taka tsakiyar katangar tare da kara karfin tsallensa ya damki sama. Haurawa ya yi ya samu Noor, bai ko kalli in da saura suke ba ya kama hannun Noor suka dira ta baya. Nan fa dayawan sojoji suka fara ɗaukar salon Leo, sai su zo da gudu su taka tsakiyar katangar su kama sama su haye. Captain yana mamakin irin baiwar Leo, kullum shi yake kawo masu salo na musamman, har ta kai in suka je wajen sabon horo suna jiran Leo ya fara, da ya yi kowa zai ɗauki salonsa. Zaysh, Unays, Vash and Juraiz matashin dake ɗakinsu Unays, su ne suka yi na biyun haye katangar, Juraiz jajirtaccen matashi ne, shi ma ɗan Naija ne, ya fito daga Kano ta dabo tumbin gwiwa, kun san kanawa dik abin da suka yi niyyar yi sai sun yi ne, kowa sai ya jirasu! Dan haka Juraiz ba baya ba!A yanzu dikka matasan sun haye ginin da salon Leo, Captain ya sanyasu suka dinga maimaitawa har na tsawon awa ɗaya, sai da suka saba sosai, a karshe ma kusan a tare dikkansu suka haye saboda an kware ya bi jiki.Daga nan aka wuce da su wani ɗaki mai matuƙar duhu dan a masu mental stress training, ɗaki ne da ko yatsanka ba zaka iya gani ba saboda tsananin duhu, haka aka rufesu a ciki na tsawon wannan lokaci, ga ƙara na harbi bindigogin dake tashi kusa da wajen, so ake yi a koya masu natsuwa a lokacin tashin hankali da wahala, su natsu su nemawa kansu mafita mai kyau, da yake kuma dikkansu natsastsun matasa ne sai aka samu abin da ake so, dan dik harbin nan da ake yi suna zaune hankalinsu a kwance, wasu ma hiransu suke yi, to kunnuwa sun saba da harbin bindigar ne ai!.Bayan awa Captain ya fitar da su aka wuce da su wajen da zasu yi rescue run. A nan ma ana koya musu wata dabara ce na yadda za su ceci abokanansu a lokacin yaƙi. An sanyasu sun sanya kaya masu nauyi a jikinsu, sannan su ɗauki abokin horonsu da suka yi kamar sun ji ciwo ba zasu iya tafiya ba, kamar an harbesu a kafa, Captain ya ce su yi gudu da su a bayansu na tsawon mita 500. Amfanin sanya kaya mai nauyi a jikinsu shine, a lokacin yaki zasu ɗauki bindigunsu, ga tarin alburusan dake waist ɗinsu, suma masu nau yi ne, sannan su ɗauki ƴan uwansu, kunga dole su sanya kaya masu nauyi yayin wannan gwaji.A wannan karon Leo yaki ɗaukar Noor, dan ya ce ya yi mashi kaɗan, bashi da nauyi! Dan haka sai ya ce Juraiz na ɗakinsu Unays ya zo. Ba musu ya je dan shi ma yana mugun yin Leo ba karya, dik wanda ya ce baya son Leo sai in hasada wlh, Juraiz kuwa bashi da hasada dan haka yana yin Leo!.A bayan wuya ya ɗaukesa, Vash ya ɗauki Noor, Zaysh ya ɗauki Ameer na ɗakinsu Unays, shi kuma Unays ya ɗauki wani katon matashi a room nasu yake shi ma, shi ne cikon na huɗunsu, suka yi ready, Captain na cewa go suka danna da gudu. Dikkansu su babu wanda ya faɗi, hakan na nufin zasu iya cetan abokansu a wajen yaki. Sosai Captain ya dinga sanyasu maimaita wannan horo, saboda yana da mugun muhimmanci a tattare da su!.Bayan kammala wannan, suka yi sallah suka yi lunch sannan suka shiga class, a ajinsu na yau an koya masu yadda ake haɗa bindiga cikin ƙanƙanin lokaci, ka shirya shi ka sanya bullets, sannan aka koya masu yadda ake goge bindiga idan ta yi datti, aka karantar da su me bullet! Me karancin gudun da yake yi a second, me karshen gudunsa a second, daga nan aka koya masu yadda ake rike kowacce bindiga. A class yau an sha artabo, dan ba kowa ya iya rike bindiga ya yi harbi ba, wasu idan bullet ya zo fita tafiya suke yi da bindigar gabaɗaya su faɗi kasa. Kun san da cewa in bullet ya zo fita da karfi jan bindigar yake yi? In baku sani ba yau kun sani, sai mutum ya jajirce ya rike da karfi in ba haka ba su wuce tare da bullet ɗin, karfin bala’i ne da fitar bullet, baku ga har wani hayaki yake yi idan ya zo fita ba?.Captain da kansa yau ya sha dariya yadda aka basu ƙananan bindigu su gwada harbi, sai dai Captain ɗin ya ga sun wuce tare da bindigar sun faɗi ƙasa, bullet ya jasu. Abin mamaki Noor bai faɗi ba, bullet bata ja shi ba, dik da bindigar koyar harbi daban, na yaki daban, amma ko na yakin aka bashi tabbas ba zata jashi ba, dan shi ɗin renon Leo ne!.Captain ya yi mamaki sosai, wai Noor ne da jarumta haka!……. Bayan sun kammala wannan class suka wuce wajen horon magana da ido, kullum sai an koya masu shi, saboda yana da mugun amfani a wajensu, yakamata ace suna da silent words wa juna!. A yanzu horar da su yana yi wa Captain mugun daɗi, saboda babu ragwaye babu mai sanya shi ciwon kai!…… Basu suka tashi horon yau ba sai karfe 7 kamar da aka saba. Suka yi sallar mangarin and Isha’i, suka yi dinner sannan kowannensu ya koma room ɗinsa. Suna shiga suka hau yin wanka. Bayan sun yi shirin kwanciya kowa ya hau neman gida. Shi kuma Leo ya kwanta ya ɗauko book ɗinsa yana bitan karatun da suka yi ɗazun, yana jinsu suna ta hira da gida ko a jikinsa. Da suka ishe shi sai ya ce dik su kashe wayoyinsu ko ya karɓa ya fasa! Daga magana ɗaya bai sake ba dik suka kashe wayoyin nasu saboda tsoronsa da suke ji. A takaice ya ce dik su fito da littafansu su fara karatu! Wani irin harara Zaysh ya dallah mashi kafin ya fito da book ɗinsa, a ransa yana faɗin. “Sai ya dinga yi mana magana kamar shi ne ubanmu, ba za’ayi karatun ba tin da kai ka haifemu”. A fili kuma dole ya fito da book ɗin ya fara karatu, dan yasan Leo baya ɗaukar wasa ko shirme, yanzu jikinsu zai gaya masu, ba duka ba zagi amma akwai horarwa! Ganshi da ɗan banzan kwarjinin da yasa suke shakkarsa.Haka ɗakin ya natsu tsit suka fara karatu, suna jiran 11 ya cika su saci hanya zuwa wajen horon dare da suka saba!. ————————🔥Sanye suke da sleeping dress mai zubin pj’s launin maroon, sun yi matuƙar kyau, dikkansu kwance suke a saman beds ɗinsu, sun saki gashin kan nan nasu har ƙugunsu. Arya tana practical a kan karatunsu na yau, amma gabaɗaya zuciyanta yana kan tinanin Leo da yau tsawon wata kenan da haɗuwarsu, basu sake haɗuwa ba, amma ya tsaya a dikka zuƙatan yaran GAT, da tinaninsa suke kwana suke kuma tashi! Su kansu basu san dalilin tinanin nasa ba!.Ta yi nisa cikin aikin da take yi na ƙoƙarin bin diddigi da kuma datsar wata camerar, shi ne karatun da aka yi masu yau. While ita kuma V tana can tana karance-karance labaran soyayya, a maimakon ta yi practical na abin da aka koya masu, ta tsaya biyewa soyayya. Manassa tana nata aikin ita ma na fannin likitanci, while Angelina ta kashe laptop ɗinta, ta ajiye shi a gefe, ta shiga bargo tamkar mai yin barci, wayarta ta kunna tana kallon film ɗin batsa a wayar, ita kuma tata bala’in kenan, tin bata kai ko’ina ba akwai ta da son sharholiya, ta iya kallon film ɗin batsa sosai, yanzu ba abin da bata sani ba, shiyasa ta matsu take son saurayi, ta ce sex zai yi daɗi tin bata ɗanɗana ba, wai a haka ma GAT yana mugun sa ido a kan yaran fa, amma ya yi sake idanunsu ya buɗe, wayayyu ne sosai, shiyasa uwa daban take, haka tarbiyarta ma daban yake, da uwar tana raye wasu abubuwan ba zasu yi shi ba. Batu na gaskiya Angelina ta fisu buɗewar ido a ɓangaren maza da son romance, ita kuma V soyayya da shagwaɓa, har da cewa ita namiji ɗan shagwaɓa zata aura, wanda zai dinga yi mata kuka idan suna romancing juna, ita kuwa Arya cewa ta yi bata ga namijin da zata so ba, suma masu zancen mazan basu da hankali ne, dan haka tana hana su V zancen soyayya, while ita kuwa Manassa komai ma daidai ne, idan anga dama ayi soyayya, idan ba’a yi bama matsalar mutum ne, ita dai karatu ne a gabanta.V dake ta faman sakin kyakkyawan murmushi ne ta ce. “Bloody i wish in samu masoyi like me yanzu, ku kashe juna da love and romance”…….. Manassa dake aikinta ne ta amsa da. “Aikuwa da an yi shirme, saurayi irinki to waye zai rarrashi wani idan ɗaya yana kuka? Nan in kika fara kuka sai daddy ya zo! Ai ke sai irin gangsters da basa dariyar nan ne zasu gyara maki zama”. Arya ce amsa da cewa. “Ke baki da wani aiki sai labaran soyayya ne? Ba zaki yi abin da zai amfani rayuwarki ba ko?”…… Turo baki ta yi kafin ta ce. “Aikinku kenan ai, ku baku san soyayya da shegen daɗi bane, ina zan ga jarumina, Angelie please ku nemo mun shi, zan faɗa mashi ina son shi! Ya zo in yi hugging ɗinsa, in yi kissing ɗinsa, huuuuuuu, I really like love and romance”. A shagwaɓe sosai ta faɗa. Siririn tsaki Arya ta ja tare da cewa. “For sure watarana wannan shauki ne zai gamasar dake! Ni sai na rasa a ina ma kike koyan wasu abubuwa”…… Manassa ce ta amsa da. “Arya, love fa akwai daɗi, there was a time da na kalli wani love film, they way suke son juna, I felt like ace ni ce”. Shiru Arya bata sake tankasu ba, saboda gabaɗaya gani take basu da aikin yi ne yasa, ita bata ga dalilin da zai sanya ta so wani namiji ba……… V ce ta katsesu da cewa. “Oh my God, bloody please ku ce masoyina a dik in da yake ya zo gareni”. Ta faɗa idanunta a kan laptop ɗinta tana rungumar Teddyn dake manne da kirjinta.”Ga masoyin naki ai a jikin roba”. A cewar Manassa. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki kafin ta amsa da. “Shi wannan ai special ne, nasan ba zan taɓa ganinsa ba bare har ya so yi, shiyasa ban saka a raina zan same shi ba, amma ba zan taɓa son wani kaman yadda nake son shi ba, hoooo look at his soft lips and his big-big sharp eyes, his hair, karshe ne shi ɗin”. Arya ce ta amsa da. “Dama ya za’ayi ki so wani kamar yadda kike son shi tin da har zanen tattoo na face ɗinsa kika je aka yi maki a baya, V you’re totally crazy a kan guy da bama a nan yake ba, check they’re product very well daga US suke, a ina zaki gansa, amma kin tashi kin je an zana maki face ɗinsa a baya saboda baki da hankali, yanzu idan kika samu boyfriend zaku yi aure ya gani fa? Me zaki ce mashi?”. Tana turo baki ta amsa da. “Dik boyfriend da zan yi sai na faɗa mashi ni fa ina son wani! Dan haka kada ya ji haushin zanen bayana”…….. Da sauri Manassa ta ce. “Ba lallai ma akwai wannan guy ɗin a zahiri ba, na fi tinanin zana shi kawai suka yi saboda ya dace da products ɗinsu, amma ke kinsan daga ganin wannan kyau ba na zahiri bane, kalli eyes ɗinsa fa, kamar na wancan guy da ya zo ɗaukarmu a school (Leo), they have sharp eyes mai rikitar da mutane, seriously babu wannan guy a zahiri, dan haka stop wahala your self and focus on what is very important in your life, in ba haka ba in faɗawa daddy, ni ko wancan Nirash ɗin ban gama yarda mutum bane!”. On a serious note ta yi maganar!. Wai kun san dik a kan waye ake wannan zance har ake cewa babu shi a zahiri? A kan hoton jikin STARS BODY LUSH, watau hoton Noor namu na amana, yaran nan a lokacin da suka fara ganin Noor a jikin man shafawan daddynsu sun yi hauka a kansa, V har mafarkinsa take yi kullum, su sauran da suka ce babu shi a zahiri sai suka cire son shi a ransu, ita kuwa V tsabar haukan son shi da take yi har da zuwa a zana mata hoton nasa ɗan karami a bayanta, ga shi ko sunansa bata sani ba, kawai tsantsar kauna ce, har ce mata su Arya suke yi bata da hankali tana son abin da babu shi a zahiri, ita dai bata sanya a ranta zata same shi ba, amma taki yarda babu shi a zahiri, ta ce tin da yana zuwa mafarkinta to akwai shi a zahiri!.”Ni Manassa ki kyaleni, ko babu shi a zahiri ni ina son shi har cikin raina, ina fatan samun babys irinsa, amma kun san me?”. Ta faɗa tana hura kumatu, ranta ya ɓaci an zagi jaruminta. Arya dai bata sake yin magana ba, ta cigaba da abin da take yi dan bata cika biyewa zancen da ya shafi soyayya ba idan suna yi, gani take shirme ne. Manassa ce ta ce. “A’a bamu sani ba sai kin faɗa”…….. Ɗan murmusawa ta yi har kyawawan fararen tas ɗin hakwaranta bayyana, ga giɓin wushirya mai bala’in kyau a tsakanin hakwaran. “Guys I really like this guy da ya zo ɗaukarmu a school, tun ranar ya shiga raina, kuma yana mun yanayi da pleasure ɗina shiyasa nike son shi”. Cike da shaukin soyayya ta faɗa. Dikkansu sai da gabansu ya faɗi jin ta ce tana son Leo, musamman Arya, da sauri ta ɗago ta kalleta, bata san time da ta ce. “Wancan banzan kike so? Shi yake burgeki?”……… Da sauri ya gyaɗa kai alamar e. Manassa ce ta amsa da. “For sure guy ɗin ya haɗu matuƙa, but meyasa zaki ce kina son shi?”. Kirjinta na bugawa ta faɗa. Siririn tsaki Arya ta ja tare da cewa. “Kowacce ta ti focusing a kan abin dake gabanta, ni bana son wannan hiran”……… V tana cigaba da rungume Teddy ɗinta cikin shauki ta ce. “Bloody bani da wani abin dake gabana face tinanin yadda zan sake ganin guy ɗin can, I think weekend zan shiga cikin barrack nemansa”. Dikkansu kirjinsu ne ya sake bugawa, Arya bata sake tsoma baki a maganar ba, ta yi shiru ta barsu da Manassa suna yi har time da daddynsu ya dawo, da sauri suka diro kasan bed ɗin suka nufi waje. Har Angelina mai kallan wancan abin sai da ya kashe ta diro da gudu.A parlon ƙasa suka ci karo da shi. Yana ganinsu hannunsa ya buɗe masu cike da tsantsar so da kauna. Da gudu suka tafi suka faɗa jikinsa suna mashi oyoyo, haɗesu ya yi ya rungume, yana jinsu har cikin ransa. Jim kaɗan ya ɗan raba jikinsu tare da kakkamasu suka wuce sama, kai tsaye room ɗinsa ya nufa dasu, sai faɗi yake yi ya yi kewansu, suma sai maimaita mashi suke yi sun yi kewansa. A saman bed ɗinsa suka haye suka zazzauna, shi kuma ya wuce toilet, hira suka fara yi jefi-jefi, Angelina gabaɗaya tana cikin shaukin romance na kallon da ta yi, har tsuma yarinyar nan take yi, while V na cikin shaukin soyayya mai ratsa gangar jiki na tina Leo and Noor da ta yi. Arya na cikin yanayin tinanin Leo da take cewa sai ta ɗauki fansa a kansa, ga shi kuma yasa da suka bar bags ɗinsu a wajen washegari a school suka sha bilala bibbiyu, takaicinsa ya kara rufeta. Manassa na cikin yanayin ko oho.A haka daddynsu ya fito sanye da bathrobe milk color ya samesu. Rige-rigen sauƙowa ƙasa suka yi, kowacce ta nufi closet ɗinsa suna faɗin su zasu zaɓa mashi kayan sakawa. Tsayawa ya yi a gaban mirror ya hau shafa STARS BODY LOTION ɗinsa. Dikkansu suka ɗauko sleeping dress kala daban-daban suka kawo mashi, kowacce tana faɗin. “Daddy nawa zaka sanya”. Yana murmushi mai ƙayatarwa, ya sauke tiger eyes ɗinsa a kan V dake rike da pjs irin na jikinsu. Hannu ya miƙa ya karɓi nata yana faɗin. “Bari in karɓi na Autata, tin da kune manya ku yi hakuri in saka nata, kunga kuma irin naku ne ai ko?”. Da sauri V ta rungumesa tana faɗin. “Love you my dad”……. “Love you all daddys baby’s”. Ya faɗa cikin shagwaɓa dan ya kwaikwayi muryar V ɗin ne. Murmushi su ukun suka yi amma ban da Arya da ita kafin a ga murmushinta dama sai an shirya. Juyawa dik suka yi suka mayar da kayan hannusu.GAT ya shiga toilet ya shirya cikin kayan da V basa, sannan ya fito suka wuce dinning room. Dinner suka yi cike da kaunar juna, sannan ya bisu room ɗinsu, a kan bed na V ya zauna dan ita ce auta, suka fara hira cike da kulawa, basa samun lokacinsa sai dare, shiyasa da daddare zai ɓata lokacin har karfe 12 yana tare da su a room ɗinsu suna hira, ya ja su a jiki, ya gwada masu kauna. V ta kwanta a jikinsa sai shagwaɓa take zuba mashi yana biye mata, suka ce suna son zuwa yawo a ƙasar waje, ya ce sai sun yi passing out zai kaisu dik ƙasar da suke so su yi sati guda kafin su fara aiki. Sai daɗi suke ji……. A yanzu na fahimci cewa a ɓangaren jami’an computer horon su Arya na tafi ne daidai da team na su Leo, kenan yanzu a tare zasu dinga aiki, misali idan za’a tura su Leo aiki tare da jami’an Computer to da su Arya zasu tafi kenan!…….. E to akwai case babba ma kuwa! ALLAH yasa kar garin ɗaukar fansa Arya ta basu wrong information ta ja a kashe kowa! Dan zata aikata wannan yarinya mai ɗan banzan zuciyan!.Ga shi dai GAT mutumin kirki, salihi jajirtaccen namiji, baya bin bayan karya, dik yadda yake son yaran nan nasa in dai sun yi rashin gaskiya tsab zai hukuntasu, baya bin bayan zalunci, ALLAH ya taimakesa yaran nasa dik na gari, Arya ce kawai mai riko da kafiyar bala’i.Sosai suka dinga hira, ba shi ya bar room nasu ba sai da dikkansu suka yi barci, ya bi ya rurrufesu da bargo, kowacce ya bata sumbata a kumatu cike da tsantsar kaunarsu sannan ya wuce nasa room ɗin ya kwanta cike da kewar mahaifiyarsu Arya a ransa! ————————🔥US. CRYSTAL PALACE.Ta sha barcin wahala sosai, a lokacin da ta farka sai ta kalli ko’ina duhu, a gigice ta tashi tana ihu, dan tana tsoron duhu sosai ga shi tana firgice na rashin uwa. Dirowa kasan bed ɗin ta yi ta fara laluɓar hanya tana kukan sunan Mammy ɗinta. Buguwa ta yi da bango, da sauri ta tashi tana murza forehead ɗinta tana kuma kuka. Laluɓe ta fara yi tana sanya hannunta a gaba, gaba ta dinga yi, bata ankara ba ta bugu da jikin wani abu mai kamar glass da bata san menene bane, miƙewa ta yi tana kuka tana sake laluɓe. Ta faɗi ya kai sau biyar kafin ta samu hanyar fitowa parlo. Nan ta ga haske, cikin kuka ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar tsakiyar parlon. Dakatar da kukan ta yi tana kallon uban kayayyakin dake tsakiyar parlon, shopping ne na dik wani abin da ɗan adam zai buƙata a room ɗinsa, harta kayan amfani na toilet, ita ma ga kayan kamranin STARS BODY LUSH, har da su shampoo ɗinsu an kawo mata.A gefe guda ga kayan kwalama kala-kala. Kallon jikinta, ba kaya sai towel, a ranta ta ce waye ne kuma ya zo ya rufe light na ɗakinta? Ganin babu mai bata amsa, kuma bata ga alamar motsin mutane a gidan bane yasa ta nufi wajen view na parlon. Jikin wall kusa da wajen akwai curtains control a wajen, da yake suna da irin shi a gidansu sai ta taɓa shi, ta danna open. Take curtains na view ɗin suka buɗe. Da sauri ta fara leƙe-leƙe, glass wall ne a wajen, ƙasa ta fara leƙawa wai ko zata g mammynta, ga gundun hawaye a fuska.Ta yi iya kallonta bata ga kowa ba, gabaɗaya C-P ɗin ma yau shiru ba wata motsi. Danna close ta yi curtains ɗin suka rufe kansu, ta dawo cikin parlon jiki ba kwari. Hannu tasa ta jawo echolac ɗaya cikin ukun dake jere a wajen, buɗesa ta yi, nan taga su rebon ne kawai a cike a ciki kala-kala na kama gashi. Rufewa ta yi ta matsa kusa da manyan, da kyar ta kwantar da guda ɗaya ta buɗe, kayyakin sakawa ne masu bala’in kyau da tsada. Abinku da yarinta, tuni ta fara murna tana jin daɗi tin ma ba’a ce mata nata bane. Wani haɗaɗɗen top white ta ciro, sai ta ɗauko ash jeans. Tuni ta hau shiri a cikinsu, a wajen ta shirya tsab, kayan sun yi mugun yi mata kyau kuma. Sai murna take yi ta ɗauko ɗayar echolac ɗin zata buɗe kekan ta ji wani irin gurnani mai firgitarwa.A miliyan ta ɗago kanta, a daidai lokacin wani ƙosasshen bujumin zaki ya sanyi kansa cikin parlon cikin tafiyar ƙasaita. Ai wani irin ihu da ta kurma tare da zabura ta miƙe tsaye, hakan yasa Zakin juyuwa da gabaɗaya jikinsa da kallonsa a kanta, suka ga juna ido cikin ido. Haba wani irin zunduma ihu ta yi tare da watsawa a guje ta bazama ba tare da tasan in da ta nufa ba. Ai da gudun gaske zakin ya rufa mata baya shi ma. Bata san in da ta nufa ba, bata san ya aka yi na sai tsintar kanta ta yi cikin wani ɗaki. Tsayuwa ta yi a tsakiyan ɗakin tana faman waige-waige, daidai lokacin zakin ya bango door ya shigo ɗakin da gudun gaske shi ma.Ihu ta zunduma, lokaci guda kuma ta ɗauke wuta diff, ta sulale ƙasa a wajen. Da gudu zakin ya yi kanta, daga bayansa ta cikin ɗakin wata murya ta ce. “Hero, come here”. Da karfi zakin ya juya, ɗakin irin dogayen ɗakin nan ne, ba faɗi sosai sai tsawo. Cikin zafin jini zakin ya yi kan wanda ya kirasa. Wannan mutumin ne dai da ya ɗauko yarinyar daga hospital, zaune yake a saman sofa, wasu rantsastsun sofa set ne a cikin room ɗin, a kusa da sofar akwai wani curtains masu shegen kyau launin dark ash da kamar sun raba ɗakin biyu. Guys ɗin su biyu ne suke zaune suna fuskantar juna, dikkansu kuma face ɗinsu sanye da nose mask, hoodie baka ce a jikinsu, sun sanya hular kayan, da alama tattaunawa suke yi.Jin motsin shigowarta yasa suka kai kallonsu a kanta. Nasan kuna son sanin su waye waɗan nan mutane! To a taƙaice bari in faɗa maku, waɗan nan shahararrun terrorist kuma gangsters ne da duniya ke haukar nemansu, but babu wanda ya san ainahin fuskansu, sunansu da ɓarnarsu kawai ake ji, su uku ne a team guda, ko muryansu babu wanda ya taɓa ji, IRON FIST shi ne takensu, dik in da suka aikata wani shahararren laifi sai sun bar tambarin IRON FIST mai ɗauke da hoton kan zaki, wannan tambari duniya ta rika makama wajen nemansu, an zana tambarin nan a ƙasashe daban-daban ya fi a kirga da nemansu, amma har yau an kasa fitar da ainahin zanen IRON FIRST na gaskiya, dan akwai wajen da suke covering in zasu bar tambarin. An yi binciken duniyar nan an gagara kamasu, to mutanen da wani lokaci basa zuwa aikata abu da kansu, suna daga ɗaki a gaban computer zasu yi abin da zasu yi. Dik kuma idan zasu fita aikata laifi suna da mask na team ɗinsu da suke sanyawa, mutane ne da basu da tsoro bama su santa ba, tsabar yarda da kai zasu iya shiga waje kai tsaye su aikata laifi ba tare da bindiga ko wuƙa ba! Ga bala’in saiti a fagen harbi, idan suka so kashe mutum tazarar mitoci a tsakaninsu suna iya harbinsa kuma ya same shi, suna iya harbin mutum a cikin mota mai tsananin gudu tsabar kwarewa, mutane ne dake amfani da ƙwaƙwalwa fiye da jami’an gwamnati, shiyasa aka gagara kamasu, tsawon shekaru an gagara gane dalilinsu na aikata manyan laifuka, kuma babu ƙasar da suka bari, dik karfin tsaronku suka yi ra’ayi shiga suke yi, da wayar mutum da ba nasu ba ma suna iya karɓa su datsi tsaron wasu tsabar kwarewa da yarda da kai, haɗarinsu ya zarce yadda ɗan adam zai iya tinani, suna da salon kisan mutum na musamman wanda dik wanda ya ga wannan kisa yasan su suka aikata shi, a shekarun baya su ne suka yi wa shugaban Amurka wani irin mummunar kisa suka kifar da gwamnatinsa, kowa kuma yasan su ne, amma an rasa hanyar kamasu, ku duba tsaro irin na shugaban ƙasa, amma suka shiga ta karkashin ƙasa suka kashesa suka fito, kwarewarsu yasa basa barin makama komai ƙanƙantarta idan suka aikata laifi! Ko a gida suke zaku samesu da nose mask, mutane ne kuma masu fuskoki da dama, saboda kwarewa basa amfani da fuska guda, kazalika yau zaku gansu da ido blue, gobe violet, jibi ash, suna iya canza komai nasu a lokaci guda, ainahin suffansu ne dai baya taɓa bayyana, dik kalar da suke canzawa na boge ne, basu taɓa fita da ainahin face ɗinsu ba, takan iya yiwuwa yanzu da suke cikin gidan ma fuskan boge ce, dan ba’a gane masu! Mutane ne basu da shaukin komai sai kisan kai da tada zaune tsaye! Basu da uwa basu da uba a wannan gida, su uku suke rayuwa! Kuma wani abin mamaki ɗaya daga cikinsu baya wani jimawa a tare da su, yana da yawan tafiye-tafiye, idan ya yi sati ɗaya da su, zai iya tafiya ya je ya yi sati a wani waje, ko suna da iyaye to sun ɓoye iyayen a wani waje ne suke rayuwa su kaɗai a nan, dukiyar da suka mallaka ALLAH ne kaɗai yasan adadinta. A takaice su waye su kenan, saura bayani zaku ji daga baya. Yanzu haka wanda Dr ta taimaka yana kwance a gadon asibiti, wanda ya ɗauko Seraph yarinyar Dr kuma babban amininsa ne, dama na faɗa maku su uku ne, to yanzu su biyun ne a nan, shi wancan yana gadon jinya, dan ya rasa jini na wuce misali. IRON FIRST basa magana, basa bari a ji muryansu sai su da junansu, shiyasa guy ɗin can bai tanka Seraph ba!…….. Watau akwai wani cakwakiya dake gaban a book ɗin nan! Hmmm! ——————-🔥Da gudu Hero ya bar kanta ya isa wajensu. Da hannu ya nuna mashi kusa da shi, kallon juna suka yi, ɗayan ya ce. “Champion who is this girl?”. ……. Kallon in da take ta wutsiyar ido ya yi kafin ya amsa da. “I don’t know her. It’s FT said I should bring her home, treat her well, give her everything she needs, but I must not let her see him again or even know that he is in the house when he recovers and returns, baya son sake ganinta kuma baya son ita ma ta sake ganinsa, kawai in kula da ita”. Shiru guy ɗin ya ɗan yi, kamar ba zai sake yin magana ba sai ku ma ya ce. “Amma hakan ba zai ja mana matsala ba?”…….. “Na yi tinanin hakan, but yarinyar bata da kowa, amma zan bashi shawarar ya kaita boarding school”…. Jinjina kai guy ɗin ya yi alamar shawarar ta yi kenan. Da haka suka cigaba da hiransu cikin yaren da ni na fassara maku, ba turanci suke yi ba, sannan maganarsu sam bata fita sosai bare a iya gane voice ɗinsu saboda nose mask da suka sanya!………. Ba su sake bin ta kan Seraph ba!Hmmmm akwaita kuwa! Yau kuma ta nan na faɗa ni Princess Teema!. To fatan dai kuna biye dani mu warware komai a tare!.STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

Back to top button