Uncategorized

Matar Makaho Part 21 complete hausa novel

 MATAR MAKAHO

Chapter 21

Zata fadi da sauri Ammar ya tarota cikin tashin hanki Ramadan ya bude firij inda ya gani a falon ya ibo ruwa watsa mata sukayi ta farfado cikin kidima take magana ina yake na tabbata d’an yusuf ne, don Allah ku taimaka ku kaini wajen sa na nemi yafiyarsa na tabbata muhammad ne, don salim baya kama da yusuf.

Da mamaki suka juya baya don yima Muhammad magana, sai kawai sukaga wayam babu shi ga kuma mamakin ina matan nan ta sansu.

Kuka take tana rokonsu su taimaka su kaita wajen muhammad, kwantar mata da hankali sukayi akan tayi hakuri ya koma inda suka sauka ne, kuma tare da yusuf suka zo, ai tana jin haka ta mike da sauri ta tsaya takalmi ta saka ta nufi kofar gida.

Ganin haka yasa su Ammar binta suna tambayarta ina zata?

Amsa ta basu akan gidan sarki zata wajen dasu yusuf suka sauka, jin haka yasa su binta a baya suna had’ata da Allah ta tsaya yanzun dai yana hutawa, amma ina bude get tayi zata fita daidai lokacin Alhaji suka dawo tsayawa yayi da motar sa yana tambyar zainab in zata? da mamaki don sam inba dalili mai karfi ba zainab sai tafi wata uku bata leka kofar gida ba.

Tambayarta yayi ina zata Amma ina ta kasa basa Amsa shuru tayi ta tsunkuyar da kai, Ammar dake gefenta shiyake sanar da uncle  insa ga inda zata, sata yayi ta koma amma kememmen Zainab taki komawa sai hawaye dayake bin fuskar ta, daka mata tsawa Alhaji yayi akan ta wuce ta koma ba musu ta juya tana kuka ta koma cikin gida, Ammar kam dariya abin ya basa watoh duk girman mace in batayi aure ba saikaga wani yaranta a tare da ita yanzun kamar Aunty zee ke kuka don ance bazata wani wajen ba.

Komawa ciki sukayi dukansu harda uncle in Ammar da mom, shiga  falon sukayi duka suka tsinci zainab na kuka a zaune zama sukayi baban ya fara rarrashinta don abin na zainab tsawa baya gyarasa.

Tambayar Ammar yayi cikekken bayani, Ba musu Ammar ya zayyana masa kome dayafaru da labarin su yusuf kuka zainab tasa tana sambatu akan kome ya faru dasu yusuf itace ummulkaba’isin kome daya same su.

Ajesu Alhaji yayi akan su zauna gobe daga shi harsu in saisu tafi wajen yusuf in tare.

Aiko washe gari da sassafe suka wuce gidan sarki Amma basuyi sa’a ba duk basanan sunje gidan su hafsa, waya Ramadan ya d’auka ya kira zulkifilu akan ya tambaya musu sunan unguwan da suke.

Bayan sun isa gidan da sallama suka shiga falon bayan an musu ido, zainab sai boye fuska take ganin sun had’a ido da yusuf dake mamakin ganinta da ubangari.

Zama ubangari yayi suka gaggaisa da juna anan ne ubangari ke neman yafiyar yusuf tare da rokonsa daya yafe ma zainab, duniya ta koya mata Hankali, duk da sun dawo Maiduguri Amma har yanzun batayi aure ba, kowa yazo wajenta sai tace bata so gashi yau tana da shekara 44 harta fara tsufa Amma shuru kullum cikin istigifari dake da nadamar abinda ta Aikata, ga mutuwar khairat daya shiga jikinta sosai don Allah yusuf da muhammad su yafe musu.

Daker aka samu muhammad ya yafe don yusuf kam a take ya yafe mata tare da neman izinin Aurenta, don zainab ta basa tausayi matuka tsawon shekara 44 ace batayi aure ba, yasan sonsa ke wahalar da ita duk da tsufa yaxo, Amma xuciyarta bai tsufa ba, ba musu Aka daidaita kome baban hafsa ma ya yafe ma abie, abin gwanin sha’awa su muhammad basu bar maiduguri ba saida aka saka sartin auren yusuf aka biya sadaki, Amma auren sai yusuf yaje nijar zasu dawo d’auren aure, duk wanda yaga fuskar zainab a lokacin zaisan lallai so ba karya bane don ta kasa boye farin cikinta.

Daga maiduguri Hafsa da kalamu dasu falmata suka wuce Abuja,saboda karatunsu, muhammad da Sumayya suka wuce Taraba harda  mahmah dasu dahdah, yusuf dasu ramadan sun wuce nijar daga Maiduguri.

Bayan komawar sumayya dasu Abie jalingo sukaci gaba da kula da jariransu yayinda muhammad ya kai khadija wajen hafsa tacigaba da zuwa makaranta daidai su tashi tafiya nijar in sumayya ta gama jego.

Kudi yusuf y sakarwa Al’ameeen a account ba kad’an ba, kamar yau suna zaune a falo su uku dashi da sumayya sai mahmah dake bawa na’ima madara gaggo na sallah a d’aki, hira suke anan ne muhammad ya kalli sumayya, ina so ki bani shawara matata cikin fulatanci yayi maganar sanin mahmah bataji.

Murmushi sumayya tayi tana kallon mijinta sai kuma ta basa amsa da hausa gudun kar su ware mahmah, “ina jinka dear”

Jin haka yasa mahmah mikewa ta basu waje.

Yauwa don Allah ki tayani nazari in sama wa yan uwana mafita don nayi nazari Abinda ke damun Adara abu biyu ne, akwai jalinci akwai bin jini na gado, akan halinsu shiyasa nake son na shawo kan lamarin nan kuma na rasa mafita ta ina zan fara?

“Gaskiya naji dadi daka ji a ranka Adara yan uwanka ne, baka kullace su a rai ba akan abinda suka maka ba, har kana nema musu tsira”?

Taya zan gujesu sumayya bayan dangin mahaifiyata ne, da kinsu ake da Abbajo bai yarda ya auri mami ba.

“Gaskiya ne ni a nawa shawaran abu na farko da zaka fara shine ka tarasu, kayi musu magana akan duk wanda yake da wance yake so koh wance take da saurayi tsayaye zaka aurar dasu, babu koh sisin iyayen su sannan ka gyara musu gidan tunda akwai fili saika ma samarukan d’akuna room and falo, suyi aure a ciki ka nema musu jari matan kuma asasu a islamiyya yara a had’a musu da boko, su kuma su inna ka basu jarin 50k  ga kowance su kama san’a, sai maganar shagari kaje ka sanar dashi akan ka basa shagon halak malak kaga zaifi samun natsuwa akan ya zauna da tantama tunda Ammar yace ya baka kyautane”

Gaskiya sumayya ngode matar Aljana Allah ya barmin ke baby, amma ya zanyi dasu bappa sulaiman?

“Ameeen dear, ni a ganina kamar daman ai suna da sana’arsu kadai taimaka wa mata da yara matasan zaifi in yaso daga baya saika basu abinda kaga ya dace”

Haka koh akayi washe gari muhammad yaje gidan adara kuma ya sanar da shagari ya barmasa shagon kyauta,  yaron har kuka yayi gwanin tausayi, sannan yanzun yasan khadija tafi karfinsa shiyasa ya fara kula wata yarinyar school nasu dake matsa masa.

Takardun makarantan sa muhammad kawai  ya d’auka a dakinsu, sauran kayan d’akin ya baiwa matan gidan Adara kyauta harda na kitchen.

Kafun wata d’aya duk samarin gidan adara da suka kai aure duk sun fitar da mata, haka ma matan don daman suna son auren, rashin kudine kawai, mazan ma wa’inda basu da budurwa jin auren bati da za’a musu yasa su neman yan mata cikin lokaci kankani, gashi ansa yara a boko ansa mata a islamiyya harda mazan ma.

Anyi bikin gidan Adara na gani na fad’a wanda ya samu hallartar jama’a da yawa kowa na tofa Albarkacin bakinsa, akan muhammad da Halakcin daya musu.

Sumayya ta kammala wankan jegon ta sati d’aya kenan, yau tun safe daga ita har muhammad in suna cikin farin ciki,adalilin khadija da kalamu da zasu zo yau don anyi hutun makaranta Khadija an kammala ss 1 zasu tafi 2, gashi yau daga ita har kalamu zasu zo Taraba tun asuba suke sanar dasu akan zasu bi fly, wanka sumayya tayi goggo tama yaranta wanka suka shirya cikin shiga ta Alfarma harda muhammad zasu je gaida maman Ammar, daga nan zasu bi Airport d’auko su Kalamu 4:00 na yamma.

Dayake yanzun muhammad ya iyya tuki shiya d’aukesu a motar zuwa Gidan su Ammar, suna fita a motar dayake zuwan bazata sukayi basu sanar da Ammar zasuzo ba, tsayawa muhammad yayi a tsakar gidan yayinda sumayya ta wuce ciki rike da na’ima ta bar masa na’ifa  da sallama ta shigo falon Amma babu kowa shuru kakeji,zama tayi koh masu gidan zasu fitoh Amma har minutes biyu bataga kowa ba, gashi Al’ameen sai kiranta yake akan yajita shuru saboda shi baya shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba.

Mikewa tayi ta nufi wani kofar dake gefen falon don a tunaninta koh dakin su maimuna ne a falon harta kama handle in kofar zata bude sai kuma ta dakata jin maganar dake tashi a d’akin.

Muryar hajiyar Ammar ke magana, yanzun Ammar kanada wance ta fini ne ka zauna kana cutar da kanka ni bangane kanka ba gabaki d’aya ka chanja yau ciwo gobe lafiya?

Ammar ne ya bata Amsa, Mom babu fa abinda ke damuwa kawai dai banajin dadi ne.

Wani irin bakajin dadi, abinda ke damunka harda tunani da damuwa ba haka kake ba Ammar  nice fa na haifeka?

Mom daman wallahi na jima ina son khadija sai kuma yayi shuru bai karasa ba 

Wace khadijar?

Kanwar Al’ameen

Toh sai akayi yaya cewa tayi bata sonka?

Ah ah mama ban fad’a mata ba,daman naso na sanar da sumayya maganar sai kuma bakina yayi nauyi kar tace daman da wani manufa nake taimakon su, gashi banason yarinyar ta rainani.

Gyara zama mom tayi yana kara kallon Ammar tun ba yauba tasam d’an nata akwai son girma.

Toh shine ita da Auntin nata suka gudu Abuja ba tare da na zayyana mata abinda ke raina ba, kuma yanzun  kawai saina ganta da yaron nan kalamu kanin sumayya, kinga yanzun ai babu halin nace mata ina sonta tunda yanzun soyayya suke koma na fahimci tana son yaron.

Ammar ka bani mamaki wallahi ita tace maka soyayya suke?

Hamma mom kowa yagansu yasan masoya ne kuma nasan koh da ba sonsa khadija take ba Albarkacin sumayya zata yarda ta aure kalamun bare ma tana sonsa.

Kaga Ammar kafito ka sanar da yarinyar nan kana sonta bakasan me Allah zaiyi a lamarin nan naku ba, ka kwantar da Hankalinka kaji inso samune ma ka shirya kaje abujan?

Mom muhammad ya sanar dani khadija na zuwa.

Toh maza ka tashi ka shirya samun ta ganka tsaf dakai kabi yayanta Airport gobe kuma sai kaje gidan su ku gaisa kaga saika sanar da ita Amma ka dubi yanda duk kabi ka rame……..

Jin abinda suke cewa yasa sumayya sauri tabar bakin kofar, jin alamun mom zata iyya fitowa da sauri ta bude kofar falo ta fita waje, muhammad dake tsaye a rumfa har yanzun rike da babyn sa, dan yanzun sunyi wayo sosai,ya tambaye ta Lafiya tun d’azun Ammar bai fito ba?

“Muje kawai ba kowa a gidan”

Da gaske?

“Don Allah ka shiga mu tafi gidan mu pls nace maka basa nan”

Ba musu muhammamd ya shiga motar yaja suka wuce gidan su sumayya.

Yad’an jima a gidan kafun kiran Ammar ya shigo wayarsa, sallama yama su dada ya wuce, bayan fitar Muhamamd ne dada ke sanar da sumayya akan ta kara ma abie magana akan Amina(goggo)ya aureta don ita hankalin matar ya burge ta, Amma duk yanda dada tayi akan ya yarda Ya nemi Amina tunda dai bata tsufa ba, da yarantanta Amma yaki Amince wa.

Sumayya karan kanta taji dadin Abin don babu shakka goggo macece ta gari duba da zaman da suke da ita yanzun a gida d’aya sam bata da dumuwa.

Sumayya ta samu Abie akan maganar daker saida takai ruwa rana kafun ya Amince da zancen,  A ranan dada ta sasa dole sai ya wuce gidan su Al’ameen sun daidaita da goggo tunda yanzun yaran basa gida sai mahmah ne kawai.

Muhammad da Ammar su sukaje suka d’auko su khadija a Airport gidan su Abie suka sauka daman sumayya na gidan sosai suka musu tarba ta musamman, Sannan a nan suke xancen Abie ya tafi zance gun goggo, aiko muhamamd yaji dadi don daman tunanin da yake kenan in ya tafi karatu abroad kamar yanda uncle zulkiflu yace masa next month zasu tafi America an sama masa gurbin karatu harda sumayya da yaransu don gida yusuf ya kama musu ashan haya, yanzun ma bikin Abbajo suke jira. 

Lokacin da abie ya dawo sosai yayi farin cikin isowar d’an nasa hira ne ya kara barkewa a tsakaninsu sai dare su sumayya suka tashi tafiya, kiran kalamu tayi da Khadija a compound ta tambayesu shin soyayya suke kuma su fad’a mata tsakanin su da Allah?

Dariya suka sake a tare sannan khadija tace wa sumayya ai tsakaninta da kalamu babu zancen soyayya asali ma Abota ce kawai da shakuwa don kalamu kamma yana da budurwa yar school nasu sunsha gaisawa da khadija a wayar Kalamu.

Hakan sosai yama sumayya dadi sallama sukayi da yan uwanta.

Sun isa gida muhammad kam kwanciya yayi ya barsu da khadija anan sumayya ke sanar da ita Zancen sonda Ammar ke mata, da kuma bata shawarwari da tuna mata irin Alkharin Ammar a karesu ya cancanci ta sosa koh Albarkacin Halakcin sa, saida ta tabbatar jikin khadija ya mutu murus kafun ta mata sallama ta wuce d’akin mijinta khadija kam tare da mahmah zasu kwanta.

Washe gari da safe bayan sun karya Al’ameen ke tambayar ta dalilin sasa su bar gidan su Ammar bayan kuma Ammar yace masa suna nan,sumayya ke sanar da muhammad zancen Ammar da abinda ta jiyo suna tattaunawa sosai muhammad yayi murna ba d’an kadan ba, haka mahmah khadija kam kunyane kamar zai kasheta, especially jin muhamamd ya shirya ya fita wai kar Ammar yazo ya samesa a gidan tunda wajen khadija zaizo.

Sumayya da khadija kitchen suka shiga bayan matsawa khadija datayi kafun ta yarda, suna aikin girki yayinda mahmah da goggo ke falo suna rirrike da yaran sumayya.

Wayar mahmah ne yayi kara a d’aki mikewa tayi da na’ima a hannunta ta shiga dakin ta d’auko wayar, ganin nabila ne yasata d’auka da sauri.

Ta bangaren nabila jin mahmah ta dauka jiki a sanyaye tace hello

Kedai nabila anyi yar banza, sallamar ma bazakiyi ba sai wani d’an banzan hello wai gaki baturiya koh?

Yi hakuri mahmah Assalamu alaikum

Amsawa mahmah tayi tana tambayar nabila lafiya?jin muryarta cike da damuwa

Dada kewarku nake yaushe akki (muhammada)zai dawo?

Toh watoh shi kike kewa kenan banda ni?

Yi hakuri harda kene mahmah

Toh make damunki nabila in baki fad’amin ba wa zaki fadawa?

Mahmah wallahi nifa son Akki nake don Allah kisa baki a maganar nan ki sanar da abba kice ke kikeso a had’amu ki taimaka mini mahmah………

Wani irin magana ne haka nabila?toh nidai baza’ayi wannan haukar dani ba, kinji na fad’a miki taya yaro da matarsa koh sanin dadin aure basuyi ba, gani tsohowar banza nazo nasa bakina a sha’aninsu salon nayi bakin jini a wajen baiwar Allah, yarinya na ganin girmana najawa kaina raini wallahi da sakel ki barni na mutu da mutunci na.

Kuka nabila ta sake cikin maganar shagwaba tace, ni shikenan babu inda zanje naji dadi,  dedena naje mata da zancen zagina tayi kema shine xaki mini haka?

Jin abinda tace yasa mahmah kashe wayar ta aje ta fita a d’akin.

Ammar yazo sun gaisa da khadija kuma ba laifi ta sake jiki dashi kad’an, kuma yana samun hankalinta, Amma ba karamin kunyar muhammad yake jiba duk lokacin da zaizo sai ya tambaye khadija a waya yayan ta na nan intace eh tofa ba zuwan zaiyi ba.

Bayan sati uku Ayau ne dubun Al’umma suka shaida d’aurin auren sarki yusuf mutallaf tare da Amaryar sa zainab Rabi’u ubangari sai kuma Abdulsalam Abdul’Aziz shugaba da Amaryar sa Amina Ahmad Adara, d’auren auren da ya samu halaktan manyan mutane daga nijar har nigeri’a tabbas yan uwan zainab sun nuna mata gata a bikinta.

Bayan d’auren Auren ne mahafin Ammar ke wa yusuf zancen khadija, wanda yace sai dai aje nijar ayi batun Auren tunda canne mahaifarsu kar yan uwa suga ana musu wariya.

Su sumayya da muhammad harda khadija ayau sukabi gida gidan yan uwa domen musu sallama, washe gari taje abuja tama mahaifiyarta sallama zasu tafi nijar wajen dangin mijinta, kuma daga wajen zasu wuce America.

Ayau ne sumayyya dasu khadija da mahmah tare da tawagar sarki da Amaryar sa,suka nufi nijar, sun samu kyakkyawar tarba, saidai fa sumayya ta fuskanci sauyi a wajen nabila wanda hakan yasata shawa nabila mur, ganin duk lokacin da taga Al’ameeen zatana wani kwarkwasa shikam baima nuna yasan tanayi ba, ga lawiza da kishi ke cinta, Amma dai ta kwantar da hankalinta ganin yanzun tana samun kulawa a wajen mijinta fiye da da.

Nabila tayita nacewa mahmah akan zancen ta da muhammad, wanda abin yasa mahmah tarar yusuf da zancen, kai tsaye yace mata, mahmah banki bin umurnin kiba amma mama inkin duba duk abubuwan da suka faru Nine na fata ballo ruwan, da ace nayi biyayya ga mahaifina da duk abinnan bai faruwa ba, duk da bawa baya wuce kaddararsa mama bazan iyyama muhammad wannan zancen ba,A tausayawa yaron nan yasha wahala A rayuwar sa yanzun lokacine daya kamata Ya huta, duba da irin halakcin da yarinyar nan ta masa bata cancanci haka ba, in shine ya taso da zancen aure bazan hanasa ba, Amma mama bazan iyya tikasta masa ba kiyi hakuri bawai don yana d’ana ba, zaki iyya tuntubarsa duk Abinda ya yanke shikenan.

Jikin mahmah yayi sanyi kuma taji shawaran da d’anta ya bata don/a dalilin Auren dole yusuf yasha wahala, hakan yasa bata ma tinkare muhammad da zancen  ba.

Gidado da badaru dayake ba boko sukayi ba,  kuma yanzun sun wuce shiga makaranta, yasa sarki bada umurnin a sasu a islamiyya,  da kuma yaki da jahilci koh karatun hausane da turanci su iyya,ya bude musu manyan shaguna a kasuwa,in sunje boko sun dawo sai kuma su tafi shago, asabar da lahadi suje islamiyya.

A kasuwa gidado ya hadu da indo kanwarsa na bara, cikin wani irin yanayi ya tisata har inda suke da zama, aiko suna zuwa saida yayi hawaye ganin wani kazamin waje kusa da bola innarsa ke rayuwa gata a kwance ba lafiya ga yarsa cikin datti ,sai abinda indo tayi bara ta sama musu, d’aukar su yayi wanda a lokacin inna koh sanin wake kanta batayi ba.

Sarki a washe garin ya tura su saudiya da inna,saboda ciwonta ya kazanta blood Cancer ne, yayinda indo ke zaune a gidan sarki tare da lantana karama.

Muhammad da sumayya sun wuce America tare da yaransu suna mai kewar kasarsu da yan uwansu.

Bayan tafiyar su akayi auren Gidado da nabila sai badaru da wata yarinya yar tsohowar unguwansu, sarkin shayi ma Yusuf ya had’asa da wata bazawara an had’asu aure.

Jikin inna yayi sauki inda sarki yasai musu gida ita da indo da yar gidado , d’aya shashin kuma gidado ne da nabila, dataga ba sarki sai Allah ta aure sa abinta.

Su sumayya basu dawo ba saida sukayi shekara d’aya, lokacin auren khadija da Ammar sukazo, khadija tayi weac dayake har lokacin tana Nigeria a abuja wajen hafsa, yayin da yaran sumayya suka cika shekara 1 da watanni a lokacin kowa yaga sumayya da muhammad sai sun basu sha’awa, gaskiya ne mahakurci mawadace, mai hakuri yana tare da riba, sannan duk mai biyayya ga iyaye zaiga Amfaninsa wata rana.

Ana bikin Ammar da khadija suka koma wajen aikin Ammar a maiduguri bayan aure ya maidata makaranta, don result nata yayi kyau sosai, su sumayya sun koma America bayan biki.

***************

Bayan wasu shekaru………

Wani matashin magidanci ne tsaye a wani hadedden compound mai d’auke da shuke shuke mai ban sha’awa, sanye yake da kakin sojoji a jikinsa wandone da riga, kansa ba hula sai gashinsa dake kwance baki kirim yana sheki, yayi farine tas yayin da idanunsa ke d’auke da bakin glass, dukar da kansa yayi yana kallon agogon sa mai masifar tsada,  dake hannunsa d’an yamutsa fuska yayi hade da dan sakin tsiririn tsaki,ganin 7:21pm Amma har yanzun gimbiyar tasa bata fitoh ba bare yaransa, jin karan bude kofar falonsu da akayi yasa sa saurin d’agowa.

Sanye take da siket baki  mai kauri yana nan kamar pencil Amma ba’a tsaga baya ba,sai takalmi mai tsini a kafarta dake d’auke da socks baki, shirt ne a jikinta white mai botur da dogon hannu, wanda tayi stokin dashi, Have sunnah ne a wuyanta baki, da agogo fari a d’aure a farin tsintsiyar hannunta, sai jakan office dake rataye a hannunta d’aya Tabar daya hannun na lilo, fuskar nan nata yayi fayau  babu kwalliya alamu dai jin dadi ya samu waje, rike take da wani kyakkyawan yaro fari yana sanye da uniform na primary bazai wuce shekara 5 ba, ga wani yaron na binta a baya zaikai 7 shima yana sanye da uniform hannunsa d’auke da jaka d’aya hannun kuma lunch-box nasa.

Da sauri ta kara hanzartawa ganin fuskar mijin nata a hade, don tasan tabbas sun sasa jira don yau dai sun makara.

Yanzun ke kullum in zamu tafi aiki da safe sai kin sani lettin kike jin dadi, ki duba yanzun minutes 30 ina tsaye ina jiranku?

“Don Allah kayi hakuri dear wallahi neman socks in na’ima nake wai bataga d’aya ba”

Toh surutun ma ai ya cinye lokacin daya saura manan, yace yana kamo yaron dake hannunta ya bude seat back ya ajesa, kallon mai shekara bakwan yayi, Au kaima salim(takwaran salim marigayi, muhammad ya hana a masa inkiya yace a barsa da sunan sa)so kake na d’aga kane koh me? kana tsaye.

Washe fararen hakoransa yayi cikin dariya ganin yau ran baban nasu a bace, yace, sorry Dady.

Shiga gaba sumayya tayi ta aje jakanta akan cinyarta da mamaki Al’ameen yake kallonta, wai sumayya ina sauran yaran ne?

“Au wai basu shiga bane tare fa muke futowa dasu”

Kinsan Allah sumayya yau in kikayi tsiya sai kija mota da kanki tunda dai naga kowa nada shi, ya fad’a a hankali yanda yaran bazasu ji ba.

“Kayi hakuri toh” kawai tace tana fita a motar daidai lokacin wasu yaran mata da zasukai shekara 10 masu tsananin kama da juna,  gasu kyawawa sanye suke da uniform suna gudu da school back a hannu d’aya nabin d’ayar da gudu.

Da sauri sumayya ta kalli wance ake binta da gudun, tazo ta makale  a bayan Dadynsu,”Na’ima mekika mata”?

Momy wallahi babu abinda na mata.

Kallon na’ifa dake hawaye a gefenta tayi,  tana tsaye batabi na’ima bayan dadyn sun ba” meta miki kika biyo ta”?

Wallahi momy colour nata d’auka guda hudu,  kum drewing zanyi dashi fa.

Ke na’ima ina naki colour da zaki d’auka mata nata?

Dady toh banga nawan bane bafa.

Da sauri sumayya ta karbi maganan jin Amsar data bawa muhammad”Daman ke haka kike kome naki ba’a gani, kina ganin da safen nan harkin batar da socks naki daker na gane inda kika aje, kome naki baya lastic wannan biro in aka saima yar uwarki sai yayi 1 month tana amfani dashi, amma ke koh kwana bayayi sai kice ba pen ah ah pen ya bata, don haka oya bata colourn ta koh na saba miki”?

Ba musu ta bude jakanta ta mikawa na’ifa abinta, sai kuma ta fashe da kuka.

Muhammad dake tsaye ne ya dubeta, toh wai kukan na menene?

Dady kuma fa bangama drewing ba gashi uncle yace duk wanda baida colour waje zai korasa bazai masa makin ba.

Ina dai akan colour ne?muhammad ya tambaye ta.

D’aga masa kai tayi alamun eh.

Toh muje a hanya saina sai miki sabo koh?yanzun ku shiga mu wuce mun kusa makara.

Dady nimafa bani da calculator?

“Da sauri sumayya ta dubi yaron ta, kaji tsoron Allah khaleefa(yusuf) ba jiya naga calculator a jakan ka ba”

Momy Abokina kullun sai uncle ya bugesa wai bayida calculator, shine na tambayesa mai yasa ba’a saya masa ba, wai Auntin sa(step mother)in dadynsa ya basa kudin saita kwace, shine na basa kyautan nawa jiya.

“Masha Allah yaron kirki haka nakeso Allah ya muku Albarka”

Gabaki d’ayansu suka Amsa da Ameeen .

Jan motan muhammad yayi mai gadi ya walgale musu makeken get nasu suka fice.

Sai da suka bi ta bookshop ya sai musu abinda suke bukata, yaran ya fara saukewa a school, kafun ya kama hanyar bank da sumayya, tun a hanya ta makala ID card nata a wuya, suna isa bank ta sabi jakanta sukayi sallama ya wuce  wajen aikin sa.

Misalin karfe 4:30 na yamma muhammad ne zaune a office yana aiki, yaji ring na wayan sa kamar bazai d’auka ba don aiki yake mai muhimmanci,d’auka yayi yana kallon mai kiran nasa da sauri yayi picking yasa a kunne,Assalamu Alaikum

Ta d’aya bangaren Ammar ya Amsa wa’alaikumu salam, Captain muna fa Airport azo ya d’auke mu.

Da sauri muhammad ya mike cikin mamaki yace What? kana nufin kun shigo Lagos koh note’s babu?

Surprise muke son muku.

Amma gaskiya ka kyauta gamunan zuwa, suna yanke wayar neman wayar sumayya yayi ya kirata

sumayya dake zauce akan kantan customer care tana aiki taji wayanta na ringing d’agawa tayi tasa a kunne ganin sunan maikiran nata, “Hello Rabin Raina” 

Hello sweetheart kin koma gidane?

“No Rabin Rai yanzun nake kokarin fita, musa driver na haraban bank yana jirana”

Ok kice masa ya wuce dasu salim, ke ki jirani ina zuwa?

“Lafiya dai naga kace mini yau sai 6 zaka dawo kana da aiki”?

Lafiya yanzun Ammar yake sanar dani sun shigo lagos suna Airport.

Ok saika zo tace tana yanke wayar, number musa driver ta kira ta shaida masa ya wuce kawai gida, sannan yacewa bahbah(tsohowar mai Aikinsu)ta kara wasu abubuwan cin zasuyi baki.

Ba’a jima ba da wucewar musa saiga muhammad jakanta kawai ta d’auka ta shiga motarsa suka wuce Airport, suna isa Jakanta sumayya ta bude ta zaro Abayan ta sakawa tayi daman akwai have sunnah a  jikinta dukansu suka sauka a motar waya Al’ameen ya d’aga ya kira Ammar.

Tsaye suke suna duduba masu fitowa, daga nesa sumayya ta hango Khadija da katon cikinta a gaba tayi kyau kamar ba khadin goggo ba hutu dajin dadi sun ratsa ta, sai Ammar dake rike da hannun yaran su biyu mace da namiji,macen baka kamar babanta sabanin na mijin dayake fari, da sauri sumayya ta dagawa Khadija hannu da sauri suka karaso garesu da gudu, yaran suka rungumi muhammad suna masa oyoyo uncle da murna suka tattaru sai gida.

Suna isa gida suka samu yaransu a tsakar gida, bahbah ta musu wanka,  suna zazzaune a gaban malamin su dake can gefen flowern tsakar gidan, ai lokacin da suka gu momynsu ta sauko a mota da Ummi(khadija)gasu Amira(Aisha) da mukaddas yasasu  rugawa da gudu suka nufesu da gudu, duk irin kwala musu kira da ustax keyi, ina sunyi gunsu da gudu da sauri suka rungume yaran suna murna.

Koran su sumayya tayi hardasu Ameer suka wuce wajen karatu, tace sai ustax ya tadasu sai su shigo duka.

Suna shiga cikin part daban sumayya ta sauke su khadija da mijinta, ta basu waje su kimtsa itama d’aki ta shiga ita da muhammad.

Bayan mangariba zaune suke akan daining dukansu suna cin Abinci, Ga yaransu a zazzaune Suma ana ci dasu, hira ake na yaushe gamo, kallon sumayya khadija tayi.

 Aunty Gaskiya shagunan ki sun habbaka last months munje jalingo, nida maimuna mukaje shagon gaskiya nasha mamaki ganin harda saloon ga gyaran jiki duka?

“Wallahi kuwa khadija kinsan yanzun shago hudu nake running Na make-up saloon gyaran jiki, lalle kuma gaskiya Alhamdulilh matar shagari na iyya kokarinta yarinyar ta burgeni akwai Amana”

Gaskiya ne Aunty nima na yaba da nutsuwar Rufaida.

“Ai shiyasa na bar mata kula da shagunan a hannunta sannan ita ke iban ma’aikata da masu training”.

Toh Allah ya kara budi.

“Ameen khadija waini ina labarin kamila ne”? 

wallahi aunty tadaiji sauki yanzun ba kadangarun sai daifa Abin ya taba kwakwalwanta.

“Toh Allah ya sauwaka,Yajikan momy(safina)da rahama”

Ameen suka amsa dukan su,bayan sun gama cin abinci Yaran suka wuce ciki yayinda su sumayya ke hira falo, sallan isha’i sukayi sukaci gaba da zaman falo ana hira.

Da gudu Na’ifa take saukowa daga upstair hannunta d’auke da system in sumayya tana  kwala mata kira ga sauran yaran na binsu  baya.

Da mamaki sumayya ta kalleta ganin vedio call suke da mutanen nijar, karban system in tayi ta aje musu akan center table dake falon,  duk suna zazzauna akan kujeran da take gaisawa suke da su nabila indo Aunty zainab da nana(Aisha takwaran mamansu muhammad)sai muwaddat dake rike da sabuwar jaririya a hannunta, gaggaisawa suke tare da mata barkar haihuwa akan basu samu zuwa ba cikin khadija wata 8 amma insha Allah zasu zo auren muhibbat.

Bawa su muhammad da Ammar system in sukayi suma suka gaisa da yusuf dake cikin iyalansa cikin farin ciki don yara biyu zainab ta haifa masa Aisha da muhin, sosai akayita hira harda mahmah data kara tsufa sosai ga lawiza duka don yau akayi sunan muwaddat duk suna hade.

Sai kusan 9 sukayi sallama khadija da mijinta sukayi part da suke sauka in sunzo, dayake yaransu dasu Na’ima zasu kwana, had’a kansu sumayya tayi har bedroom na maza wanka ta musu dukansu tasa musu kayan bacci ta kwantar dasu, tufa masu Addu’a tayi taja musu kofa, d’akinsu na’ima ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu Amira dayake duk zasu iyya ma kansu, Addu’a tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta.

D’akin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani d’an iskan kayan bacci riga da wando jikinta sai kamshi yake ta wuce d’akin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga.

Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa.

Da sauri sumayya ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje d’aya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Rabin Raina menene sirrin ne kullum dad’a kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki.

Murmushi sumayya tayi sai kuma ta tuno wani abu cikin dariya tace,kai menene haka?

Dariya ya sake tuna masa da ranan su na farko, shima Amsa ya bata, yi hakuri gado nake nema zan kwanta ne?

Itama ta sake basa Amsa, wallahi bazan kwanta dakai gado d’aya ba gadai kujera acan jeka kwanta.

Gabaki d’ayansu dariya suka sake a tare cike da farin ciki suke romancing na juna, hannu muhammad yasa ya kamo blanket in ya lulubesu.

*Alhamdulil!!!!!Alhamdulilah!!!!!!!! Alhamdulilh!!!!! nagode Allah daya nuna mini wannan rana cikin koshin lafiya, harna kawo karshen labarin matar makaho, duk wanda nama ba daidai ba ina neman afuwarsa*

*MATAR MAKAHO FAN’S INA MATUKAR ALFAHARI DAKU, DON DA KARFAFAWARKU  NA TAKA WANNAN STEPS DANAKE KAI AYAU, WA’INDA NAGA COMMENTS NAKU DA WA’INDA BANGANI BA WA’INDA NAMA REPLY DA WA’INDA BANMA WA BA, ALLAH YABAR KAUNA INA GODIYA*😃

*SANNAN INA MAI MUKU ALBISHIR HADE DA SANAR DAKU SABON LABARI NA DAKE TAFE MAI SUNA*

🏵 *ALKAWARIN MASOYA* 🏵

*WANDA NAKE DA TABBACI HADE DA YAKININ ZAI MATUKAR KAYATAR DAKU INSHA ALLAH*😎

✨Ruqeenjalal ke muku sallama✨

    Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey

Whatsapp Number 08138873799

Visit https://aihausanovels.com.ng For More Complete Documents

Back to top button