Uncategorized

Maryama Book 1 Complete Hausa Novel

 

Ɗanɗano

KHALEEFA BIN ZAYED AL NAHYAN STREET ABU DHABI CITY  (DUBAI).

Katafaren anguwa ne da ke cikin babban birnin hadaddiyar daular larabawa wanda aka fi sani da dubai, anguwa ce mai dauke da rukunin gidaje masu kama da aljannar duniya,…

Lumshe kyawawan fararen idanu na nayi, na dade ina jin yadda ake yabon kyawun zubin hallitar idanuna mutane da dama idan sun tashi yabon kyan hallita ta su kan kirani da mai idon madara tsabar irin hasken da kyawun da Allah ya bani, amma a halin da na ke ciki yanzu sabanin kasancewar su launin milk idanun sunyi jajur kai kace attaruhu aka daka aka watsa cikin su ko kuma na kwana uku ina kuka ba tare da tsagaita wa ba, saidai ba ko daya daga ciki tsabar tashin hankalin da na ke ciki ne ya haddasa min canzawar launin ido.

A hankali na juya na kuma kallon shi zuciya ta na bugawa da karfi karfi yayinda nauyin da kaina yayi ya haddasa min ganin dishi dishi,…yana durkushe gaban gadon da nake zaune ya bani baya yana ta daddaure hodar iblis (COCAINE) cikin wasu kananan leda nylon, da sauri sauri yake aikin wanda duk bayan second daya sai ya daga kai ya kalli kofa.

Rumtse idanu  na kuma yi, zuciya ta na tsananta bugu tuna cewa wai nice zan hadiye gaba daya wannan hodar iblis din a cikin cikina inyi safararta zuwa Nigeria.Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un na furta cikin raina kana nabi dogayen kafafuna farare sol da kallo daure suke cikin chains sakamakon yunkurin guduwar da nayi hakan yasa suka daure ni.Zuwa yanzu na tabbatar roko da magiya bazai min amfani ba,.

“You have to be brave” zuciya ta ta fada min, tabbas dabara ne kawai zanyi da taimakon ubangiji inbar wurin nan, if not rayuwata ta kare, safarar cocaine ba karamar risky bane ga rayuwata, cikina ne ya hautsine gami da bada sautin kululululu sakamakon tunawa da nayi wai hadiyar wadannan ledodin zanyi cikin cikina. duk da ya sanar min da hanyoyin da za’abi a fitar dasu idan mun isa nigeria hakan bai rage koda kaso daya cikin dari na irin tsoratar da nayi ba.

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


A hankali na fara bin dakin da kallo ko zan dace, aiko idanuna suka sauka kan bedside lamp dake kusa dani ga kuma wani tangaran mai dauke da rose flower duk a wuri daya, cikin dabara nakai hannuna duk biyun na dau lamp din da kuma flower vase din,…ya dukufa sai aiki yake a gaggauce hakan yasa bai maida hankali kaina ba,  rumtse idanu nayi ina tabbatar wa kaina abunda zan aikata shine daidai, baiyi aune ba yaji saukar tangaran a keyarsa ji kake garammm cikin azama ya juyo jin abin unexpected,  yana juyowa na kuma rotsa masa bedside lamp din at the same point, take yayi baya baya ya kwala wani irin ihun kiran suna na “MARYAMAAAA” ya fadi kasa jini ya fara malala a wurin, da gaggawa na fara kokarin kwance chains din da ya daure min a kafata, sai a lokacin na kula da cewa tunda ya fadi bai kara motsi ba, ga jini dake tartsuwa ta keyanshi da baki harda hanci.Zuciya ta ce ta kuma bugawa da karfi dan matsowa nayi kusa da shi a hankali nace “ABDALLAH” amma shiru ko motsi baiyi ba, na daga hannunshi ina sakewa hannun ya dawo, mikewa nayi ina ja da baya baya yayinda wani irin jiri ke kwasata, “ya mutu!” na furta da karfi a lokaci daya kuma wani irin bell yayi ring cikin kwakwalwata na kashe shi, idan aka kamani shikenan ba mai kara jin labarina a duniyar nan,…without second though na janyo bedside drawer na cire passport nawa da kuma credit card sai wayoyina guda biyu da kuma tab nawa da sauri sauri na kuma zuge wata doguwar durowa mai dauke da kayayyakina jere reras ba tare da na bi ta kansu ba na janyo wata yar akwati na bude American dollars ne shimfide dauri dauri, duk kaunata ga kudi duk irin wuyar da nasha da irin hadarurrukan da na shiga wurin tarasu amma na kasa daukansu, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban wani,dauri biyu kawai na dauka shida sauran tdakinwayoyina da na sa su a flight mode, gyalen bakar abayata na dakinZak hanzari kana na bi gefen abdallah na fice daga dakinZa.

“Act smart maryama  this is dubai not abuja nigeria” zuciyata ke bani shawara sai dai duk yadda naso bin shawaran na zuciyata na kasa jikina sai rawa yake, yayinda launin idanuna ke kara sauyawa zuwa tsananin tashin hankali,cikin sa’a na fita daga gidan ba tare da mai gadi ya tuhume ni ba sanin matsayina da yayi a gun mai gidan, cab na tsayar na shige hade da cemasa “Airport,” ina daidaita zamana cikin cab din wani irin kuka mai masifar karfi ya taho min amma haka na dinga dannewa wanda ya haddasa min rawar jiki hadi da takurewar fuska…

WRITTEN BY: ASMA’U A.I MAI UNGUWA

NOVEL NAME:   MARYAMA BOOK 1

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         347KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:    26- OCTOBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            FREE

Proceed To Download Maryama Book 1 Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button