Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 14 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na goma sha huɗu_

……..Sannu a hankali JJ ya fara shiga jikin Anoosh, tun bata kulashi harta ɗan fara sama-sama ganinsa kamar mutumin kirki. Dan a duk sanda zai zo gareta shigar mutanen ƙwarai yake yi, sannan kuma da fuskar musulinci. Bai sake yarda su MB sun masa rakiyya ba. A kuma gidan Gwaggo ake hirar. A haka suka share wata kusan uku, zuwa lokacin Anoosh ta fara sakin jiki da JJ sosai. Da wannan damar yay amfani ya dinga zuwa yana kaita school, idan ta gama lectures yaje ya ɗakkota ya maidota gida. Ganin babu wata matsala Hajiya Lailah ta barsu, sai dai tana saka musu ido sosai, sai da ta sake tabbatar da babu matsala sannan ta samu nutsuwar zuciya. Ta kuma faɗima JJ ya shirya Anoosh na shiga 300 level zata mata aure, karatu ta ƙarasa a ɗakinta. Ya nuna jin daɗinsa da hakan a zahiri, a baɗini kam dariyama abin ya bashi. Tayama kamarsa shi JJ mai buhu-buhu na ƴammata lafiyayyu dake binsa da roƙo ya ƙare da auren bebiya mai raunin gani sai da gilashi. Duk da dai Anoosh nada ƙyau sosai baya jin zai iya wannan sadaukarwar, adai cigaba da tirzawa ya samu abinda yake so yay gaba abinsa.
Tun daga randa Hajiya Lailah ta masa batun shirin aure ya fara hillatar Anoosh akan ta ɗan dinga saka mayafi mana, taya shi da zai aureta ace baida ikon ɗan ganinta kamar yanda sauran ƴammata kema samarin su yaji daɗi. Takan nuna masa ita bazata iya ba tana jin kunya, sai ya koma nuna mata to idan ta shigo motar tana cire hijjab ɗin in ya kaita school sai ta maida. Nan ma ta nuna bazata iya ba, yay fushi sai da ya kwana biyar baya kiranta a waya dan dama vc sukeyi, baya zuwa kaita makaranta. Tun abin baya damunta harya fara, dan da gaske JJ ya dasa rassan ƙaunarsa a zuciyarta ta yanda bazata iya cisgeshi ba koda taso hakan. Koda Hajiya Lailah ta lura da yanayinta da kuma daina ganin JJ na zuwa ta tambayeta sai cewa tai yayi tafiya ne. Murmushi kawai Hajiya Lailah tayi, tana mai jin tausayin ƴar tata dan ta fahimci itama irinta ce mai zurfafa soyayya akan mutum. Zata tayata da addu’a ALLAH ya sassauta mata, dan ita taga illar zurfafa soyayya wa namiji. A kwana na shida JJ yazo sakamakon kiran da Anoosh taima SJ ta vc tana kuka tace ya bashi haƙuri. Ƙin mata magana da dariya yay har ya kaita makaranta ya ajiye, haka ta nufi aji jiki a saɓule. Bayan ta gama lectures nata ta kirashi kamar yanda ta saba, uhumm kawai yace mata ya yanke kiran. Babu jimawa sai gashi nan ga fuskarsa babu alamar yasan minene dariya. Sosai ta sake shiga damuwa, dan haka suna shiga mota ta zare jijjab ɗinta hawaye na cika mata ido. Amma yaya zatai bata son cigaba da ganin ɓacin ransa. Sannan kuma a ganinta da wautar tunaninta ko addini ya yarda wanda zai aureka ya ganka. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya JJ ya shiga saki a jajjere jikinsa na tsuma, dan kuwa tabbas Anoosh cikakkiyar mace ce data amsa sunanta mace. Irin matan nan ne da ALLAH ya azurta da ƙira ta asalin gwalbar fantar da ake faɗi. Dan duk da tana a shekara ta Ashirin ko ina na Anoosh cike yake dam gaba da baya. Ga wata lafiyayyar fata mai santsi da ɗaukar ido a dalilin yawan zama cikin hijjab. Gata fara tas tamkar madarar shanu sabon tatsa. Kai komai yaji dai, rashin magana da raunin idanu ne kawai tawayar Anoosh a rayuwa. Amma shi kam ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba to a wajensa Anoosh ta cika harta zarta a ɓangaren halittar jiki. Da ace tana magana kuma idanunta na gani ras kamar a kowa shikam babu abinda zai hanashi yin wuff da ita.
Jin yay ɗiff yasa ta ɗagowa ta kallesa. Da sauri ya ɗauke idanunsa dake mata kallon ƙurilla da gaba ɗaya ya kaucema shari’a. A kasalance yaja motar suka tafi. Sai da sukaje ƙofar gida ya ce, “To sa hijjab ɗin”. Jikinta har rawa yake ta saka, dan tunda take a rayuwa bata taɓa shiga takura da matsuwa ba irin yau. Tana gama sakawa ko sallama batai da shi ba ta buɗe motar ta fice tana cin tuntuɓe. Rakata yay da wani makirin murmushi yana zuƙar baki kamar wanda yaci yaji, dan maganar gaskiya ta kwance masa lissafi. Baya jin akaf ƴammatansa ya taɓa cin karo da mai irin surar Anoosh…

_________★

        A hankali ta fito daga kitchen ɗin hannunta ɗauke da tray. Rawa jikinta ya nema farawa sakamakon sauka da idanunta sukai akan Dafeeq dake kwance a cinyar Hajiya hannunsa cikin rigarta ita kuma tana wani shafa masa kai. Khadijah ta haɗiye yawu da ƙyar zuciyarta na faɗa mata (Khadijah ki dake, karki bada wata ƙofar da matar nan zata rainaki) da wannan shawarar ta zuciyarta ta samu ƴar nutsuwa. Batare data sake kallonsu ba ta ƙaraso inda suke ta ajiye tray ɗin. Hajiya dake binta da wani irin ɗan iskan kallo ta saki wata shegiyar ƙara ta iskanci tana ƙanƙame kan Dafeeq saboda abinda yake mata. A rikice Khadijah ta ɗago zuciyarta na wani masifar harbawa. Da sauri ta juya musu baya tana ambaton sunan ALLAH ganin iskancin da sukeyi a gabanta. Zuciyarsa kam tuni ta shiga wutsilniya a ƙirji tamkar zata fasashi tayo waje. Batama san ta saki wani shegen tsaki ba ta nufi barin wajen cike da sassarfa kamar zata faɗi. Sai lokacin Dafeeq ya ma farga da ita. Ji yay wata irin kunyar Khadijah ta lulluɓesa. Zaram yay ƙoƙarin tashi Hajiya Kainaat ta kanainaye sa cikin kissa da salo irin na manyan mata da suka san takan duniya. Tuni yamanta da batun Khadijah ya shiga maida murtani. Tsabar iskanci a falon nan suka shiga fagen yaƙin ƙasa da ƙasa. Sai ga Kainaat na kurma uban ihun da bataiba a daren jiya duk dan ta haukata Khadijah. Shima dai Dafeeq tuni ya saki layi dan Hajiya ta ɗakko wata hanya ne dake tabbatar masa da yaro-yaro ne.

Kuka Khadijah ta fashe da shi da saka hannuwa duka biyu ta toshe kunnenta, dan gaba ɗaya sun cika gidan da ihun rashin mutunci. Kuka take sosai tana faman toshe kunne amma hakan bai hanata cigaba da jinsu ba. Ganin zuciyarta zata iya tarwatsewa dan Khadijah nada kishi sosai ta tashi a guje ta fito a ɗakin. Da rawar jiki tabar falon dan batai zaton anan suke iskancinsu ba. Cikin hajijiya da jiri ta fice aguje da ga falon, sai dai tana isa gate maigadi ya hanata fita, acewarsa Hajiya bata bada damar kowa ya fita ko ya shiga gidan ba. Ran Khadijah ya sake ɓaci, ta shiga zagin maigadi amma yay biris da ita. Dole ta zube a wajen tana kuka mai cin rai da zuciya. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake komawa wujiga-wujiga kamar ba Khadijah ba. Bata taɓa sanin tanama Dafeeq irin wannan mahaukacin son da kishin ba sai yau. Ji take zata iya kashe Hajiyar nan. Kai har kanta ma da Dafeeq ɗin sai dai kowa ya rasa iyayensa suyi asararsa. Tana nan zaune a tsakar harabar gidan taci kuka harta godema ALLAH Dafeeq ya fito. Wani shegen taku na rashin mutunci yake yi da gadara da isa. Babu magana babu komai yana zuwa gabanta ya wani irin ɗauketa da mari. Kafin ta gama dawowa hayyacinta ya fisgeta zuwa cikin gidan. A falo ya watsar da ita kamar mara daraja, Hajiya na zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kallo ɗaya tai musu ta watsar ta cigaba da danna wayarta. Sake ɗauke Khadijah yay da mari. Sai lokacin Kainaat tai magana a yamutse.
“Baby nifa dama ka ƙyaleta wlhy, ba kanta ta ganarmawa ba. Kaga gobe idan taji ihun ma’aurata saita kiyayi fito musu banza ƴar iska. Ƙarama dake kin iya son kallon haram. To Alhmdllh sauƙin ma dai Baby sadaki ya biya ya auran ba baɗala muke ba.”
Wani mugun kallon banza Khadijah da taƙi kuka duk da marin da Dafeeq yay mata ya shigeta ta sakarma Kainaat da jajayen idanunta. Sai kuma taja tsaki da ɗauke kanta batare datace komai ba ta miƙe. Tsawa Dafeeq ya buga mata cikin ihun faɗin, “Dan ubanki na sallameki ne?”.
Ko gezau Khadijah tai wucewarta. Hakan yasa Kainaat sake tabbatar da yarinyar nan lallai shegiyar kanta ce. Dariyar tunzura Dafeeq ta saki da faɗin, “Yaro yaro ne, kaga kaima ta nuna maka baka isaba kenan. Yarinya aiki ya sameki kuwa in dai kikace da Kainaat zakiyi kishi sai dai kare ya mutu da haushin kura.”
Cak Khadijah ta tsaya, ta haɗiye kukan dake neman ƙwace mata tare da juyowa ta na kallon Kainaat a wulaƙance. Sai kuma ta saki murmushin ƙularwa. “Tabbas karen kuwa zai mutu da haushin kurar ballagazar tsohuwar daƙiƙiya. Bari na baki fassarar zancenki dan naga girman shekarun ne kwai babu wayo a tare da ke. Ai kece karen, Khadijah kuma kura, kibar ganin asiri yay tasiri akan mijina yanzu, watarana ke da kanki zakiyi nadamar yinsa, dan Dafeeq nawa ne har abada, ki ɗauka yanzun ma aro na baki kafin na shafe babin tarihinki guzumar tsohuwa mai auren ɗan cikinta kawai”.
Matuƙa maganganun Khadijah sun ƙonama Kainaat zuciya. Ta kalli kanta da ƙyau, dan a duniya ta tsani a kirata wai tsohuwa. Amma sai gashi harda su guzuma ma wai da ballagaza. Sannan yarinya ƙarama da inda auren wuri tai zata iya haihuwar kamartace ke faɗa mata magana haka akan wani banzan namiji data aura dan biyan buƙatar ranta. A fusace ta yunƙura zata miƙe cikin sauri Dafeeq dake kallonta yana wani irin farin ciki a zuciyarsa dan ya samu nasarar farko a plans ɗinsa kenan. Burinsa yaga suna faɗa irin na kishiyoyi a kansa. Hakan zai bashi damar tafiya plan b shi kuma. Riƙota yay cike da lallashi ya na faɗin, “Kinga hajjaju na kwantar min da hankalinki dan ALLAH. Ai wannan faɗan ba naki bane dani takeyi, kuma dolene ta amshi hukunci dai-dai da rashin kunyarta. Zauna ga ruwa kisha ina zuwa”. Ya zaunar da ita a kujera sannan ya nufi ɗakin Khadijah yana zare belt ɗin jikinsa. Khadijah na kwance a godon rufda ciki tana kuka mai ƙona zuciya babu zato babu tsammani taji saukar duka a jikinta kawai. Wani irin zabura tayi da ƙwala ihu ta miƙe zambar. Dukan ya cigaba da kai mata sai dai gefen gadon yake samu ba ita ba, da alama kuma yana sane yake hakan. Jin an bugo ƙofar an shigo yasa shi fara kai mata dukan gaskiya, dan kuwa Kainaat ce ta shigo tana faɗin, “Shegiyar yarinya yanzu ai kin tabbatar da waye kare waye kuran ko? Ka jibgar min shegiya Baby har sai jikinta ya farfashe dan ubanta”.
Tamkar Kainaat ta zuga Dafeeq ne, ya cigaba da laftar Khadijah da a yanzu ta tsaya cak tamkar bama ita yake duka ba tana kallonsa kawai. Gashi ta daina kukan da take dan tanada shegen zuciya da kafiya. Ganin fa zai iya mata illa ya saki belt ɗin yana yarfe hannu. A marairaice ya kalli Kainaat dake kallonsa. “Baby wlhy hannuna ya gaji, yarinyar nan jakace bama jin dukan take ba fa”.
Hannunsa ta riƙo, sai kuma ta kwashi belt ɗin itama tana faɗin, “Ni bari naci ubanta naga ƙarshen taurin kanta.” tana ɗaga bulalar zata zubama Khadijah ta riƙe. Wani murmushi ta sakar mata tana tsareta da jajayen idanunta. A kausashe ta ce, “Har abada. Har gaban abada ba’a haifi kishiyar da zan tsaya ta dakan ba, ke wadda ma zan tsaya dambe da ita babu ita balle har nai zaman ta dakeni. Shi dai zai iya duka yanda yake so domin sunansa miji, yaci darajar wannan sunan”. Ta fisge belt ɗin.
Ba Kainaat ba hatta shi kansa Dafeeq ɗin kallon mamaki yake ma Khadijah. Ya san tanada zuciya da tsiwa kam, amma bai zaton tanada irin wannan jarumtar ba. Harara Khadijah ta balla musu su duka ta wuce toilet ta barsu da binta da kallo tamkar idanunsu zasu zubo ƙasa dan mamaki……✍️

       _😂A nima dai Dijo taban mamaki kam. Amarya da ango sai ku sake sabon shiri_.

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 15 Complete Novel

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button