Uncategorized

Macijine Shi Page 45-46 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 45/46

________________kai tsaye Adeeb  part ɗin sa  ya wuce da fattu ,wacce ke kuka kamar ba gobe ,gaba ɗaya atsorace take da ganin yanayin na adeeb.ita tsoronta ma kada wani abu yasameshi, ko ya sanja halitta .

Suna shiga Adeeb ya zaunar da fattu akan kujera ,sam baidamu da yadda jikinta ya ɓaci ba,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki yake ji cikin zuciyarsa ,lallai Rashad ya taɓowa kansa ,inhar ya ce zai nuna halin ɗan akuyancinsa akan fattu,to zai iya aikata masa komai ma,dan bazai taɓa iya daukar kowane irin abu akan fattu ba,duk ƙanƙantarsa kuwa.

Kaiwa yake da kawowa atsakiyar ƙarin falon kashi,banda dukan hannunsa ba abinda yake ,idanunsa sunyi bala’in sauyawa ,wannan karon gaba ɗaya idon nashi sun koma blue sosai ,sai wani irin huci yake kamar zaki.

Fattu kuwa ta takure guri ɗaya ,atsorace take sosai,ta kasa koda kallon Adeeb ne ,dan gaba ɗaya kamanninsa sun sauya,har wani bari jikinsa keyi.

Kuka take ƙasa ƙasa ,yayi da take jin yadda jini ke zuba ajikinta,dan har zuwa lokacin akiɗime take.

Juyowa Adeeb yayi yana kallon fattu ,tausayi ta yake ji sosai cikin ransa,yana tuna cewa itaɗin amanace agurinsa,dole ya kula da rayuwarta,bayan haka yana jin tamkar ita ɗin rayuwarsa ce ,bazai bari wani abu ya cutar da ita ba.

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 21-30 Hot Romantic Novel

Gurin ta ya nufa cikin takunsa mai cike da izza,tsugunnawa yayi agabanta tare da tsura mata ido,dagowa tayi da sauri itama tana kallonsa.da sauri ta sunkuyar da kanta tana kuka .” Dan Allah Hamma kayi haƙuri,kada wani abu ya sameka ” ta faɗa tana mai dagowa tare da kallon cikin idanunsa.

Shima kallonta yake cike da tausayawa,hannunsa ya ɗora akan fuskar fattu yana mai share mata hawaye,idanunsa akan fuskarta,

Ɗayan hannun nashi yasa tare da riƙe duka  kumatunta,yana kallonta,tsawon mintuna yayi yana kallonta ,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya  da ƙarfi  kafin ya fara magana ,cikin ƙunar zuciya .

” Hulwa ” ya faɗa ahankali yana mai kallon fuskarta.

Kallonsa take tana mai tunanin sunan daya kiranta dashi.

Jinjina kai yayi tare da ci gaba ” daga yau idan kikaji na kira sunan Hulwa ,to dake nake wannan shine sunan dana zaɓa dan kira ki dashi,saboda ke ɗin ta musamman ce agareni,kina da matsayi mai girma acikin  nan ɗina.ya faɗa yana mai nuna saidin zuciyarsa.kafin yaci gaba” ki faɗa min me Rashad yayi miki?yaushe ya fara kulaki? ” Adeeb ya faɗa trying to colmn his mine,Dan kar fattu ta ƙara tsorata .

Girgiza kai fattu tayi tare da share hawayen idanunta ,kafin cikin sanyin murya tace ” Hamma Ni bansanshi ba, amma na taɓa ganinsa lokacin da mukazo gidan nan,yayimin magana amma ban kulashi ba,sai dazu ina kwance shine yazo zai taɓani” fattu ta ƙarasa cikin muryar kuka.

Runtse idanu Adeeb yayi da ƙarfi,yana mai jin zuciyarsa kamar zata ƙone,cikin wata irin murya Adeeb yace ” ya taɓaki ne ?kuma ina ya taɓa miki?Adeeb ya faɗa jikinsa na wani irin bari.

Girgiza kai fattu tayi tana mai cewa ” bai taɓani ba shine na gudu zan fita kai kuma kazo” 

Download>>> Cousin Ne Complete Romantic Novel Document


Ƙara riƙe fuskarta yayi cike da haɗe fuska sosai yace ” ki faɗa min gaskiya Hulwa ya taɓa ki ne ko a’a” Adeeb ya faɗa cikin dan tsawa,har saida fattu ta ɗan zabura.

Kuka fattu ta ƙara sanyawa tana mai faɗawa jikin Adeeb ” Hamma ka daina kana bani tsoro ” ta faɗa cikin kuka tana kanƙameshi.

Shima ƙanƙameta yayi ajikinsa kamar zai maidata cikinsa.ahankali yake shafa bayanta alamun rarrashi,ita kuwa sai kuka take ahankali tana mai ƙanƙame dashi.

“Ya isa haka Hulwa ,ki daina kuka ,bana so zuciyata tana zafi idan na ganki cikin damuwa,Please stop crying” Adeeb ya faɗa yana mai shafa baƙin gashin fattu ,wanda ba ko ɗan kwali akanta.

Ahankali fattu ta rage sautin kukan ta,har tayi shiru gaba ɗaya,sai ajiyar zuciya take sauƙewa.

Kusan minti biyar suna rungume da juna,kafin fattu ta ɗan motsa tare da kiran sunansa”Hamma”

Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe yana sauraran bugun zuciyar fattu ,tare nashi bugun zuciyar,ji yayi suba bugawa akusan tare. 

Dagota yayi daga jikinsa yana kallonta da sauraron abinda zata faɗa masa.

Kallonsa tayi itama tana mai dan gwaɓe fuska kafin ta kalli ƙafafunta ,sannan ta ƙara dagowa tana kallonsa” jini Hamma”ta  faɗa tana ɗan yarfe hannu.

Da sauri ya kalli ƙafafun nata,aikuwa jini har kan lallausan kafet ɗin dake tsakar ɗakin.miƙewa yayi da sauri tare da miƙa mata hannu,alamun ta mike tsaye.

Kama hannun nashi tayi tare da mikewa tsaye,gaba ɗaya gurin da take zaune ya ɓaci da jini .dan dafe kai Adeeb yayi tare da kallonta yana mai faɗin” sannu ba inkijin ciwo ?kai ta daga masa alamun ehh.hannunta ya kama ya nufi toilet da ita.ruwa ya haɗa mata mai zafi da kansa,sannan yace tayi wanka .

Kallonsa tayi bayan ta gama ƙarewa toilet ɗin kallo,kafin tace ” Hamma nifa ban iya shiga kogi ba” ta faɗa cikin muryar ta mai daɗin sauraro .

Kallonta yayi tare da dan hararar ta sannan ya ce ” aikuwa yau sai kin shiga kogin nan ,ko kuma nayi miki wankan da kaina” ya faɗa yana harararta ,wai kogi ji shiririta ko ina taga kogin?

Juyawa yayi da nufin fita daga toilet ɗin dan tayi wankan ,da sauri fattu ta riƙo hannunsa ,juyowa yayi ya na mai kallonta da alamun tambayar menene.

Marairaicewa tayi kafin tace ” Hamma dan Allah ka zubamin ruwan acikin bokiti, Ni banason wannan abun , kalli fa kagani idan na shiga nutsuwa zanyi” fattu ta faɗa tana mai nuna masa wai ya kalli girman kwamin wankan.

Dafe kai kawai Adeeb yayi yana mai kallon fattu,shikam baisan yaushe fattu zata waye ba,komai ita saita juyar dashi zuwa abin tsoro.

Hannunta ya kama  zuwa bakin kwamin wankan ,cikin ɗaure fuska ya kama rigarta yana ƙoƙarin cire mata ,da sauri ta riƙe hannunsa dan harya kawo rigar wajen cinyarta.” Hamma zanyi da kaina kayi haƙuri” fattu ta faɗa tana mai zaro ido ,ganin da gaske yake ƙoƙarin cire mata rigar.

Sakin rigar yayi tare da juya mata baya yace ” kiyi wankan yanzun nan   zan dawo ” ya faɗa yana ja mata ƙofar.

Koda Adeeb ya fito daga toilet ɗin Safa da marwa yake tayi cikin dakin,ba abinda yake masa yawo acikin zuciyarsa ,sai abinda rashad yayi ƙoƙarin yiwa fattu,wato taɓa jikinta.

Hannunsa ya sanya tare da dukan bangon dakin da ƙarfin gaske ,yana huci cikin wata irin zazzafar murya yake faɗin” Rashad kayi kuskure na farko ,idan har ka sake yunƙurin taba min matata ,yayi shiru yana huci kamar wani zaki,kafin ya mike tsaye tare da barin ɗakin, shida kansa ya gyara gurin da fattu ta ɓata ,dan bazai sa wani ya gyara gurin da fattu ta ɓata ba.yana gamawa kuwa

Kai tsaye bangaren ammi ya nufa yana shiga ya tarar da ita zaune ana taje mata gashi. 

Zama yayi akusa da ita ba tare da yace komai ba.

Cikin girmamawa gaba ɗaya haɗiman suka gaida Adeeb tare da ficewa daga ɗakin.

Cike da kulawa ammi ta kamo hannun Adeeb tare da shafa kansa ” mu Prince kayi haƙuri da abinda ya faru tsakanin ka da Rashad , ba yadda banyi dashi akan ya gyale yarinyar nan, domin kuwa kai kazo da ita ,kuma a ƙarƙashin kulawar ka  take  bana son tashib hankali,amma sai cewa yayi ai ba matar ka bace dan kazo da ita ,wai shi sonta yake kuma ba wanda ya isa yashi tsakaninsu da ita.

Amma my prince kai menene alakarka da yarinyar nan ?dan musan yadda zamu bullowa lamarin ,tun kafin asami matsala”ammi ta faɗa tana mai kallon Adeeb da son jin abinda zaice akan alaƙarsa da yarinyar.

Adeeb kuwa wanda ransa ya ƙara ɓaci sosai da abinda ammi ta faɗa masa cewa rashad ɗin ya faɗa ,cikin furzar da wata zazzafar iska  Adeeb ya kalli ammi kafin yace ” amma dole na ɗauki mataki akan rashad ,bazan taba bari ya cutar da yarinyar nan ba ,dan ita ɗin amanata ce ” yana faɗin haka ya mike tare da barin dakin.

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

Murmushi ammi tayi tare da lumshe ido ,lallai burinta yana gab da cika akan waɗan nan yan uwan.

Bangaren nanny ya nufa yace ta bashi kayan fattu ,cike da kulawa nanny tace ” ayya ɗan nan ,daka dawo da ita nan ta shirya ,dan kuwa zamanta acan gurinka akwai matsala ,kasan akwai yan sa ido ” nanny ta faɗa cike da kulawa.

Kallonta kawai Adeeb yayi, tare da karbar kayan data ciro masa harda pant ɗin data sakawa always ,” zata dawo ” kawai ya faɗa tare da barin dakin.

Fattu kuwa lokacin data kammala wankan ta sosai taji jikinta yayi mata daɗi ,saidai kumasam ƙin shiga cikin kwamin tayi ta kunna shaya tayi wankanta,saidai damuwarta ɗaya yadda taga jinin nan yaƙi daina zuba. Hawaye ta share daga idanunta kafin ta janyo wani ƙaton bargo ta daura ƙirji dashi.

Ɓudewa tayi tare da fitowa falon ta tsaya jikin bango ,bata son ta zauna jinin ya ƙara batata.abin mamaki tsaf taga an gyara gurin data bata ɗin nan.

Ko waye ya gyara oho!fattu ta faɗa cikin ranta .

Adeeb ne ya shigo ɗakin riƙe da kayan fattu dake ta zuba ƙamari,kallonta yayi tare da kawar da kansa ,ajiye kayan yayi akan gado yace ” kisa  kayan ki sameni afalo” sannan ya bar ɗakin.

Bayan fattu ta sanya kayan harda pant din Dan ta gane yadda ake sakawa tunda nanny ta faɗa mata .kanta ta yane da mayafin kayan,sannan ta nufi gaban madubi,turare ta gani dan haka ta ɗauka tare da bude murfin kwalbar gaba ɗaya tana masa shafawa irin ta mai. Sannan tana yaba ƙamshin wannan man shafawa  azuciyarta.

Saida ta gama sannan ta fito falon.

Tun kafin ta gama buɗe ƙofar ƙamshin turaren ya bugi hancin Adeeb ,da sauri ya dago kansa,lokacin data ƙaraso kusa dashi gaba ɗaya falon ya kiɗime da ƙamshin wannan mayen turaren na Adeeb, turarene irin mai shegen kyau da tsada r nan, kwalbar yar karama ce ,wacce kuɗi ta yakai kusan dubu dari biyar ,ɗan kaɗan ake shafawa amma sai yayi sati bai bar jikin mutum ba.shine malam fattu ta shafa matsayin mai.

Kallonta yake hatta ƙara so kusa dashi ta tsaya .

Wasa take da yan yatsunta,yayin da kanta ke ƙasa.

Lumshe ido Adeeb yayi sakamakon yadda ƙamshin turaren nan ke ratsa dukkan wani sannan na jikinsa.

Buɗe ido yayi yana kallonta kafin ya kamo hannunta ya zaunar da ita ,hancinsa ya kai daidai wuyansa yana ɗan shaƙar ƙamshin jikinta.

Lumshe ido fattu tayi lokacin da hucin numfashin Adeeb ya sauka akan dokin wuyanta.

Kallonta Adeeb yayi idanunta alumshe ta damƙe gefen kujerar da take kai,

Kalli yarinyar nan mafa A ce kalli daga ɗan matsawa kusa da ita yadda take cakumo  kujera ,hmmm. Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa yana mai ci gaba da kallon fattu.

” Ki buɗe ido ki,saiki saki kujerar karki Yahaya ko” Adeeb ya faɗa yana mai matso da fuskarsa saitin ta fattu,duk da yadda ƙamshin turaren nan ke ƙoƙarin hawa masa kai.

Da sauri fattu ta buɗe idonta tana mai kallon Adeeb ,tare da sakin kujerar ,kunya kamar ta kasheta .

Turo baki tayi tana mai ƙif-ƙif ta ido.

” Me yasa kika samin turare?” Adeeb ya faɗa yana mai  kawar da kansa .

Kallonsa fattu tayi kafin tace ” Hamma bansa turare ba ,kawai na shafa mai ne” fattu ta faɗa kanta a ƙasa.

Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace” haka ake turare agarinku?

Download>>> Silar Fyaɗe Complete Novel Document

” Dan murmushi fattu tayi kafin tace “Hamma to mu ina zamuga wani turarema ,mufa ko mai ma bamu cika shafawa ba” fattu ta faɗa tana ɗan watsa hannu,kamar ba ita ta gama kukan tsoro ba ɗazu.

” Shiyasa kikayi min  ɓarnar turare ko? Bakisan yana da tsada ba ?Adeeb ya faɗa yana ɗan kallon gefenta.

” Ayya Hamma bansan turare bane ,kawai ƙamshin ne yayi min daɗi,shine na shafa amma kayi haƙuri Hamma zan siya maka wani” fattu ta faɗa tana ɗan dafa kafaɗar Adeeb.

Kallonta yayi kafin ya kalli hannunta data ɗora akan kafadunsa.

Zare hannun tayi da sauri tana mai sunkuyar da kanta.

“Ina zaki sami kuɗin da zaki siyamin wani? Kinsan kuɗin da ne” Cewar adeeb yana ɗan murmushi.dan yasan yanzu fattu zatayiwa turaren kuɗi.

” Karka damu Hamma zan tara kudi mai yawan da kai kusan dubu uku ,saina siya maka turaren da yawa.

Dariya ce ta kama Adeeb ,wai dubu uku !sai kace kudin sadaka .

” Shikenan ki tara dubu ukun saina kaiki kisiyamin” cewar Adeeb kenan yana mai kallon wuyanta.

Hannu yakai kan wuyan nata ya ɗan shafa cike da mamaki kafin yace ” Hulwa” dagowa tayi tana kallonsa,yace “ina sarkar nan?” 

Hannu fattu ta kai tare da shafa wuyanta ,taji wayam, shiru tayi tana ɗan tunani ,ina ta ajiye sarkar nan kuwa?amma ta kasa tunowa,” Hamma bansan inda sarkar take ba” ta faɗa cikin damuwa tana shafa wuyanta.

Shiru Adeeb yayi yana nazari,lallai sace sarkar akayi,kuma akwai wanda yake zargi ,dan haka kallonta yayi yace ” waye yazo dakinki ” shiru tayi na ɗan lokaci kafin tace Hamma Ni bansani ba dan nayi barci ” 

“Shikenan tashi muje” Adeeb ya faɗa yana mai haɗe fuska sosai,yasan ba kowa bane ya ɗauke wannan sarkar face Rashad ,kuma amma ita zata sashi ya ɗauke,shi yasan dama saita bashi matsala sosai,amma zai ɗau mataki .

Amma kuwa hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da ganin halin da Rashad ke ciki,yanzu akan wannan yarinyar Adeeb yayiwa Rashad wannan dukan.

Lallai ya taɓowa kansa.

Kuma dole mai martaba yasan da wannan batun ,

Rashad kuwa ba abinda yake sai tunanin zuwan gobe ,lallai ya shiryawa goben nan Allah ya nuna mata dan kuwa zai bar wa Adeeb babban darasi akan fattu.

Karanta Littafin>>Macijine Shi Page 43-44 Hausa Novel

Sorry kwana biyu ina biki shiyasa kuka jini shiru.

Muje zuwa masu karatu 

Mrs babi ce 💘💘💘

Back to top button