Uncategorized

Hanyoyin sace zuciyar mace cikin sauki

Akwai abubuwa da zasu taimaka maka ka samu zuciyar masoyiyarka ko kuma ka mallaketa sun haɗa da; riƙon amana, riƙe alƙawari, gaskiya, tarairaya, rarrashi, tausayawa, nuna kulawa, kau da kai, da sauransu.

Kalaman Sace Zuciya: Su kuma waɗannan wasu daɗaɗan kalamai ne, da ake furta su ga masoyiya a mabanbanta lokaci. Masoya kan ce su waɗannan kalamai ɗanɗanonsu ya fi zuma zaƙi balle sukari, sukan sanyaya zuciya, sukan raunana zuciya, sukan ƙarfafi zuciya, sukan sa salama a cikin zuciyar masoya saboda shauƙin su ga masoya.

KARANTA: “ALAMOMIN GANE MASOYIYA TA GASKIYA”

Jarabar So Da Ƙauna

Bayan kabi hanya ta 1 to sai ka bi ta 2 kuma ka fara furta wa budurwarka.

Kalaman Yabo Ga Masoyiya

Za mu bada misali: Wallahi Babila kina matuƙar burgeni, sam baki da girman kai, da fatan ‘ya’yana za su samu irin wannan tarbiyyar.

Ko kuma ka ce: Gaskiya Nafisa yadda kike mu’amula da ƙawayenki yana matuƙar ban sha’awa kin iya zama dasu yadda ya kamata.

Ko kuma ka ce: Hafsat kinsan me Hmmm wallahi yadda kika kama kanku yana tabbatar min da nayi zaɓi nagari.

Ko kuma ka ce: Gaskiya Asiya ki gode wa Allah, Allah Ya baki hakuri ta yadda duk mijin daya aureki zai kasance a cikin farin ciki na har abada.

Back to top button