Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 21 Complete Novel

*ASM Bk2021*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

…..Suna komawa gida su Abbas suka fara shirin tafiya dama tun jiya kowa ya kimtsa kayanshi ba 6ata lokaci sukae sallama da kowa aka rakosu parking space bacin an had’a masu sha tara ta Arziki Senator har 50k yaba kowanne na shan ruwa a hanya Nameer ma uban kaya yaba Kawu Amadu harda sababbi dasu takalma a cikin madaidaicin trolley sosae yayi mashi godiya d’an zaman nan da suka yi sun shaku sosae ji yake kaman karsu rabu gwaggo ma saida tayi mashi godiyar dama tun jiya ya bashi kayan, su Hajiya,Mommyn Haisam Hajiya Maryam,Laila,Jidderh,twins duk suka rakosu ana ta sake yin bankwana Farha dae na ciki tana aikin kuka dama kuma ko ba kukan take ba ba lalle ma ta rako sun ba, Hajiya ji take kamar ta bisu to amman Senator ya hana yace ba yanzu zata koma ba sai ta huta gajiyar biki Saude tun ran Asabar ta wuce ita da wasu yan’uwansu Hajiya na Daura Hajiyar ta hadasu sanin bazata koma yanzu ba Nana tabi wasu yan wurin aikinsu yanzu daga gwaggo sai Amadu Feenah da Abbas sai su Abdul.

 

 

Tunda gari ya waye Fatuu keta faman farincikin su gwaggo zasu dawo har fuskarta ta kasa 6oye hakan dama duk kad’aicin su ya isheta kullum sai taje gidan tayi zaune, bata je Makaranta ba don kuwa jibi Laraba zasu fara Waec suna tashi bayan sunyi Karin kumallo Fatun tace ma Haulat tazo ta rakata taje ta gyara gida ta tambayi innarta tace suje, bayan sun koma gidansu Fatun zagewa sukae ba 6ata lokaci suka fara gyara ko’ina na gidan yay fes dashi bayan sun gama Fatuu tace su d’aura girki amman haulat tace mata ta bari sai d’an Anjima Abuja fa ba nan kusa bace in sukae da wuri zai iya dankarewa a cikin kula tace to su je bakin hanya su siyo Nama da zasu sa a Abincin haulat tace to, basu wani dad’e ba suka dawo suka zauna a Parlor suna kallo can Fatuu ta tuna da sauran cin cin d’in da gwaggo tay mata taje ta de6o masu suka had’a da lemu suna sha, bayan wai lokaci Fatun ta kira gwaggo ta tambayeta ko sun taho tace mata eh gasu a hanya ta shiga yi masu Addu’oi gwaggon na amsawa tana yar dariya don daga yadda taji muryar Fatun akwae tsantsar farinciki a cikin ta, tana gama wayar tace ma Haulat su d’aura girkin yanzu don suna hanya tace to ta mik’e suka nufi kitchen suka fara shirye shiryen abunda zasu dafa, zuwa Bayan Azahar sun gama dafa Abincin wanda Farar shinkafa ce da miya dama suna da cefane a cikin d’an fridge d’in gwaggo na kitchen harda Coleslaw suka had’a da suka je bakin hanya suka siyo harda kayan had’in shi saidae yanka su cabbage d’in kawae sukae basu ida hadashi ba gudun lalacewa ko mayonnaise din ta saki sun bari sai sun iso sai su had’a, bayan sun gama Fatuu ta tafi kai markaden Aya da dama sun gyarata don tasan gwaggo na son kunun Aya bata dad’e ba ta dawo suka hau had’awa sai kamshi ke tashi dama Fatuu ba dae iya Abinci ba komae ta koya a wurin gwaggo haka 6angaren na yan gayun ma duk ta koya a wurin Saude, zuwa k’arfe ukku duk sun gama komae haulat taci Abinci ta koshi ita kuwa Fatuu wai sai sun dawo ba yadda bata yi da ita ba amman tak’i ci k’arshe ta kyaleta tay kwanciyarta ta hau yin bacci ita kuwa Fatuu zaune tay duk bayan lokaci take kiran layin gwaggo taji sun kawo ina wani lokaci ta samu layin wani lokaci ace out of reach can dae da yunwa ta isheta taje ta zubo Abincin kad’an ta ci kafin ta wuce toilet tayo wanka lokacin data fito an fara kiran sallar la’asar ta yi Alwala ta wuce d’aki, ubansun leshi tasa riga da skirt sabbi dal farko kamar karta sa kayan don acikin kayan da Haisam ya yi mata ne sai kuma wata zuciyar ta raya mata in bata sa ba zubar dasu za’ai kuma shi ai ba sanin bata sa ba zai yi hakan yasa ta sanya kayan, tayi kyau sosae bayan tayi Salla harda yar light make up tayi yaushe rabo ita kanta taga kyaun da tayi tay tsaye a gaban mirror tana ta sakin murmushi kafin ta koma Parlor ta tashi haulat koda ta tashi bin Fatuu tay da kallon mamaki tace “k’awata kinga kyaun da kikae kuwa wllh sai kace Amarya” wani kallo tay mata mai kaman harara tace “ke kika d’aura man auren ko” haulat na dariya tace “Eh mana keda Ya Haisam” nan da nan fuskar Fatun ta canza ta daureta sosae Haulat na ganin haka ta hau bata Hakuri tana fad’in wasa take mata amman dae tana fata daga haka ta mik’e ta fita itama sallar taje tayi tana gamawa tayi wanka dama ta taho da kayan da zata canja, koda Haulat ta fita daga parlon lamo fatuu tay tana juya Maganar haulat d’in ta tana fatan ta zamo Matar Ya Haisam to ta ya ya? Fatun ta jefi kanta da tambayar ita yanzu ta riga ta fidda ran ma samunshi matsayin miji lokaci guda ta tuna da sakonshi data gani jiya da safe a ranta ta ayyana yanzu bai ma da lokacin kirana kada matarshi taji haushi haka ta dingi tunane tunane can da ta ga abun na neman yay yawa sai ta mik’e ta hau k’ara gyara gidan tasa turaren wuta, har Magrib ta gabato basu iso ba Fatuu na zaune jigum a falo har ta fara damuwa haulat na toilet bayan ta fito ta nufi Parlon k’arar tsayawar Mota da taji a kopar gidan yasa ta fasa shiga Falon ta nufi hanyar waje tana lekawa taga sune da sauri ta koma cikin gidan tana fad’in “Fatuu gasu sun iso….” tun kafin ta rufe baki Fatun ta fito da gudu kallabinta a hannu ko ta kan Haulat bata bi ba tay kopar gida daidai lokacin duk sun fito daga cikin Motar da gudu ta nufi gwaggo ta k’ank’ameta tana fad’in “ga gwaggota ga gwaggota” dariya sosae gwaggon keyi itama tana fad’in “ga Autata ga Autata” duk suka ba su Abbas dariya Haulat ma dariyar take tayi a gefe guda, Boot Amadu ya bud’e ya fara shigar da kayayyakinsu dama su kadae suka rage don an sauke Feenah Saboda tafi kusa da shigowa gari, bayan Amadu ya fito ne yace ma su gwaggon to su shiga ciki mana sai ta maida ita ciki ma kawae gwaggon na dariya tace ai sai ta maida tan daga haka ta juya ta kalli Abbas dake tsaye ya dafa kopar Mota ta shiga yi mashi godiya da Addu’oi da fatan Allah ya huce gajiya tace sai tazo k’ara yin godiya har gida a gaishe mata dasu Abdul yana dariya yace ai ba komae suka juya yana ta kallon Fatuu itama murmushi kawae take mashi ba tare data ce mashi komae ba Amadu ma yay mashi godiya sosae ya nufi gida har sun kusa shiga gida Fatuu ta juyo ta dawo ta tsaya gefen Motar tana kallon Abbas da har lokacin yake defe da kopar Motar yana mata Murmushi, shiru tay ta kasa mashi Magana don Haisam kawae take gani sai yan kyafcen kyafcen idanu take tana d’an motsa baki,

 

“Mom Zarah kina lafiya?” Jinjina mashi kai tay kafin a Hankali tace “lafiya lou kun dawo lpy?” Kai ya d’aga mata kafin yace “ya shirye shiryen Waec yaushe zaku fara ne?” Tace “jibi zamuyi paper d’in physics practical sai Islamic da yamma” jinjina kai yay ya d’an yi shiru tana bin shi da ido can taji yace “Ya damuwar ta rage ko?” d’an tura baki tay kaman bazata ce komae ba ganin ya kafeta da ido yana murmushi yasa tana tura baki tace “eh na daina damuwa ai shima ya yi Aurenshi ya manta dani da yana kira na amman yanzu ya daina” da alama abun na mata ciwo shi kuwa Abbas fad’ad’a murmushin shi yai cikin ranshi ya ayyana kishi kumallon mata ganin murmushin da yake yasa ta sadda kanta k’asa ita kanta bata san ya akai tayi Maganar ba ji tay ya kira sunanta ta d’aga kai ta kalleshi yace “kiyi hakuri amman ba haka H,zakee yake ba shi mutum ne mai damuwa da wanda ya damu da shi in dae yasan kuna gaisawa ya jika shiru yana tuntubar mutum yaji ko lpy ke kanki ba hakanan ya daina kiranki ba hidima ne yayi yawa amman nasan da ya zama well settled zaki ji daga gareshi ke ai yar gatan shi ce kina d’aya daga cikin mutanen da ya damu dasu sosae hakan ma ne yasa ko yau kafin ya bar Kasar saida yay Maganar ki” d’an bud’a ido tay ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda yace kasa jurewa tay tace “to miya ce game da ni?” Yana murmushi yace “ya bani Amanarki ne yace kar na bari kiyi maraicin shi” zaro ido tay sai kuma tay yar dariya tace “to sai ka dawo gidan Hajiya kenan” dariya kawae yay itama tay shiru tana maimaita Maganar da Abbas d’in yay cikin ranta har taji sanyi don da tayi tunanin ya manta da ita ne,

 

“Akwae Account da yace man a bud’e maki so ki fad’a a gida zuwa gobe da safe sai muje kafin ku fara exams d’in” taji Abbas d’in ya fad’a idonta akanshi ta d’an tura baki tace “Account d’in me kuma?” Da murmushi yace “Bank Account mana yana bukata ne nasan Saboda ya samu sauk’in turo maki kud’i ne” yamutsa fuska tay kaman zatai kuka tace “to ai ya bani kud’i masu yawa da zai tafi ni bani buk’atar wasu kud’i” Abbas yace “ke da zaki cigaba da karatu aikuwa kina buk’atar kud’i sosae Mom Zaraah our future Doctor, ai dama kin bishi can kin yi karatun cikin sauk’i” wani kallo tay mashi tace “kam Matarshi taga na lik’ewa mijinta ta koro ni, nima bazan ma je ba” dariya yasa ganin yadda tay Maganar kafin yace bari ya wuce Magrib ya kusa ya tambayeta tana da passport guda biyu tace eh ganin yana k’ok’arin shiga Mota tace “Ya Abbas ka tsaya kaci Abinci sannan ka tafi” dakatawa yay ya kalleta yace mata kar ta damu sun ci Abinci a hanya kuma gida zai koma zai ci acan” tura baki tay a shagwa6e ta langa6ar da kai tace “ni dae don Allah ka tsaya kaci nifa na dafa shi” k’ura mata ido yay yana murmushi acikin ranshi yake ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa suka shak’u da Haisam sosae sam in kana magana da ita baka jin ka k’osa komae nata nada burgewa katse mashi tunani tay da fad’in “Ya Abbas zaka ci ko don Allah?” Sigh yay yace “Ok ki zubo man in tafi dashi sai in ci a gida yanzu Magrib ya kusa amman fa bada yawa ba” washe baki tay alamar taji dad’i tace to ta juya da sauri ta d’aura kallabin saman kai ya bi bayanta da kallo har ta shige hakanan shima yana son ta da Haisam don ba k’aramar fahimtar juna za’a samu ba tsakaninsu ba ita kanta yanzu yadda akanshi ta fara sanin so to ba lalle ta so wani Namiji har ta samu natsuwa da shi kaman haisam d’in ba to amman yasan kasancewarsu tare matsayin ma’aurata ba k’aramin abu bane gashi yasan Haisam baida ra’ayin mata biyu saidae hakan ba matsala bane don yasan Mutane masu irin ra’ayin nashi wanda yanzu suna da mata fiye da d’ayan amman kuma ita kanta Fanan zata iya zama shamaki kan hakan don Ya fahimci ba k’aramin kishi zatayi ba a k’arshe ya yanke duk hakan k’aramin abu ne a wurin Ubangiji in dai ya kaddaro masu zama ma’auratan, rungume da Warmers babba da k’arama ta fito sai Leda yar babba ruk’e a hannun ta sak’o robobin kunun Aya da Coleslaw tana ta washe mashi baki ta nufeshi bud’a ido yay lokacin data k’araso yace “Mom Zarah wannan ai kin kwaso man Abincin yayi yawa” bata ce komae ba ta bud’e kopar baya ta saka Warmers d’in da ledan bayan ta rufe tana dariya tace “ai ba naka bane kai kadae harda Abdul da Aunty Feenah na zubo mawa in kuka ci ina jira ka fad’i man yayi dad’i ko bai yi ba” yana dariya ya jinjina mata kai kawae ta juya tana ce mashi sai Allah ya kaimu yace Ok zai kirata ya fad’i mata time da zasu fita daga haka ya shige Motar ya tafi.

 

Tana shiga d’akin gwaggo ta nufa lokacin tana cikin cin Abincin da Haulat ta zubo mata ta nufeta ta zauna ta jingina da jikinta a Shagwa6e take fad’in “shine kuka je kukai zaman ku bacin tun ran Juma’a aka d’aura Auren baku damu da kun bar ni ni kadae ba ko” dakatawa gwaggo tay tana dariya tace “to ayi hakuri auta kamawa tay nima duk na damu da rashin ki kusa amman kuma dae ai nasan ba ke kadae na bari ba ko” tura baki tay haulat dae nata dariyar yadda Fatun keta shagwa6a, yabon Abincin gwaggo ta shiga yi da yadda suka gyara gidan tace sunyi kokari sosae hakan yasa ta warware ta fara dariya cike da tsokana gwaggo tace “shiyasa bani da wani shakku akan ku in ku kai aure” turo baki Fatun tay tace “in dae tay aure” gwaggo tace “kema ai zaki yi ne ko an dingi karatun ne ba ranar gamawa?” Tace “ai kona gama ni bazan yi aure ba” da sauri gwaggo tace “ba Amin ba ban fata in ma kina cikin karatun Allah ya kawo Nagari ai aurar dake zanyi kawae Kya idasa a d’akin mijinki” shiru tay kawae cikin ranta tana ayyana da nasamu wanda nike so ma kafin in fara karatun zanyi aure na kallon haulat tay suka had’a ido tay mata Murmushi ita kuma ta tura mata baki, Bayan Magrib duk sunyi salla gwaggo ta kwala masu kira suka shigo d’akin suka zauna ta janyo wata katuwar jaka cikin kayan da suka zo dasu ta tura ma Fatun tace “ga sak’on Yayanki nan tunda bazaki tambayeshi ba da Auntyn taki Amarya, d’an kallon juna sukai ita da Haulat cikin kama kai tace “ai na tambayi ya Abbas ne fa shiyasa banyi maki Maganar ba” gyad’a kai tay Haulat ta kai hannu ta bud’e jakar wadda ta bikin ce mai d’auke da sunayensu a cikinta ma duk tarkacen souvenirs ne da aka rarraba a bikin kaya jibgi guda sai kace d’an gidansu ne yay auren ai ko d’an gidansu ne bazata samu rabin su ba ma, wata k’atuwar Calendar Haulat ta fiddo ta bud’e har bata san lokacin data furta “Wow! Gaskia sunyi matuk’ar kyau wllh” gwaggo ta amshe da fad’in “ah ai ba’a cewa komae Haulat sai Mutum ma yaje hidimar abun sai san barka wllh amman an yi matuk’ar kokari kowa yabo da fatan Alkhairi yake masu” Haulat dake murmushi tace “Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu zaman lafiya” gwaggo ta amsa da Amin Fatuu ma ta amsa a hankali duk jikinta yay sanyi lakwas, mik’a mata Calendar d’in Haulat tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa ta zuba mata ido Haisam kawae take kallo sun yi kyau iya kyau hoto ukku ne a jiki babba na sama sai biyu a k’asa gefe da gefe sunyi shiga daban daban ta Alfarma dake nuna mawadatan Mutane ne ko ina Fanan tayi dariya shi kuma d’an Murmushi yayi wuri d’aya ne yay yar dariyar da har dimple d’inshi ya lotsa da sauri ta mik’a mata Calendar din jin kwalla na niyyar taruwar mata a idanu, Haulat taci gaba da fiddo abubuwa harda jakunkunan kwali suma masu d’auke da pic dinsu gwaggo ta sake janyo wata jakar ta fiddo yan buckets masu kyau guda ukku suma dai na bikin ne tace ma Fatuu ga kuma sak’on Hajiya suma haulat ce ta bud’e marfinsu d’aya dublan ne d’aya cincin da doughnuts d’ayan kuma Alkaki ne da cake gwanin sha’awa d’an murmushi tayi ta tambayi gwaggo ita sai yaushe zata dawo tace bata sani ba amman zata d’an kwana biyu, suna haka Amadu ya shigo ya zauna hiran bikin ya shiga yi masu harda pictures da Vedios ita dae Fatuu zugudum tayi Haulat nata washe baki tana tsuma had’i da yabawa sai faman zuzuta bikin yake da gidansu ya Haisam d’in da gaba d’aya garin Abujar don sun fita da Nameer ya zaga gari dashi bama sau d’aya ba gaba d’aya jikin Fatuu yayi weak lokaci guda ta yanke tun farko sunyi kuskuren da har sukae tunanin Haisam zai so ta don kwata kwata ba ajinta bane ma, sai da akayi isha Haulat tace zata tafi gida gwaggo ta d’ibar mata abubuwan bikin tace ta kai ma Innarta ta kuma bata kud’i farko K’in amsa tay saida gwaggon tace yaushe suka fara wasa irin haka sannan ta amsa tayi godiya itama Fatuu ta d’ibar mata komae cikin nata ta rakata har gida koda innarsu taga abubuwan da aka bata sosae tay godiya har tana zolayar Fatuu tana cewa da yake fa gwaggo ta dawo gashi nan tana ta fara’a yanzu ita dae yar dariya kawae tay daga baya tay masu sallama haulat ta rakota bakin lungu ta tafi, da wuri gwaggo tay bacci ita kuma sam baccin ya k’aurace ma idanunta tay zaune saman gado ta tasa Calendar d’in tana sake kallo bata yi kuka ba saidae wata irin kewar Haisam d’in take ji k’arshe ta kwanta hannunta kan fuskarshi tana shafawa tana d’an murmushi mai ciwo tunowa da abubuwa da dama a haka dae har bacci yay awon gaba da ita.Washe gari tana cikin yin Breakfast Abbas ya kirata yace wurin 11 zai zo ya d’auketa ya d’an shiga Jami’a ne tace to sai lokacin ta tuna bata ma fad’i ma gwaggo ba dama suna tare a falon ta sanar mata godiya ta shiga yi da yima Haisam d’in Fatan Alkhairi tace tay sauri ta shirya kar lokaci ya k’ure yazo ta 6ata mashi lokaci ta amsa to ta mik’e, kafin lokacin ta gama shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta d’an yi yar light make up k’arfe 11 saura yan mintuna yazo ta yafa gyalen da suka hau da kayan da takalma ta d’auki yar jakarta ta fita saida ta lek’a tace ma gwaggo sun tafi sannan ta nufi wajen, lokacin data isa bakin Motar kwankwasa glass tay ya bud’e yana sanye da jeans da t-shirt ta d’an lek’a tana murmushi tace gaba zata shiga ko baya sosae ta bashi dariya jin tambayar da tayi shima ya tambayeta a Motar ya Handsome ina take zama ta nuna mashi gaba yace to nan zata zauna sannan ta bud’e Motar ta shiga tana yar dariya ta gaidashi tay mashi ya gajiyar hanya ya amsa sannan yaja suka tafi, basu wani 6ata lokaci mai tsawo ba a Bank d’in aka gama mata komae bayan sun fito gari ya d’an zagaya da ita saida ya tabbatar ta warware sosae dama Abbas d’an barkwanci ne sosae yake ta saka ta dariya har tambayarshi tay game da Abincinta yace yayi dad’i sosae Feenah ma da Abdul sun yaba har santi sukae sosae ta washe baki can tace to in mark zai bata nawa zai bata, d’an jimm yay sai kuma yace “zan baki 95%” d’an jujjuya kai tay tace “Gaskia Ya Abbas ban yarda ba ka cike man 5 marks d’in kawae mana ba kace har santi su Aunty Feenah sukai ba” yana dariya yace “No bazan baki 100 ba da dai a gidan mijinki kika yi shi confirm kin cancanci 100%” d’an murmushi kawae tay bata ce komae ba, a wani Eatery ya tsaya yace suje suci Abinci batare data musa ba tace to suka nufi ciki ya tambayi abunda zata ci bayan sun zauna tace “Burger and ice cream” yar harara ya wurga mata kafin yace “I mean Abinci ba kayan kwad’ayi ba” tace “to ai suma Abincin ne tunda ana koshi” girgiza kai yay yace ta dai fad’i Abinci a shagwa6e tace “ni dai su nike so inna koma gida naci Abincin….” Tun kafin ta rufe baki ya fara girgiza mata kai kaman zatai kuka tace “Wayyo bafa haka Ya Haisam ke man ba dana fad’i abunda nike so yake man kuma kace Amanata aka baka fa” dariya sosae yasa yace shikenan yaja ma kanshi dama bai fad’i mata ba dariya itama take yasa akawo mata abunda take so d’in shima ya fad’i abunda za’a kawo masa, bayan duk an kawo masu suna cikin ci wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d’in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace “Latest Ango Mutanen US…..” Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri…………

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button