Hausa novels

Kanwar Maza Page 75 Complete Novel By Ayshercool

Page 75

 

Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya.

Mai sunan baba na fita, ya jiyo muryar jabir yana yi wa Iman tsawa “Wai iman waye wannan, meye alƙarki da shi, uban me ya zo yi wurinki?”

 

Cikin wata irin azababbiyar zuciya mai sunan baba ya koma ɗakin, motsin shigowarsa ya sanya jabir haɗiye sauran maganar sa.

 

Mai sunan baba ya taka, ya je gaban jabir ya tsaya, ya ce “Ni zaka tambaya waye ni, da dalilin da ya sanya na zo wurinta”

 

Jabir ya haɗiyi yawu cike da kishi ya ce “Na san kai yayan matar Adam ne amm….

 

Umar ya kaste shi ta hanyar cewa “Bani da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ku, ƙanwata ake aure a familynku, sai dai akwai mutunci da karrama juna, albarkacin ana auren ƙanwata a familynku, ni yakamata ka yi wa duk wannan tambayoyin ba mara lafiyar da ke kwance a gadon asibiti ba, ko ba ka san abun da yakamata ba”.

 

Da ƙyar jabir ya aro jarumta, dan gani yake, da yayi kyakykyawan motsi, mai sunan baba zai iya kai masa naushi, ya ce “Amma ka san babu wata alaƙa tsakaninmu meyasa za ka zo in da take, aurenmu fa za ayi”

 

Mai sunan baba ya ce “Amma ba ayi ba ko?” Jabir yayi shiru.

 

Mai sunan baba yayi tsaki, ya nufi hanyar fita, a daidai lokacin laila suka shigo ita da Nusaiba, bai kula su ba ya fice.

 

Laila ta ce “Waye wannan?”

 

Nusaiba ta ce “Yayan rumaisa ne ya zo duba iman, shi ya korani waje ma”.

 

“Au ya koraki waje ma, wane irin abu ne zaku din ga barin ƙarti suna kaiwa suna komowa a wurin matar da zan aura, wannan ai cin amana ne”

 

Laila ta ce “Nawa ka biyamu kuɗin gadin da zamu hana wasu zuwa wurin iman jabir? Kai ka isa kyakywar yarinya kamar iman, ka ce zaka hana masoya zuwa wurinta”

 

Jabir ya ce “Ba haka bane ba anty laila, amma ai kun san bai kamata ba”.

 

Laila ta ce “Haba jabir, kalli fa kuka take yi, da wanne za ta ji? Kuma dai naga ai baka kai kuɗin auren ba tukuna. Kai baka san ka lallaɓata ba”

 

Ya ce “Haka ne, Allah ya bata lafiya, kishi ne ya sanya ni yin hakan, zan dawo da safe” ya ajiye ledar hannunsa ya fita.

 

Laila ta ƙarasa gaban gadon, ta zauna ta rungumo iman tana rarrashinta.

 

Ta samu ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Ashe rumaisa tana da wa babba kamar haka”

 

Nusaiba ta ce “Ba ki ji ana ce mata ƘANWAR MAZA ba? Yayyenta bakwai maza, ita ta takwas”

 

“Masha Allah”

 

Nusaiba ta ce “Amma wanda ya fitan nan, shi da Hassan ɗin sa ne manya, masifaffe ne, ba shi da fara’a ko kaɗan, daga zuwansa fa wai na tashi na fita”.

 

Halin da take ciki, bai hanata sake lafewa a jikin laila ta ce “Ba masifaffe bane ba, yana da kirki”

 

Laila ta shafa kanta ta ce “Ko dai ko dai? Ko akwai wata a ƙasa ne” iman tayi shiru ba ta ce komai ba.

 

Laila ma tayi shirun, tana cigaba da shafa kan Iman.

 

Mai sunan baba kuwa, yana kan babur ɗin sa ƙirar lifan, babu abun da yake tunani sai kukan iman, kuka mai taɓa rai, ga wannan mara hankalin a yanayin da take ciki, ya je yana yi mata masifa.

 

Laila kuwa sai da ta ga iman ta samu bacci, sannan ta kwantar da ita.

 

Mai sunan baba sai da ya koma gida, sannan ya samu ya ci abinci, sai dai condition ɗin iman, da kukanta ya gaza barin zuciyarsa.

Tuni laila ta yi bacci, ita da Nusaiba, iman kuwa jin wayarta tayi vibrating a ƙasan fulo, ya sanya ta buɗe ido.

 

“Ya jikin?” Da sauri ta sake mutstsuke idanunta, ba mafarki bane ba, mai sunan baba ne.

 

What’s app ɗin ta ta buɗe, ta tura masa saƙo “Yaya umar ya ka je gida, Na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi, bacci ne ya ɗaukeni, shiyasa ban tambayi ya ka je gida ba”.

 

“I don’t mean you should reply now, bacci yakamata ace kina yi yanzu”

 

Wani irin murmushi iman ta yi, a ranta ta ce ‘Gane in da ka saka gaba sai Allah yaya umar’

 

Tayi masa reply da emojin murmushi ta ce “You are a good counsellor, na ji daɗin nasiharka, but please include me in your prayers, Allah ya bani mafita” ta haɗa da emojin kuka da na magiya a ƙarshe 😭🙏.

 

Ya sauke numfashi a hankali ya tura mata emojin kuka da cancel 😭❌.

 

“To na daina in sha Allah”

 

Ya tura mata alamar jinjina, sannan ya tura voice message, abun da ba ya yi, shi chatting ɗin ma ba damunsa yayi ba, amma yayi mata message “Na ga saura few weeks bikin saukar alƙur’aninki karo na uku, kamar yadda ki ka ɗora a status, wannan kawai ya isheki godiya ga Allah, babbar ni’im ce da baiwa, da ba kowa yake yi wa ba. Dan haka kar ki daina addu’a khadija, kuka baya maganin matsala kamar yadda na gaya miki ɗazu”

 

Subhanallah, iman taji voice ɗin babu adadi, musamman jin sunanta na asali a bakinsa, yana da very deep voice irin na cikakken namiji jarumi, wanda muryarsa kawai ta isa sanya mutum shiga hankalinsa.

 

“Alhamdilillah, yaya umar ashe kana ganin status ɗina, haka ne na kusa sauka a karo na uku, na gode sosai yaya umar, na yadda you are very simple, unlike before da kake bani tsoro” ai shi ma a nasa ɓangaren, ya saurari voice ɗin ta bai san iyaka ba, sassanyar muryarta wadda yake gauraye da sigar shagwaɓa, haɗi da iyayi mai matuƙar daɗin sauraro”.

 

Tunawa yayi da Jabir ne zai aureta, gaba ɗaya ya ji wani irin haushi ya kama shi, ba tare da yayi reply ba, ya rufe datar sa ya kwanta.

 

Yayi shiru yana tunanin, duk wanda ya auri mace kamar iman, idan bai tausaya mata ba, sai yaushe, mai zai sanya mutum ya din ga ɗaga mata murya haka, yarinyar da gaba ɗayanta kalar tausayi ce.

 

***

Sai da ta kwana biyu, sannan aka sallami iman suka koma gida, sai dai ammi ta shiga saƙe-saƙe a kan batun auren nan.

Rumaisa ta zauna ta zana takawa a plane sheet, tare da calendar a ƙasa, wadda kullum take cancel ɗin kwanan wata, na lokacin dawowar takawa.

Laila ta ce “Rumaisa meye haka? Ya zaki liƙe mini hoton gunki a ɗaki”

 

“Papan ne gunki, wallahi ba gunki bane”

 

“To ni a wurina gunki ne mana, kawai ki zana ɗan alajani ki kafe mini, baga hotonsa nan a waya ba”

 

Ruma ta ce “Ni bana son na waya, na fi son wanda na zana shi da kaina, ba kin hanamu yin video call ba, kuma ke kullum sai kin ga mijinki ba, ki bar mini zanena”

 

Lailaa kawai tayi murmushi, wasu lokutan rigimar rumaisa dariya take bata.

 

“Kin sha kununki na yamma, da maganin maman ilham?”

 

“Na sha mana, ai anty laila bana wasa”

 

Ta ce “Good, yanzu dai je ki ɗaukko jakarki ta islamiyya, da ta makarantar boko muyi karatu, kin ga exams za ku fara”

 

Ruma ta tashi ta ce “Bari in ɗaukko, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi”

 

Tana fita falo tayi kiciɓis da Jabir, ya ɗago a yastune ya kalleta ya ce “Yauwwa dan Allah yi mini magana da iman mana”

 

Cikin tsiwa ta ce “Kai ka isa? Wallahi baka isa ka aikeni na je ba, ka nemi ƴar aiken ka”

 

Jabir ya ce “Wai ke meye haka, ka kowa ma sai ki ci masa mutunci baki da kunya?”

 

“Ina dai yi wa mutane marasa kirki, kuma wallahi ba zan bari ka auri iman ba in sha Allah, yayana zata aura yaya Umar ba, kuma zaka gani, idan kana da zuciya ka canza hali, ka fara zuwa ka kula da mahaifinka, kan ka yi tunanin auren iman”

 

Ba ƙaramin zafi maganganunta, suka yi

 

Ya risuna ya gaida ammi, suka gaisa yace mata wurin iman ya zo, ammi ta ce masa iman tana bacci, likita ya ce a bari ta samu hutu.

 

Ko da jabir ya tafi, rumaisa ta din ga ziga ammi, tare da nanata mata idan har jabir bai tausayawa mahaifinsa yayi jinyarsa ba, tayaya zai tsaya ya kula da iman da ciwonta?.

Daɗin daɗawa ga masifa da tijarar mahaifiyarsa, da take iƙirarin cewa ba za a auro mata wadda ba ta da asali ba.

Kasancewar rumaisa tayi sara a kan gaɓa, domin zuciiyar ammi ta fara kaiwa da komowa a kan batun, ya sanya ta ji ita ma ta gamsu da maganar rumaisa.

 

Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara ɗan sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaɗan.

Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta ɗan ja shi da hira.

Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan riƙe mata shi, gaba ɗaya mai sunan baba mu’amala da shi sai mai haƙurin gaske, miskili ne na bugawa a jarida.

 

Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da ƴar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaɗe Saboda rumaisa.

 

Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne.

Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu.

 

Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki?

 

Mahmud ya ce “Wace mai jikin?”

 

“Ƙanwarka mana, khadija” sai da Mahmud ya ɗan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne.

 

Ya ce “Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai”.

 

Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba.

 

Mahmud ya ce “Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sauƙi, dan na ganta ɗazu tare da daughter na a garden”.

 

Mai sunan baba ya ce “Ina so mu yi magana ne, ban taɓa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau ɗaya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai”

 

Mahmud ya ce “Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya”.

 

Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce “Ina shirin kiranka”

 

Ya ce “Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba ɗaya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition ɗin da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ƙara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu”

 

Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta roƙi ya auri iman.

Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ƙalubalen rayuwa, a wannan gaɓar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu a kan lamarin, dan jin kunnensa ya ji jabir ɗin na gayawa mummy, wambai ya san maganar, turaki zaa kaiwa kuɗin auren.

 

Bai gama tunanin ba ya ji muryar mai sunan baba ya ce “Ban taɓa neman alfarma ayi wa wani abu ba, a karon farko na roƙe ka, ko dan lafiyarta”

 

Mahmud ya ce “Kar ka damu, zan san abun da zan yi a kan lamarin in sha Allah”.

 

“Masha Allah na gode sosai”

 

Mahmud yayi shiru yana kallon wayarsa, ya nunfasa ya ce “Allah ya sa rabonka ce Malam Umar, ni na yaba da dattakunka”

 

***

Laila ce suke waya da takawa, tana gaya masa ruma ta ishe ta da rashin ji, ita da ɗan ta, yana ta dariya mussaman da ta ce wai ruma ta zana mata aljani ta ajiye a ɗaki, wai hoton takawa.

 

“Anty laila bani shi mu yi magana” ruma tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar wayar.

 

Laila ta ce “Ungo ku ƙarata, ban da video call dai, bari na shiga wanka”.

 

Ya ce “Budurwar”

 

“Mmm saurayin, ya garin? Ya karatu?”.

 

“Alhamdilillah, ya naki karatun, na ji anty laila ta ce tana yi miki lesson, kun kusa fara exams, dan Allah a dage a mayar da hankali”

 

“To in sha Allah, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi”

 

“Meyasa kuma?”

 

“Ba karatu kawai ake koya mana ba, sai a din ga faɗar wasu maganganu”

 

Tun da ta faɗi haka ya san akwai ƙura, ya ce “Wasu maganganun kenan?”

 

“Wai se malamar ta din ga tsayar da mu, wai za ayi lecture, ka ji abun da take cewa kuwa?, wai a din ga saka ƙanan kaya ana karairaya sai ka ce wasu karuwai, yanzu dan Allah ya dace a zaunar da mutane ana gaya musu haka?”

 

Da ƙyar ya iya gimtse dariyarsa ya ce “Ke ya aka yi ki ka san karuwan ne suke haka?”

 

“Ai in gaya maka, da akwai wani gida a unguwarmu, sai matan su dinga saka riga da wando, ko mini skirt, suna yawo, aka koresu, na ji ana cewa gidan karuwai ne, har da vest fa suke fitowa waje ana kallonsu, na zo ina bada labari a gida, mai sunan baba ya sakani kama kunne, aka ce mini kar in kuskura abun da suke yi ya burgeni, idan mutum yayi irin wannan ba ga muharraminsa ba ɗan wuta ne. Ni fa wani abun ba zan iya faɗa ba ne, wallahi ni duk mutuncin malamr ya zube a idona ma, ni kuwa da ta fara nake tashi na tafi.

Da fa sun rainani ba su zata ina da miji ba, sai da malama ta ce musu ni matar aure ce, wai wata ta ce mini, wai zan sai maganin mata? Na ce mata ni ban san shi ba, dan Allah a chemist ana ware maganin maza da na mata?”

 

Ya ce “A’a”

 

“To a in gaya maka, na ce mata ni idan bani da lafiya asibiti ake kaini, kawai ta  nuna mini Wasu ƙulle-ƙulle da robobi mai hoton ƴan iska a jiki, Wai in saya, na rufe idona na ce a’uzubil’ahi, gaskiya ni dai a cireni daga makarantar nan”

 

Maimakon ta ji ransa ya ɓaci kawai sai ya din ga tuntsura dariya, har da tari, laila ta ƙarasa ta ƙwace wayar, ta ce “Ke dai ban taɓa ganin yarinya mara kan gado kamar ki ba? Wai ke baki da ƙawaye ne?”

 

“Nifa ƙawata ɗaya habiba, ko nayi ƙawaye mama korarsu take yi, kuma ko ba ta kore su ba, idan muka yi faɗa duka nake yi musu sai mu ɓata”

 

“Aikuwa wannan karatun, dole na zauna na ɗora miki shi, idan kin ƙi ganewa kuma shi idan ya dawo ya karanta miki yadda zaki fuskanta. Haba ke gaba ɗaya abaibai ce ba kya gane komai kenan”.

 

“Anty laila ki daina hantarata, zamu yi faɗa”

 

“To muyi faɗan mana, ke zaki yi wa kanki ai”.

 

Rumaisa ta kalleta ta ce “Saboda zaki daina sai mini garin kunun sabayar maman Khadija ko? Ba ita ce a zariya ba lambarta 0703777 7442. Sai maman Ilham mai magani ba da ke cikin garin kaduna kawo road ba, lambarta 08135613021, na riƙe komai tsaf a kaina saboda irin haka”.

 

Laila ta ce “Iko sai Allah, ke yanzu zaman hadda ki ka yi kenan?”

 

“Ai Anty laila ba komai ake faɗa mini ba, in dai an yi abu a gabana, tsaf nake haddace komai tas a kan nan nawa”.

 

“To kin kyauta, tashi ki je kitchen ki haɗa mana kayan aiki, yanzu zan zo ki gwada mini girkin da na koya miki, in gani idan da gaske kina haddace komai ɗin”

 

Rumaisa ta tashi ta ce “Yanzu kuwa”.

 

***

 

Iman duk ta kuma zama so silent, ba babban abun da yake sanyata farinciki, irin ƙoƙarin jan mai sunan baba da hira, da safe ta gaishe shi, daga nan yayi mata ya jiki. Mutum ne miskilin gaske, tana shan fama, amma wasu lokutan ya kan saki jiki, mussman idan tana yi masa hirar karatun addini.

Wani irin matsanancin tausayinta yake ji, da ya tuna Jabir, sai gabansa ya faɗi, ya san duk wani kauce-kaucensa son iman yake yi, gashi shi bai san ta ina yakamata ya fara ba, bai san meya kamata yayi mata ta din ga farinciki ba, saboda shi ya saba da bosy life, ba wasa.

 

Rumaisa ce a tsaye a banɗaki za ta yi wanka, tana ƙarewa kanta kallo a mudubin banɗaki, har da tsalle tana ɗan juyi, ganin abun arziki ya fara fitowa, yana cika.

“Wayyo daɗi kasheni, zan wuce gori da wulaƙanci, na ga me sake ce mini ƙwaila, kai za a ga jan aji idan suka ƙara girma, wayyo ni maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni yasin”

Ta gama wankanta, ta fito ta shafa mayukan gyaran fata, ta saka kaya, ta kuma tsayawa tana kallon mudubi, ta ce “Hmmm, na ga wanda zai sake ce mini ƙwaila, mu haurata da shi, har shi papan, yanzu dai sun fi ƙarfin murfin jarkar faro”

 

Ta ɗaga kai ta kalli zanenta, da take kansile date kullum, na kwanakin da ya rage ya dawo.

 

A hankali ta furta “Lokaci baya sauri”.

 

Ammi fa gaba ɗaya ta ji batun auren nan na iman da jabir ya fita daga ranta, kuma ta bi maganar rumaisa cikin tsanaki, taga lallai gaskiya take faɗa, ta sanyawa ranta aure lokaci ne, bai kamata ta jefa rayuwar iman cikin hatsari ba.

A wannan zullumin turaki ya kirata, ya sanar da ita, wambai ya ce masa zai kawo wa jabir kuɗin aure.

Takanas ammi taje gida, ta iske turaki, ta nemi ya taimaka a janye maganar nan.

Turaki ya ce “Giwa saboda ne, kin fi kowa sanin halin wambai, daga ni har ke ba zai saurara mana ba”.

 

Nan ammi ta yi masa bayanin komai, tuntuni ta so ta yiwa wambai maganar, amma ta san ba zai saurareta ba, turaki ya gamsu da maganganunta, dan ya san halin hajiya Lubabatu sarai, za ta aikata fiye da haka, ga yarinya na fama larura.

Dan haka ya ce shi da ita yakamata su je wurin wamban, su yi magana da shi.

 

Ammi kamar ta ce ba sai sun je tare ba, saboda tana fargaba wambai ba ya yinta ko kaɗan. Amma yadda ta iya, tun da suggestion ɗin turaki ne.

 

Aikuwa kamar yadda ta tsammata, wambai ya balbalesu da faɗa ta in da ta shiga ba ta nan yake fita ba, ya din ga masifa.

 

“Kana bani mamaki turaki, da ka ke biyewa matar nan, dan kawai tana sirikarka, ke ba abun farincikin ki bane ba, kamar jabir zai auri yarinyar da ba wanda ya san iyayenta sai ke da mijinki a da’awarku.

Nagartaccen yaro mai daraja daga gidan sarauta, sau nawa ana shirin aurenta ana fasawa, saboda wannan abun kunyar?”.

 

Turaki ya ce “Allah ya baka yawan rai, ba jabir ɗin ake gudu ba, ita mahaifiyarsa da ta je har gida, ta nuna bata son abun, ta ci musu mutunci har yarinyar, wanda sai da ciwonta ya tashi, ita ma fa ƴa ce Allah ya baka yawan rai”

 

“Ita lubabatun ce ta ce ba ta son auren, bayan mun gama magana da ita?”

 

Da mamaki ammi ta kalleshi, sannan ta ce “eh, har gida taje ta ce mini ba ta so”

 

Wambai ya kira wayar hajiya Lubabatu, amma cike da ƙwarewa a mugunta, ta hau salati ta ce ƙarya ne, kawai dai giwa ta ce ba zata bawa jabir auren Iman ba, amma ita ba ta ce ba ta so ba.

 

Masifar da wambai yake yi, tuni idonta ya cika da hawaye.

Turaki kansa ya san sharri ne, da tsabar mugunta, irin na hajiya Lubabatu.

 

“Tun da abun naki haka ne, ba kara ba mutunci a cikinsa, ai dama a kwanakin baya, da ake ta surutu a kak yarinyar da takawa, na ce lallai ki aurar da ita, to zan sake jaddada miki, nan da watanni uku, ko dai ki aurar da yarinyar nan, ko kuma ki mayar da ita in da ki ka tsinto ta, kuma a wannan karon ba zan canza magana ba.

Sannan abu na gaba, ƙara tayi yawa a kan wannan yarinyar sirikarki, daga zuwanta gida tana yi wa mutane sharri, tana haddass husuma, jamila ta kawo mini ƙara, na so na zauna da ku, ta ce a bar maganar, still na samu labari a kan tana yayaya cewar jamil ne ya saka aka yi garkuwa da ƙanwarsu, to ahir ɗin ta, ki ja mata kunne, gidan sarauta ba wurin wasa bane ba” Ammi ta risunar da kai sannan ta tashi ta bar ɗakin, ranta babu daɗi, yayin da tausayinta ya mamaye zuciyar turaki, tana da kyakywar zuciya, sai dai tana ta fuskantar ƙalubale kashi-kashi a rayuwarta da ta iyalanta.

 

Yanayin yadda ammin ta dawo ne ya tabbatar musu akwai damuwa, har ruma za tayi magana, amma laila ta hanata.

 

Yau wunin yau idon mai sunan Baba yana kan waya, ko zai ga saƙon iman, amma shiru, shikuma ya kasa yi mata magana, har dare shiru, gashi ya riga ya saba da daddare ɗan jan sa da take da hira, yana yi masa daɗi.

Haushi ne ya ishe shi, jin yadda Aliyu ya cika masa kunne da surutu shi da habiba, ya saka waya a speaker sai ƙyalƙyala dariya yake yi, habiba ta karkace murya tana yi masa waƙa, murya kamar an shaƙe kuliya.

 

“Kaga ka cika mini kunne, ko dai ka fita, ko kayi mini shiru.

 

Aliyu ya miƙe tsam da wayarsa, ya koma tsakar gida, duk da sanyin da ake zabgawa.

 

***

Jabir ne a zaune, hajiya Lubabatu da Mummy sun saka shi a gaba, suna ta yi masa famfo.

 

“Na sha gaya maka giwa ba ƙaunarka take yi ba, ka din ga nane musu, to gashi ƙiri-ƙiri ta hanaka auren ƴa, saboda azabar ƙarya ta je ta ce wai ni ce bana son auren nan, mun yi haka da kai? Da na nuna bana so ka dage, cewa nayi Allah ya sanya albarka, amma da yake mukafuka ce, ba ta yi niyyar baka auren ba, ta je ta ce nice bana so”.

 

Mummy ta amshe ta hanyar cewa “Banda abun jabir, kai da ake yi wa fafutukar samun kujerar mahaifinka, ina kai ina wata ƴar tsintuwa, mara asali mata gata, kai ana ƙoƙarin ka samu kujera, amma ka nacewa Adam, shi ka san me suke yi ta ƙarƙashin ƙasa, dan ganin kujerar ta koma garesu, ga mata nan bila adadin a gari, ni ko ruƙayya ma sai na baka”

 

Hajiya Lubabatu ta ce “A’a wace irin ruƙayya kuma? A dai cigaba da neman kujerar, shima uban nasu ban taɓa tunanin zai kai haka a raye ba, kalli shi adam ɗin da kake liƙewa, yadda yayi suna a ƙasar nan, duk gaku matasa amma aka ware shi, aka tura shi wakilci, yayi aure ya haifi ɗa, ga aikinnsa ga kasuwanci, kai kana nan kana fama daga kai har jamil ɗin uwar me ku ke da shi, duk da dukiyar iyayenku ku ke taƙama”

 

Jabir yayi shiru tare da gazgata maganganun da tun a baya su mummy suke gaya masa bai ɗauka ba, tare da mantawa da asirin da takawa ya daɗe yana rufa masa tsawon shekaru.

 

Mummy kuwa ƙulattar Hajiya Lubabatu ta yi, da ta ce ya auri ruƙayya ta ce a’a, wato a tunaninta ya samu mulki, aci moriyar ganga a yada kwauronta.

 

Mummy a ranta ta ce ‘Lubabatu baki da hankali, da ni ki ke zancen, lokaci yayi da zamu raba gari, kowa ya san in da ya kama’.

 

Kasa jurewa mai sunan baba yayi, ya fara tunanin ko jikin iman ne ya dawo, dan haka da kansa ya kira iman a waya.

Sallamar da yayi ta amsa cikin siriryar muryarta.

 

“Jikin ne dai?”

 

“A’a barka da safiya yaya umar”

 

“Meyafaru?”

 

“Bakomai” tayi maganar cikin sauke numfashi.

 

“Something is going wrong, feel free to share it with me”

 

“Yaya umar ba zan dameka da matsalolina ba?”

 

Cikin nutsuwa ya gyara zamansa ya ce “If you are free with me, let’s share it together”

 

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ce “An yi cancel ɗin engagement ɗina da za ayi”.

 

“Ba abun da ki ke so kenan ba?”

 

“Ba cancel ɗin ya dameni ba, tun da Allah ya sa na buɗe ido a hannun ammi, take bani kariya da nuna mini ita ta haifeni, amma mutanen da suke kusa da ita, basu bata goyon bayan hakan ba. Saboda ni ba irin tashin hankalin da bata shiga ba, kullum cikin damuwa take, kullum cikin sintiri kaini asibiti, kullum cikin neman abun da zai sani farinciki take,. Amma ni na kasa kawo mata farinciki ko sau ɗaya.

Ban san dalilin fasa Engagement ɗin ba, mai girma wambai ya ce ko tayi mini aure nan da watanni uku, ko ta mayar da ni in ta tsinto ni, babban abunda ya dameni kukan da ammi ta sha, ta ce da ta rabu da ni, gara ta ɗauke ni mu bar gidan, ni rasa me ma zan yi, ina son ammi amma ba zan so ta bar gidanta ba”.

 

A tsakiyar zuciyarsa ya din ga jin kukan iman, ya jingina jikinsa da bango, wata irin karaya ta kama shi.

 

A hankali ya ce “Khadija, kukan nan yana taɓani sosai, bana son jin kukan mace, ko ban santa ba, zamu yi waya anjima. Amma dan Allah bana son sake jin labarin kina asibiti, ya isa haka”

 

A hankali take sassauta kukan, ta ce “Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun da yake damuna, na gode sosai”

 

“Don’t mentioned, ki ci abinci ki kwanta ki yi baccinki, ki cigaba da addu’a, ba abun da zai faru sai ikon Allah khadija” shi kansa mamakin yadda ya tausasa murya sosai yake, bai taɓa zaton ya iya rarrashi haka ba.

 

Rumaisa kuwa Mahmud ta kira a wayar Anty laila, ta ce tana son ganinsa a in da suke haɗuwa.

 

Babu jimawa kuwa suka haɗu, sai dai cikin tsananin fushi ruma ta ce “Daddy anya mummy na son taga Annabi kuwa, daga ita har babar jabir fuska kamar an mari biri? Ya za ayi ta zo ta ce ba zata bari ɗanta ya auri Iman ba, ammi ta ce a fasa a janye, ta ce ita ƙarya aka yi mata ba ta faɗa ba?

 

Ammi sai kuka take yi, har da masu kiranta a waya, ana bata kyauta ba, ta hana jabir iman, gashi wambai ya ce idan ba ta aurar da iman ba ta mayar da ita in da ta tsinto ta, wai ya suke so baiwar Allah nan tayi ne, daga ita har Iman ɗin sai koke-koke suke yi, wai kai ba abun da zaka iya yi a kai? To ni zan je wurin wamban sai na tonawa kowa asiri da kaina, ayi wadda za ayi ta ƙare!

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 76 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button