*ASM Bk2010*
_Destiny may be delayed but cannot be changed….._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..Washe gari da Asuba Amadu da kanshi ya je ya tasheta tay salla yace ta tabbatar tayi Karatun Alqur’ani kuma tayi Addu’a sosae tace mashi to sannan ya wuce Masallaci shima, ba laifi taji dad’in jikinta hakan yasa ta fara yin shirin zuwa Makaranta tana gama sallar, lokacin data fita gwaggo na kitchen ta nufi can ta tsaya bakin kopa ta gaisheta don lokacin da take karatu taga gwaggon ta lek’a dakinta da fara’a ta nufota tana amsa gaisuwar tace “ya ciwon kan jiya dana dawo kina bacci Amadu yace man kina ciwon kai” d’an Murmushin yak’e tay tace mata ta samu sauk’i gwaggon tace “Oh ciwo dae ya taso ki gaba kwanakin nan daga wannan sai wannan Allah ya baki lpy mai d’orewa” sadda kanta tay ta amsa da Amin kafin ta d’ago tace mata zata tafi Makaranta da d’an mamaki gwaggon tace “Makaranta da wuri haka, ban tunanin bakwae fa ta k’arasa in ma tayi to yanzu ne” d’an sosa gefen kanta tay tana kallon gwaggon tace “ai zamu fara practical ne yau wanda zai fito mana a Jarabawa shiyasa nike son zuwa da wuri mu samu gaba yadda zamu ga yanda ake yi sosae” jinjina kai gwaggo tay cike da gamsuwa ta juya tana Fad’in bari to ta mik’o mata abun karin kumallo taci sai ta tafi,bayan ta amshi Breakfast d’in ta koma d’aki ta fara ci, ba wani da yawa taci ba ta maida kayan Kitchen lokacin gwaggon bata ciki ta bita d’aki tace mata zata tafi ta bata kud’i, dama koda Haisam ke kaisu tana bata isassun kudin tara da zata iya hawa ma Bus har tay break, saida ta lek’a d’akin kawu Amadu tace mashi ta tafi ya rakota har kopar gida yana k’ara tausarta akan ta d’age ta cire damuwa ta maida hankali kan karatunta, saida yaga tayi nisa ya koma cikin gidan, duk da bata jin k’arfin jikinta sosae haka tay ta sauri don kar Haisam ya isketa a kan hanya har ta k’araso lungun gidansu Haulat, lokacin da ta shiga d’akinsu bin ta da ido Haulat d’in tay ta kasa mata Magana saboda zullumin jin yadda sukae da Haisam jiya itama Fatun kallonta kawae take Haulat din tace mata ta zauna mana, bayan ta zauna gefen katifar itama ta zauna a kusa da ita can dae ta daure tace “kin fad’a mashin ne?” girgiza mata kai tay alamar a’a, wani sanyi haulat taji har saida tay d’an Murmushi kafin ta tambayeta ya akai bata fad’a mashi ba, farko shiru Fatun tay hakanan taji bata son fad’a mata hirar da ta iske suna yi hakanne yasa tace mata kawae ta d’auki shawararta ne shiyasa ta fasa Haulat d’in tace mata ta kyauta,
“Amman ya naga kin shiryo da wuri ko Ya Haisam dinne ya kawo ki?” girgiza mata kai tay tace” bashi ya kawo ni ba ni na taho,ban son ina ganinshi” cikin karyayyar murya tay Maganar idonta har sun ciko da kwalla Haulat ta dafata tace “na fahimta Allah yasa hakan yasa ki samu sassaucin abunda kike ji” a hankali ta amsa mata da Amin, tambayarta tay ko ta kawo mata abun kalaci tace mata taci a gida haulat d’in ta tashi ta fara shiryawa saida lokacin da suka saba tafiya yayi sannan suka tafi. Misalin k’arfe 7:30 Haisam ya parker a kopar gidan yay horn kamar yadda ya saba yi in ba kowa a waje, saida yayi sau wurin ukku sannan Amadu ya fito ya nufi Motar Haisam d’in ya sauke glass da Murmushi Amadu ya gaidashi ya amsa tun kafin ya tambayi Fatun Amadun yace mashi sun tafi tun d’azu, shiru Haisam d’in ya d’an yi sai kuma yace mashi Ok, Amadu yay mashi sai ya dawo ya amsa daga haka glass d’in ya d’aga sama ya rufe yaja Motar Amadu yabi bayan Motar da ido kafin ya d’an girgiza kai ya shige gida,
Koda suka je Makarantar Haulat na lura da ita sam bata wani saki jiki ba har gara ma lokacin da bata kaiga ganin Iv d’in ba ta d’an fara saki amman yanzu an koma yar gidan jiya, saidae tay shiru ko ta d’aga ma Mutum kai in yayi mata magana sai ta kama take bud’e baki tay Magana, ita kanta halin da take ciki na matuk’ar damunta ba kuma kamar hukuncin da ta yanke na daina ganin Haisam duk sai take jin wani irin kad’aici gashi zuciyarta sai tay ta ayyana mata fuskarshi bata da aiki sai tunane tunane,Haulat dae bata gajiya da k’arfafa mata guiwa, A ranar da daddare bayan tayi sallar isha ta fita waje wurin kawu Amadu yana ganinta yace “Juliet ya akai” yay Maganar yana yar dariya ita kuma ta d’an tura mashi baki ganin tay mashi tsaye yasa yace mata ya akai ne tace “dama bacci nike son yi na kasa shine nazo ka bani wannan Maganin na jiya” bud’a mata ido yay yace “ke kina son zama yar k’waya ne?” a sanyaye tace “a’a ba magani bane?”
“Eh magani ne amman in kika saba bazaki iya bacci ba sai da shi don haka ki je ki kwanta kawae baccin zai zo in sha Allah kiyi Addu’a” tana shirin k’ara yin Magana ta jiyo k’arar bike d’in Haisam ya dawo daga Gym aikuwa da sauri ta juya gudu gudu ta shige gida ta la6e cikin zaure tana lek’enshi har yazo ya wuce, sauke ajiyar zuciya tay ta d’an cije baki kafin ta nufi cikin gidan tana shiga d’aki ta haye gado ta kwanta tana ta tuna rayuwarsu da Haisam kwalla na gangaro mata duk ranta bai mata dad’i sai can dare ya nisa bacci yay awon gaba da ita. Washe gari ma sai ga Haisam yazo d’aukarta lokacin ta tafi Amadu ne ya lek’a ya k’ara ce mashi ai basu dad’e da tafiya ba ya amsa da Owk ya tafi, abu kaman wasa Amadu na cewa k’ilan in yazo sau biyu ko ukku ya daina zuwa sai gashi har ranar Juma’a saida yazo a wannan lokacin kunya ta gama rufe kawu Amadu hakanan yake daurewa yana ce mashi ta tafi shi kanshi ba don yana son hakan ba don sai yaga kaman ana wulakanta Haisam dinne wanda yafi karfin ai mashi haka,
Zaune take a aji duk ranta a jagule yake kukan zuci kawae take wanda akace yafi na fili rad’ad’i sanin yau saura sati d’aya Haisam ya tafi kaman yadda taji a bakin gwaggo don sam bata san Fatun ma bata zuwa gidan Hajiya ba a tunaninta in bata nan tana zuwa wani lokacin kuma tana fita da sunan zata can d’in gudun kar gwaggo ta gano bata zuwan amman data fita sai tay tafiyarta gidansu Haulat haka in Fanan ta kira waya tana amsa su gaisa don sosae take kiran layin gwaggo ta gaishe da ita wani lokacin ma in Fatun na d’aki data ji suna waya sai tay baccin k’arya, Haulat har ta gaji da bata hakuri sai dae tay ta bin ta da ido don tasan in dai Haisam ba tafiya yay ba ta tabbatar ta rasashi bazata rage damuwar da take ciki ba a yanzu, suna zaunen Malaminsu na Chemistry ya shigo bayan yan ajin sun tashi sun gaidashi yace su same shi a Lab ya juya ya fita duk yan ajin suka mik’e suka fara fita hannuwansu ruk’e da littattafansu da biro, mik’ewa Haulat tay idonta akan Fatuu da ta d’aura Fuskarta kan desk, tasan ba bacci take ba don in dae ba malami a ajin haka take yi tace “Fatuu ki tashi mu tafi Lab za’ai Practical” shiru bata tanka mata ba har saida ta maimaita mata sannan ta d’aga mata hannu alamar taje kawae, jiki a sa6ule Haulat ta koma ta zauna kaman zatai kuka tace “Don Allah Fatuu kiyi hakuri nasan kina yi wllh, amman karki bari damuwar da kike ciki ta shafi karatunki wannan Practical d’in fa kinsan shine zai fito mana a ssce kaman yadda Malam yace kuma dole ba yadda za’ai mutum yaci paper d’in Chemistry da physics ba tare daya ci Practical ba ki yi hak’uri ki taso muje” jimm ta d’anyi kafin can ta d’ago idanunta sun yi ja cikin disashewar murya tace “kije Haulat ko naje bazan gane komae ba damuwa tay man yawa wllh amman daga baya sai ki koya man” tana niyyar maida kan Haulat ta kama hannunta tace “ki daure pls, sai kinfi ganewa in a gabanki akai ni kinsan ba lalle in gane ba sosae tunda wani lokacin kece ma ke k’ara man bayani in ban gane abu ba” zare hannunta tay ba tare data ce mata komae ba ta maida kanta kan desk, ba yadda Haulat ta iya dole ta mik’e don kar ai biyu babu ta d’auki littafinta da biro ta fita. Sai lokacin da aka tashi suka fito daga Laboratory d’in kasantuwar ranar Juma’a ne d’aya saura ake tashi gaba daya, lokacin da Haulat ta shigo ajin Fatun na a yadda ta barta, d’an girgiza kai tay cike da tausayawa ta nufi seat d’in ta maida littafinta a jaka kafin ta d’an bubbuga kafad’ar Fatun tana Fad’in ta tashi su tafi gida an tashi, shiru kaman bazata d’ago ba can kuma ta d’ago idanunta sunyi jawur da alama kuka tasha tana son karatunta amman damuwa ta hana ta maida hankali ji take gaba d’aya karatun ya fita a ranta abunda zuciyarta keso ne kawae a ranta,tasan ko taje gidan ba wani samun sauk’i zatayi ba gashi bata son kawu Amadu yaga bata d’auki shawararshi ba yaji haushi dama ba k’aramin kokari take ba a gidan tana 6oye damuwarta sai tazo makarantane duk sai abun ya kacame mata gashi yanzu tasan gwaggo na nan don aikin rana take sai karfe biyu zata tafi a halin da take ciki kuma tasan da taje gidan zata gano akwae abunda ke damunta don yan kwanakin nan tana yawan tambayarta kodai wani abun ke damunta ciwoce ciwocen sun yi yawa, tunawa da wannan yasa tace ma Haulat taje kawae ita ba yanzu zata taho ba, cike da damuwa Haulat tace “haba Fatuu ya za’ai ki zauna a Makaranta ke kad’ai bayan an tashi ba kowa don Allah ki taho mu tafi” da Haulat d’in ta takura mata akan ta tashi su tafi sai tace mata akwae inda zata je ne amman sai ta d’an k’ara hutawa zata koma gidan anjima, sarai haulat tasan k’arya take ba wani wuri da zata je amman sai tace to bari ta zauna in ta hutan sai su tafi tare, cike da tsiwa tace “to in banson zuwa dake fa, nace ki tafi ai ba 6acewa zanyi ba ko zan dawo anjima” d’an girgiza kai Haulat tay ta mik’e ta d’auki jakarta ta had’a data Fatun tace bari ta tafin mata da ita ba don ranta yaso ba ta tafi tana yi tana waiwayen Fatun har ta fita ita kuma tay kwanciyarta saman seat.
Cikin sa’a Haulat ta samu Bus tana fita ta hau, daidai kwanar da aka saba aje su suka sauka da sauran yan Unguwar, bayan ta fita lungun tana shirin hawa hanya sai ga Motar Haisam ta taho shima ya dawo daga aiki dama duk juma’a a gida yake salla, tsayawa tay tana kallon Motar don ta gane shine yana zuwa saitin ta ya taka burki ya tsaya a hankali kuma glass d’in Motar ya sauka fuskarshi ta bayyana, da d’an Murmushi Haulat ta gaishe shi fuska a sake ya amsa mata yace mata an dawo tace mashi eh ya jinjina mata kai tana ta d’ar d’ar a cikin zuciyarta kar ya tambayeta Fatuu don tasan muddin ta fad’i mashi halin data baro ta to tabbas zai bita ne in kuma yaje ba makawa tasan Fatuu na iya fad’i mashi halin da take ciki ita kuma bata son hakan ya faru, kawae sai taga glass d’in ya fara d’agawa sama daga haka yaja Motar Haulat ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta juya ta tafi, a daidai gaban shagon kawu Amadu ya tsaya lokacin Amadun na shago yayi wankan juma’a yana jiran lokacin sallar ya idasa yi, yana ganin Motar ta tsaya ya fito da sauri glass d’in d’ayan side d’in ya sauka Amadun ya lek’a ta nan yana gaidashi ya amsa mashi kafin ya tambayeshi Zaraah ta dawo ne, shiru Amadu ya d’anyi alamar tunani sai kuma yace “gaskiya dae banga wucewarta ba amman bansan koda ina cikin d’aki ba don ban dad’e da fitowa ba bari in ga kota dawo” d’aga mashi kai yay ya juya ya nufi gidan bada jimawa ba ya dawo yace mashi bata dawo ba ya d’anyi shiru kaman mai tunanin wani abu sai kuma yaja Motar bayan ya amsa mashi da Ok, Yana isa gidan toilet ya shiga bayan ya rage kayan jikinshi a laundary, bada jimawa sosae ba ya fito ya fara shirin zuwa Masallaci,sanye cikin galleliyar shadda light blue ya d’aura hula data hau da kayan sai daukan ido take don yasan da ya je ba hular Hajiya sai tay Magana, haka ma takalman kafarshi kalar kayan ne agogon diamond d’in hannunshi nata kyalli sai sakin fitinannan kamshi yake ya nufi part d’in Hajiya, atare kaman ko yaushe suka tafi Masallacin bayan sun dawo suka nufi dining Area Saude tay serving nasu suka fara cin Abinci can bayan sunyi nisa da farawa Hajiya ta dakata idonta akanshi tace “wai nikam Fateema na zuwa wurinka,shirun yay yawa yaushe rabon da in ganta gidan nan, rannan da muna waya da Dijen nike tambayarta kwana biyu banga Fateema ba sai take ce man ai tana ce mata tana zuwa kilan bata iske ni ne nace to kilan dae wurin yayanta take zuwa ko kuma lokacin da take zuwa bani nan d’in amman dae gaskiya da tana zuwan zan ganta ne tunda ai ba ko yaushe nike fita ba, gaba d’aya tunda tay ciwon nan ta canja kwata kwata duk da dae dama mai irin ciwon nan komi yay ba abun mamaki bane” idon Haisam a kanta bayan ta gama Maganar yace “kinsan they’re about to start their final exams k’ilan shiyasa bata da time en zuwan” jinjina kai tay sai kuma tace “amman kai d’in tana zuwa wurinkan?” shiru ya d’anyi sai kuma yace mata eh tana zuwa ta gaidashi kuma yana kaisu skul, shi kanshi baisan miyasa yay mata k’aryar ba abunda ba halinshi ba, gyad’a kai tay cike da gamsuwa taci gaba da cin Abincinta, kasa cigaba da cin Abincin yay ya mik’e ganin hajiya na kallonshi yace mata zaiyi abu a part d’inshi ne daga haka ya nufi cikin parlon ya fice, part d’in nashi ya koma yana shiga ya zauna kan kujera yasa hannu ya dafa gaban kanshi, tun bayan da sukai Magana da Abbas abun keta damunshi a rai yana son ya kauda tunanin amman abun ya faskara zuciyarshi na damunshi da son sanin da gaske ne abunda Abbas ya fad’a saidae kuma wani bangare na zuciyar na gargadinshi kan rashin sanin shi yafi kaman yadda Abbas din ya fad’a amman tabbas ya fara zargin akwae abunda ke damunta ba ciwon da yake tunani bane kad’ai ba kamar Maganar da Hajiya tayi, yanzu ya gane tana yi ma Grandma d’inta k’aryar tana zuwa gidan alhali kuma bata zuwa,mi zaisa tay haka? ya jefa ma kanshi tambaya, to ko dae anyi mata wani abune don har yanzu yana shakkun Maganar Abbas saboda yasan wacece Zaraah tun bata kai hakan ba, haka ya dingi sak’e sak’e a ranshi gashi shi sam baison damuwa duk sai yaji ya takura shiyasa ba k’aramin abu ke tsaya mashi a rai ba, cire hannun yay ya d’auki wayarshi dake ajiye a gefe ya shiga Contacts d’inshi bayan ya bud’e, lambar kawu Amadu ya kira bugu biyu yay picking yana gaidashi ya amsa mashi kafin ya tambayeshi Zaraah d’in ta dawo yace mashi a’a gaskiya ba kowa ma a gidan don gwaggo ma ta tafi aiki amman dae yana tunanin ko sun tsaya lesson ne don yanzu wasu ranakun suna kaiwa har yamma, amsa mashi yay da Ok ya kashe wayar, tunani ya shiga yi mi zaisa ya ga Haulat ta dawo in har lesson suka tsaya tunda tare suke class d’insu d’aya, yin wannan tunanin yasa shi mik’ewa ya kai hannu kan c-table ya dau car key ya juya ya fice daga parlon, yana fita ya nufi Parking Space ya hau Mota ya fice direct gidansu Haulat ya nufa bayan ya parker a kopar gidan ya sauke glass ya kira wani yaro dake can gefe guda yace ya shiga yace Haulat tazo, bada jimawa ba sai gasu sun fito tare tay wanka tana sanye da hijab kalan kayan jikinta, da mamaki kan fuskarta take bin Motar da kallo dama tun a ciki tayi mamakin jin wai mai Mota yana kiranta kamar yadda yaron yace da ya shiga, zagayawa tay bangaren da driver mota d’in yake har saida gabanta ya fad’i ganin Haisam, d’an Murmushin yak’e tay mashi ta gaidashi ya amsa kafin yace “Zaraah fa?” wurga ido ta fara tana motsa baki a dabarbarce tace “bata koma gida bane?” maimakon ya bata amsa sai ce mata yay “kun dawo tare ne?” hannu ta d’aga tana d’an juya shi tace “a’a bamu dawo tare ba”
“Then where is she?” ya kafeta da kaifafan idanunsa duk tay kalar rashin gaskiya ta rasa yadda zatai mashi bayani can tace “da..dama zamu shiga Practical ne to sai nace ta taso mu tafi lab d’in sai tace man bata lafiya in je kawae,t..to lokacin da aka gama aka tashi da na koma class d’in sai ban ganta ba nayi tunanin taje wani wuri ne sai na d’an jirata amman shiru bata dawo ba sai na d’an dudduba sauran classes d’in amman bata nan sai nai tunanin ko ta taho gidane” still yay yana sauraranta har ta gama sannan yace “amman d’azun na ganki da bag d’inta right?” damm k’irjinta ya buga da karfi tace “e…eh ai dana koma ne naga jakar shine na d’aukko dama yanzu nike niyyar zuwa gidan in ga ko tana nan” sigh yay ya maida idonshi gaban Motar kaman mai nazarin wani abu can ya juya yace shikenan zata iya tafiya ta amsa da to ta juya da sauri ta shige gida shi kuma yay reverse ya fita daga lungun,tana shiga zaure ta tsaya ta dafe kirjinta cike da fargaba,abunda yasa bata fad’a mashi gaskiya ba tasan zai iya tambayarta miyasa Fatun tak’i biyota kuma zai iya ganin tayi rashin hankali na baro ta da tayi duk da ita tasan wacece Fatuu in ta kafe kan abu to fa sai tayi sai wani ikon Allah ne zaisa ta fasa don ma yanzu ta d’an yi sanyi saboda halin da take ciki, lokacin da ta lek’o wajen bata ga Motar tashi ba alamar ya tafi, tunani ta shiga yi na Fatun bata dawo bane har yanzu yasa yazo nemanta, can dae ta juya ta koma cikin gida, yana fita lungun ya mik’i hanyar da zata fitar dashi daga Unguwar yana hawa titi kai tsaye Makarantar tasu ya nufa, yana shiga main gate d’in ya nufi Senior Section a bakin gate ya tsaya yay horn mai gadi ya lek’o yana yin arba da Motar ya koma da sauri ya bud’e mashi gate d’in ya kutsa ciki a can gefe ya parker Motar mai maigadin ya nufo shi yana washe baki don ya sanshi sosae sakamakon yawan Alkhairin da yake masu, bud’e Motar yay ya fito bayan sun gaisa cikin cool voice d’inshi yace “Don Allah ko akwae sauran Students a ciki?” d’an jimm maigadin yayi kafin yace “gaskiya bana tunanin da sauran dalibai don gaba d’aya aka tashe su saboda yau juma’a har da yan aji shidda yau basu tsaya lessin d’in da ake masu ba, Allah yasa dae lafiya” yay Maganar idonshi akan Haisam d’in,
“Akwae Sister na da nike kawo wa so bata koma gida ba har yanzu” da sauri maigadi ya ruk’e ha6a alamar Al’ajabi yace “Hajiya dae da kake kawowa itace bata koma gida ba?” kai kawae ya d’aga mashi maigadin yace “to kuma ba’a aiketa wani wuri ba ko tace zata biya wani wuri?” jin tambayar tashi yasa haisam d’in yi mashi bayanin da Haulat tay mashi, da sauri yace “to ina ganin mu duba ajin nasu ko tana can, ai ajin kimiyya take ko?” nan ma kai Haisam ya d’aga mashi alamar eh maigadin ya wuce gaba Haisam yabi bayanshi suka nufi Science classes d’in ya tambayi haisam ajin su Fatun ya nuna mashi, koda ya shiga wayam ya tadda ajin ba kowa sai tarkacen takardu da ledojin da aka yayyadda, juyowa yay ya kalli Haisam dake tsaye gaban class d’in yace “Wllh Yalla6ai kaga dae ba kowa a cikin ajin” shiru haisam yay yama rasa tunanin da zai yi, maigadin yace bari ya duba sauran ajujuwan kai kawae ya d’aga mashi, gaba d’aya saida maigadin ya zagaye classes d’in dake wurin amman ba Fatuu ba alamarta ya dawo wurin Haisam d’in yace mashi wllh baiga kowa ba, suna cikin hakan saiga Discipline Master na section d’in ya shigo zai nufi Admin Block yana ganinsu ya nufesu yana tambayar maigadin lafiya kuwa ya mik’a ma Haisam hannu suka gaisa maigadin yay mashi bayanin da Haisam d’in yayi mashi, shima da mamaki yace “to ina taje haka, yakamata ace by now tana gida ba Sp Fateema Muhammad Ardo bace?” cikin cool voice d’inshi yace mashi ita,
“Malam nace ko a duba clilic (clinic) ko tana can tunda ance bata lafiya” maigadi ya fad’a yana kallon discipline d’in yace mashi “ai Baba bana tunanin tana can gaskiya don ko d’azun nabi ta wurin a rufe yake bamma tunanin an bud’e clinic d’in yau” gaba d’aya sukai shiru kowa da abunda yake tunani a ranshi Haisam dai yay shiru, can discipline ya kalleshi yace “Yalla6ai abunda nike tunanin za’ai shine a d’an tattambaya inda ake tunanin zata iya zuwa ko cikin unguwa haka don zai iya yuwuwa tabi wata ne tunda bata lafiya ni kaina kwanakin nan na fahimci ba daidai take ba mun kwana biyu ma bamu yi aiki tare da ita ba saidae mataimakiyarta tunda duk munsan tana da lalurar jinnu” jinjina mashi kai Haisam yay yaci gaba da cewa “nima yanzu zan fita cikin staff quarters in dan bibbincika muga, bari in baka lambar wayata in Allah yasa ka koma ka taras ta koma sai ka sanar dani nima nan in mun ganta sai a kira a sanar da kai in Allah ya yarda ma za’a ganta don ban tunanin tayi nisa” gaba d’aya suka amsa da Allah yasa Haisam yace mashi wayan na Mota ya bashi tashi sai ya saka mashi lamba d’in nashi yay mashi flashing, bayan ya saka mashi sukae sallama ya wuce suma suka dawo bakin gate saida yay ma maigadin Alheri yana ta mashi godiya da Addu’oi da fatan Allah yasa a ga Fatuu ya bud’e mashi kopar Motar ya shiga bayan ya juya ya fice daga cikin Makarantar Baba maigadin nata d’aga mashi hannu………
Jama’a ina Fatuu tayi????🤔🥹
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.