Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar ita kuma ta bishi da kallo kawai cikin alamun tsananin damuwa da tashin hankali kamar yadda sarki shardas ya bukata haka al amarin ya kasance, wato daga wannan rana suka ci gaba da renon juna biyun nata tare, ya zamana cewa fiye da rabin rana sarki shardas na bata lokacinsa tare da shadila, yana bata kulawa ko yaya yaga wani abu na damunta take zai tura a kirawo likitoci su dubata sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba kwana a tashi sai cikin shadila ya tsufa ya zamana cewa bata iya yin komai da kanta sai dai ayi mata.
.
A ranar da cikin ya cika wata tara da kwana tara ne nakuda ta zo mata, tana fara nakudar sai kawai akaga yanayi ya sauya ba tare da wanzuwar hadari ba ko tasowar iska sai akaji an fara tsawa da walkiya; al amarin da ya razana jama’a kenan aka kama guje guje.
.
A wannan lokaci da rana ne tsaka ana ta gabatar da hidimomin yau da kullum, nan fa kasuwa ta watse jama’a suka rinka rugawa izuwa cikin gidajensu suna
rufe kofa wasu kuma suka ruga izuwa fada domin a sanar da sarki abindake faruwa don ana zaton ko allolin da ake bautawa ne a kasar suka yi fishi zasu
hallakar da mutanen kasar.
.
Koda jama a suka iso fada sai suka iske boka marwas a tsaye a tsakiyar fadar shi kadai fuskarsa a murtuke yana muzurai koda ganin haka sai jama a suka zube kasa a gabansa aka yi tsit kamar mutuwa ta gifta, wani tsoho mai shekaru da yawa ya dago kai ya dubi boka marwas yace ya kai dirkar birnin Romaniya wannan kuma wace irin masiface tazo mana?
.
Ta yaya tsawa mai ban tsoro gami da walkiya suke faruwa a sararin samaniya alhalin babu ko alamar hadari?
.
Koda jin wannan tambaya sai boka barwas ya bushe
da dariya. Al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan boka barwas ya turbune fsuka yace matar sarkice zata haihu yu zata haifi wani yaro dan baiwa wanda sunansa zai shahara a ko ina cikin wannan duniya daga yau za a sami yalwar arziki a wannan birni namu mai albarka za a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali irin wanda ba a taba samu ba har izuwa ranar da wannan yaro zaiyi wata tafiya manufa ya fita daga cikin wannan gari namu.
.
Koda jin wannan batu sai mutane suka rasa abinda zasuyi tsakanin murna da bakinciki domin ta leko ne ta koma, babban abinda ya dugunzuma hankalin mutane a cikin bayanin boka barwas sunji cewar da zarar wannan yaro da za a haifa ya bar birnin duk farin ciki zai yaye don haka sai wasu suka fara tunanin to ai gwara rashin aihuwar yaron da dai a shiga farinciki da farko a karshe kuma a shiga tasku.
.
Nan fa mutane suka kama kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa. Ana cikin wannan haline aka yi wata irin tsawa mafi karfin gaske wacce ta firgita komai da kowa har gidajen birnin gaba daya saida yayi rawa, kasa tayi girgiza bishiyoyi suka kama cin wuta dabbobi suka kama guje guje suna shigewa maboya, mutane kuwa suka rude suka dimauce kamar zasu haukace, A dai dai wannan lokaci ne kukan jaririn Shadila ya cika birnin gaba daya har da amsa kuwwa izuwa cikin dazuzzuka.
.
Faruwar hakan keda wuya sai aka kece da ruwan sama kamar da bakin kwarya wata irin iska mai dadin sanyi ta rinka kadawa kamar ana cikin tsakiyar
damina alhalin ana ranine kuma a lokacin zafi ya addabi mutane faruwar wannan sabon yanayi keda wuya sai murna ta kama kowa gami da mamaki nan fa jama a suka ci gaba da cincirindo a kofar gidan sarautar birnin kowa burinsa shine yayi arba da wannan sabon jariri da aka haifa ko ya sami tabarrakinsa domin tuni kowa ya gama yarda cewa wannan jariri dan baiwa ne tunda gashi ni’ima ta sauka a birnin a irin lokacin da ba ataba samunta ba
shi dai wannan ruwan sama da ya sauka ba ruwa bane daga Allah, ruwane daga shaidanu domin kawai su juyar da hankalin mutanen dake wannan nahiya su dada dulmiyar dasu a cikin hanyar bata mabaiyaniya tunda sunyi imani da shaidanun a matsayin ababan bautarsu, bayan kofar fada ta cika makin da mutane.ana ta turereniya, gashi ruwan sama na dukan mutane sanyin iskar dake kadawa har ya fara addabar jama’a amma saboda naci sunki su tarwatse sai tsulum akaga sarki shardas ya fito daga cikin gidan.sarautar dauke da jaririn da shadila akan tafin hannayensa, jaririn tsirara yake ko al aurarsa ba arufe ba, ga sabon yankan cibi a jikinsa ruwan saman nata dukan jaririn amma ko a jikinsa sai dariya yake kyakyatawa yana ta wutsil wuts irin ta jarirai masu koshin lafiya.
.
Koda sarki shardas ya iso gaban dandazon jama’a sai ya daga jaririn sama yayi kuwwar murna take jama a suka amsa masa kuwar muryoyinsu suka cika birnin gaba daya sai da aka yi haka har sau uku
sannan sarki shardas ya mikawa boka barwas jaririn ya karba, ya fuskanci jama a yace yaku jama ar wannan birni na Romaniya kuyi sani cewa yau allolinmu sun dubi kukana sun bani da alhalin na shafe shekara da shekaru ina neman haihuwar ban samu ba ina mai tabbatar muku da cewar wannan da dana samu rahama nega kasarmu gaba daya don
haka ina son kowa ya kaunaceshi kamar yadda zai kaunaci dan cikinsa,Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai jama’a suka amsa masa da cewar sunyi Alkawari zasu so wannan da tamkar dan cikinsu.
.
Cikin matukar murna sarki shardas ya juya ya dubi boka barwas ya mika masa hannu domin ya karbi jaririn kawai sai yaga fuskar boka barwas a murtuke babu annuri nan dai ya karbi jaririn ya sallami jama’a kowa ya watse aka tafi ana ta murna ana ta kade kade da bushe bushe bayan jama a sun watse sai sarki shardas da boka barwas suka juya suka nufi cikin gidan sarautar suna masu jera kafada tsawon dan lokaci suna tafiya dayansu baice uffan ba sai sarki shardas ya dubi boka barwas yace yakai abin dogaro na yakai shamakin dake tsakanina da allolinmu ina son ka gaya mini dukkan dalilin da yasa ka murtuke fuskarka a lokacin da na umarci jama a dasu so wannan jariri na shadila.
.
Koda jin haka sai boka barwas yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki shardas cikin alamun takaici da damuwa yace ya shugabana ai wannan abu da kayi shine babban kuskurenka na farko a kan wannan yaro da aka haifa, shin ka manta ne cewa a duniya kaf baka da wani makiyi wanda yafi wannan yaro?
Shin ka manta ne cewa a halin yanzu yana matayin danka ne na cikinka, tabbas yadda suke son ka kuma zasu so ya gaji karagarka anan gaba, a lokacin
da ni dakai zamu yi shiri mu tafi neman hular lamsara shine zai hau karagarka ta mulki kuma idan muka je muka samo hular lamsara muka dawo saukeshi daga kan karagarka ba abu bane mai sauki duk da cewar zamu iya hallakashi farat daya a wannan lokaci saboda zamu fuskanci fishin jama a domin a sannan suna kaunarsa fiye da kai kuma suna matukar jin dadin mulkinsa, dolene sai daimu hallakashi a sirrance ta yadda babu wanda zai gane cewar dasa hannunmu, ni abinda nake so dakai kawai shine duk yadda za ayi kada ka kuskura wannan yaro ya san cewa ba kai bane uban sa ba har izuwa tsawon shekaru bakwai da zaka rabu dashi akwai ragowar kurakurai guda biyu wadanda bana son kayi kuskuren aikatasu, a nan gaba domin idan ka aikatasu tofa koda ka mallaki hular lamsara saimun sha bakar wahala kafin mu sami nasarar hallaka wannan yaro kuskuren kuwa shine kada ka kuskura ka bari son wannan yaro ya shiga ranka domin hakan zata iya faruwa don yaron zai taso da tsananin farin jini da shiga rai.
.
Akwai wani magani da zan baka ka rinka sha bayan kowane kwana talatin, indai kana shan wannan akan lokaci babu yadda za ayi son wannan yaro ya shiga ranka shi kuwa kuskuren da zaka yi na uku ba yanzu
zan sanar dakai ba sai idan lokacin da ya dace ka sani yayi.
.
Koda jin wannan batu sai jikin sarki shardas yayi sanyi yana mamaki da tunani har suka kule a cikin gidan sarautar bai kara cewa uffan ba.
.
Da ranar suna ta zagayo sai aka yi gagarumin taro aka gaiyaci sarakaim attajirai, bokaye, jarumai da sauran manyan mutane na nahiyar gaba daya boka barwas ne ya radawa jaririn suna Yarima HULKAS, nan fa aka shiga shagalin suna sai da aka kwana ashirin da daya kullum ana gabatar da walima a gidan sarki abinci da abinsha kuwa saida akayi ta almubazzaranci tamkar a bola ake tsunto su hatta talakawan gari ma sai da suka rinka shirya walima tsawon wadannan kwanaki sarki shardas a cikin tsananin farin ciki yake kai kace yarima Hulkas dansa ne na cikinsa wato jininsa ne hm daga wannan rana wani abin mamaki ya fara wanzuwa a cikin birnin romani ya zamana cewa fatake suna ta tururuwa a cikin birnin suna tahowa daga manyan kasashe na duniya suna kafa tushen kasuwancinsu a birnin.
.
Nan fa kasuwanci ya sami gagarumar bukasar da bai taba yi ba a nahiyar gaba daya nan da nan talauci da fatara suka yaye, arziki ya yawaita a hannun talakawa, kayayyaki iri iri akayi ta shigowa da su birnin da hajoji kala kala, kai irin kasuwancin da baya juyuwa ma a nahiyar fiye da shekaru daruruwa da suka wuce sai da akazo dashi ana yinsu tamkar dama can an saba dasu.
.
Al amarin shadila kuwa itama ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa ta farinciki tamkar bata taba tsintar
kanta a cikin wata damuwa a baya amma da zarar ta tuno da mahaifin hulkas na gaskiya wato Hailur saita kefe kanta a cikin daki tay ta kukanta ta more bata yarda sarki yasan halin da take ciki duk da cewar sarki shardas ya fara shan wannan magani wanda boka barwas ya bashi don kada soyayyar Hulkas ta shiga ransa saida yaji yana kaunar Hulkas din tamkar Dansane bana wani ba a ranar da ya sha maganin ne kadai yake jin ya tsaneshi domin a ranar ne yake tunawa da cewa nan gaba fa wannan yaro ne zai kasheshi muddin bai rigashi mallakar Hular Lamsara ba a wannan rana daga safiya zuwa dare sarki shardas baya kusantar shadila don kada ma yayi arba da Jarumi Hulkas hmm Domin zai iya hallakashi nan take saboda zuciyarsa tana tafarfasa ne kamar zata kone bisa jin tsananin kiyayyar hulkas a cikin zuciyarsa kuma jikinsa na tsuma da kyarma yana jin kamar idan bai kashe jariri Hulkas ba shi zai mutu ne a ranar.
.
A kwana a tashi sarki Shardas yana kiyayewa gami da jure duk irin abinda zuciyarsa ke raya masa akan wannan yaro Hulkas har dai aka sami tsawon shekara Uku. A sannan ne ya tsinci kansa a cikin tsananin so da kaunar yarima Hulkas harma yana ji kamar ba zai iya yin rayuwa ba idan babu shi wani iko na Allah Kuma sai shima yaro Hulkas ya shaku da sarki Shardas ya zamana cewa yama shaku dashi fiye da yadda ya shaku da uwarsa Shadila har takai cewa ko abinci baya yarda yaci sai tare da sarki shardas in ba haka ba kuwa sai dai ya kwana da yunwa shima sarki shardas din baya iya cin abincin shi kadai idan ba tare da hulkas ba kai hatta telan da yake yiwa sarki shardas dinki iri daya dana Hulkas yake dinka musu kullum sai dai kaga sunyi anko sunzo fada tare sun zauna akan karagar mulki duk da rana babu abinda yake rabasu kullum ..
.
Sai bayan hulkas yayi barci akan kirjin sarki shardas sannan shadila ke daukeshi tayi masa shimfida a kusa da gadon sarki domin ko cikin dare idan ya farka baiga Sarki ba sai dai ya fashe da kuka kuma babu mai iya rarrashinsa yayi shiru face sarki din ita kanta shadila lokacin da taga shakuwar sarki da yarima hulkas ta wuce saninta ta wuce duk tunanin mai tunani sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji zuciyarta ta fara yi mata gargadi kada ta kuskura ta sanar da yarima hulkas asalin abin dake tsakaninsu a nan gaba idan hulkas ya girma
.
A duk sa adda ta tuno da alkawarin da ta dauka na rufe wannan sirri dakuma gargadin da sarki shardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrin sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki……..
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part B.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Idan ta tuna gargadin da sarki Hsardas yayi mata da matakin da yace zai dauka idan ta tona sirrinsa sai hankalinta ya dugunzuma tayi ta kukan bakin ciki haka dai aka ci gaba da wannan rayuwa har yarima hulkas ya cika shekara shida ya zamana cewa gaba daya mutanen kasar Romaniya suna matukar kaunarsa kai ba ma yan kasar ba hatta baki sonsa suke saboda kyawunsa da farin jininsa da kuma kyawawan halayansa da irin hankalin da Allah ya bashi tamkar bai kasance yaro karami ba sannan ga shi Allah ya bashi jin kai da tausayin talakawa sabanin sarki shardas wanda ya kasance Kasurgumin Azzalumin bawa.
.
Gaba daya zaluncin da sarki shardas ke yiwa talakawa sai da yarima hulkas ya hanashi kamar matsa musu wajan karbar haraji mai yawa kai sumame na mamayar bazato a kamo bayi a kwashe dukiyar talakawa sai dai takai cewa duk inda yarima Hulkas ya gifta a cikin nahiyar kasar sai dai kaga jama a suna yi masa kirari da sarkin Gobe Yadda ake yi masa ladabi, biyayya, da girmamawa kuwa ko sarki shardas ba a yi masa haka duk da cewa kuwa ana tsananin tsoronsa hatta a cikin gidan sarautar kwau Bayi, barori, kuyangi da dakari ma suna bin umarnin yarima hulkas tamkar sarki shardas ne yake basu umarnin, kai sai da takai cewa yarima hulkas yana zartar da abubuwa da yawa ba tare da yayi shawara da sarki ba ko da kuwa shi sarki shardas baya son wannan abu ba zaice uffan ba bare ya hanashi.
.
Ashe duk wannan abu dake faruwa tsakanin sarki shardas da yarima hulkas boka barwas na lura da shi amma sai yayi shiru baice kala ba wata rana da yammaci sarki shardas na tsaye a can saman ginin wata baranda yake cikin harabar gidan sarautar sai ya hango yarima hulkas tare da mahaifiyarsa shadila sun fito rangadi suna kewaye a cikin gidan sarautar sunta rabawa bay dakaru barori da kuyangi kyaututtukanna suturori kala kala. koda ganin wannan al amari sai ran sarki ya baci zuciyarsa tayi bakikirin ya tuna cewa tunda fa aka haifi wannan yaro hulkas rayuwar kasar gaba daya ta sauya duk wani iko nasa kwarjininsa da tsarin mulkinsa ya dakushe ya zama kamar mutum mutumi sai abinda hulkas ya zartar a fada shi ake bi su kansu fadawan sarki shardas basa karbar umarnin sa sai abinda yarima Hulkas ya zartar domin a gaba daya sarakai, attajirai da talakawa sun dauki hulkas fiye da kima wasu ma gani sukeyi kamar ya cancanci a bauta masa kamar yadda ake bautawa sauran alloli na kasar saboda ganin irin abubuwan al ajabin da suka faru daga sa adda aka haifeshi kawo iyanzu duk da cewar yarima hulkas ya sami wannan dama da daukaka bai dauki wani girman kai ba ya dorawa kansa kuma hakan ba ta sa ya raina mahaifinsa ba sarki shardas face ma tsananin sonsa da yake karuwa a cikin ransa, duk abubuwan da yarima hulkas yayi a fada ko yasa aka zartar a kasar sai yaje ya sanar da sarki a yayin da suka kebe kuma ya tambayeshi idan akwai gyara a cikin abubuwan da ya aikata domin yaje ya gyara ko sau daya sarki shardas bai taba nuna cewar akwai abinda hulkas yayi ba dai dai ba bare ma ya nuna masa fishinsa a zahiri ko a badini, haka kuma duk abubuwan da yarima hulkas keyi basu sa shakuwarsa da sarki ta sami rauni ba face ma karuwa da takeyi a kullum su kansu fadawan sarki shardas da duk masu fada aji a kasar suna matukar mamakin yadda wannan al amari ya kasance domin ko a mafarki babu wanda ya taba zaton cewa akwai wani mahaluki wanda zai zo ya iya sauya halayan sarki shardas haka sarki shardas na tsaye a can saman barandar gidan sarautar yana hango yarima hulkas da mahaifiyarsa
shadila suna ta raba kyautar suturori ga hadiman gidan sarautar sai tsulum yaga boka barwas ya baiyana a gabansa take boka barwas ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya juyo ya leka kasan barandar ya dubi yarima hulkas da mahaifiyarsa, barwas ya dago kai ya dubi sarki shardas yana mai ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ya shugabana hakika in ba don ina kusa da kai da tuni ka tafka babban kuskuren da zamu hallaka gaba daya duk da cewa kana shan wannan magani dana baka a karshen kowane wata, kaunar wannan yaro a cikin ranka ta gama yin katutu idan baka yi da gaske ba makiyinka zai samu nasara a kanka.
.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki shardas suka zazzaro zuciyarsa ta kufulo har fuskarsa ta kama yatsine saboda fishi ya dubi boka barwas yace yakai dirkar birnin romaniya kayi sani cewa har gobe ban manta da asalin yarima hulkas ba na sani cewa bani da wani makiyi a doron kasa wanda ya fishi don haka duk wannan soyayya da nake yi masa ta banza ce tunda lokaci kawai nake jira wanda zamu tafi neman hular lamsara da ita ne kadai zan sami nasarar hallaka wannan yaro kamar yadda ka fada lokacin da sarki shardas yazo nan a zancensa sai boka barwas ya tuntsire da dariyar farinciki sautin dariyar tasa ne ya janyo hankalin yarima Hulkas da shadila suka Hangosu, cikin tsananin farin ciki yarima hulkas ya baro shadila a inda take tsaye ya ruga da gudu izuwa kan matattakalar bene da zata kai shi inda su sarki shardas suke.
.
Koda sarki shardas ya hango yarima ya taho gareshi sai shima ya tareshi suka rungume juna hulkas na hada idanu da boka barwas sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi wani irin tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa dama duk sa adda yarima yayi arba da boka barwas sai yaji haka Hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas yace yakai abbana kayi sani cewa yanzu nake shirin na tafi zuwa turakarka bayan mun gama raba kyaututtuka ga hadiman gidan nan na nemi wata alfarma guda daya a wajanka.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi murmushi yace haba ya kai dana shin ka taba neman wata alfarma ne a wajena na hanaka? Ai duk abinda kaji zuciyarka tana da muradi kayi nayi maka izini muddin wannan abu ba zai zubar mana da kimarmu da mutuncinmu ba, yanzu sanar dani alfarmar da kake so nayi maka Hulkas yayi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kas cikin alamun kunya da damuwa kamar ba zai iya magana ba sannan yace yakai abbana ka sani cewa tun da aka haifeni a birnin nan ban taba zuwa ko da wani garin ba daga cikin sauran manyan biranen dake kasar tamu ba, labari ya zo mini cewar hakimin birnin Istanbul ya shirya gagarumar gasa ta jarumtaka kuma an gaiyato manyan jarumai daga bangarori da yawa na duniya lallai ina son na halacci wannan gasa domin a rayuwata babu abinda nake so sama da ganin mutum mai jarumtaka da iya yaki na dade
ina rokonka akan ka koya mini yaki a matsayina na jarumin da zai shahara a wannan nahiya tamu amma kaki kuma baka taba gaya mun dalili ba tunda baka son ka sanar dani dalilin nima bana bukatar na sani
ni dai yanzu ka amince mini nayi wannan tafiya zuwa birnin istanbul.
.
Koda yarima hulkas yzo nan a zancensa sai sarki shardas yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun don haka sai ya yunkura da nufin ya juya ya dubi boka barwas domin ya nemi shawararsa amma sai yarima hulkas ya kama hannayansa yace yakai abbana kayi sani cewa bai kamata a sami shamaki ba a tsakanin da da mahaifi muddin wannan da ya kasance jinin mahaifinsa, babu bukatar kayi shawara da wani akan alfarmar da zan nema a wajanka tunda dai nafi karfinta a wajanka.
.
Koda jin wannan batu sai jikin sarki ya yi sanyi kafin ya bude baki yace wani abu sai boka barwas ya tari numfashinsa ya dubi hulkas yace haba ya kai yarima ai bai kamata kace zaka fita daga cikin birnin nan ba kaje wani wuri ba tunda kasan cewa bincike ya nuna cewa duk ranar da kayi dogon zango kasar nan zata shiga cikin fari da annobar talauci, kafin boka barwas ya gama rufe bakinsa tuni shima hulkas ya tari numfashinsa yana mai cewa amma ai cewa kayi sai idan na fita daga cikin yankin kasar nan gaba daya sannan hakan zata faru ya kai barwas kayi sani cewa kana da iyaka a tsakanin da da mahaifi don haka bai kamata ka wuce gona da iri ba yarima hulkas yayi wannan furuci ne fuskarsa a murtuke yana mai hararar boka barwas amma da ya dubi sarki shardas sai fuskarsa ta juye zuwa annuri.
.
Kawai sai sarki shardas ya maida masa da martanin murmushin yace jeka abinka yakai dana lallai nayi maka izinin ka tafi zuwa birnin istanbul domin idanunka su more da kallon abinda zuciyarka ke so koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima hulkas ya rungume sarki shardas yana mai yi masa godiya nan take yarima hulkas ya janye jikinsa daga cikin na sarki shardas ya koma wajen mahaifiyarsa
shadila yana riskarta ya rungumeta yana mai yi mata bushatar cewar sarki ya amince masa yayi wannan tafia nan take itama shadila ta cika da farin ciki amma koda ta dago kai tayi arba da fuskokin sarki dana boka barwas tagansu a murtuke babu annuri sai hankalinta ya tashi nan da nan cikin sauri ta kama hannun yarima hulkas taja shi suka juya da baya suka koma cikin gidan sarautar cikin alamun tsananin fishi boka barwas ya dubi sarki shardas yace wannan shine kuskure na uku wanda na gaya maka cewar kada ka aikatashi amma gashi idanunka sun rufe saboda soyayyarsa ka aikatashi ko dajin wannan batu sai sarki shardas ya juyo da sauri ya fuskanci boka barwas cikin tashin hankali yace ban gane abinda kake nufi ba yanzu saboda kawai na bar yarima hulkas yaje yayi kallon gasar jarumtaka a birnin istanbul shine na aikata babban kuskure?
.
Barwas yace kwarai kuwa rashin aiki da shawarata yasa ka aikata babban kuskure na uku wanda nake ta kokarin hanaka ai tunda dai ka fahimci cewar ban son ka bar yaron nan yayi wannan tafiya bai kamata ka barshi yayi ba bincike ya nuna mini cewar yarima hulkas zai sami wata babbar dama ta yakarmu a cikin wannan tafiya da zaiyi amma kuma a dalilin tafiyar ne shima zai sadu da abinda zai zamo sanadin ajalinsa anan gaba.
.
Lokacin da sarki shardas yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yaji kamar ya kirawo yarima hulkas yace dashi ya janye izinin da ya bashi nayi wannan tafiya amma kuma sai yaji ba zai iya ba.
.
Kafin ya budi baki yace wani abu sai kawai yaga boka barwas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin alamun tsananin damuwa sarki shardas ya juya ya sauka daga kan matattakalar barandar ya nufi cikin gidan sarautar zuciyarsa cike da sake sake da tunani abinda ya fara fado masa a rai shine wai shin yaya akayi nema har ya bari son yarima ya shiga zuciyarsa alhalin ya san cewa ba jininsa bane asalima ba shi da wani makiyi wanda ya fishi a doron kasa tunda komai dare dadewa sai ya nemi daukar fansar ran mahaifinsa hailur a kansa wata zuciyar kuma sai tace dashi hakika babu abinda yafi soyayya hadari a wannan duniya domin inda tun farko bai kamu da son shadila ba da tun sa adda ya kashe mijinta itama zai kasheta dashi kenan ya huta da fargabar komai don da yanzun bata haife masa alakakai ba kuma kadangaren bakin tulu wato yarima Hulkas maimakon sarki shardas ya wuce zuwa turakarsa sai ya wuce zuwa turakar shadila kai tsaye duk inda ya ratsa sai dai kaga hadimai suna zubewa kasa suna kwasar gaisuwa da isarsa dakin sai ya iske shadila tare da hulkas a zaune cikin nishadi da farin ciki suna cin tuffa a karon farko sai hulkas yaga babu cikakken annuri a fuskar sarki shardas kafin hulkas yace wani abu sai shardas ya dubeshi yace yakai dana ina son ka bamu dan lokaci zan tattauna da mahaifiyarka.
.
Koda jin haka sai hulkas ya mike tsaye yana mai yin
murmushi ya nufi kofar fita daga cikin dakin yace babu matsala fitarsa keda wuya sai sarki ya tura kofar ya rufe ta sannan yazo daf da shadila ya zauna ya sumbaci wuyanta suka rungume juna suna soyayya daga can sai yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin nata ya hankadata ta fado kasa daga kan kujerar da take zaune ya cafi makoshinta ya shaketa.
.
Nan take idanunta suka zazzaro suka kada sukayi jawur ta fara kakarin mutuwa a sannan ne ya saketa ta zube kasa tana numfarfashi kamar ranta zai fita tana mai kurawa shardas idanu.
.
A fusace shardas ya dubeta yace wannan jan kunne ne nayimiki gami da tuni bisa alkawarin dake tsakaninmu akan wannan yaro zakuyi tafiya tare kedashi zuwa birnin istanbul domin halattar taron gasar jarumtaka na duniya da aka sabayi idan kikayi amfani da wannan dama kika gayawa danki sirrin dake tsakani na dashi a bakacin ranki ki sani cewa duk abinda zai faru tsakaninki dashi boka barwas zai gani a cikin madubin tsafinsa yanzu zan fita na barki kada ki kuskura ki bari danki ya gane cewar nayi miki wani abu yanzu.
.
Koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya fice daga cikin turakar yana fita sai shadila ta mike zumbur a lokacin da hawayen bakin ciki da takaici ya zumo mata kawai sai tayi sauri ta dauko wani farin kwalli ta sanya a cikin idanunta nan take idanun nata suka washe sukayi fari kal tamkar bata taba yin kuka ba tana ajiye kwallin saiga yarima ya shigo idanunsa sun ga sa adda ta ajiye kwallin don haka sai ya zargi
cewar akwai wani abu da ya faru tsakaninta da sarki
shardas domin baiga dalilin da zaisa tayi amfani da kwalli ba alhalin dama can ta gama yin kwalliya cikin alamun zargi hulkas ya dubi shadila yace yake ummina menene ya faru tsakaninki da abbana??
.
Shin ya gaya miki wata magana ne wacce ta sosa miki rai?
Koda jin wannan tambayoyi guda biyu sai shadila tayi murmushi tace babu wata magana wacce ta sosa mini zuciya farinciki ne kawai yasa kaga alamun sauyin yanayi akan fuskata domin ya shaida mini cewar zamuyi tafiya nida kai zuwa birnin istanbul koda jin haka sai murna ta kama yarima ya rungumeta yana mai cewa burina ya cika yake ummina lallai idanuna zasu ga abinda suka dade suna mafarkin gani.
.
A wannan rana gaba daya yarima hulkas bai sami damar hutawa ba ko tsayuwa a waje daya saboda murna sai kai kawo yake yana ta shirye shiryen tafiyar da zasuyi gobe.
.
Lokacin da dare yayi sai bacci ya kauracewa hulkas da yake akan gado daya suke kwance tare da sarki shardas sai yarima hulkas ya cika da matukar mamaki bisa ganin yadda shima sarki shardas din ya
kasa yin barci sai juye juye yake yi kawai akan gado
Yarima Hulkas ya dubi sarki cikin alamun mamaki yace yakai abbana wai shin.
.
Mene ne ya hanaka barci ne a yau?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi murmushi yace yakai dana kai yarone don haka baka son dacin rabuwa da masoyi ba tunda aka haifeka a cikin wannan gidan sarauta ban taba rabuwa dakai ba tsawon sa a daya jal kullum muna tare dare da rana hatta kwanciyar barci bata rabamu yau gashi an wayi gari zakayi tafiya zamuyi rabuwa ta a kalla tsawon sati biyu a cikin wace irin damuwa da kadaici kake tunanin zan kasance?
.
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai Jikin yarima Hulkas yayi sanyi nan take idanunsa suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa bai san sa adda ya rungume sarki ba yana mai cewa…….
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Ɗaya Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part C.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Lokacin da Hulkas yazo nan a zancensa sai shima sarki shardas jikinsa yayi sanyi ruwan hawaye ya subuto daga cikin idanunsa ya janye jikinsa daga jikin na hulkas suka fuskanci juna yana mai rike kafadunsa yace yakai dana kayi sani cewa ko kadan nima bana son abinda zai sosa maka zuciya kuma babu abin da nake so sama da ganin farin cikinka amma in ba don haka ba da tsawon sa a daya zan kasance a cikin zumudi da dokin dawowarku lafiya kaida mahaifiyarka domin kune ginshikin rayuwata, haka dai sarki shardas da yarima hulkas sukayi ta hira ta bankwana har asubahi ta riskesu basu sani ba a sannan ne hulkas ya fara gyangyadi kafin a jima barci ya daukeshi faruwar hakan keda wuya saiga shadila ta shigo sanye da rigar barci wacce ke baiyana kyakkyawar surar jikinta babban abinda ya daurewa sarki shardas kai shine bai taba ganin murmushin shadila ba a duk sa adda zata shigo turakarsa da daddare sai yau tun a farkon ranar da ya satota daga sansaninsu ya kawota wannan gidan sarauta saboda ya tabbatar da cewar ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta kai tsaye shadila ta fado kan sarki shardas ta fara jan hankalinsa domin ya kwadaitu da ita maimakon ya karbeta hannu biyu sai kawai taga ya bangajeta ta fadi can gefe daya akan gadon ya dubeta a fusace yace menene dalilin da yasa yau kika shigo cikin turakata kina mai murmushi alhalin baki taba yi mun murmushi ba a dukkan dararen da suka shude na barcinmu??
.
Koda jin wannan tambaya sai shadila ta bushe damahaukaciyar dariya kamar ba zata daina ba karfin dariyar nata baisa yarima hulkas ya faka daga barcin da yake yi ba mai nauyi saboda kasancewar barcin mai nauyi ne daga can sai shadila ta tsuke bakinta ta daina yin dariyar tana mai murtke fuska ta dubeshi tace yakai mijina na dole ka sani cewa ban taba jin kaunarka ba a cikin zuciyata dai dai da darajar kwayar zarra kaine ka rabani da farin cikina kuma kaine ka shayar dani gubar bakin cikin da har abada ba zan iya amayar da ita ba sai dai ajalina ya zame mini saukin ciwon data sa mini Abinda yasa kaga na shigo cikin turakarka ina murmushi a yau ba komai bane face farin ciki bisa sanin cewa gobe zan rabu da ganin wannan fuska taka kuma ba zan sake ganinta ba har sai bayan a kalla sati byu ka sani cewa duk sa adda na kalli fuskarka sai naji kamar bakin kumurci nake kallo haka kuma duk sa adda ka kwanta dani nakanji mugun bakin ciki tamkar na kashe kaina saboda ba masoyina hailu bane yake amfani da wannan kyakkyawan jiki nawa, yanzu na kawo maka kaina ne gareka domin ka more iya son ranka saboda kwanaki goma sha hudu masu zuwa a mafarki jikin nawa zai zama na masoyina wanda ka datse rayuwarsa ka mayar da dansa maraya koda shadila tazo nan a zancenta sai zuciyar sarki shardas ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma ya daga hannu da nufin shararawa shadila mari amma sai ya kasa saboda tsoron kada ya maretan hulkas ya farka daga barci ya gane abinda ya faru tsakaninsu koda shadila taga sarki shardas ya kasa marinta saita sake bushewa da dariya a karo na biyu ba tare da tace dashi uffan ba sai tasa hannayanta biyu ta dauki danta hulkas ta rungumeshi a kirjinta ta juya ta fice daga cikin turakar shi kuwa sarki shardas sai ya bita da kallo kawai cikin tsananin takaici da bakin ciki fuskarsa nayin gatsine yana jin kamar ya zare takobi yaje ya sareta gari na wayewa sosai sai sarki Shardas ya kirawo mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira sadauki marzanu ya dubeshi yace ina son ka zabo zakwakuran dakaru mutum dubu biyu daga cikin manyan dakarunmu kayi musu jagora a cikin rakiyar matata da dana yarima hulkas izuwa birnin ishtanbul kayi sani cewa zan baku guzuri ishashshe kuma zan baku kudade masu yawan gaske domin ku kawai da dukkan bukatunku amma ku sani cewa idan kuka dawo daga birnin istanbul naga kwarzane guda daya a jikin matata ko dana ko kuma kuka dawo mini dasu babu lafiya ko babu rai a bakacin rayukan iyalanku daku kanku.
.
Koda jin wannan batu sai sadauki marzanu yarisina yace an gama ya shugaban nan take marzanu ya juya da sauri ya nufi wani bangare daban na gidan sarautar domin ya hado kan dakarun daya dace suyi masa rakiya a cikin wannan gagarumar lafiyamai hadari kafin rana ta take tuni kowa ya gama kimtsawa daga cikin jama ar da zasu yi wannan tafiya shadila da yarima hulkas kuwa sai suka caba ado mai daukar hankali suka shiga cikin keken dokin sarauta, sadauki marzanu da sauran dakaru kuwa suka hau dawakai cikin gagarumar shigar yaki suka sa keken dokin a tsakiya sai kuma kuyangi guda uku kacal da aka tanada domin su yiwa shadila da hulkas hidima a cikin wannan tafiya.
.
Ba tare da bata lokaci ba wannan zuga ta kama hanyar fita daga cikin gidan sarautar, abinda ya daurewa yarima Hulkas kai shine rashin ganin sarki shardas a wannan safiya bare suyi sallama har ya budi baki zai tambayi shadila dalilin da yasa sarki baizo sunyi bankwana ba sai.
.
Kawai ya hango sarki shardas a can saman bene yana dago masa hannu kuma idanunsa sun ciko da kwalla nan take zuciyar yarima hulkas ta karaya shima ya ji hawaye ya zubo masa take yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya kawai sai hulkas ya daka tsalle ya duro kasa daga kan keken dokin ya ruga da baya izuwa inda sarki yake can saman bene, babu shiri mai jan keken dokin yaja linzami ya tsaidashi itama shadila sai ta duro daga cikin keken dokin a dimauce don a zatonta wani mugun abune ya faru amma sai taga ashe yarima ne ya ruga izuwa inda sarki yake.
.
Lokacin da sarki shardas yaga yarima hulkas ya rugo izuwa gareshi sai shima ya gangaro da gudu daga saman benen da yake tsaye ya tari yarima a tsakiyar filin gidan sarautar suka rungume juna kuma suka kama kuka a lokaci guda saboda bakin cikin rabuwa yarima hulkas ya dada kankame sarki, yace yakai abbana mene ne dalilin da yasa kaki zuwa muyi bankwana tun dazu alhalin kasan cewa ina ciikin kewarka da tunanin rashinka a kusa dani.
.
Sa’adda sarki shardas yaji wannan batu sai ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye sarki shardas ya numfasa yace yakai dana kayi sani cewa ni jarumi ne kuma gwarzon mayaki wanda bai taba zubar da hawaye ba komai wuya da azaba kuma komai farin ciki da bakin ciki tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana amma yau gashi kai ka sani na zubar da hawaye ina mai tabbatar maka da cewa in banda mahaifiyarka babu wani mutum wanda na taba jin ina sonsa dari bisa dari a cikin zuciyata sai kai kuma a halin yanzu soyayyata a gareka ta linka dari bisa dari fiye da komai kuma kai kadai ne mutumin da nake jin cewar ba zan iya cutar da shi ba bisa duk irin laifin da zakayi mini koda kuwa bakin cikin abin dakayi min zai zamo sanadin ajalina.
.
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya sake rungume sarki ya fashe da matsanancin kuka yace yakai abbana tabbas nasan kana kaunata fiye da kima amma ni ina jin kusancinka a raina fiye da kusancin jini da hanta inaji a raina cewar idan babu kai a wannan duniyar ba zan rayu ba kuma ina jin cewar rashinka a kusa dani dai dai yake da jefani cikin kurkukun da babu ci ba sha kuma babu hasken da mutum zai iya ganin ko da tafin hannunsa face matsanancin duhun daba zai misaltu ba koda jin haka sai sarki shardas ya janye jikinsa daga cikin na yarima hulkas kansa na sunkuye yana zubar da hawaye kawai sai ya daga hannu ya yiwa sarkin yaki marzanu inkiya nan take marzanu ya rugo ya dauke yarima hulkas ya ruga da shi izuwa bakin keken dokin ya sashi a ciki itama shadila sai ta koma cikin keken dokin ta zauna nan take aka sakarwa dawakan linzami keken dokin yayi gaba su sadauki marzanu sukabi keken dokin a baya suna maiyi masa kawanya gaba daya gefe da gefe don tabbatar da tsaro.
.
Nan dai sarki shardas ya bisu da kallo har sai da suka kule ya daina ganinsu sannan ya juya ya koma cikin gidan sarautar cikin tsananin bakin cikin rabuwa da yarima hulkasa bai ankara ba saiji yayi hawaye ya kara zubo masa a wannan lokaci kuma inda yake wucewa akwai dakaru a tsaitsaye kuma ga bayi barori da kuyangi suna ta kai kawo da hidimomi
duk wanda yaga hawaye a idanun sarki sai kaga ya firgice domin kowa ya san cewa a tarihin rayuwar sarki shardas babu wanda ya taba ganin hawayansa sai yau da yake an san irin shakuwar dake tsakanin sarki shardas da dan sa yarima hulkas kuma an san cewa yau sun rabu sai kowa ya gane dalilin zubar da hawayan nasa.
.
Abin da mutane basu sani ba shine wannan hawaye bana soyayyar hulkas bane ba kadai har da takaicin tunanin ainihin alakarsa da hulkas gami da sanin cewa hulkas ba jininsa bane da kuma bakin cikin rashin samun soyayyar shadila a gareshi ta gaskiya kai tsaye su sadauki marzanu suka durfafi cikin daji suka sukayi ta tafiya babu sassauci babu tsoro ko shakkar wani abu saboda sun yarda da kansu.
.
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole a ce da mijin iya baba hakika komai yawan yan fashi da shirinsu idan suka hango wannan runduna ta su sadauki marzanu saikaga sun fasa taresu sun bace daga kan hanyarsu, ba komai bane ya haddasa hakan ba face kwarjininsu kuma ido ba mudu bane ammma yasan kima ma ana kai da ganin dakarun marzanu kasan sun cika zaratan jarumai masu tarwatsa maza domin dukkansu sun kasance manya manya masu kirar mutanen farko, gashi jikinsu a murde yake kuma sun tara kwanji da jijiyoyi kai kace da dutse aka yi gabobin jikin nasu irin shigar yakin da sukayi kuwa mai ban tsoro ce domin kowannansu yana daukeda miyagun makami yaki irin wanda idanu basu saba gani ba kai ba wai yan fashi ba hatta mugayan dabbobin daji da bakaken aljanu wadanda suka kasance azzalumai suna ganin wannan runduna sai kaga sun bace daga wajan saboda boka barwas ya shirya wadannan dakaru tuntuni da karfin sihirin tsafi mai tunkararsu sai cikakken shiryayye abin kwatance a duniya.
.
Kwana uku kacal wadannan dakaru suka shafe suna
tafiya suka iso birnin askandariya suna shigowa suka iske birnin a cike makil da jama a duk inda mutum ya duba babu abinda zai gani face kawunan jama a fiye da rabin jama ar da suke gani baki ne wadanda sukazo halattar gasar jarumtaka mafi akasarin bakin kuwa sarakai ne da attajirai da yayansu da kuma fatake da shahararrun bokaye tabbas gaba da gabanta aljani ya taka wuta lokacin da keken dokin gimbiya shadila ya kunna kai cikin birnin sadauki marzanu da dakarunsa na biye dashi sai gaba dayan jama ar dake wajan suka dare suka basu hanya kuma kowa ya zuba ido ana kallonsu aka zama kauyawa ba komaine ya haddasa hakan ba face ganin irin dukiyar da aka kashe wajan kera keken dokin da gimbia shadila ke ciki da kuma kayan yakin da dakarunta ke sanye da su domin an sanya jarin wani sarkin ne gaba daya nan fa sarakuna masu ji da kansu ma suka ringa raina kansu basu san sa dda suka rinka leken cikin keken dokin ba domin suga wanda yake ciki amma da yake an saki labulan keken dokin damar hakan bata samu ba a gunsu nan fa aka bi keken dokin a baya duuu har izuwa kofar gidan sarautar birnin ana isa sai akayi cirko cirko.
.
Kawai sai sadauki marzanu ya zaro wata wasi ka ya baiwa masu gadin gidan sarautar yace su kaiwa sarkinsu, wasikar na isaga sarki hulbasu yana budeta yayi arba da hatimin sarki shardas cikin zumudi ya mike tsaye zumbur ya taho da sauri izuwa kofar gidan sarautar yazo gaban keken dokin yana mai cewa lale marhaban da gimbiya shadila matar sarki shardas na Birnin Romaniya.
.
Koda jin wannan batu sai jama a suka zuba idanu domin suga gimbiya shadila saboda labarinta ya gama bazuwa a nahiyar gaba daya ana ta surutun tsananin kyawunta santaleliyar kafarta ta fara zurowa kasa daga cikin keken dokin tun kafin ma jama a suga ragowar jikin nata suka fara gigita da dimauta ai kuwa tana fitowa gaba dayanta aka yi arba da kyakkyawan surar da Allah yayi mata sai mutane suka kama sambatu wasu kuwa basu san sa adda suka kama dalalar da yawu ba tamkar masu hauka sabon shiga.
.
A wannan lokaci shadila na sanye da wata shudiyar doguwar riga damammiya wacce ta baiyana dukkan siffofin jikinta a fili.
.
Wohoho! kyawu kyauta ce daga Allah. Mutum ba zai iya baiwa kansa ba, kai ko namijin da bai cika namiji ba idan yayi arba da wannan gimbiya a wannan lokaci sai ya zama namiji domin mace ce doguwa wacce bata kasance siririya ba kuma ba kakkaura ba tana da dara daran idanuwa masu dan karen haske da fari hancinta dogone siriri tamkar fikakken alkalami a kasansa an dasa mata dan kankanin baki kamar yankan wuka, cikinta a shamule yake tamkar bata taba cin komai ba kugunta mai fadi ne sosai ga mazaune masu tudu kirjinta a cike yake fal kamar bata taba shayarwa ba gashin ta baki ne sidik kuma dogo ya zuba har kasan marar ta sai haske da kyalli yake kamar madubi ganin wannan kyan yasa na kasa ci gaba nake cewa sai Allah ya kaimu gobe.
.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part D.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Tana gama fitowa daga cikin keken dokin saiga danta yarima hulkas shima ya fito sanye da koren tufafi na alfarma irin nasu na sarakai shima take tsananin kyawunsa ya tafi da hankalin kowa dake wajan domin albasa tayi halin ruwa cikin farin ciki da girmamawa shadila ta risina ta gaida sarki hulbasu har ta budi baki zatace wani abu sai sarki Hulbasu ya tari numfashinta yace yake tauraruwar sarki shardas
ai nan ba muhallin yin magana bane kece bakuwa mafi daraja daga cikin dukkan bakin da suka shigo wannan birni nawa ina tsoron dukkan abinda zai bata miki rai koya taba lafiyarki don haka dolene na riritaki tamkar rai guda daya zaifi kyau mu karasa ku sami hutu da nutsuwa keda danki yarima hulkas.
.
Koda gama fadin hakan sai sarki Hulbasu ya kira sarkin Yakinsa ya hadashi da sadauki marzanu yace yaje a basu nasu masaukin shi kuwa sarki hulbasu sai ya juya Ya nufi cikin gidan sarautar Gimbiya shadila da kuyanginta su uku tare da yarima hulkas suka bi bayansu basu yi wata doguwar tafiya ba suka iso turakar gimbiya LUZURAINA matar sarki hulbasu inda suka isketa tare da danta yarima Basmar wanda shima yarone dan kimanin shekara tara wato ya girmi yarima hulkas tazarar shekara uku
koda yarima hulkas da basmar sukayi arba da juna sai nan take sukaji jininsu ya hadu kafin ma luzuraina ta taso ta taryi gimbiya shadila tuni basmar ya taso da sauri ya tari hulkas yana mai mika masa hannu domin su gaisa ba tare da shakkar komai ba kuwa hulkas ya baiwa basmar hannu suka gaisa basmar ya gabatar da kansa a gareshi a sannan ne sarki hulbasu ya gabatar da gimbiya shadila a wajan matarsa suka rungume juna cikin farin ciki.
.
Nan take sarki hulbasu ya juya ya fito daga cikin turakar ita kuwa luzuraina ta karbi shadila hannu biyu cikin matukar farin ciki kamar taga yar uwarta ta jini wadda suka dade basu hadu ba nan da nan tasa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka ci tare sama wadannan kuyangi guda uku na gimbiya
shadila sai yan uwansu kuyangi suka janyesu suka fice dasu suka taf dasu izuwa nasu bangaren koda aka fara cin abincin sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas ya jashi suka fice daga cikin turakar luzuraina yana mai cewa da umman tasa zamuyi dan tattaki domin na nuna masa gidan nan cikin daga murya luzuraina tace da basmar lallai kada ka fice daga cikin harabata domin sarki ya gargadeni akan na kula da abokinka sosai ko sauraronta basmar baiyi ya yaci gaba da jan hulkas da gudu suka nausa cikin harabar gidan basu tsaya a ko ina ba sai da sukaje wani babban fili wanda aka kawatashi da suke shuke furanni kala kala kuma aka shirya kayan hutu dana wasa a wajan kamar su lilo dawakan katako da wadansu irin gadaje na wasan yara da zuwansu wannan wuri wanda aka kirkireshi musamman saboda yarima basmar sai wajan ya burge yarima hulkas suka hau lilo suna shela kansu suna ta kyalkyala dariyar farinciki daga can sai yarima basmar ya dubi hulkas a lokacin da ya tsaida lilonsa cak yace yakai hulkas kayi sani cewa kaine abokina na farko a duniya kuma na lura cewa kaima nine abokinka na farko.
.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke yarima
hulkas ya dubi basmar yace kai kuwa yaya akayi ka gane haka basmar yayi murmushi yace ai na lura ne da duk irin yanayinka kuma da irin tsananin farin cikin da kake ciki a yau wanda ke nuni da cewar baka taba samun sakewa ba irin na yau sa adda hulkas yaji haka sai yayi ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ai ni nan da kake ganina in ba don albarkacin wannan tafiya da mukayi zuwa wannan gari naku ban taba ma fita daga cikin gidan sarautarmu ba saboda mahaifina baya son naje ko ina dare da rana muna tare babu abinda yake rabamu saboda tsananin shakuwar da ke tsakaninmu.
.
Koda jin wannan batu sai yarima basmar ya cika da tsananin mamaki yace ai kuwa rayuwarka da tawa tazo kusan iri daya domin nima haka mahaifina ya kafa min takunkumin fita baya barina naje ko ina amma sai dana shammaceshi ya zamana cewa ina shiga har cikin gari ba tare da kowa ya sani ba a yanzu hakama akwai wata jarumar yarinya da na hadu da ita wacce tayi matukar burgeni kuma ta bani tsoro domin ban taba ganin karamar yarinya mai jarumtaka kamarta ba don a gabana tayi gumurzu da karti goma duk ta bazar dasu a kasa da karfin damtsenta ba makami ina mai tabbatar maka da cewa shekarunta ba zasu fi namu ba wato ina nufin sa’armu ce, koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai hulkas ya bushe da dariya yace haba yakai abokina wannan kuma wace irin tatsuniya ce haka kazo min da ita ai wannan kawai almara ce kazo mini da ita sai dai idan harkar tsafi ce amma ba zahiri ba.
.
Koda jin haka sai yarima basmar ya kama yin rantse rantse yana cewa lallai al amarin wannan yarinya ba tsafi bane yarima hulkas yace idan har kana son na yadda da wannan labari daka bani sai dai ka kaini naga yarin yar a zahiri da Idanuna yanzu ta yaya kake ganin zamu iya fita daga cikin wannan gidan sarauta taku harmu shiga cikin gari muje ka kaini inda wannan yarinya take?
.
Sa adda yarima basmar yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ai wannan mai sauki ne kamar cire silin gashi daga cikin tandun mai muddin zaka iya yin duk abinda zanyi hulkas yace ai yanzu tuni zuciyata ta kwadaitu da son ganin wannan yarinya da ka bani labari kuma raina ya kagu damu tafi can inda take saboda a rayuwata babu abinda nake so sama da jarumtaka da iya yaki gashi kuma ko sau daya ban taba jarraba yin suba kai in dai wannan labari daka bani gaskiya ne zan iya biyan wannan yarinya dinare dubu domin ta koya mini yaki da jarumtaka ina mai rokonka daka tashi mu hanzarta shiga cikin wannan gari naku koda jin haka sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas suka duro kasa tare daga kan lilon suka ruga izuwa wani bangare daban dake gidan saida sukayi gudu na tsawon yan dakiku masu yawa sannan suka iso karshen gidan sarautar suka shiga cikin wani kwararo wanda ya kaisu inda matattakalar shaddar gidan sarautar take gaba daya da zuwa suka iske wadansu wulakantattun bayi suna ta debo kashi suna lodashi a cikin wani amalanke, koda bayin sukaga shigowar yarima basmar tare da hulkas sai bayin suka zube kasa gaba dayansu suka gaida basmar a lokacin da doyin kashin ya ishi hulkas ya kama kau da kai yana toshe hancinsa shi kuwa basmar ko kadan bai damu ba ga dukkan alamu ma ya saba da zuwa wajan basmar ya dubi shugaban bayin yace yau mu biyu ne nida abokina, ina son ku fitar damu zuwa cikin gari kamar yadda kuka saba a sirrance.
.
Koda jin haka sai shugaban yayi dariya yace an gama ya shugabana bamu ladan aikinmu kamar yadda ka saba cikin alamun damuwa yarima basmar ya ce yau na sha afa ban taho da shiri ba ama ai kasan ba zanyi muku wasa ba gobe zan baku ladanku gama fadin hakan keda wuya sai suka jiyo takun sawun dakarun dake kulle dasu cikin hanzari bayin suka boye su yarima hulkas a karkashin amalanken da suke loda kashin faruwar hakan keda wuya sai ga wadansu dakaru biyu sun shigo wajan rike da bulalai da shigowarsu sai suka tsaya a gaban amalanken dai dai inda su yarima basmar suke har daya daga cikinsu ya take danyatsan hulkas guda da katon takalminsa har hulkas zaiyi ihu sai yarima basmar yayi sauri ya toshe masa baki da tafin hannunsa daya daga cikin dakarun ya dubi shugaban bayin ya daka masa tsawa yace a cikinku waye mai murya irin ta yara tabbas daga can nesa na jiyo muryar yaro a nan har shugaban bayi ya budi baki zaice wani abu sai wani daga cikin yaransa ya tari numfashinsa yayi magana da karamar murya iri daya sak da ta yarima basmar al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan koda jin hakan sai dakarun suka kyalkyale da dariya wanda yayi magana da farko ya dubi bawan da yayi muryar yarima basmar yace tabbas kana da hikima watarana zan gabatar dakai gaban sarki domin ka debe mana kewa.
.
Koda gama fadin hakan sai dakaru biyu suka juya suka fice daga cikin wannan kwararo da ake aikin kashi fitarsu keda wuya sai bayin suka sauko buhuhuna da suka dura kashi a ciki suka zura yarima basmar da hulkas a kansu suka kulle bakin buhuhunan amma sai suka yi dabaara suka farka buhun a dai dai kan fuskokinsu yadda zasu iya shakar numfashi duk da haka sai da yarima hulkas ya kama kakarin amai saboda doyin kashi gashi an labta wadansu buhuhunan a samansu nauyi ya damesu nan take yarima hulkas yaji kwalla ta cika masa idanu yace oh duniya juyi juyi kwado ya fada ruwan zafi wai yau ni yarima hulkas nine a cikin buhun kashi saboda kawai ina son shiga cikin gari naga abin al ajabi tabbas neman duniya ba wasa bane kuma ba a samunta cikin sauki sai ansha wuya yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaji an ja amalamken da suke kai anyi gaba dasu nan fa akayi ta tafiya dasu ana wucewa ta cikin sako sako da lungu lungu na gidan sarautar har sai da aka wuce dasu ta cikin kofofi shida duk kofar da aka zo sai sun tsaya an caje buhuhunan kashin wani lokacin ma sai dakaru sun caccaka tsinin takobi a cikin buhuhhunan saboda zargin ko an sato wani abu a ciki in ba don Allah ya kiyaye ba saura kiris takobin wani badakare ta tsire ido guda na yarima Hulkas, shikuwa yarima barmas ma sai da aka dan sokeshi a kafada jini yayi tsartuwa yaji kamar ya kurma ihu amma sai ya daure a haka dai aka samu aka fice dasu ba tare da asirinsu ya tonu ba kafin a isa bakin kogin garinne yarima hulkas yaji nadama ta zo masa bisa wannan ganganci da sukayi na sai da ransu don kawai suna son su shiga cikin gari.
.
Ana isowa bakin kogin ne aka sauke buhunhunan dasu yarima hulkas ke ciki ko da aka fito dasu aka ga yarima barmas ya sami rauni a kafadarsa sai hankalin bayin ya dugunzuma ainun suka firgice, shi kuwa yarima Hulkas yana ganin rauni a kafadar barmas bai san sa adda ya kama rigarsa ya yagata ya daurewa barmas raunin don tsaida jiniba.
.
Cikin rudewa hulkas ya dubi barmas ya ce yakai abokina tunda dai ka sami wannan rauni zaifi kyau. Mu hakura mu koma cikin gidan sarauta mubar batun ganin wannan jarumar yarinya domin muje ayi maka magani da sauri koda jin wannan batu sai yarima barmas yayi murmushi yace aini idan nayi gaba bana komawa baya kuma idan har muka koma gida bamuga wannan yarinyar ba ai mun sha wahalar banza kenan mun sayar da rayuwarmu a wofi, tunda dai ka tsayar da jinin dake zuba a jikina babu komai zan iya gabatar da abinda muka fito yi lafiya har mu kammala, yanzu sai mu shiga cikin kogin nan mu wanke kashin dake jikinmu don kada muje wajan ta muna wari nan take yarima basmar ya sallami bayin akan cewa idan sun kawo sawun karshe na kashin suyi tafiyar kada suyi shakkar komai don haka suka saba yi shi dasu domin shine ya san dabarar da yake yi yake komawa cikin gidan sarautar ba tare da an ganshi ba.
.
Ba tare da bata lokaci ba yarima barmas da yarima hulkas suka ruga zuwa cikin kogin suka kwabe kayan jikinsu sukayi tumbur sai da suka wanke kayan nasu tas sannan suka fito suka shanyasu akan wata bishiya suka sake komawa cikin gefen kogin suka kama wanka a wannan lokaci ne yarima hulkas ya tsinci kansa a cikin wani iein nishadi wanda bai taba jinsa ba na farinciki walwala da annashawa abin da yafi burgeshi shine ganin yadda yau ya sami yancin kansa har yake yiwa kansa wanka da wanki alhalin bai taba yiwa kansa wata hidima ba sai dai ayi masa komai sai da kayan da suka shanya suka bushe sannan suka fito daga cikin kogin suka je suka sanya kayan nasu sannan yarima basmar ya wuce gaba hulkas na biye dashi suka nufi wata siririyar hanya wacce zata kaisu cikin gari. A wannan lokaci yammaci ne mai dauke da yanayi mai kyau da dadi domin wata irin iska ce mai sanyi ke kadawa kafin su iso cikin garin sai yarima basmar da yarima hulkas suka rude fuskokinsu da rawaninsu ya zamana cewa idanunsu kadai ake gani don kada a shaidasu haka dai suka ci gaba da tafiya suna ratsawa ta cikin unguwanni har suka iso wata unguwa dake can karshen gari kuma suka tunkari gida na karshe a unguwar wanda shi ne mafi muni da kaskanci. Da ganin gidan kasan cewa na talakawa ne fitik marasa gata ko kuma bako wanda bai kasance dan gari ba saboda an gina gidanne da katako ko kyakkyawan tsari baiyi ba tun daga nesa su yarima hulkas suka hango wani mutum mai kwarjini zaune a kofar gidan fuskarsa cike da kasumba amma kuma hannunsa guda na hagu a yanke yake sannan kafarsa guda a lankwashe take sai da sanda yake dogarawa mutumin na tsaye a can gefe daya yana kallon wadansu tsuntsaye dake ta wasa akan wata bishiya saiga matarsa wata yar kyakkyawar mace yar kimanin shekaru talatin da doriya wacce ba zatafi sa ar gimbiya shadila ba ta fito daga cikin gidan dauke da kofin shayi ta nufi mijin nata.
.
A dai dai wannan lokaci ne mijin matar ya hango su
yarima hulkas sun durfafoshi shi da matar tasa sai suka kurawa su yarima hulkas idanu kawai cikin sanyin jiki da mamaki.
.
Dama A wannan lokaci su yarima basmar sun cire rawanin da ya rufe fuskokinsu kyawunsu da kwarjininsu irin na yayan sarakai ya baiyana a fili kururu bisa mamaki sai yarima hulkas yaga mijin matar ya kura musu idanu ko giftawar ba yayi, koda suka iso daf dasu sai yarima basmar ya risina a cikin
biyayya ya gaishe da mutumin da matarsa sannan ya gabatar da kansa yace nine yarima basmar dan sarkin garin nan wanda kuma abokina ne sunansa hulkas munzone wajan yarka siyama domin muga baiwar da take da ita ta jarumtaka da iya yaki saboda abokina bai amince da tana da wannan baiwar ba a sa adda na bashi labarinta……..
Ku Taba Nan Domin Karanta Littafin Tsatsuba Na Biyu Wannan Abdulaziz Sani M/Gini Ya Rubuta.
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part E.
Na Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai mutumin da matarsa suka dubi junansu sukayi murmushi sannan mutumin ya dubi basmar yace hakika wannan abokin naka zai sha mamaki kuwa domin a yanzu hakama tuni siyama ta shiga gasar jarumtakar da za ayi a fadar mahaifinka wacce za a fara gabatar da ita gobe kuma ina sa ran cewa itace zata karbi kambun wannan gasa.
.
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya kyalkyale da dariya yace haba ai wannan ma almara ce ya za ayi karamar yarinya wacce aka ce batafi sa a taba zata shiga wannan gasa wacce manyan mutane zasuyi kuma jarumai na daga sassa daban daban na
duniya har ace talashe gasar.
.
Koda jin wannan batu sai ran mahaifin siyama ya baci ya murtuke fuskarsa nan take cikin fushi ya kwalawa siyama kira itakuwa, sai gata ta fito daga cikin gidan a cikin shigar yaki.
.
Siyama ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance duk da cewar yarinya ce yar shekara shida sai mutum yayi zaton takai shekaru goma sha saboda ta kasance doguwar gaske sai mutum ya dubi fuskarta sannan zai gane cewa yarinyace tana da cikakkiyar sura da zati irin na cikakkun mata ababan kwatance.
.
Koda yarima hulkas yayi arba da siyama sai yaji nan take ya kamu da tsananin kaunarta amma da yaga ta kalleshi tana mai gabza masa harara sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya bai bayeshi yaji kamar ya ruga da gudu saboda kwarjininta, siyama ta karaso gaban iyayanta ta risina a garesu tana mai amsa kira kawai sai mahaifin nata ya daga sandar dake hannunsa da hannun nasa lafiyayyan yayi nuni a gareta ko da ganin haka sai siyama ta zare takobinta ta kwala ihu sannan ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta fada kansa suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro ga dukkan mai kallo nan fa duk su biyun suka wanzu suna masu kaiwa junansu mugayan hare hare cikin bakin zafin nama duk sa adda takobin siyama ta hadu da sandar mahaifinta sai dai kaji kal sautin haduwar karafa gami da tartsatsin wuta na tashi tunda yarima basmar da hulkas suke ganin gumurzun mazaje masu tsananin zafin nama da jarumtaka ba kamar siyama da mahaifinta siffanta jarumtakar tasu da kwatantata ba zai yiwu ba, sai dai abinda idanu suka gani babu wani jarumi daya fadowa yarima hulkas a rai dayaga jarumtakar siyama da mahaifinta sai mahaifinsa sarki shardas hulkas ya numfasa sannan yace a cikin zuciyarsa babu, wani jarumi da zai iya fafatawa da wadannan mutumin ko yarsa siyama ya samu galaba a kansu face mahaifinsa sarki shardas
kash ina ma tare da sarki mukayi wannan tafiya da yaga wadannan jarumai masu ban al ajabi da idanunsa yanzu dama she a wannan duniya akwai irin wadannan jarumai.
.
Sai da siyama da mahaifinta suka shafe sa a daya da rabi suna fafatawa amma dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar jikin dayan ba duk da cewar suna yakinne a fusace da dukkan karfinsu da iyakar kwarewarsu tamkar abokan gaba masu neman hallaka juna.
.
Koda sukaga sun kasa cutar da junansu da makami sai sukaja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon junansu tamkar zakaru kuma suna murmushi
shidai mahaifin siyama murmushin da yake yi bana komai bane face na farin ciki bisa ganin abinda ya koyawa yasa ta kware a a kansa ainun harma ta fishi kwarewar a matsayinta na ya mace, ai dama ance kyan da ya gaji ubansa kuma barewa batayin gudu ba danta yayi rarrafe babban abinda ya daurewa su yarima hulkas kai shine ganin yadda mahaifin siyama ya iya yin wannan bkin gumurzu alhalin ya kasance mai hannu daya kuma gurgun da yake dogara sanda.
.
Kwatsam! sai siyama da mahaifinta suka ajiye makamansu a kasa gefe daya wato shi ya ajiye sandar karfen dake hannunsa itakuma ta ajiye takobinta faruwar hakan keda wuya sai sukayi alkafira a kasa suka afkawa juna suka ci gaba da kaiwa juna naushi da bugu hannu da kafa sai gashi siyama tana shanye naushi da bugu kai kace wata katumar namiji ce ba mace ba, kuma yarinya karama yar shekara bakwai tabbas horon da siyama ta samu zata iya gumurzu a tsakiyar miliyoyin dakarun yaki ma kuma ta dade tana fafatawa tana mai taka rawar gani a wannan fadan hannu ma sai da siyama da mahaifinta suka shafe kusan sa a biyu gashi dai sun hadawa junansu jini da majina kuma sun gaji likis amma saboda tsananin juriya naci da dakakkiyar zuciya sunki su daina fadan.
.
Koda matar mahaifin siyama taga abin ya wuce gona da iri ta ruga ta shiga tsakiyansu ta tsaida fadan, a sannan ne siyama da mahaifin suka zube kasa suna haki da dariya daga can mahaifin siyama ya dago kai ya dubi yarima hulkas yace shin yanzu ka gamsu kuma ka yarda cewar yata zata iya shiga wannan gasar jarumtaka da za ayi a fadar birnin nan?
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas yayi murmushi yace tabbas na gamsu kuma na yarda dari bisa dari, zata iya ya kai abul siyama idan ba zaka damu ba ina son na nemi wata alfarma guda a wajanka.
.
Cikin mamaki mahaifin Siyama yace yaro ina sauraronka fadi tambayarka naji in dai na sani zan baka amsarta, hulkas yayi gyaran murya yace ina son ka bani takaitaccen tarihin rayuwarka sannan ina son na sani shin wannan lalura da na ganka da ita ta rashin hannu da kafa daya ta sameka ne da girmanka ko kuwa a haka aka haifeka kai mutumin wace kasa ne kuma ya akayi kazo nan birnin domin ga dukkaln alamu kai bakone a garin nan bisa lura da yanayin gidanka da na gani wanda ya banbanta da dukkan gidajen birnin nan.
.
Lokacin da yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jikin mahaifin siyama yayi sanyi yayi sauri ya sunkui da kansa kas don hawaye ne ya subuto masa kawai saiyayi shiru baice komai ba, caraf sai matarsa wato
ummul siyama ta dubi yarima hulkas tace ka tambayi mijina tambayoyinda idan ya tuno da amsarsu yake shiga cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa lallai a yanzu ba zaka sami amsar wadannan tambayoyi ba sai dai wani karon.
.
Koda jin haka sai yarima hulkas da barmas sukaji sun kamu da tausayin mahaifin siyama nan take hulkas ya tako kafafunsa yazo har gaban mahaifin siyama ya dafa kafadarsa ta dama da tafin hannunsa yace ka gafarceni yakai abul siyama inda na san cewa tambayoyina a gareka zasu sosa maka zuciya su tuno maka da wani abin damuwa da ba zan gabatar dasu ba a gareka mun barku lafiya sai gobe a filin fada zamu hadu idan kunzo filin gasar jarumtaka.
.
Koda gama fadin haka sai su hulkas suka juya da nufin ya kama hannun barmas su tafi amma sai yaji abul siyama ya dafa kafadarsa cikin mamaki hulkas ya juyo suka fuskanci juna yaga abul siyama yana yi masa wani irin kallo mai nuna alamar kamar ya sanshi kuma akwai alamun dumbin magana a zuciyarsa wacce ya kasa amayar da ita daga bakinsa
har abul siyama ya budi baki zaice dashi wani abu sai kuma ya kasa yace yaro mun gode bisa ziyarar da kuka kawo mana amma nima ina rokon alfarma guda daya a wajanku amma bata komai bace face ina son kada ku sake xuwa nan wajanmu domin a duk sa adda na kalli fuskarka ina fama wani mugun rauni dake cikin kahon zuciyata.
.
Abu na biyu kuma ina rokonku da kada ku bayar da labarina ko na yata ga waninku saboda wani babban sirri na rayuwarmu har sai bayan an kammala gasar jarumtakar da akeyi a garin nan, koda gama fadin hakan sai abul siyama ya dafa kafar matarsa da hannunsa lafiyayyan ita kuma siyama sai ta tallafa kugunsa suka taimaka masa suka juya suka nufi cikin wannan gida nasu na katako.
.
Koda suka isa daf da bakin kofar gida zasu shiga sai ab siyama ya juyo ya yiwa hulkas wani irin kallo idanunsa cike da kwalla take hulkas yaji tsigar jikinsa gaba daya ta tashi kuma kaunar abul siyama ta kara shigarsa tamkar dama can sun kasance yan uwan juna nan fa yarima hulkas ya kasa motsawa daga inda yake kuma yaji kamar yace da yarima basmar ya barshi ya kwana a nan gidansu siyama domin ji yayi babu abinda yake so sama da kasancewa tare dasu kawai sai hulkas ya bisu da kallo har suka kule a cikin gidan.
.
Koda ganin haka sai yarima basmar ya rugo ya kama hannun yarima hulkas ya jashi da gudu suka bi hanyar da zata mayar dasu can gidan sarautar maimakon su wuce kai tsaye izuwa gidan sarautar sai yarima basmar ya kaisu gidan wani dan kasuwa mai suna abul yamzin wanda kullum sai ya kaiwa sarki hulkasu tulunan ruwan giyar da yake sha gami da ruwan inibi sarki hulbasu ya aminta dari da attajirin abul yamzin don haka ko caje tulunan giyar sa da na inibi ba ayi a duk sa adda ya shige dasu cikin gidan sarautar.
.
Tsakanin yarima basmar da attajirin abul yamzin akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna don haka sun san sirrin junansu sosai da zuwan yarima basmar da hulkas gidan attajiri sai aka sanyasu a cikin manyan tuluna guda biyu wadanda babu komai a cikinsu aka hada da wadanda ke dauke da ruwan giya guda goma dana ruwan inibi goma aka zuba su a cikin dana ruwan inibi aka zuba su a cikin wannan amalanke aka tura aka tafi dasu gidan sarki a can gidan sarki kuwa hankalin gimbiya shadila dana luzuraina ya tashi ainun domin ganin cewa tunda su yarima suka fita basu dawo ba har bayan tsawon sa a uku nan da nan aka baza dakaru zuwa kowani sako na gidan ana nemansu koda aka duba ko ina ba a gansu ba sai hankalin su shadila ya sake tashi suna shirin su tura aje a sanar da sarki hulbasu kenan saiga yarima hulkas da basmar sun shigo cikin turakar.
.
Koda ganinsu sai shadila ta ruga izuwa yarima hulkas cikin matukar farin ciki ta rungumeshi daga nan ta jashi zuwa cikin dakin barcinta da aka bata ta kulle kofa ta dubeshi cikin fishi da matukar damuw atace ina kukaje kuka buya haka har kukayi matukar tayar mana da hankali.
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya sunki
da kansa kas ya tuna cewa shifa a rayuwarsa bai taba yin karya ba dan haka take ya yanke hukuncin ya sanar da ita gaskiyar duk abinda ya faru tun daga
lokacin da sukaje bangaren da ake aikin kashin gidan kawo sa adda aka kaisu bakin kogi sukayi wanka sannan suka wuce gidansu siyama hatta kamannin siyama dana mahaifinta dana babarta sai da ya zaiyana mata har dama irin tsananin jarumtakar baban Siyama a matsayinsa na musaki mai hannu daya da kafa daya sai da ya shaida mata
koda shadila taji siffifin baban siyama da yadda yake yakinsa sai nan take zuciyarta ta kama bugawa da karfi, ba komaine ya haddasa hakan ba face tunowa da tsohon masoyinta hailur wato mahaifin hulkas na gaskiya domin shine kadai yake da siffa da sura irin wacce hulkas ya shaida mata yanzu kuma shine kadai mutumin da ta san cewa yana irin salon yakin da aka fada.
.
Cikin firgici da razana shadila ta mike tsaye zumbur
ta kama kafadun hulkas ta girgiza dakarfi tace a ina kaga wannan jarumi mahaifin siyama ya za ayi ka kaini inda yake na ganshi, cikin alamun matukar mamaki yarima hulkas ya dubi shadila yace yake ummina shin kinsan wannan mutum ne ko kuwa kun taba jin labarinsa ne a jana wani baniba?
.
Koda jin haka sai shadila ta tuno da gargadin da shardas yayi mata akan cewar idan ta kuskura ta shaidawa hulkas cewar bashi bane mahaifin sa na gaskiya sai ya kasheta ya lalata dukkan rayuwarta nan take shadila ta wayance ta bagazar da maganar ta nunawa hulkas cewar kawai jarumtakar baban siyama ce ta burgeta nan dai ta lallaba hulkas yaje ya kwanta saboda ya mance da komai ita kuma saita juya masa baya a lokacin da hawaye ya zubo mata tace a ranta duk yadda za ayi sai nayi naje na ga mahaifin siyama domin na gani da idanuna ko tsohon mijina ne ya zama nakasashshe kai ba zata yiwu bama ya za ayi ace hailur yana na a raye a duniyar nan amma har ya manta dani yayi wani auren harma ya haifi ya alhalin yana tsananin kaunata fiye da komai a rayuwarsa……
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMO SAURAN ABOKAN TAFIYARSU..??
.
SHIN SHADILA ZATA SAMI DAMAR ZUWA INDA MAHAIFIN SIYAMA YAKE??
.
SHIN ZARGIN DA TAKEYI CEWAR TSOHON MIJINTA NE MAHAIFIN SIYAMA GASKIYA NE???
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI FARA MALLAKAR HULAR LAMSARA
.
Don jin Cigaban wannan labari na Tsatsuba Littafi na 4 sai ku danna bulun rubutun nan