Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 17 By Hafsat Bature

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
Daga alƙalamin Boss Bature✍️
Dedicated to Aunty kubra❤
E17
Sakin baki angel tayi galala tana kallon batool, da mamaki akan fuskarta tace”saboda kawai nayi ihu sai ya 6ace a neme shi arasa, ko dai yana da ta6in hankali ne”? Tayi tambayar tana kallon batool,
Kafin batool ta bata amsa, Haris yace “yanzu ba lokacin yin magana bane, bamusan awani hali ɗan uwanmu yake ciki ba, yamakata muyi hanzarin nemo shi”
Ya kai ƙarshen maganar, tare da kai hannu ya kar6e fitilar dake a hannun batool, ya yi gaba suma suka bi bayan shi,
Ko’ina kaf sai da suka duba, Basu ga danish ba, a gajiye suka koma saman gadajensu, kowa ya zauna cike da jimamin rashin ganin danish,
Deeja tace”ni dai bari naje na kira tsohuwa,” haris ya dakatar da ita” dare yayi sosai, kada mu takura mata, mu jira zuwa gobe da safe, nasan kafin lokacin duk inda yaje zai dawo ne”
Angel dai duk ta rasa sukuni, aranta tace No wonder dama ni nasani, ba cikakken hankali gare shi ba, ”
Bacci ne ya fara ɗaukar wasu daga Cikin su, Mutun uku ne suka gaza runtsawa, Haris da Batool sai Angel, kuma dukansu idanuwansu acike suke da bacci,
Fitsari ne ya matse ta, da sauri ta sauko daga saman gadonta, hannunta ruƙe da fitila, ta nufi first door ta toilets ɗinsu,
Bayan ta buɗe ƙopar ta shiga ɗaya daga cikin toilet ɗin, ajiye fitilar ta yi a ƙasa, ta sanya hannu ta tu6e wandon jikinta ta zuƙunna tana fitsari, har wani lumshe ido take yi, saboda daɗin da taji, sai da ta kammala yin fitsarin tayi tsarki, tana ƙoƙarin mayar da wandonta, taji mutsu mutsun mutun, Hankalin ta yayi matuƙar ta shi, Kasa juyawa tayi la66anta sai kerma su ke yi, tsananin tsoro ne bayyane acikin idanuwanta, Ta wutsiyar idonta take hangen shi biji biji, koma wanene dai a zaune yake, ya jingina bayan shi jikin bango, Gefen tukunyar fulawar dake ajiye cikin toilet ɗin su,
Tafi ƙarfin minti goma a tsaye batare da ta juya ba, zuciyarta a cunkushe da tunanin wanene Acikin toilet ɗin? Mutun ko Aljan? Kenan koma wanene ya gama ganin budurcin ta,” ta ambaci hakan acikin zuciyarta, tunma kafin taga wanene Ranta ya 6aci ta harzuƙa sosai, ko aljani ne wannan ɗan tahalikin sai ya ɗanɗani kuɗarsa,
Daurewa ta yi ta cije, a wani slow ta ɗan juya tana kallon wurin,
Har saida ta zabura lokacin da tayi arba da Danish, a matuƙar ruɗe take kallon shi,
Ya ƙanƙame Jikin shi da ke ta kerma, ya saki dogayen ƙafafuwanshi ƙasa, ya jingina bayan shi jikin bango, Gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi,
Runtse ido ta ɗanyi tare da biting lower lip ɗinta, Har ta kai hannu zata rarumi bucket ta kwaɗa ma shi akai, sai kuma ta fasa ganin da alama bai ganin ta, saboda sumar kanshi data lullu6e eyes ɗinshi,
cikin sanɗa ta soma tafiya tana tunkararshi, a saitin inda yake zaune ta zuƙunna, tana kallon shi,
Abunda ya faru lokacin da angel takwatsa ƙarar nan, ya farka a firgice ya duro daga saman gadonshi tamkar walƙiya yabar cikin ɗakin saboda tsabar rikitar da ya yi ashe cikin toilet ya faɗo,
Tagumi ta zabga tana kallon ikon Allah, ta sauke ajiyar zuciya yafi sau uku, da ace yau ta kama shi yana kallonta lokacin da take Cikin yin fitsarin nan, da kuwa ya gane kuransa, Allah ne ya taimake shi saboda sam baya a hayyacinsa, baisan ma ta shigo cikin toilet ɗin ba,
Miƙa hannu tayi da niyar ta janye sumar dake akan fuskarshi, sai kuma ta fasa ta miƙe, taje ta ɗauki fitilarta, kafin ta kama hanyar fita daga cikin toilet ɗin, Bayan ta fito ta nufi cikin ɗakin kamar yadda ta tafi tabar batool da haris xaune saman beds ɗinsu a haka ta same su,
Gefen gadon batool ta tsaya tare da ɗan ranƙwafawa saitin kunnanta tace”Danish yana a toilet, ki faɗa ma haris kuje ku ɗauko shi, Amma kada ki ce ni na faɗa maki”
Buɗe ido batool tayi jin maganar Angel a cikin kunnanta”are u serious danish yana acikin toilet”
“Eh, yanzu na ganshi aciki, amma kamar baya a hayyacinsa”
Jiki na rawa Batool ta sauko daga saman gadonta, Sai da tafara gaya ma Haris cewa Danish Yana acikin toilet, tukunna tayi gaba shima yabi bayanta,
Ajiyar zuciya angel ta sauke, tare da ajiye fitilar ƙasan gadonta, Ta haura daman gadon ta kwanta, tana jiran taga sun shigo da shi, Zuciyarta a cike take da tunanin meke damun shi? yanayin abubuwan da yake yi kamar akwai wani abu dake damun shi, ‘ can kuma saita ja guntun tsoki aranta tace”Ko ina ruwana da shi, matsalar shi ce,”
Jin takun tafiyarsu yasa ta ɗan saci kallonsu, Batool ce da haris sun ruƙoshi daƙyar yake tafiya, A saman gadonshi suka sake shi, ya haye saman mattress ɗinshi ya kwanta, Haris ya janyo mashi duvet ɗinsa ya lullu6a mashi har zuwa chest ɗinsa,
Kafin suka koma saman beds ɗinsu domin yin bacci,
Juyowa tayi da niyar ta saci kallon shi, karaf suka haɗa ido da shi, Harara ta jefa mashi, tare da juya ma shi baya ta kalli 6angaren hagu,
Tunani ta shiga yi acikin zuciyarta, anya kuwa ɗazu bai kalle ta ba, lokacin da take yin fitsarin nan ba? Idan kuwa haka ne tabbas ya gama da ita, shikenan Ya gama ganin tsiraicinta, ranta ne ya bata cewa ta ƙara juya taga idan ya yi bacci, a hankali ta sake waiwayowa, karaf suka haɗa ido da shi, Ɗaure mashi fuska tayi tare da zare ma shi gray eyes ɗinta”Kallon ya isa, Ka juya ka kalli can mana, bakasan ba’a son ana bacci ta 6angaren Hagu ba,”
Yadda kasan tayi magana da gunki, Ko motsa lips ɗinsa, baiyi ba balle ma tayi tunanin zai tanka mata,
“Can’t u hear me”? a ɗan tsawace tayi ma shi maganar, jin yaƙi tanka mata kuma yaƙi daina kallon nata, yasa ta ruƙo pillownta, Ta daddage ta jefa ma shi saman fuskarshi, Salon Jan faɗa,
A hankali ya ɗaura dogayen yatsun hannunshi saman pillown ya janye shi daga kan fuskarshi, Ya ɗaura shi saman nashi pillow ɗin ya haɗa biyu kenan, ya ɗaura kan shi asama,
Rai a6ace tace”ka dawo mun da pillow ɗina, ko ranka ya 6aci,” banza ya yi mata,
“Magana fa nake maka”
Sai lokacin ya ɗan buɗe baki yace”Zo ki ɗauka, ae bani na kawo shi nan ba” shiru ta yi tana cigaba da kallon shi, ganin ta tsare shi da ido, yasa shi juya mata ƙeya,
Cike da takaici ta koma ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e fuskarta, sai da tayi addu’a tukunna ta samu bacci ya yi awon gaba da ita,
In the morning,
Kasancewar Jiya basu samu isasshen bacci ba, Babu wanda ya farka,
Cikin bacci angel ta yi Kakkauran Juyi da niyar ta gyara kwanciyarta, kwatsam idanuwanta suka sauka akan fuskar tsohuwa dake a tsaye bakin gadon ta, hannunta na ruƙe da sanda, mamaki ne ya kamata har ta soma tunanin kodai mafarki take yi, ƙura mata ta yi tana kallonta, itama kuma tsohuwar ita take kallon,
Ƙasa ƙasa da murya angel ta ambaci”A’uzu billahi minasshaiɗanin Rajim”
Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace”Ni ce shaiɗanin”?
Bata amsa mata tambayarta ba, har saida ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta jikin bango, tukunna tace “Ai kin wuce nan, idan akwai na gaba da shaiɗan to ke ce tsohuwa”
Baki asake tsohuwa ke kallonta,
“Meyasa kika zo kika tsaya a bakin gado na”? Ta yi tambayar fuska a ɗaure take kallonta,
“Zuwa nayi don in tashe ku daga bacci, naga har gari ya waye baku farka ba……” tunkan takai ƙarshen maganarta, Angel ta katse ta da cewa”Ƙarya kike yi, Idan tashin mu kika zo yi daga bacci why baki bi kowani gado ba, Sai kika zo kan gadona kika tsaya kina kallo na, wlh kiji tsoron Allah, tsofe tsofe dake kina ƙarya,” ta ƙarasa maganar tana sakar mata harara,
Jinjina kai tsohuwa tayi”Ke wai baki jin tsoro na? Meyasa baki jin shakkar yi mini magana ne?
“Inji tsorin ki akan me? Ni da nake neman hanyar da zan tarwatsa shirin ku taya kike tunanin zan ji tsorin ki? Idan ma kina tunanin hakan acikin ranki to ki daina, suma waɗanda suke jin shakkar taki don kin juya masu tunaninsu ne, Amma asannu zan dawo da su Cikin hayyacin su, ”
Shiru tsohuwa tayi tana kallonta batare data ce komai ba,
Angel kuwa taci gaba da cewa” ina zargin jiya ke ce kika kwaɗe mun kaina da sandar hannun ki, Saboda kinga ina ƙoƙarin kwance shirinki, wato so ki kayi nima ki ɗaure mun kaina ta yadda zan manta da komai, tabbas kinso ki yi nasara sai dai Allah bai baki ikon yin hakan ba, farkawar dana yi daga bacci komai dana manta sai da ya dawo cikin kaina, Kuma bazan fasa faɗa masu Allah ba, har sai na fargar da su,
*Mu haɗu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, domin neman ƙarin bayani ayi mun magama kaitsaye 08103884440*
Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete
Mu haɗu next page
(bakuyin Liking Da comment maganar gaskiya, shiyasa sometimes ma baku samun update akai Akai, tun da alama ce dake nuna baso ku ke yi ba idan kinsan kina son cigaba da karanta book dinnan kiyi comment da like, daga yau idan naga babu likes ba comment, bazan cigaba da wahalar daura shi ba)