Sirrin Rike Miji

Yanda Zaki Hada Sabulun Zuma Don Gyaran Jiki Da Fidda Kowanne Irin Tabo Cikin Sauki

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka.

Yanda zaku hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a cikin gidanku

Yana da kyau mata su san yanda ake hada irin wadannan sabulun domin gyaran jiki koh kuma don yin sana’a.

Karanta>>> Hanyoyin Magance Matsalolin Ma’aurata Cikin Sauki

Yawan shafe-shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, yafi amfani da kuma gyaran fata, toh a yau na kawo muku hanyoyi daban-daban wa’inda za a yi amfani da sabulun salo don gyaran fata.

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Zuma
  • Bitamin E
  • Man almond (za’a iya samun sa a shagunan masu saida kayan kwalliya)

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

Yanda Za’a Hada:

Za’a daka sabulun salon koh kuma a saka abin kankare kubewa a kankare, sannan sai a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun, sannan sai a zuba ‘bitamin E’ da man ‘almond’ sai a kwabasu sosai, irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya fata tayi subul-subul da laushi.

Karanta>>> Maganin Gyaran Nono Mai Saukin Haɗawa

Ga Kuma Hadi Na Biyu:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Man kadanya
  • Ruwan ganyen ‘aloe vera’

Yanda Za’a Hada:

Za’a narka man kadanya da ruwan zafi sannan a narkar da sabulun salon shima, sai a samu gora a zuba hadin man kaden tare da na man kadanya da ruwan ganyen ‘aloe vera’ sannan a girgiza su domin su hadu sosai.

Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure

Amma za’a iya amfani da shi nan take daga gama hadawa koh kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani dashi.

Yanda Zaki Hada Sabulun Zuma Don Gyaran Jiki Da Fidda Kowanne Irin Tabo Cikin Sauki Txt

Ga Hadi na Uku:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Zuma
  • Kurkum
  • Man kwakwa
  • Man Zaituun

Yanda Za’a Hada:

Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man kwa-kwa da kuma man zaituun, a zuba su a cikin gora sannan a girgiza sosai domin su hadu sosai, sai a zuba a murta.

Karanta>>> Yadda Rai Dore Yake Warkar Da Cutuka Da Dama A Cikinsu Harda Sanyin Mara Da Kuma H.I.V

Za’a iya amfani da wannan hadin nan take koh kuma a jira yayi tauri bayan sati biyu sannan a fara amfani da shi.

Wannan hadin Shima yana magance kuraje, gumi koh na fuska da wasu cututtukan fata.

Yanda za’a magance matsalan tabo a Jiki Akwai hanyoyi da dama wanda za’a bi don magance tabo a fata amma a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki domin magance tabo a fata, idan tabo ya yi yawa a fatar mace, yana boye kyawunta, don haka ya kamata a kula da fatar jiki sosai.

Ga Wasu Abubuwa Guda Uku Da Za’ayi Amfani Dasu Domin Magance Tabo A Fata Kamar Haka:

  1. Kurkum: Za’a samu kurkum sai a hada shi da madarar ruwa yanda zaiyi kauri sannan a shafa a kan tabo, sai a barshi yayi kamar tsawon minti 5 zuwa 10 sannan a wanke.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Za’a cigaba da shafa wannan hadin sau 2 a rana kamar tsawon watanni 3 koh 4.

  1. Lemun tsami: Za’a yanka lemun tsami gida 2 sannan a yaryada masa siga sannan a dirza shi a kan tabon na tsawon minti 5.
  2. Ganyen ‘Aloe vera’: Shima za’a matse ruwan dake cikin ganyen ‘aloe vera’ sannan a shafa a tabo na tsawon lokutan da za’a iya bari, sannan sai a wanke, a rinka yin hakan kamar sau 2 koh 3 a rana, sannan kuma za’a iya ci gaba da yin hakan har na tsawon watanni 3.

Ku Karanta Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Dan-adam Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Back to top button