Uncategorized

Matar Hariji Page 11-20 Romantic Hausa Novel

 

__________📝Wannan rana bacci ya gagari Lameer kwana yayi yana tufka da warwara zuciyarsa tana guri biyu kaso tamanin yanaga Hauwah kaso ashirin yana gurin Mubaraka.

Wayewar garin kamar danshi akayita ya shirya tun shidda na safe ya zauna yana kallon tagar da take nuna mishi lkc yana sauke numfashi lkc zuwa lkc yanakai idonsa ga agogo har bakwai ta cika ya miqe ya dauki key din motarsa ya dauki wayoyinsa ya sauko qasan.

A tsakiyar parlourn sukayi clear da matar gdan ta fito daga kitchen dauke da cup a hannunta  ta tsaya turus tana kallonsa cike da tsoro a hankali tace “Lameer yaushe ka dawo?” 

Shafa sumarsa yayi yace “na shigo naji dakinki a kulle da alamun kinyi bacci shiyasa ban tasheki ba ya kike ya baby Fadwah” iska ta furzar cike da godewa Allah don tasan shima ya fada ne saboda ya kare kansa amma baije ba dakinta a bude ya kwana suna sha’aninsu ita da Muneef amma a fili sai tace.

“Ayyah sannu ya hanya”

Yana tafe yake bata amsa har yakai bakin qofar ta tabe baki qasan maqoshi tace “a tafe kamar namijin qwarai tsautsayi auren me dandaqaqqen azzakari” 

Tunaninta baiji me tace ba shikuma yajita sarai saboda Allah yayi masa baiwar jin sauti kamar maciji a zuci kawai zakayi magana ya kasa jinka, ajiyar zuciya yayi ya fita ya shiga motarsa zuciyarsa babu dadi yanaso Allah ya nuna masa ranar da zaiyiwa Mubaraka cin kaca wanda zata daina caba mishi mgn har irin haka amma ya kasa samun wannan damar.

Office dinsa ya fara zuwa ya zauna zuciyarsa cunkushe da tunani damuwar daya kwana da ita ta danne damuwar da Mubaraka take tunanin ta cusa masa, ya kasa hassala komai a gurin aikin sai juya biro da kallon takarda kawai da yakeyi.

Miqewa yayi kamar Wanda aka tsikara ya fara hada takardunsa yana zubawa a jaka wadanda zai bari kuma ya mayar dasu loccar ya dauki kayansa ya fice.

A guje yabar harabar office din nasu ya nufi hanyar da zata kaishi qauyen Alqalawa zuciyarsa cike da zulumi da tunanin wanne irin cin mutunci zai fuskanta yau.

Daga garin Alqalawa zuwa rugar Sambajo tafiyar kilo mitter 6 ce tunda ya isa garin Alqalawa zuciyarsa ke bugawa da qarfi hakan yasashi nufar gidan gonarsa dake kilo mitter 2 da rugar Sambajo yayi parking anan saboda cewar da Arɗo Jibo yayi duk ranar da suka ƙara ganin motarsa sai sunsa anyi masa rotse.

Ya jima a motar yana tunanin ta ina zai fara kafin ya samu ƙwarin gwiwar fitowa ya fara ratsa kalgo da sabara yana kakkarcewa amma burinsa kawai yaje ya qara roqonsu su amince masa da auren diyar tasu saboda baijin zuciyarsa zata iya hqr da Hauwah.

Tafiya yayi sosai a cikin duhun bishiyun da amfanin gona da yayi tsayi sabida ni’imar damuna, 

Yazo giftawa jikin wani lambu ya rinqa jiyo shassheqar kukan mace, da sauri yaja ya tsaya tare da qara baza kunnuwa gabansa yana faduwa saboda jin sautin yake kamar na Jiddoh.

Da hanzarinsa ya fara laluben inda sautin yake fitowa har ya matsi gurin sosai, yadan tsaya cike da faduwar gaba da gaske kunnuwansa basuyi masa qarya ba itance zaune  sanyi da wasu kayan saqi koraye irin nasu na fulani, ta sanya kanta cikin cinyarta tanata gursheqen kuka.

Abinka da farar mace fatarta duk tayi taruwar jini alamun duka akayi Mata ta nade jelar gashinta da akayi Mata kitson doka ta daure ya sauka har qasan mazaunanta.

Matsawa yayi da sauri gabanta ya tsugunna ya sanya hanunsa ya shafa damtsenta da yayi burdin burdin, a mugun tsorace ta dago kanta tare da bude baki zata qwallah qara yayi saurin rufe Mata bakin da bakinsa ya tura harshensa cikin nata yaja ajiyar zuciya me qarfi tare da zama dirshan a qasan ya fara qoqarin janyota jikinsa ta janye da qarfi ta miqe ya ruqo hannuta da sauri yace.

“Tsaya Hauwah saurareni ki fadamin waye ya dakeki haka?” Zama tayi ta qara rushewa da kuka tace “baffa Ardo dasu baffa Laminu harda Hamma Lawal kuma… Kuma ni bansan me nayi musu ba”

Cikin muguwar hasala yace “akanme suka dakeki har suka tara miki jini a jiki haka?” Kukanta ne ya qara qarfi tana girgiza kai yace “stop crying Hauwah ki fadamin meye yasa suka dakeki?” Cikin kuka tace “ni bansanshi ba yazo yace yanason aurena kuma shidin ya kasance Kado ne mu kuma a rugarmu bama bawa Kado aure kuma muma bama auro irinsu….” 

Cikin tsananin tashin hankali da sanyin jiki yace “meye dalilin da yasa baku bawa Kado aure Hauwah idan kuma qaddararku ce Kadon ya zakuyi nidai inasonki kuma zan aureki koda ace rabon da ya qaddaramin sonki zaiyi kisa wlh saina mallakeki Hauwah wayar gari kawai nayi naji inayi miki so irin na bada rai fansa wlh ko duniya zata taru nidai inanan akan bakana zan aureki ko duniya zata qini saboda kece farin cikina…..”

Tunda ya fara mgnr jikinta yake rawa har kawo lkcn daya gama ta zabura ta miqe zata warta a guje shima ya miqe da sauri ya fincikota ya hadata da qirjinsa yace “kada ki sabarwa kanki da tsoro da gudun mijinki kinji yar fillo na, nasani zan fuskanci qalubale ta kowanne bangare akan aurenki amma na shiryawa karbar hakan matsalata kawai danginki su aminta dani wlh idan suka yarda ko a yau sai an daura aurena dake”

___________📝Kama hannunsa tayi ta gasa masa cizo Amma memakon ya saketa saima ya qara matseta yana ajiyar zuciya yace “dadi nakeji idan najiki a jikina.

Daqyar ta kwace ya sake kama hannunta ya fita da ita daga gurin ya nufi jikin wata idaniyar ruwa da ruwa yake bulbulowa ya zaunar da ita saman kujerar dake gurin shima ya zauna a kusa da ita ya zuba Mata ido.

Duk da dama Hauwah batada qiba amma wannan karon tayi rama sosai, numfashi ya sauke  yace “kin rame sosai meye ya kawo hakan?” 

Qasa tayi da kanta tana wasa da yatsun qafarta ya zuba mata ido.

Komai nata burgeshi yakeyi, a hankali ya rinqa janta da hira harta saki jiki dashi suka rinqa hirarsu da dariya sun manta da duk wata damuwa a haka har yamma tayi liqis yace ta tashi ya rakata gda.

Saurin kada masa kai tayi tace “aa kayi zamanka ni zan tafi ni daya” murmushi yayi yace “bazan iya barin ke kadaiba kince anayi miki adumbuli” 

Rufe fuskarta tayi tana dariya shima dariyar yayi yace “haushi naji sosai da wani ya rigani taba dukiyata….” 

Ai kafin ya gama rufe bakinsa ta ranta ana kare ya zuba mata ido yana dariya a ransa yace “zanyi aiki kafin ki nutsu Hauwah”

___________Da sanda ta shiga gdan ta shige dakin Gwaggonta ta fada saman gadon karan dake  dakin tana murmushi ta rungume pillow tanajin wani nishadi na musammam.

“Muhammadu Lameer ta maimaita sunan tare da sake rufe fuskarta da hannunta tana murmushi tace “dan gayu me qamshi muah muah muah bakinsa kamar yasha zuma dadi”🤣🤣

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Novel

Rufe idonta tayi tana qyalqyala dariya tace “komai nasa na yan gayune bari ma na gwada tafiyarsa na gani ko zan iya” 

Miqewa tayi tana wani gyarawa wai zatayi irin tafiyar Lameer, ta jima tana training sannan ta koma ta kwanta ta lumshe idonta tana haskosu wai gasunan a birni ya kaita makarantar bokoko irin wacce yayan gdan sarkun noma sukeyi.

Tashi tayi zaune da sauri tace “to Wai dama shi jikan sarkin nomane amma meyesa yafi su Jamilu da Daheer kyau?” Komawa ta kumayi ta kwanta tana shafa inda yayi Mata kiss tace “bakinsa qamshi ba irin na Madi ba da kullum yake warin daddawa da kuka ko asuwaki bayayi hege me qaton baki kamar wani rami” 

Duk abinda takeyi Gwaggo na tsaye ta bayan taga tana kallonta har saida taga ta gama sannan ta shigo dakin ta zauna tace “ina kikaje kikakai yamma liqis haka Ardo yanata nemanki zakuje gurin Boka Bawa” 

Turo baki gaba tayi tace “nifa bazani gurin wani Boka Bawa ba Kado yacemin shirkace kuma shirka batace kuma wlh yace yana Sona zai kaini burni yasani a makaranta  ya rinqa bani shayi da burodi…..”

Sallalami Gwaggo ta fara tace “nikam naga boni da  dannan ni Hari anya wa’e Kado ba maye bane” sake turo baki gaba tayi tace “aradun Allah ba maye bane shifa kullum qamshi yakeyi kinga ma har turare yabani sannan yace idan yazo gobe zai tahomin da kayan kwalliya na yan burni harda wannan abin nan na wanke gashi irin nasu na aljanu da muke gani a majigi a Alqalawa idan munje tallan nono bakiji wani abubama Gwaggo da zan taho yace zai rakoni nace aa shine yace saiya rakoni tunda nace anayimin adumbuli kuma yace haushi yaji da wani ya rigashi tabawa.

___________📝Wata uwar gwarza da Gwaggo tayi Mata a baki itace tasata tsuke bakinta ta dauki sandar korar shanu ta shimfida Mata a bayanta tana sababi ita kuma ta shige qarqashin gado ta buya yanda Gwaggo take fada tana zage zage yayi mugun firgita Jiddoh ta sake shiga taitayinta.

Daqyar Inna jumme ta qwaceta ta fice tana kuka ta koma bayan gida ita bata taba ganin aibin abinda ta fadaba kawai daga bada lbr sai a rufeta da mazga itakam taga ta kanta.

Daganan data gama zamanta ta gaji dandali ta nufa take sukayi tsalle tsallensu kowacce saurayinta ya kirata aka fara hirar masoya itakam da Madi ya aiko Kira cuccuwa dan aiken zagi tayi kafin ya iso gurin tabi zugar qwailayen yan matan sunbar dandalin batama nufi rugarsu ba gidan yayarta laminde ta nufa.

Mamaki ya cika laminde na ganin qanwar tata kasancewar rabonta da zuwa gidan tun kafin a fara rikicin aurenta da Madi.

Zama tayi tana bata lbrn Kado itanma fada ta rufeta dashi wai me zatayi da Kado matsiyaci ma irin na birni babu shanu babu gona sai iskanci da auri saki.

Nanfa rigima ta harqe Jiddoh babu hqr an zagar Mata Kado har fadi takeyi kuma idan Kado ya aureta kada wanda yaje gidanta tunda basa sonshi.

Tana tafe tana fada tana sababi har take gida ta shige dakin Gwaggonta taja bargo ta rufe jikinta sallar ma cewa tayi bazatayi ba tunda kowa ya tsani Kadonta 🤣

Washegari Gwaggonta batajin dadi baffanta dole ya qyaleta ta dauki tallan nono ta nufi garin Alqalawa tun kafin ta isa inuwar da suke zama ta hangeshi tsaye yana danne danne da wayarsa cikin farin uniform dinsa da yayi masifar amsar jikinsa.

Tsayawa itama tayi tana qare masa kallo har ya iso gabanta bata saniba sai ji tayi ya sauke qwaryan nonon kanta ya ajiye ya karbi bokitin hannunta yace.

“Kince bakya sona baki iya aurena amma sai kallona kikeyi why?” Turo baki tayi tace “kuma dan naga kayi kyau na kalleka shine zaka zageni da arnanci to ai nima inajin arnancin”

Murmushi yayi yace “Allah ya baki hqr fulani na ni kam ban isa ba na daina yau kinsan me nakeson ki koyamin?”

Kada masa kai tayi ya shafa siririn sajensa yace “fullanci nakeso ki koyamin naga rugarku duka bakwa Hausa kada naje cikin surukaina na zama bare” 

Dariya tayi tace “yore lale ananin ba ananin ba ananin yore laye ananin yore…”dariyarsa ce ta sanyata yin shiru ta zubawa dan qaramin bakinsa ido har ya tsuke ta sauke ajiyar zuciya ta nemi guri ta zauna tace.

“Jiyama saida Gwaggo ta bugeni saboda Ina bata labarinka nikam dai inason nayita kallonka kanayimin kyau amma su sunce Basu sonka kawai oye ka tafi ka auri kaduwa yar uwarka kaga jiyama saida Baffa yace zamuje gurin Boka Bawa”

Kallonta yayi tare da motsa bakinsa yace “waye Boka Bawa ne?” Wasa ta farayi da yatsun qafarsa daya miqe tace “shi gani yake har hanji indai yace maka zaka mutu to mutuwa zakayi wai sunce iskokine dani shiyasa nakeqin Madi ni kuma iskanci ne banaso ranan nan fah cemin yayi my zagaya duhun dawa tasamin bindira bayan ance wai wai bindira qatuwace Indon Moddibo  Dalha tunda akasa Mata bindira kawai sai tayi ciki aka rinqa yawo da ita turba turba ana nunata anayi Mata waqa wai ansa Mata bindara tayi cikin shege qarshe sai barin Rugarmu tayi ta koma birni”

Yanda take zaro masa zancen ne yasashi fahimtar inda zancen ya dosa yayi murmushi yace “kuma ke tsoronta kikeji Toni yanzu in munyi aure ya zakiyi dani nima inason kiyi ciki ai” 

Harararsa tayi ta miqe tana qunquni ya miqe ya riqe faffadan hips dinta dabai gama fashewa ba yace “duk ranar dana zama mijinki zan nuna miki bindira ta kinason gani?” 

Saurin daga kai tayi ta kalleshi tace “au kaima kanada ita?” Murmushi yayi ya shafa qasan mararsa yace “inada ita Amma ni tawa bs kamar ta kowa bace batada qarfi kamar yanda ake fada miki ba”…………..

Karanta Littafin : Raɗaɗi By Sa’adatu Waziri Gombe

_________📝Tabe baki tayi ta dauki qwaryarta tace “nikam Baffana da yan gdanmu ba yar iska bane basuda bindira ni kadama ka qara cewa kasanni banasonka kuma……” 

Rufe mata baki yayi yace “ni kuma inasonki zan aureki idanma bakiso bazanyi miki ba kawai kallonki zantayi kiyita sani nishadi ko?” Daqa masa kai tayi tace “amma ka yarda zaka nunamin din ko?” Murmushi yayi yace “har wasa zakiyi da ita ma” 

Dariya tayi ta fara juye masa nonon saida ta gama dure masa a jarka sannan ta qulle masa furar a leda tasa masa a but sannan ta dawo ta tsaya kusa dashi tace.

 “Kayyy wannan mutum oye kwai shirgege kalla fah a saitin qugunka nike” matsawa yayi yace “aa kalla sosai a saitin qirjina dai ko? Murmushi tayi tace “yawwa Ina abuna da kace zaka siyamin?”

Jan hanunta yayi ya zagaya ya sanyata a mota shima ya shiga ya zauna yace “na siyo miki amma ban gaji da ganinki ba so nake nayi miki wata tambaya inaso cikin satinnan zan turo iyayena su nemamin auranki, a yau nakeso idan na koma gda na sanar da mahaifina inason qara aure amma idan munyi aure Lagos zaa kaimin ke fah”

Wata uwar harara ta galla masa tace “tabdi kaje ka saidani kwarankwatsa dubu bazanje ko inaba”

Kallonta yakeyi da mamaki shikam tunda yake bai taba ganin sakaryar yarinya irin Jiddoh ba bude mata qofa yayi yace “naji jeki” wata leda ya dauko ya miqo mata yace.

“Ga alqawarin da nayi miki jiya ki kula da kanki zanje Lagos May be zanyi sati daya kafin na dawo kome ke akwai zanji gurin Alhajinmu.

Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro yan dari biyar bayar da baisan adadinsu ba ya kama hannunta yasa mata tare da kissing dinta yace “ki bawa Gwaggo Koda yake muje kawai inganta da kaina banson tallan nan naki”

A fari taso qin yarda suje wuronsu dashi amma yanda yayi kicin² yasata dole ta yarda sujedin bisa sharadin saidai su tafi a qafa haka kuwa akayi suna tafe yana janta da hira yana dauke da qorain nonon nata har suka iso bayan gdan cikin saa kuwa sukaci karo da Gwaggo ta debo ruwa a rafi ta tsaya tana kallonsu cike da tsoro hadi da kunya irin tasu ta fulani ta saki bokitin ta juya da sauri.

Binta yayi shima yana fadin “Gwaggo ki tsaya bafa wani abu bane don Allah ki tsaya ki saurareni”a wata kwana suka hadu da Inna Jumme ta tsaya itama ta tsaya tasan halin abokiyar zaman nata duk da Jiddoh ba ita kadai bace amma itace mace ta fari to a al’adarsu ta fulani bazata taba tsayawa tayi mgn da duk wanda yace yanason Jiddoh ba balle Lameer da dama ba qaunarsa sukeyi ba.

Inna Jumme ce ta tareshi tace “oye miye yake hwaruwa kaiko bazaka samawa kanka lfy ka fita harkar diyarnan ba tunda sunce bazasu baka ba” 

Shafa sumarsa yayi ya durqushe yace “Wlh nima nayi qoqarin hakan amma na kasa Inna nabawa Hauwah kudi ta kula da kanta sannan na bata ta kawo muku a daina dora mata tallan nono saboda bata gari Inna Hauwah tanada garin jiki kuma halittarta tana daukan hankalin maza komai zai iya faruwa ta fadamin komai da dalilin da yasa batason aurenta da Mahadi don Allah kada kuyi Mata dole kada kuja da ikon Allah wlh zan aureta kuma zan riqe muku ita amana fiye da abinda kuke tsammani”

Kallonshi Inna Jumme takeyi cikin tausayawa tanaji a ranta dama Ladingon ta ce ta samu wannan dan gayun da kota tsiya² sai anyi auren tace.

“amma ta yaya zaayi kace ta daina tallan nono bayan dashi muka saba?” 

Qasa ya sakeyi da kansa yace “eh nasani amma nasan kunayi ne domin ku samu kudin cefane to ga dubu hamsin nan ku rinqa cefane har na dawo sannan a fadawa Baffa yayi hqr yau talata to rana i ta yau magabatana zasuzo don Allah ya taimakeni ya amsheni a matsayin zabin ubangiji”………………….

________📝Cikin tausayawa Inna Jumme tayi masa gdy ta nufi hanyar da zata isar da ita gda tana zuwa ta tarar da Jiddoh tsaye tana leqensu ta cafketa ta.

Juyowa  tayi cikin muguwar kidima tana ganin Inna Jumme ta sauke ajiyar zuciya tace “inna Kado tausayi yake bani wlh kamar nayi masa kuka yau har qwallah naga yanayi dazun fah”

Kamata tayi tare da daukar ledar kayan suka shiga suka bajeshi a tsakar daki Jiddoh ta rinqa bin kayan da kallo kayane bana wasa ba ya hado Mata harda dogayen ruguna turaruka hijjabai da takalma sannan kayan kwalliya hatda relacxer ta manya guda biyu.

Wani tsalle tayi tace “Aradun Allah wannan shi zan rinqa shafawa nima jikina ya koma irin nasa ya daina kaushi da kirci Inna Jumme jikinsa fa shi har wani danshi yakeyi kuma duk jikinsa gashine irin na yan majigi”

Daquwa Jumme tayi mata tace “ke ar wannan ai saidai abawa Gwaggonki amma yayi miki yawa a man shafawa irin nasa farin nan nefa ke kuwa ai farace” 

Turo baki gaba tayi tace “aa ne yaseen shi meye yasa baiyi farin ba nidai kibani abuna na bude na gani” mangari takai mata tace “uwariyonki ko sille baki tabawa cikin kayan nan nasan baffanki bazai bari ki karba ba ki bari mu boye sai mu nunawa Gwaggnki  kudin kinsan su bakinsu daya da Ardo fah”

Shiru tayi kamar me nazari kafin ta kunto kudin daya bata kel kel dasu yan dari bibbiyu har na dubu ashirin ta zaro ido tace “Inna jaka dari ce mun shiga uku siyemu zaiyi fah”

Karba Inna tayi ta qirga jikinta na rawa tace “mun boni Jiddoh jaka dari uku da hamsin ya bamu Ina zamu kaisu?….”

“Ku kawo nan sukaji an ambata tare da bude labulen Ardo ya shigo a fusace yace “wato na lura kema kina daya daga cikin masu budewa yarinyar nan ido da kudi ko to bari kiji Jumme aradun Allah ko Moddibo ubana daya kawoni dunniya zan iya dagawa sanda akan wannan shegen yaron me idon agwagwa”

Wartar kudin yayi da qarfi a hannun Inna ya fita da sauri duka suka miqe suka bisa ya nufi madafi da aka balbala wutar kashin shanu ana girki ya cusa kudin.

Inna Jumme tace “Ardo sheden ka qona da wuta oye Ardo kanada hankali kuwa jaka dari uku da hamsin fah Ardo”

Itakuwa Jiddoh durqushewa tayi a gurin ta rusa ihu tace “na shiga ukuna Baffa ka qona masa kudinsa wayyohh Kado dama ban karbar maka kudinka ba Baffa me zance masa….” 

Sanda ya daga zai maka mata Gwaggo ta tareshi tace “oye  Ardo diyagga da gaskiyarta wannan qiyayya taka da yaron nan Lameeru tayi yawa koma meye ai bai kamata ka huce akan kudi ba yanzu idan yazo yace a biyashi me zaka bashi”

Hayayyaqo Mata yayi yace “ya kada galkena ya tafi dasu ai dama ba yau suka saba kashe mana shanu da hada baki da barayin burtali su kada mana shanu ba aradun Allah Hari da Jumme kowacce ta sake sakan baki akan mgnr makirin yaron nan jikan sarkin noma qur’anin Allah saita tafi gdan tsohonta”

Yana fadin haka ya juya ya shiga dakin ya dauko kayan kwalliyar ya fita dasu Jiddoh ta bishi da sauri cikin tashin hankali tana kuka tana fadin “ayyah Baffa kada ka rabani da kayan kwalliya na nima so yake nayi kyau na zama yar gayu….” 

Bai tsaya sauraronta ba ya zubasu a wata tsohuwar rijiya ta qarasa da gudu ta leqa rijiyar ko hango batayi saijin zubarsu ciki tayi ta zube a gurin ta dora hannunta akanta ta runtuma wani ihu tare da fizgar ledar ta rungume a qirjinta shi kuwa Ardo ya angijeta ya wucce abinsa ya barta rungume da leda tana kuka tana kirar “shikenan kayan kwalliya na sun tafi rijiya Kado yaushe zaka dawo ka kawomin wasu………………

Download : Walijam Complete Novel

________📝Tajima kafin taga zaman bazai kaitaba ta tashi ta nufi gidan tana haɗa hanya ta shiga ɗakin gwaggonta ta kwanta tanata sauke ajiyar zuciya zazzabi me zafi ya rufeta zuciyarta cike da tunanin Lameer da maganganunsa da suketa yimata yawo a ƙwanya.

___________Kada ya shiga gari kai tsaye gdansu yanufa yayi saa kuw ya tarar da Alh a falon ƙasa yana hutawa ya zauna suka gaisa dashi sannan suka gaisa da hajiya yayi shiru gabansa na faduwa yana tunanin ta inda zai fara.

Alh ne ya katseshi da cewa “Magaji meye yake faruwa ne kamar bakinka akwai magana ince dai ba matsala bace a gdan naka?”

Girgiza kai yayi yace “ba wannan matsalar bace Alh don allah alfarma nake nema a gurinka”

Da mamaki Alh ya dubesa yace “tame babana?” shafa sumarsa yayi yanason faɗar sirrin ransa yanajin tsoron tujarar hajiya.

Yanda yake kallonta ne yasa alh cewa hajiya abamu guri yaron nan tsoron masifarki yakeji” taɓe baki tayi tace “bashida gsky ne shiyasa yake tsoron faɗa a gabana” tana faɗin haka ta miƙe tayi shigewarta ɗakinta shikuma alh ya zubawa Lameer ido yana nazarin damuwa kwance saman fuskarsa yace “kai nake sauraro magaji Allahu yasa dai lfy”

Sumarsa ya shafa yace “lfy lau Alh dama inason na sanar dakai ne….” sai kuma yayi shiru bakinsa ya sarƙe murmushi Alh yayi yace “kamar ba namiji ba  kana mgn kana fargaba ita faɗuwar gaba asarar namiji ce ai Lameer ka fito kayi mgn darect mana”

Cikin in…ina yace “in…inason zanyi au…r…e ne dama…” zuba masa ido uban yayi cikin naƙaltar yanayi da mamaki yace “aure wanne irin aure Lameer kana zaune ƙalau zaka tashi hankalinka ƙanƙaninka dakai zaka tarawa kanka iyali meye damuwarka da matarka ta gda?”

“Bashida wata damuwa da ita saima ita da yake tatawa rashin mutumci kullum cikin ƙorafi take alh kai shaida ne basa wata guda baayi musu sulhu ba wani sabon tashin hankali ma watnnin nan daya sawo kai kaga yaron nan sai suyi watada watanni bai sauke mata haƙƙin aureba kuma wlh ba yau aka fara ba dama duk gdan da kaji an fiya samun saɓani to ɗaya yayi watsi da haƙƙin ɗaya, yo bandama iskancinsa Alh da tsabar ya raina mutane Lameer har nawa yake da zaice zai auri mace sama da ɗaya kuma bayqn ɗayar bata ƙoshi ba, eh mana bata ƙoshi ba mana Alh ci da sha ai duk mace tana samu a gdan iyayenta kwanciyar aure itace aure ai”

Tuda ta fara faɗan jikin Lameer yayi matuƙar sanyi baisan sanda hawaye ya fara fita a idanunsa ba tsoronsa Allah tsoronsa suce zasu hanashi auren Hauwah ya tabbatar rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen masifa da tashin hankali saboda yanzu hakan jinsa yake kamar ransa hade yake dana Hauwah.

Muryar Alh ce ta katseshi da cewa “wai hakane Magaji?” ɗagowa yayi da manyan idanunsa da suka kaɗa sukayi jah cikin sanyin jiki yace “eh hakane Alh amma don Allah kada ka yankemin ƙauna da samun dawwamammen farin ciki Alh Hauwah yarinya ce ƙarama batasan komai ba kafin lkcn da zata fara buƙatata insha Allahu nasamu lfy tunda ina neman magani”

_Kuji fa wata gwari_

Ajiyar numfashi Alh yayi yace “Wannan falsafar taka akan qarya kayita ka nemi maganin kafin ka buƙaci ƙara aure shi aure meye yakesa ayisa ne Lameer anya ma kuwa kasan sharruɗan aurevoir? To bari kaji wani abu Magaji ko matarka ta gida wato Mubaraka indai kayi wata shidda baka kusanceta ba warware aurenku ya kamata ayi saboda hasashen masana halayyar ƴa mace na duniya ya tabbatar mace lafiyayiya watanni uku take iya jure rashin namiji a tare da ita wannan dalilin yasa kaga addini ma ya sassauta musu yace suyi iddah watanni uku idan rabuwar aure ta gifta”

Ɗagowa yayi yace “amma Alh…” katseshi yayi da cewa kaje ka Lameer banson shirme fah” hawayene ya zubo a idanunsa sharrrr ya miƙe a matuƙar sanyaye ya nufi ƙofar ya buɗeya fita ya shiga motarsa ya zauna tare da buga kansa da sitiyari yace “innanillahi wa innah ilaihir raji’un”

Daƙyar ya iya yima motar key ya nufi gdansa cikin wani yanayi dashi kaɗai yasan ya yakeji a zuciyarsa yana shiga ya buɗe motar ya fita ya buɗe ƙofar falon ya shiga daƙyar ya iya sallama ya hangi Mubaraka zaune da apple a hannunta Fadwah nata wasanta ta nufoshi da tafiyarta da batayi ƙwari ba ta riƙe masa ƙafafu ya ɗagota a hankali yana amsa sannu da zuwan da Mubaraka takeyi masa ya nufi sama da ƴartasu a hannunsa ya sauketa a saman gado ya dauko choculate ya bata ya shiga bathroom  ya sakarwa kansa ruwa sannan ya dawo ya zauna a ƙasa dirshen yana kallon yarinyar jikinsa yana rawa saboda a rayuwarsa bai iyasa abu a ransa ba.

Tunda yake bai taɓajin ciwo da takaicin rashin mazantaka ba sai yau wannan wacce irin masifa ce, shidai yasan yace zai hƙr da Hauwah ma zance ne bazai iyaba yanzu meye abinda ya dace yayi?……………..

________📝Daqyar ya tashi ya haura gadon ya kwanta yana tufka da warwara zuciyarsa cunkushe da abubuwa kala².

Wannan dare shidai bai rintsa ba asubar fari yayiwa gdansu tsinke mahaifinsa yana dawowa daga masallaci ya tarar dashi zaune tare da maigadi ya tashi da sauri ta tareshi.

Shikam Alh saida gabansa ya fadi ya zubawa dan nasa ido yana ayyana wanne irin abune wannan me yake damunsa haka da zai baro gdansa cikin duhun asubar nan.

Shiga gdan sukayi yajashi har dakinsa yace “babana meye ya fito dakai da sanyin safiyar nan” shafa kansa yayi ya durqushe yace “Alh na kasa jurewa jiya ban iya rintsawa ba don Allah ka taimakeni ka amince da aurena da Hauwah wlh zuciyata ta kamu da qaunar yarinyar fiye da inda kake tunani Alh komai zai iya faruwa dani idan ka hanani auren Hauwa”

Mamaki ne ya cika zuciyar Alh Lameer dinsa me kunya wai shine yake roqonsa ya amince yayi aure to yanzu idan ya amince da wannan aure me yayi kenan? Da ace baisan matsalar Dan nasa ba dasai ya shige masa gaba yayi aure amma yasan matsalarsa.

Towai meyema ya dauki hankalinsa haka har ya damu da auren? Katseshi yayi da cewa “kace wani abu don Allah Alh wlh aure suke shirin yimata kuma itama ni takeso zata zauna dani a duk yanda nake nasan bazan samu matsala da itaba tunda yarinya ce wlh nayi maka alqawarin daganan hsr bangon duniya zanci gaba da neman magani kuma duk yanda zanyi naga na sauke haqqinsu duka zanyi insha Allah”

 

Kada kai yayi yace “naji magaji kaje zanyi tunani akai yauwa ya maganar tafiyarka Lagos?” Numfashi ya sauke yace “sunyi posting dina tun sati daya daya wucce wannan mgnr ta hanani tafiya nafiso a gama komai kafin na tafi inyaso tunda Mubaraka tana aiki idan aka daura sai kawai na wucce da Hauwah can”

Shiru Alh yayi kuma fa a mgnr dannasa akwai abin dubawa duk lalacewar namiji mace kusa dashi garkuwa ce ko banza sayi hira yace bani kaza ta bashi” ajiyar numfashi Alh yayi yace “kaje idan nayi nazari zan nemeka”

Gdy yayi tare da miqewa ya fito sukayi kicibis ds Hajiya itama ta fito saida gabansa yayi wata muguwar faduwa ya tsugunna yace “ina kwana Hajiya” tabe baki tayi tace “lfy meye ya kawoka gidannan da asubar nan?” 

Shafa kansa yayi yace “nazo naga Alh ne” tsaki tayi tace “au dama mgnr nan tun jiya baa barta ba to wlh tallahi kaji na rantse wannan auren bazaayishi ba indai nice na haifeka bazan yarda da wannan kwadon hatsin barar ba ta gdanma baka iya da itaba balle ka kawo wata” 

A hassale ya kalleta yace “wai waye yace miki bana iyawada da iyalina ne meye na ragesu dashi ci ko sha ko sutura? Me takeyiwa kanta a rayuwarta to nidai don Allah ki cire bakinki a mgnr aurena Hajiya ni namiji ne kuma tsayayye a gdansa sannan nakai lkcn da yakamata ace nasan daidai nasan akasin daidai”

Tafa hannu tayi cikin salati tace “ehhh lallai Lameer kakai harma ka isa wato ni kake fadawa cewa kai namiji ne ko tabdi lallai da aiki a gabana dannan tunda nake dakai baka taba tsallake mgnta ba sai yau saboda kaso qara aure har kake yimin tsawa”

Kallonta yayi yana mamaki wai yayi mata tsawa shikam ya rasa wacce irin uwa Allah hadashi da ita da kullum burinta taga kasawarsa tayi masa gori akai.

Miqewa yayi ya fice tanata sababin bala’inta ya nufi gdan wan babansa don yasan tunda Hajiya taqi mgnr idan bata sama ya biyowa Alh ba to baza ayiba.

Bai boye masa komai ba ya zayyane masa harda takun saqar da suke fuskanta da dangin Hauwah Mal Yahaya yayi qwafa yace “aikuwa ka taro March bakada fili Lameer shi aure nufin Allah ne amma fa zaakai ruwa rana saboda Rugar Sambajo munsansu sanin gaske tun duniya na kwance basa bawa Kado aure ni kaina na nemi aure a rugar amma daga qarshe cin mutunci ya biyo baya da qage hadi da qazafi sufa sun tsani Bahaushe musamman wanda ya hada alaqa da garin Alqalawa Lameer abubuwa da yawa sukaja wannan gabar fah saboda haka indai zakaji shawara ka janyewa auren yar gdan Ardo Jibbo saboda tujararren bafulatani ne fiye da kwatance shi duk cikin yayan Moddibo Durange shine baudadde har ya baudar da yan uwansa wlh ni kaina tsoronsu nakeji sau uku suna fasamin glass din motata saboda wani dalili nasu mara kan gado……………

Back to top button