Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 8 Complete Novel

*ASM Bk2008*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

……..Satin da Fanan ta tafi su Fatuu suka koma Makaranta sun cigaba da zuwa ita da Haulat har lokacin tana cikin yanayin damuwa ga zuciyarta tay ta raya mata Ya Handsome na can suna shan soyayyarsu da Fanan, Haulat na lura da yanayinta hakan yasa bata gajiya da bata hakuri da kuma k’arfafa mata guiwar ta cireshi daga ranta, zubar da hawaye ya zamar mata jiki Fatuu mai zafi ta dawo Fatuu mai sanyi kowa ya lura da canjawar da tayi yan Class d’insu da Malamai suna ta tambayarta game da hakan saidae tace masu kawae bata lafiya ne, haka Haulat ma duk wanda ya tambayeta sai tace bata lafiya matsalar Aljanunta ne da yake dama ansan tana dasu ba kamar wadanda sukai junior tare, ko sauran juniors ma na section d’insu sun san SP d’insu tayi sanyi, a satin sau d’aya taje gidan Hajiya ranar Juma’a ta gaishe da ita sanin Haisam bai nan, suna d’an yin fira a Falon Hajiya ke cewa “wai ni kam Fateema ko har yanzu jikinne duk kinyi sanyi ba kaman da ba” saida gabanta ya fad’i jin haka cikin rawar murya tace mata jikinne bai mata dad’i kaman ba nata ba, hajiya tace “Allah ya baki lpy ya rabaki da ciwon gaba d’aya ki huta in sha Allahu zaki samu lpy ki dawo kaman yadda kike amman kasancewarki haka ba dad’i mutum mai kazar kazar duk kin dawo sukuku” d’an Murmushi tay batace komae ba dai, bayan wani lokaci tay mata sallama ta tafi, sam Hajiya bata kawo komae game da halin da Fatuu take ciki ba sanin tana da Aljanun da gaske sannan lokacin da suka dawo daga Ajiwa ba wanda yay tunanin Fatun taga Fanan kafin ta shiga gida don koda Hajiya ta tambayi Fanan sun ga juna ce mata tay a’a ta shiga gida kuma bayan sunje sun dawo suka ce sun iske bata lafiya. Ranar Monday lokacin Satin Fanan d’aya da tafiya misalin karfe bakwae da rabi Fatuu ta fito jikinta sanye da Uniform d’in boko sun sha guga bayanta goye da k’atuwar School bag d’inta tsaf tsaf da ita tana shirin hawa hanya ta tafi galleliyar Mota dark ash ta tsaya a gabanta har saida ta dawo baya da sauri, bin Motar tay da kallo lokaci guda k’irjinta ya fara bugu da k’arfi da k’arfi don ko ba’a fad’a ba tasan waye a ciki, Slowly glass d’in kopar ya fara sauka k’asa nan take tay arba da haisam cikin shirin zuwa aiki idonshi na a gaban Motar bai kalleta ba shiru tay tana bin gefen fuskarshi da gashi ke kwance luff da kallo can ya juyo a hankali ya kalleta suka had’a ido, bin shi tay da ido kawae shima kuma haka ganin kallon da yake mata ne yasa a sanyaye tace “Ina kwana” jinjina mata kai yay ta sake cewa “an dawo lpy?” fuska a sake yace mata lafiya, kallon juna suka ci gaba da yi ganin bata iya jure ma kallon nashi yasa ta sunkuyar da idonta k’asa can taji yace “in rok’e kine ki shigo?” d’an d’agowa tay tai mashi wani kallon k’asan ido acikin zuciyarta ta ayyana sai kace ni na kirashi ni dama ka tafi…..”

“Baki kirani ba ko” bata k’arasa ba taji ya fad’i haka, a firgice ta idasa d’agowa ta zaro ido cike da Al’ajabi jin abunda yace sai kace mai jin zancen zuci duk tay kalar rashin gaskia ta girgiza mashi kai alamar a’a kafin ta maida kan k’asa,

“Zaraah” yarrr taji wani abu ya tsarga mata tun daga kan babban yatsanta har zuwa cikin kanta, kasa d’agowa tay ta kalleshi don komae zai iya faruwa a wannan lokacin inta had’a ido dashi,

“Ki shiga Mota kina sani ina late in kuma baki son shiga ne let me know sai in tafi” a hankali ta daure ta d’ago ta d’an kalleshi kafin ta kawar da idon da sauri ta nufi other side d’in Motar ta bud’e ta shiga,tana shiga ta juyar da kanta tana kallon gefe duk yana kallonta ta Mirror bai dai tanka ta ba yaja Motar suka tafi, daidai lungun gidansu Haulat ya tsaya ta bud’e Motar ta fita ya bita da kallo,lokacin data shiga d’akinsu Haulatun tana kallon fuskarta ta tambayeta lafiya kaman zatai kuka tace “Ya Handsome ne…” sai kuma tay shiru, a d’an rud’e Haulat tace “miya faru dashi?” hannu tasa tana share kwallan da suka gangaro mata kafin tace “ya dawo yanzun nan ya ganni a kopar gida ya d’aukko ni yana waje” a k’agare tace “to wani abu ya faru ne” girgiza mata kai tay tace “ni banson ganinshi ne haulatu zafi kirjinta ke yi inji kaman in fad’a mashi halin da nike ciki” dafata Haulat tay ta shiga bata hakuri tana karfafa mata guiwa, koda suka fito kafin su isa wurin Motar cigaba da lallashinta haulat tay akan ta daure karta fad’i mashi don ba abunda zai mata saidai ya bata hakuri gwara tay hakuri komae zai wuce ita dai kai kawae ta daga mata, bayan sun shiga Motar gaidashi Haulat tay ya amsa mata yana k’ok’arin jan Motar bayan yaja sun fara tafiya tace “Ya haisam ya Aunty Fanan?” fuska a sake cikin cool voice d’inshi yace “ta koma skul tace a gaidaku” da yar fara’a tace “muna amsawa” a hankali ya d’an juya side d’in Fatuu suka had’a ido duk ta kame kanta da sauri ta juyar da kanta gefe ita kanta tasan bata kyauta ba da bata tambayi Fanan ba, yana aje su a Makarantar ta d’an juya tace mashi an gode ba tare data jira amsawarshi ba ta bud’e kopar tay ficewarta lokacin Haulat bata k’arasa fita ba Haisam ya kira sunanta ta tsaya kud’i ya mik’a mata tasa hannu biyu ta amsa tay mashi godiya ya jinjina mata kai, bayan ta idasa fita yaja Motar ya tafi, akan hanyarsu ta zuwa Class ne Haulat ke k’ara lallashinta akan ta daure ta cije taci gaba da yi ma Ya Haisam kaman da duk da tasan abu ne mai wuya amman dai ta rink’a d’an kamantawa gudun kada shi kuma yaga kaman ta rainashi tana wulak’antaci tunda ba haka suka saba ba, idanunta cike tabb da kwalla tace ma Haulat “baki san ya nike ji bane Haulat wllh shiga Motar ma ba k’aramin daurewa nay ba ji nake kaman in rusa ihu saboda takaici inna tuna na rasa shi, auranshi zay da wata….” bata k’arasa ba tasa kuka haulat ta shiga lallashinta tana Fad’in ta Fahimceta, haka Haisam ya cigaba da kaisu Makarantar duk da Fatuu taso ta rink’a zillewa Haulat ta nuna mata bai dace ba tunda shi ya saba kai su tsawon shekaru ba tare daya nuna gajiyawa ba bai kamata suyi mashi haka ba,dole ta Hakuri ita kanta wani abun ba don tana so ba take mashi don Haisam yafi karfin wulak’antawa a wurinta ita ba butulu bace tasan Haisam shi ya mayar da ita cikakkar Mutum, akwae watarana bayan ya aje su a Makarantar har Fatuu zata bud’e Motar ta fita yace ta tsaya jin hakan yasa Haulat ta bud’e kopar ta fita bayan tay mashi godiya kaman ko yaushe, shiru sukae shi yana kallonta ita kuma ta sunnar da kai can taji yace “Zaraah” amsa mashi tay ba tare data kalleshi ba yaci gaba “har yanzu baki lpy ne?” shiru tay tana d’an mommotsa baki har saida yace ba magana yake mata bane sannan tace mashi ta samu sauki yace “then why are u acting strangely?” shiru ta d’an yi sai kuma tace “kawae jikina ne banjin dad’inshi har yanzu” jin baice komae yasa ta kalleshi suka had’a Ido kasa janye idon tay can yace “kina bukatar zuwa hospital?” da sauri ta girgiza kai tace tana shan magani, gyad’a kai yay yace taje da sauri ta bud’e Motar ta fita yaja ya tafi, bayan taje wurin Haulat sun nufi ajine jin tayi shiru yasa Haulat tambayarta lpy dae ko kaman bazata ce komae ba sai kuma ta fad’i mata abunda ya tambayeta tace ta kyauta da bata fad’i mashi ba amman ta daure ta d’an rink’a sakewa kar watarana a samu matsala tace mata to kawae, tun daga wannan ranar Haisam bai k’ara tambayarta ba game da canzawar da tayi sannan shi bai canza mata ba daga abubuwan daya saba yi mata.

 

Bayan Wata Biyu,

 

Lanar lahadi da rana Fatuu ta dawo daga islamiyya lokacin gwaggo bata nan aikin rana take amman da wuri ta tafi saboda zata biya wata unguwa, d’akinta ta shiga ta aje jakarta wurin da take ajewa ta nufi gado ta cire hijab d’inta ta aje tana niyyar juyawa ta nufi Kitchen don ta zubo abinci idonta ya sauka kan wani abu dake sakin k’yalk’yali a gefen hijab d’inta da ta d’aura saman gadon, tsayawa tay idonta akan abun ta koma gaban gadon sai lokacin ta lura da envelope ce, a hankali ta kai hannu ta d’aukko tana k’are mata kallo ba k’aramin had’uwa tay ba sai walwali ke tashi gwanin burgewa kaman zata bud’e sai kuma ta juya bayanta idonta ya sauka akan wani rubutu dake daga can gefe guda shima yana ta sakin kyalli anyi shi da italic style, k’ura ido tay tana karantawa kamar haka _HAIFAN 2023_ kasa gane abunda yake nufi tay tanata k’ara maimaitawa can dae ta bud’e cikin envelope d’in ta fiddo da wata takardar mai kyau da salk’i dake linke ta warwareta ta fara karanta abunda ke jiki wanda katin gayyatar daurin Aure ne na Families d’in Sen. Alee Adamu Zakee da kuma Dr. Mohammad Abraham da za’a yi ma y’ay’ansu wato _ENGR. HAISAM ALEE ADAMU ZAKEE & DR.FANAN MOHAMMED ABRAHAM_ wanda za’ayi a karshen watan da ake ciki wato nan da sati ukku masu zuwa kenan don satin farko ake za’a shiga na biyu, a Central Mosque dake Abuja,mutuwar tsaye tay bayan ta gama karantawa ta sake maimaitawa har saida ta tabbatar ma kanta lalle Ya Handsome ne nan da nan hannunta ya fara rawa cike da Al’ajabi tasa tafin hannunta guda ta rufe bakinta, yanzu da gaske dae Ya Handsome aure zaiyi ya barta, wani irin kuka cikinta ya fara yi da sauri ta wurga IV d’in kan gado ta nufi hanyar waje a dudduk’e take tafiyar saboda k’ullewar da cikinta yay Allah dae ya taimaka ta k’arasa toilet d’in ba tare da abunda take ji ya zubo mata ba,tsawon lokaci ta d’auka a ciki kafin ta fito a galabaice duk tayi sharkaf da ruwa data sakarwa kanta ta nufi d’aki hannunta d’aya dafe da cikinta,tana shiga ta isa kan gado ta fad’a tana nishi da karfi da karfi, wai ance in tashin hankali yay tsanani kuka kasa yinshi ake to hakan ce ta faru da Fatuu sam ta kasa yin kuka sai zare idanu kawae take ga wata kerma da jikinta ke yi kaman wadda sanyi ya kama,duk da uwar yunwar dake cinta ta kasa tashi taje ta zubo abincin don a halin da take ciki bata wani Abinci take bama ko ta zubo ma ba iya ci zatai ba tana kwancen akai Azahar amman ta kasa mik’ewa taje tayi sallar sai bin envelope d’in dake gabanta take da ido zuciyarta na wani irin bugu mara dad’i.

 

Bayan sallar La’asar Haisam na Masallaci Abbas ya kirashi yace gashi a part d’inshi yace mashi yana zuwa,bada jimawa ba ya dawo ya zauna kan L-shape Abbas kuma ya zaune kan armchair, gaba d’ayansu suka d’an kishingida kan kujerun da suke suka shiga tattaunawa kan bikin Haisam din Abbas yace “dazun munyi Magana da Amaryar taka kan program d’in da tace ta fad’a maka zasu yi a can saboda friends d’inta da bazasu samu zuwa Abuja d’in ba, wai Indian Night zasu yi, kenan kaga dole zamu je Lagos ni harma na tanadi kayan indian da zansa irin masu burgujejen wandon nan ko kuma in d’aura dan zani yadda suke” ya k’arasa yanata 6a66aka dariya haisam ma yar dariyar yay bai ce komae ba,Abbas yaci gaba “Maganar Dinner party dinma mun gama Magana da Saleem dress code da komae sai jiran lokaci kawae, ya kamata ma a k’ara program Dinner yayi kad’an gaskia bikin H,Zakee guda” d’age gira Haisam yay yana mashi wani kallo can k’asa yace “for me is enough, ba zakuyi wani a Lagos ba” Abbas na dariya yace “zamuyi dae ai kasan dae dole kaje,ko zamu je ba ango ne wannan kuma ai daban a Abuja nike nufin Dinner kawae yay kad’an amman ko ka k’i ma su Laila suma sun shirya wasu programs d’in don munyi Magana tace za’ai Arabian da wani can dae naku na Al’adan Ethiopia” dan ta6e baki yay kawae bai ce mashi komae ba, gyara zama Abbas yay kafin yace “Wai nikam ina Mom Zarah ne, da ita ya kamata ace muna preparation da tsare tsare don itama matsayin babbar k’awar Ango take” shiru haisam yaya idonshi akan Tv kaman bai ji abunda Abbas d’in yace ba,

“Am asking u Zakee” sai lokacin ya kalleshi kaman bazaice komae sai kuma yace “nima ina nemanta” da d’an mamaki Abbas yace “kaman ya kana nemanta bata nan ne?” “No tana nan but ta daina zuwa nan kwata kwata” tashi Abbas yay zaune yace “to why ko kai mata wani abu ne?” d’an guntun Murmushin gefen bakin yay kafin yace “in mata mi, she just changed completely” ya k’arasa Maganar yanayin fuskarshi ya canja da gani ba jin dad’in hakan yake ba, Abbas yace “to amman ka ta6a tambayarta dalilin canjawar ne?” shiru ya d’anyi kafin ya gyara zamanshi sosae yana kallon Abbas din yace “Yea,nayi hakan i think 2 to 3 times but abu d’aya take bani shine bata jin dad’in jikinta as a result of wannan ciwon Aljanu ne komi da tayi” wani guntun Murmushi Abbas yay kafin ya sake tambayarshi tun yaushe ta fara ciwon Aljanun ne yay mashi bayani tun lokacin da suka dawo Outing Fanan tazo da yadda suka je da daddare suka iske bata lpy har tay amai sosae aka tabbatar Malaria ke damunta bayan sun dawo gida Fanan ta sanar ma Hajiya bata lpy anan suka ji tana da Aljanun, yana gama Maganar ya maida idonshi kan tv shi kuma Abbas ya sauke nannauyar ajiyar zuciya idonshi akan Haisam sam baiyi mamakin rashin fahimtar Haisam d’in kan abunda ke damun Fatuu ba don yasan shi ba wani sanin so yay ba sosae iya soyayyar Fanan kadae ya sani bai tunanin daga kanta ya ta6a yin soyayya da wata, sigh yay on a serious note yace “H,zakee Zarah has fell in love with u” Maganar Abbas ta daki dodon kunnan Haisam ba shiri ya maido idonshi akan Abbas yana mashi wani kallo with suprise written boldly all over his face, ganin kallon da yake mashi ne yasa Abbas d’in jinjina mashi kai cike da tabbatarwa yace “Yea am sure tana son ka ne shiyasa ta canja maka haka don ta gane kana da wadda kake so” ido kawae Haisam ke binshi da shi can kuma yay wani guntun Murmushi ya d’an girgiza kai kafin yace “pls Abbas don’t start it,kai koda yaushe Magananka d’aya ne soyayya mata,Zarah ne zaka ce wai sona take how possible,yarinyar da bata da buri sai na tayi karatu ta zamo Doctor yaushe ta san wannan d’in” Abbas dake Murmushi yace “shine kuma bazata iya canjawa ba, sanin da kai mata yanzu ta girma zata iya having feelings for man saboda she’s quite mature for her age” wani kallo haisam ke binshi dashi ya d’an ta6e baki jin Abbas yayi shiru yasa yace “Zaraah is still immatured” da mamaki Abbas yace “amman miyasa zaka ce hakan ga abu a fili kowa ya kalli Zarah yasan ta mallaki hankalinta ta zama cikakkiyar mace yanzu” shiru haisam yay yana d’an Murmushi kafin yace “da sauranta don har yanzu bata fara menstruation ba” da wani kallan expression mai nuna tsantsar mamaki Abbas yace “Zarah ce bata fara menses ba at her age? Kai ya akai kasan hakan??” nan take Haisam ya fad’i mashi yadda suka ta6a yi da Fatun da Azumi yace “so in da ta fara na tabbatar zata sanar dani” wani kallan Murmushi Abbas yay yace “H,Zakee Zarah zatai ta zama ne bazata yi hankali ba,kar ka manta kana man Maganar abunda ya faru kusan 3 years back ai dole zata k’ara hankali besides a shekarunta yanzu sun kai ace tana menstruating in kau har bata yi kaman yadda kace to tabbas bata lafiya tana bukatar akaita asibiti ko kuma tana daga cikin matan da basu yi kwata kwata wanda bana tunanin hakan ma gaskiya” shiru Haisam yay yanata kallonshi yayin da acikin zuciyarshi yake nazarin Maganar tashi ta k’arshe yasan Abbas ba likita bane amman abunda yake koyawa ya kunshi hakan wato biology,

 

“Kayi Nazari sosae H,zakee tsawon lokaci kana tare da Zaraah ace baka ta6a sanin tana da Aljanu ba sai yanzu kuma basu tashi zuwa su sakar mata ciwo ba sai da Fanan tazo….” katseshi Haisam yay “amman Hajiya ta tabbatar da haka”,

“Eh dama ba ina nufin k’arya bane bata dasu sai dae koda tana dasu d’in to sun barta tun kafin kasanta ko kuma sune ke sakata rashin ji a can baya amman basu sakata ciwo kaman yadda take yanzu kayi tunani da kyau a gani na Zarah ta fara sonka kwatsam sai ga Fanan ranar da kuka dawo, tambayata anan da ka ga Fanan wane reaction kay? Zai iya yuwuwa ta haka ta gane akwae wani abu tsakaninka da Fanan saboda rikicewa ta shige gida tace bata lafiya sannan da kuka je da Fanan da daddare wane irin hira kukai? Shin wai ma da kuka dawo da ita akan hanya tace maka bata lafiya ne dama??” shiru bakin Haisam ya mutu yama rasa mi zaice mashi abun gaba d’aya ya gama d’aure mashi kai wai Zarah na sonshi……….

 

Tana ta kwance ba um ba umum kamar wanda tay Mutuwar kwance sai ido kawae ita kanta bata san mike faruwa da ita ba gaba d’aya jijiyoyin jikinta sun daina aiki a haka har akai la’asar ga bak’ar yunwa da ke cinta cikinta sai kuka yake amman ta kasa tashi, tana a cikin wannan halin Haulat ta d’aga labulan d’akin ta shiga da sallama jikinta sanye da Uniform d’in islamiyya, tunkarar gadon tay idonta akan fatuu ta tsaya gaban gadon tace “kawata lafiya ina sallama baki amsa ni ba” k’uri tay mata da ido ko kyafta su bata yi hakan yasa haulat kiran sunanta amman shiru da sauri tasa hannu a shoulder dinta ta jijjigata tace “Fatuu lafiya wai? Mi ke faruwa ne?” da k’yar ta iya mik’ar da yatsanta ta nuna ma Haulat Iv d’in dake gabanta ta kai hannu da sauri ta bud’e tana karantawa,a kid’ime ta d’ago ta kalli Fatun sai kuma ta zauna gefen gadon a hankali ta aje iv d’in a gefe ta fara Magana “nasan dole ne ki k’ara shiga matsananciyar damuwa yanzu amman don Allah kiyi hakuri Fatuu kaman yadda nike ta fad’i maki, ki d’auka Allah bai kaddara Ya Haisam mijin ki bane” sai lokacin ta yunk’ura da k’yar ta tashi zaune idonta akan Haulat da wata irin murya ta wanda ya karaya tace “amman Haulat wllh ina son ya Handsome Allah ne shaidata….” sai lokacin kwalla suka fara zubo mata da ganin yadda take kukan zaka san ba k’aramin ciwo take ji a cikin zuciyarta ba” dafata Haulat tay taci gaba da bata hakuri tana nuna mata kowa da irin k’addararsa a rayuwa ta d’auka wannan ce tata ita dae kai kawae take d’aga mata can Haulat tace “da zuwa nayi mu tafi islamiyya bazaki ma iya zuwa ba ko?” girgiza mata kai tay tace zata je,

“Da alama ma tun da kika dawo da safe kike cikin wannan halin naga ko Uniform baki cire ba, kin ci ma Abinci kuwa?” girgiza mata kai tay alamar a’a tace “to in zubo maki zaki ki ci ko?” shiru ta d’anyi sai kuma ta d’aga mata kai don tana jin yunwa sosae, mik’ewa Haulat tay taje Kitchen bada jimawa ba ta dawo ruke da plate din dafa dukan taliya da wake ta mik’a mata ta sake fita taje falo ta d’aukko mata ruwa, bayan ta dawo komawa tay ta zauna gefen gadon tana rarrashinta akan tayi hakuri ta daure taci, ba wani mai yawa taci ba don sam bakinta bai mata dad’i tace ta k’oshi ruwan ne dae ta shanye shi duka,bayan ta gama saukkowa tay ta nufi hanyar fita walking Slowly Haulat ta tambayeta ina zata tace alwala zatayo, saida tay Azahar sannan tayi la’asar kafin ta mik’e ta daukko jakarta Haulat tace ta kawo ta rike mata tace ta bashshi daga haka suka fita, Kawu Amadu na shago bai dad’e da bud’ewa ba don baccin rana ya sha sai bayan la’asar ya bud’e Haulat ta gaidashi kafin suka wuce, tunda suka fito idonta akan gidan Hajiya suna zuwa daidai kwanar dake jikin gidan Fatuu ta ja ta tsaya haulat ta juyo ta kalleta ganin tayi tsaye yasa ta tambayeta lafiya ko bata iya zuwa,

“Haulat kije kawae ni zan je in fad’i ma Ya Handsome halin da nike ciki gaskiya nasan yana nan tunda yau Lahadi” waro ido haulat tay a rud’e tace “Fatuu kar kiyi haka don Allah ki daure, wllh ko kin gaya mashi ba abunda zai maki saidae ya baki hakuri to kinga gara ma kar ki fad’i mashi d’in don k’imarki na iya ragewa a idonshi” kaman zatai kuka tace “naji koma mi zai faru ni ban damu ba in dai ya sani, kuma tunda shi mai tausayi ne nasan yana iya tausaya man ya aure ni har rokonshi ma zan iya yi ko matsayin mai aikinsu ce ya Aure ni” bud’a baki Haulat tay tasa tafin hannunta ta rufe cike da al’ajabin jin kalaman Fatuu, ganin tana niyyar juyawa yasa ta kamo hijab d’inta a rud’e take fad’in “Fatuu kar kiyi haka don Allah, wllh ni nasan ba zai aureki ya had’a ki da Aunty Fanan ba danginsu bazasu ta6a yarda ba…..” bata k’arasa Maganar ba sakamakon buge mata hannu da Fatun tay ta nufi gidan Hajiyar kai da gani bata cikin hayyacinta idanunta sun rufe,tsaye Haulat tay ta rasa mi zatayi ta tsaida Fatuu, zuciyarta ta raya mata ko taje ta fad’i ma kawu Amadu sai kuma wata zuciyar tace ko kafin ki fad’i mashi ma ai aikin gama ya riga ya gama, sharr kwalla suka fara zubo mata ta fara fad’in “duk ni naja maki wannan halin Fatuu dana sani ban maki Maganar nan ba” k’arshe dae data rasa mafita kawae sai ta juya ta nufi hanyar islamiyyar tana share hawayen dake zubo mata, Fatuu na zuwa tabi ta k’aramar kopa dake bud’e tana zuwa bakin fence door ta kutsa kai part din Haisam……………

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wannan no 09013n804524._

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button