Uncategorized

Babban Yaya Complete Novel

  

“Wato Alhaji Umaru Naga alama saboda Ina zaune aqauye ban’isa na fadi magana a aiwatar da abinda nayi umarni ba”

Daga d’ayan bangaren Wanda aka kira da Alhaji Umaru yadafe goshinsa,(馃う馃徎鈥嶁檪锔?) waye Kuma yata6o musu Babban yayan nasu?

Ajiyar zuciya ya sauke tareda gyara Zaman wayar dake kange a kunnansa yace “Yaya meyake faruwa? Kaida waye?”

“Au tambayata ma kake meyake faruwa? Umaru dakai da Usmanu kunfi kowa sanin abinda kuka aikata, tayaya zaku bar yaro agabanku shekara da shekaru yana zaune babu iyali? Shekara d’ai d’ai har shekara Talatin da shida NAUFAL yana zaune yana abinda yaga Dama yaqi aure, kukuma saboda ku ‘Yan boko ne kun rabu dashi yana abinda yaga Dama, ni danake Nan qauye ba zance kuyi abu kuyiba, a’a Sai abinda kukai niyya”

Cikin ladabi Alhaji Umar yace “Wallahi tallahi Yaya Bahaka bane, mu kanmu muna bakin kokarin mu akansa, bamu San Yaya zamu yi masa ba, munyi munyi dashi yakawo yarinyar dayake so Amma yaqi”

Cikin fishi Wanda aka kira da Yaya yace “zancen banza zancen wofi, kunje can qasar turawan dayake rayuwa ne kunganshi akame awaje daya? Tayaya yaro baligi irin NAUFAL zaku zuba masa ido? Yafada muku shi gunki ne kokuma dutsi da bazai buqaci mace ba? Jinake haka muke ganinsu a TV tsangal tsangal da gajeran wando suna tamola Waida sunan sana’ah, to Kana katse wayata, ka kirashi kafada masa cewa ni Abubakar yayan mahaifinsa Kuma me iko da fada aji acikin dangin Arabo, nace yakira  yarinyar Amini na su daidai ta, idan ma ‘yar bokon yake nema irinsa itama yarinyar ba’a qauye tatashi ba bare ya rainata kamar yanda ya raina ni, zan sako Maka lambarta katura masa “

Alhaji Umar yace”To Yaya, insha Allah zanyi yanda kace, ga Alhaji Usman ku gaisa”

Yafadi maganar yana kokarin janye wayar daga kunnansa

Cikin sauri Yace “A a, barshi kawai, ai duk bakinku d’aya” daga haka yakashe wayar sa.

Alhaji Umar yadago Kansa ya kalli Usman batare da yace komai ba, kallo daya zaka musu ka tabbatar su din jini daya ne, kama suke da juna sosai kamar harta 6aci, basuda jiki sosai kasancewar su asalin buzaye

Alhaji Usman yace”magana yake akan Naufal ko?”

Alhaji Umar ya daga masa Kai, sannan yafada masa yanda sukayi dashi, batare da damuwa ba yace” Babu damuwa, katura masa number kawai, ya kira yarinyar, idan munyi sa’ah Wannan Karon andace shikkenan, mu Dama fatanmu ace yayi auren “

***      **      ***

Sanye yake da Jessy ajikinsa fara tas me dogon wando,kafarsa na d’aukeda farin kambos, kunnansa d’aukeda wani Bluetooth fari me shegen kyau, jogging yake Kansa aqasa, Amma duk da haka mutane Sai magana suke masa yana daga musu hannu kasancewar sa marar son surutu, wayar sa tafara qara yana duba Screen  din wayar yaga ansa My Dady, dole ya dakata da gudun dayake tareda riqe waist dinsa yana Dan qaramin haki, dago Kansa yayi tareda amsa wayar bakinsa d’aukeda sallama

Sai a lokacin nasamu damar qare masa kallo, fari ne sosai ko’ina na jikinsa farine tass, hadaddan Gaye ne na fitar Hankali, yanayin tsarin idonsa ma kadai ya’isa yasa Nan take yasiye zuciyar yanmata, inde ka Kalle shi sau daya, dole saika sake waigawa domin sake kallon sa, gaida mahaifin nasa ya farayi Amma yana magana dimples dinsa suna futowa.

Alhaji Umar yace “akwai number wata yarinya Habiba Dana turo ma yanzu, kakirata ku daidaita, Yaya ne yace abaka number, yarinyar aminin sace, idan kun gama daidaita wa saika samu lokaci kadawo gida a tsaida maganar aure, banason jin wata magana Kuma daga baya”

Yana gama yimasa Wannan jawabin yakashe wayarsay dalilin dayasa Dady yakashe wayarsa, duk lokacin dasuka masa maganar aure Sai yasan irin maganar da yayi yaroqesu akan su qara masa lokaci, to lokaci har yanzu shiru yaqi zuwa 馃

Wata zazzafar is’ka ya furzar daga bakinsa, cikin wata daddad’ar murya wadda daqyar zakaji meyake fad’a yace “ita Kuma wannan ta wacce hanya zanbi narabu da’ita?” wani tunani yayi, Nan take ya dauki shawarar zuciyar sa yayi Dialing number da’aka turo masa ta Habiba

Bugu uku ta dauka, batare da tayi sallama ba tace “Hello waye”

Sai yaji wani iri banbarakwai, kamar shi ace yakira waya Ana tambayarsa waye, Kuma ba kowa ke tambayar sa waye ba Sai budurwa, shida a koda yaushe yanmata sune suke bibiyarsa saboda su samu kusanci dashi Amma basa gabansa,ya tabbatar inda ace tasan asalin Wanda yake kiranta to babu makawa zata Iya zuba ruwa aqasa Tasha saboda tsananin murna.

Jin shiru har yanzu ba’ayi magana ba yasa tace “Hello wake magana ne?”

Saida yaja wasu second sannan yamotsa pink lips dinsa yace “Sunana Naufal Umar Arabo” 

Saida taji yace Arabo sannan tace “Okay, ko kaine Yaron Dan’uwan Alhaji Habu Wanda yake zaune a qauye?” 

“Yes” 

Shine kawai abinda yace 

Daga Nata bangaren tace “Ai sunyi magana da Abbanah, yace zai turomin d’ansa naganshi idan yamin Sai manya su shiga cikin maganar” (馃槺馃槀) 

Baqin ciki ne yakama shi,ya yatsina fuskar sa, yaso ace yayi tozali da wannan yarinyar yaga me take taqama dashi har haka, har shi zatacewa idan yayi mata? Takuwa San waye shi? 

Lumshe Idonsa yayi, hakan da yayi saiya Bawa gashin Idonsa damar bayyana, Zara-Zara dasu dogaye kamar na mace, fuskar Nan tasa murtuk babu alamar fara’ah yace “Yes, nine” 

Itama tace “Sai cewa kake kaine kaine, kakasa cewa komai, kana magana kamar me koyon magana, yanda baka son had’in Nan nimafa baso nake ba, karkayi tsammanin sonake, kanamin magana daqyar Kanata wani yauqi saikace mace, fadamin zakai yaushe zaka zo naganka, bawai Kiran waya ba, saboda ni ba’acemin zaka kirani ba, ance min ne zaka zo naganka ko zakamin “

Zuwa wannan lokacin Kam ransa yagama 6aci,(馃槚馃槚) 

Amma wani bangaren na zuciyarsa dad’i yakeji, ko babu komai yasan yarinyar bazata bashi matsala wajan rabuwar su ba tunda itama bata so, sassauta muryarsa yayi, ya dedeta Kansa, kamar me koyon magana yafara magana a rarrabe”Mene..ne yauqi?”

“Uhm au bakama San menene yauqi ba? Tabdi jam, Allah kenan mehada budurwa da samari Kala Kala,yau Kuma da Wanda nahadu kenan, nikuwa naso ace naganka bawan Allah,Inga mutumin dabai San menene yauqi ba, kafadamin yaushe zaka zo?” 

Be damu da wannan dogon surutun Nata ba, asali ma so yake su qarqareta ayau dinnan kowa yakama gabansa, ahankali yace”ni… ni banda lokacin zuwa”

Daga Nata bangaren tace “to Ahaka zamuyi aure bakada lokacin kaina?” 

Wani irin murmushin gefen baki yayi, cikin ransa yace anzo wajan, a fili kuwa saiyace “Banda lokaci, Ina wajan neman kudi, kinsan kudi sune gaba da komai, ni kaina banda lokacin kaina bare in samu lokacin wani, kawai neman kudi nasa agabana” 

Tace “Okay, kana so kacemin kudi sune abin so fiye da komai arayuwarka?” 

“No, ba rayuwa ta kadai ba, harma da rayuwar Wanda yake kokarin shigo wa cikin rayuwa ta, kudi sune gaba da komai awajena” 

Tace “to Malam Naufal Umar Arabo, inban manta ba haka kacemin sunanka ko? to Ina ganin Bama Sai kazo ba, kayi zamanka kawai, Allah yahada kowa da rabonsa” qit takashe wayar ta 

Baisan lokacin da wani farinciki ya lullubeshi ba, har dimples dinsa suka lotsa, cikin murna yace “yessss”  sannan yaci gaba da Jogging dinsa

***      **      ***

Labarinsu

Alhaji Abubakar Arabo,Alhaji Umar Arabo, dakuma Alhaji Usman Arabo, uwarsu daya ubansu daya, ‘Yan asalin qasar Niger ne, buzayen dasuke rayuwa cikin Sahara, sunada mutuqar dukiya da Tarin shanu, sau Tari mutanan Nigeria suna zuwa wajan su siyan shanu domin su kiwata su siyar dasu da tsada, kasancewar inda suke rayuwa babu isasshen abincin dabobi, daga baya sukai hijra suka dawo Nan Nigeria, sukaci gaba da juya dukiyar su har Allah yayi mata Albarka suka zama manyan masu kudi da ake damawa dasu ayau. 

Alhaji Abubakar shine Babba, suna kiransa Baba Habu, yana zaune a Jigawa shida matarsa da yaransa maza guda biyu sa’annin Naufal ne Amma sun dade da aure harma sunada yaransu

Saikuma Alhaji Umar shine na biyu, suna kiransa da Dady yanada Yara guda bakwai, NAUFAL shine Babba, Suna kiransa da Babban Yaya, Sai Yan biyu maza,Sa’ad da Sa’eed, Sai Anty Maryam, tayi aure tanada yaro daya,me sunan Naufal, suna kiransa da junior, Sai Yan biyu mata, intisar da ihsan, saikuma yar auta WAHEEDA

Sai Alhaji Usman Arabo, shine Dan qaramin su,suna kiransa da Uncle Usman, Allah bai bashi haihuwa ba, yanada matarsa guda daya, suna cemata Hajiya Anty, ma’aikaciyar Asbiti ce

Dukansu mutum ukun Nan Abubakar, Umar, Usman, suna kyautatawa junansu, matansu na can Niger sune de har yanzu atare dasu, suna mutuqar girmama juna, gaba dayansu kama suke da juna daga matan, har mazan, dakuma yayansu, duk fararene, saide na wani yafi wani, Amma dukansu farare ne, kana ganinsu zaka San buzaye ne na asali, tsabar kyawun dasuke dashi ne yasa ake Kiran Family din nasu da Suna (Arab Family) , Amma dasuka dawo Nan gida Nigeria, Sai Yan Nigeria suke cewa Arabo Family 馃槂

Kamar yanda nafada Naufal shine babba acikin yaran Alhaji Umar (Dady) shekararsa Talatin da shida, beyi aure ba, iyayen sunaso yayi aure kasancewar sa babba a gidan, yana kula da qannansa yanda me karatu baya zato, shiyasa ko wani abu ne yafaru saide kawai iyayen su fada masa, shikuma zai warware komai, kwata kwata baya wasa da yan’uwan nasa, idan kaga ya ware yana fira wasa da dariya to da abokan sa ne, musanman yayan Baba Habu dasuke jigawa, koda yaushe fuskarsa a daure take, bala’in tsoransa sukeji  musanman qannansa mata, kana laifi kadan zai daka Maka tsawa, shiyasa suna ganinsa kowacce take shiga taitayinta, babu ruwansa duk wacce tayi masa laifi zaneta yake, suna komai duk abinda suke so, saide yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, saide Hijab, Kuma suna kiyayewa mutum daya ce take bashi ciwon Kai acikin qannansa, itace auta WAHEEDA, itace tafara kiransa da BABBAN YAYA, daga Nan kowa yake fada masa, babu Wanda zakaji yace Yaya Naufal, saide BABBAN YAYA.馃憣馃徎

Cikakken Dan qwallon qafa ne Wanda akeji dashi afadin qasar tamu ta Nigeria dakuma kewayen ta, lokacin daya gama Degree dinsa na biyu, (Masters) iyayen sunso yayi aiki a qarqashinsu, domin su qara habbaka kasuwancin su, Amma BABBAN YAYA yace inaaa! Shifa harkar qwallo zai fara, saboda Dama can tun yana qarami abinda yake so kenan, daga Alhaji Habu na qauye har mahaifin sa Alhaji Umar Qin bashi goyon baya sukayi, daqyar Alhaji Usman yadage akan su harya shawo kansu suka yarda, da farko Yan kano pillars yabugawa Ball, daga baya wata qasar ta daukeshi, daga Nan Kuma yakoma qasar Spain, Bayan wasu shekaru yakoma qasar dayake a yanzu yana buga musu Ball inda yake daukar albashin sa Mai tsoka duk sati.

Lokacin dazai fara Ball babu sunan daya fad’o masa Arai sai Wanda fitnanniyar qanwar sa WAHEEDA tasaka masa, BIG BROTHER, shiyasa jikin Jessy dinsa, p-cap dinsa,sunan BIG BROTHER ne ajiki, Yan gari, Yan unguwa, fan’s dinsa na ko’ina kowa Big Brother yake ce masa, inde yashiga cikin jama’ah kawai haquri yake, saboda yanada masoya masu dimbin yawa, kawai Yan gidansu ne suke kiransa da BABBAN YAYA, Amma jama’ah kowa da kowa Big Brother ake ce masa,yanmata kuwa kullum cikin kiransa suke, yana alfahri da hakan.

Iyayensa sunaso yayi aure saboda shekaru irin nasa, Amma yace shi har yanzu baiga wacce ta kwanta masa ba, tun yana qarya yana cewa zai kawo wacce yake so aqara masa lokaci, har iyayen suka dawo daga rakiyarsa suka fara hadashi da yaran abokai da Kuma yan’uwa, Amma har yanzu duk wadda aka hadashi da’ita yasan irin dabarar dazai mata Dan su rabu cikin hikima, kamar de yanda ya kasance a tsakanin sa da Habiba Yanzu 馃お

Duk cikin yanmatan da’ake hadashi dasu babu wadda yataba baiyana mata Kansa, inde yakira wayar su yana fada musu cewa sunansa Naufal, baya cewa Big Brother saboda yasan cewa muddin yafadi wannan sunan, to babu Wanda bai sanshi ba, wannan kenan 

***      ***      ***

Tafe suke hannunta dauke da wani yaro Wanda bai wuce shekara uku ba, Sanye take da hijab pink colour, me hula, ta gaban hijabin kadai zaka iya sanin cewa Allah yayi mata tarin suma da yawa, kasancewar wuyan yayi mata yawa kadan, yarinya ce bazata wuce 18 years ba, ranar datake dukansu itada Yaron yasa ta yatsina fuska, Amma duk da haka kyawun fuskarta yana Nan, duk da babu kwalliya kodaya a fuskar, Sai haki take da alama Yaron yamata nauyi, suna zuwa bakin get din gidansu ta sauke Yaron, kudi tafuto dashi daga cikin handbag taware 5k tabawa Yaron sannan taja hannun sa suka qarasa gida, babu kowa afalon nasu, Kai tsaye dakinsu tashige, mutum uku ne zaune a Dakin, ‘Yan biyu daya tana yiwa daya tsifa, saikuma wata Babba tana duba littafin azkar, gaba dayansu kama suke da juna, kana ganinsu kasan jini daya ne, hijabin jikinta ta cire ta wullar dashi anan, lokaci daya tsantsar dirin jikinta ya baiyana, mace ce har mace, gata yar qarama Amma Allah yamata baiwar kyakykyawan jiki. 

Yaron yatafi da gudu wajan mamansa yace “Momy munje Kuma anbamu kudi da yawa, Nima anty Waheeda tabani, kingani?” ya qarasa maganar yana nuna mata kudin hannun sa

Murmushi tayi tace “Lalle Waheeda kice kudi kuka samo keda junior”

Zama tayi a bakin gadon tareda cire ribom din kanta, hakan yabawa dogon gashinta damar zubowa gadon Bayan ta

Tace “eh Anty maryam, dubu goma aka bamu, shine naraba mana”

Kafin wadda aka kira da Anty Maryam tayi magana, daya daga cikin Yan biyu tace “Qarya kike Waheeda, Anty wallahi qarya take, kawai cutar Yaron tayi, kamar bakisan halin Waheeda ba, Allah qwace masa kudin zatayi”

Cikin rashin kunya ta kalli me maganar, duk tsananin kamar dasuke kasancewar su identical twins Sarai Waheeda take ganesu, tace “to Ihsan na qwace din, ai tare aka aikemu da junior din ko? Kiyi abinda zakiyi”

Anty Maryam ta kalleta tareda riqe ha6a, tace “lalle Waheeda wuyanki ya’isa yanka, yayun naki kike fadawa haka?”

Wadda ake yiwa tsifar ce tatashi ta nufi Waheeda tace “Na hanaki daukar min hijabi na Amma kinqi yarda ko, tsabar masifa da naci kinada hijabai bazaki saka ba kin goge su kin 6oye saide ki dinga daukar namu kina sakawa saboda Kin raina mana Hankali, nayi Miki last warning karki sake daukar min hijab, sannan Ihsan ba sa’arki bace karki sake mata rashin kunya “

Cikin tsiwa tace”wallahi yanzu nafara saka hijabi saide in bangani ba, baki Isa kimin in qyale kiba intisar”

Anty Maryam tace “Waheeda kanki daya kuwa? Dama rashin kunyar Taki haryakai haka?”

Ihsan tace “rabu da’ita Anty, ai taga kanmu daya ne,Mp muke itama shi take yi, brezia muke sakawa itama shi take sakawa,taga ta girma tafimu nonuwa, tayi tsawon qafa, Gani take shekarunma daya muke da’ita, yau kuwa zakici ubanki, zaki San kin mana rashin kunya”

Tashi tayi tsaye ta kallesu ta watsar tace “ai Dama ba yau kuka fara hademin Kai ba, Naga su Sa’ad ma qarewa, balle ku Yan biyun qarshan zamani, qarqari kumin taron dangi kumin duka, to bazaku birgeni ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata”

Anty Maryam tatashi tsaye tace “lalle Waheeda kullum girma kike kina sake zama marar kunya, zan fadawa ummah abin naki yayi yawa, yanzu har takai su Yaya Sa’ad ma sunansu kike fada” tana fadar haka tafice daga Dakin cikin fishi 

Ihsan ta kalli Intisar, basu tsaya wata wataba suka rufe Waheeda da duka, intisar takama gashin ta tanaja, Ihsan kuwa Sai dukanta take, dama haka suke, hadin kaine dasu sosai, duk lokacin da Waheeda tamusu rashin kunya haduwa suke suyi mata shegen duka

Hajiya Anty ce tashigo gidan, tana Sanye da kayan likitoci komai fari, tana Sanye da glass fari a’idonta, kana ganinta kaga mace yar Gayu, da alama daga Asbiti take wajan aikinta, da kukan Waheeda tafara cin Karo, Kai tsaye Dakin nasu ta nufa, ‘Yan biyu suna ganinta suka daina Dukan Waheeda, haka tadago kanta idonnan yayi jajir tace “Kuma wallahi saina Rama, bashi kuka dauka”

Hajiya Anty batace dasu komai ba taja Dakin tarufe, tawuce wajan ummah, Sai a lokacin ummah tashigo Dakin nasu taji ba’asin fadan, da alama Hajiya Anty ce ta turo ta, Dan lokacin dazata shiga Dakin nasu ma mita take tana cewa fitinar Waheeda ta isheta鈽癸笍

Da yamma sukai baqi daga qauye, a lokacin hajiya Anty tana nan bata tafi ba, megadi ne yayi musu jagora har cikin falon gidan, Anty Maryam de Takoma gidanta, Amma gaba dayansu yaran suna Nan,  ‘Yan biyu suna zaune waje daya suna ganin wani abu a wayar ihsan, Waheeda kuwa tana zaune agefe cikin kujera ita daya, tunda ‘yan’uwan suka daketa taketa kumburi, taso ace ummah da Hajiya Anty basa Nan, dasai tahada wa ‘yanbiyu wata muguntar da bazasu taba mantawa da’ita ba, yanda ta zauna waje daya tayi shiru zaka rantse wata kamilar yarinya ce, saboda ta nutsu sosai kamar ba’ita ba,itace tafara tashi takawo musu lemuka da ruwa, sannan ta gaishe su, aikuwa suka amsa cikin girmama wa, tasake komawa wajan zamanta ta zauna, Ummah takalle su cikin sakin fuska tace “Saide kuyi hakuri fa, Amma bamu gane Kuba”

Namijin ne yafara dariya yace “Hajiya ai ‘yan’uwan kune daga wani gari Kaburma, ai Alhaji Habu ne yace duk lokacin da muka shigo Garin naku, mu qaraso mu gaisa nida iyalina, aini kamar qani nake awajansa” yafadi maganar yana Kallan Waheeda 

Waheeda ta Kalle shi dakyau, Bama qanin bane kenan, kama ce, tunda yace kamar qani yake a wajan Baba Habu, Kai Shima de Baba Habu da yayime-yayime yake, ita Kuma umma Sai washe musu baki take

Hajiya Anty tace “Amma kun kyauta wallahi, ai Gara daban wuce gida ba, yanzu gashi munga juna”

Matar datake gefen namijin tace “Eh wallahi, ai Baba Habu akwai zumunci, Amma wadannan Yan biyu ne ko?”

Ta qarasa maganar tana Kallan Yan biyu

Dariya sukayi sannan suka amsa mata, Tajuya tasake Kallan gefen da Waheeda take zaune tace “kekuma fa qawata kinyi shiru babu ruwanki da kowa”

‘yanbiyu ne suka hada ido suka kwashe da dariya, Wai Waheeda ce babu ruwanta, shine abunda ya basu dariya

Matar tace “yakuke mata dariya, ai Naga tayi shiru da alama zatayi hakuri,qawata ya sunanki?”

Waheeda tayi murmushi tace”sunana Waheeda”

Kallan mijinta tayi tace “Baban Halima kaji suna me dadi, idan nasake haihuwa Nima ka sakawa yarmu irin wannan sunan”

Dariya yayi, ya kalli Yan biyu, ya kalli Waheeda, yace “yanzu Nan duk ‘ya’yanane?”

Dariya sukayi kawai, babu wadda tace masa komai, yace “toku Yan tagwaye wayece babba acikin ku?”

Ihsan tace “nice babba, Sai Intisar, Sai qanwarmu Waheeda”

Washe baki yayi yace “ikon Allah kenan, toke ashe kece Gambon su”

Waheeda tace “Uhm…” Daga Nan tatashi tayi daki

Matarsa tace “Allah sarki, kunga ita tatafi daki ma babu ruwanta baiwar Allah, Baban Halima Bari naje wajanta musha hira”

Tatashi tabi Bayan Waheeda, duk yanda taso share matar hakan bai iyu ba, Dan dolenta tasaki jiki da’ita suka Sha hirarsu, Sai yamma lis suka tafi, Hajiya Anty taje gidanta takawo wa matar atamfa da kudi, ummah Kuma tabasu kayan abinci sannan tasa driver yamaidasu har gida.

Da daddare suna zaune afalo gaba dayansu, Ummah da Yanbiyu maza Wanda suke bin Babban Yaya, Sa’ad da Sa’eed,, saikuma yanbiyu mata su Ihsan, kowa Assignment dinsa yakeyi, mazan ne daya yana kallo a TV daya yana danna wayarsa, Sa’eed ne ya kalli Waheeda yace “ke tashi ki daukomin bread a kitchen, yana Nan akan fridge”

Hankalinta yanakan rubutun assignment dinta tace “qarami ko babba?”

Lokaci daya shida Dan’uwan nasa suka kalleta, mamaki ya kama Sa’eed, harshi zai aiki yarinyar Nan Amma tana tambayar shi qarami ko babba? 

Miqewa yayi tsaye yanufeta, tana dago kanta ta ganshi yanufota tatashi da gudu tayi kitchen, yanda take gudun yasa dogon gashin kanta yake bazuwa a fuskarta,hips dinta kuwa Sai rawa yake, haka tadinga tsaki cikin ranta, saboda bata so idan tana tafiya taji suna rawa 

Waheeda kyakykyawa ce ta qarshe, tanada kyau Wanda kallo daya zaka mata kagano hakan,duk cikin yan’uwanta tafi kowa kama da Babban Yaya, yanda yake magana dimples suna futowa haka itama, musanman idan tayi dariya, kana ganin ta ka ganshi, shiyasa ko ba’a fadaba inde kagansu basai ka tambayi waceba, kaima kasan jininsa ce, kamar su tayi yawa, saide basa zama inuwa daya, baya sakar mata fuska, inde tayi laifi tana ganinsa jikinta yake rawa, saboda tasan watan azabar ta yakama, tayi laifi yakamata ya daketa hakan bazai Hana gobe tasake yin wani laifin ba,babu Wanda bai Santa ba a school dinsu, kana cewa Waheeda Virus za’a nunama ita, wannan shine Nikname dinta, dazaran tayi laifi anyi mata hukunci batada wata Sara saide tace baza’a birgeta ba Sai an kashe ta ankaiwa Ummah gawarta 馃ぃ, Amma bata taba fadawa Babban Yaya ba, saboda tasan karonsu babu dadi, Amma yasani Sarai tana fadawa mutane hakan. 

Waheeda tanada kyawun sura, hips dinta da breast dinta yafi qarfin shekarun ta, harma tafi yan’uwan Nata, Kuma tana tafiya suna rawa, sauqin ta daya dokar da Babban Yaya yakafa musu tasaka hijabs. 

Washe gari Sunday babu makaranta, gaba dayansu suna tareda Ummah a kitchen suna hada breakfast, gaba dayansu tasosu take su shiga kitchen tare, wani lokacin Kuma tabarsu su kadai suyi, wayar Ummah ce tafara qara, tana dubawa taga Baba Habu ne daga jigawa yake kiranta, cikin mamaki tace “Yaya Habu da wannna safiyar lafiya kuwa?” 

Dauka tayi, Bayan sun gaisa yace “munyi magana da Malam Iliyasu, Dan kaburma, Wanda naturo su suka kawo muku ziyara jiya, yayimin waya yanaso abashi auren gambo” 

Umma duk saita kasa gane kan maganar tasa, tace “Wacece gambo Kuma Yaya?” 

“gambo nawace daku Binta? Gambo de qanwar yanbiyu, Waheeda, yacemin yanaso abashi ita yaqara ta biyu” 

Ummah tayi murmushi tace “Haba Yaya, ai tsakanin da kunya, abar maganar Nan kawai, jiya fa bakaga yanda matarsa tasake da yaran Nan ba, musanman ma Waheeda, ta daukemu kamar yan’uwa, Kuma yanzu taji mun dauki ‘ya mun Bawa mijinta ai abun babu dadi Yaya” 

“a a yazakice babu dadi, ai be haramta ba, zai iya auren ta, Sai suyi zamansu, kude bakwa so yaranku su rayu a qauye, kiyi magana da yarinyar idan tana so shikkenan Sai awanketa a kaita Dakin mijinta” 

Umma ba tasake musu dashi ba, tace masa “to shikkenan Yaya, Allah ya tabbatar da Alkhairi” daga Nan ta kashe wayar 

Yanbiyu ne suka kalleta, Intisar tace “Ummah Wai meyake faruwa?” 

Ummah tace “Ina baqinmu najiya, Wanda su kazo daga kaburma?, to shine yace Yanaso abashi Waheeda, zai aure ta, shikuma yarasa wazaiso Sai wannan shashashar” 

Yanbiyu suka kwashe da dariya 

Cikin sauri tadago kanta ta kalli Ummah tace “Tabdi, Amma Yama raina min Hankali, yana Kaburma yarasa wazai Burma aqauyensu Saini? Ni wallahi Bana sonsa” 

Ummah tace “aikuwa Yaya Habu yace inde kin amince za’a bashi” 

“Ummah Bana sonsa, Kuma ai Babban Yaya yahanamu kula kowa” 

Da wannan maganar Tata Ummah ta gamsu, saboda tasan Burin yayan nasu bai wuce ace yaga sunyi karatu Mai tsawo ba. 

    Washe gari da safe, qarfe bakwai daidai, aharabar gidan tayi musu,gaba daya compound din gidan interlock ne, Sai wasu manyan motoci masu numfashi guda hudu dasuke parking space, daga can Gefe Kuma wani waje ne aka ware aka qawata shi da grass masu yawa, Sai ball dasuke zube a wajan, da alama suna buga ball ne wani lokacin. 

kowacce tana Sanye da uniform dinta, uniform din yayi musu kyau sosai musamman Waheeda, farar Riga ce me dogon hannu Wanda yake d’aukeda links,tareda Dan qaramin hijab Wanda da kadan yarufe musu breast dinsu, Sai siket ruwan toka da kadan ya wuce gwiwarsu, Bai sakko qasa sosai ba kasancewar makarantar bata musulmi bace, Yan biyu Kam sun saka doguwar safa fara, taboye musu qafarsu, Waheeda kuwa bata saka safar ba Shiyasa farar qafarta ta baiyana sosai tamkar baturiya, safar tana hannunta, saikuma school bag dinta me shegen kyau data rataya a hannunta guda daya, Hips dinta ya futo sosai acikin siket din dukda buje ne, dukansu babu me dankwali saide hijabin kowa akwai hula ajiki, ta Bayan hijab dinta kuwa kana iya hango duhun gashin kanta Wanda ta nannadeshi tayi acuci maza dashi. 

bataje kusa da yan biyu ba,Dan tasan bakoda yaushe suke zama inuwa daya ba

Driver ne da Kansa yabude musu Bayan motar suka shiga, yarufe sannan yaja sukabar harabar gidan, yana sauke su a makaranta yajuyo, Dama haka yake idan ya sauke su juyawa yake, saikuma an tashi zaizo ya dauke su. 

Kowa Class dinsa ya nufa, yanbiyu suka nufi Ss3 duka su biyun, ita Kuma Waheeda tayi Ss2, takusa shiga aji Aryan yasha gabanta, cikin sauri taja baya ta tsaya tace “Haba Aryan miye hakan?”

Yanbiyu suka juya suka kalleta, sukayi qwafa tareda shigewa aji, jiya jiyan Nan tagama cewa Ummah Babban Yaya yahanasu kula Samari, saboda Dan Kaburma yace yana sonta, Amma gashinan kullum saita kula wannan tatsitsin Yaron me kama da lagwani, sunmata magana akansa Amma taqi ji, ajinsu daya itada Yaron, saboda maza da mata ahade suke, saide kowa da layinsa.

Hannunta yakama suka shiga cikin ajin, ko kadan batayi yunkurin qwace hannunta ba, ajin babu kowa saisu kadai, kasancewar sun shigo da wuri, Kallan ta yayi yace “Waheeda jiya kwana nayi Ina mafarkinki, Kuma kinsan de bazan iya Bari har Aunty tashigo ajin Nan batare danayi tozali da kyakykyawar fuskar ki ba”

Fararen idanunta tajuya tace “Allah da gaske? To in hakane Bani labarin mafarkin Naka”

“bazan baki labarin mafarkin danayi ba saikinmin alqawari Zaki barni na tabbatar da abunda yafaru acikin mafarkina”

Tayi tunanin wani labarin daban zai bata, Kai tsaye tace “nayima, Ina jinka”

Hannunta yasake kamawa duka biyun yana shafa tafin hannunta, yarage murya cikin sigar rada yace “Waheeda Ina sonki sosai, karki Bari arabamu kinji” ya qarasa maganar yana turata jikin bango, idanun tane sukai wuri-wuri tafara kallon qwayar Idonsa, tace “Aryan miye hakan ne? Mekake yi haka?”

Kallan idonta yayi yace “abinda nagani amafarki zan tabbatar dashi a yanzu” yana gama fadar haka ya Dora hannunsa akan Boobs dinta yamatsa da qarfi, lokaci daya taji wani irin shock ya kamata, tunda take ba’a taba taba mata nono ba Sai yau, kokarin dauke masa hannunsa take daga qirjinta Amma takasa saboda yanda ya musu ruqo Bana wasa ba, kana ganin yanda yake matsawa da qarfi kasan sabon shiga ne, hannunsa guda daya tabige saboda azabar zafin datake ji, maimakon yasake ta saiya maida hannun kanta, ya riqe tudun gashinta da tayi acuci maza dashi yahade bakinsu waje daya (馃槺)

Adede  lokacin Uncle Tunde yazo wucewa ta Bayan window na ajin, anan yayi tozali dasu, ihu yasaka yana kururuwa tare da nuna su Waheeda da hannu, Nan da Nan malamai suka taru, Kai tsaye office din Director aka tafi dasu,kan kace me, har labari ya watsu cikin makaranta, saida aka kira yanbiyu agabansu aka kwantar da Waheeda da Aryan aka zanesu, sannan director da Kansa yace ya Koresu daga makaranta, da’ita da Aryan dasu kansu Yan biyun, yace baya buqatar ahalinsu acikin makarantar sa

Kuka Yanbiyu suka fara, suna bashi hakuri, idanunsu yayi jajir kasance warsu farare, Amma Haka sukaqi hakura, Waheeda tatashi takade jikinta tace “aikin banza aikin wofi,babu tambaya babu komai kawai za’a rufe mutum da duka,kukuma kun tsaya Sai wani koke-koke kuke Kuna basu haquri, ai bazaku nunamin ranku yabaci ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata, idan kun gama kukan saiku taho mutafi” tana fadar haka tafice daga office din, babu Wanda yamata magana acikin malaman, saboda sunsan batada kunya, Waheeda Virus zata fadi abinda yafi haka. 

a bakin titi suka hadu da’ita,basuce mata komai ba Sai sharar hawaye kawai suke, itace ta tare musu adedeta suka shiga, haka Kuma itace ta fada masa inda zai kaisu, har lokacin yanbiyu kawai hawaye suke sharewa.

Amma kana Kallan fuskar su kasan cewa akusa suke, sun cika sunyi fam, kawai neman fashewa suke, suna hanya Sai tsaki take saki ita kadai, saboda gaba daya breast dinta bala’in zafi suke mata,damuwar ta daya, kar Babban Yaya yaji, ta tabbatar idan yaji wannan labarin ta mutu! sukuma yanbiyu sunyi tunanin dasu take wannan tsakin, saboda haka Saita qara tunzura su, Ana ajiyesu daga napep din tayi gaba, suka biyo bayanta tajuya taga yanda suke tafiya atsorace, ita kanta tsoron yanda zatayi bayanin abinda ta aikata take yi bare Kuma su, Amma yanda taga jikin Intisar yana rawa Sai abun yabata haushi, lokaci daya tasaki wani tsaki zataci gaba da tafiya

Yanbiyu suka hada ido, dama gashi taja ankoresu daga makaranta, aikuwa basu tsaya sauraren komai ba suka rufeta da duka, megadi hankalinsa yanakan radio Sai ihun Waheeda yajuyo, cikin sauri yanufesu yafara rabiya

Ummah tana zaune afalo tana break fast, tunda su Waheeda suka tafi school Sai yanzu tasamu ta zauna tana cin abinci, wayarta dake Gefe ne tayi qara, number Hauwa’u tagani matar Iliyasu Dan Kaburma, ta dauka suka gaisa cikeda kulawa, umma tace “Hauwa ashede Zaki kiramu, yagida yame gidan naki dasu Halima?”

Hauwa tayi dariya tace “Hajiya wanne megida? Ai kwanan mu daya da zuwa garinku tunda muka dawo narasa gane Kansa, Sai nemana yake da tashin Hankali Ina rabuwa dashi, qarshe ma yace natafi gidanmu ya sallameni, Sai daga baya nakeji ashe neman aure yake, shiyasa yasakeni, ai Bama tare Ina gidanmu hajiya “

Gaban Ummah ne yayi mummunar faduwa, haqiqa idan zancen Hauwa’u ya zama gaskiya to akan Waheeda mijinta yasake ta, tunda shine yayiwa baba Habu magana yana son yaqara auren, salati tafara a fili takasa dainawa har Hauwa’u ta kashe wayar Dan itakan tayi tunanin saboda zancen sakin da aka mata ne yasa Ummah wannan dogon salatin 馃槀

Wayarce tasake qara, sunansa ne yake yawo akan screen din wayar NAUFAL SON,tayi tunanin Hauwa’u ce tasake kira shiyasa Bata duba taga me Kiran ba kawai ta daga, megadi ne yashigo da gudu yana fadin”Hajiya! Hajiya!! Hajiya yarafa suna harabar gida suna fada, gaba dayansu suna Dukan qanwar tasu, narabasu sunqi rabuwa”

Ummah batace komai ba tafuto compound din gidan anan taga yanbiyu suna kuka suna Dukan Waheeda, jikin Ummah har rawa yake saboda bata gama fita daga alhinin labarin da Hauwa’u tabata ba na saki,tsawa ta daka musu “Intisar, Ihsan miye hakane? Meta muku?”

Cikin shashshekar kuka Ihsan tace “Ummah kamata akai da saurayinta a aji yana shan bakinta, shine director yakoremu gaba dayanmu, Kuma yace baya son ganin ahlinmu acikin makarantar sa” 

Lokaci daya idanun Ummah yakawo ruwa, cikin rawar murya tace “innalillahi wa inna ilaihirraji’una Waheeda!!!” 

Duk abinda yake faruwa Babban Yaya yanaji ta wayar, saboda bai kashe ba, ita Kuma Ummah tama manta ta daga waya, yana jin yanda muryarta take rawa alamun tana gab da fashewa da Kuka yayi sauri yakashe wayar.

To…. da alamade yau sarar Waheeda zata tabbata, za’a kashe ta akaiwa Ummah gawarta 馃槀馃ぃ

To masu karatu, Yaya kukaji wannan chapter? 

WRITTEN BY:     AMNAH EL YAQOUB

NOVEL NAME:   BABBAN YAYA COMPLETE

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         870KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      26- APRIL -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦200

Proceed To Download Babban Yaya Complete Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 1”

KARANTA LITTAFIN: “TUBALI BOOK 1 CHAPTER 2”

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button