Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 9 Complete Novel

*ASM Bk2009*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

……..Kallon Abbas haisam yay yace “let’s say abunda ka fad’a gaskiya ne amman miyasa Zaraah zatai hakan, ban tunanin na ta6a yi mata wani abu da zai sa tay tunanin am in love wit her, so i don’t believe all what you ave said” ya k’arasa Maganar yana d’an shaking kanshi alamar rashin yarda, Abbas yace “ai shi so ba ruwanshi da wannan H,zakee wani kallonshi kawae zakai kaji kana sonshi,kuma kai har kace ba kai mata wani abu da zata ji son ka ba duk irin kyautatawar da kake ma yarinyar…….” katseshi Haisam yay da fad’in “ita kadae nike ma haka ne?”,

girgiza kai Abbas yay “nasan ba ita kadae kake kyautata mawa ba sai dae Maganar gaskia tata is special kana kulawa da yarinyar over ta yadda wani ma zai iya yin tunanin sonta kake, nasan ba wani abu bane hakan a wurinka duk wanda yake tare da kai yasan kai Mutum ne mai kyautata ma mutane wanda a zamanin nan da muke ciki da wuya asamu Wanda Allah ya bud’a mawa yake irin Alkhairin da kake, ba kuma don ganin idonka ba kamawa tay nake fad’a nasan ba so kake ba, sai dae kasani ka sake ma Zarah da yawa ta yadda ko siblings naka ban tunanin suna samun hakan daga gare ka hakan kuma zai iya juya komae” shiru haisam yay yana binshi da ido har ya gama sannan cikin cool voice d’inshi yace “komae nake ma Zaraah inada dalili Abbas, yarinyar is an Orphan marainiyane ita da Uncle d’inta and farkon dana fara Magana da ita na fahimci tana da ambition mai kyau wanda in aka tallafa mata zatai achieving don tana da kokari sosae, saidae kuma i found her behaviours so strange because i never came across wani da yake behaving yadda take shiyasa na fara tabbatar da lafiyanta ta hanyar tambayarta daga baya na fahimci haka take kuma tana buk’atar ta canja behaviours nata ta maida hankali kan karatunta shiyasa nai amfani da daman glass da ta fasa man” jinjina kai Abbas yay sosae ya gamsu da Maganar Haisam d’in sai yanzu ya fahimci komae dama kuma suna tallafa ma marayu sosae ta Foundation d’in Hajiya,

 

“Wato ka gane H,Zakee, ita zuciya abu kad’an ke canja ta ba kamar kyautatawa don ingantaccen hadisi na Manzo (S.A.W) yay magana akan ita zuciya an halicce tane akan son mai kyautata mata da kuma k’in mai munana mata, nasan kasan da hakan to anan son zai iya kasancewa na soyayya ko akasin hakan to kwata kwata ba abun mamaki bane wllh don Zaraah taji tana sonka,zata iya tunanin kuma kaima son nata kake shiyasa kake mata hidima sosae kamar yadda nima can baya na fara zargin hakan bani kadae bama har Najeeb yay tunanin hakan har ina cewa wannan overtaking zai man kenan ya fara da biyu” ya k’arasa yana dariya shima Haisam dariyar yake kafin yace “da dae ba waccan sarkin kishin zan aure ba, just don nace bazan aureta ba fa ta kwanta Medical bed yanzu taji kuma zan hadata da wata in Aurensu i can’t even imagine abunda zai faru kuma kaima kasan bani da ra’ayin mata biyu wannan sai kai da Najeeb, nayi mamakin ma yadda akai kakai yanzu da mace d’aya i thought by now kana da 4 wives” wata yar iskar dariya Abbas yasa shima Haisam d’in dariyar yake yace “saurin mi kake ka jira ka gani tunda Addini ya bamu dama ni bazan cuci kaina ba kai dai kaje ka k’arata da guda d’aya kaida gwauro baku da maraba ba kamar in ta fara aiki” d’an ta6e baki yay ya maida idonshi kan tv, duk wannan Maganganun da suke akan kunnan Fatuu dake lafe a gefen kopar parlon Haisam sakamakon lokacin da Abbas yay mashi waya yace yana parlonshi da ya dawo daga Masallacin shigewa kawai yay ba tare da ya rufe kopar ba ita da kanta ta rufe saidae bata idasa datsewa ba, Lokacin data shigo part d’in nashi sai kuma ta tsaya tana wasi wasin zuwa wurinshin can dae ta shiga cike da tsoron abunda zai biyo baya hakan yasa ta rink’a tafiya cikin sand’a har ta haye balcony d’in ba tare data yi wani kwakkwaran motsi ba tana zuwa bakin kopar ta jiyo muryar Abbas da yake shi yana d’aga murya in yana Magana ba kamar Haisam ba, duk da shima Haisam d’in ya d’an d’aga murya don ba wuri d’aya suke zaune da Abbas d’in ba yana can bangaren armchairs wannan dalilin ne yasa ta lafe ta kasa kunne tana sauraransu cike da tashin hankalin jin akanta suke Maganar,kenan Abbas ya gano tana son Ya Handsome ta fad’a a ranta, ba komae yafi tada mata hankali ba sai Maganar Haisam ta k’arshe da yace baida ra’ayin mata biyu da kuma zance kwanciyar Fanan gadon Asibiti, hannu tasa ta rufe bakinta sosae gudun kada tay abunda zasu gane tana a wurin, a hankali jiki a sa6ule ta juya har wani duhu take gani ba tare data ankare ba wurin sauka daga stairs d’in balcony d’in kafarta ta zame ta tafi gaba d’aya ta fad’a kasa tumm k’arar faduwar har cikin falon hakan yaja hankalinsu duk suka kalli kopar parlon Abbas ya mik’e yana fad’in bari ya duba yaga miye, tana fad’uwar cike da k’arfin hali duk da buguwar da tay ta yunk’ura ta mik’e da sauri ta nufi hanyar fita tana kaiwa bakin fence p door Abbas na fitowa ta fice da sauri saidae yaga bayanta kawae lokaci guda kuma ya shaida wacece, d’an cije baki yay had’i da girgiza kanshi cike da tausayawa ya ayyana a ranshi kenan ma tana zuwa Haisam d’inne bai sani ba,juyawa yay ya koma cikin falon ganin Haisam na kallonshi yasa yace mashi baiga komae ba k’ilan yara ne ya d’aga mashi kai kawae, komawa yay ya zauna idonshi akan Haisam dake kallon tv ya rasa mima zai ce mashi ya yarda abunda ya fad’i mashi game da Zarah gaskiya ne, can dae yace “H,Zakee yanzu in da gaske Zaraah son ka take ya za’ai?” juyowa yay ya kalleshi ya d’age gira yace “kai zan tambaya wannan ai tunda kai ka kawo issue d’in” shiru Abbas yay shi kanshi baisan mi zai ce ba, ta ko ina abun ba mai sauk’i bane ganin Haisam ya kafe shi da ido yasa yace “kawae na tambayane amman in ma hakanne bai wuce ka bata hak’uri ba in ace ta fad’a maka, yanzu kuma da bata fad’i maka ba rashin sanin is the Best ka rabu da ita kawae, amman fa kasani kayi breaking heart d’in yar Mutane wllh” d’an Murmushin gefe yay kawae ya maida idonshi kan tv don shi jin Abbas d’in kawae yake ba don ya yarda ba.

 

Tafiya take saidae bata san inda take wurga k’afarta ba don wani duhu take gani Allah dae ya taimaka ta k’arasa gida lafiya hannunta guda dafe da gaban kanta, tana shiga d’akinta ta aje jakar hannunta a tsakar dakin tasa hannu ta cire hijab d’in jikinta ta cillar da ita can gefe ta haye can tsakiyar gadon ta zauna ta d’age k’afafunta sama tasa hannuwanta ta k’ank’amesu tana ta zare ido yayin da zuciyarta ke tariyo mata maganganun Haisam can ta saki k’afafun ta kama kanta da duka hannuwanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka cikin kukan take fad’in “Ni in baka aure ni ba Ya Handsome ba gadon Asibiti zan kwanta ba mutuwa zanyi……” haka ta dingi maimaitawa can ta sark’e ta fara tari kan kace mi sai amai ta saddo kanta k’asa don ta kasa saukkowa daga gadon dama kitson kalaba ne akanta gaba d’aya sun saukko har k’asan d’akin kan carpet,tun tana aman d’an Abincin da ta ci har takai ba komae da yake fitowa sai kumallo gaba d’aya ta gama galabaita, tana cikin wannan halin Amadu ya shigo ya shiga toilet bayan ya fito yana niyyar fita ya jiyo kakarin aman da take yi da mamaki ya juya ya nufi d’akinta don shidae yasan ta tafi islamiyya don data dawo baiga wucewarta ba, lokacin da ya d’aga labulen d’akin cike da al’ajabi yake kallonta yama kasa shiga saboda tsoro, ganin halin da take ciki yasa ya kira sunanta shiru bata amsa ba har saida ya k’ara kiran nata sannan cikin mawuyacin hali ta d’ago mashi hannu tace “Kawu Amadu…..” yana jin hakan ya kutsa kai da sauri ya nufi inda take yasa hannu ya d’agota ya maidata saman gadon sosae kafin ya zauna yana kallonta a razane ganin yadda ta koma sai faman nishi take yace “miya sameki ne haka, ba kin tafi makaranta ba?” fashe mashi tay da wani kukan tace “Son Ya Handsome nike amman shi baya sona” waro ido Amadu yay baki bud’e yake kallonta jin abunda ta fada wanda bai ta6a zaton ji daga bakinta ba, mamaki shimfid’e a kan fuskarshi yace “dama saboda shine kike ta ciwo?” jinjina mashi kai tay alamar eh, wani d’an guntun Murmushin mamaki mai d’an sauti yay yana kallonta cike da Al’ajabi can yace “to ke ya akai kika fara sonshi haka ina ma kika san wani soyayya da har zaki jefa kanki cikin wannan halin?”

yunk’urawa tay da k’yar ta ja jiki ta jingina da bango tana nishi cikin jin jiki ta fara bashi labari tun farkon yadda akai ta fara sonshi dalilin Maganar da suka yi da Haulat har zuwa yanzu data je ta iske suna fira da Abbas, murus bakin Amadu ya mutu sai faman bin ta da ido yake sosae kuma yaji ta bashi tausayi don yasan wacece ita sam soyayya bata gabanta don wani lokacin shida kanshi yake ce mata in bata da saurayi taya zatai aure ta tafi ta basu wuri sai tace ai in tazama likita miji sai ta za6a,

“Na fahimci komae, kiyi hakuri kinji, naji dad’i da baki sanar dashi ba don ko kin gaya mashi ba abunda zai maki saidae ya baki hakuri tunda kinga saura kwanaki ma bikinshi kuma dama bai kamata ma kice mashi kina son shi ba duk yadda kike ganin kuna mutunci dashi sai wani abu ya ragu na daga mutuncin da yake kallonki dashi don mace da kunya aka santa balle ke da kike cikakkar bafullatana wad’anda aka sani da tantsar kunya, ba wani abu bane don mace tace tana son Namiji tunda ga misali nan akan Manzo (S.A.W) da Nana Khadija Allah ya kara mata yarda ta furta tana sonshi saidae ita a lokacin ta girmeshi kuma bazawara ce,shiyasa in budurwa ta furta tana son namiji sai ad’auketa mara kunya mara kamun kai duk da ba haramun bane”

“To Kawu Amadu ya zanyi da sonshi yana damuna baka ji yadda nike ji a kirjina ba, ba irin k’ok’arin da banyi in fitar da son nashi ko na huta amman kullum k’ara yawa yake wllh” ta k’arasa Maganar fuskarta sha6e sha6e da hawaye harda majina, Amadu dai sai kallonta yake abun gwanin ban Al’ajabi wai Fatuu ce so ya maida haka acikin ranshi yake fad’in nifa shiyasa ba ruwana da wata soyayya nafi gane ma in nemi kudi tunda naga sa Mutane hauka yake ga misali nan a gabana, a fili kuma sai ya mik’a mata hannu ta matso kusa dashi cikin sigar lallashi yace “na fahimci yadda kike ji amman ki daure ki cije ki fitar dashi zaki iya nasan ke ba raguwa bace kar ki bari sonshi yay galaba a kanki ya rusa maki mafarkinki na zamowa kwararriyar likita da muke burin yin Alfahari da ita bama mu kadae ba gaba d’aya k’asa zatai alfahari dake in kika dage, lokacin sai kiga Allah ya kawo maki wanda ma yafi shi” da sauri tay mashi wani kallo wanda ya fahimci kona miye yace “nasan Ya Haisam na dabanne samun irinshi zai matuk’ar wuya amman fa bawai baza’a iya ba shima ai cikin Mutane aka sameshi ko to tabbas akwae wasu irinshi wanda ma suka fishi komae, kyau, nasaba da sauransu ke dai kawae ki dage ki cimma burinki zaki ce nina fad’a maki zaki ga yadda maza da suka amsa sunansu zasu yi rububin samunki don kema d’in sarauniyace cikin mata Allah ya baki komae sai abunda ba’a rasa ba tunda mutum tara yake bai cika goma ba amman dae dole sai kinyi yak’i sosae da zuciyarki, sannan in kuma kika bari tay galaba akanki to kuwa zata kaiki ta baro ki ne, ki dage da Addu’a dare da rana nima yanzu tunda na sani zan tayaki da Addu’ar kar ma ki bari gwaggo taji wannan Maganar don ba lalle ta fahimce ki ba tana iya yi maki fad’a ma, kuma kar kiji haushin Haulat abunda ta fad’a maki nima kwanaki sai da nayi tunanin hakan har ina Addu’ar Allah ya tabbatar amman daga baya tun kafin in san da akwae wadda zai Aura na fahimci kawae kyautatawa ce, don haka mu bar ma Allah komae ki d’auka shi d’in ba rabonki bane don wata bata taba Auran mijin wata haka wani ma bai taba Auran matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro mashi matsayin abokin rayuwarshi in kuma shi d’in rabonki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba zaki ga yazo ya aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kad’an daga cikin ikon Allah ne Abunda baka taba tunanin zai yuwu yasa ya yuwu, kiyi hak’uri kinji d’iyata kuma yar k’anwata” ya k’arasa Maganar had’i da jawota jikinshi ya rungumeta ta gefe tay lamo tana nazarin maganganunshi acikin ranta, yayin da shima a cikin ran nashi yake fad’in dole ya k’ara kiyayar so,

 

“Amman kawu Amadu inason in daina ganin Ya Handsome yanzu, don duk in na ganshi ciwon k’aruwa yake” yaji ta fad’a cikin sanyin murya,d’agota yay yana kallonta yace “Amman baki ganin zaiyi tunanin wani abun ace ya daina ganinki kwata kwata?”

“Eh nidae nafi son hakan kawae ai dama ya kusa tafiya ko” jinjina kai yay yace “shikenan daga yanzu zan rink’a taimaka maki har Allah yasa ki daina jin son nashi idan yazo d’aukarki da safe zan sanar dashi cewa Haulat tazo kun tafi nasan in akai haka sau biyu ko sau ukku zai yi tunanin ko kuna wani abunne a Makarantar yasa kike tafiya da wuri tunda yasan kun kusa fara jarabawa k’ilan ya daina zuwa, to amman bikin nashi fa bazaki ba?” da sauri ta d’aga mashi kai alamar eh, d’an Murmushi yay ya girgiza kai a ranshi yace rayuwa kenan wazai yi tunanin hakan zata kasance a tsakaninsu, komawa tay ta kwantar da kanta a kafad’arshi duk jinta take wani iri,shiru sukai na d’an wani lokacin kafin yace “nasan kina jin yunwa ko?” kai ta d’aga a sanyaye tace “amman ban iya cin komae bakina ba dad’i” yace “daurewa zaki fa karki illata kanki da yunwa su basu san ma kina yi ba kuma ba Abunda zasu fasa koda wani abu ya sameki, bari in kawo maki abu ki ci” ta d’ago daga kafad’ar tashi ya mik’e ya fita, bada jimawa sosae ba ya dawo dama saida ya kulle shagon ya shigo gidan har ya isketa a halin, k’aton biscuit da cup cake guda biyu ya d’aukko mata da lemu ya tasata gaba bayan yasa ta wanko bakinta saida taci sosae ta rage biscuit d’in bada yawa ba yace zaije yayo salla ta daure itama tayi tace to, saida ya gyara inda tay amai sannan ya tafi, ana idar da sallar ya dawo lokacin tana kwance akan sallayar yace taje tayi wanka zata ji dad’in jikinta ya rakata kar bakin toilet d’in bayan ta shiga ya shige d’akinshi, saida ya tabbatar ta gama shiryawa ya koma d’akin ya isketa akan gado tayi lamo ya shiga ya tambayeta akwae abunda take so tace mashi bacci take son yi amman yak’i zuwa, shiru ya d’anyi sai kuma yace mata yana zuwa ya fita, mashin d’inshi ya hau ya nufi bakin hanya can wani babban chemist yayi ma mai shagon bayanin kanwarshi ce ke cikin damuwa tana son yin bacci amman yaki zuwa in akwae Maganin da zata iya sha mara illa ya bashi yace mashi akwae ya d’aukko mashi,bayan ya dawo yadda ya barta haka ya isketa sai wurga ido take ya bata Maganin yace ta bari sai tayi sallar isha tasha tace mashi to tay mashi godiya yace ba komae shidae fatan shi ta cire damuwar a ranta tace in sha Allahu zata cire daga haka ya juya ya nufi Masallaci don yin sallar isha da aka fara itama ta mik’e ta fita tayo Alwala tazo ta kabbara sallar tana gamawa ta d’aukko maganin ta sha kafin ta haye gado, lokacin da Amadu ya k’ara dawowa wurinta har tayi bacci d’an Murmushi yay a fili ya furta “ciwon so ya kama manya,wato dae ashe ciwon nan da gaske ne, nifa na d’auka duk iskanci ne mutum yay shame shame wai shi ciwon so yake, to Allah ka k’ara kare mu da sharrin ciwon so Amin” daga haka ya kashe mata hasken d’akin ya tafi. Bada jimawa ba gwaggo ta dawo tana shigowa gidan d’akin Fatuu ta nufa bayan ta kunna globe ta hangota kudundune saman gado tana ta bacci a ranta ta ayyana yau da wuri akai bacci kenan ta juya bayan ta kashe hasken, tana fitowa tay kacibus da Amadu da ya shigo yana k’ara mata sannu da zuwa don yayi mata a waje,tace “Fatuu Lpy dae ko naga tayi bacci da wuri” da d’an Murmushi kan fuskarshi yace “Eh to da sauk’i tace man wai kanta na mata ciwo shine na bata Magani ta sha”

“Bata ma je islamiyya ba kenan” yace “a’a taje” jinjina mashi kai tay tana shirin nufar d’aki shima ya juya yaji ta tambayeshi Fatun taci Abinci kuwa yace mata eh taci daga haka ya fice itama taci Abinci

tayo wanka ta kwanta don a gajiye take.

 

Tun bayan da ya gama komae ya kwanta Maganar Abbas ke ta mashi kai kawo acikin ranshi, duk da bai gasgata ba amman kuma wani sashi na Zuciyarshi yana neman takura mashi da zancen, kwance yake jikinshi sanye da sleeping dress riga da wando farare masu laushi yana facing saman d’akin sai faman tunane tunane yake, ba Maganar data fi damunshi sai ta Abbas da yace ya sani yay breaking heart d’in yar Mutane, hannu ya kai ya shafi forehead d’inshi ya bar hannun ba tare da ya cire ba idanunshi a runtse ya fara tariyo rayuwarsu da Fatuu tun farko har zuwa yanzu,wani lokacin yay d’an Murmushi wani lokacinma yar dariya yake har hakoransa su bayyana a haka har ya gangaro zuwa girmanta gaba d’aya rayuwarta cike take da nishadi da wuya kaga tana k’unci, ko ta d’aure fuska na d’an lokaci ne zata washe kaga tana dariya, in bai manta ba zai iya cewa rabon da ya ga farinciki akan fuskarta tunda suka baro Ajiwa Dam ne, a hankali ya cire hannun dake dafe da goshinshi ya bud’e idanuwanshi, yunk’urawa yay ya tashi zaune ya jingina bayanshi da headboard ya kai hannu ya d’auki wayarshi dake kan side drawer, bayan ya bud’eta direct images dake a gallery d’in wayar ya shiga yay scrolling har zuwa inda pictures d’in da sukai a Ajiwa suke ya fara kallonsu da Murmushi akan fuskarshi, kai da kaganta a hotunan zaka fahimci tana cikin tsantsar farinciki ba kamar yanzu ba duk ta canja kamar ba ita ba, a hankali ya maida wayar inda ya d’aukko ya ajiye ya d’age kanshi sama yana jin wani iri a zuciyarshi lokaci guda ya ayyana in dae da gaske shine silar shigar Zaraah halin data ke yanzu bai ji dad’in hakan ba………..

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button