Mawaki Rarara Yafi Da Yawa Cikin ‘Yan Siyasarmu.
Akwanakin Baya Ne Mawakin Siyasarnan Kuma Shugaban Na Mawaka Alh.Dauda Adamu Kahutu Rarara Ya Rabawa Al’umma Mabukata A Kauyensu Na Kahuta Wanda Ya Raba Buhu Dubu Biyu Da Tamanin (2080) Hadi Da Kudin Cefane .
A Jiyane Mawakin Ya Sake Irin Wannan Rabo Na Kayan Abinci Da Kudin Cefane Wanda A Kalla Ya Raba Kusan Buhu Dubu Biyu Da Wani Abu Ga Kuma Kudin Cefane Babu Shakka Wannan Abun A Yabane Kuma Yakamata Sauran Jama’a Masu Arzikinmu Ko ‘Yan Siyasunmu Suyi Koyi Dashi Wajan Taimakon Al’umma Musamman A Wannan Lokaci Na Tsadar Kayan Masarufi Da Rashin Kudi.
Kamar Yadda Nace Rarara Yafi Yan Siyasunmu Babu Shakka Haka Abun Yake Domin Cikin 100% Na Yan Siyasunmu Befi 10% Bane Suka Tallafawa Al’ummarsu Wanda Suma 10% Din Dan Abunda Suka Bayar Be Taka Kara Ya Karya Ba Domin Kamar Ni Anan Jihata Ta Bauchi Dan Karamar Hukumar Darazo Wacce Take Bauchi Ta Tsakiya Banga Wani Tallafi Da Gwamna Ko Sanata Da Ya Kawo A Al’umma Ba Sai Wani Dan Majalisa Wanda Yanzu Yake Cikin Zango Na Biyu Da Yake Wakiltar Darazo/Ganjuwa Ya Raba Wata Yar Jaka Domin Bazamu Kirata Buhu Ba Wacce Abunda Yake Ciki Befi Shinkafa Kwano Biyu Ba Da Taliya Guda Biyu Wanda Shima Rabon A Cikin Kashi 100% Na Al’ummar Yankin Na Darazo/Ganjuwa Befi 0.5% Bane Suka Samu Amma Duk Da Haka Ma Iya Cewa Yayi Kokari Domin Duk Cikin Namu ‘Yan Siyasun Shine Ya Kawo Tallafin.
Daga Karshe Muna Yiwa Alh.Dauda Kahuta Rarara Addu’ar Allah Ya Saka Masa Da Alheri Allah Ya Cigaba Da Bashi Nasara A Cikin Rayuwarsa Yadda Yake Ciyar Da Al’umma Abinci Shima Muna Rokon Allah Ya Ciyar Dashi Abincin Aljanna Damu Baki Daya.