Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 71 By Ayshercool

Viper ya tsaya ƙyam yana kallon Alhaji mu’azzam da ya miƙo masa hannu.A rikice Nabila ta ce “Amm eh, ai na ma warware na ji sauƙi, ka shiga, ka jira ni a office ɗina, yanzu zan dawo”Viper ya kalli Nabila ya ce “Koma ciki” sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon Alhaji mu’azzam wada.Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa.Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu’azzam, ya sauke facemask ɗin sa yana kallon cikin idonsa.”Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da nake so, kuma nake fatan na aura?”Viper ya tsananta riƙon da ya yi wa hannun Alhaji mu’azzam ya ce “Ka gaya mata wani abu ne?””Kamar me fa?””Ka san abun da nake nufi” yayi maganar yana ƙara tsare shi da ido.Alhaji mu’azzam ya ce “Kana tsoron wani abu ne?””Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaɗi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara, nike da alhakin kai ƙarshen wannan lamarin, idan ka yi wani yinƙuri da zai kawo tangarɗa ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa”.Alhaji mu’azzam ya yi murmushi ya ce “Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma Nabila, kar ka zama mai……”Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma” ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu’azzam ya mayar da facemask ɗin sa ya bar wurin.Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ɗin ta, cike da fargaba da tsoro.Kankarofi ya turo ƙofar office ɗin Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya ƙarasa ya ce “Madam ya na ganki a tsaye ne?”Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce “Bisimillah zauna mana”Ya zauna ya ce “Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ƙarfin jikin?”Ta ce “Jiki da sauƙi Alhamdilillah””Amma dai babu wani mummunan rauni ko?”Ta ce “Eh, gocewar ƙashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sauƙi””To Alhamdilillah, na ji daɗi ƙwarai, ya shari’a kuma?”Tayi murmushi ta ce “Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana””Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na miƙa buƙata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office”Ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce “Wahalar da kai kuma?”Ya kwantar da murya ya ce “Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala””Matanka fa biyu, ni gaskiya…”Ba kya son mai mata ko?” Ta jinjina masa kai alamar eh.”To meyasa?””Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi”Yayi dariya ya ce “Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ƙaddararsa. Da dabara da wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ƙaddara, da wataƙila haryanzu fatima tana raye da ni ta aura””Wacece hakan?””No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na taɓa ƙallafa raina a kan aurenta, Allah bai yi ba””Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta huɗu?”Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza ɓuya.”Karki damu, labarin ne akwai sarƙaƙiya, idan ya zo ƙarshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna”Noƙe kafaɗa tayi, tana ɗan tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su tattauna wannan maganar.****Naja’atu Bunkure ce zaune a office ɗin Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta.”Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari’ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar barazana ce gareka da mahaifinka Shari’a saɓanin hankali ce”Abdul ya ce “Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon ma ki yi wani abu””Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka ɓata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwaɓe fa, zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba”Abdul ya yi murmushi ya ce “Naja’atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama”Naja ta tafa hannu ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fyaɗe ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani””Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina shi ne zata zauna safe””Shikenan, zamu ɗauki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace”Ya ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa.***Indabo kuwa gaba ɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, tun yana ƙirga adadin shigarsa banɗaki, har ya sare lissafi ya ƙwace masa.Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper ya kira shi a waya.Embassy ɗin Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce.Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa ɗa? Amma ya za ayi common ɗan daban gari, ya saka a kama masa ɗa a ƙasashen ƙetare?.Waya ya ɗauka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ƙafar da ake yi, wurin kama Aminu Viper, tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a ɗauke shi daga garin kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum ɗaya, alhalin yana yawonsa a gari, da aikata abun da yake so.Yayi ta bashi haƙuri, tare da bashi tabbacin suna iya ƙoƙarin su, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan ɗan daba guda ɗaya tal har haka, ya din ga ɓata lokacinsa a kansa.Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu karɓi aikin daga hannunsa su bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki.Shi ma haƙurin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper.***Abdul da la’asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi ɗai-ɗai a kan gado.Ta buɗe ƙofa ta fito, ta tarar da shi ta ɓata fuska ta ce “Abdul meye haka?”Ya buɗe ido ya kalleta.”Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli takalmi har bedroom ba a wancan ɗakin nake ajiye maka ba?Lumshe idanunsa ya yi, ta ƙarasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa, dan ta san ƙarshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema.Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin ɓalle masa labcourt ya cigaba da shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel ɗin ta, ta buge hannunsa da ƙarfi ta ce “Tashi kayi sallar la’asar na san baka yi ba” ya buɗe idonsa ya kalleta.”Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la’asar””Zan yi in anjima, yanzu na gaji”Ramma ta buɗe baki ta ce “Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Saƙara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt ɗin ya ce “To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin san na daina” yana maganar ya nufi banɗaki.Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba.Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta ta san tayi ƙiba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man.Ya fito ya tayar da salla, ta ce “A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka zata zo maka a kabari” ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta ɗaukko masa azkar ta ce “Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata ɓarna kala-kala” haka ta saka shi a gaba, ya idar suka je ya ci abinci.Gaba ɗaya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi.Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya sanya yake ƙara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne.System ya kunna ya ce “Your excellency zo ki ga wani abu””Wanke-wanke zan yi na ɗora abincin dare””Karki damu, zan yi mana takeaway””Sai dai idan zaka yi wanke-wanken”Abdul ya ce “Na ji zan yi”Ta ƙaraso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya buɗo wani form ya ce “Kin san na menene wannan?””No””Form ɗinki ne na makaranta”Ta kalleshi ta ce “Makarnta kuma?”Ya ce “Eh mana, ko ba kya so?””Ina so, amma gida zaka mayar da ni?””Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ƙasar waje zaki tafi jami’a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya ba sai kin kammala in sha Allah””Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?””Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya budurcinki da na karɓa ta ƙarfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama” ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa daga idanunta.Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce “Ki yi haƙuri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ƙalubalen da yake a gabana nake ta ƙoƙarin karewa a waje ba, amma dai ki yi haƙuri dan Allah” a hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka.***Nabila kuwa da file ɗin Viper ta tafi gida, ta kai shi ɗakinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking ɗin kurakuran da aka tafka a cikin shari’ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari’ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci.Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ƙara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba.Ta ɗaukko system ɗin ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfiɗa sallaya, da kayan ciye-ciyenta, ta zauna ta cigaba da aikinta.Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana wayar, bai san tana wurin ba.”Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda ɗaya ne, nima na daɗe da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni ɗazu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ruɗe, nayi mamakin yadda aka yi mutum ɗaya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta kuɓuce mini.Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ƙarƙare wayar ya saka a aljihunsa.”Dama har zuwa yanzu baka taɓa ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?””Eh” ya bata amsa a taƙaice.”Hmm””Ko zaki bani hoton nasa ne?””Ni a su wa?””Ke a ‘yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba”Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta.****Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A ɗin Indabo ya ce “Ɗan sake duba na da kyau mana malam”P.A ya ce “Na kalleka””Shekaru huɗu rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban taɓa karɓar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ƙi ba wasu lokutan ina karɓa in yi abun da ya dace, duk da hakan ma saɓa doka ne. Ba za a haɗa kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari’a ba, idan na ci amana na tsayawa ƙarya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ƙwace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ƙwace ni? Kotun Allah saɓanin tunanin ɗan Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata buƙatar lauya, ɗan sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci.Duk da na san badaƙalar da ake tafkawa a cikin harkar shari’a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga faɗa, yar cikina ce amma ina sauraron programs ɗin ta, kuma ko kaɗan ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na karɓa, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai ɓaci. Kai in taƙaice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari’ar nan, ba a buƙatar kuskure a ciki, kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya”P.A ya jinjina kai ya miƙe tsaye, ya ce “Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai” ya juya ya fita daga office ɗin.***Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai ɗaga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan murɗaɗɗen hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na ɗan lokaci ne, ana jimawa ta manta.Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls ɗin ta, har guda uku.Bai kula ba, ya fara ƙoƙarin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing.Walid ya ɗaga yayi sallama, ta amsa ta ce “Oga walid barka da wannan lokaci””Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama’a””Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ƙi ɗagawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har haka ne?” Walid  ya kalli Viper, sannan ya ce “Wanka yake yi yanzu ya fito”Ta ce “Ai dama kai kare shi zaka yi, baka taɓa yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima”Da sauri Walid ya ce “A’a ba za a bari ba, ko na haɗa ki da shi?””Ba zai kulani ba ai na sani, shiru zai yi mini kamar kurma, in dai yana lafiya shikenan sai anjima””Kin ga Nabila, tsaya ki ji mana, gaba ɗaya ke ce baki fahimci Al’amin ba, ba wulaƙanta ki yake yi ba””Ba wulaƙanta ni yake yi ba kace? Idan ba wulaƙanci ba, mai zai sanya ya ce baya so na, wallahi ban taɓa cewa ina son wani ba, ina zaman zamana, ƙaddara da rashin ya ja ni ya kai ni har in da yake, yayi ta wulaƙanta ni bai damu da rayuwata ba, amma ko haushi bana ji naƙi zuciya, ko kwana biyu nayi ban ji ɗuriyarsa ba sai na damu” ta ƙarasa maganar cikin damuwa, da alama abun ya na damunta sosai da sosai.”No, Viper mutumin kirki ne, kuma abun so, in dai ka zauna da shi zaka so shi, saboda yana da halaye masu kyau sosai da sosai, kina kallon muma da muke tare da shi, wasu lokutan haka yake yi mana, amma muna duba halaccinsa a garemu ne, kema baki fahimce shi bane””Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga siraɗin gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini”Walid ya ce “Ki yi haƙuri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke””A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?” Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta.Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ɗaga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar aljihunsa ya yi gaba.***”Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse” Sumayya ta yi maganar tana ƙare mata kallo.Baba magajiya ta ce “Gara dai ki yi mata, ko ta ji, taƙi gaya mini meyake damunta, sun samu saɓani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ƙarewa take yi kamar kuɗin guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta” Sumayya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce “Wallahi kuwa baba magajiya, da ‘yar ƙibarta tafi kyau, haba jarumar mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ƙwarin gwiwar? Muje mu zanta na ji menene ya faru”.Suka tafi ɗakin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce “Gaya mini menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi faɗa da Abba, me ki ka yi?”Ta kalli sumayya ta ce “Sumayya haka soyayya take dama?””Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?”Ta girgiza kai ta ce “Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya.Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ƙarƙashin ƙasa da kaina””A’a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ɓaci””Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani abun ba za ayi mini shi ba””Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya”Ta numfasa ta ce “Ƙaddara ta kaini ta baro sumayya”Sumayya ta waro ido ta ce “Kamar yaya?””Son abun da ba zan samu ba nake yi””A’a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ɗin tukuna ma dai”Nabila ta tashi, ta saka key, ta buɗe wardrobe ɗin ta, ta ɗaukko file ta zo ta ajiye a gaban Sumayya.Sumayya ta ɗauka ta fara bubbuɗewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin matsananciyar kiɗima da tashin hankali ta ce “Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila”Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ƙasa.Ta daki kafaɗar Nabila ta ce “Kin san in da mutumin nan yake, da gaske haɗuwa ku ka cigaba da yi da shi, har ki fara son ɗan daba?””Ɗaga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya””Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta haƙilo yana fama, ko ɗazu an kawo mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ɓaɓatu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya ne?””Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka faɗa tabbas ina haɗuwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan taɓa bari hukuma ta kama shi ba”Sumayya ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila? Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ɗan daba mashayi, dan ta’adda?”Ta girgiza kai ta ce “Sumayya ƙaddara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da zaɓin yin wanda ya dace”. Ta tashi ta nufi wardrobe ɗin ta, ta mayar da file ɗin.”Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba””Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne dai-dai”Sumayya ta ɗauki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan bata taɓa tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ɗin ba.Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ɗin jami’an tsaro, ta ɗauki, jakarta ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan.Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce “Sir dan Allah ka yi wani abu a kai, rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ɗan ta’adda take shirin kasadar karewa”Yayi murmushi ya ce “Sumayya ƙawarki ba ta ji, bar ta ai ɗaukaka take nema, mu yi mata fatan nasara””A’a sir, dan Allah ba zata iya ba”Kankarofi ya ce “Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ɗin sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu’a, in da ki ka ga ana buƙatar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi ƙoƙarin dakatar da ita, wannan gargaɗi nake yi miki” ya kashe wayar.Sumayya ta ce ‘Naga ta ta kaina ni sumayya”***Suna zazzaune a ɗakin, suna ta shan sigari, ya ɗaga kai kawai ya ganta a tsaye a ƙofar ɗakin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba.Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask.Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye.Liti ya ce “Su ‘yar anace ce da yamaccin nan ashe” Walid ya ce “Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da hayaƙi, gashi ke ba kya son hayaƙi”Viper ya yinƙura ya tashi, ya ce “Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta jagwalgwala ki” yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a  jiki ta fito da harshenta.Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ɗin sa, irin ina saurarenki.Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara gajiya, yana zuƙar sigarinsa, yana fesarwa a gefe.Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ƙasa, ya kalleta amma ta haɗe rai.”Ina jinki ya aka yi?””Alhaji mu’azzam da ku ka haɗu, dama ka san shi ne?””Haka ya ce miki?””A’a, tambayarka kawai nake””Ki bar maganar sa kawai””Saboda me?”Ya ce “Saboda haka na ce””Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda zan ɓullowa lamarin, ka gaya mini shi menene alaƙarka da shi?”.A hasale ya ce “Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ɗin ba shi da wani amfani”.”Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam” tayi maganar tana kallon ƙwayar idon Viper.

Ayshercool 08081012143

Back to top button