Hausa novels

Gargadar So Chapter 44 By M Shakur

Rasa tacewa Mama tayi amman taki giving up ina sai inda karfinta yakare kawancen nan saisun dawo dashi, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “Malam duk naji bayaninka kuma banki ba hujjujinka masu karfi ne, konine naga wacce ke shirin cutar da yarana zan dakatar, amman kuma ka kalli abin ta wannan fuskan mana, ina duk ba Aliyu ne sanadi, dalili, da haddasanan fadan ba? Malam ai komi yakare yanzu, Hawwa tayi aure, babu sauran fada kuma” Baba yayi murmushi irin na manya yace “ke mace ce Maimuna bazaki taba gane yanda zuciyan maza yakeba, idan namiji ya daurama kansa soyayyan wata har abada soyayyan nan baya fita daga ransa, daukeni a misali har gobe ina matukar kaunar marigayiya mahaifiyar Hawwa, shi son gaskiya baya mutuwa, inhar Ni’ima natare da Hawwa dole zata dinga ganin dabi’u wajen mijin nata dazai dinga konamata rai daganan kishi ya motsa afara tunanin illata wani ko kisan kai, maganin kar ayi karma afara naga Ni’ima, Ni’ima taganni, ayayyafe amman adawo tare ban aminta ba, kawai ahakura Aliyu yariga yabata komi, Hawwa takamu da hawan jini hakkinane na kareta gwara ta nisanci mutanen da zasu bata matsala arayuwanta wato Ni’ima da Aliyu dan haka kiyakuri kawai Maimuna, ahakura da kawancen tunda yazo irin gabar nan, zanje nayi kari daganan naje asibiti” yayi maganan yana mikewa bayason zancen bakaramin daurewa yayi yamata maganan hankaliba amman ya tsani Ni’ima da dabi’un datayi, yarinyar ta basa tsoro baitaba sanın haka Ni’ima take ba, tashi Mama tayi dasauri tace “dan Allah Malam ayakuri, Malam kabar yaran nan sudawo tare sunason junansu Malam” dakin Umma Baba yafada Umma ta watsama Mama harara dan basa shiri sabida uwar kawar Hawwa ce rai ba dadi Mama tawuce tabar gidan.Kari Baba yayi tareda Ramla sannan ta shirya suka fito tare wajajen 11 daidai motar Baban Yaseer na parking Baba ya tsaya turus yace “je gida Ramla natashi tafiya saina kiraki” komawa ciki tayi, Baban Yaseer yafito yazo wajen Baba cikeda mutunci suka gaisa Baba ya zauna kan kujera shikuma ya zauna a tabarma yadan sosa kai yace “Baba zan fara da baka hakuri bisa ga abinda yafaru jiya, Baba kayakuri yawancin maganganun da Ni’ima tayi na tabbatar cewa karya tama Hawwa, kowa yasan hakan ba halin Hawwa bane, Baba dan Allah kayakuri” murmushi Baba yayi yace “bakomi nahakura komi yawuce” ijiyan zuciya yasauke yace “saikuma ahhhhhmmm” yadanyi shiru yana sosa kai Baba yace “ina jinka” kanshi ya sauke kasa yace “Baba inaso kabani daman auren Hawwa! Baba ina matukar son Hawwa, namaka alkawari Baba zan kula da ita nakuma riketa amana Baba, Baba dan Allah dabi’un Niima kada su sa ka ki bani wlh Baba zan kula da Hawwa namaka alkawari babu abinda Ni’ima zata iya mata”Ijiyan zuciya Babayasauke anatse yace “Aliyu” dagokai Aliyu yayi yakalli Baba yace “Na’am Baba” Baba yayi murmushi yace “Aliyu kai d’a nagari ne da babu iyayen dabazasuyi alfaharin samunka amatsayin d’a ba, Kanada hankali natsuwa da kirki babu wanda bazaiso yahada zumunci dakaiba” yayi shiru chan yace “Allah yana jarabtanmu da abubuwa da dama, wani zubin yana nunamana duk yanda mukakai ga son abu bamu samuba sabida banamu bane” faduwa kawai gaban Aliyu keyi Baba yace “ina sonka Aliyu sosai amman y’ata Hawwa bataka bace, jiya nadaurama Hawwa aure da Ibrahima, Hawwa tariga tazama matar wani!” Faduwa gaban Aliyu yayi dasauri yakalli Bab idanunshi har twitching suke sabida bugawan kirji yama kasa magana Baba ya lumshe idanu yabude, Baba yace “kayakuri Hawwa tayi aure, inaso kaima kaje ka gyara rayuwanku da Ni’ima, ku daidaita kanku, ku shirya ku kula da yaranku, yanzu Hawwa tafita daga tsakiya, babu wani abu dazai kara jawo muku fada, inaso naga ka koma yanda kake d’a da Ni’ima gwanin ban sha’awa, ku manta da komi acigaba da rayuwa anama juna fatan alkhairi kaji Aliyu”baki Aliyu yabude zaiyi magana saiga hawaye mai zafi sun sauko daga idanunshi dasauri yakai hannu ya share yajuyar da kai yana huci zuciyanshi na kuna yanason Hawwa sama da tunanin kanshi, waye Ibrahima? Yaushe Hawwa ta sansa? Ko sanarwan da Baba yayi sanarwa a masallaci ne yasa aka samo Ibrahima? Zafi yaji ranshi namai hawaye suka kara zubowa ya share da sauri still yakasa magana, ba karamin tausayi yabama Baba ba, kana gani kasan Aliyu na son Hawwa sosai, ahankali yace “kayakuri Aliyu, nasan yanda so yake, baya neman shawara idan zai kamaka, amman kayakuri, ka rungumi kaddara, ka gyara aurenku da Ni’ima ka rungumi iyalinka kaji” gyadama Baba kai yayi yakasa motsi Baba yayi shiru yana kallonshi yakai kusan 20min ahaka sannan yatashi muryanahi narawa sosai kaman zai fashe da kuka yace “natafi Baba” Baba ya gyadamai kai duk jikinshi yayi sanyi but this is the right thing, yawuce yatafi Baba shima yayi shiru, saida yaga barinshi unguwan ya kwalama Ramla kira suka tafi abinsu.Da kyar cikin ikon Allah Baban Yaseer yakai gida gateman dinsu na gaidashi ko iya amsawa baiyiba yawuce yabude flat nasu yashiga yashiga bedroom nasu yazauna yafara fuzar da iska da baki sosai, hawaye masu dumi suka shiga zubomai yasan da Ni’ima duk batai haukan nan ba wlh Baba zai iya bashi Hawwa, yanzu ga shi Baba yaki, yasan rigiman Ni’ima yasa Baba yaji gwara ya aurar da Hawwa ga kowama ko wutan da Ni’ima ta kunna tamutu, iska yakara fuzarwa hawaye masu zafi suka zubomai baitaba sani rana zaizo dazaiji yanajin tsanan Ni’ima ba sai yau jiyayi ya tsaneta completely, bazaima so yaganta ba ko ya kalleta sai iya shaketa, yana ahaka wayanshi yahau ringing share fuskanshi yayi ya daga wayan Ni’ima yagani na kiranshi harta katse wayan bai daukaba tanamai kira na biyar ya daga yakai kunne baiyi magana ba, murya chan kasa tace “Baban Yaseer dama nakira nacemaka kayakuri ne da duk abubuwan dana maka natuba dan Allah let’s forget the past and move on for the sake of yaranmu” Wani kaluluwan abu Baban Yaseer yaji yana tasomai yana zuwa wuya Ni’ima tace “Babyna kaji nasan bazaka iya fushi dani for long ba please kayakuri” kasa rike abun dake wuyan nashi yayi cikin tsantsan tsana yace “bazan taba dawo dake ba, and for yarana ko da ke ko bake zasu rayu, na tsaneki Ni’ima na tsaneki da ko muryanki banso na sake ji, I hate you with everything in me, na tsaneki” yazare wayan ya katse ya jefar yazauna akasa yana dafe kanshi yashiga kurma ihu sosai kaman mahaukaci he’s so heartbroken, gateman yazo yana buga kofansu yana “Alhaji lafiya, Alhaji Alhaji”.

Back to top button