Labarai

Fatalwar Delu Part 16

Fatalwar Delu Part 16

 

🤡 FATALWAR DELU 🤡

Part 16

Kingboy Isah 👑

Short story

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

 

Zuwa can kuma sai zuciyata ta fara tunano mini da abinda na manta tun farkon fitowarmu. Wato ambaton Allah, na kanyi mamaki yanzu ta ya idan wani abun tsoro ya tunkaro ni bana yin yunkurin neman tsarin Allah daga garesa, idan da munayi na tabbata duk wasu abubuwan sai sun zo da sauki. Amma a zuciyata ina da yakinin akwai suddabarun da su Surayyah suke yi mun wanda nake mantawa da ambaton Allah ko kokarin yin karatu yayin da suke kokarin cutar da mu. Au’uziyya na shiga karantowa a zuciyata yayin da naji tayi nauyin karanta addua’a ko yin karatun alqurani. Cikin kankanin lokaci na fara jin dukkan karatu da addu’oin da na iya a makaranta suna dawowa kaina, kai tsaye na daga kai na kalli Surayyah hade da cewa, “Tabbas kinfi karfina a fanni da dama domin Allah ya baki tarin baiwa, sai dai kuwa dukkan baiwar da Allah ya baki kin watsar da su a banza tunda kinki tsayawa ga Allah ki bauta masa domin lahirarki tayi kyau. Daga karshe kin watsar da asalin yadda Allah ya halitto ki kin shiga rigar wata kina tutuya da sunanta, karyar da kikawa kanki wai kece Surayyah alhalin kuma Surayyah da kike magana ta dade da mutuwa tana can kwance a kabarinta, wanda ya mutu baya dawowa duniya ke kawai aljana ba Surayyah ba”.

“A cikin aljannun ma ke shaidaniyar aljanace, wacce ta ki yarda da halittar da Allah yayo ta da shi take kokarin canzawa kanta halitta da asali. Ba kin tambayeni taya zan iya ganin bayanki alhalin kin fini karfi da baiwa ba? To ki sani wanda ya baki baiwar nan nima bai barni haka ba, ya bani tawa baiwar wacce in nayi amfani da ita baki isa ki cutar dani ba. Tun farko sakacin mantawa da shi a lamuranmu ne ya jefamu cikin wannan mawuyacin hali, amma ki sani yanzu na dawo cikin hayyacina”. Ko da na zo nan a zancena ba zato ba tsammani sai gani nayi Surayyah ta mike tsaye ta daga kai sama ta kwarara uban ihu mai karfin gaske, nan take gashin kanta ya mimike tsaye alamu na nuna cewa ta cika da matukar bacin rai. Ai kuwa cikin wata iriyar murya dake fitar da amo da karsashi ta ce, “Nura yau idan ban kasheka ba tabbas ni ba Surayyah bace ‘yar Delu. Dole na kashe ka, dole na kasheka yanzun nan”. Ta karasa maganar cikin hargagi, nan take kuma ta dunkule hannunta da iya karfinta ta kawo min naushi dai-dai fuskata. Ina kwance cikin igiya ai kuwa da karfi na wuntsilar da kaina na gocewa naushin ta sama kasa, karfin naushin nata sai da ya huda kasar wajen dake yashi ne hannunta ya shige a ciki yar kura ta tashi.

Na tabbata in da naushin nan ya sameni to fa sai dai uwata ta haifi wani domin idan ana wuce lahira sai na wuce, wannan ya tabbatar min da cewa tayi dukan ne da nufin ta hallakani farat daya, kasancewar saitin kaina ta kawo dukan. Nan take ba jinkiri na fara karanta ayyatul qursiyyu da dukkan karfin muryar da ta rage min. da gamawa na tsallaka bakara, gani nayi Surayyah ta dafe kai tana kwarara ihu, ga dukkan alamu radadi take ji na karatun da nake. Ni kuwa sai naki dakatawa na cigaba, duk ayar da ta zo kaina karantota nake cikin gaggawa da daga murya, musamman da na lura karatun da nake yana tasiri a jikinta. To taya ma ba zaiyi tasiri ba, bayan na gano cewa shaidaniyar aljana ce kawai ba wani fatalwa ba, cikin wata iriyar murya mai ban tsoro da fita uku-uku take fadin, “Nura zan kashe ka idan baka daina ba. Zan kasheka zan kashe zan kasheka. Ka daina”. Magana take tana rike da kanta yayin da naga tana ta mimikewa tamkar wacce wani abu yake cizonta a jiki.

 

Ina kallon duk abinda take yi dake fitilar da na yar ta haske wajen baki daya. Ba zato ba tsammani sai gani nayi fatar jikinta ta fara tsagewa daga fuska har hannuwa, tsoro ne ya cika ni amma har lokacin ban daina karatu da karfi ba, a dai-dai lokacin ne naga igiyoyin da suka daureni sun kunce da kansu, ina ganin haka na yi saurin mikewa tsaye ina kallonta yayin da nake cigaba da karatu. Kafin lokaci kankani sai ga halittar Surayyah ta canza daga suffar mutum zuwa wata mummunar suffa da ta fi dacewa a kira da dodanniya. Ita ba dabba ba ita ba mutum ba haka zalika ita ba aljana ba, lokacin da nayi arba da wannan suffa tata ba karamin firgita nayi ba amma sai na daure na cigaba da karanto duk ayar da ta zo raina da karfi, ganin har lokacin halittar na kwalla ihu tana rike kai. Zuwa can ta dago da jajayen idanunta ta kalleni nan take kallon da tayi min ya haifar da tsoro a zuciyata naji kamar na juya da baya na ruga a guje, amma sai na dake. A hankali ta fara tunkaro inda nake tana fadin, “Idan baka daina karatun nan ba sai na kasheka, ka daina ka daina na ce”.

Ai ina ni yanda take matsowa gareni ma sai naji na kara kaimi wajen yin karatun da karfi. Wani irin ihu ta bude katon bakinta tayi, wanda da faruwar haka sai ji nayi wata iska ta kwasheni sama ta makani da kasa, tabbas na daku dai har sai da nayi tunanin na karya hannu ko kafa. Yin shiru da nayi ina wash! wash! Ne ya ba Surayyah dama rugowa a guje ta yo kaina, ai kuwa ina kyalle ido na ga tayo kaina cikin azababben gudu da ba irin na mutane ba, sai kuwa na daga murya daga kwancen na fara kwalla karatu da karfi makoshina har dishewa yake. Da faruwar haka Surayyah ta durkushe a wajen kafin ta karaso gareni tana ihu. Ni kuwa ina ganin haka na yunkura da kyar saitin kanta daga nesa kadan nake karato ina tofa mata, ba’a dade ba naji sautin ihun da take ya karu tana kiran “Mama mama zai kasheni”. Ba dadewa kuma sai gani nayi ta kama da wuta tana ci. Wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyata ai kuwa na kara kaimi wajen yin karatun.

Fatalwar Delu Part 16

A bangaren Boka Girgije kuwa lokacin da ya rage daga shi sai Fatalwa Delu nan take tsoro ya shigesa ya fara zare ido musamman da ya hasketa ya ga ba abinda take sai murmushi da fuskar nan tata fari fat babu kyan gani. Layoyi ya shiga zarowa kala-kala yana karanto kalmomin tsafinsu yana jefa mata amma bisa ga dukkan alamu abin yaki tasiri domin ita sai dariya take, hakan ne ya kuma bashi tsoro. Daga karshe ma da ya lura da cewa layoyin nan ba sune mafita ba sai ya cire jakar ya ajiye a kasa nan take aka shiga kallon kallo tsakaninsa da ita. Zuwa can kuwa sai ya saita hanya ya zuba a guje, irin gudun da ake cewa na ceton rai. Hannunsa daya rike da fitila daya kuma sandarsa wacce har lokacin bai rabu da ita ba. Har zuwa lokaci babu riga a jikinsa daga shi sai jan wando sai kuma jan kyalle da ya daura a kai. Yana cikin gudun nan ya rika jiyo dariyarta a bayanshi amma da zarar ya juya ya haska sai ya ga wayam ba komai. Bai ankara ba sai ji yayi ya ci karo da mutum, yana dago kai ya ga ba kowa bane face Fatalwa Delu tsaye tana kallonsa tana kyalkyala dariya, baya da baya ya fara ja yama rasa me ya kamata yayi, domin ya tabbata gudu ba mafita bane a garesa ba zai taba iya tserewa fatalwar nan ba. “Dan Allah kiyi hakuri Fatalwa Delu ba da ni ake rigimar nan ba wallahi tsautsayi ne ya jawo ni ciki, wannan dan iskan yaron ne mai taurin kai ba yadda banyi ba domin a fasa zuwan nan da ni amma yaron nan sai da ya tunzura ni na taho”.

Wata gigitacciyar dariya Delu ta kyalkyale da ita, jin haka ya kara jefa tsoro a zuciyar Boka Girgije yana karkarwa ya ce, “Wallahi laifina daya shine jifarki da laya da nayi, shima ba a son raina bane don in gwada jarumta a gaban yaran nan ne, amma yanzu na amince zaki iya ramawa da dutse ma in dai zaki rabu da ni”. Yana zuwa dai-dai nan ta daka masa tsawa hade da cewa, “Shikenan tunda ka yarda in rama, maza ka tashi ka ceci kanka zan ta aiko ma jifa idan ka iya tsira da ranka daga nan zuwa gidanka to shikenan ka tsira. Amma idan ka kasa kaiwa gida ko kuma ka fadi kasa ka tabbata sai na kasheka”. Zuciyarsa ce ta shiga luguden bugu, kamar yayi kuka ya ke rokonta afuwa amma ta ce wannan umarni ne ba zabi ta bashi ba. Ba yadda ya iya haka ya tashi ya wullar da sandar hannunsa ya tattare kafar wando ya rike fitila gam sannan ya sheka a guje ya nufi hanyar kauyen nasu. Tun kan yayi nisa ya fara jin saukar dutse a baya, wannan ta sa ya fara gudun yana kokarin gaggaucewa, amma duk da haka dutsina na samunsa. Wani dutse da aka kwala mai a kai ne yasa ya ja birki yana fadin “Kai-kai, kai-kai, dan Allah kiyi hakuri Delu ki barni haka na daku”. Amma ko da ya juyo bai ga Delun ba yana cikin haske-hasken fitila ya sake ganin wani dutsen yayo kansa babu shiri ya tsugunna kasa dutsen ya wuce ta samansa ai kuwa ya tashi ya sake shekawa a guje, gashi gajere shiyasa gudun da yake baya sauri.

Suna cikin wannan dauki ba dadin ne Fatalwa Delu taji karan Surayyah, a tunaninta ba wani abu bane amma jin kara na karshe da kuma kiran sunanta da Surayyah take yi, shine ya tabbatar mata lalai ba lafiya ba, don haka cikin hanzari ta juyo ta nufi inda ta ji karan a cikin gudunsu irin na aljannu cikin lokaci kankani sai gata ta bayyana a gabansu, kusan a tare suka bayyana ita da kanin Surayyah. A lokacin Surayyah ta kusa konewa kurmus, tana ganinsu ta shiga mika musu hannu daga kwance da take wuta na ci a jikinta. Don haka a rikice sukayi kanta suna tambayar abinda ya faru da ita, “Mama ya… ya… ya kashe ni, ku gudu karku tsaya zai kasheku”. Abinda Surayyah ta shiga fadi kenan, ita kuwa Delu nan take ta fara kurma uban ihu, mai karan gaske, wanda yasa ba shiri Nura ya duke hade da rufe kunnuwansa, dama yana daga gefe yana kallonsu amma ya dakata da karatun da yake. Kokarin daga hannu Surayyah ta fara tana nuna Nura da yatsa, a dai-dai wannan lokacin ne kuma hannun nata ya langabe yayin da wata irin wuta ta kamata mai yawan gaske cikin dan kankanin lokaci ta kone kurmus ta zama bakin hayaki ta bi iska. Da faruwar haka Fatalwa Delu ta mike tana wani irin gurnani, yayin da shima yaron karami kanin Surayyah ya rikide zuwa katon karen nan ya rika kallon Nura yana gurnani tamkar mayuwancin zaki. Hantar cikin Nura ba karamin kadawa tayi ba musamman da ya ga Fatalwa Delu ta rikide ta zama wata irin dodanniya mai matukar ban tsoro da firgici, ba shiri ya tashi ya zura a guje saboda tsorata da yayi.

 

https://aihausanovels.com.ng/labarai/fatalwar-delu-part-15

Back to top button