Page 76
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!
*ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*
Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.”
Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD’i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K’UDIRAR ALLAH….
(*Ina ma’abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma’ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)
Cikin hanzari Mahmud ya ce “A’a rumaisa kar ki ce zaki yi wannan gangancin, Mummy ta fi gaban yadda ki ke tunani”
“Shikenan saboda ana tsoron ta, sai a zuba mata ido ta yi ta abun da ta ga dama? Tayi ta yi wa mutane fuska biyu”
“Kina da gaskiya rumaisa, amma Mummy ta wuce tunaninki, ki bi komai a sannu, kar aikin da muke tayi ya rushe, ina ƙara baki haƙuri, komai zai wuce dan Allah kar ki rusa mana aiki”.
Rumaisa tayi ajiyar zuciya tare da share hawayen da ya taru a idonta.
Ta ce “Shikenan, akwai Allah ai”.
Mahmud ya numfasa ya ce “Haka ne. Ammm rumaisa”
Ta ɗaga kai ta kalleshi.
“Ya aka yi ki ka san zancen filin turaki, har ki yi wa jamil maganar, na ji zancen a bakin jabir, yana yi wa mummy”.
“Wai shi jabir ɗin nan wane irin munafuki ne?”
Mahmud ya ce “Kusan duk bakinsu ɗaya, kuma Mummy ta fara saka mini ido, shiyasa nake son ki din ga haƙuri, komai zai zo ƙarshe in sha Allah”
Ta jinjina masa kai, ta juya za ta tafi ya ce “Na ce ba” ta tsaya ta waiwayo.
“Ya ake ciki game da iman?”
“Kana da labari ai, ko ayi mata aure nan da watanni uku, ko a mayar da ita in da aka tsinto ta, haka Wambai ya ce”.
Mahmud ya ce”Ina ga rabon abokina ne ya rantse”.
“Wa kenan?”
“Yayanki umar” rumaisa ta kalleshi ta ce “Kana nufin ka san yana son iman?”
Ya ce “Na sani”
Ta waro ido ta ce “Ya aka yi ka sani?”
“Actions ɗin sa sun nuna mini, kina ganin zai iya auren iman nan da watanni uku?”
Ruma ta yi shiru sannan ta ce “Daddy, rayuwa a ƙasarmu akwai wahala sosai, yaya umar ya sadaukar da rayuwarsa a kan inganta tamu, ya riga yaya Abubakar gama karatu, ya koma master’s. Yanzu an kaiwa yaya Abubakar kuɗin aure, ya ce ba shi da shirin aure shi yanzu, dan haka ya mayar da hankali a kan ginin yaya Abubakar sosai, ya bar nasa, ga yaya Aliyu shima ya ce za a kai masa kuɗin gaisuwa, duk da yaya umar mutum ne mai zafi, amma kullum burinsa mu cigaba, duk wanda ya raɓe shi zai gane hakan.
Sun haɗa gwiwa, sun buɗe shagon sayar da takalma, shi da wani cousin ɗin mu, yana da ƙoƙarin neman na kansa, amma duk mu muke cinye komai, ba shi da komai a sanina, daga filayensu da aka ce tun kan babanmu ya rasu ya sai musu, ya fara gina nasa ya ajiye, sai babur ɗin sa, dan ma yanzu yaya Huzaifa yana ɗinki, Yasir harkar wayoyi yake, yaya Umar ba zai iya auren iman nan da wata uku ba gaskiyar magana”.
“Kina ganin zai amince ayi supporting ɗin sa daga nan ɓangaren mu?”
Ruma ta ce “Taɓ, ba zai yarda ba gaskiya”
Mahmud ya ce “I see”
“Amma ya dai rarraba takardunsa, amma dai bai samu aiki ba. Daddy dan Allah idan da yadda za ayi, ka tayani ya samu iman, yana sonta sosai, amma ban sani ba ko za a bashi ita”.
“Zasu bashi, zan san abun yi”.
“Na gode sosai Daddy”
“Ni yakamata na yi miki godiya daughter” Rumaisa ta yi murmushi, ta tafi.
Kamar wutar daji, haka aka cigaba da yi wa ammi surutu, na bata da halacci, duk irin ƙaunar da Jabir yake nunawa ɗanta, amma ace ta kasa bashi ƴa.
Laila ta din ga bata ƙwarin gwiwar ta daure, ta kawar kai, kada ta tankawa kowa.
Tsananin tausayin iman da Mai sunan baba yake yi, ya sanya kusan kullum sai ya kirata ya rarrasheta, ya bata baki, sai dai ya shiga zullumi shi dai ya san bashi da halin aure a nan da watanni uku kawai, duba da auren Abubakar suke ta shiri, kuma yana jin yadda yake ƙara so da tausayin iman, ba shi da burin da ya wuce ya ganta a kusa da shi, ya gatan ta ta, ya bata kulawa.
Babu kunya babu tsoro, jabir ya kira Adam a waya, ya ce da haɗin bakinsa da na matarsa aka hana shi auren Iman.
Takawa ya ce “Jabir ni da nake nan, ya za a yi na ziga cewar a hanaka iman”
“Saboda tun asali da na zo maka da zancen, ka ce baka so”
“And you keep going, ka dage sai ka aureta, ai Allah ba azzalumin sarki bane ba jabir, kuma shi Allah na kowa ne, tun ina nan aka fara maganar nan, sai dai bance komai ba na cigaba da yi wa iman addu’a da fatan alkhairi”
Jabir ya ce “Dole ka faɗi haka Adam, a duniyar nan waye ba ya yi wa Allah laifi?”
“Idan ma so kake ka ce ina aikata wani abun a ɓoye nima, ɗan adam ne ni, amma na san dai bai kai naka muni ba jabir”.
“Na gode sosai da sosai Adam, tukuicin ƴan uwantaka kenen, na gode ka nuna mana iyakarmu daga ni har Jamil, saboda ka auri wannan yarinyar, har ni za ta gayawa ban isa na auri iman ba, tun da yayanta yana son iman, kun kyauta” ya kashe wayar sa.
Adam ya dafe goshin sa ya ce “You again mimi? Subhanallah”
Ammi kuma rarrashin iman ta din ga yi, da nuna mata komai na Allah ne, kuma yana da iyaka, dan haka ta kwantar da hankalinta, a wannan karon ma kalaman Wambai barazana ce kawai.
Kwanci tashi asarar mai rai, takawa ya cika watanni biyu cif da yin tafiya.
Kullum idan ya kira video call zai ga kowa amma ban da rumaisa.
Yau laila ta cewa rumaisa za ta yi video call da takawa, rumaisa har da tsalle tana murna, laila ta yi dariya kawai.
An samu improvement sosai a game da rumaisa, dan yanzu tana iya turancin laila, tana ganewa har tana iya yi mata reply, sannan ta sakata ta rage tsalle-tsalle.
Sai dai bakin nan yana nan, sai ma abun da yayi gaba, tsiwa da rashin mutunci ma ba ta fasa abun ta ba in dai an taɓa ta.
Tun da ruma ta dawo gidan da zama, Samha ba ta sake zuwa sashin ammi ba, wurin Mummy ta daina zuwa gaba ɗaya.
Laila da kanta ta yi wa rumaisa light makeup, suna yi suna faɗa, ita ba za ayi mata ba, dan haka a hoda da jambaki kaɗai kwalliyar ta tsaya, ta tafi amsa waya rumaisa ta gudu.
Sai da ta je ta kuma nemo ta har da murɗe mata kunne, ta ce idan har ba ta daina taurin kai ba, to wayar ma za a fasa yin ta.
English wears ta bawa rumaisa ta saka, wando da rigarta body hook mai kyau, ta gyara mata gashin ta sosai, sannan ta kalli ruma ta ce “Banda shirme da shiririta, kin san dai abubuwan da na koya miki ko?”
“Ni wallahi kunya nake ji”
Laila ta ce “Ba zaki yi ba kenan?”
Ruma ta ɗan turza ƙafa ta ce “Anty laila wallahi kunya nake ji”.
Laila ta rufe system ɗin ta ce “To a fasa wayar”
Tayi sauri ta riƙe ta, ta ce “A’a kiyi haƙuri”
“Idan baki yi ba, ni da ke ne”
Fuskar laila ya fara gani, ya ce “Madam haka muka yi da ke? Ina budurwata ne?”
“Wai wani irin shakiyanci ne haka? Wani budurwarka?”
Rumaisa sai so take ta leƙa ta hango shi, amma laila ta hanata.
Ya ce “Eh, ba ta zama matar ba tukun, yanzu dai buruwata ce kamar yadda muka tsara, so muke mu ko yi soyayya mu ji me ake ji”
“Papana”
“Mimina” ya amsa tare da cewa “Laila hasko mini matata laila”
Tura wa ruma system ɗin ta yi, hannunta riƙe da kofin kununta, ta ce “Papa, Innalillahi yaushe rabon da na ganka? Ka yi ƙiba” tayi maganar tana dariya.
Ƙura mata ido yayi yana kallon ta, ta ɗan yi saroro ta ce “Ba network ne naga ka ƙame?”.
Tuntsirewa da dariya yayi, ya ce “Ciko ki ka fara ne?”
Tayi turus tana tunanin cikon me?.
“Cikon me?” Ta tamabaye shi cikin rashin fahimta.
Laila ta ce “Takawa ka raina yarinyar nan da yawa, ka yi a hankali fa, kar ka zo kana mata kuka”.
“Anty laila dan Allah me yake nufi, cikon me na yi?”
Adam ya ce “Madam ba ruwanki, ki ƙyalemu, mimi juyo sosai mu gani inyee”.
Ba ta san me yake nufi ba, ta ce “To ka gaya mini, cikon me?”
Takawa ya ce “Don’t mind me, me ki ka sha a kofi ne?”
Ta ce “Hmm ka san me?” Daƙuwa laila tayi mata da hannu, tana girgiza mata kai.
Ruma ta ce “To ba zan gaya maka ba, tun da dama baka gaya mini cikon me nayi ba”.
Wani lumshe ido yake yana dariya.
“Why are you laughing at me ne?” Tayi maganar tana wani lumshe masa ido da shagwaɓa.
Ba shiri ya tashi zaune, laila ta jinjina mata 👍.
Ya ce “Kaii, mimi wannan turanci haka, kar ki sa in dawo yanzu, wannan kashen idon fa, ni wannan al’amarin ne kaina ya kulle, ya daga tafiyata wata biyu kawai, in ga abu unexpected gaskiya ban yadda da ku ba. Kin ƙara ƙiba kin yi kyau, boy ma naga sai wani kumatu yake yi.
Kin ga yadda kayan nan suka yi miki kyau, rabon da na ga ko kwalli a idonki tun ranar biki, kamar na zuro baki nayi miki kiss”
Rufe baki tayi tana kallon anty laila, dan tana zaune a ƙasa.
“Daina juyawa kina kallonta, juyo sosai ni zaki kalla, so nake na tantance abun nan gaskiya ne, ko kuma yaudarata ake so ayi?”
“Wai me?” Rumaisa ta yi maganar cikin rashin fahimta, dan duk ba ta san akan me yake magana ba.
Ya ce “Zauna sosai, mana in ganki da kyau, juyo sosai”.
“To ni ka daina yi mini wannan kallon mana, Allah zan kashe”.
Sosai takawa yake dariya, ya ce “Laila you must explain this, you want scam me ba?”.
Laila ta ce “Za ka ga scam ganin idonka, time off sai wani lokacin kuma”.
Takawa ya ce “Wane time off kuma, laila zan kai ƙararki fa, ban gama ganinta ba, mimi look at me na” yayi maganar yana dariya.
“Papa ina ta so in ganka amma ka sakani a gaba sai dariya ka ke yi, kamar kaga comedy, shikenan ba zan ƙara video call ɗin da kai ba”.
Ya ce “Haba little mimi, farinciki ne ya isheni na ganki, kar ki bar laila ta haɗamu, da na dawo zamu tafi honeymoon, mu yi spending so much time together, mu fanshe tsawon lokacin da muka yi bama tare, mu buga ball tare, mu yi gudu tare ko?”
“Eh kuma zaka goyani ma”
Dariya yake sosai ya ce “Ba zaki canza ba ai”
Ta ce “yauwwa meye honeymoon, zuma da kuma wata kenan?”.
“Eh duniyar wata zamu je, mu sha zumar soyayya”
Ta buɗe baki ta ce “Innalillahi, soyayya har na ji kunya” laila ta kashe system ɗin ta ce “Sarkin shirme, sai kuma wani lokacin”.
Adam kuwa dariya ya cigaba da yi ya ce “Daga tafiyata anya laila tana da gaskiya? Allah ya kaimu na dawo gidan. Mimi rigima”.
***
Mai sunan baba ga damuwa ta addabe shi, amma ya rasa da wa zai yi sharing ɗin ta, ya kasa gayawa kowa, sai ƙumbiya-ƙumbiya yake yi.
Har gara Mahmud, ya ɗan saki jiki ya ce masa, da yana da hali da ya auri Iman.
Sai dai a hankali yake ƙara shaƙuwa da iman, yake kuma sake fuskantar ta, ita a rayuwarta sam ba ta ɗauki duniya da zafi ba, komai nata simple ne.
Waya yake yi da ita, zuciyarsa na azalzalarsa a kan yayi proposing ɗin ta, amma bai san yaya za ta kalli abun ba. Tana ta yi masa zancen shirin da suke yi a kan bikin saukar Alqur’ani da za ta yi.
“Yaya ake ciki game da maganar aurenki, kin samu wanda zaki aura nan da 3months ɗin ne? Na ga you are calm now”.
Ta numfasa ta ce “A’a yaya umar, kamar yadda ka bani shawara ne, na barwa Allah komai ina ta addu’a, na san ya isar mini, na cigaba da gudanar da rayuwata”
“Duk cikin samarin naki, ba wanda zaki zaɓa ya fito?”
Iman ta ce “Ni bani da saurayi”
“Ban yadda ba”.
“Yaya umar na daina soyayya, idan Allah ya kawo aure kawai zan yi, dama wasu wai an ce dan ina da kyau suke so na, idan suka ji bani da asali sai su fasa, wasu kuma dan ina gidan sarauta, idan suka ji bani da nasaba da sarauta sai su fasa”.
“Mhmm ke baki yadda ki na da kyan ba? You are beautiful, ban taɓa cewa abu yayi kyau ba, amma na yadda Khadija mai kyau ce”
Iman ji tayi ya fasa mata kai, wani murmushi ya suɓuce mata, ba ta taɓa zaton mai sunan baba yana magana haka ba.
“Khadija”
“Na’am yaya umar”
“Ina son ganinki, zamu yi magana”
Kasa ɓoye farin cikinta tayi, ta ce “Yaya Umar yaushe zaka zo?”
“Zan zo in anjima da yamma, ina fatan ba zan janyo miki matsala ba?”
“A’a ba matsala, Allah ya kawo ka lafiya” bayan ya kashe wayar ta ce “Allah ya sa ya ce yana so na, am already in love with you yaya Umar”.
Ammi ta samu a ɗaki, ta sanar da ita cewar za tayi baƙo, ammi ta ce “To shi kuma wanene?”.
“Ammi wani ne”
“Iman, kar dan saboda wambai ya faɗi wannan maganar, ki je ki jajubo wanda ba mutumin kirki ba, dan ke ki ka ce ba zaki sake kulawa ba”.
“Ba haka bane ammi, kawai dai na ji yakamata na sake bawa wani dama, ban sani ba ko za a dace”
Ammi ta ce “To shikenan, Allah ya jishe mu alkhairi, na san dai za ayi surutu, ki kai muku kujera ta bayan sashin nan. Ni da kin gaya mini da wuri ma, da ba zan bari ki kawo shi gidan nan ba, kar aje a ɓata lamarin, Allah ya kawo shi lafiya. Ni dai ina sake gaya miki, ba a garaje a wurin zaɓar miji iman, kar takura da matsi, su sanya ki yi zaɓen tumun dare “.
“To ammi in sha Allah”
Kamar wannan ne karonta na farko da zata fara zance, murna da nishaɗi kawai take yi.
Nusaiba ta kalli yadda take ta shiga tana fita, tana haɗa masa abun da za ta karɓe shi “Lallai da gani wannan baƙon na musamman ne, yayi awon gaba da zuciyarki da yawa”
Iman ta yi murmushi ta ce “Anty Nusy kenan”.
“Iman kiyi haƙuri, a baya nayi ƙoƙarin goyon bayan uncle J, duk da ba kya son sa, sai daga baya na fuskanci lallai, akwai ƙalubale idan ki ka aure shi, na yadda da maganar rumaisa, wanda bai tausayawa mahaifinsa ba, yaushe zai tausaya miki. Kin san kodayaushe ni mai sonki ce, ban so ki da jabir, dan muzguna miki ba my Iman”
Iman ta tura baki ta ce “Gaskiya i feel bad, na ga kamar yayata ta daina so na, ba ta son abun da nake so”
Nusaiba ta dafata ta ce “Haba my iman, ke kin san ban da kamar ki, kawai dai wanda ki ke so ɗin ne, nake ganin kamar baku dace ba, ya fiye tsauri da jin kai. Kuma bana son mutane su yi miki dariya, ace duk wannan gwagwarmayar baki auri mutum na mussaman da zaki samu kwanciyar hankali ba, ba dan ina ƙyamar sa ba, amma kin san zaku fuskanci ƙalubale”
“Anty Nusaiba ba yadda ki ke tsammani bane, mutumin kirki ne, ba wulaƙanci ne da shi ba, miskili ne, ba jin kai ne da shi ba, kama mutunci ne da rashin son raini, amma mutum ne mai tausayi sosai. A yanzu ba dukiya nake nema ba anty nusaiba, kwanciyar hankali da soyayya.ki yi mini Addu’a, idan shi ne allhairina, Allah ya tabattar mini, amma kar ki gayawa ammi tukuna, sai yazo yau na ji me zai ce mini”
“Kar ki damu, ina yi miki fatan alkhairi ko yaushe ƙanwata”.
“Na gode yayata ta kaina” Nusaiba ta yi murmushi ta fice daga kitchen ɗin.
Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daɗi, sai dai an rasa wanda zai yi magana, kasancewar shi wannan ne zuwansa na farko zance, ita kuma yayi mata kwarjinin da ya saba, ko ɗaga kai ta kasa, sai kallon wuri ɗaya kamar mara gaskiya.
“Ki yi tayi mini surutu a waya, har na rasa abun cewa, amma yanzu kin sakani a gaba kina sunkuyar da kai, kamar kinga dodo, daga gaisawa kin yi shiru”.
Muryar nan ba ƙaramin narka mata zuciya take yi ba, murmushi ta kuma yi ta sunkuyar da kai.
“Shikenan, Khadija ɗago in gaya miki dalilin zuwana wurinki” da ƙyar ta ɗan ɗaga kai.
“Kallona zaki yi, bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ƙanwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taɓa gwadawa ba ma.
Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?”
‘Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji’ ta tambayi kanta.
“Ba kya son talaka ko?’
Ta girgiza masa kai alamar a’a.
“Talk”
“A’a yaya umar” tayi maganar muryarta na rawa.
Umar ya ɗan tsura mata ido ya ce “Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faɗa, ba ta ji ne, but am good person ko?”
Ta ce “Yes you are”.
“Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu”
Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daɗe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi baƙin tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba.
Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ƙamshin turaren mai sunan baba take ji.
Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku.
Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama.
Suna zaune a falon, suna kallo, suna taɓa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye baƙonta ya kuma suka yi da shi?.
Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama.
Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ƙarasa gaban iman, ya bata envelope ya ce “Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki”
Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar ɗin yake nufi ba.
Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce “Wanda ya zo wurinki ɗazu” sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope ɗin.
Laila ta ce “Iman, sai ɓoye-ɓoye ki ke yi, yakamata ayi mana ƙarin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki” tayi maganar cikin wasa.
Mahmud ya kalli Ammi ya ce “Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?”
Jiki na rawa ammi ta ce “Ni, eh mana Mahmud mai ze hana”.
“Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?” Rumaisa ta faɗa lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi.
Bai ce komai ba ya ɗan murmusa, ruma ta ce “Waye ya kawo mana lemo?”
Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce “ko ciki zamu shiga ne?”
Ya ce “To”
Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin ɗaci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru.
A ɓangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ƙwace mata shi, ta ƙarfin tsiya.
A bedroom ɗin ta suka tsaya, ta ƙarasa ta saka hannunta, tana sake kaɗe masa makeken gadonta, da yake a ɗame da bedsheet fes da shi ta ce “Bismillah zo ka zauna”
Ya nemi wuri ya zauna a ƙasan carfet, ya ce “ki zauna, ni nan ya isa”
“To nima bari na zauna a nan ɗin, ai ba wani abu” ta zauna a ƙasa kusa da shi.
Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, farincikin ta ya kasa ɓuya, sai ƙoƙarin mayar da hawaye take yi.
Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce “Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma ɗan mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman ɗin zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaɗan ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo”.
Ammi ta ce “In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wulaƙanta mini ita ba, ba damuwa, zan iya ɗaukar ɗawainiyar komai ni nayi masa”.
“Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ƙoƙarin sa a kan kula da ita.”
“Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haɗa mana kanku gaba ɗaya ƴaƴan galadima”.
“Amin ammi na gode” ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshsheƙar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye.
Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi.
Ruma ta ce “Ammi, me yayi miki me ya ce miki? Ɓata miki rai yayi?”
Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta riƙe hannun ruma ta ce “Bayan tsawon shekaru, da fidda ran ɗa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, ɗa na ya kusa dawowa gareni, duk ƙoƙarin ki ne rumaisa na gode”
Rumaisa kasa riƙe hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce “Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi”
Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu’a, da ita da iyayenta.
“Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke ƴa ta”.
Laila ta ce “To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani”.
Nusaiba ta ce “Muna zaune ta yi mana wayo, ta ƙwace mana ammi ba”.
Bisa kasada umar yayi proposing ɗin Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji.
Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan.
Ta ɗan numfasa ta ce “Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da baƙonta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa”
Laila ta ce “Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai”
Ammi ta ɗan waro ido ta ce “Mai sunan baba wai?”
“Eh ina ga shi ne”
Ammi ta ce “Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara’a baya son mutane, mamansa na yawan faɗar zafin ransa”.
Laila ta ce “Ammi ki yi musu addu’a kawai, ke ba ga ɗanki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin “
Ammi ta ce “Haka ne, Allah ya sa kar a samu matsala daga baya, bari na ji ta bakin Iman ɗin, sai mu ga abun da yakamata ayi”.
Laila ta ce “To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya sa daga haka a samu ƙarshen wannan matsalar.
Ammi ta amsa da Amin.
Takawa na tsaye a valcony, hannunsa ɗaya riƙe da kofin tea, ɗaya kuma da takardar zanen da rumaisa ta saka masa a kayansa, sai dai kurman zane tayi, ba tare da bayanin komai ba, kuma da alama saƙo ne mai muhimmanci take son isar masa a zanen.
Kusan kullum sai ya kalli zanen nan, kuma kamar yadda ta ce kar ya tambaye ta, yasan da zarar ya matsa, ba lallai ta yi bayani.
Babban abun da ya fi ɗaukar hankalinsa, shi ne SMOKE, da ta rubuta da manyan baƙaƙe, sai daji da ta zana da dogayen bishiyu, sai aisha durƙushe a gefen bishiya ta riƙe ciki.
“Mimi what’s the meaning of this?” Yayu maganar yana shafa zanen, hawayen sa na ɗiga a kan zanen.
***
Litattafai ne a gaban Iman, tana karatu, Ammi tayi sallama, Iman ta amsa.
“Sarki littafi, ina fatan kin gama karɓo komai, da za ayi amfani da shi na bikin saukar?”.
“Eh ammina, everything is ready”
Ammi ta miƙa mata leda ta ce “Sidi ya kawo, ya ce a baki in ji umar”
Iman ta karɓa ta duba, keyholders ne, da jotter yayi mata na sauka.
“Auta haryanzu baki ce mini komai a kan yadda ake ciki ba, kin amince da mai sunan baban, kina ganin babu matsala?”
Iman ta ɗago da sauri, ba ta zaci ammi ta san waye ba.
“Ko da baki gaya mini, na gane waye, amma iman kina ganin babu matsala? Zaki iya zama da shi?”
Iman ta jinjina kai ta ce “Ammi yana da kirki”
Ammi ta yi murmushi ta ce “So hana ganin laifi, amma ya san halin da ake ciki, ya amince da hakan?”
“Eh ya sani”.
“To Alhamdilillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi” ammi ta tashi ta fita.
Iman ta bi Ammi da kallo har ta fice.
Mai sunan baba yana zaune a gaban mama, yana cin abinci, duk suna tare da su Aliyu, Abubakar yana kwance a gefen mama yana danna waya.
“Babana” mama ta kira sunansa.
A hankali ya ɗaga kai ya kalli mama.
“Ashe neman aure ka ke ban sani ba?”
Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon mai sunan baba.
“Mun yi waya da hajiya, ta ce sun baka dama ka fito, sai dai ban san zancen ba sai ɗazu da ta kirani a waya”.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.