Sirrin Rike Miji

Yaushe Mata Suke Fara Jinin Al’ada

*JININ AL’ADA…..*

πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•πŸ§•

*FUTOWA TA πŸ‘‰01*

*YAUSHE MATA SUKA FARA AL’ADA*

Mata sun fara jinin Al’ada ne tun daga lokacin mahaifiyarmu Nana Hauwa ita ce ta fara lokacin da Allah subhanahu wata’ala ya futar dasu ita da mijinta Annabi Adam saw daga cikin Aljannah zuwa duniya, bayan ya hane su da kada su kusanci wannan ita ciyar, daga wannan lokacin sai Allah subhanahu wata ala ya hukunta jinin Al’ada ga “yaya mata na Annabi Adam (AS).
Farin jakada saw yana cewa lallai lamarin jinin Al’ada lamari ne da Allah subhanahu wata’ala ya dora sa ga mata “yayan Annabi Adam (As).

Tun daga wannan lokacin mata suke jinin Al’ada har zuwa yau babu wata ‘ya mace da bata jinin Al’ada sai dai wani lokacin akan iya samu dai dai ku da basa yi.

*MU HADU A FUTOWA TA πŸ‘‰ 02*

*Rubutawa… ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
08145437040

Back to top button