Gargadar So Chapter 108 By M Shakur
Baki Khaleel yabude zaiyi magana yakasa kuka yazomai wuya, baida dauriya ko kadan when it comes to Hawwa, Hawwa tashiga kokarin kwace hannunta tace “nace ka sakeni” make mata kafada yayi Hawwa tace “Khaleel wlh wlh kaji nayi rantsuwa ko bazan zauna dakai bafa, listen Khaleel ni ba yarinya bace, nayi karatu I have a degree, I have masters, I still went ahead naje police school, currently running PHD dina but online, I’ve gathered years of experience from my field of work, I know men like you, narcissist! I’ve come across men like you, I’ve dealt with men like you, forget kama Babana kome kamusu da Ammi na da yan uwana suna sonka, but listen here basu ke zaman auren nan dakai ba, I am the one!” Hawwa tai ihu tace “I am the one in this marriage not them! I know in da ke min ciwo, I know abinda ke damunna, staying in this aure ko barinsa is completely my decision and I’ve decided nagama aurenka as of now, you married me for revenge dama duk wani abinda kakeso ka samu nothing is left, so no point nazaman auren da last last sakina zakayi dazaran ka gama moreni kuma naga ma ai kagama morewan, so ka sakeni Ibrahim I don’t want you! You’re not a husband material, you were never groomed to be a husband so I am out, I don’t want you, kai na tsaneka na tsani mai sonka ma!” Hawaye ne suka sauko daga idanun Khaleel ya lumshe idanunshi da sauri suka zubo suka gangara har gemunshi kirjinshi namai zafi sosai, Hawwa tace “bana kaunarka banama kaunar ganinka, I can’t stand the sight of you plus stink na alcohol danake perceiving a jikinka, Khaleel I hate you kasakeni!”Sake zubowa hawaye sukayi daga idanunshi, Hawwa na kallonshi ganin yaki magana kaman zata rufeshi da duka kawai dan yarike mata hannuwa ne, yanda baiyi magana ba yakara kunnata tace “Ohhkay bazaka sakeni ba?” Khaleel yasake shiru yaki cewa komi, zuciyanta na tafarfasa tace “fine! First thing idan gari yakarasa wayewa I’m going to shari’ah court to file for a divorce idan bazaka sakeni ba kotu zatasa kasakeni, idan kaki kotu zata raba auren!” Kuka dan kufcemai abaki yayi amman yayi maza yarike kallonta yayi cikin ido muryanshi yayi rauni iya rauni ahankali yace “okay!” Muryanshi sounds kaman mai mura tsabagen kuka sai kawai yasaki hannayenta yasauke su yawuce wajen kofa yabude yafice da sauri sauri Hawwa tabishi da kallo sai kawai ta duka tareda zama awajen ta rungume kafafunta tana kifa kanta akan kafafun wasu kalan hawaye na zuba daga idanunta gwanin ban tausayi.Da kyar Khaleel yakai dakinshi yana shiga yamaida kofan yarufe yazauna jikin kofan jikinshi har wani rawa yake ya rungume kafafunshi yafashe da kuka, he loves Hawwa so da baimasan daga ina yafara ba daga ina ya tsaya ba, baitaba tunani akwai ranan dazaizo wai shine ke tsoron sakin wata ba sabida he doesn’t wanna loose her.Har gari yayi haske Hawwa na zaune wajen nan da kyar ta lallaba tashiga bayi tadauro alwala tafito tai salla tazauna akan dadduman tana azkar bini bini tana share hawaye, 7 daidai ta share fuskanta tass ta mike tafada bayi, wanka tayi tafito tashiga closet ta shiga shiryawa cikin wani adire da aka mata dinkin bubu purple ta daura dankwali tadauki handbag tazari purple gyale da flat shoe tafito, babu komi fuskanta banda mai but tayi kyau, skin nata sai wani glowing yake wayanta tadauka takalli screen is 8:00 na safe flat shoe din tasaka ta warware gyalen tayafa tabude kofan ta daidai shima Khaleel na bude kofanshi suka hada ido, jallabiya ce ajikin shi fara daga gani bai runtsa ba idanunshi sunyi jazur sun kumbura, ko 3seconds Hawwa batayiba tana kallonshi tadauke kai kawai tafito abinta tana jawo kofan ba tsoro ko shakka, Khaleel ya tsaya chak yana kallonta hanyar staircase tayi tashiga sauka duk yana kallonta yakasa motsi zuciyanshi nawani irin abnormal bugawa, key motan jiya data bari a falo ta dauka yana wajen yaji tabude kofa tafita, wani irin iska Khaleel ya fuzar kaman wuta sabida zafi yana tsaye awajen yaji ana budemata gate kawai gabanshi yahau fadi, faduwa sosai, yaji jiri na dibanshi, kanshi na sarawa, dasauri yafara taba bango yana dukawa ahankali karya fadi ya lallaba ya danna wani bottun awayanshi saiga Salman yashigo dakin dagudu yace “Yallabai” yakirashi da karfi yana kallon ko’ina a falon shiru sai kawai yawuce sama ganin Khaleel gaban dakinshi akasa yasa yayi wajen dagudu yace “Sir I saw your emergency alert meke damunka”?Khaleel nawani irin nishi kaman mai shirin mutuwa yace “bring car nan banson su Momy su ganni, take me to My Doctor in our hospital” arude Salman yace “okay okay, Sir you will be okay kaji nothing will happen to you” Salman yatashi da gudu yafita waje mota yatada da kanshi yakawo har gaban flat nasu yashiga ciki yawuce sama a sume yasami Khaleel a shimfide awajen hannayenshi duka biyu a saman kirji kaman ya mutu.




