Halysaah Page 86 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 86…Khaleesat tayi shiru jin abinda yace, can ta tallabi chin dinta tana jiran jin maganar da zai yi da yace kar ta kashe masa waya, ganin shima shirun yayi babu kuma alamar zai ce komai ta langwabe kai tace “Karar min da katin za ka yi?” Taji bai tanka ta ba, after some seconds ta turo baki tace “Sai da safe” A nan taji yace “Ke…” Dariya ya bata, amma ta hade rai tace “Ban gane ba, kawai kira fa nayi ince maka ya jiki nothing more” Kallon screen din wayarta tayi jin shigowar sako taga katin dubu ashirin ya tura mata, zaro ido tayi ta bude baki tana kallon amount din, bata san sanda tayi dariya ba tace “Ni nace maka bani da kati da zaka turo min har na 20k?” Taji bai tanka ta ba, tace “Hummm” A hankali tace “Tohm Nagode Allah ya saka da alkhairi, thank you soo much” He was still not saying anything, ta langwabe kai tace “Zan iya kashewa yanxu?” Sai a sannan taji yace “Ai sai katin nan ya kare” Bata san sanda tayi dariya ba sosai tace “Wanda ka turo min yanxu ko kuma katin da nake da shi kake nufi” Yace “I don’t know for you” Tace “To ai ko nawa ma zai iya yin 3 hours bai kare ba, wanda ka turo min kuma ban san awanni nawa zai yi ba” Jin bai ce komai ba ta ajiye wayar ta sauka daga saman gadon ta tafi gun boxes dinta ta bude zata saka kayanta cikin wardrobe, sai kuma ta koma ta dauko wayar taga he is still on the line, ta langwabe kai a hankali tace “Ni fa aiki zan yi wallahi, should I cut the call?” Taji yace “Ke” Taɓe baki tayi ta ajiye wayar ta koma ta ci gaba da abinda take yi, ta dau lokaci me tsayi tana ta gyara kayanta bata sake komawa ta duba wayar ba, aka bude kofar dakin Aunty Farida ta shigo rai bace zata fara mata mitar abinda Nenne tayi yanxu a parlor, Khaleesat tayi saurin yi mata alamar tayi shiru tana nuna mata wayarta dake kan gado, Aunty Farida ta juya ta kalli wayar, Khaleesat ta karasa saman gadon ta dauko wayar tana kallon screen din taga bai fa katse ba har lokacin, mamaki hakan ya bata, da gaske katin yake don karar wa kenan, ta kai wayar kunne tace “Hello, ga Aunty Farida nan za ku gaisa” Taji yace “Ohk” mika ma Aunty Farida wayar tayi ta koma ta ci gaba da abinda take yi, sun kusa 10 mins suna magana da Aunty Farida har abun ya bata mamaki ashe yana bude baki yayi magana me tsawo haka dai, daga karshe suka yi sallama da Aunty Farida ta mika ma Khaleesat wayar ta fita daga dakin, Khaleesat ta kai wayar kunne tace “Sai da safe” Yace “Ai ban ƙona katina ba Malama” Ta hade rai tace “Toh sai cajina ya kare bayan ba wani magana muke yi ba” Yace “Na hanaki magana?” Kallon screen din wayar tayi taga minti nawa aka dauka all this while, zaro ido tayi ganin miss calls din Jay a saman screen din wayar, da sauri tace “Kaga Housemate dina yana ta kira ban sani ba kuma” Yace “Ni na hanaki sani?” Zata yi magana taji ya katse wayar, ajiyar zuciya ta sauke ta zauna gefen gado tayi dialing number Housemate, har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai dauka ba, ajiye wayar tayi hoping zai yi returning call dinta amma har bayan minti goma taga bai kira ba, ta kalli agogo dake nuna karfe sha daya dai dai, sake kiransa tayi bai daga ba, Khaleesat ta dauko kayan baccinta ta saka don tayi wanka tun wajen karfe takwas da rabi, Hijab ta daura a kai ta fita zata je tayi ma Umma sai da safe, ba a dau lokaci ba ta dawo daki ta kwanta tana duba wayarta hoping Jay ya kira amma taga akasin haka, sosai taji ta damu, to ko dai yayi bacci ne, gashi sanda ya kira ji zai yi she is on another call, sai yayi tunanin tana ganin kiran nasa bata ɗaga ba, sosai jikinta yayi sanyi ta rasa yanda zata yi, Aunty Farida ce ta shigo dakin tace “Har kin kwanta ne Khaleesah” Khaleesat ta daga kai ta kalleta, Aunty Farida ta zauna gefen gadon tana kallonta tace “Yana kiran ki ne dama Junaid” Khaleesat tace “A’a ni na kirasa bashi da lafiya nayi masa ya jiki, Housemate dina ya gaya min he is sick” Da damuwa Aunty Farida tace “Ayyah, to Allah ya basa lafiya, ai ban sani ba da na tambayesa ya jikin” Khaleesat dai bata ce komai ba, Nan Aunty Farida ta hau bata labarin abinda Nenne tayi daxu, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don abinda ya tsaya mata a rai daban, har daga karshe aunty farida tayi mata sai da safe ta fita wajen karfe sha biyu da minti ɗaya, Khaleesat ta jawo wayarta a sanyaye ta kunna data ta bude WhatsApp, dai dai sanda Jay yayi updating Status with Ajay’s picture, wishing him a Happy Birthday, tayi masa reply tace “Baka ga kirana ba?” After some minutes ya maido mata sako yace “Just woke up now” Kasa rubuta masa komai tayi jin abinda yace, after some minutes tace “Toh shikenan” Ya maido mata da reply din “Good night” Bata sake ce masa komai ba ta kashe data tayi kwanciyarta zuciyarta babu dadi. Da asuba bayan Jay ya dawo masallaci ya nufi part din Ajay don ko masallacin ma bai je ba, kwance ya samesa har ya koma bacci bayan yayi sallan sa a daki, Jay ya kalli drugs din da ke ajiye kan beside drawer da ruwan gora, ya karasa kusa da shi ya kai hannu forehead dinsa to feel his temperature, yaji his temperature is normal, although sau uku yana shigowa part din nasa cikin dare to check up on him, a zuwansa na karshe ne ma yaga Mai martaba a dakin shi ma, bude ido Ajay yayi bayan Jay ya kai hannunsa goshinsa yana kallonsa, Jay yace “Good morning Bruh, wishing you more fruitful years ahead” Ajay har ya mance yau ne ranan zagayowar haihuwarsa, juyawa yayi, yayi kwanciyar rub da ciki ya mayar da idonsa ya lumshe without replying him don bacci yake ji saboda maganin da ya sha, Jay ya juya ya fita daga dakin, Bangaren Maminsa ya tafi yayi sallama yana tsaye kofar dakinta ta amsa sannan ya shiga, har lokacin tana zaune saman darduma rike da counter, ya zauna yana kallonta ya gaisheta, da murmushi fuskarta tace “How was ur night Dear?” Jay yace “Alhamdulillah” Mami tace “Jiya na shiga part dinka wajen karfe sha daya naga kayi bacci” Jay bai ce mata komai ba, don idonsa biyu ba bacci yake ba sanda ta shigo, shi bai ma yi bacci ba sai kusan karfe daya da rabi jiya don gaba daya baccin kaurace masa yayi, Mami tace “Hadiyah ma wai nan da sati biyu zata dawo ko?” Jay yace “Ohk…” Don shi bai ma sani ba, after some seconds a hankali yace “Pls Mami Ina son maki magana ne amma don Allah ki fahimce ni, zan shiga damuwa idan kika yi misinterpreting dina cause kece mutum na farko da nake saka ran zata fara fahimta ta bayan Mai martaba, I need you to consider my points plss Mami” Yana kai wa nan ya daga kai ya kalleta yaga kallonsa take with full attention don har taji hankalinta ya tashi ganin damuwar da ya bayyana karara a fuskarsa cikin kankanin lokaci, shiru yayi bai sake cewa komai ba ya sauke idonsa, Mami ta kwantar da murya tace “Kana da wani a duniyar nan da zaka gaya ma damuwar ka da ya wuce ni ne Jawwad? Why is it taking you so long to voice out what the issue is? Kusan wata biyu kenan kana min nuku nuku ka ki gaya min menene matsalar, ko ka taɓa min wata magana ne kaga ban baka goyon baya ba ko da kuwa bana son abun nan son? I don’t think there is anything I can’t do for you, ka kwantar da hankalinka ka min bayanin menene ke faruwa” a hankali Jay yace “Ohk, dama Mami gaskiya ni yanxu ina da warce nake so zan aura, na duba abubuwa da yawa naga i and Hadiyah are not compatible, dama ita din zabin ku ce ba zabina ba, a wancan lokacin saboda inyi biyayya yasa na amince ban yi ma kowa gardama ba, yanxu kuwa i have my choice Mami kuma ina sonta sosai, ki yi hakuri Mami ban san yanda zaki dau wannan zancen ba, amma goyon bayan ki shine kwanciyar hankalina….” Shiru ya ɗan yi na few seconds har sannan kansa na duke yana kallon kasa, a hankali ya ci gaba yace “Amma kuma i have no issue marrying them both saboda gudun abinda zai je ya dawo considering our relationship with Hadiyah is in this family, in dai za a amince min ni na yarda zan hada su duka…. Zan kuma yi adalci tsakanin su in sha Allah” Mami dai kallonsa kawai take yi babu ko kiftawan kirki, bayan kusan minti ɗaya ya daga kai a hankali ya kalleta jin she is still silent, ta ɗan yi murmushi ta ajiye counter din hannunta tace “Wannan ne maganar dama Jawwad” Sosai yaji gabansa ya fadi, ya dai yi shiru bai ce komai ba yana kallonta yana jiran jin abu na gaba da zai fito daga bakinta, ajiyar zuciya yaji ta sauke me nauyi, after few seconds cikin nutsuwa ta fara magana tace “Toh a yanxu dai i am speechless Jawwad, cause this is something I never saw coming, gaba daya kaina ya kulle, amma ita yarinyar a Amurkan ku ka hadu ko a ina ka santa?” A hankali Jay yace “Can na santa, she is schooling there also” Mami ta gyada kai tace “Ohk that’s good, brief me a little about her, amma bana son karya Jawwad kuma kasan haka” Jay ya daga idanuwansa ya kalleta, murya can kasa yace “Mai martaba yasan da maganarta Mami, kuma har ya hadu da ita a can wani zuwa da yayi Maryland, shi ne ma ya bani shawaran hadasu su biyu for peace to reign, sannan yace In fara magana dake akan maganar tukuna” Mami tace “Ohk, er wace gari ce yarinyar?” Jay yace “Kano” Mami ta jinjina kai sannan tace “So shima Junaid ya goyi bayan ka kenan dai akan hakan?” Jay yace “Eh, yasan komai” Mami tace “Ba damuwa, er wace unguwa ce a Kanon?” A hankali Jay yace “Tudun Yola” Mami ta gyada kai tace “Shikenan, ni yanxu kwanciya zan yi Jawwad, idan na tashi anjima ma ci gaba da maganar” Jay yace “To Mami” kansa a kasa ya mike ya fita daga dakin Mami ta bi sa da kallo har ya kullo mata kofa, tana ta zaune saman darduman har bayan fitarsa da kusan minti goma sannan ta mike ta fita daga part din nata, bangaren Junaid ta nufa ta bude kofar parlorn ganin baya cikin parlor ta karasa har Bedroom dinsa, yana kwance yana danna wayarsa don tun da Jay ya shigo daxu ya tashesa bayan ya fita sai ga Mai martaba da Aunty, bayan su ma sun fita Ammi ma ta kirasa shi ne bai sake komawa baccin ba, duk idan ranan zagayowar haihuwarsa ta zo yakan je Abuja wajen Ammi ne amma wannan karan baya jin yana da strength din zuwa Abujan, ya daga kai yana kallon Mami da ta shigo dakin ko sallama babu, ya mike zaune ya ajiye wayar hannunsa tun kan ya gaisheta tana dukan tafin hannunta da yatsu biyu tace “Wato yanda kayi bakin jini cikin family ka zama kamar mujiya shi ne bari ka goga ma Jawwad shi ma a ki jininsa ko? duk wata salon mugunta da rashin mutunci ka san shi Junaid, to bari kaji in gaya maka… yanda ka ba Jawwad muguwar shawaran yayi fatali da auren Hadiyah yace shi wata daban zai aura ba ita ba haka tun muna mu biyu da kai zaka koma ka zaunar da shi ka sake basa shawaran ya bar wannan zancen, don ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba kai ne algungumin da ka zugasa Jawwad ba haka yake ba, wannan ba halinsa bane, sam bashi da tsaurin idon da zai zauna yace min shi baya son zabina yaga wata daban yana so, wallahi muddin ina numfashi a duniya babu wata yarinyar da Jawwad zai aura da ta wuce Hadiyah kuma daga ita babu ƙari, ban haifar ma ko wace ‘ya mace miji ba bayan Hadiyah, don in dai ita yake aure babu me rabani da shi ko ya nisanta ni da shi bayan iya shi kadai Allah ya bani, tarayyar ka da Jawwad kwata kwata babu alkhairi a cikinsa sai sharri, babu yanda zan yi ne amma na tsani ganin ku a tare har cikin raina don bakin jininka kake shafa masa ta hanyar dora sa a keken beran da kake yi, babu alkhairi a tarayyar ku sai sharri wallahi, don haka tun wuri muna mu biyu da kai ka koma ku warware wannan kullin da ku ka yi da shi don koma er uban wacece bazai aureta ba billahil azeem, sarai nasan wannan zugin ka ne ba na kowa ba tunda ka tsani ganin yana zaune lafiya da kowa, ci gabansa ma ai ba wani so kake ba, kuma muguntar ka da sharrin ka tsaff zai kare maka, Balle ni ko me zaka yi ma baya bani mamaki don kusan gado kayi…..” Ajay ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakinsa ya kulle kofar don in dai ya zauna ya ci gaba da sauraron maganganun karshen nan da take shirin yi tsaff zai mayar mata, Mami tace “To ai ba sabon abu bane, fitsara ai ba yau ka fara ba, kai da baka san darajan iyayenka ba ma balle na wasu, meye kuma baza kayi ba, in sha Allahu sai Allah ya kawo karshen alakarka da Jawwad don babu alkhairi cikinta sai sharri da hassada” Tana kai wa nan ta fice daga dakin rai bace ta tafi bangaren Aunty….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via 07087865788*
