Hausa novels

Yar Makafi Complete Document


Description/Story:

Yar Makafi! Complete Hausa Novel Document Written By Fresh Ummee Zeey

 

Description

*’YAR MAKAFI…*

♦ ♦ ♦ ♦

🎗 🎗 🎗 🎗

 

 

“`written by…..✍🏼“`

*FRESH UⓂMIEY XEEY*

Da

*NABILANCY LUV💘*

 

 

*♻REAL EXCLUSIVE WRITER’S FORUM*

 

 

PAGE……….1 TO 5

 

Tuk’i yake cikin nutsuwa da alamarsa yana cikin nishadine wakar larabawa yakeji yanabi yana gyada kansa da murmushi akan fuskarsa

 

Wayarsa ta dau tsuwwa kirane ya shigo saida ta kusan katsewa kana ya dauketa nan take yasha mur fara,ar fuskarsa ta gushe lokaci guda bakin ciki ya xiyarceshi baya qaunar mu,amalarsa da yr nacin nan Lubna sonshi take tamkar ta haukace shikuma kinta yake wulakanta ta yake amma taki hakura

 

Yaja tsaki tareda ajiye wayar amaxauninta ta sake kira akaro na biyu yakatseta tareda kashe wayar gabaki daya

 

Adai dai round about na danjar dangi yaja ya tsaya da saurinsa ganin wasu makafi zasu gifta ta gaban motarsa tareda yarsu data rike musu sanda

 

Allah ne yataimaka dabai gogesu ba yakurawa yarinyar ido fara ce kal gashinta har gadon baya bazata wuce shekara sha tara sha takwas ba amma dai baxatai ashirinba danma tanada garin jiki

 

Ta gaban motarsa suka gifta sukaje gindin motar dake gefensa suna bara

 

Take yaji zuciyarsa ta tsinke tausansu yaratsasa gasu dai fes dasu amma da alama babu karfi ba matallafi

 

Yarinyar ta dauke masa hamkali jinta yai har kokon ransa kyanta yafi tafiya dashi tamkar balarabiya haka ya fasaltata

 

Dai dai glass din motarsa sukaxo suna barar

 

Ya zuge glass din ahankali take Allah yabashi sa,a suka hada idanu da ita baisan sanda yasakar mata murmushiba

 

 

” Allah ya tsare Allah yak are mallam ataimaka mana da sadaka sbd Allah da annabi.

 

Muryarta ta sukurkutar masa da zuciya dan bakinta kawai yake kallo

 

Dubu daya ya miko mata yana murmushi

 

Da rawar jiki ta karba fuskarta cike da mamaki

 

Tace ” banida canji ”

 

“rike duka ” yammata nabaki sadakarta sbd Allah da annabi kinji.

 

Da gaggawa tahau gyada kanta fuskarta da fara,a alamun jindadi ya ziyarci ranta tace ” Allah ya karba ya biya bukata.

 

Kafin yai magana ta janyo hannun iyayenta dake gefenta sunyi gaba

 

Yabisu da kallon tausayawa tabbas saiya taimaka mata kota wata hanyar ne domin zuciyarsa ta kamu

 

 

danja tai musu alamar tafiya haka yaja motarsa yai gaba yana aiyano yarinyar aransa domin yaci alwashin saiya dawo gareta kota halin k ‘akane

 

*****- ****** ******

 

Sai da Dr ma,aruf yajera kwana uku yana xuwa shatale talen dangi gun danjar nan duk don yaga wannan yr makafin amma baiganta ba sai hankalinsa ya tashi matuka gashi baisan wanda zai tambaya ba tunda ba sanin sunanta yai ba

 

Akwanakin ukun nan shiyasan halin daya kasance domin yanda yake ganin rana haka yake ganin dare

 

Fuskarta kawai ke mata gixo muryarta na masa burari akunne

 

Akullum sukuku yake wuni ko agida saida aka gano shi domin mahaifiyarsa gaba ta tusashi da tambayar meya faru dashi kwana biyu taga canji atare dashi

 

B ‘oye mata yai domin ba yanxu yakamata tasaniba balle yasan ma babu fanin sanin ga mum din nasa tunda yasan halinta ba kaunar mu,amala da talakawa takeyiba gashi kuma tana so ya auri diyar kanwarta Lubna

 

Ko agun aiki baya da kuxari aikinma gefe yake dashi dan dai babba ne babu me takura masa balle abashi quiry.

 

Abokinsa Dr lurwan kawai yagayawa matsalarsa shima saida ya matsa kana yagaya masa

 

Aiko dayake shi din me damuwa da damuwar sane tuni akwana na hudun da baijeba yatusashi agaba suka je bakin danjar

 

Ckn sa,a suka hangosu daga nesa Dr ma,aruf nahangosu yaji wani sanyi aransa da murnarsa ya nuna wa Dr lurwan su da hannu

 

Dayake ackn go slow ake ta koina acunkushe gun yake da abun hawa

 

Gashi bata bangarensu makafin suke ba

 

Kusan minti sha biyar ba,a basu hannu ba

 

Gashi yadaina hango yarinyar da iyayan nata

 

Ko da cunkoson ma yarasu da aka basu hannun gefe sukai farking suka hau hange ko Zasu ganosu amma abin mamaki ko kusa ko alama babu makafin nan da yrsu

 

Ran Dr yai matukar baci yahau tsaki

 

Dr lurwan shiya kira wani me saida biscuit yahau tambayarsa makafin nan matashin yace dasu ai yanxu suka tsallaka titi suka tafi.

 

Dr lurwan yace ” ko kasan gidansu kanina?

 

girgixa kansa yayi yace ” walh bansaniba don basu dade da fara xuwaba bakine.

 

Dr ma,aruf ya doki gaban motar yana jan hucin takaici

 

Lallabashi abokinsa yayi suka hau mota suka tafi akan gobe zasu dawo…

 

 

File Name   Yar Makafi
Title   Yar Makafi Complete Document
Author    Ummiey Zee Nabilancy
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Love Story
Published Date    17/10/2024
File Size    170KB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Yar Makafi Complete Novel Document By Ummiey Zeey

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button