Hausa novels

NIHAAD Chapter 54 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

54

It took Khalil a while kafin ya iya controlling urge dinsa a lokacin, it wasn’t easy for him, duk da dama babu abinda yayi niyyar mata, amma sai da ya kai zuciyarsa nesa kafin ya iya hakura ya kyaleta, ya koma can gefe ya kwanta breathing rapidly, jin yanda take kuka kamar warce aka ma duka ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dake kusa da gadon yana kallonta, da sauri ta boye fuskarta da gadon tana ci gaba da kukanta, har sannan jikinta bai daina rawa ba, she is so afraid, he realized bakuwa ce gaba daya a lamarin, she is not use to it, ya koma kusa da ita ya dagota ya rungumeta ya lumshe ido yana jin yanda zuciyarta ke bugawa, ita dai taki yarda su hada ido jikinta sai rawa yake, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace “Toh me aka maki?” Tayi shiru bata ce masa komai ba, suna nan a haka for almost 10mins har yaji she is completely calm, a hankali yace “Nihad” Da sauri ta daga kai ta kallesa saboda yanda ya kira sunan nata, yana kallon kwayar idonta yace “Me ke kai ki hotels a baya?” Sauke idonta tayi bata ce masa komai ba, lokaci daya hawaye ya cika idonta, still taki ce masa komai, shi ma bai sake ce mata komai ba, ya dauko rigarta ya mika mata sannan ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, kafin ya fito har ta shirya, ta jinginar da kanta jikin gadon tayi nisa tunanin da take, har ya karaso kusa da ita yana kallonta bata sani ba, wayarsa da ya fara ring ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ya dau makullin mota yace “Tashi mu tafi” Mikewa tayi tana kallonsa, ya nufi kofa ta bi bayansa, har suka isa gida babu wanda yace komai a cikinsu, tunanin da yake a zuciyarsa daban, ita ma haka, yayi parking a compound sai a sannan ya juya ya kalleta yace “Kina da National ID card?” Ta ɗan kallesa, sai kuma ta gyada masa kai, yace “In kin shiga ki dauko min” Bata ce komai ba ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo ta nufi entrance din gidan walking slowly, jinginar da kansa yayi da kujeran motar ya lumshe ido, he wish things won’t go as hard as he is seeing it now, he wish his parents will understand him, Nihad bata tadda kowa main parlor ba ta tafi bangaren Mumy, Mumy na kallonta bayan ta zauna tace “Ina Ibrahim din?” Tace “Yana waje” Mumy tace “Kun samu Innar?” Nihad tace “Ehh” Mumy tace “Bata dai yi fada ba ko?” Girgiza mata kai kawai Nihad tayi, Mumy tayi shiru, bayan wani lokaci ta kalli Nihad tace “Bayan kun fita zuwa gidan Inna daxu Umma ta shigo wai kina ganinta baki gaisheta ba shine hakan ya dameta shi yasa ma ta bar gidan, bana son ki nuna mata komai Daughter, pretend as if everything is okay, kar ki nuna mata komai har ku bar gidan nan kin ji?” Nihad dai sai kallon Mumy take, Mumy tace “Kwana nawa yace za ku yi?” Nihad ta sauke idonta a hankali tace “Nima ban sani ba” Mumy tace “Toh kiyi hakuri kar ki nuna mata komai, idan kun hadu ki gaisheta yanda kika saba” Nihad dai ta kasa cewa Mumy komai but deep down her tasan she will never greet her, don duk duniya babu wanda take jin tsanarsa a zuciyarta irin Umma. Khalil na zaune tare da Aminu wajajen karfe goma Amina ta iso wajen tana kallonsa tace “Abbanmu yana kiranka” ya ɗan kalleta wanting to make sure da shi take ko Aminu, Aminu yace “Tace Alhaji na kiranka mutumina” Khalil yace “Toh” Juyawa tayi ta bar wajen ya mike ya saka ID card din Nihad da Sudais ya kawo masa a aljihu sannan ya nufi cikin gidan, Umma na zaune parlor ta kafe ma TV ido duk da gaba daya hankalinta ba kan kallon yake ba, malamin nata da suke zuwa wajensa tare da Hajiya Turai sun ƙona man mota a banza sun je har kauyen da yake a kusa da Zaria amma wai bashi da lafiya an kawosa asibiti cikin kano, haka nan suka juyo a hanya kuma mota ta lalace masu, sai da ta kashe ya fi dubu saba’in wajen gyaran motar, suka ɓata awa kusan uku kafin aka gama gyaran ta kamo hanyar gida a wahale ga yunwa…. suna hada ido da khalil bayan ya shigo parlon ya dauke kai ya nufi kofar parlon Abba, ta bi sa da kallon mamaki don haduwarsu na farko kenan tun zuwansu gidan, Ya tsaya bakin kofar parlon yayi sallama, sai da yaji Abba ya amsa sannan ya shiga, Umma ta kalli Amina tace “Ko dai ya gaisheni ni ce ban ji ba Amina?” Amina tace “Ba wani gaisheki da yayi wallahi” Mikewa tayi ta nufi parlon Abban da sauri ita ma, Khalil na zaune kasa ya sunkuyar da kansa bayan ya kara gaida Abba, Abba yace “Wani garin ku ke?” Khalil zai yi magana Umma ta shigo, Ta nemi waje ta zauna parlon tana ɗan murmushi, Abba ya kalleta, can kuma yace “Is there any problem?” Da sauri tace “Aa babu komai, sannu Khalil, fatan kun zo lafiya?” Khalil ya kalleta yace “Alhamdulillah” Tace “To madallah” Abba ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Idan zaka kwanta ka tafi dakin Farooq, dakin nasa a bude yake…” Khalil da kansa ke kasa yace “Toh Nagode” Abba yace “Shikenan you can leave” Mikewa yayi ya fita daga parlon, Umma dai sai murmushin yake take tace “Allah sarki, sun dawo nan garin kenan?” Abba ya dau wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne. Nihad na kwance saman gadon Mumy bayan tayi shirin bacci Mumy ta shigo dakin tace “Baxa kije ki ji ko yana bukatar wani abun ba Nihad?” Nihad ta daga kai tana kallon Mumy, Mumy tace “Duk da nasan akwai komai dakin farooq but ki je kiji if he is comfortable” Nihad ta mike zaune, Mumy ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita, bata gansa a dakin ba hakan yasa ta dawo tayi kwanciyarta kawai. Washegari bayan khalil ya shigo gaida Mumy ya sanar mata za su koma a ranan, Nihad dake zaune dai sa kallonsa take tana tunanin inda za su koma, Mumy tace “Toh ka samu Alhajin ka sanar masa?” Khalil yace “Na ɗan fita dazu, kafin in dawo kuma ya fita” Mumy tace “Toh ka kirasa a waya sai ka gaya masa” Khalil yace “Toh in sha Allah” mikewa yayi ya fita daga parlon, Mumy na kallon Nihad tace “Toh ki tashi ki fara shiri” lokaci daya jikin Nihad yayi sanyi, amma saboda bata son Mumy ta fahimci komai ta mike ta shiga bedroom dinta kawai kamar zata shirya, zaunawa tayi kan gado ta hade kanta da pillow hawaye na sauka idonta, Umma tayi sallama ta shigo parlon Mumy, Ta zauna saman kujera bayan sun gaisa da Mumy tace “Ina er tawa?” Mumy ta mike tace “Yanzu ta shiga ciki bari in duba” Daga haka ta shiga daki Umma ta bi ta da kallo, Nihad na jin muryar Umma dama ta shige bandakin Mumy ta sa makulli, Mumy ta ɗan yi jim a dakin, can ta juyo ta fito tana kirkiran murmushi tace “Kamar wanka take, tana bandaki….” Umma tace “Toh, ni sai naga kamar ta kullaceni, tana ganin na watsar da al’amarinta bata san Alhaji babu me iya masa ba sai Allah, kuma Allah shine shaida, nayi bakin kokarina kema shaida ce amma hakan ya so ya zame mana ɓacin rai da Alhaji, har yake ga kamar ina goyon bayanta ne, Nihad gani take kamar nayi shiru naki cewa komai akan abinda ya sameta nan kuma ba haka bane Allah ya ga zuciyata, babu yanda na iya ne abun ya fi karfi na” Tana magana tana matsar kwalla, Mumy dake ta kallonta babu ko kiftawa ta kasa ce mata komai, Umma tace “Toh idan ba kullatata tayi ba menene? Ni Nihad bata taɓa min haka ba wallahi, a jiyan nan da da tashigo da wajena zata fara shiga kafin ma ta zo nan, amma bata yi hakan ba, to kinga ai ta kullaceni kenan, duk sai jikina yayi sanyi na fita na bar gidan” Mumy ta sauke idonta kasa don bata da abinda xata ce ma Umma, banda zafi babu abinda zuciyarta yake, da Umma bata gurbata ma ‘er ta rayuwa haka ba, da zagewa tayi kawai su zuba kishi amma da bata ma er ta abinda tayi mata ba, daure kawai Mumy take a zaune a wajen, Umma ta sauke ajiyar zuciya jin Mumy ta ki cewa komai, tace “To amma zasu kwan biyu ai ko?” Mumy tayi karfin halin girgiza kai tace “Anjima za su koma” Umma ta buda ido sosai tace “Yau din nan? Ikon Allah, ni na zata sun zo su kwana biyu ne? Toh a wani kauyen suke ne halan?” Mumy tace “Ban sani ba gaskiya” Umma tace “Allah sarki, Allah me yanda ya so….”
Nihad na shirya sauran kayanta dake gidan a cikin Trolly Mumy ta shigo dakin tana mata wani kallo tace “Ke kika kirata kika ce kin zo??” Nihad ta daga kai tana kallon Mumy tace “Wacece?” Mumy tace “Ban sani ba” Nihad tace “Mumy ni ban kira kowa ba ni da bani da waya, kuma ai kinga ban yi amfani da wayarki ba” Mumy tace “To wa yace mata kina nan?” Nihad tace “Ai ban san wacece ba” Mumy tace “Sai kije ki duba” Nihad ta mike tsaye ta nufi kofa ta bude ta fita parlon Mumy taga babu kowa, can main parlor ta fita, tsaye tayi parlon tana kallon Husnah dake zaune ta sha baƙin glass, Husnah ta mike da sauri ta rungumeta cike da murna tana kare mata kallo tace “Besty, meye rayuwa? yanzu da sai dai mu ji kin zo kin tafi babu daga hannu? Haba Nihad, amana bata ce haka ba ai, nafi karfin haka a wajenki” Nihad ta karasa ta zauna parlon tace “Wa yace maki na zo?” Husnah tace “Wallahi na zo wucewa ta anguwar nan ne nace bari dai in shigo mu gaisa da su Umma da Mumy, kawai sai na samu labarin wai kina nan, nace what?? abun ya daure min kai nace kina nan shine babu notice, yanzu ko ta waya kin daina neman mu Nihad, Duk kusancinmu ace kin ya da mu haka?” Nihad dai sai kallonta take, Husnah na gyara zama tace “Toh yanzu ya ake ciki? Naga kin yi haske amma kin rame, ina mijin naki?” Nihad tace “Lafiya lau” Husnah tace “To wai wani garin ku ke?” Nihad na kallonta tace “Ban san sunan wajen ba” Husnah tayi kasa da murya tace “Kar kice min kin hakura kin zauna da shi Nihad har abu ya shiga tsakaninku Nihad” Nihad tace “Do you have any problem with that?” Shiru Husnah tayi tana kallonta, Can tayi yake tace “Aa kawai tambaya nake kawalli, kinsan har yanzu Aliyu Jikamshi bai daina damun Naf a waya ba shi yasa ma nake maki wannan tambayar, wallahi Aliyu bai hakura ba har yanxu” Nihad dai bata ce mata komai ba, Husnah tace “To wai har yanzu baki da waya?” Nihad tace “Bani da shi har yanzu” Husnah tayi kasa da murya ta bude jakarta tana kokarin ciro waya tace “Toh ko in baki karamar wayata ki saka layi kawai, sai mu dinga magana….” Nihad tace “Aa yanzu bana bukatar waya” Shiru Husnah tayi tana kallonta da mamaki, Nihad tace “Toh naji dadi nagode da ziyara Husnah, ina son zan je in ci gaba da abinda nake yi a ciki” Husnah ta buda baki tana kallonta ta kasa cewa komai, Nihad ta mike tace “Toh sai anjima, nagode” Kai kawai Husnah ta iya gyada mata, Nihad ta juya ta bar ta a parlon ta koma parlon Mumy, Husnah ta mike da sauri ta shige bangaren Umma…
Bayan Azahar Khalil na zaune balcony tare da Nihal, Hira suke amma gaba daya hankalinta baya jikinta, she is carried away with her thought, sannan tun dazu ake kiran wayarta amma bata dagawa daga karshe yana lura da ita ta sa wayar a silent, yace “Nihal” Firgit ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta kirkiri murmushi tace “Na’am” Yace “Pls tell me what ur problem is, Or don’t u trust me?” Nihal dai sai kallonsa take, can ta ɗan kirkiri murmushi tace “Sure i do… but i told u nothing, I don’t have any problem….” Khalil dai kallonta kawai yake, Da sauri tace “Yaushe xa ku koma?” Yace “Today” Ta wara ido tace “Yau din nan? Amma ai rana yayi” Ya girgiza kai yace “Bai yi ba” Tace “Ohk, nima next week zan koma makaranta in sha Allah” Yace “Allah ya kai mu, but if there is anything feel free to call and talk to me Nihal” a hankali tace “In sha Allah” Yace “Bani account number din ki” Ta ɗan buda ido tace “Ahh haba wallahi Nagode, ka bar shi” yace “I asked for it” shiru tayi bata ce komai ba, ya ciro wayarsa yace “Gaya min” Ta kallesa tace “Amma…” Ya dakatar da ita yace “Ki bani nace” Ta sunkuyar da kai ta karanto masa account din, cikin few seconds taji alert a wayarta ta duba taga dubu hamsin ya sa mata, ta daga kai tana kallonsa, ya mike yace “Ki duba min ko ta gama shiryawa, lokaci na wucewa” Tace “Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi” Shi dai bai ce mata komai ba, ta tashi ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta fito da trolly din Nihad, wanda duk hijabs dinta da wasu kayanta ne a ciki da turarrukanta, daurewa kawai Nihad take kar ta fashe da kukan da ke cin ta, Mumy ta gama mata nasihar da zata mata sannan tace “Ki je kar ki bata masa lokaci, Allah ya tsare, in kin samu waya ki dinga kirana kin ji?” Nihad ta gyada mata kai kawai tana goge hawayen idonta ta nufi kofa, Mumy ta bi ta da kallo ita ma hawayen har ya cika idonta, Aminu ya taho ya saka jakar Nihad a bayan motar yana kallon sabon drivern gidan cike da tsangwama yace “Kwata kwata baka san aikinka ba Iliya, kana ganin an fito da jakar ai da gudu zaka dauka ka saka a booth, haka ake yi ba wai ka tsaya kamar soja ba” Dreban yace “Wai kai ina ruwanka da ni a gidan nan ne bawan Allah” Aminu yace “Oho dai ka ji da warin bakinka” Daga haka ya koma gate, shi dai khalil na jingine jikin motar yana kallonsu, sai kuma kawai ya shiga ciki don yi ma Mumy sallama, Mumy tace “Toh Allah ya tsare Ibrahim, ayi ta hakuri da ita don Allah, idan tayi maka ba dai dai ba kar kayi kasa a gwiwa ka kirani kaji” Kansa na kasa yace “Nagode Allah ya kara girma” Tace “Ameen, Allah ya maku albarka” Ya amsa da “Ameen” sannan ya bar parlon ya fita zuwa compound, ba a dau lokaci ba Nihad ta fito tare da Nihal, Nihal ta bude mata back seat tana kallonta tace “Allah ya tsare sister….” murmushi Nihad ta mata tace “Ameen” Daga haka ta kulle motar tana kallon Khalil tace “Safe trip” Khalil yace “Thank you Nihal” ya bude front seat ya shiga ya kulle, drivern ya ja motar suka bar parking space, Tun bayan barin Husnah gidan Umma ma ta fita shine har yanzu bata dawo ba, Aminu na tsaye gate tun kafin motar ya karaso yake daga ma Khalil hannu baki har kunne, suna isa gate khalil ya sauke glass din motar ya mika masa cash din dubu dari, Aminu yayi washarere da baki yana kallon tulin kudin da khalil ke mika masa ya kasa amsa, Shi kansa dreban sai gwale ido yake yana kallon kudin don dari biyar biyar ne sababbi, ita dai Nihad na bayan motar tana kallonsu, Khalil ya kamo hannunsa ya damka masa kudin sannan ya kulle glass din yana kallon drivern yace “Mu je” Drivern ya ja motar suka bar Aminu tsaye galala da kudi a hannu, Bayan sun hau saman titi drivern na kallon Khalil cike da ladabi yace “Ina muka nufa ranka shi dade?” Khalil yace “Airport” Nihad ta daga kai ta kallesa, drivern yace “Toh Yallabai yanzu kuwa” Daga haka ya nufi airport da su, suna isa Aminu kano bayan yayi parking Khalil ya sauka daga motar, da sauri Drivern ya zaga ya sauke kayan Nihad dake bayan motar, ta bude motar ta sauka ta tafi ta amshi trolly dinta a hannun drivern, Khalil ya ciro dubu biyar ya basa yace “Mun gode” Drivern har da risinawa ya dinga masa godiya, Khalil ya amshi trolly din hannunta ya nufi cikin airport din ta bi bayansa tana tafiya a hankali…. Suna shiga cikin airport din bayan ya amsar masu Boarding pass sai ga kiran Mami, sai da gabansa ya fadi, yau ta kirasa yafi a kirga, ya dai daga kiran yana sauraronta don bata basa space din magana ma, can yace “Calm down Mami, ina airport yanzu haka” Yana fada mata haka ta katse wayarta, sai da suka jira for almost 30mins kafin jirgin ya tashi zuwa Abuja.. kamar jira Nihad take jirgin ya tashi ta fara bacci, ya jawota kusa da shi a hankali ya kwantar da kanta saman shoulder dinsa, shi dai yasan banda Mami babu abinda zai kai sa Abuja, but he just have to go because of her, jirgi na sauka a Abuja bayan sun fito daga cikin jirgin hankalin Nihad ya tashi, yanzu gidansu zai sake mayar da ita kenan, tunanin hakan yasa taji kamar ta fashe da kuka, suka dau cab a airport din bayan khalil ya sanar masa inda zai kai su, tafiyar kusan minti arba’in suka yi, Nihad taga wani anguwan daban suka shigo, ta dinga bin ko ina da kallo har mai cab din yayi parking dai dai wani gida wanda ya haduwa iya haduwa, duk manyan gidaje ne a layin kamar wannan, Khalil ya sauka daga cab din don tun a hanya yayi masa transfer, mai cab din ya bude booth ya ciro trolly din Nihad, Khalil ya amsa yana kallonsa yace “Ka jirani zaka ajiye ni wani waje yanzu” Mai cab din yace “Ok sir” Daga haka ya nufi gate din gidan ya ciro makulli a aljihunsa ya bude sannan ya juya yana kallon Nihad dake tsaye, karasowa tayi a hankali kusa da shi ta tsaya, ganin jira yake ta shiga gidan kawai ta shiga shi ma ya shiga sannan ya kulle gate din, ta dinga bin compound din da kallo, it looks so beautiful, duk gidajen da taje a Abuja daga gidansu sai wannan a kyau, don ko na Aunty Maryam bai kai wannan kyau ba balle nasu Nadeeyah, kuma sabon gida ne kamar ba kowa ciki, yana gaba tana biye da shi har suka iso entrance din shiga cikin gidan, ya bude kofar da makulli ya shiga ta bi bayansa, waow the parlor is breathe taking, komai na ciki sabo ne dal, ya ajiye jakarta yace “Ki tafi sama kiyi sallah, i will be going out now” ta marairaice tace “Ni kadai a katon gidan nan?” Yace “Ke yarinya ce?” Ta dinga kallonsa gabanta na faduwa amma ta kasa ce masa komai, daukar jakar yayi ya wuce sama ta bi bayansa da sauri, ya bude wani daki ya ajiye jakar a ciki ya juya yana kallonta, ta shigo dakin tana bin ko ina da kallo yace “Ki shiga bandaki kiyi alwala” Daga haka ya juya ya fita sannan ya sauka downstairs, ya fita daga gidan ya kulle gate din da makulli ya shiga cab din dake jiransa don baya son Mami ta sake kiransa.

 

Click Here To Read Nihaad Chapter 55 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Back to top button