Hausa novels

Kanwar Maza Page 59 Complete Novel By Ayshercool

Page 59

 

*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

 

 

Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.

 

Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a ɗaki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.

Ƴan uwa sai bawa rumaisa haƙuri suke yi.

 

“Meye haka?” Ya faɗa a kausashe.

 

Gwaggo ta ce “Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daɗi za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi”

 

“Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya”

Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar ɗakan mama.

 

Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.

 

***

Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.

Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta ɗaga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.

 

“Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?”

 

“Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?”

 

“Babu ɗaya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?”

 

A hasale Samha ta ce ‘Look wakili, i don’t have time, for all this now allow to rest”

 

Khalifa ya ce “Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ƙure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ƙafarsa ba zaki hango ba, let’s join hands together”

 

Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faɗin “Shashasha kawai”.

 

Iman ita kaɗai a ɗakinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.

 

Ɓangaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. Taɓe baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.

 

Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.

Ta wuni a uwar ɗakan mama, tun ƙarfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ƙarfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.

Maƙwabta na ta mamakin wani hamshaƙin ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.

 

A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ƙi tsayawa.

 

Mai kwalliyar ƙawar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.

 

Ƙarshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.

Ya je ya tarar duk an yi wa ƙawayenta kwalliyar ban da ita.

 

Ya kalleta ya ce “Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?”.

 

“Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa” ta yi maganar cikin kuka.

 

Bashir ya ce “Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi”.

 

Adam dai ya ƙule ƙarshe, Bashir ne yayi ta bata haƙuri, sannan ta tsaya aka yi.

 

Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri ɗaya da na Adam.

 

Hauwwaliya har da tsalle, tana koɗa rumaisa.

 

Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.

 

A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haɗe cikin shadda iri ɗaya, hatta huluna da agogo iri ɗaya suka saka, motar na tsayawa, ta buɗe ta fice ta nufi wurin su Usman.

 

Abdallah ya din ga ɗaukar rumaisa a hoto.

 

Usman ya ce “Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da ɗan hasken da ba zai ishemu ba”

 

Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce “Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki”

 

Bisa ga al’ada, ƙawayen amarya da ƴan uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ƴar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ƴa da uba.

Abun ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ƴar mitsitsiyar yarinya.

 

Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maroƙa da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.

 

Rumaisa ta kalli yadda hall ɗin ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba ɗaya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na ɗibarta.

 

Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya riƙe hannunta, sai da ta ɗan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ƙoƙarin ɗaukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Adam amma ya riƙeta sosai.

 

Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ƙanwar zaratan maza har bakwai.

 

Iman ce ta fito stage, ta karɓi mic, tare da gabatar da addu’a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.

 

Jabir ba ƙaramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ƴar talakawa mara kunya.

 

Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ƙawayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.

 

Dangin su Adam sun so su farfaɗi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya riƙe gulmarsa.

 

Jabir ya rasa nutsuwarsa, ga tunanin auren adam,ga iman ta ɗau ado, sai shiga take yi tana fita, yayin da ita kuma hankalinta ke kan mai sunan baba, har fata take Allah ya sa ba kallonsa ake yi ba, dan dangin nan akwai tarin ƴan mata.

 

‘To sai me ina ruwanki?’ wata zuciyar ta tambayeta.

 

Aliyu habiba ya saka a gaba, yana yi wa dariya ƙawar amarya an sha ɗauri, ƴar baƙa kyakykyawa.

 

Iman ta ƙarasa ta cewa Usman “Yaya ban san sunanka ba, na san dai duk sunanku yaya, kuma duk kamarku ɗaya, koda yake na san yaya Aliyu”

 

Usman ya ce “Usman nake, ma’abocin haske, ƴar balarabiya ya aka yi ne?”.

 

Ta yi murmushi ta ce “Dama ban sani ba ko kun zo da abokanku, ga in da aka yi muku reserving can, za a fara dinner ne, gara mu fita kunyar kowa”.

 

Usman ya ce “Abokai kai, kin san mu yawa ne da mu, bari in tattaro su wuri ɗaya, dama zan zo mu zauna in baku amanar ƙamwarmu, dan Allah a kula mana da ita, ayi haƙuri da ita, idan aka taɓata zuciyar maza bakwai ce za ta girgiza ”

 

Iman ta yi dariya ta ce “Wane mu mu yi mata ba dai-dai ba ma, ai sai mu sha duka” tun da suke zuwa gidansu rumaisa, maganar kirki ba ta taɓa haɗata da yayyen rumaisa ba, sai yau da Usman yake yi mata halin na sa.

 

Umar yana jin su, kasancewar yana kusa da su.

 

Jabir ya ƙaraso in da Iman ke tsaye a wurin usman ya ce “Sweetheart, ina son magana da ke fa, ina aka yi wa abokan aikinsa reserving, suna daf da ƙarasowa, na ga ke ki ke ta arranging mutane”.

 

“Uncle J, ina wani aikin ne, ga uncle bashir nan, da shi muka zo wurin nan ɗazu, ya san yadda aka tsara komai fa” ta yi maganar cikin muryarta ta shagwaɓa.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

“Yes na ji, zo mu je dai, ko na ɗagaki yanzu na yi waje da ke, idan ya so gobe a ɗaura auren da namu”

 

Usman dai murmushi kawai yake, iman kuwa ba a son ranta ba, ta bi bayan jabir.

 

Suna yin gaba ya hau ta da faɗan, dan me za ta je wurin maza ta tsaya. Ba ta iya bashi amsa ba, ta tsaya tana kallon sa kamar za ta fashe da kuka, babu tsammani mai sunan baba ya gifta ta bayansu yana waya, ta ɗaga kai suka yi ido huɗu, da sauri ta koma cikin wurin dinner.

 

Kwaɓe fuska rumaisa take yi, tana nema ta yi kuka, Adam ya ɗan sunkuyar da kansa ya ce “Meye kuma?”.

 

“Ni na gaji, sai kallona ake yi, kamar wata mara gaskiya, ni bana son kallo, kuma ma yunwa nake ji, ina jin bacci ma kaina ciwo yake yi, na gaji da hayaniyar nan” ta ƙarasa maganar bilhaƙƙi za ta yi kuka.

 

“Yanzu a gaban mutanen zaki yi kuka ranar aurenki, salon ace auren dole za ayi miki, ko ki janyo mini zagi ko?”

 

Tura baki ta yi ta ce “Ba auren dolen bane, ni na ce na fasa, amma aka ƙi fasawa, wayyo mama ni na gaji”

 

A ransa ya ce na shiga uku, wannan Yarinyar tana neman ta jaza mini abun faɗa.

 

Mc kuwa koɗasu kawai yake yi, saboda shagwaɓa rumaisa take yi, da ya sake fito da yarintarta, ba shiri adam ya din ga yaƙe, dan kar a fahimci wani abu.

 

Abdallah ya hango, yayi masa alama da ya je, adam ya ce masa ya samo abinci ya zo ya bawa rumaisa, kar ta yi masa kuka.

 

Sai da Abdallah ya dungure mata kai, ya ce “Wace amaryar ki ka ga tana cin abinci a wurin bikinta?”

 

“Ni yunwa nake ji, ga su hauwwaliya can suna cin abinci, bari na je mu ci tare”

 

“Dalla zauna na je na samo miki, wai yunwa ranar aurenki dan abun kunya” ya sauka yana mita, ta bi bayansa da harara.

 

Da ya samo abincin, sai da su Aliyu suka raka shi, suka yi mata rumfa, ba a iya ganinta, Aliyu ya ɗebi abinci a cokali ya kai bakinta, wai ita ba abinci za ta ci ba, naman za ta ci, gani ta yi an bawa kowa abinci ita ba a bata ba.

 

Suka din ga zaginta suna bata naman, shi dai adam jinjina kai kawai yayi, ya yi wa Allah godiya da babu wanda ya san wainar da ake toyawa.

 

An sha hotuna kamar babu gobe, rumaisa ta ɗaga kai ta kalli Iman da ta zauna a kusa da ita, mai sunan baba yana gefenta aka yi musu hoto.

 

Hatta ammi ta je wurin, an yi mata liƙi sosai da sosai, an ci an sha, manyan mata sun yi rawa sun yi liƙi.

 

Yayyen rumaisa ma da abokansu, haka suka din ga yi mata liƙi, wannan ya ja ta nan ayi mata hoto, sai ka rasa waye angon ma a cikinsu.

 

Adam ma basarwa yayi, ya din ga yi mata liƙi, kuɗi ba kaɗan ba, ta din ga kallonsa ta ga ko yana sane, amma yaƙi kallonta kar ta yi wani shirmen. Babban abun da ya fi burgeta, shi ne fareti, da kuma crossing sword ɗin da abokan aikin su Adam suka yi musu.

 

Gajiya kam rumaisa ta yi ta, dan har gyangyaɗi ta fara, da ƙyar take iya buɗe idonta, ga takalmi mai tsinin gaske a ƙafarta.

 

Sai sha ɗaya da rabi na dare aka tashi, rumaisa tana ta sauri ta bi su yaya Abubakar, amma takawa ya sakata a gaba zuwa motar da suka zo.

 

Tana shiga ta zauna ce “Wayyo Allahana, na gaji”

 

Ya kalleta yayi shiru, basu je ko ina ba ta hau bacci, gaba ɗaya ta kife masa a jiki, kai da jin yadda take sauke numfashi ka san ta gaji da yawa.

 

Sidi ya ce “Sir amarya ta gaji da yawa”

 

Adam ya ce “Gashi har ta yi bacci”

 

Sidi ya ce “Allah mai iko, ba zan manta scene ɗin da ku ka yi making, ranar da ku ka fara haɗuwa ba, and she’s now your wife”

 

Adam ya ce “Shhhhh, a daina tayar da wannan maganar”

 

“Sorry sir”

 

Adam ya gyara mata kwanciyarta, ya ɗaukar pose ɗin ta, ya buɗe, ga sababbin kuɗi nan a ciki, fal. Ya girgiza kai ya riƙeta a hannun sa.

Rumaisa kuwa jin ta take kamar a kan katifarta, har da gyara kwanciya.

 

A ƙofar gida ya tarar da yayyenta, suna jiran su ga ta ina za su ƙaraso, ya sauke glass ɗin motar, gaba ɗaya suka ƙaraso.

 

“Ta yi bacci fa” ya faɗa yana kallon Usman.

 

Usman ya ce “Ai haka take, da yin magariba take bin bango, a bata ta ci ta yi bacci, kamar ƴar kaza”.

 

Adam ya ɗagata zaune da niyyar ya tasheta, amma ina baccinta kawai take yi.

 

Mai sunan baba daga in da yake tsaye, yana hango cikin motar, rumaisa ba ta san ma me ake yi ba. Haka nan ya ji wani irin kishi ya taso masa, ƙanwarsa a kwance a jikin wani ƙato. Takawa ya ɗaga kai suka haɗa ido da shi, ya wani cukule fuska.

 

Aliyu ya zura hannunsa, ya ɗauko rumaisa gaba ɗaya, ya nufi gida da ita,, da gayya Adam ya fito daga motar, ya ce “Kai Ali ka yi a hankali, kar ka yi mata rauni fa, a kawo mini nakasashshiyar amarya gobe, ba zan karɓa ba, da na san bacci za ta yi daga nan ai gida zamu wuce kawai”

Aliyu ya ce “Tuba nake, zan kula sosai”

 

Juyawa mai sunan baba ya yi, ya shiga gida, ƙasan zuciyarsa istigfari, da tunanin meye nasa na jin haushi kuma, bayan komai daɗewa dole wataran ta zama matar wani.

 

Aliyu ya shimfiɗe rumaisa a katifar mama, Gwaggo cewa take “Wannan an yi shashasha amarya, haka take da wannan nauyin bacci haka, ta bar mutane da dakonta”.

 

Mama ta ce a tasheta ta yi sallar isha’i, lawisa ta ce sun yi salla a gidan kwalliya, kafin su tafi.

 

Tana magagin, mama ta dafa ruwa, ta kaita banɗaki ta wanke mata fuska, ta yi mata wanka tas, ta lulluɓota ta kawota ɗaki, ƴan biki na ta yi mata dariya, sai dai har a cikin ranta ji take ruman ba ta wuce wankan ba, ƙaddarar aure zata rabata da ƴar da take matuƙar ƙauna.

 

Ɗakin samarin nan kuwa, kusan kwana suka yi babu bacci, suna ta ɗan tattaunawa, a kan biki, da kuma jajanta rabuwa da tilon ƙanwarsu, kuma kallabi a cikin rawunansu.

 

Mai sunan baba kuwa ya naɗe, ya lumshe idanunsa ya yi shiru, ba abun da yake ganowa sai kai wa da komowar iman a wurin nan, da yadda suke yawan haɗa ido. Tsaki ya ja ya nemi wuri ya kwanta, sai dai tunanin gobe dai-dai lokacin, rumaisa na gidan wani, ya hana shi bacci, ya din ga yi mata addu’ar shiga gidan miji a sa’a.

 

 

Bayan idar da sallar juma’a, aka ɗaura auren rumaisa da adam, ƴan unguwar da basu san waye mijin ba a ranar suka ji.

Unguwar ta cika da dawakai, da manyan motoci na alfarma, duk in da ka kalla, jami’an tsaro da kuma masu rawuna ne.

 

Sai dai tun da aka ɗaura auren nan, rumaisa jikinta yayi sanyi, take ta uban kuka, duk yadda aka so rarrashinta abun ya gagara.

 

 

Tuni hotunan biki suka zaga duniya, kowa da abun da yake tofawa, na alkhairi da akasin haka.

 

 

Samha kuwa kaiwa take ta yi tana komowa a ɗakinta, tana fatan aikin da ta bayar ayi mata, ya yiwu ba tare da samun wata matsala ko akasi ba, dan ta riga ta ƙudirce wa kan ta ɗaukar fansa, ko da tsiya ko da arziki.

 

Ammi a wani event center, ta shirya taron wunin bikin, sai dai abu ya so ya zama rigima, in da facalolinta da masu goya wa mummy baya, suka din ga ci mata mutunci, wai saboda Aisha ba ƴar ta ba ce, ta shirya irin wannan biki haka, kuma aka samo yarinya mara galihu ta aurawa mahaukacin ɗan ta.

Duk yadda ammi ta so jurewa sai da ta kusa zubar da hawaye, Nusaiba ba ta da hayaniya, balle iman, Laila ce masifaffiya dama, kuma ba ta ƙasar da ita kaɗai ta ishi duk wani mai bakin magana.

 

Da la’asar mama ta kira ammi, ta ce mata za a kawo rumaisa nan wurinta, ta gaisheta ta yi mata faɗa, sannan a wuce da ita gidanta, ammi ta ce ba sai an kawota ba, saboda wasu dalilai, zuwa magariba zata turo da waɗanda zasu ɗauki rumaisa.

 

A yammacin aka yi kilisar dawakai, takawa ya haɗe cikin kayan sarauta, rumaisa ma aka yi mata ado da alkyabba, aka yi ta musu hotuna.

 

 

 

Da magariba rumaisa ta yi wanka, ido duk ya kumbura saboda kuka, Yasir da ya shiga ya fita ya ga tana kuka, shi ma sai ya fashe da kuka, ta tashi ta saka kaya ma abu ya gagara mama sai daurewa take yi, amma hawaye ya cika mata ido.

 

Jiki a sanyaye mai sunan baba ya shiga ɗakin, ya tarar da ita a zaune, tana kuka mai taɓa zuciya.

 

“Rumaisa” ya kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleshi.

 

“Tashi ki saka kayanki, kar dare yayi sosai”.

 

“Dan Allah mai sunan baba ku yi haƙuri, wallahi na fasa ni ba zan tafi na barku ba, mama dan Allah ku yafe mini ku barni na zauna a gida, ni ba zan iya rayuwa babu ku ba” tayi maganar cikin kuka.

 

“Tom, mun ji, amma fara saka kayan” da ƙyar ya saka kaya, ya ciro turare a aljihunsa ya fesheta da shi, mata sai rangaɗa guɗa ake yi.

 

Ta riƙe mama tana wani irin kuka.

 

Ya saka hannu ya cire nata daga jikin mama, ya ja hannunta yayi waje da ita.

 

Suna fita mama ta shiga ɗaki, ta fashe da kuka, dan an kai in da ba zata iya jurewa ba.

 

Suna tafe a mota tana kwamce a jikin mai sunan baba, tana ta kuka, kamar ta shiɗe.

 

“Am sorry, kiyi haƙuri haka lamarin aure yake, da haka kowace mace take tara nata iyalin, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, ya sanya alkhairi. Ban da rashin kunya da raina miji, mijinki ne ibada zaki je ki yi, ki nemi aljanna na san duk an gaya miki, ki girmama mahaifiyarsa, matar nan ina ganin mutuncinta saboda son da take yi miki. Sannan kuma Sabir ko Allah ya baki naki ɗan, kar ki canza soyayyar da ki ke yi masa, ki yi haƙuri ki saka a ranki, ƙofar sabon ƙalubale zaki buɗe ki shiga. Duk da ƙanƙantarki nauyin aure ya hau kanki sai haƙuri, kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, ki jure ki daure duk ƙalubalen da zaki fuskanta wataran sai labari, ina yi miki addu’a Allah ya sassauta miki jarrabawar gidan aure, don babu auren da babu jarrabawa”

Haka ya din ga yi mata nasiha, har suka je gidan, gida ya tsaru kamar ba na rumaisa ba, ko ina ya ji kaya.

 

Ana kai rumaisa wata ƙanwar ammi, ta sake saka mata alkyabba a kan kayanta, suka din ga yi mata guɗa a ka, amarya ƙanwar maza, dan su suka kawota ɗakin ma.

 

Sun daɗe tare da rumaisa, kowa da irin faɗan da yake yi mata. Sai da kowa ya watse, Tawagar angwaye suka ƙaraso, gida ba kowa sai tsirarin mutane da zabga-zabgan ƙarti.

 

Suna zuwa mai sunan baba ya tashi ya ce su tafi.

Rumaisa ta riƙe rigarsa ta tashi tana kuka “Dan Allah yaya umar, kar ku tafi ku barni, ku tafi da ni, ko ku zauna da ni a nan ɗin, dan Allah yaya. Yaya usy, yaya Abubakar, dan Allah duk ku zauna, Abdallah kar ku tafi, Yasir dan Allah” mai sunan baba duk ya kaɗa musu kai alamar su tafi.

 

Iman tana cikin waɗanda suka rage, gaba ɗaya tausayin rumaisa ya cika mata zuciya.

 

A hankali ya fincike rigarsa daga hannunta, ya juya, ta sake riƙo rigarsa.

 

Ya juya a kausashe ya ce “Wuce ki je ki zauna” a razane ta saki rigar ta sa tana kuka.

Yana juyawa sai hawaye, karo na farko da abu ya daki zuciyarsa ya saka shi kuka. Ya saka hanky ya goge, ya kalli Adam ya ce “Ga ta nan amana ce, marainiya ce, ko ka ci, ko kula da ita” yayi maganar wasu hawayen na cika masa ido.

 

Adam har mamaki yake, wace irin soyayya suke nuna wa rumaisa haka.

 

Bashir ya ce “Za a riƙe amana in sha Allah. Yallaɓai aje a rarrasheta dan Allah, tana cikin damuwa”.

 

Adam ya ce “Sai ma ka faɗa? Ba daga ni sai ita zaku tafi ku bari, wannan kuma ya rage nawa” dariya abokansa suka yi, suka yi musu addu’a sannan suka watse.

 

Ya koma ya shiga ɗakin na ta, tana tsaye tana ta kuka, ya ƙare mata kallo sannan ya ce

“Yau sarki mai koriyar alkyabba, ya baki alkyabba saura ɗana ki a kan doki. Sannan ke kuma ki cika alƙawarin sanya shi durƙusa miki a kan gwiwoyinsa”.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 60 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button