Hausa novels

NIHAAD Chapter 73 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

73

Khalil na fita dakin Abba ya kira Farooq, Farooq bai daga wayar ba ya mike kawai ya bi bayansa, he is so heartbroken, main parlor ya samesa tsaye, ya tsaya shi ma yana kallonsa bai ce komai ba, Khalil yace “This is not the rightful time for that conversation saboda condition din sa, u have to stop it plss, it’s not appropriate for his health” Farooq dai bai iya yace masa komai ba sai kallonsa yake, Khalil ya juya ya fita daga parlon, Farooq bai sake komawa dakin Abba ba, ya nufi dakinsa walking slowly yana ganin kamar mafarki kawai yake. Inna na ganin hawayen da Abba yake ta rushe da matsanancin kuka cike da takaici tace “Wallahi kin cuce mu Sumayya, kin cucemu, Allah ya isa bamu yafe maki ba, ashe duk ke kika lalata masa gidansa duk kokarin da yake na ganin ya ba ‘ya yansa tarbiya nagari, duk kokarinsa na ganin ‘ya yansa sun zama na kirki kin tarwatsa masa, daga me Video dake yawo a gari sai warce aure ya mutu an korota gida sannan uwa uba wai yau cikin shege a zuri’armu, cikin shege fa?? ya ya zaki yi da wannan hakkin sumayya? Kuma saboda karancin tsoron Allah kike nema ki alaqanta duk wannan abun da Ibrahim, dama can kafura ce ke kawai wacce babu Allah a ranta, to bazan boye maki ba a gaskiya zamanki ya zo karshe a gidan nan, ni kaina baxan jure ci gaba da ganinki ba balle shi wanda kika cuta ga har ciwo ya kama sa, ki tattara yanaki yanaki ki kama gabanki kawai Sumayya, ganinki kadai ya isa yasa Ibrahim yaki warkewa wallahi, ki je duk inda za ki mu kuma baza mu hana yaranki zuwa gareki ba tunda ke kika haifesu, alhakin abinda kika so ma Nihad ne ya sauka kan er ki, Sumayya kin cuci Ibrahim don Nihal din ma er sa ce ba abinda zai canza hakan, shi yasa aka ce in zaka gina ramin mugunta ka ginasa karami, ke ko baki yi wannan tunanin ba…” Umma dai bata ce komai ba sai kuka take ta dafe kanta, Mumy ta kasa dago kanta ita ma hawayen ne ke sauka idonta, Nihad kuwa gaba daya ta shiga rudani jin Inna ta ambaci cikin shege, waye kuma yayi cikin shege, Nihal?? No it can’t be Nihal, Tashi Usman yayi ya fita daga dakin cause he can’t endure it anymore, Umma ta mike tana share hawayenta da zumar fita ita ma, taji muryar Abba a hankali yace “One more thing Sumayya….” Ta juya ta kallesa, yace “Tell me what u know about Nihad’s Video….” Ta ɗan yi shiru na few seconds, sai kuma hadiye kukan da take tace “Kawayenta ne suka yi drugging dinta sannan suka mata video din suka kuma saki a duniya…” Mumy ta daga kai da sauri tana kallon Umma, Inna ta sake salati tana zaga dakin hankali tashe, Alhaji Abubakar dai is totally speechless, a hankali Abba yace “U asked them to do that?” Umma ta girgiza kai tace “Sai bayan da suka yi ni nasani, i never asked them to do that…” Yace “Shikenan, Kije… ni kam na yafe maki, a duk zaman mu idan akwai inda na kuskure maki ko yaranki ina neman gafara, Allah ya yafe mana baki daya” Tana share Idonta tace “Ameen, ni baka taɓa min komai ba, Allah ya baka lafiya” Daga haka ta juya ta nufi kofa inna ta bi ta da sauri tana hawaye tace “Ai komin dare ana samun a kori kura, aje a samo ki kwashe kayanki Sumayya kada abu ya lalace mana ni da ke cikin dare” Mikewa Kamila da Amina suka yi suka bi bayan uwarsu ko warce da hawaye fuskarta, Abba ya kalli Mumy dake kallonsa tana hawaye ita ma, cikin sanyin murya yace “I am sorry i never played my role well as a father, i am sorry i broke my family….. I am sorry for everything” Alhaji Abubakar yayi karfin halin cewa “Kar kace haka Ibrahim, komai kaga ya faru a duniya Allah ne ya tsara hakan, stop thinking u failed ur family, u never failed them, u were and will always remain a good father…” Da kyar Abba na kallon Mumy yace “Ki kira min Nihal” Alhaji Abubakar ya dafasa yace “Noo, not now Ibrahim, sai ka kara samun lafiya sosai, yanzu a bar wannan maganar haka, u need rest for now pls” Abba bai kuma ce masa komai ba, Mumy ta share hawayenta ta mike ta nufi kofa a sanyaye ta fita daga dakin, Nihad dai ta kasa tashi a inda take sai kuka take a hankali, ganin Abba kallonta yake ta mike cike da karfin hali ta tafi can kusa da shi ta durkusa cikin rawan murya tace “Abba kayi hakuri, all this is happening because of me, i caused all this, i am sorry Abba, May be you shouldn’t have….” Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Abba dai sai kallonta yake ya kasa cewa komai, nan kuwa tuna irin yanda Allah ya dora masa sonta a zuciyarsa tun tana er yarinya yake, wanda tun a sannan bai iya boye son nan ba har girmanta, kaf ‘ya yansa babu warce yaji har ransa kamar ita, and Umma used that against him by helping him to love her whereas ba haka bane a zuciyarta, Umma used that to runined him and his family, Hawaye Nihad ta gani a idonsa ta fashe da kuka sosai ta ma rasa abinda zata ce masa ta daura kanta a jikinsa cikin rawan murya tace “I am sorry Abba, i am so sorry Abba” murya can kasa yace “I will always love and Cherish u Nihad, you still remain my favourite, Allah ya baki zaman lafiya da mijinki, Allah ya baki ikon yi masa biyayya kamar yanda mahaifiyarki ta min, Allah ya baku zuri’a dayyaba, at last everything turns out to be in ur favor…. ” Ganin irin kukan da take yi Alhaji Abubakar ya mike ya dagata yace “Tashi ki je Mamana, Allah ya maki albarka” Har kofar fita parlon ya rakata sannan ya koma gun kanin nasa. Har kusan karfe sha biyu Nihad bata hakura da kukan da take ba, gani take kamar saboda ita duk abubuwan nan suka faru, and condition din da Mumy ta gaya mata Nihal ke ciki contributed wajen kara daga mata hankali ta kasa daina kuka, tsabar yanda hankalinta ya tashi bata iya ta je dakin Nihal din ba, she don’t even know what to say to her, it’s till hard to believe wai she is pregnant, Mumy ta fito parlor ta dalilin wayarta dake ring ta duba taga Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi tare da yi masa sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Mumy hope ban tashe ki bacci ba” Mumy tace “Aa ban kwanta ba tukun” Yace “Dama zan ce maki magungunan ta na cikin akwati ne” Mumy tace “Ohk bari in duba” Daga haka yayi ma Mumy sai da safe ta katse wayar, ta mike ta nufi akwatin Nihad ta bude ta ciro magungunan sannan ta duba prescriptions din ta bata ta sha,Tana shan maganin ba a dau lokaci ba bacci me nauyi ya dauketa. All through the night Mumy bata wani rintsa ba, to ina ma taga kwanciyar hankalin bacci, lokaci lokaci kuma take shiga dakin Nihal ta dubata sannan ta dawo ta ci gaba da sallanta, Inna kuwa na parlon Abba a nan aka mata shimfida da bargo don taki bin Alhaji Abubakar gida, ita ma dai bata yi baccin kirki ba sai sallah take tana roka ma ɗan ta lafiya a wajen Allah, duk a daren ta yanke shawaran kawai ta dau Nihal ta kai ta Bauchi wajen kanwarta har Allah ya sauketa a can don idan har uban na ganinta a gabansa da kyar ya samu lafiya har ya tashi, gwara kawai ta nesantata da shi, ta kai ta can inda bata san kowa ba tayi rainon cikin tunda taji ance baza a zubar ba, Umma ma dai yanda taga rana haka taga dare nan babu ko digon bacci a idonta, yanda take ji kuma a jikinta tasan jininta ya kara hawa, a daren nan tayi mugun da ta sanin duk abubuwan da ta aikata, tayi da ta sani ya fi a kirga, kamar yanda Inna ta fada babu abinda yaranta suka rasa gun Abba kawai son zuciya ne ya kai ta ya baro, duk da baya nuna masu irin son da yake ma Nihad din a fili amma basu taɓa kawo bukatunsu ya ki yi ba ko ya hanasu, Nihal ce dama bata iya tambayarsa abu, komai take so sai ta bi ta hannun Umman, shi ko Abba idan baka tambayesa ba he will assume u don’t need it, Nihad kam kullum cikin tambaya take kuma kullum cikin bata yake, Usman da Farooq throughout the night suna tare da Abban nasu a dakinsa, Khalil dai lokaci lokaci yake shiga ya duba jikinsa a cikin daren, idan ya dubasa kuma ya koma dakin Farooq, Mumy na son shiga ta duba Abban amma ta kasa zuwa sanin Inna na parlon nasa sannan su Farooq na bedroom dinsa. Karfe hudu da yan mintuna Mumy ta samu ta kwanta bacci ya dauketa, 4:30 Khalil ya fito daga dakin Farooq ya nufi bangarem Abba, duk da an hour ago ya shiga ya dubasa last, kwance ya samu Inna a parlon tana bacci har da minshari, wanda daxu da ya shigo idonta biyu tana ta sallah, walking gently don kar ya tasheta ya nufi dakin Abba, dazu da ya shigo Farooq ne kawai ke bacci Usman idonsa biyu, amma yanzu kuwa duk bacci suke saman Carpet din dakin, ya karasa saman gadon yana kallon Abba don ba a position din da ya bar shi dazu ya samesa ba ya karkace kansa dake kan pillow, dukawa Khalil yayi murya can kasa yace “Abba ya jikin?” Abba bai ce masa komai ba, ya kai hannu zai gyara masa kwanciyar saboda kar wuyarsa yayi ciwo sannan ya danne hannunsa me matsala, Khalil ya fi 20 seconds yana kallon Abba babu ko kiftawan kirki, can ya kwantar da shi da sauri ya cire pillow din da yake kai gefe yana duba every pulse that he can check a jikinsa, ji yayi kafafuwansa sun kasa ci gaba da daukarsa, bai san sanda yayi kneeling down nan kasa ba yana ci gaba da kallon Abban, lokaci daya ya hade kansa da gefen gadon hawaye na sauka idonsa a hankali yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un a zuciyarsa, Muryar Farooq yaji yace “Ohh i slept off….” Khalil dai bai iya ya dago kansa ba, Farooq ya mike ya dawo kusa da su yace “Ya samu baccin?” Hawaye kawai ke sauka idon Khalil ya kasa ce masa komai, Farooq ya kalli position din da Abba yake sai kuma ya kalli Khalil da sauri, lokaci daya yaji gabansa ya wani fadi, ya duka gaban Abba da sauri ya riko hannunsa yana jijjigawa yace “Abba… Abba” Yaga ko motsawa Abba bai yi ba, kiran da Farooq ke ma Abban ne da karfi ya tada Usman, ya tashi tsaye da sauri, Farooq ya kai kansa chest din Abba jikinsa na rawa and he heard nothing like heartbeat, ganin abinda Farooq yayi Usman ya nufosa hankali tashe yace “What is the meaning of that???” Shi dai Khalil ya kasa dagowa ya kallesu, he was weak all over, hawaye ya kasa daina zuba a idonsa, Farooq ya hade kai shi ma da jikin gadon hawaye na sauka idonsa yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” hayaniyar Usman ne dake ta jijjiga Abba yana kiransa ya tada Inna, da gudu ta shigo dakin a rikice, jiki na rawa tace “Menene kake kiransa haka Usuman??” Usman ya fashe da kuka ya durkusa nan kasan dakin, Inna ta tafi saman gadon da sauri ko ina na jikinta na bari tana cewa “Ku gaya min me ya samesa, me ya samu ɗan nawa? Wayyo Allah na ku gaya min don Allah” Ganin babu me shirin bata amsa, ga Khalil da Farooq sun ki dago kai, Usman kuma yayi zaman dirshan a kasa ya rike kai yana kuka, ta fashe da matsanancin kuka da gudu ta fice daga bangaren ta shigo main parlor a gigice ta saki salati da duk karfinta, sai kuma ta fasa ihu ta daura hannu a ka tana zaga parlon, Mumy ce ta fara fitowa da sauri daga ɓangarenta a tsorace, Sai ga Umma ma ta fito da su Kamila, Nihad ma ta fito daga parlon Mumy, Inna na kallon Mumy ta kara kwala ihu tana girgiza kai tace “Na shiga uku Maryam, wayyo Allah na Maryam, na shiga uku na lalace, su ce min wasa suke min, Innalillahi wa inna ilaihi raji’una….” Sai kuma tayi collapse nan kasa, Umma dai jikinta sai rawa yake ta kasa karasowa cikin parlon, Mumy bata kara kallon Inna ba ta yi bangaren Abba duk jikinta na rawa ta shiga, Nihad bata san sanda ta bi bayanta ba ita ma da sauri, dai dai sanda Khalil ya mike ya ja ma Abba abun rufansa ya rufe har kansa Mumy ta shigo dakin, Banda kuka babu abinda Farooq da Usman suke, Mumy taji wani jiri ya debeta ta fadi a sume nan kasan dakin, wani kara Nihad ta kwala da karfi ita ma ta sulale nan kasa…. Kafin wayewar gari gidan Abba ya cika babu masaka tsinke da jama’a, ko wajen parking babu a layin, abokansa na wajen aiki, yan uwa da abokan arziki, makota, wa enda ya taimaka a rayuwa, childhood friends duk dai gasu, babu wanda bai ji mutuwarsa ba, da yawa al’umma sai da suka yi kwalla, shaidar da Abba ya samu kuwa ba a cewa komai, an masa shaidan mutumin kirki me rike ibada sannan me tausayi da taimakon talaka, Aminu kuwa kai kace Mahaifinsa ne ya rasu don can bayan gidan ya tafi ya dinga kuka yana buga kai, haka Saminu da Isiya, karfe takwas saura Janar da abokansa biyar suka iso gidan tare da Mami da su Mimi…. Mami was more than shock ta kasa kallon Mumy ta nemi waje a parlon dake cike ta zauna tana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji’una a zuciyarta zuwansu gidan da kuma position din da Abban ya zauna cikin parlon yana magana cikin girmamawa cike da dattako kawai take tunawa, irin kukan da Umma ke yi a parlon dole a tausaya mata, duk ta birkice ta dawo kamar wata tabaɓɓiya, Mumy dai ba um ba um um sai hawaye don zuwa lokacin sumanta uku, Aunty Jamila dake gefenta tana ɓata baki cikin nutsuwa ita ma dai kukan take, haka frnds dinta su hudu da ko wacce kokarin kwantar mata da hankali take, Karfe tara aka tafi kai Abba makwancinsa, a sannan ne Mumy ta kara realizing da gaske tayi loosing mijinta forever and she couldn’t endure it any longer, hakan yasa su Aunty Jamila suka shiga da ita part dinta. Bayan an dawo daga kai Abba Mami ta samu Khalil a compound tana tambayansa Nihad don tun da suka zo bata ganta ba, tana son tasan halin da yarinyar take ciki, bai iya ya daga kai ya kalli Mami ba yace “Tana asibiti tare da wata Aunt dinta, she miscarried the pregnancy….” Mami ta kasa cewa komai tana kallonsa, can tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, hope she is fine amma?” Yace “Yanzu zan je can din, an mata alluran bacci ne tun wajen 6” Mami ta kasa cewa komai, she really pitied the family sosai, a hankali tace “Toh ka je, Allah Ubangiji ya bata lafiya, ita ma mamarta da alluran baccin aka samu aka yi mata” Yace “Bari dai in je asibitin in dawo, kakarta ma na asibiti” Mami tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Juyawa Khalil yayi ya nufi gate, a sanyaye Mami ta koma cikin gidan….

*Barrister yace harba masu haka nan ko ba yawa su yi maneji* 😟

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Download NIHAAD Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Back to top button