Ya dau lokaci yana kallon ta, cikin rawar murya Jalila tace “Sannu ya jiki?” shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa, “Ko inkira maka Jawwad” still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi “Inkira maka likitane” takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta “Kukan mekikeyi? Nakumamiki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?”
Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace “kidenamin kuka, nagaya miki kincikamin kunne”
“Yi hakuri na dena” tasa hannu ta share hawayenta, Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace “Sannu ya jikin naka?”
“Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni” murmushi likitan yayi sannan yace “kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma dawo da kai Rai a hannun Allah”
Jawwad yace “rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza’a sallameshi ba seya warke gaba daya”
Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace “Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi” Sannan likitan ya kalli Jalal yace “Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni”‘imar ubangiji meze daga maka hankali haka? ” kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa ” Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo’in ciwon ido dake sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic ” shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace “Shikenan doctor za’a kiyaye Insha Allah”
“Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki” doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace “Kaji abunda doctor yace ko? Please and please kakiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa” Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace “Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin”
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace “Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba”
Jalila tace “Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye” takarasa maganar tana dan tura baki, Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace “itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin” Jawwad ya mike ya fita, Jawwad na fita Jalal yai kokarin komawa ya kwanta beci Abincin ba da sauri Jalila tace “Ai bakaci Abincin ba” ya kalleta “Bazanci ba” yakuma kokarin kwanciya Abincin ta dauka ta dora a inda ze kwanta tace “wai meyasa kafiye taurin kaine? Cewa fa akayi kaci Abinci”
“Ke har na kaiki taurin kaine? Waima ina ruwanki danine? Dan giya, mara tarbiyya, zan lalata miki dan uwa, me kike nema a gurina, dauke Abincin ki bazan ciba, kintaba gayamin idan na mutu bakida Asara to meye naki na damuwa da banci Abinci ba?” yasa hannu ya dauke Abincin ya dora akan drower na kusa da gadon sannan yace “Dama a duniya daga daddy se Jawwad ne suke sona se yan uwan daddy, nan duniya idan na mutu ba wanda yakeda Asara, sesu”
kura masa ido tayi “Meye kuma kike kwalalamin idanuwa haka, kidena kallona” yai kwanciyar sa.
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Kawai Jalila ta mike ta fice daga dakin, Ajiyar zuciya Jalal yayi dayaga ta fita ya dakko Abincin data zuba ya ci ya aje sauran. Jalila na fita tasamu guri ta zauna a waje ta dakko wayarta tafara chatting tana daga kai ta hango Ilham da mahaifiyarta a harabar Asibitin kallo daya tayiwa Saudat tagane itace mahaifiyar Ilham,
da sauri Jalila ta tashi ta koma dakin Jalal, tana zuwa taga yaci Abincin yana kashingide ya lumshe ido, yana jin motsinta ya bude ido,
“Ke meya dawo dake, ko dama bakida zuciya?” cikin tsiwa tace
“dama ina naga zuciya, tunda kaima bakada ita”
Dan zare ido yayi, ashe halin nata yana nan
Ta fara hada kan kwanuka, Ilham ce da Mamanta suka shigo da sallama yanajin muryarsu yai Sauri ya rufe idonsa. Kai kace bacci yake, Tunda Ilham taga Jalila a gurin Jalal ta hade rai kaman taga kashi
Jalila ta maze tace “Sannunku da zuwa” yawwa maman Ilham ta amsamata, tabasu guri suka zauna Ilham se harar Jalila take, ita kam Jalila data kalli Ilham seta mata murmushi Maman Ilham tace “Yame jiki?”
“da sauki Mama”
“naga alamar kaman yana bacci ne ko?”
Jalila ta waiga ta kalleshi yawani rufe ido kaman gaske amma idonsa biyu, se Jalila ta kudurce wani abu a ranta dan haka Jalila tace “
eh likita yamasa Allurai yasamu bacci, likita yace baze farka ba se bayan Awa biyar, yanzu besan me ake ba”
Maman Ilham ta kalli Jalila tace
” Sedai bangane wannan ba, bakowa a gurinsa seke? ko itama a dangin babanasa take?”
Ilham tai farat tace “Inafa,” yar shishshigi yar wahala dai, me hana ruwa gudu, me cusa kanta inda Allah be kaita ba” Jalila tace “haba Ilham, wani ma se yazata banida kirki, menamiki haka ina laifin kice, Sauro me hana giwa bacci, Raina kama kaga Gayya” Jalila ta karasa maganar tana murmushi tace “Mama bari in saka wayata a caji, in karbo muku ruwa a waje” Jalila ta mike ta dau wayarta ta dan daddana sannan tasaka ta a caji ta fita. Ba’a wani dade ba, Jalila ta turo kofa ta shigo da ruwan roba ta ajiye musu ko sha basuyi ba suka tashi sukace tafiya zasuyi. Tai musu sallama suka mata banza Ilham nata gaya mata bakaken maganganu bata damu ba suna fita taje ta dauki wayarta ta bude, maganganun dasukayi tsaf tayi recording dinsa tai Saving tajuya ta hada kan kwanukan da Jalal yaci Abinci, bude idonsa yayi yana kallon ta tana dagowa suka hada ido
“Akwai matsala ne?” Jalila ta tambayeshi
“Wani Apple kika hanani ci kika musanya ranar da mukayi baki?” tambayar tazo mata a bazata, ta dan tabe baki sannan tace “Apple kuma ni ban san zancen ba”
“Karya kikeyi” Hade rai tayi sosai
“Eh kasan na saba” tacigaba da abunda take, ko ina yasan wannam maganar oho masa, ta mike tsaye taji ya janyo ta da karfi kan gadon, take jikinta ya hau rawa ta tsorata sosai ta ware ido tana kallon sa
“Ina tambayar ki kina rainamin hankali wani Apple kika hanani ci, kuma meyasa?”
“ni nace maka ban san zancen ba, ka tambayi wanda suka gayamaka mana, ni kacikani” kara karfin rikon yayi taji kaman ze karya ta, sannan yace “ke bana son karya, for the last time ki gayamin” kawai ta fashe da kuka, mamakine yakama shi, in wani ya shigo se a zata wani abun yayi mata, dan haka a hankali ya sake ta ta mike da sauri ta koma waje, tana fita ta dakko wayarta kunna maganganun Ilham da mamanta. Kawai taji maganar Ilham tana cewa
“Umma wannan itace munafukar da nake gayamiki duk lokacin danayi wani yunkuri zanyi wani aiki akansa itake lalatawa, na dade da gane take takenta sonshi take, amma taki yadda tana rainamin hankali, tasamun Ido ta hanani sakewa, duk lokacin danayi Yunkurin wani abu idonta na kaina, seta wargaza gashi ta hadani dawata tsinanniyar karuwa wai budurwar Jalal ce, hatsabibancin yarinyar nan ya wuce tunaninki, harda wani alwashin indai tana Raye seta rusa shirina akan Jalal” mamanta tace
“Ke sokuwar inace? Kika kasa gayamin tuntuni mu dau mataki akan shegiya”
“Umm har gurin Malam na kaita amma yace baze iya komai akanta ba, dakike ganinta ita ta musanya Apple din dana sawa maganin ranar, makira tsinanniya” umma ta girgigiza kai tace
“Tab aikuwa da sake, dole muyi wani abu karta bata mana aikinmu, amma Khadija kuwa tazo taga halin dayake ciki?” Ilham tace “Ai ingayamiki baya son ganin ta, kinga abunda ya dinga yi kuwa sekace ya haukace, dakinsa na nan kaman kantin mahaukaciya ya fasa komai a dakin, sangartacce ubansa na dawowa za’a canza masa komai” suka cigaba da maganganun su a zatonsu duk Jalal bacci yake besan mesuke ba, ita kuwa Jalila tana sane tayi haka.
Shiru Jalila tayi tana tunani “Kenan Jalal yaji duk maganganun da sukayi shine yake tambayata? Kafin kuga bayana zanga naku”
Jawwad ta hango ya taho da leda a hannunsa, yana zuwa inda take yace “Am sorry na tafi nabarki ko? Na dade bansamu maganin bane, bari inzo in maida kw gida nasan kin gaji”
“To Yaya sannu da zuwa”
“Yawwa babyn Yaya” yai mata murmushi ya wuce, yakai minti goma sha biyar sannan ya fito ya dauki Jalila suka tafi gida. Suna zuwa gida gaban Jawwad yafara faduwa, sakamakon tarar da Maama a harabar gidan da sukayi a tsaye da alamu a zuciye take, Jalila ta fito daga mota, Maama ta dinga jefamata wani irin mugun kallo, Jalila ta basar tace “Maama sannu da gida” tafada tana kokarin wucewa cikin gida “Dakata algunguma” ta dakatar da Jalila, Jalila ta tsaya ta sunkuyar da kai, Jawwad yafito ya rufe mota yakaraso gurin Maama yace “Maama, meyafaru ne?”
“Ubanka ne yafaru, daga gidan ubanwa kuke? Da kuka fita tun farar safiya se yanzu kuke dawowa?” Jawwad ya dan girgigiza kai yace “Kiyi Hakuri, ta rakani gurin Jalal ne, muna Asibiti tun dazu”
“Yimin shiru makaryaci banza da na wofi, kai ko kunya bakaji ka dingamin karya, Asibitinne se yanzu zaku dawo, tafara janka gantali ko, wallahi ka biye mata kafara aikata wani abu dayasaba da al’adunmu se ranka yabaci, tun yaushe Nake maka magana akan Naja, fafur kaki kaje ko inda take, tunda abun naka hakane Naja ta dawo gidan nan, kuma kobakabso seka Aure ta” ta juya ta kalli Jalila tace “Kekuma ko mayyace sekin kyalemin dana, akan me ke baki da zuciya ne? Wallahi kifita daga idona, shegiya mayya” ba Jalila ba hatta Jawwad seda ya dago Ido suka kalli Maama a tare, Jalila ta juya ta shige cikin gida ta barsu a gurin, tana shiga palour ta fara kicibisa da yaya mairo da Naja, a ranta tace “Ashe wannan ibilishiyar matar ce tazo shiyasa yau akemun saukalen Rashin mutunci, tun daga harabar gida ai shikenan”
Aibata gama zancen zucin ba ta tsinto muryar Yaya mairo tana fadin “Ga shedaniyar nan makira, wallahi kozaki mutu gidan nan ma se ya gagareki zama, kuma seya Auri Naja, danbazamu Aura masa Arniya ba, wadda uwatta ta gudu tazabi barbadanci ta battaba, Nutsatsiya zamu aura masa yar musulmi” Jalila ta tsaya ta waiga taga daga ita se su a palourn Maama tana waje tana cigaba da saukewa Jawwad kwandon jaraba, Jalila tace “To ayi mugani mana, karewar nutsatsiya masallaci Zaku Aura masa, sannan kika kuma zagarmin uwa wallahi sena kira taki uwar na zaga dan uwa bata fi Uwa ba” Naja ta mike a fusace tace “Ke dan uwarki uwatawa zaki zaga”
“badai uwata ba, wannan tsohuwar banzar kika zaga, kinbiyata ladar haihuwarki datayi, kuma Na zageta ita wacece? Ko fin tawa uwar tayi? Kuma wallahi takuma zagarmin uwa sena fasa mata kai da wannan flask din” Jalila ta nuna tea flask din da takaiwa Jalal Abinci a ciki, hangame baki Yaya mairo tayi Jalila tace “Yanzu nasan ciwon kaina, ina zubarda hawayena ne a inda yakamata, nadena asararsu akan maganganun ku, iyakaci duk tsufan mace ta zagarmin uwa sena rama wallahi, Sannan ke Naja naji ance kindawo gidan nan da zama, kinyi kwantai ana cusa masa ragowa yana baya so amma, saboda ansan baki da mamora, se cusaki akeyu, to kinkawo kanki, bacin ran da uwarki ta dinga kunsamin tsawon shekaru sena ramasu akanki wallahi, kuma kafin inbar gidan nan sena sena tabattar da kin barshi tukuna” Jalila ta juya tai wucewarta daki yayinda Naja da yaya mairo suka rasa abun cewa, Naja tai karfin halin cewa “Lallai yarinyar nan rashin mutuncin ta yakara yawa, amma karki damu, ni zan saita mata zama namiki alkawarin, setabar gidan nan da kafarta, kuma sena Auri Jawwad, kiyi hakuri zan ramamiki” Naja na rufe bakinta, sega Maama sun shigo ta sako Jawwad a gaba tanata masa masifa shikam ya sunkuyar da kansa kasa har suka shigo cikin palourn
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Nan Maama da yayarta, Yaya mairo suka saka Jawwad agaba da fada, shikam yayi shiru yakasa cewa komai babban abunda yake kona masa rai be wuce yadda suke cin mutuncin Ummi ba, matar da basuda tabaccin tana raye ko bata raye, seda sukayi suka gama sannan ya mike ya bar palourn, Yaya mairo tacigaba ds zuga Maama tana kara cusa mata tsanar Jalila a ranta. Yaya mairo ta tafi tabar Naja a gidan, koda Nana ta dawo gida ta tarar da Naja a gidan ba karamin haushi taji ba, dan sam Allah be hada jininta dasu ba.
Jalila takira Hanan a waya, tagayamata abunda ke faruwa, Naja ta dawo gidan da zama ita ake so Jawwad ya aure. A fusace Hanan tace “Kan bala’i, wallahi ba’a isa ba” cikin mamaki Jalila tace “Kamar yaya kenan?”
“kamar yadda nagaya miki, ai wannan fadan banaki bane Jalila nawane, ai muna nan zuwa Kanon very soon, ina baze yuwu ba, ai gara in barmiki Jawwad da ina gani ya Auri wannan yarinyar, gentle man like Jawwad, be dace da Auran ballagaza kaman wannan yarinyar ba dukda kasancewar ta yar uwassa” Hanan ta dinga masifa karshema ta kashe wayarta. Mamaki duk yakama Jalila dama dagaske Har yanzu Hanan bata hakura da Jawwad ba? Haka Jalila taita tunani.
Washegari aka sallamo Jalal daga Asibiti ba laifi jikinsa yaji sauki sedai rashin kwarin jiki, Jawwad ne ya dawo dashi daga Asibiti, Dakin Jalal sam yayi kaca2 da kwalabe da abubuwa dan haka suka wuce dakin Jawwad.
Jalal ya kula da yanayin Jawwad kaman ransa a bace yake, dukda Jalal dinma nasa ran ba dadi amma yace
“Jawwad meyake damunka ne? Saura kacemin bakomai dan fuskarka ta nuna”
Jawwad yace “Jalal duk na rasa meyakamata inyi” nan ya kwashe komai yagayawa Jalal”
“Bazaka Auri wata Naja ba”
“Wallahi Jalal nima bana sonta amma Maama ta dage na rasa ya zanyi”
“Karka damu zamu samu mafita amma wannan yarinyar ba matar Aure bace, dan sam baku dace ba” Jalal yaita kokarin kwantar wa Jawwad hankali yayin da shikuma gefe guda tasa damuwar nakuma sassakar zuciyarsa, musamman idan ya tuna maganganun dayaji Ilham tanayi da mamanta akansa.
A ranar da yamma daddynsa ya dawo, bagan magariba Jawwad yaiwa Jalal rakiya zuwa gidansu, har palourn daddy sedai daddy beji dadin yadda ya tarar Jalal yai rashin lafiya be Sani ba, Jawwad yace “Ai yaji sauki daddy ya warke, bekamata kana can mu tayar maka da hankali ba gashi yaji sauki” daddy yace “Hakane ya jikin naka?”
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace “Naji sauki” Mummy ce ta shigo palourn da cup din tea a hannunta, tazo ta samu guri kusada daddy ta zauna sannan tace “Ya jikin naka?”
Banza yayi yaki kulata, sema dauke kai da yayi, Jawwad yace “Jalal Mummy namaka magana fa” wani uban tsaki yakuma yi ya dauke kai, daddy yace “Haba Son Mum cefa, at least kagaya mata how you feel zataji dadi” mikewa Jalal yayi ya nufi hanyar fita Jalal yabishi yana cewa “wai Jalal wani irin mutum ne kai? Baka kyauta ba meyasa kake hakane, mahaifiyarka cefa?” tsayawa yayi ya kalli Jawwad yace “Ta haifeni ne kawai, amma bata amsa sunan uwata ba, ka gayamin ya dace abunda taiwa dangin mahaifina, shikenan ni haka zan kasance bawanda ze dinga rabata, ba soyayyar uwa, ba dangi ba abokai, haka zan kare Rayuwata, kaikadaine ka iya jure halin mahaifiyata kae taredani har zuwa wannan lokaci, Jawwad yaushe zan samu sassauci akan kaddarorin Rayuwata why me? Mahaifiyata amma kullum itake kokarin rusani itafa ta haifeni, bata tausayamin kodan irin Rayuwar dana shiga saboda ita? Kowa ya gujeni nazama abun kyama, shikenan nasan matakin dazan dauka” yana zuwa nan a zancensa kawai ya juya ya fice da Sauri, Jawwad ya mike ze bishi daddy yace “Son kyaleshi, inka bishi maybe ya sauke maka yabata maka Rai karkaje inda yake a yanzu, zoka zauna nan ina so zamuyi magana da kai, Jawwad ya dawo ya zauna, Daddy ya kalli Mummy yace” Khadija dan kina mahaifiyar Jalal, dole kicire girman kai ki nemi Afuwarsa dan tabbas kin cutar dashi,
Mummy tace “Nifa ina mamakin cewa dakuke nice sila, wace uwace zata sa hannu danta ya lalace, menayi dayazama nice silar lalacewar sa, Jalal ne yakamaga yanemi yafiyata batamin randa yakeyi”
Ta mike a fusace tabar palourn, Jalal kam yana fita yacikaro da Ilham a harabar gidan yabita da wani mugun kallo na tsantsar tsana, seda tasha jinin jikinta, yasa kai ya fice a fusace, Jalila na kan step din palour taga Jalal ya shigo gidan ya nufi part din Jawwad, se hada hanya yake kaman baya ganin gabansa sosai daga inda take ta hango kaman da hawaye a idonsa, da Sauri yakarasa part din Jawwad ya tura kofa ya shiga aiko itama da sauri ta sakko tabi bayansa.
Amma tana zuwa kofar dakin seta tsaya tafara tunani “to idan naje mezan ce masa? Inkuma ya makeni fa?” juyowa tayi zata koma, kawai taji kaman Jalal yana fidda numfashi da Sauri.
Da sauri ta bude kofar ta shiga, yana tsaye yana kaiwa yana komowa, idonsa yazama abun tsoro saboda ja, ga jijiyoyin kansa duk sunfito sun mimmike, gashi da kyar yake sauke numfashi, se faman runtse ido yake, da Sauri Jalila takarasa tace “Jalal meya sameka? Wani abun yafarune? Ko jikinne?”
Banza yai mata ya juya mata baya, da sauri ta zagaya gabansa tana kokarin kallon fuskar sa, amma yasa hannu ya hankade ta, bige hannu tayi ajikin center ta rike gurin tana dan cije lebe tareda ya mutsa fuska alamun taji zafi, ta bugu sosai a hannun, mikewa tayi takuma komawa inda yake, a hankali ta ga ya sulale ya zauna yana motsa bakinsa alamun yanaso yai magana amma yakasa, kawai ya lumshe ido hawaye na fitaa a gefen idonsa, gaba daya yanzu Jalila tausayinsa takeji, tabbas Jalal na cikin kaddarar rayuwa amma hanyar daya dauka ba itace mafita ba. Taje gabansa ta zauna ta dan kura masa ido na wasu mintuna sannan tafara magana cikin nutsuwa da kwantar da harshe
“dukkan dan adam ba abarinsa ba tareda jarabbawa ba, Kowa da kalar tasa kaddarar, inkaji ta wani sekaga taka ba komai bace, Annabi Ibrahim alaihi salam, Annabin Allah ne, ya kira mutanensa akan bautar Allah shikadai, amma Mahaifinsa be musulinta ba, hakan besa ya saba masa a matsayinsa na mahaifinsa ba, karshe ma har wuta aka hada domin a kasheshi amma Allah ya tsallakar dashi.
Annabi Yusuf alaihi salam, Mahaifinsa na matukar Kaunarsa amma se aka Jarrabeshi akan Yan uwansa, suna masa hassada da kaunar da mahifinsu kemasa kaga matsayin sa na Annabin Allah amma har kurkuku yayi, amma daga karshe kaga daukakar daya samu.
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Annabi musa alaihi salam shima yayi gwagwar maya, bayan Allah ya tsalakka dashi daga sharrin fir’auna, kalli butulcin da mutanensa sukayi masa, kowane Annabi da kalar jarrabawar da Allah yai masa. Annabawa kenan ina gamu daba kowan kowa ba, wasu na Kabari, wasu na Asibiti se an kwantar an tayar, wasu na prison basu ba kara shakar iskar yanci, wasu na gidan masu rangwamen hankali, wasu na gidan marayu ana musu kallon shegu, wasu guragu ne, suna maula a gefen hanya, wasu yaki yasa sun rabu da iyalansu da yan uwansu, duk cikin wannan ba wanda Allah ya jarabceka dashi, karka zama me butulci da Ni’imomin ubangiji no matter how worst the situation is kazama me gode masa, kanada dama, kanada lokaci kayi kokari ka gyara barnar dakayi a baya, ka yafewa mahaifiyarka inka yafe mata se Allah ya shiga cikin lamarin ka. Anyway for now don’t try to kill yourself without changing your life style. Yai shiru idonsa a lumshe amma nasihar Jalila yaji tana tasirir a zuciyarsa a zuciyarsa ya shiga Fadin Astagfirullah wa atubu ilaihi, amma deep into his heart in ya tuna yadda take masa rashin mutunci se haushinta yakama shi, a fili ya bude idonsa yace
“Tashi kibani guri bana son ganinki a inda nake, kinadaga cikin mutanen dasuka kara saka zuciyata cikin garari, da tashin hankali, kinsan yadda nakeji inkika jefeni da kalmar mara tarbiyya, kin dade kina gayamin maganganu masu kona zuciya, a maimakon kalaman kwarin gwiwa, ki tashi kibani guri karki kara zuwa inda nake, nasan da Umminki tana nan nasan komai munin halina bazata taba kyamata ko tagayamin bakar magana ba, bazata taba zama cikin masu kyamata ba, ta nunamin so da kauna, kuma batun yafiya tsakanina da mahaifiyata wannan abunda ya shafeni ne, i never expect such type of behavior from you, why? Why do you hate me before, baki taba tunanin me ya jawomin nake irin wannan rayuwar ba, Never judge book by it’s cover, please dismiss from here, in ina ganinki kina kara batamin rai” Idon Jalila kyar akansa bata ko kyaftawa har yayi gama yana huci,
“Naji zan tashi, Nagode sosai, karka manta da kashedin likita, kaci Abinci kasha magani, sannan ka rage shaye2”
“bazan ba uwatace ke dazaki dinga min kashedi haka? Wai ina ruwanki dani ne, meya shafeki da inyi lafiya ko kar inyi”
“A’a ba daya, in kayi inma bakayi ba kanka kayiwa ba Jalila ba, Amma kaji tsoron Allah, kakiyaye dokokinsa sannan ka kulada ibada” ta mike jiki a sanyaye ta fito waje, maganganun da Jalal ya gayamata babkaramin bata mata rai sukayi ba, dukda taji zafin maganganun da Jalal yagaya mata, amma idan ta tuna itama abubuwan data dinga masa abaya setaga bata kyauta ba.
Daddy ya kalli Jawwad yace “Jawwad Abbanka kuwa yana gari ina son ganinsa” Jawwad yace “A’a Daddy be dawo ba tukuna yana lagos amma a satin nan ze dawo Insha Allah” daddy yace “Allah yadawo da shi lafiya, Yaww Jawwad naji Jalal yacemin ka kamalla Masters dinka last Couple of months ko?” Jawwad yace “Eh Daddy Alhamdilillah na kamalla, ina jiran sakamakone, atayamu da Addu’a” daddy yai murmushi yace “Kullum cikin yi muku nake? Kuma nasan da sakamako me kyau zaka fita Insha Allah, nasan yarona akwai himma ai, dama vacancy na samu, federal zata dauki ma’aikata a farkon sabon shekara anbani vacancy na mutum daya a babban branch din NNPC na Abuja, shine nace ka turomin CV dinka ta Email dina, inkuma zaka karo karatune kuma to, semuga yadda za’ayi kaje ko England ne can wajensu Mahmud ka karasa” shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai yakasa cewa uffan daddy yace “Jawwad kona bata maka raine?” Jawwad ya girgigiza kai yace “Daddy banida bakin yi maka godiya, tun ina karami kake dawainiya dani, amma ina tunanin dan uwana, daddy Jalal shifa me za’ayi wands za’a tallafawa Rayuwarsa” daddy yai ajiyar Zuciya yace “Jawwad bana tunanin koda Jalal yanada dan uwa ciki daya ze nuna masa kaunar da kake masa, Amma Jawwad ba yadda zanyi ina za’adauki Jalal aiki a wannan halin da yake ciki, yana shaye2 baya son mutane, ga zafin zuciya kana gani ko mahaifiyarsa baya raga mata, anyi2 yakoma makaranta yaki ” Inda na godewa Allah ko bayan raina Jalal yanada kadarorin da in ya tattala ze iya rike kansa, inkuma yabarnatar shikenan” Jawwad yace “Daddy bazanyi musu da hukuncin ka ba, amma inaso Jalal ya samu makoma shima, koya koma karatu koya samu aiki, amma idan na tafi Aiki na barshi a wannan halin senake ga kaman banyi masa halacci ba, kuma shaye2 munmasa addu’a muna fatan ze dena very soon, tunda ya rage ba kaman da ba” shiru daddy yayi yana kallon Jawwad dayake magana idonsa taf Hawaye dake nuna hakikanin gaskiyar abunda yake fada har zuciyarsa.
“Jawwad kenan Allah ya dawwamar da haske a cikin Rayuwarka, gwagwarmaya da kaunar dakake wa dana banida abun biyanka, Allah yatemakeka ya baka abunda kake nema duniya da lahira”
“Ameen daddy” daga haka ya tashi ya fita.
Oga KB yana zaune yatasa Samira da wata katuwar bulala, da alamu jibgarta yagama yi, jikinta duk a kumbure dan fuskarta a kumbure gefen idonta yana zubar da jini, Oga KB yace “Tun tsawon wani lokaci kike tareda Jeje?”
Cikin kuka tace “Ranar muka fara haduwa da shi” kafin ta rufe baki yakuma zuba mata bulala tareda fadin “Karya kikeyi, munafuka zaki gayamin ko sena takeki na kasheki, matsiyaciya yanzu shikenan Sunana yagama lalacewa a idon duniya, nida ‘yata a gidan karuwai, dana san irinki za’ a haifamin da tun a ciki sena zubar dake, Wallahi idan Nagano wanda ya shirya min wannan manakisar sena kasheshi kowaye, ki gayamin tun yaushe kuke tare?”kokuma yanzu inkasheki da poison na kashe banza shedaniya”
“Shekararmu biyar Tare dashi” zaro ido yayi “Shekara biyar amma bansaniba, Cigaba ina jinki se akayi yaya?”
“tun ina secondary muke tareda shi, bayan haduwa ta da Saleema, nasanshi ne ta hanyarta, daga baya yake nunamin yasanka, Yaronka ne akwai aikin dayake maka, duk lokacin danazo maka da bukata baka damuwa da bukatuna, kafi son faruk dani, kana cewa bazaka kara yadda da mace ba koda yar cikinka ce, nikuma bukatuna bakamin, umma ma bayimata kake ba, balle nima ina sa rai, shine Jeje yajani a jiki shine ya koyamin bin maza, yana baani kudi masu yawa sannan ya hadani da masu kudi Shida Saleema, Sau biyar ina zubar da ciki biyu duk nasane” Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Kabiru mikewa yayi ya shake Samira yana fadin
“Samira anya kuwa nine Ubanki, kodayake a rina barewa bata gudu danta yai rarrrafe uwarkima karuwanci tayi ta tuba na Aureta, watakila bayan na Auretanma bata tuba ba” Mahaifiyar Samira ta fito a fusace tace “Sakarmin ‘yata wallahi bazaka kasheta ba, tun dazu inamaka kawaici shiru kawai nake, tunda abun naka yazoda cin fuska bari in tunamaka, kana tunanin hakkin uwarka ze kyaleka ne,? kokuma shi yaron dakasa aka lalata ba dan wasu bane? Yaronne yai maka laifi? Kokuwa uban me ya kaika gidan karuwai? Duk nasan abunda ka keyi kyaleka kawai nakeyi dan haka sakarmin yarinya ni Addu’a nake Allah ya shirya yaran musulmi amma wannan bakar zuciyarta ka me cike da sharri dole kaima kaga sharri akan yaranka”, A fusace yayo kan mahaifiyar Samira, amma Samira ta rike rigarsa cikin ihu da kuka take cewa “Wallahi karka sake ka tabamin uwa, nidin dai ko kasheni kayi nasam baka da asara, ai a ranar da aka kamamu a gabaana zizo yace kaima ana kaimaka karuwai gidan hutawarka, tunda na taso katsaneni saboda kawai ni macece ka fifita soyayyar danka namiji akaina, gaka da kudi amma baka moramin komai danme yasa bazan nemawa kaina mafita ba” jin hayaniya yasa tuni mutane suka fara shigowa dan ganin meyake faruwa, Alhaji Kabiru yasa hannu yai wurgi da Samira, take ta fafi bata ko motsi, nan da nan mutane sukayi kanta amma ana dagata sega Jina nata zuba daga jikinta. Shikam Alhaji Kabiru motarsa ya dauka ya fice daga gidan be zame ko ina ba se gidan Jeje, Yana zuwa Jeje baya nan, dan haka ya tafi Club din dayasan lallai zs same shi a can Jeje yana nan, yanata shaye2 shida wasu mata, tareda wasu abokansu.
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
A fusace ya daka musu tsawa yace su basu guri, daya ta kalleshi cike da maye tace “Wollah ba inda zamuje, ji mutum kazo kasamemu sannan kace mufita
“Jeje yace “Am sorry Guys don’t mind him” Jeje ya dawo da dubansa kan Alhaji Kabiru yace “I thinks you said it’s over between me and you ba, bayan tsawon lokaci dana dauka inamaka aiki, inamaka bauta dan ka kamani da ‘yarka,’ yan sanda sunkamamu, shine kacimin mutunci kamanta halaccin danayi maka”
“Shut up!!!” yayi wa Jeje tsawa
“Duk wahalar danayi maka A rayuwa, tun kana karamin dan isaka na daukeka naimaka gata, na dinga yimaka wahala tsawon shekaru, baka cikamin burina na ganin ankai Jalal kurku a kasksance uwarsa da ubansa na kuka ba, memakon ka maida hankali akan aikin dana saka, sema komawa da kai kana cin amanata, yar cikina kake lalata da ita, kakoya mata bin maza, ga shaye2 ta tabattarmin da sau biyar tana zubar da ciki biyu daga ciki kuma nakane, Ka saurari abunda ze biyo baya, hukuma ce zata rabani da kai”
“Kafin ka kaini gaban hukuma yakamata ka amsawa kanka wannan tambayoyin? Kai yara mata nawa ka lalata?
Ko agaban Allah wace hujja zaka bayar na bada kwangilar lalata Rayuwar ABDUL JALAL da sunan daukar fansa?
Uwa uba karka manta da babbar haramtacciyar harkallar da mukeyi na saida makamai da miyagun kwayoyi” cak Oga KB ya tsaya yayinda Jeje ya kyakyake da dariya yace “Ramin mugunta kenan inzaka gina, gina shi gajere dan kila kai zaka fada”
Wani mugun bakin ciki da bacin raine yakama Oga KB ya juya ya shako wuyan Jeje yafara bugashi akan tebur, dayake a buge yake sam jikinsa babu kwari, nan take matasan dake gurin su taso sukayi kan Oga KB, dan har jini yafara fita daga hancin Jeje, Oga KB na juyawa ya rarumo wata kwalbar giya ya bugawa Jeje a goshi nan take Jeje yafara zubar da jini hakan be isheshi ba seda yakuma soka masa kwalbar nan a kafada, Jini ya dinga fita a jikinsa nan take jiri ya kwashe Jeje ya fadi kasa, da kyar security din gurin suka rike Oga KB suka tafi dashi suka kuma mikawa ‘yan sanda shi. Sannan aka dauki Jeje zuwa Asibiti rai a hannun Allah.
Ita kuwa Samira da aka kaita Asibiti ta galabaita ashe wani cikinne a jikinta bata saniba, da kyar aka ceto ranta sedai an tabattar da mahifarta ta lalace bazata kara daukar ciki ba har abada.
Jawwad yakoma gida ya tarar da Jalal a part dinsa, a zaune a akan kujera, Jawwad yaje kusada shi ya zauna, ya dinga masa nasiha tareda rarrashi akan abubuwan dayakewa mahaifiyarsa, Jalal yai shiru yaki kula Jawwad har yai surutansa yagama dan babu alamar Jalal ya dau Nasihar Jawwad, seda ya bari Jawwad yagama tsaf sannan yace “inka gama bani aron key din motarka”
“ina zakaje?”
“In tuhumata zakayi bar abunka”
“A’a ni na isa, gashi amma kabi a hankali kasan bakada lafiya kayi driving a hankali” Jalal bece komai ba yasa hannu ya karbi key yafita.
Jawwad ya nemi guri ya kwanta ya dan huta yana tunanin karamcin da daddy yake nuna masa. Jawwad yasamu yayi bacci, se bayan la’asar ya farka, yaje yai wanka yai salla yana kokarin neman Abunda zeci ya tuna dakin Jalal yana nan kaca2 yasan inba’asa an gyara ba Jalal baze gyaraba ko dakin ze shekara ahaka, kuma ze iya zuwa yayi shaye shayensa yace ze shiga ya kwanta ga kwalabe da ya farfasa a zube a dakin, Jawwad ya mike ya fita, yana fitowa kafin ya kaiga bakin gate yaji muryar Naja ta kashe murya tana masa magana “Yayana dan Allah inbazaka damuba sonake ka rakani unguwa” Jawwad ya kakalo murmushin dole yace”
“Eyya am very sorry, kinga aiki zanyi ne yanzu na gaggawa dan Allah kiyi hakuri” yana gamawa bejira mezatace ba ya fice daga gidan, tsayawa tayi turus tarasa me zatace. Haka ta juya takoma cikin gida tana cizon yatsa, tana komawa daki ta tararda Jalila tana gyara gashin ta agaban mudubi, ta dinga tsaki tana aikin banza, ita dai Jalila bata kulata ba, seda tagama tsaf ta dauki mayafi ta daure kanta ta dau wayarta ta fice, tana bukatar yin waya domin jin inda harkalarta ta kwana.
Jawwad yana zuwa yafara tattarre Kwalaben dakin yana sakasu a dustbin yana bawa megadi yana fita dashi, Jawwad ya duba bega tsintsiya ba dan haka yakoma gida don ya dakko, yana zuwa ya hangota tana waya, kallo daya tayi masa tai murmushi ta sauke wayar tace “Ya dai naga kayi gumi haka? Meyafaru?”
Murmushi yayi yace “Wallahi Jalal nake gyarawa daki, yayi fata2 da komai, kuma in ban gyara masa ba a haka ze barshi, kar inje ya bugu yace ze shiga dakin ya kwanta a haka” Jalila tai murmushi tace “Allah yasadaka da dukkanin wani alkhairi na duniya da lahira hakika ka cancanci yabo, Yaya Aliyu Jawwad sha gwagwarmaya, amma meyasa sekai zaka gyara masa?”
“Kinsan halin dan uwan nawa, bakowa yake so yashigar masa daki ba, baya son sa ido”
“Hakane muje in tayaka”
“Anya kar in takura miki fa”
“Bawani takura gyaran gida aina matane” ta rakashi suka dakko tsintsiya suka fito akan idon Naja suka fita tare aikuwa tasaki Ashar, Da sauri Nana ta kalleta “Lafiya kike mana Ashar haka sekace ba musulma ba”
“Dalla rabu dani yanzu nacewa Jawwad ya rakani unguwa yace bazashi ba yanada abunyi, amma kalli sunfi ta tare da wannan jakar yarinyar, zasu gane kurensu bari Maaman ta dawo” Nana ta tabe baki tace “Wallahi Naja duk inda kikaje sekinja masifa, muna zamanmu lafiya amma kinzo zaki tayar mana da hankali Aikin banza kawai” Nana ta mike ta fice tabar mata dakin.
Jalila ta dinga taya Jawwad suna kwashe kayan daya fasa suna fita dashi a hankali dakin yafara hankali kula tayi kaman Jawwad yagaji sosai tace “Yayan Baby what’s wrong” yace “Baby yunwa nakeji sosai, ga Jalal yafice ban san inda ya tafiba koya ci Abinci oho”
“Allah sarki jekaci kadawo ina jiranka, Abincin yana nan a kitchen”
“God bless you my dear, yanzu zan dawo Insha Allah”
Sosai Jalila tacigaba da aikin dakin, bedroom din zuwa palour ta gyara komai, taje tana goge kan fridge kawai ta bude, kwalabene manya da kanana, tanagani tasan giyace ga kwalayen sigari nan duk ya shiryasu a ciki sekuma kwalayen madara da Apple a ciki amma kwalaban giya sunfi yawa, fito dasu ta dingayi daya bayan daya ta taresu agabanta ta girgigiza kai, ta tattaresu guri daya tadinga bude kwalbar tana tsiyaye giyar a cikin dustbin, ta zazzage tabar nan a cikin shara, tacewa megadi yafita da ita. Ta koma dakin ta juya baya tanata mopping taji an rikota ta baya..
Da sauri ta waiwayo don ganin waye ya cukumota haka, tozali tayi da Ilham ido cikin ido, a fusace Jalila tace “Malama lafiya? Meye haka sekace wata mara hankali”
“Nikike cewa mara Hankali? Uban me kikeyi a dakin nan?” wani irin kallon rainin hankali Jalila tayi mata
“Uban da kikeyi shina keyi, Dan Cikani mana” kara rikon Ilham tayi “Bazan sakekiba, munafuka ranar kinje gurinsa kin zauna a Asibiti dan shishshigi, yau kuma uban me yakawoki dakinsa? Makira Annamimiya”
“Ilham ba ina binki a sannu bane dan ina tsoronki, uban dayake kawoki dakinsa shiyake kawoni kicikani”
“Bazan cikaki ba se kin gayamin uban meye hadinki dashi da har zakizo dakinsa wai kina gyarawa, akan me wayasaki, ke nifa ban yadda dake bama wallahi” hankade ta Jalila tayi ta nunata da yatsa, kikakuma gigin tabani wallahi sena baki mamaki, inkin isa in yazo shikije ki titsiye shimana kokuma kema ki dinga shige masa in zaki samu gindin zama, wallahi Ilham ki kiyayi shiga sabgata inbahakaba sekin gane bakida wayo, bar yimin kallon haka, sakarya kawai”
A Fusace Ilham tayi kan Jalila ta riko hannun da Jalila ta fadi akai sanda Jalal ya tureta fadi, “Wallahi sekin gayamin meye hadinki da Jalal, sannan meyasa kike shishshigi a lamuransa, bazaki bar gurin nan ba sekin fadamin uban da kukeyi” “Dalla cikani, ubankine Jalal din ko dan kekadai aka halliceshi, sha3 mutumin dabata taki yake ba, inma wani abun mukeyi kema kizo kuyi”
Jalila ta fizge hannunta aikuwa Ilham ta dauka mopper tayo kan Jalila, tana cewa “Wallahi sekin gayamin yau senaga uban da yatsaya miki koni koke, matsiyaci ya kawai, wallahi sena miki dukan dabazaki sake shigowa gidan nan ba.
Jalila tai sauri ta dauki Ruwan mopping ta shekawa Ilham shi gaba daya a jikinta, sannan ta bita tana kwala mata bokitin. Seda yafara fashewa a jikin Ilham, inda Allah ya temaketa bokitin robane, Jawwad ne yakawo kai yaga ana wrestling, Ilham ta durkusa tanata ihu Jalila tana bugamata bokiti tana huci, da sauri yaje ya riketa yana fadin “Subhanallah lafiya kuwa? Jalila meye haka?” A fusace Ilham tace
“Dole ka tsaya kana tambaya mana kaima munafuki, wallahi tun wuri kajamata kunne inbata kiyayeni ba sena illata ta wallahi, nikika jika da ruwan datti kika dakeni ko? Wallahi sena sa kinyi danasanin zuwanki duniya”
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
“Karki fasa, nikuma bazan gaji da lakada miki dukaba tunda bakya gane yaren mutane sena jakuna in an dakeki” Jawwad yace “Jalila yimin shiru, Ilham dan Allah kiyi hakuri komene nasan Jalila ce bata da Gaskiya, rigimanmiya ce tun asalinta dan Allah kiyi hakuri”
“wallahi ni inada gaskiya, akanme zatazo tana zagi……. Jawwad yace” yimin shiru ko in zane miki jikinki yanzun nan, bata hakuri sannan ki wuce kitafi gida sarkin fada kawai” Jalila tai murmushi tace “Ilham dan Allah kiyi hakuri, sharrin shedanne, Insha Allah inkika dena shiga harkata bazan kuma tabaki ba, amma kika cigaba da rainamin hankali zaki gane bakida wayo” Jalila ta juya tai ficewarta, Ilham tacigaba da zazzaga bala’i Jawwad yana ta bata hakuri. Seda Ilham tagama zazzagewa Jawwad rashin mutunci sannan ta bar dakin, Jalila tagama gyara dakin fes, sedai ruwan mopping data zubawa Ilham duk ya kwantaa a gurin, Jawwad yasa abu yai mopping din gurin, har kusan goma na dare sannan Jalal ya dawo, koda ya dawo gidansu ya wuce, yaje ya siyo kayan shaye2, yana shiga dakinsa ya ganshi fes kaman ba dakin ba koba a fada ba yasan Jawwad ne ya gyara, ya danyi Murmushi ya karasa inda fridge dinsa yake amma me yaga an kwashe komai na ciki se madara, iya saninsa Jawwad baya taba masa kayan shaye2 tunda suka taba fada akan haka, a fusace ya mike ya fita harabar gidan yana kwalawa Me gadi kira, a sukwane me gadin yazo dan Jalal baya shiga harkarsa indai yaji yamasa wannan kiram to akwai matsala Jalal yace “Bayan Jawwad waya shigarmin daki? Seda gabansa ya fadi take ya rikice yace yace “Ammm Ilham ce yallabai” a fusace Jalal ya juya ya shiga cikin gida, dakin Ilham ya nufa yana zuwa ya tarar ta fito daga wanka tana sanye da rigar wanka, tana duba goshinta inda Jalila ta daketa da bucket cike da tsana yace “Ke ubanwa yabaki izinin zuwarmin daki?”
“Nikuma?” “tambaya ta ma kike zan tattakaki, ina kayana da kika kwashe a fridge?, nakine koke kika ajiyemin, ina kayana”? Yafada cikin shouting
“Ni ban taba maka kaya ba, kaje dai ka duba” fizgota yayi ya dauke ta da mari, “nizaki Rainawa hankali kinsan nawane kudin kayan nan kuwa, ki gayamin ina kayana ko in shakeki, inkuma kinfara shane kema se inji” dafe kunci tayi tana kuka “Ban saniba, niban daukarma komai ba, meyasa kai Azzalumi ne wallahi se Allah yasaka……. Tas! Yakuma wanka mata mari wallahi sekin fitomin da kayana, gobe in ance kikuma shigarmin daki bazaki ba yai kanta, da sauri ta haye gado tana ihu sosai “Nashiga uku, atemakeni wallahi ya haukace ze kasheni, bashida hankali ” kalmar hauka data kirashi yakara bata masa rai, kan gadon yabita ya shaketa dama kuma a buge yake,
Da sauri Mummy ta nufo dakin a gigice, tana zuwa ta tarar ya shake Ilham idonsa yayi Jawur, Daddy ma da sauri ya fito ya nufo dakin, a gigice Mummy tace
” Jalal meye haka inka kasheta fa?”
” Na kashe banza, ubanwa ya kaiki dakina kika tabamin kaya”
Da kyar daddy ya kwace Ilham a hannun Jalal, Daddy ya kalli Ilham yace “Ilham meya kaiki dakinsa mekika taba masa?”
“ni wallahi bani bace ba, Jawwad ne ya shiga, kuma nida naje Jalila na tarar tana gyra dakin, ni ban taba masa komai ba” takarasa fada tana kuka
“Jalila tabbas itace” ya fada a ransa juyawa yayi ya fice daga dakin da sauri. Daddy yaita bawa Ilham hakuri, suka fita suka bata guri, Ilham fashewa tayi da kuka “lallai Jalila bata da mutunci, bayan dukan datayi min shine taje ta kitsamin sharri, wannan wce irin Jarabace” haka Ilham taita kuka. Shikuwa Jalal yana komawa dakinsa yarasa mezeyi ya huce, Jalila ba karamin Asara tai masa ba, yasan itace ba wani ba, giyace me matukar tsada da wuyar samu, ga kwalayen sigari duk ta kwashe masa haka ya kwanta yana tunanin mezeyiwa Jalila ya huce ne.
Nana tanata waya da Mahmud, abun nasu ya rikide yakoma Soyayya, Jalila ta kule a cikin bargo tana chatting, Zahra take sanarmata ankuma kama baban Samira, ya zaneta ashe tanada karamin ciki, sannan yaje Club yakama Saurayin Samira ya sossoka masa Kwalba, A sukwane Jalila ta tashi zaune, takira Zahra, Zahra na dagawa tace “Jalila kinga sakona ko?”
“Eh nagani Zahra dan Allah dagaske kike koda wasa?”
“Haba Jalila yazan miki wasa a wannan maganar wallahi gaskene, har wasu sunje dubata tana Asibiti”
“Thank you for the Update dear, nagode sosai Zahra Allah ya biyaki” ta kashe wayarta, ta shiga tunanin mezatyi wanda zata sa A rike Alhaji Kabiru wannan karon kar asakeshi a gurfanar dashi a kotu.
Take Suleiman ya fado mata a rai, wani dan guntun murmushi tayi, tamike ta shige toilet ta rufe kofa sannaan ta kira suleiman, sun dade suna waya, tagaya masa komai, tace dan Allah inda wani taimako daze mata yayi, a karbi case din abawa wanda zasu jajirce a gurfanar dashi a kotu, yamata Alkawarin zeyi iyayinsa, sannam intanada wani sheda ta tura masa, ta turawa suleiman dukkan waya da chat dasukayi da Alhaji Kabiru, ta tiramsa har recording din maganar su Samira da barazanar da suka dingayiwa Zahra, Suleiman yace insha Allah zeyi kokari yaga me ze iyayi, yace zesa amasa bincike, kafin yazo kano tai masa godiya sukayi sallama sannaam ta fito daga toilet din, tana fitowa Nana ta dan tsuramata ido sannan tace “Jalila kekam me kike a bayi haka, kinkusa awa daya fa, murmushi Jalila tayi tace
” Ke Awa nawa kikayi kina waya, kai Nana Allah ya shiryeki da sa’ido wallahi” sukayi murmushi gaaba daya banda Naja, data ketawani hura hanci tana shan kanshi, Jalila ta kalli Inda Naja take sannan tace “Bari inzo inkira Yaya Jawwad inji in yayi bacci, in beba ya tayani hira, Tunda ke Nana naga hankalinki nakan wannan Mahmud din” Nana tai murmushi tace “Jalila bazaki gane ba Mahmud ya hadu, he is so romantic”
“Aifa gashi nan gaba daya kin Afka soyayya ba kyaji ba kya gani” suka kuma dariya, Naja ta tsurwa Jalila ido, jira take taga Jalila ta kira Jawwad tai mata rashin mutunci amma taga Jalila tayi kwanciyar ta. Can cikin bacci Jalila ta farka, take jin surutu kasa2, tai shiri setaji Naja ce take waya da Saurayi kusan karfe ukun dare, ga wayar tasu batsace kawai sukeyi, Jikin Jalila yai sanyi, “Yanzu wannan ake kokarin a hada salihin bawa kaman Jawwad da ita, bazan taba bari hakan ta faruba, ai gara Hanan da wannan” Naja tacigaba da wayarta dan tunanin ta gaba daya bacci sukeyi, haka Jalila takasa komawa Bacci har Asuba.
An samu Jeje ya farko da kyar, ya zubarda jini sosai, dan haka ana bukatar akara masa wani, duk abokan shaye shayensa suka zame sukece bazasu iya ba, suma jinin be wadace su ba, balle su bashi, Jeje yace dan Allah agayawa Jalal yasan ko kowa ya hanashi Jalal ze bashi Jini, sukace dan dai sako zasu gayawa Jalal.
Kusan kwana hudu Jalal be kara ganin Jalila ba, Jalal yarasa yadda zeyi ya ga Jalila, ko gidansu yaje ya dena ganinta, sannan kuma ta dena zuwa gidansu, gaba daya ransa a bace yake, saboda wannan mummunar Asara datayi masa, shiba kudinne damuwarsa ba se wahalar samu da irin wannan giyar take dashi, kuma ita kadaice in yasha yake jin yaji yadda yakeso. Yana zaune yaji karar mota, ya leka ta window palourn sa yaga Daddy ne yafita shida Mummy, jinjina kai yayi, Wayarsa ya dauka ya kira Jawwad, tana fara ringing Jawwad ya dauka, Jalal yace “Kana inane?”
“Maama ta dan aike nine, ya akayi?”
“Kagayawa kanwarka Mummy na nemanta”
Jawwad yace “to bari in kirata zatazo” ya kashe wayar, Jawwad ya kira Jalila a waya yagaya mata, bata kawo komai a ranta ba tace zataje.
Jalila ta dauki gyalen doguwar rigarta ta saka, ta fito ta tafi gidansu Jalal, sam ta manta da tasaka an fita da kayan giyar Jalal.
Koda taje gidan ba kowa, abun yabata mamaki, ta hangi Ilham a kitchen tana hada Abinci, dan haka ta dan Jira Ilham tafito, tana fitowa Jalila tace “Yawwa Ilham, ina Mummy kuwa? Ance tana nemana” A fusace Ilham ta kalleta “Ban saniba matsiyaciya jarababbiya, wallahi senasaki kuka kaman yadda kikemin, saboda kin iya makirci, kikayi min sharri gurin Jalal bayan dukan da kikamin, shima yazo ya shakeni ya kusa kasheni, wallahi in sharri ne gidan kika tarar, sekin gane bakida wayo, ina nan ina shirya miki trape kuma wallahi sekin fada” cikin mamaki Jalila tace “Ke ni ban gane wani makirci na miki ba, shi makircin ba kekika sanshi, dan Allah ina Mummy”?
“Ninake nemanki ba itaba” waigowa tayi ta kalli Inda Jalal ke tun karo ta, tsayawa tayi kaman wata gunki tana kallonsa har ya karaso inda take, A fusace yakamo hannunta yai waje da ita yana janta, Ilham na ganin haka tace “Allah yasa yamata dukan mutuwa” cikin sanďa ta biyo bayansu. Be tsaya da ita ko ina ba se part dinsa a gaban fridge, ya bude fridge din ya kalleta a fusace yace “Ina abubuwan da kika kwashemun a fridge?” kallonsa tayi ido cikin ido, ta dauke kanta tai masa shiru “Magana nake miki ina kayaana?”
“Meye kayan naka?”
“Tambayata ma kike?”
“Eh, ai bansan wani kayan bane gara ka gayamin, idan nina dauka, se ince maka nina dauka inbani bace ba zance bani bace”
“Ke meyasa a rayuwarki, kikeson rainamin hankali ne? Kekika dauka ko kaffara bazanyi ba, ina kayana ko in kakkaryaki yanzun nan” ta kalleshi cike da tsiwa da gadara tace
“Na dauka na zubar a shara, nabayar an fita dashi ansaka a bola” ta kare maganar tana kallonsa up and down, wani mugun takaici ne ya kama Jalal, shi takewa wannan gadarar haka, hannunta ya janyo, sukazo daf suna iya jin numfashin juna sannan yace “Ubanwa yasa ki daukarmin kaya, kekika ajiyemin?”
“ba uban daya sani, nina sa kaina, kaga sakarmin hannu, last week ka hankade ni kakusa karyani yanzu kuma kana kokarin karasamin hannu, cikani” lallai Jalila ta kai makura wajen iya rainin hankali, ta masa laifi kuma tana masa gadara
“Ka cikani nace kobaka jinane, kaikam Allah ya shiryeka, kota lafiyarka bakayi, se tsabar masifa da taurin kai ni cikani….
Wanka mata mari yayi, wanda yasa Jalila dena gani na wani dan lokaci,
“bansan a dadin lokutan dana dauka ba ina miki kashedi akan kifita daga harkata, ke wace irin mara zuciya ce, wace irin uwar shishshigi ce ke? Darajar Ummi da Jawwad kikeci da tuni na kakkaryaki na karya banza, ina ruwanki da mara tarbiya wanda baya ganin darajar iyayensa, ina ruwanki dani? Ke kullum burinki kiyi abunda zaki bata min rai ko?” tuni Hawaye ya wanke mata ido, dan sau daya aka taba marinta shima Hanan ce, kuma seda ta koyawa Hanan din darasi, idonta na kwararar da hawaye, cikin nutsuwa tace
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
” Hakane na fiye shishshigi, kuma inka karyani ka karya banza, amma da ina cin darajar Ummi da Jawwad koda wasa bazaka mareni ba, dan nasan Jawwad baze taba marin wanda yafito daga ahalinka ba, Nagode sosai da wannan marin da kaimin, bazan taba mantawa ba, Allah yabaka Hakuri, Allah ya huci zuciyarka nadena maka shishshigi Insha Allah, Kacigaba da shan giyarka Jalal da dukkan wani nau’i na shaye2 karka dena, bazan kuma takura rayuwata akanka ba, na tafiyar da lokuta masu tarin yawa akan tunani dan ganin kazama mutum kamar kowa, sannan mutane sudena kyamatarka, nashiga damuwa da gwargwamaya saboda kai, but this is what I deserve from you, dana san abunda naimaka ze bata maka rai ta kai gaka mareni da banyi ba, ina me baka hakuri, Insha Allah dana kammala abunda nake zan dena maka shishshigi, balle incigaba da bata maka rai” gaba daya jikin Jalal yayi sanyi, be gama gane inda magamganun Jalila suka dosaba
“Cikani in tafi” yana kokarin yin magana, cikim Zafin Rai tace “Kacikani Jalal tun kafin in rama marin dakayimin, kaine mutum na biyu daya mareni a rayuwata, wadda taimin na farko seda na tabbatar da na koya mata darasi, kaima wasu dalilaine zasu hanani ramawa ka cikani nace maka” tai maganar tana Hawaye, gaba daya Jalal ya rikirkice, ta fizge hannuta ta fito waje ta tafi gida, seda ta tsaya a waje ta gyra fuskarta ta maze sannan ta shiga gida.
Ilham da take labe kuwa gida ta koma tana murna tareda yiwa Jalila Allah yakara.
Shikam Jalal guri yasamu ya zauna yai shiruu yana tunani, danasanine ya lullube shi, meyasa ya mareta ya akayi har ya mareta, “Jalila ce fa ya akayi na mareta ne? Mtseww yarinyar nan ta fiye shishshigi da taurin kai” magamganun Ilham da mamanta da sukayi a Asibiti ne suka dinga dawo masa. Mikewa yai da sauri yabi bayan Jalila amma kodayaje gidansu ma tariga ta shige cikin gida, dakin Jawwad ya tafi ya zauna yai shiru duk abun duniya ya dameshi musamman inya tuna Hawayen daya gani a fuskarta. Wayarsa ce tafara ringing, lambace ba suna ya daga yasa a kunensa, anan aka sanar da Jalal Jeje yana kwance a Asibiti rai a hannun Allah yana bukatar jini amma an rasa me bashi, bill din Asibitin dana magani ma ba’a biyaba, Jalal yace Insha Allah gobe zezo Asibitin aduba jininsa in yayi daidai asawa Jeje, sannan ze biya bill din Asibiti.
Jalila bata taba zaton Jalal ze iya marinta ba, yau taki kula kowa har dare ba wanda ta kula, duk yadda Naja taso ta tsokane ta suyi rigima Jalila taki yadda.
Washegari karfe sha daya na safe Jalal ya shirya ya tafi Asibitin da Jeje yake, ya tausaya masa ganin halin dayake ciki, bakowa a gurin Jeje se shikadai gashi ba’a wani kula dashi saboda ba’a biya kudin Asibiti ba, Jalal yana zuwa yabiya kudin Asibiti, sannan yasa aka canzawa Jeje daki, Jalal yana zaune agaban gadon Jeje, yana jira likitocin suzo aje lab a duba in jininsa zewa Jeje, ‘Yan sanda biyu suka shigo dakin suda wani babban mutum sekuma Jalila mamakine yakama Jalal ya tsaya yana kallonsu, Kokusa Jalila bata nuna tasan Jalal ba sukaje gaban gadon Jeje, y’ansandan suka mikawa Jalal hannu suka gaisa, amma hankalin sa yana kan Jalila, ta kalli babban mutumin ta nuna Jeje tace “Yallabai wannan ne, shine wannan” mutumin ya gyada kai yace “aidaganinsa kaga criminal, ni kaman na taba ganinsa a wani guri, amma wannan fa, dan uwansa ne kokuwa? Shima wannan da gani drunker ne” kalmar drunker da Suleiman yafadawa Jalal, Jalila taji bataji dadi ba, amma ba yadda zatayi tunda Jalal yana shaye2
Jalila tace “Yallabai yanzu zakaji komai daga bakinsa” ta taka a hankali ta tafi gaban gadon Jeje ta tsaya ta kalleshi ya kalleta tace “Yau nacika maka alkawarin dana dade inayi maka, senaga bayanka, inaga kusan sau hudu ina gayamaka wannan kalmar, bari inbaka wani sako kagayawa ubangidan ka Oga KB, kokuma ince Alhaji Kabiru, kagaya masa Ni Jalila Aliyu Imam, ni nasaka aka kamaka da shi da ‘yarsa a gidan karuwai” gaba daya suka juyo suna kallon ta.
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
❤️❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku 😍😍😍😍
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool