Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 75 By Hafsat Bature

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔🥺

*Daga alƙalamin Hafsat Boss Bature✍️*

Dedicated to Aunty kubra💘🌹

75

💋PRISONERS💋

“Ita mu ke jira ta fito daga wanka, Ki koma ɗaki ki kwanta, Yanzu zamu shigo Ciki” Hibba ce ta bata amsar tambayar ta, juyawa jamimah ta yi zuwa cikin ɗakin su ta koma saman gado ta haye tare da kwantawa.

“yanzu haka zamu zauna muna ta jiranta? Shiru duk irin bugun ƙofar da mu ka yi babu alamun zata buɗe mana, Anya kuwa lafiya? Ni tsoro na kada ace wani abun ne ya same ta,” a cewar Deeja, hankalin su duk ba a kwance ya ke ba.

“In sha Allah ma ba abun da ya same ta, Zai iya yiwuwa bacci ne ya ɗauke ta a cikin toilet ɗin ko kuma zurfin tunani ta shiga…..” tunkan Batul ta rufe baki Sarah tace “wani irin bacci ne wannan mai nauyin gaske da har za’a dinga bugun ƙofa mutun bai farka ba? In kuma zurfin tunani ta shiga ai yaci ace bugun da muke ya dawo da ita hayyacin ta, Gaskiya bana tunanin haka sai dai wani abun ne na daban,” kowa na tofa albarkacin bakinsa,

“Yunwa nake ji, ƙwara ku zo mu haɗu Mu ci ganyen nan idan mu ka kammala sai mu ƙara jaraba Bugun ƙofar” A cewar Parveen, Atare su ka matso kusa da kwandon, Kamar akuyoyi haka suka dinga kwaso Ganyen Suna Cunkusa shi Cikin bakunan su, a tsiyace su ke taunar shi, Zuciyoyin su duk ba daɗi, damuwar rashin Angel ta hana su sakat.

Suna tsaka da Cin Ganyen kunnuwan su suka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙofar ɗakin su, A firgice su ka ɗago Suna kallon Junan su! Zuciyar su cike da fargabar Motsin buɗe ƙofan da su ke Ji, Tun da sun riga sun san An kawo masu Abinci, shiru su ka yi an rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi A cikin su, hatta ganyen da suka cusa a Cikin bakunan su sun dakata da taunar su, babban abunda suke jima fargaba kada ace Tsohuwa Zafreen ce ta kawo masu ziyara, Tuni kowannan su Yasha Jinin Jikin shi.

Garam! Su ka ji an datse ƙofar alamar wanda Ya shigo Ya fita, nauyayyiyar Ajiyar zuciya kowaccen su ta sauke, Kafin wani yai yunƙurin motsa La66ansa Muryar Jamimah ta karaɗe kunnuwan su.

Wata irin razananniyar ƙara ta fasa Mai kuwar gaske, Hankulan su A tashe su ka mimmiƙe da gudun gaske suka faɗo Cikin ɗakin a sukwane Suka ci uban burki Suna faman Haki, A tsakiyar ɗakin su ka ganta Ɗaure da bargo a jikinta Sai tsalle ta ke yi, babu wanda Ya lura da me ta ke Yima Murna, Rai a6ace Parveen tace”Wannan wani irin rashin Hankali ne jamimah? Salon kawai ki kara tada mana hankulan mu shine kika fasa Ihu kamar mai ta6in Hankali”? Jin muryar Parveen Yasa ta juyo tana kallon su fuskarta ɗauke da murmushin Farin Ciki,.

“An dawo mana dasu Ƴan uwan mu dole in yi farin Ciki…..” Tun kan ta ƙarasa maganar Kusan atare Suka kai idanuwan su akan benan Ɗakin su! Wani irin bugu zuciyoyin su suka yi atare, Abu ne da basu Yi tsammanin shi ba, Tamkar A mafarki Haka suke ganin su, sun kasa Yarda da abunda idanuwan su suke nuna masu!

A tsaye su ke cirko cirko saman Matakalar benan, su biyar babu Danish Daga ganin su babu ƙoshin Lafiya atattare dasu, Fatar Jikin su Ta yi haske Hatta Haris da ya ke da duhu fatar shi ta canza, Sun rame sun bushe kamar babu Jini a jikin su, ƙafafuwan su kansu ba adai dai su ke ba, musamman ƙafar Mubeen da ta javed rawa su ke Yi kamar zasu kasa, Sumar kansu Kuwa Duk a hargitse Dama Allah yayi su da tarin sumar kai, Ba kamar Javed Da Gabriel sai Naufal, yanayin yadda suka yi tsayuwar Ya nuna sam babu kuzari a jikin su Kamar waɗanda Aka ɗebi Naman Jikin su, Sun faɗa sun zabge……..”

Muryar Deeja Na rawa ta furta sunan HARIS! Mamaki ne ƙarara akan Fuskokin su, Lamarin Ya yi matuƙar ɗaure Masu Kai, Cikin karyayyiyar Murya Parveen Ta furta Sunan NAUFAL! Hannun Batul dafe da saitin Zuciyar ta ta furta Sunan JAVED!! Muryar Hannah A disashe ta ambaci Sunan MUBEEN! Cikin shessheƙar Kuka Azeeza Ta ambaci Sunan GABRIEL! kamar a mafarki haka suke ganin su, Jikin su ba ƙaramin sanyi yayi ba, zuciyoyin su sun karaya sosai, Ganin yadda ƴan uwan nasu Suka Ƙi motsawa, Bakomai ya ɗaga masu hankali ba face Ganin Yadda Haris daya fi su ƙiba Ya koma Ramamme uwa su Javed, Sun fita hayyacinsu, Daga ganin idanuwan su ba ƙaramar izaya suka sha ba, Allah kaɗai yasan Azabtarwar da su ka yi masu na tsawon watannin da su ka yi a hannun su.

Tuni idanuwansu Deeja sun Cicciko tab da ƙwalla, Parveen tana kuka tace”Wlh kamar basu ba! Kamar an canza mana ƴan uwanmu! Ku kalli yadda suka rame ko magana ma basu Iya yi, Ni ina tsoron kada ace irin na unaiza su ka yi masu……..” daƙyar ta ƙarasa maganar saboda kukan daya ciyota, Cikin rauni na murya Deeja Tace”Haris kaine ka koma haka? Ina Jikin ka ya ke? Javed Mubeen Naufal baku Iya magana? Meyasa ku ke kallon mu kamar Ba ku gane mu ba”?

“Ba kallon su Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Yakamata muje gare su, wata’ƙil Sun kasa yin tafiyar ne” A hankali su ke tafiya suna tunkarar su kamar sunga abun tsoro, Koda su ka ƙaraso gaban benen Atare suka dakata da yin tafiyar suna kallon su, Gwanin ban tausayi farar fatar wuyan su harda jajayen ta66una na yakushi, Wurin yayi jawur La66an su duk sun faffashe sun bushe, Gabriel hada busasshen jini saman Ƙaramin lower lip ɗinsa daya ciza launin shi pink, Fatar idanuwan su sun yi ja alamar sun yi kukan mutuwa Sakamakon wata azabtarwar da aka yi masu.

Fashewa su ka yi da kuka tamkar ransu zai fita Yayin da su ke cigaba da bin ƴan uwan nasu da kallo mai nuni da tsantsar Tausayin su da su ke ji.

Azeeza Ce tai Ƙoƙarin matsawa ta haura saman matakalar farko har takai ga inda Gabriel Ya ke atsaye, Faɗawa ta yi saman jikin shi tana cigaba da yin kuka, Ganin ta ta6a shi bai nuna yaji zafi ba yasa Deeja matsawa Ta rungume Haris a jikinta, Da sauri batul ta hau benan ta Ruƙo Javed ta kwantar da kanshi saman kafaɗarta, Parveen ta nufi Naufal ta janyoshi ta rungume shi sosai tana cigaba da yin kuka, Hanna ce ta ruƙo Mubeen ta haɗa shi da jikin ta, Yadda suka ƙanƙame su A jikin su suna yin kuka tamkar ran su zai fita, Sun yi kewar ƴan uwan su sosai.

Matsawa saman benen Yasmin da su rubina su ka yi, A bayan su Batul dake rungume da ƴan uwansu maza suka ɗaura kawunan su, Gaba ɗaya sautin shessheƙar kukan su ce ta karaɗe Ɗakin nasu, Jamimah da sarah ne kaɗai su ka rage a tsaye bakin benan suna kallon su Idanuwan su cike tab da ƙwalla.

Batul da ke ruƙe da javed taji Jikin shi ya saki gaba ɗaya ya tafi zai sulale ƙasa da sauri ta daddafe shi a haka suka Zauna saman Matakalar benen, ta tallabo fuskar shi da Hannayenta biyu “Javed! Pls ka yi mini magana Inaso insan a wani hali ku ke ciki” Daƙyar ya ke iya kallon fuskar ta, saboda raunin da idanuwan shi su ka yi mashi kamar zasu lumshe, hatta numfashin su da hucin zafi Ya ke fita.

“Haris Ɗina ne ya koma haka? Inna lillahi Wa’inna ilaihirraji’un! Wlh ba zamu ta6a yafe masu ba, Allah ya isa tsakanin mu dasu Mugaye Azzalumai, Duk sun canza masu Halittarsu, ko magana ma ba su iya yi” cikin jin Ƙunar rai Deeja ta yi maganar, har lokacin bata janye haris daga jikinta ba, Kamar zata maida shi Cikinta,

“Dan Allah Naufal ka buɗe baki Ka yi magana, Hankalin mu ba a kwance ya ke ba, Muna so Muji koda muryoyin ku don mu tabbatar da cewa kuna da Lafiya” parveen ce ta yi maganar, fuskar ta sharkaf da hawaye yayin da ta ɗago da kan Naufal daga saman kafaɗar ta, Bawan Allah sai bin su da ido Ya ke yi, fuskar shi Ta yi jawur saboda hasken da ke gare shi, Dama duk Cikin mazan In ka cire Danish a wurin haske sai Naufal mutun na gaba Javed ne Duk da shi ba fari bane sosai amma Baya a cikin jerin baƙaƙe Launin fatar shi Chocolate ce, Yana da tarin sumar kai, iya kafaɗar shi ta tsaya, Bayan shi sai Gabriel Kalar fatar su Kusan ɗaya Da Javed babu bambanci, Kamar za suyi hauka wurin yi masu magiya akan su yi masu magana ko sun ji sanyi acikin ran su, Gaba ɗaya sun manta da zancen Angel tun da su ka yi tozali da Ƴan uwan nasu.

“Jikin su ba ƙwari, Muna ƙara masu ciwon nasu, Mun ishe su da surutu, Mu taimaka masu Su shiga cikin ɗaki su kwanta,” Hibba ce ta yi maganar, Ruƙo hannun haris Deeja tayi a cikin nata, Ba ta yi tsammanin zai motsa ba sai ji ta yi ya sanya hannu ya dafa kafaɗarta, Hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalin ta Yayi ba, A hankali su ke yin tafiya suna tunkarar cikin ɗakin, Ruƙo hannun Naufal Parveen tayi da taimakon ta ya dinga ɗyangyasa ƙafar shi suka nufi gadon shi, Yayin da Batul ta ruƙo javed ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta a haka suka nufi cikin daki, Ita kuma Hannah ta taimaka ma Mubeen, Ya rage saura Gabriel da Azeeza ke a rungume dashi, ta rasa ya za ta yi ta taimaka mashi su shiga ɗakin, Gaba ɗaya su Hibba sun bar bakin benen babu wanda Ya lura da Gabriel da su ka bari saboda babu shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu dashi, Sunfi Jinsu Javed shiyasa Hankalin su yafi karkata akansu.

Tana so ta taimaka mashi sai dai bazata Iya ba, Saboda tsayin dake gare shi Ga ƙirar Jiki, tsawonta daƙyar Ya kai waist ɗin shi, ruƙo hannun shi ta yi a cikin nata tare da jan shi don su shiga ciki ko motsi wannan baiyi ba, hakan yasa ta fashe da kuka tare da ɗaga murya tana yi ma su batul magana “Wai bazaku zo ku taimaka mashi ba? Kun barshi shi kaɗai a tsaye” babu wanda Ya juyo ya kalle ta Hankalin su ba akanta ya ke ba, Tsagaitawa tayi da yin kukan tare da kallon fuskar shi wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, Ya galabaita sosai, Cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunan shi, bai amsa mata kiran da ta yi mashi ba, Sai dai taga Ya zuƙunna saman matakalar benan Yana faman Fitar da numfashi mai ɗumi.

“Ka tashi mu shiga ciki, Inaso na taimaka maka” A hankali yake bin ta da kallo fararen idanuwan shi sun canza launi zuwa ja, daga gani ba ƙaramin jin jiki ya ke yi ba, azeeza sarkin tausayi hada sanya Ƙasar rigarta saman fuskar shi tana share mashi gumin da ke tsastsafowa, acikin zuciyarta ba ta ji dadin yarda su Batul suka manta da zancen shi ba, Shi kaɗai suka ware, marairaice mashi fuska tayi “Pls ka tashi mu je ka kwanta, baka da lafiya fa, Nasan baka jin dadin Jikin ka,……” tunkan ta ƙarasa maganar Gabriel ya yunƙura ya miƙe, Daurewa kawai ya ke yi don ba ƙaramin jiri yake gani acikin idanuwan shi, ƙoƙarin Yin tafiya yayi Ƙafarshi ta Hagu taƙi bashi haɗin kai, Gaba ɗaya Ya tafi zai kife ƙasa, Azeeza ta fasa uwar ƙara haɗi da ambaton sunan shi, hakan ne ya jawo hankalin su Parveen ga kallonta A lokacin har sun taimakama su Haris sun kwanta saman gadan su, Da gudun gaske suka nufi Gabriel dake ƙoƙarin faɗuwa, Da ya ke Namiji ne Allah yayi shi da ƙarfi bai bari Ya faɗi ƙasa ba, Handrail ɗin benan Ya dafe da hannun shi, Sai faman Huci ya ke fitarwa, Nannaɗaɗar sumar gaban goshin sa duk ta rufe idon shi, Koda su parveen suka ƙaraso ganin ya dafe Hannun benan yasa suka sauke ajiyar zuciya, Azeeza kamar jira ta ke yi su ƙaraso ta dinga surfa masu bala’e akan sun tafi sun bar ta da shi, bayan sun san ita ƙarama ce, da ace ya faɗi kasa kanshi ya bugu me suke tunanin zai biyo baya, Faɗa sosai ta rufe su dashi, ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai faman tada jijiyoyin wuyanta take yi duk akan Gabriel.

“Allah ya huci zuciyarki Azeeza bada son ranmu muka ƙyale shi ba, Hankalin mu ba a kwance Ya ke ba, Amma yanzu kiyi haƙuri, zamu shiga dashi Ciki” Fuskar Yasmin a hautsine tayi mata maganar, ɗaure fuska azeeza tayi hada ruƙe qugu tana binsu da kallo.

Parveen da Yasmin ne suka taimaka wurin ruƙo Gabriel Suka nufi Cikin ɗakin dashi, agaban gadon shi suka sake shi ya hau ya kwanta, Daga gefen shi Azeeza ta hau ta kwanta tana ƙare mashi kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar shi kewar shi da Tausayin shi.

a 6angaren Haris Deeja ce zaune saman gadon shi, Eve da yasmin suna zazzaune gefen gadon shi, Sai sannu su ke yi mashi, Sam ya kasa amsa masu, Sai dai yabi su da ido,

Javed Yana a kwance saman gadon shi, Batul da Sarah ne Zaune gefe da gefen mattress ɗinshi, Ji su ke kamar su ɗauke masu ciwon Jikin su saboda tsabar tausayinsu da su ke Ji,

Idan muka koma 6angaren Naufal Shima Yana kwance Ya lumshe idanuwan shi, Parveen da Hibba suna a zaune saman gadon nashi, suna yi mashi sannu.

A yayin da Hannah da Rubina suke akan gadon Mubeen, hakan ba ƙaramin sanyaya zuciyoyin ƴan uwan nasu yayi ba, Ganin yadda suka nuna damuwa akan su,

“Yanzu ya zamuyi? Ko abinci babu da zamu Iya basu nasan dole suna jin yunwa,” parveen ce ta yi maganar,

“Ko ruwa ne mu fara basu Mu ga idan zasu sha” a cewar Batul, Jin suna maganar ruwa yasa Jamimah ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta lalubo robobin ruwa taje ta miƙa ma Deeja, Bayan ta kar6a taje ta miƙa ma parveen kafin ta nufi Batul ta bata ɗaya” da sauri ta koma ta ɗauko sauran robobin ruwan guda biyu Ta kaima Hanna ɗaya, sannan ta nufi gadon Gabriel Ta miƙa ma Azeeza, Hannu tasa ta kar6i robar ruwan tare da miƙewa zaune ta cire murfin kallon shi tayi, Still idanuwan shi Na akan fuskarta,

“Ruwa ne ka tashi ka sha” tayi maganar tana nuna mashi robar ruwan, Da ƙyar ya yunƙura Ya tada kanshi saman pillow, Yatsun hannun shi sai kerma suke Yi ya gaza iya ruƙe robar, hakan yasa ta kafa mashi ita saitin bakin shi ya soma kur6ar ruwan Yana bi ta makoshinsa, A tsanake Azeeza ta ke kallon fuskarshi Ya canza sosai, kamar ba Gabriel ɗin da ta sani ba.

Bayan kowannan su Yasha ruwan, Jamimah ta tattara robobin ta maida su ƙarƙashin gado ta killace su,
Har yanzu babu wanda Ya tuna da Angel a cikin su, bacci ne ya fara ɗaukar su Javed, cikin ƙanƙanin lokaci baccin yai awon gaba dasu, ganin sun samu bacci yasa hankalin su Batul ya ƙara kwanciya. Kamar sun samu tv haka suka tasa su agaba suna kallon su yayin da su ke yin bacci,

Farin Cikin su ragagge ne, Abu Biyu ya tsaya masu aransu, Na farko Meyasa ba a dawo da Danish ba, Bayan An riga tafiya dashi? Na biyu me aka yi masu na tsawon watannin nan? basu da amsar tambayoyinsu.

“Allah sarki Danish ɗinmu shi ba’a dawo mana dashi ba, Na yi tsammanin dukan su zamu gansu” Batul ce tayi maganar, Deeja tace”saboda mugun nufin su akan shi sunƙi dawo mana da ɗan uwanmu, Nafi damuwa dashi saboda halin da aka tafi dashi, ”

Da alama ransu ya 6aci sosai na rashin dawo masu da Danish, tsawon Awanni Sunyi zugudum babu mai Magana a cikinsu, Wuraren marece Mubeen Ya farka daga bacci, A matuƙar firgice ya zabura ya miƙe zaune Yana haki Gaba ɗaya idanuwan su akan fuskar shi, Kafin su yi yunƙurin tunkarar shi Ya duro daga saman gadon shi kafar shi kamar zata 6alle A haka ya dinga janta ya nufi Sashen toilet ɗinsu, Da gudu Hannah dasu Yasmin suka bi bayan shi, A cikin toilet suka tarar dashi Ya zuƙunna gaban fanfo Yana kwara amai, Wani irin Farin abu mai yauƙi yauƙi ya ke fitowa daga bakin shi har ta hancin shi ya dinga gangarowa, Wa’iya zubillahi! Zuciyoyin su sun karaya da ganin yadda Mubeen ke kwara aman fargabar su kada ya mutu kamar yadda unaiza ta tafi tabarsu, Tuna wannan yasa hawaye wanke fuskokinsu, A gaban shi suka zuƙunna suna kallon fuskar shi, Sai nishi yake yi Yana jan numfashi a wahalce,

“Mubeen dan Allah ka jure, bamu so wani abu ya same ka, Kaga Muna ƙaunar ka sosai” a hankali ya ɗago da idon shi kan fuskar Parveen da tayi maganar, Girgiza kanshi ya yi yana faman cizon la66an shi ya soma magana “Kada ku tada hankalin ku akaina, lafiyata qalou,” tun daga kan yarda yai maganar zai ƙara tabbatar maka da Babu lafiya a jikin shi, ya faɗi hakan ne kawai don ya kwantar masu hankalin su,

“Wlh baka da lafiya Mubeen, Kalli yadda idanuwan ka suka canza launi, kamar ba mubeen ɗin mu ba”, murmushi ya ƙakalo akan fuskar shi Yayin da ya ke kallon Hanna da ta yi maganar,

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

(Mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button