Hausa novels

Halysaah Page 177 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 177 months later Mai martaba ya biya aka kai Khaleesat Turkey For therapy sannan a binciki lafiyarta don abun nata is getting too much day by day, suka je ita da Aunty Farida, likitan ta, da Mukhtar da yayi masu rakiya, a watannin da suka yi a Turkey Aunty Farida babu wani improvement din da ta gani sai kara rikicewa ma da lamarin Khaleesat ya kara yi, ga wani kakkaryewa da gashinta yake yi, kana jan gashin zai biyo ka kuma me yawa, hankalin Aunty Farida ya tashi sosai, nan ta fahimci kawai rokan Allah za a dukufa da yi mata babu wani zancen asibiti, haka nan suka tattaro suka dawo Nigeria kawai. Bayan sun dawo Nigeria Aunty Farida tayi shawara da Mami a bari ta tafi da Khaleesat kano tunda ta fita takaba, duk da bata san yanda ake yi a gidan sarauta ba amma tana son ta tafi gida da ita, a hankali Mami tace “Haka ne Farida, in tayi nisa da Emirate din nan damuwarta zai ragu ta fara accepting reality, zan yi magana da Mai martaba da Hajja sai a kai ku Kanon in sha Allah, ni kaina nayi wannan tunanin” A ranan kwana Khaleesat tayi tana kuka kamar ranta zai fita wai ita bazata je Kano ba she want to be in her husband’s part, sai da Mami ta dinga lallabata kan cewa kwana uku kawai zata yi a kanon sannan a dawo da ita duk don ta yarda ta bi Aunty Farida, a haka tabi Aunty Faridah suka koma kano tare da kayanta kala uku kacal. Mami ta fito bangarenta wajen karfe biyar na yamma ganin tun da gari ya waye Jay bai shigo ba, a kwanakin baya part dinta ya dawo kwana gaba daya yace mata he is having nightmares, wani lokacin ma a dakinta yake kwanciya duk da baccin nasa rabi da rabi ne, sai ya kai karfe uku bai yi bacci ba, wani lkcin har kusan asuba, yanxu kuma all of a sudden taga ya koma ɓangarensa, kuma sai ya kai yamma bai fito ba, tana isa ta bude kofar parlon ta shiga, breakfast dinsa ta gani a parlon da lunch da aka shigo aka ajiye duk babu wanda ya taɓa a ciki, tayi ta kallon abincin, sai kuma ta karasa Bedroom dinsa, knocking tayi hade da sallama tace “Jawwad” jin bai yi responding ba ta bude kofar dakin ta shiga, sai taji yana bandaki yana wanka, ta kalli saman gadon taga alamar tashinsa kenan, satchets din pills da ta gani kan gado ta karasa ta dauka tana juya satchets din tana kallon maganin, ta kalli kofar bandakin sai kuma ta juya ta fita daga dakin ta koma part dinta tana ta kallon maganin, wayarta ta dauka tayi snapping pills din sannan ta tura ma Likitan dake duba Khaleesat tana tambayarta magungunan menene, after a while Likitan ta tura mata feedback, Mami ta dinga kallon feedback din Dr din with shock, sosai jikinta yayi sanyi, lokaci daya hawaye ya cicciko idonta ta dafe kanta da taji yayi mata nauyi, ta fi minti goma zaune parlon cikin tashin hankali daga karshe kawai ta mike ta tafi bedroom dinta tana hawaye, After almost 30 minutes taji sallamansa a bakin kofar dakin, ta amsa tana ci gaba da gyara kayan da take yi a press dinta, ya shiga dakin ya ɗan kalleta sai kuma ya sunkuyar da kai ya zauna, a hankali yace “Ina wuni Mami?” Mami bata kallesa ba tace “Lafiya lau, sai yanxu ka tashi?” Ya gyada mata kai kawai, Tace “Tun safe?” Ya sauke idonsa yace “Ina tashi inyi sallah” Mami bata sake ce masa komai ba tana ta gyaran kayanta, a hankali yace “Mami kin shigo part dina ne?” Mami ta kallesa a karo na farko tace “Me ka gani?” Yayi saurin sunkuyar da kansa yace “A’a kawai tambaya nayi….” Tace “Ban shiga ba” Shiru yayi yana tunanin ko Hadiyah ce ta shiga, duk da har sannan bai maidata ba amma ta kan shigo tayi masa gyare gyare ta share ko ina ta goge, barin idan yana part din Mami idan ya koma zai ga ta gyara ko ina, to amma bai ga anyi gyara ba a part din ai tunda yana ciki, kuma yasan ta shigo taga yana baccin shi yasa bata yi gyaran ba, Mami tace “Ka ci abinci ne?” Duk da bai ci ba ya gyada mata kai kawai alamar ya ci, don yasan ba iya ci zai yi ba, Mami zata yi magana aka bude kofar dakin ta juya tana kallon kofar, Khaleesat ce ta shigo dakin tana tafiya kamar iska zai kadata ta fadi, da mamaki Mami ke kallonta har ta karaso cikin dakin ta zauna kasan carpet looking so tired, ta kwantar da kanta jikin gadon Mami, Mami ta karasa kusa da ita ta zauna gefen gado tace “Halysaah” Khaleesat ta daga idanuwanta a hankali ta kalleta, Mami tace “Daga ina kike?” Murya can kasa tace “Kwana uku ai aka ce zan yi” Mami ta dinga kallonta don shekaranjiya suka tafi, can dai tace “To ke da wa kika dawo yanxu?” Tace “Ni kadai” Da mamaki Mami tace “Ke kadai? A mota suka sa ki kika dawo? Ki gaya min gaskiya Khaleesat, basu sani ba kika taho ko?” Lokaci daya hawaye ya cika idonta, ta fara kuka a hankali tace “To baza su bar ni in dawo ba Mami” Mami ta dafe kanta, can tace “Yaushe kika bar gidan?” Tana goge hawayen dake zuba idonta a hankali tace “Da safe” Mami tace “A ina kika hau mota?” Shiru tayi, sai kuma ta daga ido ta kalli Mami tace “Bani da kudin mota, sai na tafi tashar Mariri da kafa, wata mata ce ta biya min kudin mota a tasha da nace mata banda kudi” Mami ta kasa cewa komai, shi dai Jay ya jinginar da kansa da kujera yana kallonta cike da tausayinta, Mami ta jawo wayarta don ta rufe layin da aka santa da shi tun jiya ta bar personal line dinta a kunne, tasan kilan su Aunty Farida na ta kiranta, ta kalli Jay tace “Wayar ka a kashe yake ne?” Ya gyada mata kai, Mami na bude layinta sai ga kiran Aunty Farida ya shigo, suna gaisawa Mami tace “Wallahi yanxu ta shigo Farida shi ne ma har na kunna wayar nasan kuna ta nemana….” Mami ta kasa cewa komai tana sauraron Aunty Farida, can ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Za mu yi magana Farida” Daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleesat dake hawaye, cikin rawan murya tace “Mami ni nafi son in zauna a nan har sanda zai dawo, don Allah ayi hakuri a bar ni in zauna a nan, kar ya dawo bai ganni ba” Tana fadin haka ta fashe da kuka a hankali, Jay ya mike kawai ya fita daga dakin walking slowly, ya koma parlor ya zauna rike kansa, Mami dai ta kauda kai jin idanuwanta sun ciko da kwalla, can Mami ta share idonta tace “Yaushe kika fito daga gidan Halysaah?” A hankali Khaleesat tace “Ana sallan asuba” Mami bata sake ce mata komai ba ta mike ta nufi bandakinta tana share hawayen dake zuba idonta, ga damuwar Jay dake neman lalata rayuwarsa ga kuma na Khaleesat yanxu, duk abun ya taru ya hade mata, ruwan wanka ta hada ma Khaleesat a bandakin ta sannan ta fito tace “Ki je kiyi wanka, bari in sa a kawo maki abinci…” Khaleesat ta mike ta nufi bandakin tana tafiya a hankali, tsabar wahala har wani disashewa haskenta yayi…..

Back to top button