*_Typing📲_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_Shafi na talatin da uku_
___________
Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846
Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria
Ummu khalifa 01017018846
______________
……Zama tai a ɗan takure, sai dai a bazata taji ya saƙalo hannunsa ta bayanta ya kwantota saman kafaɗarsa, batare da ya sake magana ba ya cigaba da aikinsa. Ta jima idanunta a runtse dan kunya, kafin ta buɗesu a hankali tana kallon abinda yake a laptop ɗin. A haka masu aikin Mamy da suka kawo mata abincin sukai sallama. Zata tashi ya sake maidata yana amsa musu sallamar, sai kuma yace su shigo. Kamar Khadijah zata fasa ihu dan kunya, amma shi sai taga aikinsa ma kawai yake. Ta gefen ido ta kalla masu aikin, sai taga tunda suka musu kallo ɗaya basu sake yi ba. Ko gaishesu da sukai kawunansu a ƙasa suke. Shi hannu ma kawai ya ɗaga musu, sai itace ta amsa musu. Koda suka shiga kitchen ɗin ma suka fito sam basu kallesu ba har suka fice, a hankali ta sauke ajiyar zuciya har yana iya jinta. Sai dai baice komai ba face ɗan murmushi daya saki kaɗan ya cigaba da aikinsa. Kusan awa ɗaya suna a haka, tun tana noƙe jikinta harma ta saki wani barci-barci ya fara rinjayar idanunta dan ƙamshin turarensa ba ƙaramin ratsata yake ba da saukar mata kasala. Laptop ɗin ya rufe ya ajiye tare da sauke ƙafafunsa dake a table ƙasa. Sai kuma ya ɗan kalleta yana mai kai hannunsa saman fuskarta ya shafa. Firgigit ta buɗe idanun, ganin yanda fuskarsa ke gab da tashi ga hannunsa akan tata fuskar ya sata ɗaga kanta a kafaɗarsa da ɗan sauri.
“Da’alama kin gaji da yawa, ansha rawa wajen party shekaran jiya ko?”.
Juyowa tai da sauri batare data tuna dawa ma take maganarba, idanunta a ɗan ware bakinta na nuna alamun ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni wlhy bana rawa, kuma dai ai kowa yasan banyi ba”.
Wani irin harmutsawa jinin jikinsa yayi saboda yanda tayi ɗin, ga idanunta sun sake wani haske har ƙyalli suke, baƙin ya ƙara baƙi, lips ɗinta sun ɗan tattare kaɗan. Samun kansa yay da jinjina mata kansa, idanunsa na a cikin tsakkiyar nata idanun, kamar mai raɗa ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Uhmm nima shaida ne bakiyi rawan ba, amma yanzu zakiyi min nawa a ɗaki ko….”
“Rawan!”.
Ta faɗa cikin ƙara waro idanunta sosai waje, irin nuna alamun matuƙar mamakinsa ɗin nan.
A wani irin sake kasancewa a kasalance ya jinjina mata kansa yana lumshe idanunsa da buɗewa cikin nata ya furta, “Uhhumm Baddo”.
Kamar wadda aka maido hayyacinta ta miƙe zabar, sai kuma cikin sassarfa ta nufi barin wajen da bashi amsa muryarta na rawa. “Ni ALLAH bana rawa”. Wuff ta shige ɗan lungu bedroom ɗin ta. Murmushi mai bayyana haƙora ya saki, sai kuma ya taune lips ɗinsa da ƙarfi yana ɗan kaima kansa ƙaramin mangari ya ce, “Abaan kai ɗin nan ko”. Sai kuma ya sake sakin murmushin da komawa cikin kujerar ya wani lafe. Shi gaba ɗaya ma ji yake yana neman rasa control ɗinsa akan yarinyar nan. Anya Ibrahim da Adams ba saida suka tofeshi ba kafin su kawo wannan batun ga Mamy. Abin da mamaki fa, sam mantawa yake da cewar Khadijah ta taɓa aure kafin shi ɗin, kallon wata ƙaramar yarinya budurwa sharaf yake mata, koda yake yarinyarce ai, 20years fa, ko ƙanwarsa daya bama shekaru masu tazara sosai ta girmeta fa. Ai dami a kala kawai ya tsinta…
Tafi minti takatin da shigowa sannan ya shigo, dan harta canja kayanta zuwa na barci. Wando da riga ne masu santsi da basu kama jikinta ba, sai hula data saka amma duk da haka kwantaccen gashin gaban kanta sai da ya fito. Zaune take a saman gadon ta jingina da fuskarsa littafin addu’oi a hannunta. Ta rage fitilar ɗakin sai lamp na side drawer kawai da take amfani da shi wajen ganin rubutun littafin. Shigowar tasa sai da ta ɗan sakata razani, dan duk ta saki jiki akan bazai biyota ba. Ta ƙasan ido take binsa da kallo har ya hawo gadon, ganin ya ɗan zuba mata ido ya sata ɗauke nata ta maida ga littafin. Tsahon wasu sakanni kuma sai ya matso jikinta gab. Wani yarr taji saboda jin saukar kansa a kafaɗarta amma ta dake. Hannunsa ya ɗaura saman nata dake riƙe da littafin ya ɗan jawo kaɗan shima yana kallon rubutun larabcin. A haka suka cigaba da karantawa a tare batare da yayi magana ba. Ganin sun kammala karanta na barcin tana neman buɗe wani shafin kuma ya sashi zare book ɗin a hankali, jikinta ya ɗan ranƙwafo har tana ɗauke numfashi ya ajiyesa a side drawer ɗin, sai kuma ya nufi sauka gadon yana faɗin, “Kina da alwala?”.
Kanta ta jin jina masa alamar eh. Shima sai ya jin jina nasa da bata umarnin ta sakko. Sun gabatar da salla raka’a biyu, ya kama kanta yay addu’a tare da yi musu addu’ar zamar lafiya da samuwar zuri’a mai albarka sannan suka sake komawa garon. Zama ta sake yi kamar ɗazun, batare da yace mata komai ba ya rage ƙarfin lamp ɗin ƙasa sosai. Sake maida kansa yay a kafaɗarta kamar ɗazun ya riƙo hannunta cikin nashi ya matse har sai da ta ɗan zabura kaɗan.
“Mrs Abaan Omar Modibbo!”.
Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa idonsa akan hannunsu dake cikin na juna. Zuciyarta na bugawa da sauri-sauri a hakanli itama ta ce, “Uhmyim”.
“Thanks you Baddo da kika amsheni a matsayin miji duk da ban taɓa zuwa gareki na nuna kaina ba, bazan ɓoye miki ba kin matuƙar burgeni da kika amshi auren nan a yanda yazo miki batare da nuna koda a fuskarki an miki ba daidai ba. Lallai ke kin cika ɗiya tagari abin alfaharin kowaɗanne iyaye. ALLAH yay miki albarka, ALLAH ya yarda dake fiye da yanda ni mijinki nake jin na yarda dake. UBANGIJI ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya. Baba ya sanar dani komai akanki, ina son ki manta da abinda ya faru baya domin kuwa ƙaddararki ce, ita kuma ƙaddara duk iya gudunka baka isa tsere mata ba. Tun randa muka tsinceki a bakin hanya tabbas naji tausayinki sosai a raina, duk da kuwa ban san minene dalilin shigarki a halin da muka gankin ba. Bayan mun kaiki gida na tafine da tunaninki a wannan yinin, sai dai kasancewata mutum mai yawan sabgogi ina komowa Abuja namance komai daya shafeki na cigaba da harkoki na. Kasancewar irin rabuwar da mukai da matata ta farko Mamy kullum cikin roƙona take kan na fidda matar aure. Nakan bata amsa da cewar ba yanzu ba, idan kuma naga ta damu sai nace mata ta zaɓamin kamar yanda ta zaɓa min ta farko. Hakan kansa ta ƙyaleni, dan tana ɗaurama kanta laifin a kan yanda matar data zaɓamin ɗin ta kasance a baya. Sam lokacin da muka kaiki gida ban san su Adams nada alaƙa da gidanku ba, duk da nasan an saka musu date ɗin aure kuma zasu auri yara ƴan gida ɗaya ne. Ban taɓa maganarki kuma da su ba duk da su ɗin sun wuce yarana na business sun zama tamkar ƴan uwane gareni saboda gaskiyar su da riƙon amana. Dan sukan iya zuwa cikin gidan nan suci su sha suyi hira da Mamy harma suyi kwanaki, haka nima nakan ziyarci iyayensu a duk sanda na samu dama in har na shiga Kano. Mamy itace ta haɗa lefensu su duka, bayan ta kammala haɗawar ne tai kiransu dan su gani, sannan baifi saura sati uku bikin nasu ba, ni lokacin ma bana ƙasar. A randa sukazo ɗin ne Ibrahim na waya da ƙanwarki sai maganarki ta shigo ciki akan miki ɗinkunan fitar biki, alokacin Mamy na tare dasu, dan harta gaisa da Ni’ima ma. Bayan ya gama wayar yake cewa Mamy zai bada a saya miki kaya kema kamar kala biyar haka dan kayan lefen nan sun masa ƙyau, anan ne Mamy ke tambayar wacece ke ɗin kuma, dan duk zatonta wata budurwarce kuma daban, shine suke bata labarinki. Mamy macece mai tsananin tausayi, sannan da kike ganinta nan ƴar gwagwarmaya ce akan mata, a take ta nema ganin hotonki, tare da alƙawarin tsaya miki kiyi ilimi. Su Adams duk basu da hotonki sai da suka kira su Zuhrah suka tura musu. Ta jima tana kallonki fuskarta da murmushi, a bazata sai ji sukai ta ce, “Ni dama ɗan rigimar ogan nan naku zai amince ai da sai yay mana wuff da wannan black beauty girl ɗin kawai. ALLAH yarinyar ta shiga raina matuƙa”.
A take maganar tata ta ɗauki hankalinsu, musamman ma Noor da tai ta zigawa akan a min magana akuma turamin hoton. Tun Mamy bata ɗauki zancen serious ba harta amince a washe gari tai kirana, kai tsaye tace tamun mata na duba ga hoto nan ta tura min ta email ɗina na gani idan tamun. Duk da maganarta ta shigeni, kuma ba auren ne a gabana ba sai kawai na amsa mata da cewar na amince in har yarinyar ta mata. Harga ALLAH banga hotonki ba, dan ko buɗesa ma banyi ba na goge. Farin cikin da naji Mamy da Noor na ciki ya samun jin zan iya amsar auren koda bazan soki ba, dan matata ta baya ta gama ciremin sake jin son wata mace a rayuwata. A ranar Mamy ta aika su Adams Kano domin yin magana da Baba, ban san hidimar da suke ba dan tun a ranar na manta da batun wani tayin aure da Mamy tamun, ashe su suna nan sunata kai kawo dan da farko Baba yaƙi amincewa har sai da Mamy taje kano da kanta sannan, lokaci baifi saura kwana takwas bikin su Adams ba aka tsaida namu zancen. Ban dawo Nigeria ba sai ana saura kwana uku, na kuma zo ne da shirin bikin su Ibrahim. Sai kawai na samu an gyara gidan nan tsaf harma wasu a baƙin Adamawa sun fara isowa. Humm abin yaban mamaki, amma yanda naga mamy ta ɗauki abin da muhimmanci ya sakani danne zuciyata na cigaba da binsu da ido. Sam banyi niyyar zuwa dinner ɗin nan ba amma Mamy ta matsa tare da magiyar su Adams dole nai shiri aranar nabi jirgin ƙarfe shida zuwa Kano. Kin san wani abu?”. Yay maganar ƙarshe cikin sigar tambaya yana ɗan matsa hanunta dake cikin nashi da ɗan ɗaga ido ya kalleta. Kanta ta girgiza masa a kasalance.
“Tun kafin mu shigo cikin hall ɗin nan na fara cin karo da zazzaƙar muryarki da tai matuƙar ratsani kina addu’oi. Jinai na kwaɗaitu da son ganin mamallakiyar muryar tunkan na shigo ciki, sai dai muna shigowa muka samu kin gama. Ni ne na turama Awwal saƙo cewar a sake sakaki ki fito kiyi addu’a…..” da sauri ta waro masa idanunta alamar mamaki, murmushi ya sakar mata da cigaba da faɗin, “Lokacin da kika miƙe jinai kamar na zama tsuntsu naje naga fuskarki, dan sam bana ganinki da ƙyau, har sai da kika kammala kika koma mazauninki. A lokacin ne na iya ganin fuskarki, ji janai zuciyata na neman fitowa ta baki, da ƙyar na iya controlling kaina, abinda zai kuma baki mamaki har lokacin banfa gane ki ba, dan kin canja gaba ɗaya daga waccan ranar. Sannan kuma ban san kece matar da Mamy ta zaɓamin ɗin ba har sai da aka sake kiranki matsayin yayar amare da zata bada tarihinsu. Anan ne zuciyata ta shiga waswasi har lokacin da tsageran yaron nan ya fito ya fara miki liƙi, kawai saina samu zuciyata da shiga ƙunci harna kasa dannewa na turama Ibrahim saƙo, amsar daya bani ta sakani miƙewa zimbir na nufeku, sai kuma ga Awwal yazo min da batun wai kece ai muka kai gida watanni takwas da suka wuce. Bayan mun kaiki gida na koma masauki ban iya barci ba Khadijah, kwana nai ina jerama UBANGIJI godiya dan wlhy a ƙanƙanin lokaci ya dasa min ƙaunarki a zuciya irin wadda ban taɓama wata ɗiya mace da sunan soyayya ba a rayuwata. A washe gari na matuƙar jin ƙagara a ɗaura mana aure, dan kawai saina samu kaina da tsoron karfa tsohon mijinki ya dawo yace bai sake ki ba, ban samu nutsuwa ba har sai da naji an ɗaura mana aure. Ina sonki Khadijah, ina matuƙar sonki har cikin jinina, ina fatan nima zaki soni ki ƙaunaceni koda ƙanƙanine dan ALLAH. Karki wahalar dani domin ni mai rauni ne akan soyayyarki”. Hannunta dake a cikin nashi ya ɗorasa saman ƙirjinsa, cikin sake raunana murya da kafeta da mayun idanunsa masu matuƙar haske da girma ya furta……✍️
Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 34 By Billyn Abdull
_____________
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA…🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*