Karfe A Wuta Chapter 15 By Ayshercool
A take ya hankaɗe uwar a gefe, ya yi wa ramma wani irin miskilin murmushi, ya nufe ta yana wata irin tafiya, irin ta riƙaƙƙun ƴan iska ya ce “Hi baby girl, long time almost 2months kenan fa ko?”Hawaye ne ya fara bin fuskar ramma, jikinta ya hau rawa.Ya sanya hannu ya dafa jikin bango, yana ƙare mata kallo ya shafi sumarsa ya ce “To ya ki ke, kin warke?”Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, tana tuna waccan ranar, da irin yadda ya keta mata haddi cike da zalunci.Ya ce “Ohh, wai waccan ranar ce haryanzu ba ki manta ba ki ke kuka? Ya wuce ai wancan, kin bar ni da tsananin kewarki, duk ruwan da na sha komai sanyin sa, ya daina kashe mini ƙishirwa”.Ya kai hannu ya ɗago fuskarta, ya shafi hawayen da suke ta ambaliya a kan fuskarta.Yinƙurawa mamanta ta yi da sauri, tana kururuwa ta ce “Kar ka taɓa mini ƴa, mugu azzalumi, wai babu wanda zai kawo mini ɗauki ne?”Ya kalli su Salim ya ce “Ku saka mini matar nan a silent”Haka suka rirriƙeta, suka ɗaure mata baki, suka shaƙa mata wani abu, a take jikinta yayi laƙwas.Ya sake kallon ramma ya ce “An ce akwai unborn ɗi na a cikin ki ko? da gaske za ki haife shi kuma?”Cikin kuka ta ce “Ban yafe maka ba, ka lalata mini rayuwa, ban sanka ban taɓa ganinka ba, ka biyo ni gida kana wulaƙanta mini uwa, dan bamu da kuɗi, Allah ya saka mini” tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfin ta.Salim ya sunkuyar da kai ya yi shiru, haka nan ya ji abun yayi masa wani iri a zuciyarsa, sauran matan da suke lalata da su, suke kai kan su, wannan kuma yarinya ce ƙarama.Dariya ya yi ya ce “Dan kin ce baki yafe ba, ba zai hana ni shiga aljanna ba, kun ƙuduri aniyar neman hakkinku, duk da an yi muku tayin kuɗi kun ƙi, zan nuna muku ƙarfi da izzar kuɗi a ƙasar nan”.Ya danƙi hannun ramma, da jikinta ya ɗauki zafi sosai.Tana ihu tana kiran mama, ya ja ta suka fice daga gidan, suka sakata a mota suka tafi da ita.*****Ɗan mama ne ya shiga ɗakin Viper, ya tarar da shi yana ta sintiri a ɗakin.”Ka daɗe ka yi ƙarko uban gidana”Viper ya tsaya cak, yana jiran ya ji me zai ce.”Na yi aikin da ka saka ni, ya tafi yadda yakamata “Ya kaɗa kai tare da yi masa alamar ya ƙaraso.”Ina labarin malam lawan?””Kamar dai yadda ka ce, an kula da komai, sai dai babu wanda ya sake zuwa, gashi yanzu yana yawo a cikin unguwa”.”Madaki fa?””Shi ma kamar dai yadda ka sani, Honorable indabo yake yi wa aiki yanzu”.”Ina buƙatar isassun kayan aiki, a kwanakin nan zan dirar masa, mu ɓalla ƙarfe, sai dai mu yi mutuwar kasko, ayi wadda za ayi”.”Ba yanzu ba” suka ji muryar Walid.Suka mayar da hankalinsu kan sa.Walid ya ce “Viper da sauran lokaci, kai ka san madaki ba haka kurum yake daba ba, da zai kasu cikin sauƙi, da tuni mun kawar maka da shi, ka ɗan saurara tukuna”A hasale ya ce “Ba zan saurara ɗin ba tukuna””Viper!”Ciki ƙaraji ya ce “Walid ka ƙyale ni”Walid ya girgiza kai ya ce “Da zan iya, da tuni na yi, mutumin nan ya fi ƙarfinmu ko ta ina, idan ka yi amfani da zuciya wallahi ba zamu yi nasara ba, ka bari mu bi komai a hankali mu lissafa, yadda ko mutuwar kasko ce mu yi”Cikin ƙaraji ya ce “Ba zan jira ba, na gaji, na gaya maka na gaji. Na so bin komai a hankali, meyasa ka kawo mini yarinyar saboda me? ka san ka ƙara tunzara zuciyata yaya ka ke so na yi, so ka ke sai na haukace tukuna? Kalli yadda na koma walid, kalle ni, abun da nake ta ƙoƙarin dannewa ka fama mini, dan me zaka kawo mini wannan yarinyar sannan ka ce na nutsu how? Ta ɗauki wayata ta tafi, ka na da tabbacin hannun wa wayata za ta shiga? Idan aka tashi kama ni, kana da tabbacin su waye za su kama ni, idan na ƙare a haka ban aikata abun da nake ƙuduri ba fa? Ko dai ka nemo duk in da yarinyar nan take na kasheta, ko kuma a yau ba sai gobe ba, sai na yi gaba da gaba da madaki ko na kashe shi ko ya kashe ni, amma kafin nan sai na fara gaba da gaba da wancan dabban” tuni gumi ya tsatsttsafo masa, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, kafofin gashinsa ya bubbuɗe.Walid ya taka gabansa a hankali, cike da shirin ko ta kwana, dan ya san ƙarshenta sai ya ba shi gwale-gwale, ko ya mangare shi.Ya shammace shi, ya soka masa sirinji a damtsensa, kasancewar jikinsa babu riga, ya fara yi masa allura, sannan ya fara yi masa magana.Walid ya ce “Na san na yi laifi, amma ka bari na gyara laifina da kaina, na san abun da ka ke ji ɗan uwa, ba kai kaɗai ka ke ji ba Al’amin”Viper ya zubawa walid ido, ya rasa me zai yi, yana tsaye ya kashe masa jiki, ba zai iya komai ba, kasa tsayuwar yayi, ya tafi zai faɗi walid ya riƙe shi ya kwantar, ɗan mama kuwa dama tuni ya arce, dan yana tsoron a shaƙe shi.Barrister Naja’atu ce zaune a katafaren ofishin ta, tamkar na matar gwamna, yana ɗauke da duk wani kayan alatu da ake buƙata.Sannu a hankali take shafa screen ɗin wayarta, daga bisani ta saka wayar a kunnenta.”Honorable, ka isa Abujan ne?”.Ya amsa da “Eh ma sauka””Ok, yaya maganar yarinyar nan da Abdul ya yi raping?””Yes, he handle the case himself, yayi maganin abun”.Ta ce “Ok, ina fatan ka ja masa kunne, kar ya je ya aikata wani shirmen da ba zamu iya gyarawa ba”.Ya ce “No, kar ki damu, zai yi abun da ya dace”.Tayi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan, dama ina tsoron ya yi wani shirmen ne, amma tun da ka ce haka, shikenan”Ta katse wayar, ta mayar da hankalinta kan sakatariyarta da ta shigo.Cikin gyatsine ta ce “Ke kuma ya aka yi?””Kin yi baƙi ne ma””Suwaye?””Eh to, da alama dai ƙorafi suka kawo, ke suke…..”Ke bani da lokaci, ayyuka sun yi mini yawa, su ganki ko wani daban, hutawa nake buƙata, wannan jaraba a uzzurawa rayuwarka, london zan wuce ma ni this week na je na huta. Ki fita ki je ki sallame su” ta juya jiki a sanyaye ta bar office ɗin.Salim ya kalli Abdul da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana shan giya a cikin wine cup ya ce “To wai yanzu ya zaka yi da yarinyar nan da ka kawo ka ajiye, Ga abun da aka tsara, kai kuma ga abun da ka yi?”Ya ɗan girgiza giyar a cikin kofin sannan ya ce “Gani na yi za ta ci bulus idan ta tafi a haka, sai na gama moreta zan aikata kawai””Amma ba ka ganin, hakan zai iya kawo matsala, yanzu ko a nan gaba?”Ya girgiza kai ya ce “Ba wata matsala, na ɗan lokaci ne, zan gama abun da zan yi da ita, zaka iya tafiya ma kawai”Ya jinjina kai ya ce “To shikenan”Sannu a hankali ta buɗe idonta, ta din ga gani dishi-dishi, ta kasa tantance a ina take, dan ba ta taɓa ganin wurin ba.Ji ta yi an rufe ƙofa, ta ɗaga kai ta kalli mai shigowar, take gabanta yayi mummunar faɗuwa, duk da idonta bai gama washewa ba, amma sarai ta gane shi.”Kin tashi kenan? abun da aka shaƙa miki bai taka kara ya karya ba, amma ki ka yi wannan dogon zangon” yayi maganar lokacin da ya tsuguna a gabanta yana kallon idonta.Ƙirjinta ya din ga bugawa da sauri da sauri.Ganin ba ta ce komai ba, ya sanya ya tashi ya fita, babu jimawa ya dawo da plate a hannunsa, ɗauke da indomie da kifi a ciki, sai ruwan roba, hannunsa ɗaya kuma ledar magunguna ce.Ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya fara haɗa alluran.Tayi shiru ta zuba masa ido, har sai da ya ce “Ki ci mana, allura zan yi miki”Cikin kuka ta ce “Dan Allah kar ka kashe ni”Abdul ya yi wani murmushi ya ce “Saboda me?””Ni dai kar ka kashe ni, dan Allah ka mayar da ni wurin babata”Ya kalleta ya ce “Kashe ki fa sai na yi, ba dai ke taurin kai ba ke da babar taki, zan nuna muku cewa talaka ba komai bane illa bawa kuma takalmi ga masu kuɗi da dukiya, ba yanzu zan kashe ki ba, sai kin gama yi mini amfani tukuna.Yanzu ki ci abincin nan, zan yi miki allurai na zazzaɓin da yake jikinki”.”Ni ba zan ci ba” ta yi maganar za ta tashi tsaye, amma ya daka mata tsawa ya ce “Wallahi idan ba ki ci ba, a yanzu zan kashe ki, ko gawarki babarki ba zata gani ba”.Babu shiri ta fara cin abincin, sai dai a loma ta uku, ta hau amai, ta amayar da duk abun da ta ci.Cikin tsananin takaici ya ce “Ke mahaukaciyar ina ce zaki yi mini amai a nan? Nan yayi miki kama da wurin juye ƙazanta?.Tayi shiru ta sunkuyar da kai.”Tashi mu je in nuna miki in da duster da mopper suke ki gyara”Cikin tsoro ta tashi, tana jiri tana bin bango, haka ya saka ta gyara wurin da ta yi aman.Bayan ta gyara, ta shiga banɗakin tayi alwala, ta fito ta tayar da salla, ba tare da ta san ina ne gabas ba, da kuma adadin sallolin da ake bin ta ba, dan ba ta san adadin lokacin da ta shafe, ba a hayyacinta ba.Ya dawo ya tarar da ita a zaune, a takure wuri guda, bai kulata ba, ya ƙarasa ya sanya hannun sa a goshinta, ya ji shi da zafi rai. ɗaga ta ya ja ta ya dungurar da ita a kan gadon.Ya kama hannunta, ya saka sirinji, ya fara ɗaukar jininta.Bayan ya gama ɗaukar jininta, ya yi mata wasu allaurai duk a jijiyar hannunta.Ta zubawa saurautar Allah ido, dan kasa magana ta yi, tun yana allurar ta fara jiran jin alamar ciwonta ya ƙaru, dan ta sallama kashetan zai yi kamar yadda ya faɗa, amma bayan ya gama yi mata ya tashi ya fice, ya kulleta a ɗakin, ba tare da ta ji yanayinta ya sauya ba.***Abun duniya fa ya ishi Nabila, wayar Viper ta zame mata wahala, dan kuwa kashe ta tayi gabaki ɗaya, sai dai duk in da ta zauna, musamman da daddare, idan ta shiga cikin duhu, Viper ne yake yi mata gizo, har abun ya fara tasiri a yanayin mu’amalarta.Tana toilet tana wanka, wayarta ta din ga ringing babu ƙaƙƙautawa, ta kammala wankan ta fito, ta ɗauki wayar tana dubawa.Lambar Nasir ta fara kira, ta nemi wuri ta zauna a gefen gado, tana jiran ya ɗaga.”Ina ki ka shiga ne? Ko kina wurin aiki ne?”Ta ce “A’a, yanzun nan na dawo gida””Baki da lafiya ne?””No, gajiyar aiki ce kawai””To, aikin ki yayi kyau arfa, na yi waya da mu’azzam, gayen nan da ki ka faɗa mun kama shi, tare da tabar wiwi da ƙwayoyi”Sassanyar ajiyar zuciya ta yi ta ce “Alhamdilillah ala kulli halin, Allah shi ne abun godiya, what next?”Ya ɗan yi shiru sannan ya ce “Na saka lallai su fara tuhumarsa, ya faɗi in da Viper yake”.Zuciyarta ta din ga raya mata ko ta sanar masa kai tsaye, abubuwan da suke gudana, ta bashi wayar hankalinta ya kwanta, amma zuciyarta ta gargaɗe ta a kan aikata hakan.***In da ya bar ta a kan gadon, nan ya je ya sake tarar da ita, ta tashi ta zauna ta dunƙule jikinta a wuri ɗaya tana bacci, sai ajiyar zuciya take yi.Wani irin murmushi ya yi, yayi miƙa lokaci guda, ya fara rage kayan jikinsa.Motsinsa ya sanya ta farka, fes ta buɗe idanunta, sai dai hankalinta ya yi mummunan tashi, ta ja da baya, ba ta ƙaunar ganinsa ko kaɗan.Ya hawo kan gadon ya nufota, ta din ga ihu tana kiran sunan Allah, ta na yi masa magiyar ya ƙyaleta, ya mayar da ita gida.Amma kamar ya kamo ƴar kaza, haka ya danƙota zai yi mata rashin mutunci, sai dai yana haɗa ta da jikinsa, ya ji kamar ana hura wuta a Jikinta, saboda zafin zazzaɓi, gashi sai wani irin ƙarni take yi, da warin man kaɗanya da take shafawa ya haɗe da ƙarnin koren sabulun da take wanka da wanki da shi.Ba wannan ya fi damunsa ba, rashin saukar zazzaɓin jikinta ne bai so ba, dan ko a yanzu a galabaice take.A ɓangaren ramma ma, warin giyar da yake yi, da ƙamshin turaren sa ya sanya ta fara yinƙurin amai, ba shiri ya cikata, ta sauka da gudu, ta tafi banɗakin da yake cikin ɗakin, ta din ga kwara aman, sai dai ruwa kawai take amayarwa, bayan shi babu komai a cikinta.Ta gama aman tana ta sauke numfashi, ta lallaɓa ta fito, tana bin bango, sai dai ta tsaya cak tana kallon sa yadda ya zuba mata ido.Cikin kuka ta haɗa hannayenta ta ce “Dan girman Allah ka yi haƙuri, ka mayar da ni in da ka ɗauko ni, hankalin mamana na san yana can a tashe, dan Allah ka yi mini rai ka yi haƙuri” ta ƙarasa maganar tana zubewa a kan gwiwoyinta tana bashi haƙuri”.Strip ɗin gwajin ciki ya ɗago da yake hannunsa, wanda ya gwada da jininta da ya ɗiba ɗazu ya ce “Ke ce mace ta farko da ta fara ɗaukar cikina, kin kafa tarihi, tun da ki ka ce ba za a zubar ba, nima na ji ya shiga raina, ina son abuna, zaki haife shi kafin na kashe ki, kuma ba zan kashe ki ba sai bayan kin haihu” ta yi shiru tana cigaba da zubar da hawaye, wai ita ce ɗauke da ɗan shege a cikinta, a wani keɓantaccen wuri tare da ɗan iska, saboda kawai ba su da kuɗi, sai yau ta ƙara tabattar da illar talauci.Ya miƙe tsam daga kan gadon ya fice ya bar ta a ɗakin, ba tare da sanin makama ko abun yi ba.Sumayya ce a office ɗin manager, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa.Ya kalleta ya ce “Sumayya yaya aka yi ne? Ko yayi miki wani abun ranar da ku ka yi program ɗin?”Ta girgiza kai alamar a’a.”To menene? Na ga kin yi editing ma kin tura mini, komai yayi normal, na ce a saka idan lokaci yayi kin yi ƙoƙari sosai, ina ga program ɗin hannunki zai dawo gaba ɗaya”Ta sauke numfashi ta ce “Sir”Ya amsa da “Yes ma”Sai kuma ta yi shiru.”Ki gaya mini mana idan da wani abu” ta girgiza kai ta tashi ta fita.Addu’a ya din ga yi a zuciyarsa, tare da fatan Allah ya sa ba wani abun indabo yayi mata ba, dan ya san halinsa sarai.Nabila tana office ɗin ta, tana aiki, barrister Habib ya buɗe ya shiga da sallama.Miƙewa tayi tsaye ta ce “Sannu da zuwa, da ka kirawo ni ai”Ya ƙarasa gaban teburinta ya ce “Babu damuwa, aikin da ki ka ba ni ne na yi”Tayi murmushi ta ce “Taimakon da na nema dai aka yi mini”Shi ma murmushin ya yi ya ce “Zan tura miki court ɗin da aka fara yi masa shari’a, da sunan wurin wanda za ki je ya binciko miki file ɗin, akwai dai wani abu a ɓoye”.Cikin sauri ta ce “Ok, ai daga nan ma kana tura mini sai na tafi”Ya ce “Wait, ki tafi yanzu ba ki da aiki ne?””Ai na kusa kammalawa saura kaɗan ne”Ya ce “shikenan, zan tura miki ta what’s app, amma ki bi a hankali, fa kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba””In sha Allah, na gode sosai”Yana fita ta fara lissafi a ranta, tun kan viper ya je hannu, za ta bibiyi cases ɗin sa na baya, domin a shirye take da ta ƙalubalanci hukumar shari’a ciki har da alƙall da kuma hukumar gidan yari, kan sakin Viper ba tare da ƙa’ida ba, ta san ko ba ta yi nasara ba, za ta yi suna sosai.Tattara jakarta ta yi, ta fita bayan da saƙon barrister Habib ya shiga wayarta.Ba ta wani sha wahala ba zuwa kotun da ya bata adress ɗin, tun da dama sananniyar magistrate court ce a kano.Ofishin rijistra ta je, suka gaisa da mutanen wurin, sannan ta tambayi office ɗin mutumin da barrister Habib ya gaya mata.Aka yi mata iso, sannan ta gabatarwa da mutumin kanta, da wanda ya turo ta.Ya karɓeta da mutuntawa sannan ya ce “Baiwar Allah, gaskiya ta in da ki ka biyo, babu yadda za ayi na kasa yi miki alfarma, amma riƙe file ɗin nan, tamkar saka hannu ne ki ɗaukko ƙarfen da yake cikin wuta ne, dan Allah kar ki je ki yi wani abu da bai kamata ba, tun kan ki zo aka yi waya, aka ce a baki idan kin zo”Nabila ta ce “In sha Allah, babu wani abu da zan yi, ina ɗan yi wani bincike ne kawai”.Ya ja ta suka tafi wani wuri a cikin kotun, suka shiga can wani office, da ba zaka ce akwai mutane a wurin ba, sai da suka shiga can ciki, suka iske wani mutum yana ta aiki a computer.Suka gaisa, wanda ya rakota ya ce “Oga, ga baƙuwa mun yi, Barrister Habib ne ya aikota, shi kuma daga top oga, ya ce a kawo ta file ɗin Al’amin viper zaka ɗaukko mata”Shiru mutumin yayi yana kallon ta sannan ya ce “Ya sunanki?””Nabila yusuf maitama””Me za ki yi da file ɗin?”Ta ɗan rausayar da kai ta ce “Wani bincike nake yi ne”Ya mayar da hankalin sa kan mutumin da ya rakota ya ce “Ka gaya mata illar da ke cikin hakan?””Na gaya mata, ko ma dai menene na gaya maka wanda ya ce a ba ta ai”Yayi ajiyar zuciya yana cigaba da yi wa Nabila kallon tuhuma, ya tashi ya shiga wani wuri.Ta kalli mutumin da ya rakota ta ce “Yallaɓai, meyasa file ɗin yake da hatsari har haka?”Yayi murmushi ya yi ƙasa da muryarsa ya ce “Yana da alaƙa da rashin gaskiya”Mutumin ya fito ɗauke da file ɗin, duk ya yi ƙura, hannu na rawa ta karɓa ta ja kujera ta zauna, ta fara dubawa.Sannu a hankali ta din ga bin bayanan ciki, da binciken rahoton ƴan sanda a kai, sai dai komai ba straight forward aka yi shi ba, gaba ɗaya kanta ya kulle, ba ta fuskanci wani abun kirki a ciki ba.”Amma sir, ina ƙarshen shari’ar, ai wannan ba a yanke hukunci ba, ranar ƙarshe da aka ɗaga shari’ar an ce sati uku za a sake zama, yanzu kusan shekara biyar, ba a sake rubuta komai ba”Mutumin ya ce “Eh yadda ki ka gani a haka yake”Cike da mamaki ta ce “Dan Allah wane alƙalin ne ya yi masa shari’ar?””Yana abuja” suka bata amsa a taƙaice.”Wannan documentation ɗin, sam ba a yi shi ma yadda za a fahimta ba, amma dan Allah….Wanda ya ɗauko mata File ɗin ya ce “Mu fa babu abun da za mu iya sake gaya miki, ba wanda yake da damar zuwa wurin nan sai staff ɗinmu, dan haka ki tashi ki tafi”.Ta miƙe tsaye ta ce “Na gode sosai”Ta fito daga office ɗin tana mamaki, ta ja ta tsaya tana kallon office ɗin, a abun da ta fuskanta wuri ne da ake ɓoye files na musamman.”Yayi kisan kai!” Ta faɗa a fili.”Ba abun mamaki bane ba, da gani zai aikata abun da ya fi kisan kai, amma menene dalilin ajiye shi shekara biyar, ba ayi masa shari’a ba, an ɓoye file ɗin sa a wuri na musamman, ya shekara biyar a prison, kuma kwatsam an sake shi, babu document na wanke shi aka yi daga laifin ko kuwa, duk da an rubuta ya amsa laifin, amma wane hukuncin aka yanke masa? Wayyo Allah kaina zai fashe” ta yi maganar tana dafe kanta, da ya yi mata nauyi.***A tsaye yake a kanta yana ƙare mata kallo, yanayin yadda take a kwance ya tabbatar masa da salla ta yi.Ruwan robar hannunsa ya fara zuba mata a Jikinta, hakan ya razanata ta tashi a gigice.Ya watsa mata sabulu da soso a jiki ya ce “Ki tashi ki je ki yi wanka, ba na son ƙazanta, kar ki haifar mini ɗa mai dauɗa”Ta yinƙura ta tashi da kyar, tana jiri, ga yunwa ga zazzaɓi ga kwana da ta yi amai, ta din ga bin bango, har ta isa banɗaki.Ta daɗe a banɗakin tana kuka, sannan ta yi wankan ta fito, ta tarar da shi a kan gado a zaune yana danna waya.Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “Dalla cire wannan kayan, ƙazamar banza da wofi, har amai ki ka yi a jikin kayan amma ki ka mayar da su jikinki” kallonsa take yi, to tsirara yake son ta zauna?Ya buɗe wardrobe ɗin da ke ɗakin, duk kayansa ne a ciki, ya jefa mata wata shirt, ya ce ta ɗauka ta saka.Banza ta yi masa, ta kawar da kanta gefe, wanda hakan ya hasala shi, yana zuwa gabanta ya kwasheta da mari, abunka da jiki babu ƙwari, take ta faɗi ƙasa, ta riƙe fuskarta.”Ke kin isa ina magana ki yi mini banza, ƴar wahala mara amfani, ɗauki ki saka kan na tattakaki”Ramma ba ta ƙaunar duk da abun da zai taɓa lafiyar jikinta, haka ta zura rigar nan, ta zo mata har gwiwa, sai rufe jikinta take yi.Ya danƙota, ya fita falo da ita.A falon ya haɗa mata baƙin shayi, sai soyayyen dankali da ketchup ya ce ta ci.Gaba ɗaya a tsorace take, saboda kar ya kuma dukanta, haka ta din ga tsakura tana ci tana hawaye.Ta gama ci, ya ɗaukko alluran zazzaɓi da yake yi mata yayi mata.Ta lura yana da mai aiki a gidan namiji, har girki da gyaran gidan shi ne yake yi masa su.Ya kashingiɗa yana kallon tv, ita kuma tana gefensa a ɗarare, sai mutsu-mustu take yi tana share hawaye.Sahidar yatsunsa ya gani kwance a fuskarta, har ya ɗaga ya basar ya cigaba da kallonsa yana kaɗa ƙafa.***”Allah ya taimaki maigida””Menene labari?””Na samu kiran waya ɗazu, wata yarinya ta je an kaita har ofishin secret files, an ɗaukko mata file ɗin viper ta duba””Wacece ita?””Yarinyar da ka ce ayi amfani da ita a kama Viper”Da sauri ya ce “What? Ya aka yi ta san da file ɗin ta je? Waye ya ce a bata?””Wallahi ban sani ba, amma an tabattar mini da ga sama su ma aka ba su umarnin ba ta””Sama ina, waye ya bayar da umarnin?””Ban sani ba wallahi, kuma da gaske lawyer ce, idan kuwa haka ne, za ta iya yiwuwa da gaske ta haɗu da Viper, ƴar jaridar nan raina mana hankali ta yi”Indabo ya numfasa ya ce “Kar ku yi gaggawa, kar ta san mu na bibiyarta, ka bi ta hannun ƙawarta, ku samo me take son samu a kansa, idan ta ƙi, ku kamata ku azabtar da ita”.Ya amsa da “Ok sir”.Daga kotun, gida arfa ta tafi, tun daga shigarta, Sauda ta fara tsokanarta da faɗa, amma ba ta ita take ba, ɗakinta tafi ta cigaba da tunani da lissafi.Kamar wadda aka zungura, ta ɗaukko wayarta ta kira Nasir.Murya ƙasa-ƙasa ya ce “Arfa ya dai? Mun shiga meeting ne”Kamar za ta yi kuka ta ce “Yaushe za ka dawo?””Zamu yi waya an jima, ki yi haƙuri””Kar ka kashe mana dan Allah, ni ina cikin damuwa magana nake son mu yi, wani abu zan baka”Ya ce “Wani abu me?””Abu ne mai muhimmanci a kan viper, amma sai ka yi mini alƙawarin ba zaka yi mini faɗa ba ko ka gayawa abba ba”Tattara nutsuwarsa ya yi ya ce “I hope, ba wata kasadar ki ka je ki ka aikata ba”Ta girgiza kai ta ce “Ba wata kasada da na yi, ni dai ka yi ka dawo, kan na mutu”A rikice ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, menene ki gaya mini””Ka kwantar da hankalinka, kawai dai ka yi ka dawo, abun yana da muhimmanci, na san yadda zaka same shi kai tsaye””Kin ga ba zan iya jira ba, gaya mini menene sai na aika su Mu’azzam, dama wanda aka kama ɗin nan ya ƙi magana””Sai ka dawo gaskiya” ta kashe wayar gaba ki ɗaya, dan kar ya biyo ta, ta sake dafe kanta.Sumayya na news room, tana jiran lokaci ya cika, ta gabatar aka turo ƙofar aka shigo. Sak tayi tana kallon mai shigowar.Mutumin da honorable ya saka ya karɓi wayarta ne, ranar da ta je gidansa.Ya ja kujera yana kallonta, ya ce “Ya dai, kin yi mamakin ganina ne? Mintuna goma sha biyar suka rage miki, kan ki fara karanta labaran, zaki yi mini aiki”.Ta zuba masa ido, amma ba ta ce uffan ba.”Meyasa ki ke yi mana ƙarya a aikinmu? Da gaske ƙawarki ta haɗu da Viper?”Cikin ɓacin rai Sumayya ta ce “Na gaji da amsa wannan tambayar, idan ba ku yadda da ni ba, ku nemeta ta amsa muku mana”Ya shafi sajensa ya ce “Zamu gani ai, yau ta je court ɗin da aka yi wa Viper shari’a, ta karɓi secret file ɗin sa ta duba, zaki kira ta, ki ji dalilin zuwan ta, da kuma abun da za ta yi da file ɗin”Sumayya ta girgiza kai ta ce “Nabila ba wani abu da za ta amfana muku, kawai na san ƴar rigima ce, so take ta yi suna ta ɗaukaka ta taimakawa yayanta shikenan”Yayi dariya ya ce “Za mu gani, daga yanzu zuwa azahar ɗin gobe, idan baki kawo rahoton dalilin bin diddigin shari’ar Viper da take yi ba, abun da ba kya zato zai faru” ya miƙe tsaye ya ce “lokaci ya cika, ki gabatar da aikinki”Sumayya ta dafe kai cikin matsananciyar damuwa, tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce.Murtala ne ya shigo yana faɗin “Afuwan sisyna, mamager ya kira ni ne, na saita komai ki fara”.”Ba ka ga mutumin da ya fita yanzu ba?”Ya kalli ƙofar ya ce “Ban ga kowa ba”Tayi ajiyar zuciya ta ce “Shikenan mu fara”.***Ƙaramar wayarta ce isheta da vibration a ƙasan pillow, ta ɗaga ta ce “Bacci fa nake ki ke ta kiran wayata”.”Haka dai, daga bacci sai kwalliya da cin abinci, ke har kin koma gida kin kwanta, ni tun 9 gani har 5 ban tashi ba”Nabila ta ce “Ke ba na samun bacci a ƴan kwankin nan wallahi””Meyasa?””Wallahi a tsorace nake, ba na iya bacci, gani nake kowane lokaci viper zai kashe ni, cewa yayi fa sai ya kashe ni, sonake Yaya ya dawo na danƙa masa wayar nan, na huta, wai da wayar wa ki ka kira ni ne?”Sumayya ta ce “Wayata ce ta ɗauke, ina ki ka je ne yau?””Wurin aiki mana, amma da labari sosai, mu haɗu gobe in Allah ya kaimu””Yakamata mu haɗu kam, dan na ga mutuniyarki bunkure, a gidan honorable Indabo”Daga kan gadon da Nabila take ta miƙe tsaye ta ce “Amma ba ki gaya mini ba sai yau?””Na san halinki ne, uzzura mini zaki yi, ke bari na tafi gida ma yi magana”Ta kashe wayar, ta kaiwa murtala wayarsa, dan ta fuskanci mutanen honorable na bibiyar kiran wayar da take yi.Wuni guda ramma ba ta sake saka Abdul a idonta ba, sai dai kukunsa idan ya kammala girki, ya ƙwanƙwasa mata ƙofa ya ajiye mata abinci.Tayi kuka har ta gaji, ta koma addu’a, tare da fatan Allah ya kuɓutar da ita daga sharrin zaluncin Abdul.Tana zaune a ƙasan carfet, har wurin sha biyu na dare, ya shigo yana kokawa da ƙofar ɗakin, saboda a buge yake.Ta tashi tsaye cikin tsoro, sai dai ba tare da ta yi masa laifin komai ba, ya hau ta duka, ya din ga ball da ita yana taka ta da ƙafarsa, tun tana kururwa har ta kasa sai ajiyar zuciya, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ba ta iya yi.Tamkar dabba haka ya afka mata, ba tare da la’akari da ƙarancin shekarunta ba, kodayeke ina tunani ga wanda hankalinsa ya gushe?.Bai farka ba sai kusan tara na safe, yayi miƙa ya tashi yana kallon ɗakin, da sauri ya kalli gadon bai ganta ba, ya kalli jikinsa, ya tashi yana mayar da kayansa, kawai ya ga jini a gefensa, har zuwa banɗaki, cikin hanzari ya nufi banɗakin, ƙofar tana buɗe dan haka ya shiga, ya tarar da ita a zaune ta jingina da jikin bath jini yana ta zuba daga jikinta, ga jikinta duk a kumbure saboda duka, idonta a rufe.Ya ƙarasa ya durƙusa ya ɗaga hannunta ya saki, ya ga ya koma babu alamar numfashi a tare da ita, rigarsa dake jikinta, tayi sharkaf da jini. Dafe kansa yayi yana tuna abun da ya faru jiya, kamar mafarki.
