Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 14 Complete Novel

  

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy     

 FOURTEEN📍

          Gudu take kamar zata tashi sama saika dauka titin nata ne dan yanda take driving kamar ita kadaice a hanyar….

Mamaki yake wani irin gudu me motarnan keyi,duk yanda yake tinanin yana gudu akan hanya sai yaga nashi wasa ne yau,shi bama wannan ba tafiya ake besan inda aka nufa ba,kuma shi baa tambayesa ina zaa kaisa ba,karfa yayi gudun gara ya fada rijiya?…. Gabansa ne yaji yayi mugun faduwa,a hankali kuma ya fara jin abinda yakeji duk sanda take guri,irin abinda yakeji yau sai yafi na ko yaushe ji yake kamar tana cikin jikinsa saboda yanda yakejin kusancinta dashi,gashi dai akan hanya suke kuma ba mota ko daya sai tasu,toh kodai ita ke driving?,juyawa yayi dan ya tabbatarwa zuciyarsa abinda yakeji,ko kafin ya karasa juyawa yaji komai ya tsaya masa chak!,be kuma kara sanin inda kansa yake ba!……..

Duk da irin gudun da take shekawa hankalinta nakan tukin sosai,saboda yanda take over speeding yasa bata bin hanyar da mutane kebi sosai koda it takes following a long way ne….. Daga sama,kamar wacce aka kwace steering a hannunta taji motar ta kwace mata,daganan bata kara sanin meya faru ba……

        Tinda aka kirata a waya aka sanar mata me wayar yayi accident kasancewarta last person data kirashi,gashi takira har sau uku,taji komai baya mata dadi,ta rasa Deen wani kalan yaro ne marajin magana,badan Allah yana karesa ba da yanzu ya dade da mutuwa,koda yake dole sai lokacin mutum yayi zai mutu,if she can recall ce mata yayi baya abuja,sai gashi an kirata tazo ‘Nisa Premier Hospital’ anyi accident dame wayar…… 

Tinda tazo hospital din take kuka ganin doctors din sunki cewa komai sai kai kawo kawai sukeyi,itama kasa zama tayi ta dinga zagaye gurin……

Tana cikin wannan halin call ya shigo wayarta,kallon screen din tayi,ganin me kiran yasa ta dauka da sauri tana fadin

       “Jamila na rasa meyasa Deen bayaji,kinganni a Nisa,kira kawai akayi wai sunyi accident shi da wata”

     “ Subhanallah! Accident kuma?,I hope it’s not fatal?”…. Jamila ta fada on the other side 

Fashewa da kuka tayi tace

      “I don’t even know,tinda nazo Doctors din basu ce komai ba,sun dai cemin I should calm down”….

      “Toh shidawa sukayi accident din,naji kince da wata?”

    “Haka naji fah,I was shocked,bansan wacece ba wallahi”…..

   “Oh Allah,to Allah ya tashi kafadunsu duka,harna tausaya musu wlh”….

     “Ameen” Ta fada jin tadan samun relief,dama ance ‘a problem shared is a problem solved’….

      “Ai banga ta zama ba,I’ll be on my way tomorrow Insha Allah”…..

      “ Toh Allah ya kaimu,tinda kin guji Nigeria,sai irin wannan dalilan ke kawo ki”….

     “Hmmm mubar zancennan pls,I’ll call you later”…. Jamila ta fada tana kashe wayar….. 

          Tsaye khaleel da sameer suke a gaban burnt building din fatima zainab,idan akwai abinda yafi shock toh khaleel yashiga,he couldn’t believe what his eyes just saw,like how can someone be this wicked?… Anya wasu suna tinanin kiyama kuwa?, Yanzu akwai wanda ze iya kona mutum dama?,shi besan tsanar da mama take yiwa abun sansa ya kai hakaba,gsky baze kyale ba dan in aka cigaba da tafiya a haka tabbas wataran saidai a kirasa ace masa fatima zainab ta mutu,so dole ya dau mataki……

Sameer ko sakin baki yayi yana kallon ikon Allah tinda shi besan komai ba,kallon khaleel yayi yace

     “Dude gobara akayi a part dinnan ne?”

      “Yes,not quite long”…

        “Innalillahi,I hope ba kowa a ciki?”……

Kamar ya fadamasa wa akaso konawa,sai kuma ya fasa yace 

          “Fortunately ba kowa a ciki!”….

         “Toh Alhamdulillah,Allah ya kiyaye gaba”….

         “Ameen,mu karasa part dina”….. 

Saida khaleel yayiwa sameer providing duk wani abu daze bukata sannan ya sake fitowa,so yake yaje ya ganta koya samu nitsuwa dan yasan bazata wuce part din momma ba,plus he needs to do something about mama…… Hango daddy yayi da shigowarsa kenan ya nufi part din fatima zainab ganin kamar gurin a kone yake…… Karasawa inda daddy yake yayi yashiga kallon building din kamar be gani ba dazun,shidai haryanzu ya kasa dena mamakin wannan abu….. 

Kurawa building din ido daddy yayi yana mamakin yanda abun ya faru,kuma a rasa wanda ze kirasa ya fadamasa,saidai kawai yazo ya gani?…. Kallon khaleel daya tsaya a gefensa yayi yana tinanin shikuma yaushe yazo?….. 

      “Son yaushe kazo?”… 

     “Not quite long!”…..

     “Kaga abinda ya faru ko?,Amma daughter bata ciki ko?”…. Daddy ya fada kamar khaleel a gidan yake da ze san meya faru

      “Yes abinda ya kawoni kenan,Abdul ne ya kirani yake fadamin,he overheard conversation din mama akan kona fatima zainab”….. 

Saida kirjin daddy ya buga duk da be kamata yayi mamaki ba tinda yasan yanda mama ta tsani fatima zainab,a rikice yace

       “I hope dai bata ciki?”….

       “It was confirmed that tana ciki,tambayi me gadi kaji,koda fire extinguishers sukazo suka kashe wutar sun tabbatar da komai na ciki is completely burnt,so ko gawarta an kasa ganewa,ta mutu a ciki”…. Khaleel ya fada da gangan duk da yasan bata ciki amma so yake ya ruda daddy yanda dole ya dau mataki akan mama,sai daga baya kuma yace bata mutu ba….. 

Zubewa a kasa daddy yayi ya daura hannu aka ya shiga salati kamar wani zararre,a gigice yace

      “Nashiga uku,kace ta mutu? Innalillahi wa ilaihi raji’un,nooooo!”…….

Gyada kai khaleel yayi alamun tabbatarwa dariya na cinsa a rai,in banda rudewa irin na daddy taya zaace fatima zainab ta rasu aganshi a tsaye kan kafafunsa?,ai kila ma da tini ya bita… Amma yaji dadi da daddy be kula da hakan ba,da alamu plan din shi will go well….. 

Mikewa daddy yayi a zabure cikin ihu yace

     “Ina hafsan take,nace ina take?,Wayyo Allah ta kashe yar mutane?”….. 

Sai kuma ya nufi gurin megadi da sauri be ko jira yaji abinda khaleel zece ba….. 

Da sauri khaleel ya nufi part din momma dan ya samu suyi magana da fatima zainab,ya kuma boyeta har sai plan dinshi ya tafi daidai,saidai me? Yana zuwa yaga be ganta ba,nan hankalinsa ya tashi yashiga duba ko ina….

Megadi daya dawo bayan komai ya lafa ya kwashe komai tass ya fadawa daddy,ya kuma tabbatar masa da tana cikin kuma ta kone(dan shi besan bata ciki ba)….

A hargitse daddy ya nufi part din mama,ko sallama beyi ba ya shiga bugun kofar ganinta a rufe kasancewar mama ta rufe dan gudun kar fatima zainab ta kara dawowa…. Da karfi ya cigaba da buga kofar yana fadin

    “Hafsah zoki bude kofarnan kafin na ballata”… Dan ganin kofar a rufe ya kara tabbatar masa da batada gaskiya…. 

Jin muryar daddy yasa mama ta fito tana dingishi ta nufi kofa dan su husna har lokacin basu budeba…

Bude kofarta yayi daidai dajin saukar wani kykkyawan mari a kuncinta da yariga yayi jahur dalilin marin da tasha a gurin fatima zainab…. 

Dagowa tayi da sauri murya na rawa tace

    “Alhaji lfy? Ni ka mara?” 

    “An mareki din munafuka,azzaluma,Allah ya isa tsakanina dake,kuma ki saurari sammaci daga court dan yanda kika kasheta toh kema sai an kashe ki wallahi!”….. Ya fada a hassale 

     “Wai wa kake magana a kai ne?,ni wa nakashe?”

Wani marin ya kara mata sannan yace

    “Au baki san wacce kika kashe ba,ki bari in kika ganki a gaban kotu sai ki musu bayanin yadda kika konata”…..

Take idan mama ya rena fata,cikin rawar baki tace 

    “Wlh bata mutu ba,bata kone ba,kuma……”

     “Karya kike azzaluma,an tabbatar min da ta mutu,kuma saina tabbatar da anbi mata hakkinta,wlh sai ankashe ki kamar yadda kika kasheta,ki saurari sammaci daga kotu”….. Yana fadin haka ya fita daga part din,ya nufi police station direct……..

          Tinda Doctor yace tazo office hankalinta yake a tashe,cike da zullumi ta zauna tana jiran abinda zece… Dan rubuce rubuce Doctor din yayi sannan yace “Matarsa ce ne?”

Kallonshi tayi alamun bata fahimcesa ba,tace

  “Bangane ba Doctor”

   “I mean patients din da sukayi accident,mata da miji ne?……

Rasa me zatace tayi,dan ita kanta bata sani ba,kuma a tantirancin Deen tsap sai ya iyayin aure baa sani ba,so kartace ba matarsa bace a samu matsala daga baya….. Gyada ma Doctor kai kawai tayi alamun eh matarsace….. 

      “Well Alhamdulillah zamuce akan su duka dan komai yazo bayanda muke tinani ba,amma akwai dan investigation da mukeyi akan ita matartasa,idan mungama we’ll let you know,meanwhile are you his mom?”…….

 Murmushi tayi jin ance komai yazo da sauki sannan tace 

     “Yes,zan iya ganinsu yanzu?”

     “Sure,let me lead you”…..

 Ya fada yana mikewa,bin Doctor din tayi har suka karasa dakin da aka kwantar dasu,nuni ya mata da tashiga ciki,shikuma ya koma office…….

Tinda tashiga takejin gabanta na faduwa,su biyu kadai ne a well furnished room din,kasa karasawa tayi ganin bugun zuciyarta ya tsananta,wani irin abu takeji da takasa fassarawa,hakan kuma tasan yanada nasaba da anxiety din data shiga,ga pressure din da Deen ke sawa rayuwarta……..

Karasawa tsakiyarsu tayi,saita rasa gurin wa zata fara zuwa,ta dade tana sake sake a ranta kafin ta samu courage din zuwa bed din Deen,kallonshi tashigayi hawaye na zuba daga idanuwanta,wannan wani kalan rayuwa ne,ka haifi mutum baka haifi halinsa ba?inba dan hannunka baya rubewa kayar ba da tini ta fita sabgar rayuwarsa?,shi kwata kwata be san ciwon kansa ba,bai damu da damuwar kowa ba,be damu da wani hali zesa mutane a ciki ba,shidai duk abinda ya raya masa shi yakeyi,kamar wanda aka chanja mata dan Deen dinta ba haka yake ba sam,lokaci daya rayuwarsa ta koma gefen hagu batareda wani dalili ba,yanzu gashi accident yayi wai da mace? Macen da basusan wacece ita ba,tasan dai akwai dalili dan Deen baze tabayin zina ba,inma tare suke zaune saidai in aurenta yayi…..

“Rabbis samawati wal ardi ka shiryamin shi”

Ta fada hawayenta na zuba akan fuskarsa…. Sai kuma ta janye ta nufi gadon da fatima zainab ke kwance…… 

Wani mugun tausayinta ne ya kama Deen dan tinda ta tsaya akansa ya farka,saidai yaki bude ido,be karajin tausayinta ba saida yaji hawayenta na zuba akan fuskarsa,shida kanshi ya rasa yanda zeyi da rayuwarsa,shi sam baya ganin rashin jin da yake su kuma sai su dinga masa kallon tantiri,Fisabilillahi meyayi toh?,ganin ta nufi inda fatima zainab take yasashi binta da ido,sai a lokacin yagane a gadon asibiti suke,toh kenan accident sukayi?,toh ina take?,kodai itace a kwance…. Daurewa yayi ya mike a hankali duk da bashida lfy amma baze iya hakura ba,dole shima yaje ya ganta….. 

Tinda ta karasa gaban gadon da fatima zainab take bugun zuciyarta ya tsananta,kasancewar an rufe mata rabin fuska ya sata yaye lullubin…. Sauran kadan ta zube a kasa da ganin fuskarta,Deen daya tawo ya tareta da sauri duk da bawani karfi yakeji sosai ba amma dayake yanada dauriya bazaka gane hakan ba,da sauri ta juyo ta kallesa tace 

    “WACECE ITA?”…. 

Be kulata ba dan besan meze ce mata ba,kawai ya karasa gaban bed din yayi yashiga binta da kallo……

Dafe kirjinsa yayi ya matsa gefe da sauri yana fadin

   “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel”…..

Ganin Deen be bata amsar tambayarta ba yasata fita da sauri,tana dialing number jamila,ringing uku Jamila ta dauka….. Baki na rawa tace

     “Ya hayyu ya kayyum jamila you wouldn’t believe what I saw,anya bamu shiga uku ba kuwa?”….

A kideme jamila tace

    “Ya allahu me kika gani,dan Allah fadamin yaya?”…..

I seriously don’t wanna announce this,but I just have to….. 

In kun kula zakuga I haven’t been updating regularly because I’m really busy trying to fix some essential school issues….. 

So,I’m officially taking a break now,ku bani 1 week,maximum 10 days,sai in dawo mu dora daga inda muka tsaya😁….. 

I would really appreciate your duas in ban takura ba☺️

Love you all😌❤️

Sai kun ji ni🤝

    Unique Barakancy!

Back to top button