Halysaah Page 178 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 178 Mami ta zauna gefen gadonta cikin yanayi na damuwa tana tunanin inda za su samo Yakumbo, don gaba daya Yakumbo ta bar masarautar tace bazata iya ci gaba da aiki ba ta koma garinsu, babu wanda zai ce ba ɗan da ta haifa ne ya bar duniya ba saboda irin halin da ta shiga, da farko ita ma rashin lafiya ta dinga yi a gidan kullum cikin kuka, daga baya kuma ta tattara tace bazata iya ci gaba da zaman masarauta ba, aka yi considering dinta aka barta ta tafi, Mami ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta dau kwayoyin da ta gani dakin Jay ta fita daga dakinta, fita tayi daga part din gaba daya, hoping zata samu ganin Sarki tunda zamansa a fada ya ragu sosai yanxu, cause his health is deteriorating day by day, har sannan he is not stable karfin hali kawai yake since he have to rule…. Jay na komawa ɓangarensa ya tarar da Hadiyah a parlor ta kwashe both breakfast da lunch da masu aiki suka ajiye masa ta kai kitchen ganin babu abinda ya taɓa a ciki, tana gyara parlon, ya tsaya yana kallonta yace “Ina maganin da kika dauka saman gadona?” Juyawa tayi ta kallesa, sai kuma ta girgiza kai tace “Ban shiga dakin ba” Ya tsaya for some seconds kafin ya karasa cikin bedroom dinsa, sosai ya sha jinin jikinsa don ya fara zargin Mami ta shigo dakin nasa. Aunty na zaune a second parlor din Sarki tayi tagumi tayi nisa cikin tunanin da take, Mami ta shigo parlon da sallama, Aunty ta gyara zamanta tana amsa sallaman sannan suka gaisa, Mami tace “Za a samu ganin Mai martaba yanxu kuwa Fulani?” Aunty ta kalli kofar dakin that is slightly open tace “Ina jin bacci yake yi, da yake bai ji dadi ba yau gaba daya” Mami tace “To Allah Ubangiji ya kara masa lafiya” Mami zata bar parlon taji muryar sarki yana mata izinin ta karaso cikin dakin, Aunty ta kalli kofar dakin da mamaki don tuntuni yace kar ta shigo masa bacci zai yi, ashe Idonsa biyu all this while, damuwar yanda baya son tana kasancewa kusa da shi ne yasa ta zauna parlon tayi tagumi, Mami ta karasa har Bedroom din Mai martaba ta shiga ciki da sallama, yana zaune edge din gado ya kunna wutan dakin don duk labulayen a sake suke kuma irin labulen da baya nuna hasken waje ne, Mai martaba yace ta tura kofar dakin, kulle kofar tayi akan idon Aunty dake zaune parlor tana kallon ikon Allah, sannan Mami ta zauna kan Carpet ta gaida Sarki tana yi masa ya jiki, yace “Alhamdulillah Fulani” Tace “Allah Ubangiji ya kara maka lafiya Mai martaba” Yace “Ameen” Tace “Dama magana na zo mu yi ranka shi dade, amma tunda jikin ba dadi yau, zan bari ka ji dama dama sannan sai in maka maganar in sha Allah” Mai martaba yace “A’a yi maganarki Fulani, kullum a haka ake ai, sai dai ace Alhamdulillah” Mami ta sauke ido tace “Haka ne ranka shi dade, Allah ya bamu ikon cin jarabawa” Ya gyada kai yace “Ameen” Ta ajiye masa satchets din magungunan hannunta ya dauka yana kallo yace “Wannan fa?” Ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “I saw this in Jawwad’s room daxu da na shiga, kwana biyu naga ya dena zuwa part dina don can ya koma yake kwana kwanaki, sai naga for weeks ya dena zuwa, kuma sai ya kai yamma bai shigo ba, yau sai naje har part din nasa, shi ne naga magungunan nan kan gadonsa shi kuma yana bandaki” Sarki na jujjuya magungunan yace “Na menene wannan din Fulani?” Mami ta kasa cewa komai at first, lokaci daya hawaye suka kawo idonta tace “Shi ne na dau hotonsu na tura ma Dr din dake duba Halysaah, sai take sanar min Hard drugs ne” Tana goge hawayen dake zuba idonta ta karasa maganar, Mai martaba yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, hard drugs Fulani?” Mami dai bata ce komai ba tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Sarki yayi shiru, nan da nan damuwa sosai ya bayyana a fuskarsa, after a while Mami tace “Jiddah kuma ta dawo, ko sani iyayenta basu yi ba ta biyo hanya babu kudin mota babu komai, ina bedroom ta shigo a galabaice yanxu” Nan ma Sarki ya kara lumshe ido ya bude yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Mami dai bata sake cewa komai ba, bayan kusan minti uku da shirun da Sarki yayi ya sauke ajiyar zuciya, ya fara magana with calmness yace “Fulani, don’t you think it’s best Jawwad ya auri Jiddah, may be they will get to move on by so doing” Mami ta daga kai tana kallon Mai martaba, wasu hawayen suka fara sauka idonta tace “Tun ba yanxu ba nake wannan tunanin Mai martaba, sai dai matsalan ina ga ba lallai Hajja tayi na’am ba saboda Hadiyah, kaga har yanxu bai maida Hadiyah ba….” Mai martaba yace “Zata amince, ni zan mata magana in sha Allah, wannan ne kadai mafita for their sanity both” Mami tace “To Allah ya sa Hajjan ta amince, don nima zan yi farin ciki da haka” Mai martaba ya dau wayarsa yace “Bari in kira Jawwad din” Mami tace “Ai kamar wayarsa a kashe yake in dai ba yanxu ya kunna ba” Sarki yayi dialing numbersa, yana fara ring Jay ya daga, Mai martaba yace “Ka taho Bedroom dina ka sameni yanxu Jawwad” Daga haka ya katse wayar, not too long after sai ga Jay ya bude kofar dakin da sallama, yana ganin Mami a dakin sai da gabansa ya fadi sosai, ya karasa cikin dakin ya tafi har gaban Mai martaba ya zauna a kasan carpet kusa da Feet dinsa cikin sanyin murya ya gaishesa, Sarki dai kallonsa kawai yake, sai kuma ya kauda Idonsa don duk sanda yaga Jay sai ciwon rashin Ajay ya dawo masa sabo a zuciya, kullum a haka yake a masarautar sai in bai ga Jay ba, Satchet din drugs din sarki ya nuna masa calmly yace “Meye wannan Jawwad?” Jay ya dinga kallonsu babu ko kiftawa, lokaci daya ya sunkuyar da kansa ya kasa cewa komai, Mai martaba yace “Hard Drugs Jawwad? Since when did this start?” Jay ya kasa cewa komai, sai kuma ya daura fuskarsa a kan Knee din Mai martaba idanuwansa suka ciko da hawaye trying not to breakdown amma muryarsa na rawa yace “Bana iya bacci ne Abba, i keep on hallucinating each night, during the day kuma i can’t think straight….” Yana magana ne hawaye na zuba idonsa zuwa knee din Mai martaba, Mami ta dauke kanta jin nata hawayen sun fara zuba, Mai martaba ya kasa cewa komai, dama Mami na gaya masa Hard Drugs ne yasan dalilin da zai sa ya dinga sha don ba halinsa bane, After a while Mai martaba ya dake yace “If all this is happening to you Jawwad me yasa baza ka tsananta Ibadarka ba ka nemi mafita wajen Ubangiji? You think taking this harmful drugs is the way out for you Jawwad?” Da kyar Jay yace “Wallahi ina addu’a Abba, kullum ina yi” Sarki yayi shiru, sai kuma ya kwantar da murya yace “Jay ina tunanin hadaka aure da Jiddah, nasan ta haka in sha Allah za ku yi move on da kai da ita” Lokaci daya Jay ya daga kai yana kallon Mai martaba babu ko kiftawa, sai kuma ya fara girgiza kai da kyar cikin rawan murya yace “This will be the least thing I will do on planet earth Abba, ta yaya zan auri matar Junaid? Ta ya zan auri matar ɗan uwana? Wallahi bazan taɓa yin haka ba no matter what” Mai martaba have to gather enough courage kafin ya iya cewa “Ina Junaid din yau?” shi kansa da ya fada hakan sai da idanuwansa suka sauya kala, Jay ya rufe fuskarsa a kafar Mai martaba hawaye na zuba idonsa yana girgiza kai cikin rawan murya yace “Ko baya nan bazan taɓa aurenta ba Abba, Wallahil Azeem bazan iya aurenta ba, babu aure tsakanina da ita har abada, da ace yana nan yau ni me bar masa duk ma abinda na mallaka ne ko da goman Halysaah yace yana so kuma ina da, to zan bar masa ne har abada, don Allah ka gafarceni ranka shi dade kayi min rai kar ka min wannan maganar kuma it will make me loose my mind, instead na yarda zan maida Hadiyah ko yanxu aka ce in maidata zan maidata, Amma babu aure tsakanina da matar da Junaid ya aura till the end of life” Mai martaba ya juya ya kalli Mami dake hawaye, after some seconds yayi patting bayansa gently yace “Shikenan in sha Allah babu wannan maganar kuma Jawwad, amma kai Musulmi ne idan baka sa ma ranka dangana har yanxu ba sai yaushe kenan zaka yi haka? I want you to come back to ur normal life ka ci gaba da aikinka da duk wani abu da kake yi Jawwad, ta haka ne zan kara samun kwanciyar hankali amma shirun nan naka da damuwar da kake ciki for this long is also destabilizing me, ina son ka ci gaba da zuwa wajen aikin ka, ka ci gaba da harkokin rayuwarka, with or without Ajay life have to move on” Jay bai ce komai ba hawaye masu zafi na zuba idonsa, yasan bazai taɓa move on without Ajay ba, it will going to take him forever to heal, sai yanxu yasan cewar Ajay was always part of him, shi din wani bangare ne na jikinsa da bai sani ba sai yanxu, Mai martaba yace “Ka tashi kaje ka kwaso min duk sauran abubuwan da kake sha” Babu musu Jawwad ya mike yana share idonsa ya nufi kofa, Mami ta bi sa da kallo har ya fita. Gradually Khaleesat ta fara loosing all hope after waiting and waiting with no sign of Ajay, amma duk sanda taji she is loosing hope sai tayi maza tayi renewing hope din nata da kanta, har yau taki yarda her husband is gone, she believe he is alive and will come back soon, a yanxu kukanta ya karu a kan na da, damuwarta ya karu, rashin baccinta ya karu, gashin kanta kuwa duk ya lalace kamar bata taɓa gashi har gadon baya ba, she is always looking pale and not healthy, duk wani halin da take ciki tun bayan da taji mijinta is late ya ninku kan na da, kullum da safe sai ta bada labarin abinda Ajay yace mata a mafarki don ko baccin minti goma tayi sai tayi mafarkinsa, tana tashi zata ba likitan ta labari, har Mai martaba ta sha zuwa har parlonsa ta gaya masa abinda Ajay yace ta gaya masa a mafarki, ko gaisuwa ko kuma ya kusa dawowa, a haka kuma Sarki zai biyeta cike da tausayinta, ana zaune kawai haka zata tattara duk wasu kananun kayansa da suke a wanke ta kara wankesu sannan ta linke ta mayar masa cikin press, dakinsa ma haka zata gyara duk ta fesa turarensa in every angle, likitan ta sai dai tayi ta kallon ikon Allah, lokaci daya Khaleesat ta fara fama da matsanancin ciwon kirji, gashi baya tasar mata sai cikin dare, Dr dinta ta fara tunanin Ulcer ne ya kamata saboda bata cin abincin kirki, ita dai a duk shekarun aikinta na likitanci tayi attending to cases iri iri amma bata ci karo da irin na Khaleesat ba, almost 2 years amma abunta sai gaba yake yi, gashi in tana baka labarin abinda Ajay yace mata a mafarki zaka ga with seriousness take bayarwa har cikin ranta, har alkawari ta sa Khaleesat ta daukar mata na cewa zata rage damuwa tunda Ajay yace mata zai dawo, haka zata yi ta biyeta duk don ta dawo mutum amma sai ta dau alkawarin kwana biyu sai abu ya dawo sabo fil ta karya alkawarin, likitan ta dinga jin Khaleesat kamar kanwarta don halin da take ciki ita kanta yana damunta cause she is too young for this kind of cruel pain, she watch her everyday struggling to eat, struggling to sleep, struggling to do everything whereas kowa lafiya yake duk abubuwan nan da take struggling tayi, sai taji ina ma zata iya dawo mata da farin cikinta ta dawo yanda take a da…. Sai a yanxu Khaleesat ta fara nuna jin haushin Jay da take yi a zuciyarta, tana ganin ya tafi shi ya dawo amma bai dawo mata da Ajay ba, bai yi protecting mata shi ba he only protected himself on that very day, ko ganinsa tayi sai ta tashi ta bar wajen ta fara kuka, ta dawo abun tausayi a gidan sarauta, kowa tausayinta yake gashi taki zaman gidansu a Kano, sau uku in an kai ta take dawowa Bauchi, don har gwara zaman da take a masarauta wani lkcin zaka ganta tana hira da Likitanta ko Mami ko Hajja kamar ba ita ba har da dariyar ta sosai, har da su Kilishi da Hajiya A’isha hira take yi tana basu labarin Ajay ko mafarkin da tayi, to a cikin hiran ne zata fashe maka da kuka just like that kamar warce aka tsikara, ko kuma in tana dariya ya rikide ya koma kuka, a Kano kuwa rasa gane kanta ma ake yi gaba daya, ya kai ya kawo an fara ganin abun nata is not normal anymore, still Sarki yasa aka kara kai ta asibitin ƙwaƙwalwa har kasar waje amma babu sign din ko wani ciwon ƙwaƙwalwa tare da ita, Mai martaba ya nemi a bar ta a Masarauta ana ci gaba da yi mata Therapy har zuwa sanda zata dawo normal tayi move on tunda da lafiyarta aka rabota da gidansu don haka bazai yiwu ta koma gida cikin wannan halin ba, Dr din da take kula da ita daban wanda yake mata Therapy daban, Nenne kuwa duk kauyen da taji ana bada taimako haka zata shirya duk nisan sa taje nema ma jikarta taimako, tun Umma na boye damuwarta har sai da ya fito sarari, tana son masarauta su sakar mata erta ta dawo gida ta rungumi abarta amma ana jin nauyin gaya ma Sarki haka, don da sun bada ita ma Nijar tayi niyyar tafiya da ita yanda zata yi nisa da Nigeria din gaba daya, ana haka aka yi diagnosing Khaleesat da mild ciwon zuciya, jikin likitan ta yayi sanyi sosai, ita da take tunanin Ulcer ce ashe Heartache ne, hankalin kowa ya tashi a masarauta, ba a ma san ta yanda za a fara gaya ma iyayenta ba, Jay was very very worried don shi ne ma ya daurata kan medications, wannan dalili yasa zamansu ita da likitanta ya fi yawa yanxu a babban lambun Masarauta, saboda ta dinga samun access da nature’s view and greenery, haka nan za su wuni da likitanta a lambun wani lokacin sai su kai har Magrib a nan, time to time Jay kan shigo lambun dubata, tana ganinsa sau tari sai ta juya baya ta fara kuka, wani lokacin ya karasa har inda suke wani lokacin kawai ya juya ya fice daga garden din cause he can’t stand her cry, it’s making him emotional too……Abinsi Benue state riverine area….Wata yarinya ce da bazata wuce shekaru ashirin ba durkushe gaban murhu tana ta fifita wutan murhun, komawa tayi ta zauna kan kujera karama tana jiran dahuwar abinda ta daura kan wuta, daga gefenta kuma wata matashiya ce dake ta weaving din tabarma da kaba ita ma daure da zani, bayan wani lokaci yarinyar ta bude tukunyar dake kan murhun ta juye tulin manyan kifin da aka yi ma farfesu yana ta tafarfasa a clay bowl babba dake gefenta, ta mike ta gyara daurin zaninta tana yi ma matashiyar matar dake zaune magana da Yarensu na Jukun Wanu, warce da alama mahaifiyarta ce, dukawa tayi ta dau bowl din kifin dake ta tafarfasa a clay bowl din ta nufi wani thatched roof hut, ta duka ta shiga cikin dakin sannan ta durkusa ta ajiye bowl din hannunta tana kallonsa, yana zaune kan tabarma a hut din ya jingina jikin ginin kasan, tayi masa alama da hannu cewar tana zuwa ta dauko masa ruwan da zai wanke hannu, ya gyada mata kai, mikewa tayi ta fita daga hut din, tana fita waje da yarensu take gaya ma uwarta ya tashi zaune, uwar ta ajiye kaban hannunta sannan ta mike ta shiga bukkan ita ma, murmushi tayi da jagulallen Hausanta take ce masa sannu fa, ya gyada mata kai yana mayar mata da murmushin ta juya ta fita daga Bukkan, yarinyar ta koma ciki da ruwan wanke hannu da kwaryan palm wine, ta ajiye ruwan wanke hannun da Palm wine din a kusa da shi, hannunsa ya hade waje daya alamar godiya, tayi murmushi kawai, ya wanke hannunsa cikin ruwan da ta kawo, sannan yayi mata alamar ta tafi da Palm wine din bazai sha ba yana girgiza mata kai, daukar kwaryan palm wine din tayi ta fita, ya kalli kifin dake ta tiriri ya kai hannu ciki ya yanki kadan ya kai baki ya fara ci a hankali……
