Hausa novels

Zakuna Biyar Page 18 By Princess Teema

Lion bai yi magana ba for almost 5 mins, sannan yai masu dropping messages na bayanai a computers ɗinsu. Sun san bayayin dogon magana, dikkansu basa tsawaita magana, amma na Lion and guru is worst, magana ta minti ɗaya ba zasu iya yin bayani ba, sun gwammaci zaman typing su tura ba magana ba, shi Champion idan ta kama yana daurewa ya yi magana har na mintuna biyu.Already sun saba dama dik abin da suka tambaya a rubuce yake turo masu amsa, suma a rubuce suke tura tambaya, sai basu wani damu ba, a natse suka buɗe message ɗin kamar haka. “Kun taɓa ganin yadda ƴan ta’adda suke fitowa dan kansu kawai ne? Ƴan ta’adda! Wasu jama’a ce da ake kirkirarsu musamman dan a fitinawa al’umma, kun taɓa tambayar kanku ina iyaye da ƴan uwan waɗan nan ƴan ta’adda? Kun taɓa tambayar kanku meyasa ƴan ta’adda suke da horo kan sanin makamai tamkar yadda sojoji suka sani? Za’ayi musayan wuta da ƴan ta’adda da sojoji, idan bullet ɗinsu ya kare a ƙasa da minti ɗaya suke sake sanya bullets a bindigunsu tamkar yadda aka horar da sojoji sanya bullets a bindingu cikin gaggawa, kun taɓa tambayar kanku ya aka yi suka iya dikka wannan? Ko dai a kullum kuna rigingimu tsakaninku da ƴan uwan da kuke tare da su cewa sune ke kasheku?”.Wani dogon note ya sake tura masu kamar haka a kasan wannan. “Terrorists! Kalma ce wacce aka kirkira, ƴar ta’addan dake Avaris waɗan da ake ta ikirarin sun addabi al’umma dikkansu kauyawa ne, dakikai ne da basu taɓa shiga class ba, ya aka yi suka iya karatun sanin makamai karatun da ya fi kowanne wahala? Sanin ita kanta bindiga ba karamin wahala bace, ya aka yi suka san dikka wannan? Ya aka yi suke da bindigun da suka fi na sojijin Avaris karfi da sabonta? Ta ina suke samo makamai masu karfi da kayan aiki tamkar jami’ai? Sun fi wasu jami’an ma kayan aiki in gantattu! Why?” Amsa, a bayan kowani ɗan ta’adda ko ɓarawon daji akwai manyan dake bashi umarni kuma dake koya mashi aikin ta’addanci, ƙalilan ne daga cikin ƴan ta’addan suka fito daga kasar Avaris ɗin, kalilan ɗin kuma jahilan ciki aka kwasa game da yi masu karya da sunan jahadi suke yi wa musulunci, da rashin iliminsu aka yi amfani wajen sanyasu aikata abin da suke yi! Amma ainahin ƴan ta’addan idanu baya ganinsu, mutane ne da aka kirkiresu, tsawon shekaru aka horasu, mutane ne da basu da wani dangi bare su san daɗi dangi har su ji tausayi, basu da iyaye, su kawai an kirkiresu ne saboda taaddaci da kashewa, shiyasa ba zasu ji tausayin kowa ba, ba zaku taɓa gane kan wannan rigima a yanzu ba, sai bincike ya natsa damu cikin WORLD SYSTEM komai ya yi nisa zaku gane mecece ainahin ta’addanci, su waye ainahin ƴan ta’addan da ake dangatawa da musulmai alhalin basu ma da addini kwata-kwata, dik wanda yake matsayin member na wannan taaddancin bashi da addini wlh! Ko kiristoci na kwarai basa kisa haka ɗai, saboda sun karanta Annabi Isa ya haramta!. Tin da suka gama karantawa suka natsu tsit suna nazartar kalaman Lion, dik abin da ya faɗa gaskiya ce, ba yadda za’ayi ace rana tsaka ƴan ta’adda su bayyana a waje, su kori jama’a a kauyuka su kwacesa su zauna, lallai tsawon shekaru ake ɗauka wajen horasu a kan hakan, tamkar yadda ake hora sojoji, idan an gama horasu sai su bayyana, ba ƴan ƙasar Avaris bane, bakin haure ne, wlh ainahin ƴan ta’addan ba ƴan kasar bane! Suna amfani da ƴan ƙasar ƙalilan daga cikin jahilan da sukaki karatu ne, sai su fake a bayansu suna taddancin, ƴan kasan da ake yi wa kallon ƴan ta’adda lallai karnukan farautar jiga-jigan dake laɓe a bayansu ne, manyan basu fitowa fili su yi aiki kai tsaye ne saboda gudun aga banbancin launin fata da sauyin harshe, shiyasa suna gefe suna koyawa karnukan farautar tasu ɓarna, ban da haka dakikin da bai je makaranta ba yaushe yake iya magana da correct English? Baku taɓa jin ƴan ta’addan suna turanci ba ko? To iyayen gidansu dake koya masu harbi da bindiga da sauransu turanci kawai suka iya! Dole su koyi turanci na magana yau da kullum.(Can naga wani ɗan ta’adda a media yana video yana cewa we have a lot of informance everywhere, I said eyeee this guy hear English well-well, he pass me da na yi FGC makarantar da ba’a magana da kowacce yare a cikinta sai turanci, ashe ni dik shirme na iya, ga wani a kwana can ya kware ba tare da zaman class ba. ALLAH kai mana kyakkyawan karshe, ba lallai a yanzu ku gane in da na dosa ba, saboda tushe nake son ɗauko maku, but keep reading, zaku gane sosai a gaba!)Nazarta kalaman Lion for almost 10 mins suka yi, sannan Champion ya hau typing kamar haka. All what you said is true, but ƴan kasar ba zasu taɓa fahimta ba, everything is damage now.Typing amsa Lion ya yi da cewa. Shiyasa aka shirya masu rikicin addini, rikicin akida da rikicin ƙabilanci dik dan kada a bar hankalinsu ya natsu waje guda har su iya fahimtar gaskiya, kasan ƴan kasar Avaris ba dai ƙwaƙwalwa ba, ko dame kake ji sun bugeka a kaifin tinani da basira, shiyasa ba za’a barsu su natsu har su yi tinani ba dan an san confirm sai sun gane gaskiya, wannan dalilin yasa rayuwarsu aka mayar da shi tamkar season film, kowani sati da sabon season da za’a shiga masu, a kowacce rana da kalar episode da ake buɗe masu suna kallah, an rikita tunaninsu, idan zasu aikata laifi ma baka ga sai sun kawarwa da ƴan kasar hankali sun basu abin da zai ɗauke masu hankali daga kan kasar ba? Saboda sun san ƴan baiwa ne a kasar, in basu ɗauke masu hankali ba lallai ganosu zasu yi. Two days ago ba an je an yi kidnapping wasu mutane a kauyuka ba? Aka yi districting na hankulan mutane, dik suka koma magana a kan wannan case na satar mutanen da aka yi, a wannan lokacin ne suka shigo da sabbin ƴan ta’adda cikin ƙasar, bayan sun shigo dasu ne kuma al’ummar ƙasar nata faman koke kan ɗauke masu mutane da aka yi, shi ne suka fito da batun bayyanar sabon ƙungiyar ƴan ta’adda sai ya ɗaukewa al’umma hankali daga kan ƴan uwansu da aka sace, suka koma batu kan ƴan ta’adda, nan da gobe ko jibi zasu sake fito da wani sabon season ɗin dan su rufe bakin mutane a kan sabbin ƴan ta’addan nan, jama’a su koma tattaunawa a kan sabon season da za’a sake masu, shikenan tsohon season zancensa ya bi iska.Are you thinking what I’m thinking kuwa my people?.Guru ne ya ce. “Exactly abin da ka faɗa, amma kai a tinaninka meyasa Avaris ta tura su Leo Mission na farko a kan tsofaffin kungiyar ƴan ta’addan da suka jima a harkar?”………. A wannan karon da baki Lion ya amsa masu da cewa. “Kwarewarsu Nirash suke son gani, kowani jami’i AZURE ta yaye sai sun turashi aiki wani waje domin su gwada iya kaifin basira da kwazonsa, dan su san in da yakamata su ajiye shi”. Champion ya karɓa da cewa. “Suna tinanin su Leo ba zasu iya mission a kan waɗan can gogaggun ƴan ta’addan bane, saboda suna tinanin su ba ƴan kasar Avaris bane, so da wuya idan suna da kaifin ƙwaƙwalwa”…….. Guru ne ya amsa da cewa. “Ai sun yi kuskure in kuwa haka ne, domin kuwa Nirash ai ba renon AZURE kai tsaye bane ma, su karisar mana da aiki suka yi, ko GAT ɗinsu da kansa Nirash zai iya koya mashi aiki a yanzu”.Ni kuma na karisa masu da cewa bugu da kari daga Nirash har Vash ɗin jinin Avaris na gudana a jikinsu ta ɓangare mai karfi! Dan haka kowa sai ya jira!. ALLAH ka bamu irin IRON FIST a duniya, dan ba zan ce a ƙasarmu kawai bama, a ko’ina akwai musulmai, dan haka ALLAH ya bamu ire-irensu ta ko’ina su ci mana uban azzalumai!!.Lion ne ya ce. “Kada ku taɓa sanya hannu a mission na su Nirash, let them fight, ban yarda ku bibiyi abin da suke yi bama, kamar yadda muka fafata muka kwaci kanmu har muka zama abin da muka zama yau, suma haka zasu fafata”…….. Lion yasan halin Champion sarai, wlh Aryan yana mugun son Leo fiye da yadda kuke zato, ba dan blood is thicker than water ba da na ce ya ma fi Lion son Leo, shiyasa ya taka masu birki, dan yasan tsab Champion zai tsaya masu, karamin aikinsa ne, shi kuma Lion yana son su wahala, su gwabza, su zama mazan gaske masu kwatar kansu kamar dai IRON FIST ɗin!!.Cigaba da tattaunawa suka yi, daga karshe suka yanke shawarar da kansu zasu mayar da Nirash and Vash jibi, suna da buƙatar kaiwa Avaris ziyara, su ɗan yi yawo a cikinta na kwana biyu kafin su dawo, dan aikinsu ma ta cigaba masu. A kan wannan matsaya suka tsaya, daga nan suka tashi wannan zama.Lion da kansa ta ɗauki zafi wanka ya yi ya kwanta, a cikin 24h bawan ALLAHN nan ya samo waɗan can bayanai a kan WORLD SYSTEM, kunga kuwa dole kansa ta yi ciwo, shi kuma guru wasu drugs ya ɗebo a drawer ya watsa a baki ya bi da ruwa bayan ya yi wanka kenan, sai ya koma kan computers dan ya zurfafa bincike kan mission nasu Leo, shi hankalinsa bai kwanta a kan irin mission da aka basu ba, jami’an baya da AZURE ta yaye guru ya fara dubawa, duk waɗan da aka yaye babu waɗan da aka baiwa mission mai wahalar nasu Leo, to meyasa?. Ga shi gwamnatin Avaris ke shirya wannan mission ɗin, daga hannun Minister tsaro na ƙasa takardan yake fitowa.Shi kuwa Champion wajen Seraphina ya koma, irin wannan dalilin ne yasa Lion ya tsani mata su shigo cikin al’amurransu, da ace a baya ne suka yi irin wannan zama da yanzu Champion yana gaban computer yana kara zurfafa bincike, amma kunga yanzu ya tafi wajen Seraphina ba tare da ya sake bi ta kan case ɗin ba. ———————–🔥Turesa V ta sake yi da karfi tana sanya mashi kukan cewa da zafi, ba zata iya jura ba, take ta fara kuka hawaye bibbiyu, hakan ba karamin ɗaga mashi hankali ya yi ba, da sauri ya kwanto jikinta ya rungumeta, rarrashinta ya fara yi yana faɗin ta daina kuka ya fasa yi.A ransa ba wai ya fasa bane, yanzu ne dai zai kyaleta, amma he promised him self da zai bata maganin da zai sa ta fita hayyacinta ta yadda ba zata ji zafi ba, gobe sai su yi. Da haka ya daure ya kyaleta tare da rungumeta yana wasanni da sassan jikinta har barci ya ɗauketa ita.Shi kuma ya zareta daga jikinsa a hankali, toilet ya fara shiga, sai da ya yi wanka sannan ya fito sanye da bathrobe ya nufi wajen daddynsa, amma sai da ya gyara mata kwanciya ya rufeta da bargo. Tsaye ya isko daddynsa yana waya, a gefen bed ya zauna tare da zubawa daddyn nasa idanu. Sai da ya kammala wayar, waya ce dama da kamfaninsu kan kayar da za’a fitar zuwa ga abokan cinikayya. A kusa da Noor ya zauna tare da jawosa jikinsa yana tambayarsa ya aka yi ne. Kwamciya a jikin daddyn nasa ya yi, a shagwaɓe ya faɗa mashi dik abin da ya aikata.A tinaninku daddy zai mashi faɗa ko? To ku dawo tunaninku, ba musulmai suke ba. Cike da farinciki daddy ya ɗago haɓarsa, yana murmushi ya ce ɗansa ya girma ya kuma zama jarumi, har da ce mashi ya gwada jarumtarsa kada ya zama rago, a zuwan farko ya sama masu babys maza, wai kun san yadda daddy yake ji da Noor kuwa? Ai kwarara mashi gwiwa ya yi tamkar abin arziki zai aikata.Kamar Noor zai yi kuka ya faɗawa daddy ai V ta ce da zafi ya ɗaga mata kafa, kuma shi yanzu yana buƙatar mace. Nan fa daddy ya faɗa mashi ya kara kokari, tamkar shi ne mahaifin V har da ce mashi gobe ya saya mata zoben aure shikenan ta zama matarsa, daga nan daddy ya ce bari ya je ya ganta, yana son sanin wacece daga cikin su huɗun. A takaice dai daddy ya baiwa Noor goyon baya ɗari bisa ɗari.Da sauri Noor ya riko daddy, yana ɗan turo baki ya ce. “Daddy ka bari sai da safe ka ganta, yanzu ta yi barci kuma bata da kaya a jikinta”……. Fasa zuwa ya yi, ya zauna suka cigaba da hira har dare ya tsala. Sai can ya miƙe ya koma room ɗinsa, saman bed ya haye, a kusa da ita ya kwanta tare da kara ja masu bargo, bai sake taɓata ba saboda kada ya shiga cikin wani hali.Less short the story. Washegari daddy ya sai zoben zinari wa Aunty Lisa, ya sanya mata, suka yi da daddy Noor kan cewa after tafiyar su Noor Mission za’ayi party ɗin bikinsa da Aunty Lisa, kun san su suna iya yin aure da shekara uku ma kafin ayi party, to shi abin da yasa ba za’ayi shagali yanzu ba yana da gagarumin aiki a gabansa na wannan mission da su Noor za su tafi, kuma su sojoji kun san aurensu yana da lokacin, sannan abu ne da ake ɓoye shi, ba’a cike shelanta aurensu ba, dayawansu auren sirri suke yi, musamman manyansu, dan haka daddy GAT ya ce ko za’ayi party guda ɗaya za’ayi, kuma a nan US za’ayi ba’a Avaris ba, dan a yanzu ma baya son Avaris tasan ya yi aure, sai gaba.GAT bashi da ishasshen lokacin ɓatawa a US, dama kwana ɗaya yake da niyar yi, saboda tafiyar su Noor, dan haka da safe suka shirya komai da daddy Noor ya ɗauki yaransa suka wuce airport da Aunty Lisa. A lokacin da za su tafi Noor sun rakasu har airport shi da daddy and Aunty Lusi, Aunty Luna bata je ba, tana da meeting mai muhimmanci so ta tafi attending. A gefe guda da suka je airport sai satar kallon juna Noor and V suke yi, ko kaɗan Noor bai damu dan basu yi abin da ya so su yi jiya ba, dan yasan barrack ɗaya suke ai, kuma shi ma gobe zai koma. Daddy Noor kuma sai albarka yake sanyawa V har ta gagara hakuri sai da ta yi wa Noor message a kan ya faɗa mata me ya faɗawa daddynsa da ya kara sonta sosai har haka? Meyasa yake sanya mata albarka.Sai bayan sun dawo gida ya duba wayansa ya ga saƙonta, one side smiling ya saki kafin ya rubuta mata reply kamar haka, na faɗawa daddy abin da muka yi daren jiya ne shiyasa ya kara sonki, ya ji zaki haifa mashi jika da wuri……. Da jin haka sai ta ji ta yi danasanin hana Noor kanta da ta yi, dan yadda daddy ya damu yake son jika gaskiya bata kyauta ba da ta zama bata bari sun kama hanya ba, amma da ta tuna ai Noor zai dawo gobe, suna da lokaci a tare, sai kawai ta ji daɗi.In kara takaice maku labarin nan after one day su Noor dik suka yi wa AZURE diran mikiya, a rana guda dik suka dawo saboda basa wasa da lokaci. Harta Zaynish ya dawo, amma fa kafin ya dawo sai da ya saita gidan Ummie, tin daga kan uwar mijinta, uban mijin nata, wannan shegiyar Auntyn nasu, gabaɗaya kannen mijinta tattarasu ya yi, ya basu capital warning, ya ce masu wlh a kan Ummie ba irin hukuncin da ba zai masu ba, zai iya sanya bindiga ya harbe mutum kuma ya harbe banza! Shi ba sojan Nigeria bane a yanzu, karkashin ikon gwamnatin AVARIS yake! Yakamata su san wannan, dan haka su shiga hankalinsu. Ko da zai dawo kuma bai bari Ummie ta sanar masu cewa ya koma ba, ya ce mata kada ta gwada masu ya koma, dan zasu iya cigaba da yi mata iskanci, yanzu dai biyayya sama da ƙasa ake yi mata, har amarya da aka sha jinya aka dawo, yanzu zaman lafiya take da Ummie, ai dik wanda ya sha dukan soja so ɗaya ko a mafarki ba zai so ya sake haɗa hanya dashi bama bare duka, mutanen da in suka mareka sai ka ji kamar ba’a duniya kake ba, kunnenka ya daina jiyo sautin komai, dole amarya ta natsu. Yanzu dai Ummie ta samu saukinsu sosai, kannen mijinta mata Aunty sama Aunty ƙasa, marasa kunyar karya, ai komai waje yake samu, yanzu dai dik sun haɗa malaman jikinsu, wata mara kunyar kaunar Faisal ɗin ma wai son Zaynish take yi, ta tattaro kayanta dik ta dawo wajen Ummie, sai ladabi da biyayya take yi mata, har aiki dik ita take yi mata, burinta kawai ta dinga ganin Zaysh da har ya gama zamansa a gidan bai taɓa ɗaga ido ya kalleta ba, magana wannan baya yi wa mutane kuma baya amsa nasu idan sun yi mashi, idan kun ji Zaysh yana magana to da Ummie ne, bayan ita sai Faisal da suke waya, idan ba su ba sannu baya haɗa shi da kowa.Da Ummie tai mashi maganar aure zai ce ta zaɓa mashi mata kowacece in dai ita ta zaɓa mashi zai aureta. To kannen Faisal sun ji haka shiyasa suka makalewa Ummie dan ta zaɓawa Zaysh su, suka kirkiro halin kirki na karya, ladabi tamkar kaza a cikin miya. Shi dai Zayah har ya gama hutunsa ya koma kallo wannan bai haɗa shi da su ba, da zarar ya fito ma zasu gudu cikin ɗaki, suna tsoron haɗa hanya da shi, sai dai su dinga leƙansa ta window har ya fita, idan yana gidan amarya bata zama a waje, tana ɗaki, sai ya fita take fitowa ta yi aiki da sauri ta koma ciki.Da ya koma Ummie ta ce masu ya yi tafiya ne zuwa Niger zai je ya ga gida ya dawo, bata faɗa masu ya koma ba, ya kara bunƙasa mata shagonta, yasa an kawo mata abays daga Egypt, Dubai and Turkey sosai da kuɗin da su Noor suka bata, ya gyara mata kasuwancinta kafin ya koma. A takaice kun ji yadda Ummie take ciki. Idan na ce zan tsaya rubuta maku komai labarin ba zai gudu sosai ba, ainahin labarin yana gaba, yanzu dik sharar fage ce, so ba zan tsaya ɓata lokacina a kan abubuwan da basu da muhimmanci sosai a labarin ba, fatan kun gane?. To a yanzu dai dikkan sojojinmu sun dawo barrack, sun kuma dukufa a kan aikinsu, shirye-shiryen tafiya mission suka fara yi ba kama hannun yaro, a cikin kwana biyu da ya rage masu su tafi sai da suka shiga practical, aka kara horar dasu, sannan aka faɗa masu mission ɗinsu na farko. Daga nan suka dawo suka ƙara shiri, tin da Noor ya dawo basu haɗu da V ba, saboda gagarumin aikin dake gabasu, ko waya basa yi, ita ma bata damu ba, saboda shirin da suke yi ita ma, zasu fara aiki a yanzu, za’a gwada kwarewarsu, shiyasa ita da Arya and Angelina suke ta faman shiri, ita kuma manassa idan baku manta ba na faɗa maku ita Surgeon ce, ba jami’a bace, idan kun ji Surgeon General ko Surgeon Brigadier yana nufin likitan dake kula da rundunar dake karkashin Brigadier ko General ɗin ne, to ita Manassa Division Surgeon ce, watau likita mai kula da majinyatar runduna na musamman, ita zata yi aiki ne a medical corps na soja. Dan haka dole zata tafi Mission da su Noor, saboda sune runduna na musamman, dik idan sojiji zasu tafi mission ana haɗasu da kwararrun surgeon saboda in sun ji rauni, an harbesu ko sun faɗa wani waje sun ji ciwo sai ayi jinyarsu, so a taƙaice ita Manassa ba jama’a bace, likitar sojoji ce. A wannan rana irin ta yau dikkan jami’an da aka yaye zasu tafi Mission ɗin da aka sanyawa suna DEATH OR LIFE (DOL) kenan a taƙaice. Gabaɗaya sojojin da suka yi imani da cewa mutuwa ba’a bakin komai take ba sune a tsaitsaye a cikin hall na AZURE. Tabbas Noor ya yi mamakin ganin V a cikin tawagarsu, bai yi zato ba, ita ma bata taɓa zaton da su zata tafi ba, sai kallon juna suke yi daɗi tamkar su kurma ihu.Dikkan jami’an babu alamar wasa a tattare dasu, dikkansu a shirye suke tsab wa mutuwa. Zasu tafi wannan mission na farko ɗin ne a karkashin ikon Brigadier General na ƙasa, shi zai kula da mission ɗinsu na farko, dan haka yasa ƙananan sojoji suka fara shirya masu rucksack ɗinsu, watau wannan jaka katuwa ta sojoji, wannan jaka da kuke gani tana ɗaukar abubuwa fiye da tinaninku, a matsayinsu na masu tafiya Mission ga abubuwan da aka shirya masu a cikin wannan jaka.Combat uniform na yadi nai karfi da kwari, akwai tactical shirt wasu rigunar aiki ne ta musamman, sai jacket ɗinsu saboda sanyi. Bayan uniform akwai combat trousers da ake basu, yana nan kalar kayan sojiji, amma shi wando ne mai tarin aljihuna fiye da uniform ɗinsu. Akwai manyan gloves ɗinsu dan kariya ga hannuwa daga yankar wuƙa, zafin ɗaukar bindiga musamman a lokacin yaki idan bullet na fita daga bindiga yana masu zafi a hannunsu, to wannan kakkarfar gloves ɗin zai taimaka masu sosai.An baiwa kowani soja body armor, ballistic vest ɗai-ɗai, body armor rigar kariya ce daga bullet, kazalika dik an basu plate carrier dan sanya ƙananan wuƙarsu na soja, ƙaramin bindiga and wayarsu na na ujila da sauran abin da ba’a rasa ba. Kowani soja an bashi helmet wasu ballistic helmet, waɗan nan huluna ne na soja dan kariya ga kai daga wajen buguwa da sauransu. Sannan dikkansu an basu camouflage, wasu kuma ghillie, kaya ne dan ɓoyewar sojoji a lokacin yaki, kamar ciyawa haka aka yi kayan, idan sun sanya ba zaku taɓa cewa mutane bane, musamman idan suka kwanta, sai ku zaci shuka ce a wajen, dik dabarun yaki ne. Dik an basu tactical belt dan ɗaukar ƙananan kayan aiki da holster.Sannan dikkansu sojojin an basu service rifle, wasu assault rifle, bindigu ne wanda dayawan sojoji dasu suke amfani. Sannan mutum uku daga cikinsu watau manyan cikinsu an basu pistol gun, Leo kuma sidearm, ƙaramin bindiga ne da zasu iya rikewa da hannu ɗaya dan kariya ta kusa ko faɗar gaggawa, uku daga cikinsu da aka bawa sun haɗa da Leo, Noor and Zaysh, su ne position one to 3 ɗin.Sannan an basu rocket propelled grenade, kayan ne da aka yi dan lalata manyan abin hawa masu ƙarfi, in case ko ƴan ta’addan suna da motocin yaki ko abin hawa su ce zasu gudu, to zasu yi amfani da wannan dan lalata shi. Sannan kowani soja an bashi optics wasu kuma scopes dan hangen nesa, saboda ya taimaka masu wajen inganta daidaito harbi ko ganin nesa, zasu iya duba nesa ko su hango me abokan gaba suke yi. An kuma basu bipod dan ya rinƙa daidaita bindigarsu a lokacin harbi.Kowani bindigarsu an mashi suppressor, na Leo , Noor and Zaysh kuma an masu silencer, hakan yana rage amon karar harbi da flash light da yake kawowa, hakan zai taimaka kada abokan gaba su riskesu da wuri. An basu wasu mahaukatan flashlight, mutane ukun nan kuma weapon light, wasu irin light ne masu balain haske wanda in suka haska sai waje dik ya zamto tamkar rana, baku ganin torchlight na sojoji ne? Hasken balai garesa, ga shi da haska nesa sosai, in suka dalla shi sai ya kashe ido.Dikkansu an shirya masu night vision goggles ta yadda ko a cikin duhu tana amfani da ƙarfin intensification na haske, komai duhu in dai yana fuskansu zasu iya yin aiki kuma zasu iya ganin abu!. Sannan dik an sanya masu ɗan karamin thermal imagers, na’ura ce ta gano zafi ko a cikin duhu, idan abu mai zafi ya nufosu zai yi alerting nasu da sauri. Sannan dikkansu an mallakawa kowannensu handheld radio dan sadarwa ga juna, ƴan rundunan zasu dinga amfani da shi saboda sanarwa ga juna halin da suke ciki, an yi masu connecting na shi dikka, in ɗaya ya yi magana dikkansu zasu ji, kuma zasu dinga karɓar umarni daga ogansu Leo, fatan kun ganesa?.Dik da wannan sai da aka kara masu da headset with boom mic, shima dik na sauraran juna ne da magana da su kai tsaye, gudun ko ta kwana ne, ida wancan baya bada abin da akeso sai su ɗauki wannan.An basu data mai karfi dan satarwa, an saita wayoyinsu da na’urorin su Arya. Dikka waɗan nan abubuwa fa wannan shegen rucksack ɗin nasu ya kwashesa, ga kayan sakawansu still a ciki, jakar ta cika dam, sai da aka sanya masu belt aka iya rufe jakar, ta yi mugun nauyi, amma a haka zasu ɗauka a bayansu. Mazan fama ba, soja ba dik kai ba!.A ɓangaren Manassa an zuba mata Individual first aid kit mai shaƙe da kayan farko na taimakon gaggawa, a cikin akwai irinsu bandages, tourniquet, hemostatic agent da sauransu dan ceto ran soja da gaggawa. Sannan an sanya mata combat medic kit, kayan aikin likita masu yawa sosai kuma masu amfani da za’a buƙata a gaggauce dan jinyar raunin filin daga ƙananan zuwa matsakaita a yayin mission.Dikkansu an basu water bladder dan su samawa kansu ruwa a koma ina suke, kuma ruwan zai zama mai tsabta har su sha su yi abin da zasu yi. Dik an basu ƙananan sleeping system mai caji da rana dan in suna barci wani motsi ya zo komai nisan shi wannan ya ankarar da su. An basu entrenching tool na karfe wanda ake haɗa shi da notika, idan sun isa wajen da zasu kafa tantina suna iya haɗa shi, kamar shovel haka yake, dan su tona rami aka basu.Sannan dikkansu an basu gas mask wasu kuma cbrn mask, mask ne dan kare numfashi daga iskar guba, iskar sinadarai ko biological hazards dake yanki, takan iya yuwuwa akwai gurɓacewar yanayi a in da suka nufa, wannan mask zai hanasu shaƙar gubar. Sannan an basu cbrn suit mai kama da jacket, yana kare gangar jikinsu daga iskan sinadarai ko gurɓacewar yanayi. An basu cbrn hands gloves, da kuma ear protection dan kare kunne daga ƙarar makami, suna sanya shi kada su rasa jinsu saboda karar bindigu.Su Arya jami’an computer na musamman kuma an shirya masu compass & maps gps unit a laptops ɗinsu, kuma dik abin da aka basu mai caji da rana ne, dan shi rana a ko’ina akwaisa, lantarki kuwa kun san babu, shiyasa aka masu masu amfani da rana kamar solar kenan. Sannan an haɗa masu gps enabled devices, wannan zai taimaka masu wajen daidaita matsayi daga nesa sosai. An shirya masu na’urar hangen sama, ga su unmanned aerial vehicles, ƙananan drones dan hango sama daga nesa, ga portable drone controllers dan sarrafa uvn na waje.Uwa uba an haɗa masu counter drone systems wanda zai iya gano drones na abokan gaba idan sun turo masu, su suna iya turawa abokan gaba ƙananan drone ɗinsu, su yi control ɗinsa ya je har in da miyagun suke, suna zaune a cikin tantin da suka kafa a sansani suna kallon dik wani motsin ƴan ta’adda a laptop ɗinsu suna kwasan bayanansu suna sanarwa sojojinsu. Kai an fa shirya masu kaya dayawa, sannan aka shirya masu ɗanyen abinci, su zasu girka kayansu da kansu, su Arya aka shirya masu laptops ɗinsu a cikin rucksack, sannan aka basu bututun iska saboda faɗawa kogi ko wani rami na ruwa.Tambayana a nan shi ne, shin masu karatu sojijin ƙasarku haka ake basu kwararrun kayan aiki a lokacin da za’a turasu faɗa da wasu ƴan ta’adda? Ko iya bindiga kawai ake basu?.Dikkansu suna sanye da uniform a jikinsu, har da su Arya yau an basu uniform, sun kuwa yi balain kyau, tamkar dan su aka yi kayan, sun kara kwarjini da firgita makiya.Dikka sojojin ƴan uwansu suna wajen dan yin bankwana dasu, ta yiwu su dawo a raye ko kuma akasin haka, kowa zai ga ɗan uwansa na karshe ne a yanzu. Ummie bata zo ba, dan Zaysh ya ɓoye mata, ya ce mata dai zasu shiga wani aiki, zata iya kiran wayansa ta ji a kashe idan babu rana basu yi caji ba, amma dik in ya kunna waya zai kirata. A haka ya kyaleta, dan baya son ɗaga mata hankali. Babban soldiers eagle aka kawo dan ɗaukarsu ya yi dropping ɗinsu a bakin dajin da zasu shiga mission na farko, idan ya saukesu a wajen sai su kutsa cikin daji da ƙafarsu. Suna ta ɗagawa ƴan uwansu hannu suka fara shiga jirgin a jere cikin tsari haɗe da ɗan pareti, da haka suka shige cikin jirgin suna kallon ƴan uwansu, Leo yana ta kallon Champion and Lion da guru dake tsaye a babban filin tashin jirgin AZURE, dikkansu suna sanye da nose mask, ga katuwar jacket da suka sanya, p-cap a ciki kafin su sanya hukar jacket ɗin, sun yi kyau kam matuƙa.Sai da jirgin su Leo ya ɗaga sannan IRON FIST suka bar barrack ɗin, suka koma hotel da suka sauƙa, ba yau zasu koma ba, dan akwai binciken da suka zo yi dan tabbatar da wata gaskiya da basu faɗi ba, so zasu ɗan yi kwana biyu a nan.Daddy Noor ma sai da ya ga tashin jirginsu sannan ya koma gidan GAT ya hau shirin komawa US. Su V da suka zo tafiya sai da zuciyarsu ta ɗan kaɗa, dan basu taɓa tafiya aiki ba kun sani, dole su ɗan tsorata, amma Arya yarinyar nan tamkar babu zuciya a kirjinta sai dutse, ko kaɗan bata tsorata ba, sai ma cewa da ta yi su yi sauri su tafi, dan ita ma ta shiryawa mutuwa, bata da tsoro ko kaɗan yarinyar, ita dai V ta ji kwarin gwiwa ne kawai a waje ɗaya shi ne Noor yana tare da ita, tasan dik wuya zai tsaya mata. Manassa and Angelina kam ba’a magana, ita Manassa komai normal ne, baka gane tana farinciki ko bata yi, kamar Vash take, komai daidai ne, ko su mutu ko su rayu dik daidai ne, ita kuwa Angelina har da guntun hawayenta, wai na kewar daddynta ne hawayen, kuma karya ne, zuciyarta ne ya fara karaya, ta ji tsoron su mutu, dama a cikinsu dik ita ce mai tsoro gaskiya fiye da Manassa, tana da saurin karaya, karfin hali ai sai Arya, balai, yarinyar nan ko mutuwa ake yi ba zata fasa abin da ta sanya a gaba ba, ita ta gado daddynta sak, dan kafin ya taka matakin GAT ai sai da taurin zuciya da jajircewa, to ita dai da kwarin gwiwarta suka nufi can.Jama’a an iso in da nike son mu iso, sojojinmu sun tafi Mission, yanzu zamu shiga ainahin labarin ZAKUNA BIYAR, yanzu zamu isa ga ainahin jigon labarin, masu hawan jini, masu low bp ayi hakuri da abin da alkalamina zai rubuta a wannan karon, na san fore sure zuƙata zasu kaɗa, hankula zasu tashi, amma amin afuwa, ilimi da farkar da al’umma nike burin yi! Sannan zan so wannan ɓangare dana kira da jigon labarin nan kada ku tsallake waje ko ɗaya, da daɗi da ba daɗi dik ku yi hakuri ku karanta, dan amfananku ne, ba karamin amfani zai yi maku ba!! Muje zuwa kan jigon labarinmu a yanzu!.—————–W-S-Hospital🔥Cikin wajen tamkar ba’a duniya take ba, ta ko’ina glasses ne da wutar lantarki, zaku rantse da ALLAH dik lantarki duniya a nan wajen ake karar da shi, ko da sunan wasa wuta bata motsawa a wannan waje bare a ɗauke, jikin bangon ainahin wajen kakkafar bango ce da zaku yi zaton samudawan da ne suka gina shi ba mutane ba, dan gini ne da aka yi su da duwatsu masu karfi sosai. Amma daga ciki ko’ina na glass ne, ga kayan zamani ta ko’ina. A dunkule kenan, mu kara kutsawa ciki dan ganin meke going. Ƙofofin wajen masu ƙarfi ne sosai haɗe da kimiyar tsaro na zamani mai ban mamaki, suna amfani da fasahar tsaro mai ƙarfi, tare da makullai na lantarki, akwai wani sashen ma da babu wanda yake iya shiga sai mutane uku, dan wajen door ɗin kuna taɓawa shocking ne a jikin, sai dai a ga mutum ya ƙandare in ya taɓa.A gefe guda ga wani side tamkar fagen kwaje-kwaje na hospital haka aka yisa, dan ga ɗakuna da beds dayawa a side ɗin, kowani ɗaki da dalilin hasasarsa a wajen. A wani side ɗin kuma ɗakuna ne masu kyau da gadaje masu rai da lafiya na majinyata, ta kowani kusurwa akwai CCTV, a saman bene kuma akwai wani ɗaki mai cike da computer dan kula da cameras dake ta ko’ina.Hospital ɗin yakasance da ɓangarori guda biyar, kai tsaye mu je ɗayan ɓangaren. Wajen cike yake da glass, dik ɗakunan wajen glass wall ne, filin cike yake da dabbobi kala-kala masu haɗarin gaske, dabobin da idanu bai taɓa ganin irinsu ba, kowacce dabba tana cikin glass tamkar a gidan zoo, ga manya-manyan macizai, kunama, kifaye, kai harta cinnaka akwai wajensu, suna cikin glass, side ɗinsu yana da mugun girma sosai, kuma dik cike yake da waɗan nan dabbobi. Ɓangarorin hospital ɗin nan kowanne da abin da ya kunsa, ba zan fayyace maku me a ciki gabaɗay ba, sai tafiya ta yi tafiya, dan haka mu je zuwa, kun dai ji ɓangare na farko na dabbobi ne kawai!. Akwai nurses dayawa a hospital ɗin, amma dikka mata ne babu namiji ko ɗaya, sai dai dik nurse da zaku gani a wajen sai kun kalleta kun sake kallo, babu munana a wannan waje, ga su da zubin ƴar tsana, sirara ga shape, farare tas-tas da su, rigarsu na aiki guntaye ne zuwa tsala-tsalan cinyoyinsu masu kama da madara saboda hasken jikinsu, suna da hakin gashin mai shegen kyau wanda suka ɗauresa a tsakiyar kai, kansu da hular aikinsu, ga su da tsabtar balai, komai nasu cikin tsantsar kula da natsuwa suke yi, one thing about them, dik wata malamar asibit dake wannan Hospital ɗin shekarunta ɗaya da sauran, dikkansu they’re age mate, babu wacce ta girmi wata a cikinsu, kuma dikkansu yanzu 18 years suke da shi, sannan abin da zai baku mamaki dayawa daga cikinsu suna ɗan kamanceceniya da juna, wasu ma ida ka gansu zaka zaci twins ne, sannan sun kai su 40 a hospital ɗin.Abin da mamaki ko? Ace shekarunsu su 40 ko sama da haka dikka ɗaya, sannan dikkansu mata ne ba maza tamkar dama zaɓosu aka yi, kai ko zaɓosu aka yi sai haka!. To akwai dai manyan likitoci maza guda uku, sannan akwai masu gadi zaratan maza madaka karti dake sanye cikin uniform ɗinsu mai zubin overall, ga wasu dakakkun takalma a kafafunsu mai balain karfi Kai in takaice maku tsaron wajen nan wane mutum ya iya giftawa, ko tsuntsaye basa iya zuwa wannan waje, dan lantarkin dake wajen ba zai bari dik wata halitta mai rai ta gifta ta sama ko ta ƙasa ba.Akwai benaye guda biyar daga gefe masu hawa ɗai-ɗai, sannan akwai ƙananan gidaje wa ƙannanan ma’aikatan lafiya da guards masu tsaron wajen, kamar general government hospital ne fa, kun san shi ne ake yi wa ma’aikata gidan zamansu a cikin hospital ɗin. Mu ƙara kutsawa ciki. —————————🔥 Wasu matasan likitoci dake sanya cikin kayan aikinsu ne suka fito daga cikin elvator da ta tsaya a sama a yanzu, maza ne su uku da a kallan shekarunsu zai iya zuwa ɗaya kamar yadda kansu watau tsawonsu yake ɗaya, komai na jikinsu iri ɗaya ne, harta hands gloves na hannayensu da nose masks na fuskokinsu iri ɗaya ne, ankel boot dake kafafunsu ɗaya, kansu na sanye da huluna masu zubin na sanyi, suna sanye da doctors nose mask ne, wanda ya hana ganin fuskokinsu sai idanu kawai. Komai na jikinsu farare ne tas, sun fito a cikakkun kwararrun likitocin nasuA TAƘAICE SU WAYE SU?!. DR JAMES. surgeon dr, suna yi mashi laƙabi da likita mai gani har hanji, saboda kwarewarsa a aiki, ga iya tiyata bisa tsari, sannan akwai tsantsar natsuwa da zallar rashin yin magana, dan ko kusa ko alama baya ɗaga ido ya kalli mutane bare magana, baya dariya, kai ko fuskansa ba’a samun gani bare dariyarsa, likita ne da ya shahara a kan aikinsa over, Sai DR KAMAL, bokan turai, assistant surgeon mai gani har hanji ne, kuma halinsu ma iri ɗaya. Sai kuma DR MARK, waɗan nan uku shaƙiƙan aminai ne na gaske, suna kuma kaunar junansu sosai.Kai tsaye a bakin wani kofa da aka rubuta P-P a jikin door ɗin suka tsaya. Na tsakiyansu watau mai DR JAMES ne ya ɗan gyara hand gloves na hannunsa kafin ya zareta, sannan ya ware yatsunsa ya sanya a jikin fingerprint dake jikin kofar. Take door ɗin ta yi scanning kafin ta buɗe kanta. Turawa ya yi, kusan a tare suka shige ciki. Ɗaki ne tamkar ɗakin tiyata, an shirya komai da ya danganci tiyata, ko’ina tsab a cikin ɗakin, ga wani sanyin Ac dake tashi, akwai doguwar sofa mai zaman mutum uku a cikin ɗakin, sannan akwai wasu manyan kwalabe da freezers bayan gadon tiyata, gefe guda akwai drawers. Kusan a tare suka zauna a saman wannan sofa ɗin tare da ɗaura kafafunsu ɗaya bisa ɗaya, dik cikinsu babu wanda ya yi magana da ɗan uwansa, sai DR JAMES ne ya mai da hand gloves ɗinsa tare da duba time a agogon dake manne a hannunsa. A daidai wannan lokacin wasu nurses mata guda biyu kyawawan gaske suka shigo cikin ɗaki, suna turo wani bed. Wata macece kwance a saman bed ɗin, tana sanye ciki kayan tiyata, an shiryata tsab, da alama an yi mata komai da ake buƙata, dan ga shi tana barci alamar anyi mata alluran barci. A daidai bed dake cikin ɗakin suka gungura gadon su tsaya, sannan suka kama matar suka mayar da ita saman gadan cikin ɗakin, a natse suka tura gadon da suka zo da shi suka fita waje. Kada ku manta dik nurse’s dake cikin wannan hospital ɗin shekarunsu ɗaya watau 18 years, na kara tina maku ne dan yana da muhimmanci ku rike hakan kada ku manta.A tare waɗan nan likitocin suka miƙe tsaye, wajen drawers ɗin nan suka nufa. Kowa ya sanya kayan tiyata, gloves, mask, gown, suka cire wanda suka zo da shi kenan. DR JAMES ne ya umarci DR JAMES da ya je ya duba kayan aikin da nurses ɗin nan suka shirya komai yana na intact ko?. Karisawa gaban table dake kusa da gadon DR KAMAL ya yi, duba kayan ya hau yi, an shirya irinsu scalpel wukar tiyata, retractors na buɗe ciki, forceps & clamps, needle holder & surgical needle, electrocautery machine na goge jini, suction machine na fitar da jini ko ruwa, sutures zaren da ake ɗinki, sterile drapes na rufe jikin maras lafiya, catheter na fitar da fitsari.Hannu ya ɗaga tare da ɗaga yatsa ɗaya yana yi wa DR JAMES alamar da komai yana nan yadda yakamata. A tare suka kariso wajen domin fara aikinsu. DR JAMES ne ya fara checking na bp, pulse, oxygen, da heart rate na mara lafiyar, sai da ya tabbatar bata a cikin haɗari sannan ya sanya mata catheter dan fitar da fitsari.DR MARK ne ya matso ya fara tsabtace wajen ciki zuwa gwiwa da ƙafa na maras lafiyar, ya yi amfani da disinfectant watau chlorhexidine. DR JAMES ya rufe maras lafiya da sterile drapes, sannan ya duba lokaci a agogon hannunsa dan ya tantance matakin da Anesthesia da suka bata yake. A natse ya ɗago ya kalli DR MARK, da sauri ya ɗauki scapel ya miƙo mashi tare da ɗaukar cutton ya matsa kusa da shi.Ta sama suprapubic incision bikini cut ya fara yankawa a natse game da kula sosai. Ya buɗe tsoka da peritoneum har ya isa mahaifa. DR MARK ya ɗauko retractors ya miƙa mashi, da shi ya yi amfani wajen buɗe wajen sosai ta yadda zasu ga abin da suke yi da kyau.Da fallopian tubes suka yi amfani dan gani mahaifar, DR JAMES ne ya fara da yanke ligaments da jijiyoyin dake rike da mahaifar, cikin kula sosai suke yi ta yadda ba zasu samu matsala ko su rasa wata jijiya da zai yi sanadiyar kashe mahaifar ba. DR MARK ya gyara electrocautery dan hana zubar da jini sosai.Kun san me? Tin daga ovaries suka tsinke mahaifan nan, suka ciresa gabaɗaya, da alama wannan mata bata son ta sake haihuwa ne, domin kuwa idan ovaries suna nan za’a iya yi mata dashen wata mahaifa lokacin da ta buƙata, amma babu su yana da matuƙar wahala, a yanzu ma ba’a samu hanyar dashe ovarries ba. DR KAMAL ne ya ɗauko wani kwalba mai kama da cikin mace DR JAMES ya sanya wannan mahaifa a ciki, suka rufe kwalbar, DR KAMAL ya karɓi kwalbar ya fita da ita ta wata kofa dake cikin ɗakin wacce zata fidda shi ta part na kwajinsu.Kallon DR MARK DR JAMES ya yi. “Done my work!”. Yana gama faɗar hakan ya bi bayan DR KAMAL ta kofar da ya fita. Binsu da kallo DR MARK ya yi, sai da suka fita sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa ya fara ƙoƙarin karisa nasa aiki. Rufe duct ɗin mahaifa and vaginal cuff ya fara yi da zaren ɗinki. Sai da ya ɗinke peritoneum, fascia, muscles, subcutaneous tissue, sannan fata a hankali cikin kula sosai, yana yi yana mai da idanunsa kan fuskar matar, ga idanun nasa dara-dara da su Masha ALLAH.Bayan ya kammala komai ya duba yanayin lafiyar maras lafiyar, ya duba yanayin jininta ko tana buƙatar ƙari ko kuwa aa, ya duba bp, hr, fitsari, da zafin jiki, ya duba komai a natse, ya yi sa’a komai lafiya, dama ya tsammaci hakan, saboda sun saba wannan aiki ba’a samun kuskure, so ba yau bane farau.Wata allura ya ɗauko, ya haɗa ya yi mata a damtsen hannu, sannan ya kira wasu nurses guda biyu suka shigo bayan ya tattara dik sauran kayan tiyatar ya mai da su muhallinsu, yazama tamkar ba’ayiwa matar komai ba. Umarni ya yi wa nurse’s ɗin da su ɗauki matar izuwa recovery room na ɗan lokaci dan ta samu damar farfaɗowa daga anesthesia.Daga nan ya zaro wata farar takarda, rubutu ya fara yi cikin kwararre da kuma kyakkyawan handwritten ɗinsa mai bala’in kyau, abin da yake rubutawa a jikin takar shi ne, za’a bar mara lafiyar a asibiti ta yi kwana biyu zuwa biyar dan a kula da lafiyarta, sannan a bata nasogastric tube dan kada cire mahaifar ta hanata cin abinci, a kula da cimar da za’a rinƙa bata, a mayar da hankali a kan dik wani motsinta a cikin ƴan kwanakin nan dan tabbatarwa ta samu ingantaccen lafiya, kaɗa a barta ta yi aiki mai nauyi.Ya yi dogon note tare da naɗe takardan ya bi bayan nurses ɗin izuwa C-R ɗin. A jikin matar ya ajiye note ɗin tare da ɗauko wata takarda ya yi sign, sannan ya ɗauki wayansa ya matsa gefe kaɗan. Call ya yi kamar na minti ɗaya, ya katse kiran ya fita waje. Da fitarsa bai fi da mintuna 40 ba sai ga wasu nurses mata guda biyu sun shigo ɗakin, matar suka ɗauka suka fice, suna tura gadon nata har izuwa wajen wani daki da majinyata ke hutawa, suka sanyata a cikin, daga nan suka bar room ɗin, babu kowa a cikin ɗakin sai ita kaɗai, ko’ina tsab-tsab ga kamshi da sanyin AC dake tashi, . Shi kuma DR MARK bayansu DR JAMES ya bi. Cikin wani glass room ya shiga, komai na ɗakin glass ne except wall. Ɗakin gabaɗaya kewaye yake da kwalabe na glass masu kama da cikin mace, an shirya kwalaben a shirye datsan-datsan, kusan rabi da kwatan kwalaben ɗauke suke da mahaifar mace a ciki, tamkar yadda ake dashen mahaifa wa cikin mace haka aka yi dashen wa waɗan nan kwalabe dake ɗauke da ruwa tamkar yadda mahaifa yake a cikin mace, gabaɗaya kwalaben kuma suna haɗe ne da na’urar dake basu daidaiton yanayi ya hanyar amfani da wutar lantarki. TO FA, ABIN AL’AJABI! ME SUKE YI DA MAHAIFA KUMA?.Karisawa kusa da su DR MARK ya yi, a natse ya ce. “Done my work”……. Hannu DR JAMES ya jinjina mashi alamar ya yi kokari, sannan ya mai da hankali kan aikin da suke yi. Buɗe wata kwalba mai kama da cryo storage tubes ya yi tare da gyara hands gloves na hannunsa, ya ɗauki wannan mahaifa ta wannan mata, a natse cikin tsananin kula suke komai. Da kallo ɗaya zaka yi wa yadda suke aikin nan kasan cewa kwararrun likitoci ne na gasken-gaske, in short su likitoci ne da irinsu basu wuce a kirga ba ma a duniya, matakin kaifin ƙwaƙwalwa da bincikensu ya zarce yadda kuke tinani, they’re gifted, amma dik da haka cikin taka tsantsan suke aiki yadda zaku san aikin mai haɗari da wahalar gaske ne suke yi, idan aka samu matsala kaɗan komai na iya lalacewa su tabka babban asarar da ba zasu taɓa son hakan ba!. A cikin wannan kwalba DR JAMES ya sanya wannan mahaifa, sai da ya tabbatar zamanta ta yi daidai sosai, sannan ya kunna wata naura dake jikin kwalbar dan canzawa mahaifar yanayi izuwa yanayin cikin mace, take cikin kwalbar ta kawo wuta sky blue mai ɗan haske, ta fara fitar da siririn sauti mai bada vuuuuu kamar vibrate na waya. Da sauri DR JAMES ya juya ya rungumi DR KAMAL alamar sun yi nasara, matsawa DR MARK ya yi shi ma suka rungumi juna sosai, sannan suka raba jikinsu. A natse suka fara takawa suna bin dik kwalaben dake cikin wajen suna dubasu, tamkar suna duba wani abin haka. Sai da suka tabbatar komai normal sannan suka nufi hanyar fita a tare. Kai tsaye side na dabbobin dake cikin wajen suka nufa, suna tafiya ne a kai ɗaya. Kewaye suka fara yi a wajen dabbobin, yana da girma sosai wajen, guards dake tsaron wajen kawai sun fi mutum 20, kun ga kuwa ai wajen da girma. Kowani dabba da irin abincin da yake ci, ga kwanon abincin kuma a gabansa an zuba mashi, waɗan nan guards ɗin suke baiwa dabbobin ruwa da abinci, har macizai dikka suke ciyar da su, shiyasa aka samu jiga-jigan guards madaka karti masu rai da lafiya dan kula da su.Sosai suka yi yawo a cikin wajen, suka tabbatar da komai yana nan yadda ya dace, sannan suka fito suka nufi office ɗinsu. A kan hanyarsu na komawa office suka ci karo da wasu kyawawan nurses guda biyu dake sanye cikin kayan aikinsu, sun yi matuƙar kyau tsab-tsab da su. Face ɗinsu da nose mask suma. Har ƙasa suka durkusa suka gaida Dr’s ɗin cikin girmamawa. Kai na gaji da rubutun, haba, ku ce Princess dakata ki bari haka, ya isa ki huta mana! Amma dik kun yi shiru sai typing nike yi kamar ba’a sona! To sai Monday idan mai dikka ya kaimu!.

Back to top button