Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 25 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na ashirin da biyar_

____________

*_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥

*_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥

*_KASANCE D’AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_

*_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_*

*KWANKWASON JIMINA miss xoxo*

*TSUTSAR NAMA Billynabdul*

*GUDUN K’ADDARA Huguma*

*AMEENATU Mamuhghee*

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA  LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

__________

…….Saki dai dole Dafeeq yayi sa, sannan akai komai a rubuce kowa ta saka hannu aka bama kowa nasa copy ɗin d.p.o ma ya ajiye nasa. Khadijah ta dinga sakin ajiyar zuciya da jinta sakayau tamkar wadda akaima rahama. Haka suka taho gida Dafeeq na kallonta harda cin tuntuɓe mahaifiyarsa na jansa tana masifa da hararar Babansa. Dan gaba ɗaya yama fi kowa bata takaici daya kware musu baya ya zaɓi bare akansu har yana gurfanen bada haƙuri akan abinda ita bataga inda sukai laifi ba.

      Sosai Baba ya sake jerama su Baba Hakimi godiya. Suka kuma haɗa musu shatara ta arziƙi dan sun ce yau kam gida zasu kwana tunda an gama komai. Sanda zasu wuce Khadijah harda kukanta. Haka dai sukai musu sallama suka tafi badan rai yaso ba. Amma dai in sha ALLAHU Baba yace zuminci ya ƙullu kenan. Khadijah batai ƙasa a gwiwa ba bayan wucewar Baba Hakimi ta sake neman gafarar iyayenta dama ƴan uwanta. Suma basu ja zancen ba sukace komai ya wuce ai sun yafe mata. Baba da Mama suka sake mata nasiha da nuna mata illar abinda tayin. Ranar ma taci kuka dan harda su zazzaɓi tasha da ciwon kai. Daga ƙarshe dai ƴan uwanta suka koma tarairaiyarta suma…

      ★

  A gidan su Dafeeq kam bala’i ne ya nema kaurewa tsakaninsa da Kainaat daya tattara laifin komai a kanta mahaifiyarsa na kareta. Amma ita sai tai biris da shi saina murmushi da take dan a ganinta dai ta baƙanta masa rai. Kuma koba komai iyayensa sun kwana a bayan kanta. Duk da ma ba haka taso ba wlhy. Taso ace anyi bala’i iya bala’i da iyayen Khadijah ta yanda sai Dafeeq ya wajigu kamar na wata ɗaya ya fita a hayyacinsa. Amma koba komai dai hakan ma nasara ce.
Tsawatawar iyayensa ya taƙaita wannan fitina. Sai dai a ransa ya ƙudiri aniyar wlhy sai tayi dana sanin masa wannan abun datai masa. Oho bata damu ba, dan itama dai ta shirya masa tsaff. Bai yi niyar su koma Adamawa ba sam. Sai dai fa maganganun mutane da ALLAH wadarai da akema iyayensa da shi kansa akan Khadijah ya hanashi sakat a anguwa. Musamman ma da akace yanzu Kainaat ya aura tare da jin labarin tushen auren nashi. Shike nan mutane suka samu nayi dan duk wanda dai ya kalla Kainaat yasan ba sa’ar auresa bace duk da dai a addinance bawai haramun bane. Amma dai ana fassara shi nashi auren akwai manufa a ciki tunda ance Kainaat nada kuɗi.
Hankali tashe ya tattara Kainaat suka koma inda suka fito akan sai komai ya lafa zasu dawo. Dan ya ƙudiri aniyar baro Adamawa zai dawo gida Kano da zama. Kainaat kuwa da ita wasan yanzu aka fara….

       *_BAYAN WATANNI_*

    Tafe take cikin ɗan sauri-sauri, sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarta ba irin ta ɗiya mace. Hijjab ne har ƙasa a jikinta da niƙab dan babu ta inda ake ganin komai nata sai ƙwayar ido. Komai ya canja a rayuwarta, canjawar da take tabbatar da ita a sabuwar Khadijah Muhammad Kura. Duk da watanni bakwai ɗin nan da suka biyo bayan abinda ya faru sun sake zuwa mata da wasu abubuwa ne mabanbanta wanda tai tsammani babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya. Taso komawa ta cigaba da karatunta, amma sai Baba ya tabbatar mata da cewar ta makaro kuma. In dai a gidansa ne ta gama karatu kenan wannan shine horon da zai mata akan kuskurenta. Sai dai zai barta ta koma islamiyya bazai taɓa tauyeta a neman ilimin addini ba, na boko kam sai dai idan aure ta ƙara mijin ya maidata amma shikam badai shi ba. Duk irin roƙo da magiyar da taima baba bai saurareta ba. Haka tanaji tana gani dole ta jingine maganar makarantar boko ta koma islamiyya kawai ƴan uwanta ma bata sha’awa. Dama dai ta kusa sauka ta tafka waccan tsiyar, dan haka a yanzu ta sake dagewa sosai fiye da da gashi har tayi saukar tunda dama tana gab. Zakuma ai bikin saukar da ƴan uwanta ne a ranar ɗaurin aurensu da ya rage saura kwanaki huɗu kacal a yanzu. Sam bata kula kowa a yanzu. Kai ko kallon wani namiji da wata siga batayi, dan duk ta haɗasu ta musu kuɗin goro a littafin rayuwarta. Bayan kammala iddarta samari da yawa harma da magidanta sun fito da niyyar aurenta amma ta dakatar dasu. Shi dai Baba dama baice mata komai ba, hakama Mama iyakarta da ita nasiha da shawara. Sai su Ni’ima ne keta zugata akan ta fidda miji a haɗa bikinsu dan ALLAH. Murmushi kawai take musu tace ba yanzu ba, ita da aure ma tana jin har abada. Sukan nuna jin haushin maganarta, itako ta tattarasu ta share kawai….
Isowar napep da take jira ya katse mata tunani. Sai da ta sanar masa ina zata sannan ta shiga tare da fiddo wayarta ƙarama ta daddana dakai kunne. Daga can Zuhrah ta amsa mata. “Aunty kin taho ne?”.
Kai tsaye ta ce, “Eh, ina fatan dai kun gama gyaran jikin”.
“Eh muna kammala, kema muke jiran dan har an gama mana komai ma. Dan ALLAH ki maza kizo a miki kema. Kefa kaɗai ya rage”.
“K nifa ku rabani da wannan gyaran jikin. Kunbi kun takura min kullum aka gama muku sai kun takura an yaɓamin wannan kayan naku a jiki ina dalili. Yau ma kawai zanzo ne saboda biyanta kuɗinta da kuma Baba daya ce dole nice zan tsaya a kanku muna komawa gidan”.
Dariya Zuhrah tai da faɗin, “Aunty Khadijah masifa, shike nan sai kinzo mudai muna jiranki.” wayar ta yanke itama tana taɓe baki, minti kaɗan suka iso anguwar. Ta biya mai napep ɗin ta shiga. Ta samu an kammalama su Ni’ima komai. Kamar kullum yauma sukai kanta su da mai gyaran jiki sai da aka mata aka kuma tsareta tasha abubuwan da ake basu wai maganin sanyi, ƙyalesu kawai take ana tasan wani ba maganin sanyin bane ba. Dan kusan sati biyu kenan ita ke kawosu ta wuce islamiyya, idan an tashi ta biyo ta ɗaukesu su koma gida. Baba ne ya sata wannan aikin badan komai ba sai dan tsoron yau da gobe. Sai da aka gama mata komai batare da jira ya daɗe ba ta maida kayanta da hijjab suka wuce gida akan idan taje can tayi wanka. Dama haka take yi ita kullum. Daga haka sukai sallama da mai gyaran jiki akan ita zata samesu gida gobe dakai ƙunshi…

     Washe gari akai kamu, a kuma ranar akama amare ƙunshi, tare da tsare Khadijah itama akai mata exactly kalar nasu. Tun a ranar baƙi suka fara cika gida musamman ƴan uwansu da zasuzo da ga kura asalin garin babansu kenan. Duk da sun san da batun Khadijah kowa yazo ya ganta sai ya tanka da sake maido da zance baya. Hakan yasa ta dinga jin hawaye sai dai ta faki ido ta share kawai. Ganin zance yana neman fara yawa a kanta Mama tace su koma gidan makwafciyarsu Maman Daddy tunda mijinta baya nan. Hakan ne ya bama Khadijah salama. Idan ba doleba kuma bata yarda ta shiga gidansu sam. Washe gari ta kasance ranar ƙunshi na ƴammata. Ga baƙi nata sake kunno kai dan wannan shine biki na farko da za’ayi a gidan tunda dai Khadijah ba’a gida akai nata ba. Cika iyakar cika gida yayi, Khadijah dai tana tare da amare amma bata shiga cikinsu ta barsu da ƙawayensu. Tana daga gefe matsayinta na babba ta kama kanta. Ana gobe ɗaurin aure ne ta kasance ranar dinner da anguna suka lallaɓa baba da ƙyar ya amince musu ayi a ranar, dan da an ɗaura aure yace bai yarda da wata bidi’aba kuma. Hakan yasa suka saka dinner ɗin daren ɗaurin aure. Washe gari ayi walima da saukarsu bayan an ɗaura aure. Da dare a miƙa amare ɗakinsu shike nan.
Sam Khadijah batai niyyar zuwa dinner ɗin nan ba. Amma aka sakata gaba. Kai har sai da takai Ni’ima tai rantsuwar in har Khadijah bazataje ba wlhy itama bazaje ba. Jin haka yasa itama Zuhrah tace itama ta fasa sai dai anguna suyi abinsu su kaɗai. Khadijah ta ɗauka wasa suke, sai da taga mai kwalliya tazo sunƙi yarda a musu sannan ta yarda zataje. Haka suka tsaya a kanta aka fara mata kwalliya ƴar dai-dai misali sannan suma akai musu tasu irin ta amare tare da zuba musu ado na gani na faɗa. Su duka sunyi ƙyau sosai cikin lassai masifar ƙyau ja sai Masha ALLAH. Haka itama Khadijah tai wani kalar ƙyau na masifa kamar ka haɗiyeta. Balle yanda jikinta da fatarta suka wani sake murjewa dayin fresh tamkar bata shiga rana. Ƙamshin gyaran jiki ko da akai musu yasa koya suka motsa zakaji wani shegen ƙamshi mai motsa zuciya da ratsata kwanya. A yanda komai na Khadijah ya canja saika rantse bata taɓa aure ba ma. Dan kusan yanzu ne take kan ganiyar zama cikakkiyar macen ta. Sosai material ɗinta fari da adon pitch flowers da akaima fitet gown yay masifar kwantawa a jikinta tamkar an zana shi. An mata ɗaurin daya kwanta sosai ta gaba gashinta ya fito hakama baya jelar da aka naɗe da ribbon sai ƙyalli suke. Ba ita kaɗai ba yaran gidansu duk suna da gashi dan sun gada a wajen mahaifiyarsu ne, Jamilah ma duk ta fisu. A wajen saka mayafi ne aka fara rikici, tace ita bazata iya fita da mayafi a kafaɗa ba da wannan gown ɗin. Su Ni’ima sai roƙonta take itako ta dage hijjab zata saka. Sai da Zuhrah ta hau mata kuka sannan ta yarda badan ranta yaso ba ta saka gyalen pitch color shima dan bata son taga ɓacin ran ƴan uwanta a yanzu, sai dai a saman kanta ta ɗora ta lulluɓa duk da bawani ya sauka mata ƙasa sosai bane yanda take so. Dan bayanta da bata so a gani dai sun fito ƙirjin kawai ya rufe. Ganin hakan yasa ta saki jelar gyalen ta baya na gaba kuma ta yanashi ta yanda ya rufe mata ƙirjin, sai hakan ya taimaka mata sosai amma kuma ta gefen data saki gyalen ana gano gashinta baƙi siɗik da aka faka a tsakkiyar kan ya fito tsakkiyar ɗaurin ɗan kwalinta. Haka dai ta haƙura suka fito kasancewar abokan ango na zaman jiransu.
Duk da mijin Zuhrah dana Ni’ima sun girmeta matukar girmamata suke kamar yanda ƙannenta ke mata. Dan haka tunda suka fito suke faman tsokanarta da faɗin, “Kai kai Aunty Deejoh wannan ai kece ma amaryar kawai gaskiya. Gaba ɗaya ai kinsa kwalliyar amaren ɓoyewa. Murmushi tai mai sanyi tana girgiza kanta, dan tasan dai tsokanace kawai. Inata ina amare da suka fito tamkar taurarin dake jikin wata ɗan daren sha bakwai. Mota guda suka ware mata wai ita kaɗai za’a ɗauka ai babbar ya uwa. Ita saima suka bata dariya. Haka dai ta shiga dan shima wanda zai ɗauketan duk ya wani rikice abokinsu ne. Ganin yanda yake wani rawar ƙafa yasata jan girma dan ita a yanzu kam duk maza haushi suke bata saboda kallon Dafeeq take musu. Duk yanda ya isheta da surutu bata tanka masa ba har suka iso inda za’ai dinner ɗin. Waje kam yay ƙyau sosai matuƙa. An masa docoretion irin ankon ƙawayen amarya da abokansu. Alhmdllh daga mijin Ni’ima har na Zuhrah matasan masu kuɗine kuma abokan juna tunda a dalilin saurayin Zuhrah shima na Ni’ima yaga Ni’imar ya maƙale, dan kowa naji da kansa, dan haka suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen shirya komai yanda zai ƙayatar. Yako ƙayatar ɗin.
Lokacin da za’a buɗe taro da addu’a mc ya shelanta ganin malama Khadijah Muhammad Kura babbar yayar amare. Ji Khadijah tai kamar ta fasa ihu, ganin bata da niyyar tashi Ni’ima ta tura mata saƙo a waya, cikin magiya take roƙon dan ALLAH taje. Ido ta ɗago ta kalla Ni’imar, sai taga duk sun ƙwaɓe fuska ita da Zuhrah kamar zasuyi kuka.. Dole ta daure ta miƙe zuwa inda ake buƙatarta ta amshi mp ɗin ta fara addu’a. Tsitt hall ɗin yay kawai ana saurare zazzaƙar muryarta mai fita da matuƙar sanyi da nutsuwa. Wadda ake iya ji harta waje kasancewar ƙofar dake a buɗe.
Tana kammalawa ta miƙa wani a cikin abokan ango yazo yana gwargwaɗa ma mc magana a kunne. Ita dai wucewa tai ta koma wajen zamanta. Yayinda mc ya fara shelar faɗin, “Masha ALLAH! Masha ALLAH!! Tofa jama’a sai mu sake gyara zama domin kuwa oga kwata-kwata, mai gayya da aiki ogan waɗan nan anguna guda biyu. Gwarzon matashin nan uban matasa ya iso wannan waje mai albarka tare da tawagarsa domin taya angunan biyun nan murna. Dan ALLAH a tafama bango goya marayu uban marasa uba, kai masu uban ma ubansu ne fa. Dan yarone amma mai zuciyar dattawa. Kai dan ALLAH ku bashi tafi”. Ji kake raff-raff!! Kowa ya zubama ƙofa ido da fatan son aga waye zai shigo. Duk da kuwa wasu a wajen sun san sunan wannan oga na anguna, wasu ma sun sanshi a fuska musamman abokansu da danginsu………✍️

Click Here To Cuta Ta Dau Cuta Chapter 26 Complete Novel

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA…🔊_

  _ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA  ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

         _1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

           _2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

              _3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

        _4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button