Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 39 Hausa Novel

Kuka ta sakar mishi mai sauti ya kawo idanu ya zuba mata yana mamaki a ƙasan ranshi, ganin ta ƙi fita ya sa bai bi ta kanta ba ya ɗauki maganin ya hadiye ya tura mata taje ta ɗauka ta mayar inda ta samu ta sake ja ta tsaya, Miƙewa yayi ya isa wurin Sallarshi ya tada sallah.Bayinshi ta shiga itama tayi Alwala ko kan ta fito ya idar da isha nafilfili yake yi itama ta fara nafilfilin sai uku da wani abu taji ta gaji shima yana zaune ne kanshi da yake jin kaman zai fashe jingine da jikin gado, Miƙewa tayi taje ta kwanta a inda ta kwanta da farko nan ƙasa tana kallonshi zuciyarta cike da tarin tsantsar tausayinshi tana kuma mamakin irin karfin halin da tayi har bacci ya sureta bata sani ba.Karfe biyar da rabi ya buɗe idanunshi ya miƙe yaje yayi alwala, har ya wuce ta kaman yayi fitanshi ya kyaleta sai ya tuna irin kulawar da ta bashi a daren na jiya da irin yadda tayi ta zubar da hawaye akan damuwarshi, ko da Abeeha ce ba zai barta ana sallah tana bacci ba, tsugunawa yayi don bashi da wani ƙarfin magana ya sa hannu ya ɗan ja hijab ɗinta firgigit tayi ta tashi tana kallonshi don baccin dama rabi da rabi ne inda bata saba ba, Miƙewa kawai yayi ya fice bai ce komai ba.Da sauri ta miƙe taje ta yi Alwala ta zo ta gabatar da sallah, bata tsaya doguwar Adu’a sossai ba ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf ta share ta saka turaren wuta kan ta fice zuwa babban kitchen, duk abincin da aka ci jiya a wurin makoki order ne daga manyan restuarants yau kuma a gidan za’a girka don haka tana bukatar ganin me zasu yi Dukda ba wasu mutane ne na waje ba kadan da suka Kwana duk na gida ne.Pepper soup ne na cowtail da bread sai tea da suke zubawa flasks flasks daga nan ta wuce wurin Abeeha ta samu idanunta biyu suka gaisa take tambayarta jikinta ko da Abeeha ta tambayi “Ya Yaya Rayyan?”Bata wani damu ba ta ce “Ya fita masallaci”Murmushi Abeehar tayi ɗan kaɗan Allah sarki ta je ta kulan dashi kenan.Shi kam daga masallaci mota ya ɗauka ya fice asibiti su jannah sai ganinshi suka yi, da sauri ta sauƙo ta zo ta riƙe shi zata fara kuka ya rabata da jikinshi ya ja hannunta zuwa bakin gadon ta zauna.”Menene na kukan? Uhmm? Lafiyar ki ya kamata ki yi focusing a kai mun riga mun yi rashi, haƙuri kuma ya zame mana dole ki bar kukan nan”Kai ta gyaɗa tana share hawayen dake silalo mata, bata jin tausayinsu kaman yadda take jin nashi don yana maganan ne kana jin yadda ɗaci dake shimfide bisa zuciyarshi ke hauro wa har kan harshen shi.Ya gaishe da matar uncle Mansur dake ɗakin ɗayar cousin ɗinsu ya gaishe shi ya amsa suna ƙara yi mishi gaisuwa.Sai da yaje wurin bills aka tabbatar mishi mijinta ya biya komai ya dawo ya nemi da su zo su koma gida tunda ta ji sauƙi, tattara wa suka yi ya ɗauko su har gida ya shiga ciki ya duba Abeeha a lokacin Afeefah bata nan, ko da zasu fara kuka ganin juna faɗa ya hau su dashi dole suka yi shiru ya gaisa da iyayen da suke ciki kan ya miƙe ya nufi sashensu har lokacin kuma kanshi kaman zai rabe amma juriyarshi ya hana shi kwanciya.A tsakiyar parlorn suka haɗu ta fito daga ɗakinta sanye da doguwar riga mai faɗi sai karamin hijab da ya shiga da kayan, ganin shi ya sa ta dake tare da danne tsoron ta ta furta”Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?”Da ɗan hanzari tayi maganan ganin zai wuceta.”Lafiya”Ya amsa kan ya wuce ya shige ɗaki, zama tayi don ta san kila yanzu wanka zai yi sai da ta ɗauki awa kan ta miƙe ta nufi dining ta haɗa mishi tean ta ɗauki bowl ta dibi pepper soup ɗin ta haɗa a karamin tray ta nufi ɗakin, ya yi wanka manyan kaya ne a jikinshi kaftan baƙar yadi mai taushi da ya sake fito da ainihin hasken fatar shi sannan ramarshi ma ya bayyana, a kan couch yake zaune yanzu ma yayi relaxing sossai idanunshi a rufe, waya ya gama yi da likitarshi bata nan ta samu labarin rasuwa hankalinta ya tashi roƙon shi take akan ya samu ya zubar da hawaye yayi leting damuwarshi fita ko kaɗan ne in ba haka zai iya samun matsala ya dai mata shiru ne amma bai san ko zai iya ba yana son yin shima ko zai samu sassauci amma taurin ranshi na dayawa, kuma hakan na da alaƙa da training da ya samu a farkon rayuwarshi.Shigowar ta bai sa ya buɗe idanu ba har ta ja ɗan table ta ajiye mishi tray ɗin ta tsuguna “Ya Saraki..!”Har ranshi ya ji sunan, bai san Meyasa duk ta kirashi hakan sai ya ji kaman an kirashi ba kuma dole zuciyarshi take motsawa ta wani ɓangaren kuma sai yaji kaman Mammi ce ta ƙira shi, dole ta sa ya buɗe idanu ya kalleta ta sauƙe nata ƙasa don ba zata iya jurar kallon cikin idanunshi ba ko a yana ƙalau ma bare yanzu da suke a birkice.”Ga abin kari nan na kawo maka, Don Allah ka ci ka samu ka sha magani.”Idan dutse ya tanka to ya tanka, jin shirun yayi yawa ta ɗaga ido ta kalleshi yana lumshe da idanun abin shi.”Don Allah dai ka ci Ya Saraki! Ko babu daaɗi ka lallaɓa ka ci ko kaɗan ne a yanzu ba mu da wani majingina bayan kai, ko da ni bana buƙatarka su Adda Abeeha suna da buƙatarka bare ma dukkanmu kaine bangon mu a yanzu ba za mu so ganin komai ya same ka ba a wannan gaɓar da bamu warke raunin tafiyar Mammi daga rayuwar mu ba..”Muryarta ya shiga rawa hawaye ya shiga silalo mata.Sunan Allah yake ƙira a hankali”Ya Allahu!”Kalaman sun dirar mishi da wani rauni da baya tunanin ya taɓa jin irin raunin zuciyarshi na rawa sossai, yadda ta furta cikin kuka ya sa yaji idanunshi kaman za su iya kawo ruwa muddin ta cigaba da irin waennan kalaman cikin sanyin murya da Salon karya zuciya.”Ki je zan ci!”Ya faɗa a hankali, bazata taji kalaman kuma hakan ya sakata jin daaɗi tunda ya yarda zai ci ta miƙe ta kawo mishi magungunan shi kusa kan ta fice sai da ta fita ya buɗe idanu ya zubawa kofan da ta rufe sama da seconds goma kan ya ɗauke ya mayar kan abincin, ya kuwa sha pepper soup ɗin mai yawa ya sha tean tare da magani ya ajiye ya miƙe ya koma kan gado ya kwanta don jiri yake gani a cikin maganin akwai na saka bacci ko da bai so ba dole baccin ya ɗauke shi dama ya saba ko da zai sha da daddare baya iya bacci amma in da rana ne yana yi ba tare da mugun mafarkin shi ba.****”Malam Labaran Haƙƙin uba zuwa ga ‘ya’yansa yana da matuƙar muhimmanci musamman a musulunce, wannan haƙƙi yana tattare da nauyin kulawa, tarbiya da tabbatar da rayuwa ta gari ga ‘ya’ya ciki sun haɗa da: Samar da halal ɗin haihuwa wannan ba sai na yi dogon jawabi ba na san ka fahimta ya kasance an samu wannan yaro ta hanyar aure kaman yadda addini ya tanadar.Alhakin samarwa yaro suna mai kyau da ma’ana wadda bai sabawa Addini ba.Ciyarwa da sutura uba na da nauyin ciyar da ‘ya’yansa da matansa daidai gwargwadon iko, hakanan da saya musu sutura da tufafi daidai gwargwado.Ga babban wato ilimi da tarbiya, koyar dasu abubuwan ibada sallah, azumi da sauransu. Samar musu da ilimin zamani da horo da zai sa su zama masu amfanar da kansu da al’umma.Ka ga tarbiya a kan hali ba karamin alfanu yake da shi ga yaranmu ba dole ne akanka ka basu horo a kan gaskiya, amana, girmama manya da kyakyawar mu’amala da mutane.Suna da alhaki akanka na basu kariya da tsaro hakan ya haɗa da hana su mu’amala da miyagun abokai ko dabi’u kaman su shaye-shaye, fasikanci da sauran su. Malam Labaran uba kan zama abin koyi ga ɗa wajen addini, hali da mu’amala ina so ka yi nazari a iya tunanin ka matsayinka na uba kuma miji me ka sauƙe a cikin waennan?”Inna Larai ta numfashi “Wallahi malam liman ina ga bayan hakkin farko na samar da su ta hanyar aure babu abin da Malam Labaran ya sauƙe ciki ko haihuwa aka yi mutumin nan baya ragon suna.”Inna Asabe da kanta ke ƙasa tace “Mun samu tawaya sossai saboda rashin ilimi da rashin sani gashi mun lalata rayuwar ‘ya’yanmu”Malam Labaran yayi shiru jikinshi a sanyaye kenan shi fa Allah zai kama da laifi? A hankali yace “Toh malam liman wani hanya za mu bi mu gyara abin da muka ɓata tun farko? Hakikanin gaskiya ina samun abin da zan iya rufawa kaina asiri da gidana amma son zuciyata ya sa nake kyashin sayowa in kawo, kowa ta kanshi yake kaman rayuwar bariki hatta sutura wannan na manta rabon da in saya ma kowa a gidan, Dukda ina kallonsu da suturu da ma wasu ababen ƙawa amma ban taɓa tambayar ina suka samu ba sai ma fata nake in ga nasu in kwace ko in sace…kaico kaico da wannan rayuwar jahilcin”Hawaye ne ya zubo mishi don sai a yanzu yake fahimtar irin illar da jahilci yake dashi, ga yaran duk sun lalace ya tabbatar babu mai auren su a tunaninsu Afeefah ce ba zata auru ba saboda yadda tayi tambari a garin sai gashi ta auri wanda kaf kauyen basu da kamarsa, haƙiƙa yayi matukar nadamar abubuwan da yayi tayi a baya na tsantsar rashin ilimi.”Hanya ɗaya ne jal kuna raye lokaci bai ƙure ba, ayi Adu’a a nemi yafiyar waenda aka zalunta babban hanyar shine a nemi sani akan addini.”Nasiha ya cigaba da yi musu mai ratsa jiki sai gashi duk jikinsu yayi wani irin sanyi, inna Larai dake fama da azabar kafa kawai ta kama kuka, lallai Allah mai girma ne kuma baya abu kan kuskure hassada da bakin ciki akan rayuwar Afeefah ya ja ta jefa kanta da kanta ga halaka.Anan aka saka kawu Labaran mayar dasu dakunansu, inda ya nemi zai dinga zuwa daukar karatu masallacin da malam liman ke koyawa kowani bayan Magrib haka zai yi kokari ya ga ya sauke duk wani hakkinshi amma bai san inda zai ga Afeefah ba.”Za ta zo ne! Dole zata neme ku don ku ne dolenta”Kanshi ya duƙar ba tare da ya yarda da zata zo ɗin ba don su kaɗai suka san irin cutarwan da suka yi mata.****Samha ce zaune da Abeeha bayan Magrib tana ɗan janta da hira yayinda jannah ke kwance akan gado idanunta a lumshe Afeefah tayi sallama ta shigo ɗakin.Idanu suka hada da Samha, sai tayi kaman bata santa ba ta ɗauke kai ta nufi wurin jannah “Addah jannah sannu, ya jikin? Akwai abin da kike bukata ne?”Ta girgiza kai”Babu, bacci ma zan yi yanzu ki huta da zirga-zirgan nan haka please tun safe kece nan ke ce chan baki huta ba”Afeefah ta ɗan murmusa kadan Dukda ta gajin iya gajiya rabon da tayi irin wannan wahalar ma tun Dutsen-wai, ita ce kitchen ita ce kaiwa mutane abinci da sauran dai duk wani zirga-zirga da za’a rike mutum a gida a yayin hidima ko ta aure ko ta mutuwa.”Shikenan Addah jannah, Allah ya kara sauƙi… Adda Abee Allah ya bamu alkhairi wanka zan yi na kwanta””A huta gajiya Afeefah sannu”Tayi murmushi kawai ta juya ta fita.Samha da ta zuba mata idanu tun shigowarta gabanta na wani irin faɗuwa tana sake kallon irin sauyawar da tayi da kyaun da tayi ga kamshi kaman wacce ta tsumu ta tashi cikin arziki ta miƙe tsaye tana kallon Abeeha”A..Abeeha wanchan ba Afeefah ba?””Kin santa ne?”Abeeha tayi tambayar kaman bata san labarin komai ba.”Afeefah Afeefah…!”Sai ta rasa wani kwatance zata yi da Abeeha zata gane “Afeefah dai wacce ta fito daga wani kauye wai shi Dutsen-wai?”Abeeha tace “kila kama dai, wannan Afeefar kaman sister take a wurin mu kuma ita ce matar Yaya Rayyan”Wani irin kallo Samha ke mata zuciyarta na bugawa da ƙarfi ko a mafarki ta ganta zata gane ta, Afeefah ce ta koma haka? Wait Afeefah ce take auren Rayyan? Rayyan fa! Kwakwalwarta ya kasa ɗaukar wannan zance za ta yi magana Sameera ta shigo “Samha mu tafi tun dazu Yaya Saleem ke faɗan mun ajiye shi”Bata tsaya jiranta ba ta fice, Abeeha tace “Ki je kar yayi faɗa, mun gode sossai fah sai da safe”Ta ɗauki Jakarta ta fice zuciyarta fal mamaki da saƙe-sake to ko bata gane Afeefar bane? Kai dole in sun zo gobe ta nunawa mommy da su Sameera ita ko ita ce bata gani da kyau ba haka ta danne maganan ta kasa yi da kowa har suka bar gidan zuwa gidansu akan gobe ma zasu shigo.Ita kam Afeefah ko tsayawa tunaninsu bata yi ba dama damuwarta Saleem ne kuma fahimtar ya dawo daidai hankalinta ya kwanta don haka bata da wani issue da su, wanka tayi ta nemi cotton peach kayan bacci riga da wando dogo ta saka sai da tayi isha ta yi shafa’i da wutiri ta miƙe ta kashe komai na ɗakin ta ɗauki wayanta ta fito gabanta na faɗuwa, rabon da su hadu tun safe da ta bashi abin kari don da rana yana parlorn waje da su Saleem so a chan aka kai musu abinci basu haɗu ba, bata san ma ko ya ci ko bai ci ba haka dai ta nufi ɗakin tayi knocking tare da tura kofa ta shiga, kallon wurin yayi sai suka haɗa idanu yana zaune akan gadon kafafunshi biyu na cikin bargo bayanshi na jingine da pillow ramarshi ya sake fita ainun.Ɗauke kai yayi chan ƙasan ranshi yana mamakin yadda a yanzu take shigo mishi ɗaki don tsabar neman magana ya kore ta kuma ta mishi kuka bai sani ba ko tare aka gina musu ɗakin ne oho, abin da ke damunshi ya dameshi don haka bai kula ta ba har ta ɗauko bargo ta shimfida inda ta shimfida jiya taje ta ɗauko pillow ta zo ta ajiye sai ta matsa kusa dashi “Ya Saraki sannu! Ya jikin? Kana bukatar wani abu ne?”Ya buɗe ido ya kalleta ta ɗauke kai kaman ba zai amsa ba sai taji ya ce “Da sauƙi”Daga haka bai sake magana ba taje ta ɗauko ruwa ta zo ta ajiye a bedside ko zai buƙata, wayanshi ta gani a kan couch taje ta ɗauko tazo ta ajiye mishi gefen ruwan kan taje ta kashe wutan ta zo ta kwanta ta bar shi da mamakin ƙarfin hali irin nata…

Back to top button